Share this page
ya fara da cewa yanxu tunda har ta amince tana sonka to ba kullum zaka rika zuwa g'idan su ba? Da sauri zahradee yace meyasa abba? Alhj yace zuwa tadi kullum yakansa mace taji ta tsaneka' k'uma koda ba h'aka ba idan kuna bawa juna iska duk lokacin da kuka h'adu zakuji kunfi marmarin juna. "amma idan kana zuwa gunta kullum tun kana f'adi mata Gaskiya wataran karya zakayi kaga daganan ma zaisa raini ya shiga tsakaniku. "idan k'uma kabari raini ya shiga tsakanika da mace ko wlh koda aurenta kai bazakaji dadin zama da'ita ba. "ni k'uma son bazanso ka auri matar da zata rainaka ba banle harmu da muka haifeka taga girmanmu. "zahradee yace h'akane abba. "alhj Kailani yaci gaba da cewa abu na biyu k'uma dan Allah zahradee kada kabari shedan ya rinjayeka ku aikata abinda zaizubar mana da mutunci da k'uma darajar g'idan nan' duk da nasan ba aikinku bane daga kai har yayyanka amma tuni yanada kyau ko? "murmushi zahradee yai. "Alhj Kailani yace koma menene son kayi kahuri idan akai auren zakuyi. "Da sauri zahradee yace ehhhh abba' ya karisa mgnr ne h'ade da bude ido😳 sbd mmkin mgnr. "Alhj yace son da alama har yanxu kuruciya na tare dakai' sbd gani nayi kanka na rawa' gara na dungayi ina yimaka girgadi sbd kada kaje ka jawomin na barin gari. "murmushi zahradee yai h'ade da susa kai. "mikewa abba yai h'ade da cewa son ni zani na kwanta. "Aisha na shiga cikin g'ida dakinsu kawai ta nufa taje ta tube snn ta kwanta' amma ba bcc takeyi ba' mgnr zahradee ne yake mata yawo a kwakwalwarta' tana f'adin ashe dama duk zuwan da yakeyi gun abbana sona yakeyi shine abba be taba sanar dani ba sai yanxu? "meyasa abba yake h'aka? Meyasa abba yake hanani tsayuwa da samari? ga kawayena wanda na girma da wanda suka girmeni abba su iyayyansu basu hanasu tsayuwa da samari sae ni? "kodae auren dolene yakeso yai min? Kodae yariga ya bawa wani nine bansaniba? "kai ina' inda h'akane da bazai bari na fita gun zahradee ba' sbd kafin yasan waye zahradee na rigashi sani zahradee sbd muyi school daya dashi' To dama shi zahradee tun ina yar'karamata yake sona komai? "ba tare da tabawa kanta amsa ba bcc ya dauketa. "washe gari kuwa gun yadda zahradee yaso zuwa gun Aisha dole ya hakura sbd mgnr da abbansa yai masa' washe gari kuwa a masallacin kofar g'idan su Aisha yai sallar isha. "koda aka idar saeda yadan tsaya saeda yaga takwas yayi dobt snn yai sallama cikin dauren g'idan' abdul ne ya amsa umma tace kamar muryar zahradee amma jeka ka leka kaga waye. "kada abdul ya leka zahradee ne ya gani bayan sun gaisa ne ya dawo ciki ya sanarw umma' umma tace tashi kije.... "Da sauri abba yace taje ina? Idan zamanki take a g'idan to taje' jin hakan yasa umma mikewa ta shiga d'akin' kusa dashi ta zauna h'ade da sa hannu ta dafe masa kafada snn tace maigidana dan Allah kayi hakuri' abinda yasa nace h'aka gani nai anriga an zama daya shiyasa. "yace kekika daura masu aure? "a'a. "To kince anzama daya? "dan Allah kayi hakuri nayi kuskure amma insha Allahu bazan karaba' Allah ya huci zuciyar angon Hafsatu. "shima kansa besan lokacin da dariya ta subto masa ba' snn yace jeki kice taje amma koda ta dade dan inaso na rufe g'ida na kwanta. "To tace h'ade da mikewa. "hujab kawai ta sanya batare data tsaya kwallyaba da nufi kofar g'ida abdul na biye da'ita suka tafi gun zahradee. "Da sallama suka isa gun ita da handbag d'inta' shima zahradee dake tsaya da fara'arsa ya amsa h'ade da karisowa gun data tsaya ita da abdul. "rike wa abdul hannu yai snn yake my little bro da kake? Abdul yace lfy klau' zahradee yace yah school kana kokari kuwa? Abdul yace sosae ma' zahradee yace okey yanxu fadi min yau me aka koya maku a school din? "abdul yace umh"uhm" uhm" yauwa' kasan yau wenesday ne ko? Zahradee yace eh! Snn abdul yace to dama duk ranar wenesday Englash language mukeyi. "zahradee yace a Englash din wani topic aka koya maku? Abdul yace Diff b/w news paper and magazine. "zahradee yace fisrt tell da meaning of news paper before we tolk abourt the diff. Abdul ya fara da cewa The news paper it's unboud printed publicatino issued at regular which prints information in unboud words and after supplemented with pictures.... "zahradee dake tsaya yace ya'isa h'aka kanina ashe dae kana da kokari. "dariya Abdul yai' Aisha dake tsaye ta daure fuska sbd tasan halin Abdul sarai da bakar surutu' idan aka biye tashi sae ya kwana yana zubawa ba damuwarsa bane. "Gani Aisha ta danke fuska ne yasa zahradee cewa Abdul shiga mota ka zauna ugo wayata kayi game. "bude masa motar yai ya shiga snn ya mika masa wayar' gani yadda ta daure fuska yasa zahradee cewa kiyi hakuri Aisha na bata maki rai ko? "Aisha tace to ba kaine ka kama jan yaro da surutu ba. "zahradee yace a'a Aisha bazaki gani bane nima kaima mmki Abdul ya bani sbd yadda akai masu explanation ba kowani yarone zai fahimta ba' sbd yadda akai masu bayani ba method din secondry level bane' wanga method din na yan' hghth intitut ne' maybe qua teacher ne. "Aisha tace ni zantafi sbd abba yace kada na dade' zahradee yace tun yanxu Aisha? Aisha tace abba ne yace kada na dade shiyasa. "zahradee yace to shikenan gobe ko jibi nadawo' juyawa yai gun Abdul yace fito katafi g'ida. "Abdul yana fita zahradee sa hannu yai cikin mota ya dauko wata yar'karamar jaka ya mikawa Abdul snn sukai sallama. "tashige cikin g'ida' shima yashiga mota yai na g'ida. "tun daga lokacin soyayya mai karfi ya shiga tsakaninsu kullum cikin msrarin juna suke da dakin gani juna dan ma duk su biyun iyayyansu na take masu birki. "komai zahradee ya samu na Aisha ne tun mafaifinta yana hanata amsa idan ta kawo abu tace zahradee ne ya bata sae abbanta ya hauta da fada' idan zahradee din yazo da kansa yake daukar kayan ya meda masa dasu' duk irin fsdar da zaiyi bazaisa zahradee ya amshi kayan ba. "zannuwa kuwa adon nida abuna akeyi duk wasu sabbabin yayi idan bbn zahradee ya kawo saeya cirewa Aisha a ciki' gani aiyuka suna masa yawa baya samu zuwa gun Aisha sosae yasashi siye mata waya ya bata a cewarsa idan besamu zuwa ba zai kirata ta wayar surinka hira. "boye wayar tai basu bari abbnta yasa tanada waya ba' daga ita sae mmnta suka sani' idan har zahradee zai kira sae dae lokacin da abbnta baya g'ida ko k'uma lokacin suna dadinsa shida umma suna hira snn zahradee zai kira suyi hira'gudun kada abba yaji ringing din wayarne yasa tasashi a silet wani lokaci sae yaita kira har ysgaji bata daga ba sbd ba'ajin ringing din wayar. "duk lokacin da zahradee ya kira Aisha bata daga ba zahradee yana shiga cikin damuwa sosae amma daya samu lokaci yazo hira shine yake tambayarta dalilin h'akan' Aisha tai masa bayani tun daga lokacin ya daina damuwa k'uma ya rage yawan kiran da yakeyi mata' a cewarsa idan tananan lfy shikenan. "kwanci tashi babu wiya a gun ubangiji su Aisha ana shirin zana weac duk yawancin student su biyu amma banda Aisha' sbd tunda ta sanarwa abbnta besake cemata komai akai ba' itama bata sake tutubarsa da mgnr ba' shiyasa yau da taje school aka koreta ta dawo g'ida. "sbd takaici ko shiga napep batayi ba haka tai ta cin kafa tana tafiya' dan kwata2 basufi su biyar ba da'akewa mgnr kudin duk yawancin student su biya. "Tana cikin tafiya kamar daga sama taji ana jawo mata school bag ta baya' da sauri ta juya dan gani ko waye' juyawar da zatayi zahradee ta gani yana mata murmushi' wasu hawaye ne suka zubo mata. "Da sauri ya hadiye dariyansa h'ade da tambayar lfy Aisha? Hawaye da suke zubo mata ya hanata yi masa bayani. "Gani a bakin titi suke yasa zahradee rike mata hannu zuwa gefe snn yace lfy Aisha ta waye ya bata maki rai? Aisha tace babu komai' zahradee yace banyarda ba' babu komai shine kike kuka? Aisha kodae matsayina bakai na kisanar dani damuwarki bane?. "a'a ba haka bane. "In ba haka bane to menene? "Shiru tai kanta a kasa. "tsareta yai da ido yana sauraran abinda zatace' gani tai shiri batada niyar fadi yasashi cewa shikenan Aisha tunda banida matsayi da kima a gunki da har zanga kina cikin damuwa na tambayeki' ni natafi. "sa kai yai zaitafi da sauri Aisha tace dan Allah katsaya' idan na tsaya me zanmaki tunda ban'iso naga kina cikin damuwa na tambayrki ba. "Shiru Aisha tai har yakare snn ta fara da ida-ida h'ade da wasa da yatsun hannunta. "daga nan ne tazare komai ta fadi mata' zahradee yace shine yasaki shiga damuwa? To yanxu abinda nakeso dake shine kishare hawayenki snn sae muje school din naku. "Sae da ta share hawayenta tsaf snn ya tare masu napep yace a kaishi school din su Aisha' suna tafe suna hira' amma a nasa zuciyar cewa yake wlh yau duk yadda abba zaiyi dani Sae dae yayi'idan wlh da kudinsa zanbiyawa Aisha kudin makaranta. "suna isa suka sauka ya baya mai napep snn suka karisa cikin school din' office din principal Aisha ta kaisa' bayan sun gaisa ne zahradee yake tambayar nawane kudin da zaisa a kori Aisha a school. "principal yace ba masu yawa bane 53,750 ne kawai. "jin among din yasashi hadiyar yawo da karfi' shidae har ga Allah yasan bashi da sisi nashi na kanshi sae na abba dake hannunsa akan yaje yasa masa a cikin account dinsa' gani yai shiru yasa principal cew malam yah dae? Faskewa yai h'ade da cewa babu komai nawama kace? Yace 53,750' a zuciyar zahradee yace jarrr uba' wlh yau duk yadda abba zaiyi dani sae dae yai amma wlh saena biyawa Aisha kudin school din nan. "haka ya ciro naira dubu dubu babu ko chaji yabawa principal. "amsa principal yai h'ade da godiya. "shima zahradee godiya yai h'ade da mikewa suka fita' sae da Aisha ta rakashi har bakin gate din school din tai masa godiya snn ta koma ciki'. "shima daga nan kasuwa ya nufa sbd babu mgnr zuwa wani bank kuma tunda ba kudin. 📖🖊 ☘☘ ☘ AURE IBADA NE FASAHA ONLINE WRITES F. O. W. ☘. MMN USWAN 1⃣4⃣ "zahradee yana hawa napep be tsaya ko'ina ba sai kasuwa gun bbnsa. "yana isa ya biya me napep kudinsa snn yakarisa cikin shagon' yana shiga bbnsa yace har kasa kudin? halan yau bank babu queue ne? "Eh" kawai zahradee yace h'ade da susa kansa. "yace yanxu kasa ko tun dazu? "Shiru zahradee yai. "zahradee da kai fa nakeyi. "Nan zahradee yafara inda inda. Cikin dimaita yace tun dazu. "okay kawai alhj Kailani yace' daga sann yace gaba da uzurinsa. "Itako Aisha ba karami dadi tajiba' duk da tasan kudin ba yafi karfin mahaifinta bane amma taji dadin h'akan da zahradee yai mata' sbd ya taimaketa a lokacin da take bukatar taimakon. "duk irin bayani da uncle keyi masu Aisha bata san me yake fadiba sbd ta fada duniyar tunani' seat mate din tane ta tabeta h'ade da tambayata da Aisha wht 're u think about? "Cikin gigita tace nothing. "okay kawai tace. "Da dare bayan su zahradee sun dawo daga kasuwa' suna cikin hira sae mgnr kudin ya fadowa alhj' nan yasa cewa so har yanxu fa banga alert ba' ace har yanxu matsalar network ne? "Nan zahradee yace dan Allah abba kayi hakuri". "A kan mefa son? "Wlh abba a gaskiya amfani nai dashi. "Cikin rashin nuna damuwa abba yace son me kai dasu? "zahradee yace wlh abba lokacin da ka aikeni bank ina kan tafiya kenan da yake a kafa nake shine na hadu da Aisha tana tafe tana kuka' ni kuma gani halin da take ciki yasani tsayuwa na tambayi ko lafiya' shine take sanar dani cewa koranta akai kudin weac kuma cikin week dinga za'a rufe idan bata buyaba shikenan' ni kuma gani haka yasa nai amfani da kudin da ka aikeni na biya mata. "kafin abba yace komai su yya shamsudee da Nurudee suka haushi da fada' h'ade da cewa bazan kawai mara wayo waya sanima ko ba rabonka bace ita' kaje kana faman wahalar da kanka a kanta' b'ude baki yai zaiyi ngd da amma!. "shamsudee yace amma me wlh idan kai wani mgn saena mareka' in kuma kana gani kamar karyane to ka gwada. "Gani duk sun taso masa yasa abba dake zaune dakatar dasu' hannu kawai ya nuna masu alama su bashi gu. "duk mikewa sukai sukabar masa gun. "bayan sutarsane abba yace zahradee. "na'am abba. "wlh zahradee wannan inaso yazama shine farko k'uma shine karke' wlh zahradee inda wani daga cikin yan'uwanka ne sukai min h'aka na wlh da sae sun bayani kuduna' amma sae yazamanto kaine' kae waya cemaka ana h'aka ma? "itace tace kama iyayenta basuda kudin biya mata school feel ko mai? "A'a abba' nine dae kawai. "to kada kakara' idan k'uma kakara wlh saena hukuntaka. "nagode abba in Allah ya yarda bazan karabama. "to shikenan. "Da yamma bayan bbn Aisha badawo daga kasuwa suna cikin hira da ummanta shine umma take sheda masa da cewa zahradee ya biyawa Aisha kudin weac. "Nan alhj muhmmed ya hau fada inda yake shiga ba nan ne yake fita ba daga karke yace takira masa Aisha tazo. "mikewa umma tai taje dakinsu ta kirata sukazo tare har kasa Aisha ta duka snn tace gani' alhj yace wato Aisha irin sakayyar da zakinmi kenan ko? Yanxu sbd Allah abinda kikai yadace kenan? "Cikin sanyin murya Aisha tace abba wani laifine nai maka? "Aisha ba laifi kikai min ba amma sbd Allah har abin yakai ga kije ki roki zahradee yabiya maki kudin weac?. "Cikin kuka Aisha tace roko k'uma abba? Wayace maka rokonsa nai? Wlh abba ni ban rokeshi ba' shine dae yai niya ya bayamin kudin' idan ma kana gani kamar karyane wlh abba ka kirashi ka tambayeshi kaji. "Alhj muhmmed yace Aisha ni bance kina karyaba ba sbd tun farko bansanki da karya ba ' amma abinda nakeso ki fahimta idan har yar' uwansa sukaji labarin h'akan gani zasuji kamar nakasane' Aisha kifi kowa sani idan a kankune abinda ya kama daga 1 naira zuwa million idan akan school ne ni me kashe makune' k'uma kifi kowa sani banaso rainin wayo' idan har sukace zasu rainamin wayo akan h'akan wlh bazan dauki walakanci ba. "Shiru Aisha tai har yakare mgnr sa snn tamike batare da tace masa komai ba. "AFTER 5 MONTH "Su Aisha suzana weac dinsu cikin sa'a k'uma paper su yai kyau' gani sun samu sakamako mai kyau k'akan yasa abba ya nima mata diploma dake cikin garin bauchi' da yake yanxu wani irin lokaci ne da muke ciki wanda idan kanada abin hannu komai zakayi a doran kasa' karma ace kasarmu NIGERIA. "hakan yasa besamu matsala ba wajan nima mata addmi' yana zaune a gida aka gama masu komai' attanding lecture kawai tafara batare da tasan wahalar komai ba. "tana karatune a bangaren business' koda Aisha ta sanar masa da mgnr samu school dinta yai murna sosae sbd a yadda yai lisafi mgnr bikinsu zaizo masa daedae da lokacin da yake so. "dinkuna yai mata sosae da siyayya a cewarsa yanxu zata fara harkan big girl dole saeda manyan shiga sbd gudun rainin wayo. "Aisha tai murna sosae da zahradee ya kaimata kayan gidansu. "Ranar monday Aisha tafara attanding lecture. FANS KUYI HAKURI NA RASHIN JINA KWANA BIYU WLH EXAM NE YA BOYENI AMMA YANXU NA GAMA SAE JIRAN SAKAMAKON. ZAKU RINKA JINA KULLUM KODA BAMAI YAWABA. NAGODE SOSAE ☘☘ ☘ AURE IBADA NE FASAHA ONLINE WRITES F. O. W. ☘. MMN USWAN ZANYI AMFANI DA WANNAN DAMAR WAJAN TAYA YAR'UWATA ZAINAB SHU'IABU MARUBUCIYAR YARAN MIJUNA MUNAR KAMMALA LITTAFINTA HAKIKA KIN WA'AZARTAR KUMA KIN NASHADANTAR KIN BAJE KOLINKI WAJAN NUNA FASAHARKI. KUKA KURAN DA KIKA SAMU ACIKI ALLAH YA YAFE DARANSAN DA AKA DAUKA A CIKI ALLAH YABADA IKON AMFANI DA SHI. 1⃣5⃣ "Cikin sa'a Aisha tafara karatunta k'uma alhamdullh sbd duk yawancin lecture din da ake masu tana fahimta sosae' idan ma bata fahimta ba idan zahradee yazo hira in har ta sanar dashi zama suke sosae yaita yimata bayani har sae ta fahimta snn zantafi g'ida. "Itama Aisha dayake tanada brain shiyasa da zaran yai mata bayani take dauka. "zahradee ya taka rawar gani sosae wajan karatun Aisha' duk da shima mahaifinta ba baya ba amma da h'aka zahradee yaci gaba da yimata hidima wani lokaci shiyake kaita school' idan h'akan besamu ba suna tashi lecture zaije ya daukota da motar abbanshi. "Alhj Kailani yai f'ada har yagaji amma duk a banza' gani h'aka yasa alhj sakarwa zahradee motar' shikuma ya siye wata. "shima zahradee yana kammala project din sa aka turashi service a kasar kudu IMO state amma abinda dan NIGERIA idan kanada hanya h'aka alhj Kailani yashiga ya fita aka barshi a nan bauchin yai service dinsa. "Da h'aka zahradee yake raba kansa biyu sbd yana tashi daga aiki yake zuwa kasuwa gun bbnsa' sbd zahradee yanada wani abu daya duk yadda zaiga harkan kasuwanci abbansa sae yayi h'akan yasa abba ke matukar sonsa. "Gani Aisha tayi nisa da karatun yasa zahradee birgewa abbnsa a dole shifa sae dae aje g'idan su Aisha a nemo masa aurenta tunda tayi nisa da karatun kusan aiya cewa ma kadin yarage mata. "Duk yadda alhj yai dan yashawo kan zahradee akan yabari har takare amma zahradee yaki. "Sbd zahradee gani yake kamar bazaikai lokacin ba' ko k'uma idan lokacin yai Aisha tace bata sosa. "Da yaga kamar alhj bashi da niyar tafiya nimo tasa auren Aisha yasa damuwa idan ko kasuwar da yake zuwa ya dae na' idan yafita aiki tun safe baya dawowa g'ida sae dare yana shiga kai tsaye dadinsa yake shiga ya rufe kofa batare da ya tsaya parlour hira da yan'uwa ba. "Ba komai bane yasa alhj yaki tafiya nimawa zahradee aure ba so yake saeya kare gini da yake masu shida yayyinsa sbd bayaso su zauna gun daya da sirikansa yafiso suyi nisa da juna' shiyasa beje nimawa zahradee auren Aisha ba' yafiso idan ya kammala a lokacin ne da kanshi zai daukesu ya kaisu gun sugagi snn sae yatada mgnr bakin. "Amma rashin sani da yafi dare duhu yasa zahradee yakewa mahaufinsa h'aka sbd duk a ganisa ba nima masa aure Aisha ne za'ayi ba. "Gani yadda zahradee yashiga damuwa sosae yasa abba da kansa yabi zahradee har dakinsa' lokacin zahradee yana zaune ya tasa wayarsa a gaba yana kallon pict din Aisha' har alhj ya shigo zahradee besani ba. "gun yasamu ya zauna h'ade da sa hannu ya tabo kafadar zahradee snn ne zahradee ya dago kansa' gani abbnsa ne yasashi cewa abba yaushe ka shigo?. "murmushi abba yai h'ade da cewa son kenan pict din sirikan tawa ake kallo h'aka? To nima abani naga sirikansa tawa. "murmushi zahradee yai h'ade da susa kansa' batare daya tanka ba. "hannu yasa ya amshi wayar saeda ya karewa wayar snn yace sirikan tawace h'aka? Lalla kam dole dana ya rikikice ya rinka fushi dani sbd naki tafiya nima masa auren ta. "jin h'aka yasa zahradee daure fuska. "murmushi alhj yai snn yace zahradee. "Cikin karkashin murya yace na'am abba. "Alhj yace ba naki tafiya nima maka auren Aisha bane kawai h'aka akwai wasu aiyuka da nakeyi ne nafiso idan nagama snn na sanar daku snn k'uma na nima maka auren. "juyowa yai snn yace abba wani irin aikine zai hanaka nimami aure? Aikin da kikeyi ya shafi mgnr aurena da Aisha ne kome? "himmm abba ni tun ba yanxu ba tuni nariga na gano kawai dae baka sona da Aisha ne. "Subbuhanalillah son kada kaimi mumunar fahimta wlh har ga Allah ba nufina ba kenan son. "abba inba nufinka ba kenan abba to menene a zuciyarka? Abba kana gani tunda Aisha tafara doploma din nan samari suke ta kawo mata hari' idan ma Allah yasa tana sona' wlh da ba dan son da takemin ba nasan da bazata kuni ba sbd ba kananun mutum bane suke zuwa gun ta' harda manyan attajirai. "murmushi kawai alhj yai. "Gani irin murmushin da abba yai yasa zahradee cewa Allah kuwa abba. "Alhj yace son kenan' ba komai ne bane nakeyi illa gani ne nake yimaku kaida yan'uwanka wanda idan kunyi aure zaku zauna a ciki sbd banaso mu zauna gu daya daku a cikin g'idan nan... " abba idan akan inda zamu zauna ne abba ni inada kudin da zai'ishemu nakama haya har kakare mana gini. "mikewa zahradee yai yazo gaban alhj ya duka har kasa snn yace abba dan Allah dan annabi idan soyyayar da kakewa shugabanmu annabi muhmmedu (S. A. W.) abba ka taimakeni ka taimaki rayuwata kaje ka nemamin auren Aisha' wlh Allah abba ni kaina bansan irin sonda nakewa Aisha ba' idan har narasa Aisha a rayuwata abba zanshiga wani hali abba. "Shiru alhj yai yana me jijina mgnr zahradee. "can yasa hannu ya dagosa ya zauna snn yace son karka damu insha Allahu gode da yamma zantura kawunka da bbnka habu suje nima maka auren Aisha... "wani irin tsanle zahradee yai h'ade da rungume abbnsa yana murna. "abba yace saurareni d'kyau kaji abinda zanfadi maka' zahradee. "na'am abba. "zantura a nimo maka auren Aisha amma da sharadi' kudi da kake mgnr kama haya dasu zaka bani na karisa maka gini bangarenka dashi. "abba na amince bari yanxu nai maka transfer dinsu zuwa account dinka. "murmushi kawai alhj yai ya fita. "washe gari da yamma bayan sallar la'asar dayake ranar saturday koda sukaje bbn Aisha yana g'ida beje ko'ina ba' koda sukasa akai masu sallama dashi tare suka fito da dan'sakon' gani manyan mutunine yasashi karisawa da sauri gusu suka gaisa. "bayan su gaine alhj muhmmed yace gashi be sheda kusa ' daya daga cikin su yace alhj Kailani me zannuwa ne ya turomu. "jin h'aka yasa alhj yasasu sake gaisawa snn yai masu iso zuwa parlour sa' a take yasa aka kawo masu abinci dasu juice da ruwa. "hada hannu sukai sukaci bayan su gamane snn sukace dama alhj Kailani ne ya turomu nimawa dan'sa auren yar'ka. "Alhj muhmmed yace kai madalla abu yai kyau kaga dama kadan yarage mata ta kammala karatun da takeyi. "nan dae suka daedae ta alhj muhmmed yace dama DEC ne zata kare tana karewa JANUARY sae ayi bikin kawai a huta. "suma suyi marna sosae dajin h'aka. "Sae da suka dan jima suna tattaunawa snn sukai sallama. "koda labari ya'iske zahradee ba kasamin murna yai ba' h'ade da hamdalla yana mika godiyar sa gun ubangiji. 📖🖊 ☘☘ ☘ AURE IBADA NE FASAHA WRITERS F.O.W.☘. MMN USWAN 1⃣6⃣ "Yana gama murnarsa ya dauki wayarsa ya kira Aisha' wayar yai ringing har saubiyu bata daga ba sbd bata kusa DA wayar sae a na uku snn taji ringing din wayar a guje tazo ta daga h'ade da sallama. "Zahradee yace hello my Aisha ta'kina inane nake ta kira baki daga ba? Aisha tace Ina kitchen ne nida umma muna aiki shiyasa ban daga ba. "Ayya yaya umman take?tana lfy? "Klau. "Aisha ta. "Na'am. "Nasan kisan komai basae na f'adi maki ba ko? Na fa? Mgnr aurenmu mana Aisha. "Himm zahradee kenan kaedae wlh kacika gaggawa. "Gaggawa fa kikace Aisha' eh ma naji idan a kankine'kenan bari ma kiji wlh a yadda nakeji banki ace yau an daura mana auren ba' idan yaso sae ki karisa karatun a gida na. "Uhm" nidae banyarda ba' h'aka kawai sae anzo anyi kahanani karisawa' nidae nafiso na kammala snn koma menene sae ayi. "Himm'aisha kenan dan bakisan yadda nake jinki a zuciyata bane yasa' wlh Aisha nafi kowa son naga kinyi karatu'koda bakiyi aiki ba. "Eh" dae naji' nidae saena kare snn. "Aisha ki kwatar da hankalinki nima mgn kawai nakeyi' ko tsaida watan bikin ma da akayi shima abin farin cikine aguna'fatana kawai Allah ya nuna mana lokaci darai da lfy. "Shiru tai tana murmushi. "Kiran

Chapter 7 of 38