har akai la'asar gani h'aka ne yasata daukar waya ta kira number sa.
"duk kiran da Aisha takeyi zahradee na kallo amma be daga ba' wani irin dadi kawai yakeji' gani be daga ba yasata yimasa text da kazo kaci abinci.
"yana gani da sauri ya b'ude text d'in' yana gama karabtawa yai mata reply da ganina zuwa.
"dama yana cikin g'ida mikewa yai ya kami hanyar cikin g'ida har zahradee yakai kofar d'akin Aisha ko me yatuna k'uma oho komawa yai da baya yana fita ya kira Amatulrahaman yace taje dakin Aisha ta amso masa abinci.
"to kawai tace.
"tun daga lkcn zahradee besake shiga cikin g'ida ba sbd yanajin kunyar yadda zaihada ido da Aisha'da yamma koda Hjy ta aika masu da abinci h'aka Aisha tasake ije masa' tana idar da sallar isha'i tasake wani wanka ta zauna zaman jiran zahradee nan ma bedawo ba' Aisha ta zauna har dagaji da zama goma yayi gashi bcc takeji cire kayan tai ta sanya na bcc snn ta kwanta.
"shiko zahradee yana can da yayyinsa tare sukaci abinci sbd duk a tananinsu har yanzu Hjy bata basa izini shiga dakin matarsa bane.
"bayan su gama ci zama sukai sunata hira har 11PM gani h'aka gashi dama su Shamsudee sufara bcc mikewa yai yafita zuwa bangarensa' lkcn Aisha na zaune tana tunanin abinda ya hana zahradee shigowa' tana cikin h'aka sai gashi yai sallama ya shigo.
"Aisha dake zaune bakin gado ta amsa snn ya kariso ciki'sannu da zuwa tace masa h'ade da mikewa abinci ta dauko masa' zahradee dake zauna a kan cushion one ster a gabansa ta'ije masa abincin hade da ruwa.
"murmushi kawai yai cikin jin kunya yace nakoshi sbd nariga naci dasu yaya.
"to" shikenan".
"kwashewa tai ta ije a gefe snn tashiga toilet ta h'ada masa ruwan wanka tana fitowa ta sanar dashi.
"ngd kawai ya ambata snn ya shige.
"shiru-shiru zahradee befito ba' yasa Aisha kwanciya' tana kwanciya bcc ya dauketa.
"shima zahradee din lekawa yai yana gani tai bcc shine yafito yazo suka kwanta.
~~~ ~~~ ~~~~
"baba"!
"yawwa sannu Khadijat".
"Fatima".
"na'am Nasir".
"wlh Fatima inajin jiki".
"h'aba Nasir Dan Allah kadai na f'adin h'aka.
"himm Fatima kenan jinake a jikina kamar bazan tashiba.
"Fatima najin h'aka fashewa da kuka tai h'ade da rungume Nasir dake kwance akan gadon asibiti snn taci gaba da cewa Dan Allah Nasir kadaina f'adin h'aka ita cuta ba mutuwa bace' insha Allahu zaka tashi Nasir.
"hannu Nasir yasa yana lallashinta' haba Fatima kidai na kuka duk wanda kikaga ya mutu to fa ki tabbata lkcn sane yai' h'aka k'uma wani baya rayuwa da rayuwar wani Fatima' amma a yadda nakejin jikina him".
"kae Nasir insha Allah babu inda zaka munanan tare' Nasir idan kamutu kabarni yaya kakeso nayi Nasir?" Nasir tunda nake a duniya bantaba son wani d'a namiji ba sai kai Nasir' Nasir kasancewarka gareni tabkar wata tsokace a cikin jikina wanda idan babu inda ba lalla bane na rayu.
"Dan Allah Nasir kada kamutu katsaya mu zauna tare har tsawon rayuwarmu.
"Fatima kenan' wani abu da bantaba sanar dake ba shine tunda nake a rayuwata a lkcn banfi 20 years old ba nakan tashi cikin dare na roki ubangijina abubuwa da yawa amma duk cikin rokon da nake masa bantaba rokonsa da yasa nayi tsawon rai ba sai bayan haduwana dake' na karkata akalar rokona da ubangiji yaban tarin dukiya mai yawa da kuma ya mallakamin ke sbd nabaki kyakykyawar kulawa koda bamuyi tsawon zama tare ba.
"nasha f'adi idan ubangiji ya cikamin burina duk wata hanya ta sabon ubangiji zankiyaye' saidai kinsan d'an"Adam tara yake becika goma ba Fatima.
"ba mmki aure-auren da nakeyi shine kalar tawa jarabtar da Allah yai min.
"Fatima ngd da Allah ya hadani dake me sonane' inda watace da yanzu ta tafi tabarni.
"Dan Allah Fatima koda bayan rai nane ki rikemi Khadijat da Jabeer tabkar ina raye' zanyi alfahari dake a duk inda nake sbd nasan kasa zairinka kaimin lbrin kabarina Fatima.
"Fatima najin h'aka tasake kankame Nasir tana kuka".
"gani h'aka yasa su Khadijat da Jabeer zuwa su rike mmnsu suna kuka.
"Nasir dake kwance shima hawayene kawai yake gangare masa.
"bayan kwana biyu jikin Nasir ya tsananta duk abinciken da doct kamal zaiyi yayi amma a cewarsa bega komai ba k'uma gashi jikin babu sauki.
"h'akan yasa Fatima yanke shawarar sanarwa Alhj Rabi'u guduma wato mahaifin Nasir halin da suke ciki.
"washe gari kafin azahar saiga Alhj Rabi'u a binnin kebbi gani halin da Nasir ke ciki yasa Alhj daukar Nasir zuwa gida kano' Nasir na motar bbnsa da yyasa ke tuki' Fatima k'uma dasu Khadijat suna motar Nasir din wanda bilyaminu ke tukasu.
"kai tsaye gidan su Nasir suka nufa.
"duk'yar uwa su hadu' kani da yayyi kowa yana kawo kalar nasa shawarar' Bbn yayansuAlhj Tasi'u dake zaune a abuja shida matarsa Allah yasa lkcn suma suje gani gida yacewa abbansu Alhj Rabi'u idan har ya amince me zaihana baza'a fita dashi kasar waje ba kawai.
"alhj rabi'u yace eh" kam h'akan zaifi amma wani harzari ba guduba nidai yanzu kufi kowa sani bazan iya doguwar zama ba' saidai acire wasu daga cikinku hade da matarsa kutafi tare.
"Alhj tasi'u dake zaune yace Abba kada kadamu zamusan yadda za'ayi.
"kwana biyu da mgnr aka fita dashi kasar Cairo Egypt Fatima ne da yayyinsa biyu suka tafi.
"alhamdullh yanzu kan anfara samu canji akan da' idan shima kansa yafarajin canji a jikinsa.
"watan su Fatima daya bbnta Alhj Sunusi yaje dubasu' Fatima taji dadi sosae gani abbanta yazo gani su.
"kwanarsa uku da tafiya ya dawo gida Nigeria.
~~~ ~~~ ~~~
"bayan kwana bakwai da bikin zahradee Hjy ta daina samasu abinda suka farayin nasu' saidai idan suyi zahradee yacewa Aisha tarinka tasa Hjy.
"Aisha tace to.
"tun daga lkcn idan har Aisha tai girki takesawa Hjy' h'aka ma yau tuwan shinkafa tai da miyar vegetable duk da ba mai yawa bane amma h'aka tasawa hjyn da kanta ta dauka da sallama tashiga d'akin Hjy gani babu kowa a d'akin yasata ije kular tafita.
"lkcn Hjy na kitchen tana abincin yamma'Aisha na ijewa ta koma bangarenta' hjy bata shigo d'akin ba saeda tagama abinci tsaf snn tashigo dan yi wanka h'ade da sallah.
"can gefe ta hango kular Aisha' batai ta kansaba sbd dama ba cin abincinta takeyi ba' su Amatullah ne da Amatulrahaman sukeci.
"sumadin ba kullum ba sbd gaba dayansu ba yara bane'dan a yanzu da h'aka Amatullah tana three hudreen ne ita k'uma Amatulrahaman tana two hudreen ne a tabawa balewa university dake bauchi.
"toilet Hjy tashiga tai wanka hade da alwala bayan ta idar da sallane ta bude abincin da Aisha takawo mata' gani leda dayane yasata meda murfin ta rufe bata sake bi takansa ba k'uma.
"zahradee yana dawowa daga kasuwa kai tsaye bangare su Hjy yanufa shida Abba' dama dabi'ar zahradee ne duk lkcn daya dawo kasuwa saiya fara zuwa gun Hjy su gaisa sann zaije bangarenshi.
"da sallama ya shiga Hjy na zaune kan sallaya tana lazumi a ladabce zahradee ya gaidata.
"da fara'arta ta amsa hade da tambayar kasuwa".
"alhamdllh".
"hannu yasa ya ciro bandir din two hudreen naira note yabata h'ade da cewa Hjy ga wnn kyasiye goro.
"Hjy tai murna hade da samasa Albarka.
"zahradee na duke sai faman cewa amin yakeyi.
"mikewa da zaiyi hannu tasa ta jawo kular Aisha tace gashi kakaiwa matarka.
"to kawai yace snn ya amsa.
"yana amsa ya fita' bagarensa yanufa' yana shiga Aisha ta taresa da murna tana f'adin sannu da dawowa.
"yawwa sannu.
"mike mata kular yai yace Hjy ce tace na kawo maki.
"kakawo k'uma?" dazufa na kaimata abincin a ciki' kodai har sugama dashi ne?".
"kibude ki gani mana.
"to"
"koda Aisha ta b'ude yadda takai ko taba ba'ayi ba aka dawo dashi.
"shirutai tazubawa kular ido.
"yah dai Aisha?".
"kagafa yadda nakai abincin h'aka aka dawo dashi".
"kamar yya?".
"gashi kagani fa".
"dama iya kacin abinda kika zuwa kenan ko yafi h'aka?".
"a'a" iya kacinsa kenan".
"sbd Allah Aisha wani irin abinci kenan kamar za'abawa mage' dubafa kigani' fushi kenan tai k'uma ko nine h'akan zanyi.
"idan banda rainin wayo wani irin abincine wnn sbd Allah' yau koda bakisanta ba kya dauki wann figigin abincin kibata.
"amma"..
"amma me?".
"gani nayi ranar da nayi da yawa fada tai sosae wai albazaranci ne.
"eh kema kanki ranar kinsan baki kyauta ba.
"sbd h'aka idan har kinaso mu shirya kije kibata hkr kawai.
"hkr k'uma?".
"Eh" kifita kawai kije tun kafin tabiyomu nan ta hadamu gaba daya.
"to kawai Aisha tace duk idanuta sun cika da kwalla' hijab tasa tafita.
"haka kawai kizo ki jamin wani mgn agun Hjy bayan kisan ba kyalemu zatayi ba dagani har ke.
📖🖊
☘☘
☘
AURE IBADA NE
FASAHA ONLINE WRITERS F. O.W.☘.
MMN USWAN
3⃣0⃣
"sallamu'alaikum"
"ami'waalaiki salam'waye?".
"nice Aisha.
"dama Aisha ce tatsaya tana doka wata uwar sallama kamar bakuwa.
"a sanyaye Aisha ta kariso ciki".
"lfy?"
"lfy klau Hjy" dama rokonki nazoyi' Dan Allah kiyi hkri.
"wani abune ya faru?".
"a'a" mgnr abinci ne".
"zahradee ne yadawo da abincin dana samaki yace kekikace a dawo dashi' sbd kinyi fushi.
"shidin yace nayi fushi?".
"Eh shiyasa yace nazo na baki hkr".
"shidin ko?".
"OK tashi kije ki kirashi k'uma kuzo tare.
"to Hjy".
"mikewa tai yaje kiran zahradee din.
"tana fits Hjy tace duk zakuci ubanku dani.
"zahradee na zaune a bakin gado yana jiran Aisha' tana shigowa yace kinbata hakurin?".
"Eh"Amma tace kaje".
"naje k'uma?".
"Eh" wai muje tare".
"to muje' zahrdeee yana gaba Aisha na baya suka shiga dakin' duk dukawa sukai a gabanta snn yace gani Hjy.
"Hjy gani".
"basai kacemi gaka ba'naga zuwanka' tunda ba makauniya nake ba.
"kacewa matarka tazo tabani hkr sbd nayi fushi ko" kayi shiru kamar ba dakai nakeba.
"Eh"h'aka ne".
nice nace maka nayi fushi?".
"a'a".
kaga zahradee banason mananu maganganu daga kai har matarka baku isheni' abincine k'uma ba dole bane sai kunbani' kafi kowa sani bacin sbincinta nakeyi ba'kosu Amatullah dinma su ba kowani lkc sukeciba shiyasa tun farko nace a'a kubar kayanku kace a'a to ga irinta kenan.
"Eh" Hjy nine nace arinka sawa koda bazakici".
"zahradee Kaine bazan boye maka ba' kane kakeso bani abincinka amma matarka bataso...
"da sauri Aisha tace a'a Hjy wlh ba h'aka bane' gani nayi kwanaki da nake sawa da yawa bakwaci shine na rage hannu sbd kada yazama albazaranci.
"eh' kinada gskya shugaban'yar tattali tunda daga g'idanku ake kawo abincin ba.
"ooo!!!! In Laila abin mmki baya karewa nine yau za'a koyamin yadda ake tatta.
"to bari kiji tunda badaga gidan ku ake kawo abincin ba' baki isa kice zaki kawomi wani kauli da ba''adi ba.
"dakawa zahradee tsawa tai h'ade da cewa ashe dama duk abinda makeyi da sanika....
"a'a" Hjy wlh bansani ba' kenan kinsan inda na sani bazan kyaleta ba Hjy.
"shiru Aisha tai kanta na kasa tana hawaye.
"to bari kiji daga yau na kashe kawomi abincinku' k'uma kada kiyi tunanin abinda kikeyine yasa 'a'a ra'ayi nane kawai sbd koda shakeni zakiyi bansan tast din abincinki.
"zahradee dake duke inba hkr da yakebawa Hjy ba babu abinda yakeyi.
"itako Aisha kuka kawai takeyi.
"Hjy taci gaba da cewa yarinya tun kafin kisan zakizo duniya nake girki banle zuwanki jiya-jiya kice abincinki zai tsolemi ido.
"suna cikin h'aka ne Abba yai sallama ya shigo da sauri Aisha ta mike tabar dakin' zahradee dake duke Abba yace son yaya akai ne?".
"da sauri zahradee ya dago yana me cewa Abba.....
"kae tashi kafita.
"mikewa yai yafita.
"bayan fitarsa ne Abba yace Hjy yaya akaine?".
"da fara'arta tace name fa Alhj?".
"ganisu nai anan".
"babu komai".
"washe gari da safe bayan su zahradee da Abba sufita kasuwa' batai aikin komai ba sbd bcc da takeji sakamakon rashin bcc zahradee ya hanatayi da dare.
"har bcc ya fara daukarta taji ana knocking da farko batai niyar tashi ta bude kofar ba'amma jin knocking yaki karewa yasata mikewa tazo ta bude.
"gani Hjy ne yasata dukawa tace ina kwana Hjy.
"ba gaisuwarne damuwata ba' me yasami idon naki sukai jazirrr h'aka?".
"babu komai bcc ne kawai nakeji.
"bcc?".
"Eh".
"ke kika sani' wann damuwarki ne' me aikin bece ya gaji ba'saike da kike kwance akeyi maki' tashi muje kimin.
"mikewa tai tabita' Hjy na gaba Aisha na baya suka shiga kitchen Hjy ta nununawa Aisha lugu da sake na kitchen din snn tace tana bukatar da goge mata ko'ina harda su gas kuka da electric tace duk ta gogesu tas baya tagama k'uma tai mata wanke-wanke.
"to kawai Aisha tace Hjy na fita Aisha na binta da kallo.
"tunda Aisha tafara aiki bata gama ba sai bayan azahar snn takare.
"zuwa dakin Hjy tai ta sheda mata cewa takare'da fara'arta tace ngd Allah yai maki albarkw".
"amin Aisha tace snn takoma bangarenta.
"tana shiga bakin gado ta zauna tai shiru h'ade da uban tagumi tana tunanin abubuwa kala-kala' itadai tasan tsakaninta da zahradee batada matsala h'aka yayyinsa da kanninsa h'ade da Abba matsslarta dayane shine Hjy.
"me nayi mata da bata sona?" idan akan mgnr haihuwane Ai ba'ita yakamata ta damuba zahradee yakamata ya nuna damuwa amma bedamu ba sai Hjy?"
"to kodai kiyayyane?".
"wani zcy yace aa Aisha Hjy bata kinki.
"tunda mafi yawanci lkc idan Abba yaiwa su Amatullah da Amatulrahman kamar su kayan kwalliya zannuwa turaruka da dai sauransu sai Hjy ta cirewa Aisha tabata batare da zahradee ya sani ba' shima Abba da yaga h'aka idan har zaimasu siyayya saiya hada da Aisha.
"shiru tai taci gaba da tunanin dalilin dayasa Hjy take mata h'aka.
"gani la'asar yayi ta mike zuwa toilet tai wnka hade da alwala' tana idar da sallah tashige kitchen dan dora sanwa. tanayi tana wanke-wanke da h'aka har tagama tasawa Hjy tana.
"bata kaiba daki ta koma taje tasha kwalliyarta cikin doguwar rigan shadda snn taje ta dauki kular abincin takai dakin Hjy.
"da sallama ta shiga lkcn Hjy na sallah Amatullahi ne zaune a kan cushion saida suka gaisa snn Aisha ta ije abincin'har ta mike Amatullah tace ina zaki k'uma.
"daki zani".
"daki? me zakiyi a dakin?.
"idan Dan nine akai wnn kwalliyar to kizoki zauna kusa dani.
"murmushi kawai Aisha tai tafice batare da ta tanka mata ba.
"bayan Hjy ta idar da sallah ne tacewa Amatullah ta dauki ahbincin ta medawa Aisha.
"haba Hjy me k'uma tai' Dan Allah kiyi hkr mana.
"ni bataimi komai ba' cine kawai bazan yiba.
"to mu zamuci' ko sister?".
"eh"
"to shikenan gaku gashi ai.
"bayan zahradee ya gama cin abinci ne yaje dakin Hjy gaisheta' yana shiga su amatullah suka muke hade da cewa sannu yya da dawowa.
"yawwa snnuku.
dukawa yai ya gaida Hjy' bayan su gama ne Hjy tace zahradee".
"na'am Hjy".
"yanzu kakai wata nawa da aure?".
"lahhh Hjy har kinmance?" biyar kenan fa".
"alhamdullh gara da Allah yasa kana sane' yanzu yaya mgnr alkawarinmu?".
"alkawari k'uma Hjy?".
"eh" alkawari".
"gskya Hjy ni babu wani aure da zankara' tunda babu abinda Aisha ta rageni dashi...
"kafin zahradee ya kare Hjy ta daukesa da mari' har yaushe kazama h'aka zahradee ashe fitsaran naka yakai h'aka?" wato kai kaji dadi mace to wlh baka isa ba' idan ubanka aure k'uma babu fashi.
"wlh Hjy hkr zaki dani wlh babu wani auren da zanyi' da sauri zahradee ya mike yabar daki.
"salati kawai Hjy keyi h'ade da mmkin zahradee.
"zahradee yana fita dakin Abba ya nufa' yana shiga Abba yace son yaya akai ne na ganka h'aka.
"abba kaji Hjy fa wai dole saina kara aure.
"aure k'uma?".
"Eh" h'aka Hjy tace".
"to kai me kagani?".
"nidae gskya Abba bazan kara kowani aure ba'sbd duk abinda nakeso Aisha tana nai min.
"to son mgnr haihuwa k'uma fa?".
"haihuwar me Abba? Dan Allah abar mgnr haihuwarnan h'aka tunda na samu Aisha ta.
"lalla son har yanzu kai yarone' to wlh bari kaji mgnr aure ba fashi Dan a gskya inaso naga yaranka kafi ba koma ga ubangiji.
"kae Abba harda kae?".
"kwarai da gske son.
"bayan fitar zahradee ne Hjy ta shigo da sallama Abba yace madam yaya akai.
"murmushi Hjy tai sann tace yanzu sbd Allah Alhj h'aka zamu zubawa zahradee ido?".
"na me fa?".
"mgnr aure mana".
"haba dai Hjy nifa tuni nariga na yanke shawara gobe kafin na karisa kasuwa zanje gidan Alhj Musa nagansa da wata yarinya'yar kyakykyawa mai hnkli' dama kwanaki muyi hirar dashi akan Akwai yaron da yake zuwa gunta koda akai masa mgnr yafito sai yace iyayensa sunce basu shirya ba.
"to kinga idan ya amince ina nimawa zahradee aurenta' suma su Shamsudee da Nurudee duk mgn zanmasu sufito da yarinyar da sukeso sbd nagaji da zamansu h'aka.
"amma shi zahradee inaso ya rigasu' idan har Alhj Musa ya amince koda wani satine a shirye nake.
"yawwa Alhj har naji dadi' Allah ya shige nama gaba".
"amin".
📖🖊
☘☘
☘
AURE IBADA NE
FASAHA ONLINE WRITES F. O. W. ☘.
MMN USWAN
3⃣1⃣
"washe kafin Abba yaje kasuwa yabinya g'idan Alhj Musa' bayan sun gaisa ne Alhj Musa yake tambayar Abba lfy ya gansa da safe h'aka?".
"murmushi Abba yai sann yace wlh wata mahimmiyar mgn ce take tafe dani.
"to Allah yasa dai ba laifi naiwa uban dakina.
"duk dariya sukai' snn Abba yace h'aba dai.
"saida ya daidaita zamansa snn yace dama roko nazo h'ade da niman iri.
"kamar yaya Alhj Kailani? ban fahimtaba.
"himm Alhj Musa kenan" ina nufin nazo nemawa d'anka ne auren'yarta.
"wacce'yar'taka kenan daga ciki?".
"zainab wanda kwanaki mukai mgn akan cewa yaron da yake zuwa gunta kace ya turo magabatarsa amma beturo ba.
"Allah sarki wlh har na mance kamar muyi mgnr dakai.
"to yaya ake cikine?".
"wlh har yanzu shiru".
"alhamdullh'dama tsorona kada nayi nima akan nima.
"a'a wlh babu damuwa.
"aini na fika jin dadin wnn zance'sai wani dani daga ciki? yaran nawa da yawa.
"h'aka ne' zahradee ne?".
"wanne kenan daga ciki?".
"wanda yai aure kwanaki.
"Allahu Akbar' shine har zaikara? ikon Allah kenan.
"to idan har kasan babu wata matsala shikenan.
"insha Allahu babu komai" kasan kowani iyaye yanaso yadda aka mutu aka barsa shima yanaso yabar baya.
"kwarai da gske' to Allah ya tabbatar mana da alkairi.
"amin" ngd.
"amma wani hanzari ba guduba ya kamata yazo su daedaeta tsakaninsu.
"Ai dole' bayan su daidai ta mukuma ta rage namu.
"h'aka ne amma Dan Allah banaso a dauki lkc me tsayi.
"uban daki kenan' a yadda na tsarawa kaina dama koda Allah besa kazo da mgnr ga ba zainab bazata wuce wnn shekara ba batai aure.
"sbd koda ace Allah bekawokaba akwai wanda nake saran zanbata sai k'uma ga yadda Allah ya shirya.
"h'aka ne' to ngd ngd sosae Allah ya shige mana gaba.
"amin nima ngd.
"da yamma bayan Abba yadawo kasuwa yasa aka kira masa zahradee ga Hjy agun bayan kowa ya tattara hankalinsa gun daya snn Abba yace zahradee".
"na'am Abba".
kasan tunda nake dakai a rayuwata bantaba niman wani abu a gareka bako?".
"Eh" Abba.
"k'uma bantaba dora maka wani abuda nasan bazaka iya bako?".
"eh"Abba.
"to Dan Allah na tambayeka?".
"Allah yasa nasani Abba na".
"yanzu a naka tunani yadda nake sonka nake fifitaka da sauran'year uwanka ko zaka fadimi dalilin dayasa nake maka h'aka?".
"him' Abba kenan nasan sbd soyayyar da kakemin ne yasa h'aka.
"bayan h'aka fa?".
"shinedai nasani".
"son kenan sbd kyautatamin da kakeyi ne da k'uma tunda nake dakai bantaba saka wani abu ka musantami ba ko ba h'aka bane?".
"murmushi kawai zahradee yai.
"snn Abba yace a yanzuma umarni ne zanbaka ba niman iziniba son' sbd na duba duk cikinku kaine kafi dacewa dashi...
"cikin rawar jiki zahradee yace Abba f'adi koma menene shi insha Allahu zanyi maka shi.
"a'a son kafin na f'adi saikami alkawarin babu musu tsakanina dakai.
"insha Allahu Abba bazan taba musa makaba' bana fatan Allah yakawo ranar da zaka umar ceni da abu nai maka musu.
"allahamdull' ngd son.
"dama mgnr aure...
"aure Abba?".
"Eh" aure".
" ne muringa mu gama mgn da iyayen yarinya' yanzu ku muke jira kawai musa rana.
"amma Abba"...
"a'a"son kada muyi h'aka dakai.
"tun daga snn zahradee besake mgn ba".
"yanzu koda zuwa gobe ne sai kaje ku daidai ta' k'uma ka tabbatar kasiyewa kanka girma a gun yarinya daraja' kada kaje ka aikata abinda zaisa uban yarinyarnan ya daina gani girmana.
"son idan h'aka ya kasance wlh bazaka sake ji dadina ba.
'to Abba zankiyaye.
"tashi kaje Allah yai maka albarka.
"amin ngd Abba".
"bayan fitar zahradee ne Hjy ke tambayar Abba yadda sukai da Alhj Musa' Abba ya zaiyana mata duk yadda sukai Hjy tai murna sosae h'ade da cewa amma Alhj idan sun daidai ta tsakanisu ba lkc me tsayi za'a saba ko?".
"Eh" nima h'aka nakeso' shiyasa ma naiwa Alhj Musan mgn' shima yace h'akan yayi.
"to alhamdullh' Allah ya shige mana gaba".
'min Hjy".
"tunda zahradee yashige daki kwanciya kawai yai batare da mgn ba'Aisha tai tambaya har tagaji amma zahradee be tanka mata ba' da ta gaji da tambayar kwancita tai h'aka suka kwana.
"da yamma bayan su dawo kasuwa zahradee na kwance a dakinsa around 8-20 Abba ya tura Hjy ta kirasa sakamakon duk wayayinsa a kashe suke.
"koda Hjy taje a bakin kofa ta tsaya snn tai sallama' Aisha dake kwance ne tazo ta bude'gani Hjy yasata dukawa tace snn Hjy.
"yawwa snn' ina mijin naki?".
"yana ciki".
"kice masa abbansa yana kira".
"to Hjy".
"da sauri tamike ta koma cikin dakin ta sanar dashi Abba na kira" Dan karamin tsaki yai hade da mikewa.
"toilet ya shiga ya watsa ruwa snn yafito batare daya shafa mai ba wadrop yaje ya bude ya dauka wata dankareriyar shadda lemon green yasa snn ya dauki turare ya feshe jikinsa dashi hade da kwashe wayoyinsa ya zuba a aljihu.
"shiru Aisha tai tana kallonsa kawai sbd mmki irin wnnn kwalliyar.
"har yakai bakin kofa' tana zahradee ina zaka a irin wnn lkc ga k'uma wata uban kwalliya da kasha h'aka.
"murmushi yai h'ade da dawowa ya rungumeta snn yace I'm srry baby Abba zaya aikeni tun jiya g'idan wani abokinsa bansamu zuwa sai yanzu amma kiyi hkr bazan dade ba zandawo.
"to shikenan saika dawo' but pls dear take care of ur self.
"OK I'll" tnx.
"har zahrdee yakai bakin kofa da sauri Aisha tace au!! zahrdee ga key din mortar ka.
"yana amsa ya fita gun Abba yafara zuwa son har kafito?"
"Eh" Abba nafito'zantafi kenan".
"a dawo lfy k'uma Dan Allah a kiyaye.
"to Abba".
"zahrdee yana fita supermarket ya nufi yana isa kayane ya diba na tashi hankali kamar su turarika mayuka sabulai sweet chocolate dai sauransu ya hada snn ya karisa gidan su zainab.
"a bakin yai parking snn yafita zuwa cikin g'idan lkcn Alhj Musa da matarsa mahaifiyar su zainab da kishiryata duk suna parlour zahrdee yai sallama.
"Alhj Musa ne yai masa izini daya kariso cikin parlour' yana shiga dukawa yai cikin girmamawa ya gaidasu kansa na kasa.
"dukkansu suka hada baki suka amsa hade da tambayarsa iyayensa.
"Alhj Musa yacewa Hjy Hulaira kishiyar mmn zainab taje ta sanarwa zainab tai bako.
"batare da bata lkc ba ta mike da zafin namarta ta shige ciki.
"gani h'aka zahrdee yace Abba ni zantafi' Alhj Musa yace to zahrdee idan kaje ka gaidamin iyayen naka.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 38