Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Copied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen2⃣) WHATSAPP NO: +2347039625239 ☘☘ ☘ AURE IBADA NE FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.☘ TRUE LIFE STORY MMN USWAN ABIN LURA Yana da kyau mu kula mu gane cewa munufar yin rubutu ko karatun kanshi ba wai don nishadi bane kawai ko rage lokaci, a'a, muna yine don fahimtarwa da wa'azantarwa ta hanyar nishadantawa don muyi gyara kan kurakiran da muke aikatawa. Misalin a lokutan da yawa mukan dauki aure wani abin da ake yin shine don a samu dadi a cikin shi, in dai ba kuskuren fahimta nayi ba wannan shine burin yawancin mata har ma da wasu mazan akan aurarrakinsu, har ma auren da yawa kan kasa kai kabari a dalilin an kasa samun abin da za'ayi zaton samu tun farko. Don haka naga bari mu tunatar da juna don mu kara fahimtar menene AURE? Farko dai dukanmu mun sani mu kuma yarda cewa, shi aure IBADA NE, haka nan mun yarda shi aure raya sunna ne na manzo rahma ( S.A.W.) daga yin shine kuma zamu mallaki rabin addininmu, ma'ana duk kokarinka akan aiyukan ibada matukar baka da aure, to ladanka rabin na mai aure ne. Ina gani daga wannan kawai ya'isa mu fahimci cewar, akwai wani babban al'amari mai wahala gaske a cikin shi. Kamar misali biyayya mai karfi da aka sanya tsakanin mu da mazajenmu, mafi yawancin mazajen namu bass mu'amala damu irin mu'amalar da za ta sanya muji saukin yi musu wannan biyayyar, domin basa bamu 'yancin da shari'a ta bamu, basa yi mana adalci da manzon rahma yayi musu wasiyya da suyi mana SBA tsabar son zuciya irin tasu da sonkai. Muna mata munada namu komisino din Allah ya ganar damu amin. JINJINA Ga dukkan wani wanda Allah ya jarabta ya kuma yi hakuri da jarabawar da Allah yayi masa, hakuri kyau. SADAUKARWA Sadaukarwa wannan littafi ta tabbata ga dukkan matan da suke aure suke kuma hakuri da abinda Allah ya kaddara musu a gidajen mazansu, Allah ya kara mana hakuri da kuma jin tsoronsa Amin. GAISUWA MAI TARIN YAWA GAREKI HJY ZABBA'U BUKUR PARCK JOS PLATAEA STATE Bazan mance dake ba uwar daki ta gari Allah ya kara girma da daukaka yaiwa dukiya albarka amin 0⃣1⃣ "Zauna take cikin dankararriyar parlour wanda yasha kayan alatu a jin dadin rayuwa' tasha kyau har tagaji cikin foguwar rigar shadda wanda yasha aikin sama mai ruwan kore. "Bini saeta kalli window dan ta kagu taga mijinta ya shigo' da taji shiru mikewa tai taje gidin window ta yaye labulaiyar da yake jikin bango ta tsaya shiru batafi mintuna da tsayuwa ba saega shigowar sa da sauri taje ta yanayin parking ta bude masa mirfin mota. "Yana fita da rungumesa hade da yi masa sannu da xuwa. "Murmushi yai hade da cewa yauwa Aisha ta'ya gida?". "Tace alhamdllh. "Suna tafe tana gaba yana biye da'ita suka shiga ciki kai tsaye dakinta suka shiga tana ije handbag dinsa ta shige toilet ta hada masa ruwan wanka snn tafito bedroom ta sameshi zaune a bakin gado. "Dukawa tai ta tana tayashi cire takalmin kafarsa shima hannu yasa yana cire botir din wiyar riganshi. "Mikewa tai ta dauko masa towel ta mike masa ya yana daurawa yashiga wanka kafin yafito taje kitchen ta kwanso abinci takai masa dinning ta jere masa. "Yana fitowa jallabiyarsa yasa yafito parlour gani bata gun dinning ya nufa kai tsaye daga ido da zatayi taga yana xuwa da sauri ta saki abinda takeyi taje ta gyara masa kujera ya zauna hade da cewa har ka fito. "Murmushi yai hade da cewa nafito Aisha ta sannu da aiki' kedae baki gajiya da yimin hidima. "Murmushi kawai tai masa plate ta dauko tafara xuba masa abinci' gani hannunta na rawa sbd nawin plate din da sauri ya tanlafo hade da yimata dariya yana fadin kinga abinda nake fadi ko? "Tace na mefa Yallabai?" Yace na rashin cikin abinci mana. "Murmushi Aisha tai hade da cewa to ai bacin abinci be kesa kiba ba' gaba daya hannayesa ya hada ya tablafo habansa dashi ya xuba mata ido ko kibtawa ba yayi yace to menene?". "Tace nifa haka Allah yayini... Da sauri ya tareta da cewa ai banace ba haka Allah yayi kiba nima kaina nafi sonki a haka kodan naji dadin sarrafaki yadda nakeso. "Da sauri tasa hannu ta rufe fuskanta sbd kunya. "Jawo plate din abinci yayi ya fara ci hade da cewa xubamin ruwa. "Daukar jug din ruwan tai ta xuba masa yanaci suna hira har yagama snn ya mike hade da cewa biyoni inada mgn dake. "To kawai tace tamike ta bishi tana gaba yana baya suka shige dakin ta. "Bakin gado ya zauna' gani ta tsaya a tsaye jingine da bango yasashi cewa ki zauna mana. "Snn ta samu gu ta zauna a kasa hade da nade kafa tana fuskantarsa saeda yasake kallonta snn yace Aisha. "Tace na'am. "Yace da farko dae nasan ke me hakuri ne kuma mai biyayya wanda bata bujirewa umarni maigidanta ko ba haka ne ba?". "Yana mgnr ne hade da dago fuskanta. "Murmushi kawai tai masa. "Snn yaci gaba da cewa shiyasa duk cikin matana nake alfahari dake' sbd kedin ta dabance. "Aisha dake zaune taji kanta yakara girma sbd yadda maigidanta yake yabonta. "Yaci daga da cewa Hauwa ce ta kirani tace tana hanya dawowa daga tafiya kuma kinga be kamata ta dawo bata sameni a gidan ta bako?". "Shiru Aisha tai bata tanka ba. "Yace kinga daganan idan na fita gidan ta zan wuce sbd na riga na sallami Fatima kece kawai be sanarwa ba shiyasa nazo na sanar dake' sbd gudun musake irin wancen karo. "Wasu kwallane suka cika mata ido kafin ta ankara sun xubo. "Da sauri Nasir yace subbuhanallah Aisha menene kuma haka meye abin kuka kuma?" Hannu yasa ya dagota ya dorata akan cinyarsa yana share mata hawaye snn yace dan Allah banaso na sake gani hawaye sun xubo akan kyankyawar fuskanki kina jina ko. "Kai kawai ta daga masa. "Snn yaci gaba da cewa wlh Aisha ba lalla bane kisan irin sonda nake maki bazan mance farkon ganina dake ba' tun daga lokacin Allah ya jarabcemi da sonki. "Idan zan zauna ina jero maki irin sonda nake maki da kuma yadda nakeji a cikin zuciyata idan naganki cikin bacin rai ba lallane ki amince ba daga karkema zakice karya nake maki ko kuma kice dadin ba amma wlh Aisha ina matukar sonki. "Murmushi tai hade da cewa nagode. "Nasir yace kukan yakare ko yan'mata na?". "Murmushi tai hade da boye fuska cikin jikinshi. "Mikewa alhji Nasir yai hade da daukarta cak kamar jinjira ya juya ya shinfidata a gado snn ya cire jallabiyarsa hayewa kan gadon yai hade da cewa bari naiwa yan'mata na tausa. "Tsanle Aisha tai tana fadin nashiga uku' da sauri Nasir ya cabkota ya maidata karkashinsa Aisha tace dan Allah Yallabai kabari. "Da haka yaci gaba da janta da wasa har yasamu ya biya bukatar sa snn suka tashi yana rike da'ita suka shiga toilet sukai wanka yaxo ya shirya yatafi gidan Hauwa sbd kada ta iso baya gida. "Duk da tana shakkansa amma kuma yafi kowa sani halinta batada mutunci' mafi yawancin har gara yaiwa Aisha da Fatima zasu dauke amma ba Hauwa ba. "Nasir yana fita Aisha taje ta kwashe kayan abinci dayaci takai kitchen. "Ko kafin alhji Nasir ya'isa har Hauwa tarigashi iya gidan yana parking yashiga daga cikin gidan' wani irin kallo tai masa snn tace sae yanxu kaga damar xuwa ka taroni?". "Murmushi yai hade da cewa sannu da zuwa malam Hauwa. "Karisawa yai gun da take zaune ya rungumeta yana fadin kinsha hanya. 📖🖊 🍀🍀 🍀 AURE IBADA NE FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.🍀 MMN USWAN 0⃣2⃣ "Murmushi itama tai masa hade da cewa haba alhji sbd Allah ka kyauta kenan?" Tun kafin na isa na kiraka na sanar dakai ina hanya a tunanin kafin na'iso zakazo nan kajirani ne ashe ba haka bane. "Yanx sbd Allah ka kyauta kenan? murmushi alhji yai snn yace amma kinsan kafin nazo sae naje na sallami yan'uwanki ko?". "Hauwa tace ina xuwana dasu wann matsalar kace ba tawa bace idan ni babu ruwana dasu' amma kasan tunda ba dadewa zanyi ba anan har nakoma ko?" Tunda kaga ba dade zanyi ba nan da jibi zantafi. "Alhji yace Hauwa kenan dadina dake son kai babu ruwanki da damuwar wani taki kawai kika sani. "Murmushi ita tai kasa snn suka gaisa hade da hiran yaushe gamo. "Hauwa ita matar alhji Nasir ta biyu a da' gun cikinsu daya kafin ya aureta amma bayan sunyi aure tabar aikin ta koma international business xuwa kasashen larabawa dana turawa tana saro kaya shiyasa ita kanta batada lokacin kanta banle na wani. "Ita da maigidanta sae sukai wata 2-4 basu hadu ba tun alhji yana korafi har yagaji ya hakuri sbd babu yadda zaiyi da'ita. "Bayan sunyi sallar isha'i yafita yaje family kitchen ya siyo masu abinda zasuci sbd yasan koda yai mata mgn cewa zatayi tagaji baxata iya shiga kitchen ba'maje fada banxa banle sarki yai sako ba daga tafiya take ba bata shiga kitchen sae tayi ra'ayi banle yau da ta dibo gajiyar hanya. "Shikuma alhji Nasir a rayuwarsa babu abinda ya tsana a rayuwarsa kamar yaje siyo abinci a kanti a cewarsa da girman sa da mutuncinsa bayan haka gashi da mata har uku amma ace yana siyan abinci a waje?". "Wancan karo da taxo Aisha yasa tai masu girki akabawa draver ya kawo masu gidan Hauwa' Hauwa batasan daga ina ne abinci yake ba saeda takare ci snn take tambayar Nasir. "Nasir yace daga gidan Aisha ne'Hauwa tace wata Aisha kuma?". "Yace Aisha amaryata a take ta haushi da fadi inda take shiga banan take fita ba'tsayawa yai yai shiru yana kallonta mmki ita kanta Aisha bataso girka wanga abincin ba sanadiyar takura mata da yai akan girkin harda kuka saeda ta amma besa taki yiba sbd son da take masa da kuma shakkansa. "Amma a wanga karo na kanti kawai ya siyo sukaci bayan sun gama cine sukai wanka suka kwanta duk yadda Nasir yakai ga sha'awar Hauwa amma haka ya hakura da haka har saeda yai kwana biyu a gidan ta kwananta biyu snn ta shirya kayanta xatabar gari ta koma gun harkokinta. "Tunda Nasir yabar gidan Aisha batada lfy a tunaninta da safe zaizo gani kwanansu ne kamar yadda yasaba idan har ba gidanka ya kwana ba da safe kafin yatafi aiki sae yaxo gani kwananka snn yakarisa gun aiki. "Amma idan Hauwa na gari baya iya yin hakan sbd Hauwa gogaigiyar yar'barikine wanda tasan duniya duniya ya santa duk wata hanya ta kisisina ta dade da saninsu dan ma Allah yasa tana shakkan Nasir ne yasa take rage wani abu. "Sbd idan tabari ransa ya baci abin baya masu kyau. "Dan Nasir mutum ne mai taurin kai da fushi ga kuma nuna isa' shiyasa baya daukar rainin wayo duk matanshi susan da haka. "Duk da zazzabin dake damuji haka lallaba da shiga makwabtanta gidan mmn juwairiya ta aiketa siyo mata danyan kubowa sbd tun da Nasir yabar gidanta takejin cin miyar kubuwa danya. "Taso inda Nasir yaxo da safe ne sae ta sanar dashi idan yaxo koda balyaminu ne yaron aikinsa sae yabashi ya siyo mata sbd ya hanata fita ko'ina gashi kwanarsa biyu be leko ba hakan yasa taje ta nimi yar'aike. "Kafin ta dawo daga makwabta Nasir ya shigo gani bata parlour yasashi shiga har bedroom nimanta ninma be ganta ba sae yaleka toilet ko tana ciki nan ma batanan parlour ya koma ya zauna yana tunanin ina taje sbd a iya sanisa yasan bata da kowa a garin kuma batasan wani ba toma yaya za'ayi tasan wasu sbd tunda aka kawota garin babu inda ta taba zuwa kuma babu wanda yake shiga mata sbd Nasir yariga ya hanata hulda da kowa. "Suma kansu yan'uguwa gani suke tafi karfinsu sbd babu mai kudin mijinta a uguwarsu shiyasa suke tsoro shiga gidan. "Haka ya zauna yana faman tunani ire-iren haka yasa juyi da key din motar dake yatsarsa kamar daga sama yaji sallamarta tana shigowa parlour suka hada ido da sauri ta sunkuyar da kanta kasa hade da komawa da baya tai shiru. "Mikewa yai yaxo inda take tsaye ya xuba masa ido batare da yai mata mgn ba'gani irin kallon da yake mata ne yasa tafara hawaye. "Da sauri ya daka mata tsawa yana cewa wlh idan baki daena min kuka ba saena yimaki abinda baki taba zato ba. "Aisha najin haka da sauri ta goge hawayen'Snn yace ina kikaje?". "Nan tafara inda inda' Nasir yace badake nakeyi ba?". "Wasu hawayen ne suka sake zubowa tace gidan su mmn juwairiya naje. "Yana me kikaje yi a gidan?" Dama kinsaba fita kenan idan bani... "Da sauri tace a'a yau ne kawai shidinma sbd juwairiya naje na aika ta siyomin kubewa danya. "Nasir yace ina Bilyaminu? Tana tunda katafi be shigo gidan ba dama idan bakanan becika xuwa ba sae in kana nan. "Yace to meyasa baki kirashi a waya ba'yazo ya siye maki?". "Shiru tai taci gaba da kwalla. "Nasir yace banace bana son gani wanga hawayen na rashin dalili ba. "Da sauri tasake kamo bakin hijab dinta ta goge hawayen. "Snn yacigaba da cewa amma kinsan hukunci matar da tafita bada izinin mijinta ko aisha tunda lokacin da kika fita har dawowarki kinsan ubangiji yana tsine maki kuwa?". "Shiru tai. "Idan yanxu ban yafe maki ba haka ubangiji zaici gaba da tsine maki tunda bada izinina kika fita ba. "Dukawa tai har kasa tace dan Allah kayi hakuri in Allah ya yarda hakan bazai sake faruwa ba. "Yace na yafe maki tashi kije ki dauko min abinci. "Shiru tai takasa ce masa komai. "Yace da kefa nakeyi. "Snn tace ban dafa komai ba. "Matsawa yai dab da'ita hade da rike mata hijabin dake biye da'ita yace yaushe rabonki da girki. "Tana hawaye tace yau ne kawai'shidinma sbd banajin cin komai ne sae tuwo kuma bansamu mai siyomin kubewa ba shiyasa.... "Cikin tsawa ya dakatar da'ita hada da haushi ya yaye mata hijab din dake wiyarta. "Fisgota yai xuwa bedroom gaban miroow ya tsaidata yasa hannu ya cire mata rigar dake wiyarta hade da cewa nasha gaya maki banaso ganiki da wanga zulubbuwar riganga. "Tanage da'ita sae pan gashi ko bra bata dashi yaka kanta yai dab da mirror din yace dubeki fa dan Allah aisha' Aisha meyasa kikeson jawomin zagi ne?". "Sbd Allah yanxu idan yan'uwanki sukazo suka ganki haka me kike gani zasuce?" Ba sae suga kamar ina cutar dakece ba. "Ita dae tana tsaye kanta na kasa babu abinda takeyi sae kuka. "Nasir yaci gaba da cewa idan bakici dan kanki ba ai kyaci dan d'an dake cikinki sbd Allah waye zaiganki yace kinada ciki har na wata uku' dubi yanda kika koma fa. "Wlh Aisha duk irin son da nake maki idan har kikeyi sanadiyar cikinga ya samu matsala daga har ke ina me tabbatar maki ranmu zai baci a gidan nan. "Sake fashewa tai da wani kuka snn taci gaba da cewa tun ranar da kabar gidan nan banida lfy ko bcc banayi kuma bana iya cin komai koda naci baya zama. "Gani irin kukan da takeyi ne yasashi kamota ya rungume yana fadin ya'isa haka daena kuka haka Aisha towel din dake gefen gado ya jawo ya daura mata snn ya kamata ta kwanta sallamar juwairiya ne ya katseshi mikewa yai yaje ya amso kubewar ya'ije mata a kitchen. 📚✍🏻 ☘☘ ☘ AURE IBADA NE FASAHA ONLINE WRITES☘ MMN USWAN 0⃣3⃣ "Yana eje kubewar komawa yai dakin ya samu bakin gado ya zauna snn yace ni dae aisha zantafi. "Aisha dake kwance ta tashi zaune snn tace katafi ina?". "Nasir yace g'idan Fatima mana. "Aisha tace g'idan Fatima komawa? 'Haba Yallabai meyasa kakemin h'aka sbd Allah' Idan ba mantuwa nai ba ranar da Hauwa tazo nice fa da girki amma h'aka ka tsanleke kaje g'idan ta ban nuna damuwata ba sbd nasan ba'a tare kukeba na barka katafi g'idan ta har kwana biyu yanxu da yakamata ace ka nan shine zakaje g'idan Fatima kuma bayan nan yakamata ka dawo. "Gaskiya Yallabai bazan boye maka zan'iya hakuri akan komai amma banda irin wanga abubuwan' sbd Allah kodan kaga ni banida kowa ne a garin nan sae kai yasa kakemin h'aka Aisha tana mgnr ne da fashewa da kuka 😭. "murmushi kawai Nasir yai ha'de da jawota jikinshi yana lallashinta yana cewa to ya'isa h'aka Aisha ta Idan banda abinki ni banga abin kuka ba 'k'uma mgnr kice bakida kowa a garin nan sae ni' naji dadin h'aka amma k'uma kada ki mance kinada Allah da manzonsa ga k'uma to ai kece mai gata gaki da Allah da manzonsa ga k'uma ni mijinki da h'aka ke kikafi kowa gata dan h'aka ki dai na damu kanki "Shiru Aisha tai tana sauraransa har ya kare' snn yace dan h'aka banaso ki sake irin wanga tunanin kina jina ko? " " ni zanfita zanje na duba kwana su Fatima da yara na dawo'dan Allah kada ki shiga ciki sbd bilyaminu zai kawo sako kada yanxu yai ta sallama kina ciki. "Aisha tace amma dan Allah kada ka dake ' Nasir in sha Allah. "mikewa tai h''ade da cewa me kakeso ci na dafa maka kafin ka dawo? "murmushi yai h'ade da jawota yace yan'mata na duk abinda kika dafa inaso. "murmushi tai snn tace Yallabai kenan. "Yan'mata fa kace. "Yace Eh mana amma tawa ba! Ba tani Ba. "murmushi cikin shagwaba tace da!'kenan. "kallanta yai snn yace yanxu fa?". "sai da ta kwalkwale da dariya snn gave na girma. "murmushi yai h'ade da cewa Aisha ta kenan ni zantafi sai na dawo. "Aisha tace to sai ka dawo. "alh Nasir yace bako rakiya? " "murmushi tai snn suka jera tare'har bakin kofar parlour ta rakashi ya tafi. '"Kai tsaye kitcher ta shiga ta fara aikin abinci' tana cikin aikin kenan ta jiyo sallamr bilyaminu a parlour da sauri ta saki aikin da takeyi taje gun bilyaminu. "Bayan sun gaisa bilyaminu yace alh ne yace na kawo sako. "gun Aisha ta nuna masa ya'ije kayan' har yajuya zaifita sai Aisha tace bilyaminu katsaya kaci abinci mana. "Yace wlh Aisha sauri nakeyi' Aisha tace to bari na zuba maka katafi dashi. "Da sauri ta shiga kitcher ta zuba masa a foodplast ta kawo masa. "amsa yai h'ade da godiya ya tafi' Bayan fitarsa ne Aisha tayi kokarin daukar kwalayen da bilyaminu ya shigo dashi amma ta kasa sbd sunyi nawi da yawa. "H'aka ta barsu a gun ta koma kitcher taci gaba da aikin ta' tana karewa ta kwashi abincin ta kai dinning ta jere masa snn ta shiga wanka. "Tana fitowa daga wanka ta dindisa kwalliyarta cikin riga da sket ta koma parlour ta zauna zaman jiran alh ya dawo. "Shiru Shiru tun tana kokarin dinne bacin rai har sai da ya kamata' ita kadae take zaune kallon TV ma ya gagara kashewa tai ta shige dakinta kan gado ta fadi tana koka. "Gani har magrib yayi Yallabai be dawo ba yasa Aisha ta mike ta shiga toilet tai alwala tazo ta fara sallah' sai da tai magrib da isha'i snn ta dauki wayarta ta kira alh'Yai ringing har three miss call amma be daga ba h'akan yasa ta hakura da kiran taje ta rufe kofar parlour snn ta dawo ta tube tasa rigan bcc ta kwanta. "har bcc ya fara daukarta sai taji wayarta yana ringing, koda ta duba number Nasir tagani tana dagawa yace xo ki b'ude min kofa. "Sauka tai daga kan gadon taje ta b'ude masa h'ade da amsar ledan daya shigo dashi snn tace sannu da zuwa shige wayarta tai batare da ta tsaya jiran sa ba. "Shiko tsayawa yai ya rufe g'idan snn ya kariso parlour' ko kafin yazo ta'ije masa ledarsa ta shige dakinta ta kwanta. "kai kawai ya kada snn ya bita cikin dakin' koda ya shiga ganinta yai kwance ta kama bakin aiki wato kuka. "Karisawa yai bakin gadon ya zauna snn yace Aisha. "banxa tai dashi taci gaba da kukanta. "Nasir yace da kefa nakeyi k'uma nasan kina jina. "Snn tace na'am. "Yace tashi inaso muyi mgn dake. "A hankali taja ta zauna kamar bazata tashi ba' Bayan ta zauna ne ya kalleta snn yace inaso kisa hannu ki goge hawayen nan da suke xubowa na rashin dalili ko k'uma yanxu kiyi me dalili. "Aisha najin h'aka da sauri tasa hannu ta goge hawayen tass' Snn yace tashi ki mayar da kayan da kika cire' A sanyaye ta sauka ta dauko kayan har zatasa sai yace a'a kananu nakeso kisa min ba wanga Ba. "Meda kayan tai ta dauko english wear tasa riga ce wanda bata wuce iya cinyaba sai karamar wandonta itama bata kai cinyaba ba. "Bayan ta gama sawane ya juyo sai da ya kare mata kallon snn yace saura kwalliya. "H'aka ta dauki kayan tai' duk tana yine tana hawaye har tagama. "Nasir yace banace banason gani kwalla suna xubowa daga idan ki ba. "Hannu tasa ta share h'ade da cewa ba kuka nakeyi ba. "Sai da ya kare mata kallon snn yace yauwa ko kefa' tsayawa tai kanta na kasa 'yace jeki ki dauko min abinci na. "fita tai taje parlour ta kwaso masa abincin sa yanaci yana hira yace ta dauko ledan daya shigo dashi. "mikewa tai taje ta dauko ta kawo masa' yace ta zauna ta b'ude ledan tana budewa kayane ta gani kananu masu kyaun da tsada kala

Chapter 1 of 38