g'idan shu'aibu ba' Aisha kinfi kowa sani yadda muke son juna' shiyasa na fita harkanta' gani h'aka sai taga kamar tsoronta nakeyi' taci gaba da fadimi irin mgnr' ranar data kureni nima na f'adi mata abinda yake fadimi' hnklinta ya tashi yana dawowa ta tirkeshi ina kwance a daki ina jinsu' to kinga da banyi hkr bafa"
"Dan Allah Aisha kiyi hkr Ku zauna lfy da Zainab k'uma ki nunawa zhrdee yai adalci a tsakaniku"
"shiru Aisha tai tana rauraran ubaida"
"k'uma yaya mgn ciki ki?"
"wani ciki k'uma?"
"da farko lkcn da kika auri Nasir inace kince kintaba samu ciki?"
"eh nasamu"
"bayan fitarsa kinkara samu wani?"
"baki sakeba?"
"eh"
"kafin kiyi barine kikayi ciwo ko baya bari ne"
"kafin nayi barine"
"bayan h'aka k'uma baki sake samu wani ciki ba"
"to idan ba wani ikon Allah ba zaki iya samu ciki"
"meyasa kikace h'aka ubaida?"
"kintuna Rabi'a Zakariyya da kai secondary tare"
"eh na tunata"
"kinsan tun bayan aurenta da tai wani ciwo akace bazata haihuba"
"to yadda ta haihu' wani ciki nema da'ita"
"Allah da gske ubaida?"
"Allah sarki na tayata murna"
"to yanzu abinda yakamata muyi shine zanyi kokari na tambayi Bbn Abba yabarni naje g'idan ta na tambaya maki ita wani hospital ne sukaje da mijinta har suka samu waraka"
"anya da gske kina gani zansamu kuwa?"
"ke matsalata dake rashin wayo' me zaihana tunda da farko kintaba samu da kamar tun farko baki samu bane sai kice"
"to shikenan ngd sosae kawata shiyasa nake sonki"
"dariya sukai"
"amma Dan Allah Aisha ku zauna lfy da Zainab' bakisan rashin zaman lfy a g'idan magidanci yana rufe masa kofofin samuba?" dan Allah ku rungumi mijinku ku zauna lfy da abokiyar zamanki' ko mijinku kofofin samusa yakara budewa' yanzu ma kenan be rageku da komai ba' ina ga yafi h'aka?" Allah ya baku miji kyakkyawa ga kudi ga kyau kamar shine yai kansa' har gara ma Zainab tunda ita farace tas' ke kuwa f...
"kinaso kice ta fini kyau kenan?"
"a'a ni banceba"
"to yanzu meye lfy?"
"lbrin me?" h'aka kawai nabaki kizo kisa zhrdee na ihu' dariya sukai h'ade da tafi"
"daukowa tai ta bawa Aisha wanda zata bata snn sukai sallama' da yamma zhrdee yazo ya dauki Aisha suka koma g'ida' kai tsaye dakinta suka shiga Aisha na ije mayafinta taje da sallama d'akin zainab' Zainab na jinta amma ta kyale da Aisha taji shiru ta dauka ko bcc ne tai yasata ta koma d'akin ta' ta shiga toilet yi fitsari taga period yazo mata yatsa ta ciza sbd bayaso h'aka ba"
"fitowa tai ta shirya jikinta' shiko goge wanka yashiga yai yasa kayan bcc yazo kwanciya yau kam dole a saurara' shima kansa beyi dadi ba' dan a hannu yake' h'aka ya matse suka kwanta"
"washe gari da safe bayan zhrdee ya fita kasuwa Zainab ta lallaba tafito kitchen SBD yunwa takeji' itama Aisha ta fito daga d'akin ta zuwa kitchen tana gani Zainab a kitchen tace Zainab ina kwana"
"can kasa ta amsa da lfy klau' daga sann bata sake tankawaba sbd mgn ma aiki take gani"
"Zainab lfy kuwa?"
"banza tai da'ita"
"tana diban ruwan zafi takoma daki' shiru Aisha tai tana kallonta"
"tunda Zainab tashiga daki bata sake fitowa ba' har dare' ko abinci batayiba.tana kwance kawai tana faman juyi a gado ga jikinta yafara kunburi' tana kwance har zhrdee ya dawo kasuwa saida yashiga d'akin Aisha suna gaisa h'ade da hira snn yafita zuwa d'akin zainab' koda yashiga danita yai kwance' tace kadawo"
"nadawo ya g'ida?"
"lfy klau' ya kasuwa"
"alhamdllh"
"tubewa yai ya shiga wanka' duk a lkcn Zainab na kwance' har yafito bata tashiba Zainab tashi ki dauko min abinci na mana"
"banyi ba"
"sbd me?"
"banza tai dashi' shima dagaya haka be tankaba tea kawai ya h'ada yasha snn ya kwanta' can cikin dare Zainab taji zhrdee yana shafeta' da sauri tace lfy?" shiru yai yaci gaba' gani abinda yake da niyar yi da sauri tasa hannu zata turoshi' da karfi ya riketa h'aba zhrdee wann wani irin rashin imani ne? tun yaushe nake cemaka banida lfy amma baka kulani ba' Dan ma tsabar rainin wayo tun yaushe rabonka dani?" yadda yazo d'akin ga h'aka kake fita sai yau da Aisha ta haka kanta snn zakazo guna?"
"Dan Allah Zainab ki tsaya wlh ba h'aka bane"
"idan ba h'aka ba menene?"...
" kafin ta karisa Dan ne mata baki yai himmm".
"kuka Zainab taimasa sosae yana kwance yana numfasawa Zainab tace Allah ya'isa mgu kawai"
"wlh idan kika karami Allah ya'isa saina fasa maki baki"..
" koda safe Zainab bata iya tashiba tana kwance zhrdee yai wankansa ya shirya zuwa kasuwa' har Zainab tabar girki zhrdee beyi tunani kaita hospital ba"
"bayan kwana biyu gaba daya ta aune lallabawa tai ta mike zuwa d'akin Hjy' tana tafe tana kuka dakar take tafiya sakamakon zafin da kafarta yake mata".
" tana shiga d'akin Hjy kadan yarage ta f'adi da sauri Hjy ta tareta tana fadin lfy Zainab meya sameki h'aka? "
"Zainab na kuka tace banida lfy ne"
"kamata tai ta zauna tana kare mata kallo taga tuburin da tayi"
"daukarta tai zuwa hospital' tana isa takira Abba ta sanar dashi gasu a hospital snn ta sanarwa zahradee' cewa yai gashinan zuwa' suna shiga gun doct ya dubata yace jinitane ya h'au sosae k'uma tana bukatar hotu' daki aka kaita a take doct ya samata drip da alluran bcc"
"Abba da zhrdee sukazo tare a waje Abba yatsaya zhrdee ya shiga ciki d'akin' gani Zainab na bcc yasa Hjy tace muje waje' suna fita tace garin yaya Zainab ta zama h'aka?"
"shiru yai yana sushe2" Hjy tace ba dakai nakeyi ba??????
📖🖊
☘☘
☘
AURE IBADA NE
FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.☘.
🌳impacting valuable knowledge and entertainment is our concern🌳
story written by Mmn uswan
baki ko harshe basuda malaman da zasu furta waje godiya a gareku' a gskya naji dadin sosai yadda kuke bibiyan littafina mai' nagode nagode Allah yabar kauna da zumuci amin🤝,
TSOKACI
Ga masu cewa suna da nasama littafin be dace dashi ba' kuyi hkr ba haka bane rashin fahimtane' ko k'uma nace rashin sani menene AURE yake nufi yakawo h'aka' amma ga wanda yasan me ake kira AURE k'uma me AURE yake ciki tabbas yasan tana cike da kalubale kala kala' walau ka'auri wanda kakeso ko k'uma wanda bakaso' shiyasa tun farko idan baku manceba na sadaukarwa wanda Allah ya jabceta ta hanyar AURE k'uma ta cinye zarabawan' Dalilin dayasa nasama littafin suna kenan AURE IBADA NE.
Dan haka Allah yasa mudace amin.
4⃣1⃣
"sann zhrdee yace dama cewa nayi ta jirani naje kasuwa na dauko abu snn mutafi asibiti"
"idan na tambyeta tace ba haka bane fa".
" haka nema Hjy k'uma ki tambyeta"
"to shikenan' ni zanshiga daga ciki'"
"to kawai zhrdee yace' Hjy na shiga zhrdee ya zauna da Abba suka fara hira"
"Zainab bata tankaba sai yamma snn ta falka lkcn drip d'in dake jikinta ya kare' Hjy ta zare alluran snn ta dagota ta zauna sai faman sannu Hjy kecewa Zainab' tace zakici abinci?"
"kai kawai Zainab ta kada' abaki tea' tasake kada kai' to me zakici?"
"Zainab sai hawaye".
" gani hak yasa Hjy kwaleta kawai' a cewarta maybe bakinta babu dadi ne"
"bayan magrib yan'gidan su Zainab sukazo bbnta da inna Hulaira dasu mami'har d'akin abbanta yashiga gani gani yadda ta koma yasashi nuna bacin ransa a fili yana f'adi har yana cewa abashi ita sutafi g'ida"
"daga Hjy har inna hkr kawai suke bashi h'ade da cewa hawan jinine amma da zaran ta sauka shikenan zata dawo normal yadda take"
"himm kawai yace snn yace Allah yabata lfy"
"Zainab na kwance tanaji duk abinda abbanta yake f'adin' kwallane kawai ya gangaro mata ta gefen ido sbd su sake meda mata da wani drip d'an k'uma"
"inna dake gefenta kusa da'ita take share mata hawaye' ido kawai abbanta ya zuba mata h'ade da tunani kala2 a zcyrsa gani shirun da yai be yasa inna jansa da hira"
"zhrdee be koma g'ida ba sai bayan sallar isha sbd bayan ya yabar hospital shida Abba kasuwa ya koma yaci gaba da harkokinsa' koda Abba ya lekashi a shago yana tambyarsa da wani lokacine zai koma hospital yace Akwai abinda takeyine yanzu amma yana kammalawa zaikoma' to kawai Abba yace snn yakoma nasa shagon".
"zhrdee be sake leka Zainab ba koda ya tashi daga kasuwa g'ida ya koma daidai da lkcn dasu Abba dasu yya Shamsudee suma su dawo daga nasu kasuwa duk suka gaisa h'ade da tambyarsa me jiki"
"yace da sauki" shigewa ciki sukai suda Abba' shikuma ya shige d'akin gimbiyarsa Aisha' lkcn tana zaune tasha kwanlliyarta ta hakince akan cushion tana jiran ya dawo' duk da tasan ba'ita ne da girki ba amma be hanata amsar mijinta ba"
"zhrdee yana shiga a guje taje ta rungumesa' shima rungumeta h'ade da cewa baby na gskya kinyi kyau sosae' murmushi tai snn tace Allah ko nawa?"
"Eh'mana Aisha ta"
"to ngd"
"murmushi tai masa snn ta amshi jakar hannunsa suka karisa ya zauna' ruwa ta dauko ta bashi' bayan ya shane take tambyarsa jikin Zainab"..
"cikin mmki yace waya sanar dake Aisha ta?"
"Amatullah ne ta sanar dani lkcn zasu tafi sch k'uma Hjy batanan g'ida babu komai sbd takai Zainab hospital"
"eh h'aka ne' naso sanar dake amma k'uma...
" amma k'uma me?"
"babu komai"
"zhrdee kenan' to menene Dan ka sanar dani?" nima naso tafiya na dubata amma k'uma nace bazan fita ko'ina ba bada izini mijina ba".
"ido kawai ya zuba sbd jin dadin mgnrta"
"gani irin kallon da yake mata yasata sa hannu ta shafe masa fuska' da sauri yasa nashi hannu ya jawota jikinsa ta fado matsota yai yana mata cakulkuli tsalle take masa a jiki tana dariya taso guduwa amma takasa' gani tana kwallane yasashi kyeleta' da sauri ta mike tabar jikinsa"
"saida ta numfasa snn tace to yanzu yaya za'ayi?"
"kamar yaya Aisha ta?"
"nifa banyi abinci ba"
"why?"
"uhmm' uhmm'me?"
"just like that"
"konw prbm tunda yau h'aka kikaso mijinki yai Azumi dare' mikewa yai ya h'au gado ya kwanta"...
" da sauri Aisha ta kamosa tana f'adin wlh wasa nakeyi ".
" hannunsa ta kamo tana ja' cikin wasa yace a'a yau Azumi zanyi tunda h'aka matata keso' a'a Dan Allah katashi kaji' jawosa tai ya mike snn taje ta kawo masa abinci".
"yanaci suna hira' amma idan kagama ka huta saimuje gun Zainab mu dubo jikin nata ko?"
"fuska a daure yace nagaji bazan iya zuwa ba"
"Dan Allah kayi hkr ka daure mana muje"
"kiyi hkr kawai Aisha"
"kamar yaya?"
"kibar mgnr zuwa nan kawai"
"Dan Allah kayi hkr ka daure muje kasan dai idan mukayi h'aka bamu kyauta bako"
"ke kikasan wnn k'uma"
"duk da taji dadin f'adin h'akan da yai amma ta matse tana cewa h'aka zhrdee wani irin mgn kakeyi h'aka? tunda ka'iya yiwa Zainab h'aka wataran nima kana zuwa guna".
"hanlalinki daya kuwa Aisha harke kinasa ran Akwai ranar da zan walakantaki?
"kwarai kuwa' tunda ka'iya yiwa Zainab".
" ita Zainab d'in tafikine a guna?"
"kawarai kuwa"
"sbd me"
"uwar ya" ya"kace ita"
"pls Aisha expln to me the wy I'll undstn"
"OK" abinda nakeso ka fahimta shine Zainab matarka itace uwar ya"ya"ka tunda tana dauke da cikinka a jikinta' koda yau kace ka saketa baku rabuta sbd kunriga ku h'ada jini' amma nifa idan yau kace ka sakeni shikenan mu rabu kenan tunda ba h'ada komai dakai ba' Dan h'aka Zainab ba abin walakantawa bane a gunka"
"cikin fushi zhrdee ya mike yabar abincin da yakeci h'ade da cewa kada kisake fadimi mgnr banza irin wnn' ba h'aka ba wlh ba'a jimu dake"
"cikin taushin murya tace to shikenan insha Allahu zan kiyaye' mikewa tai h'ade da daukar kyale tace tunda hakane kace ka gaji bari naje na shiga taxi nadubo jikinta juyawa tai takami hanyar fita".
" tsawa ya daka mata kitsaya' bazaki tsaya ba? ko badake nakeyi bane Aisha"
"duk tanayine idan taga abinda zaice"
"gani bata tsayaba da sauri yaje ya fisgota ta dawo ciki snn yace waya kitsaya na kaiki' amma sainayi wanka tuku" to tace' toilet tashiga ta h'ada masa ruwan wanka yashiga yai' yana fita jallabiya kawai yasa suka fita zuwa hospital"
"lkcn idonta biyu suka shiga da sallama Zainab na jingine a hango gani shigowarsune yasata rufe ido da sauri' har kasa Aisha ta duka ta gaida Hjy da inna
"da fara'arsu suka amsa tana' Aisha tace ya maijikin?" jiki da sauki' Allah ya kara sauki'duk sukace amin"
"har cikin zcyr Hjy taji dadi sosai da gani Aisha a hospital tazo gaida Zainab"
"zhrdee dake tsaye shima dukawa yai ta gaidasu inna tace masa ya maijiki?"
"murmushi kawai yai"
"Hjy da inna suka fita"
"suna fita Aisha taje kusa da Zainab daidai kafarta ta zauna' shiko zhrdee kujeran bota dake gefe ya zauna yaci gaba da latsa wayar dake hannunsa' Aisha tace Zainab ya jiki?"
"batare data b'ude ido ba tace da sauki' Allah ya kara sauki' shiru Zainab tai bata amsa ba'snn shima zahradee yace ya jiki?"
"da sauki tace"
"daga snn besake mgn ba'itama lallabawa tai ta kwanta h'ade da kauda kanta gefe".
" Sufi thirty minutes babu Wanda yai mgn tsakanisu hatta Aisha da zhrdee d'in' mikewa yai yace tashi muje"
"ina?"
"g'ida mana?"
"nidai inda zaka yarda dasai na kwana da'ita Hjy da innarta suje g'ida'idan yaso da safe sai nadawo"
"daure fuska yai snn ya daka mata tsawa da Dan Allah kitashi muje"
"jin tsawar da yai ne yasa Hjy shigowa h'ade da tambyar lfy?"
"a'a dama cewa nayi yabarni na kwana da Zainab idan yaso ku sai kutafi g'ida ku huta"
"aiko da kin kyauta wlh"
"itama inna shigowa tai' gani ta shigone yasa zhrdee fita h'ade da cewa idan kinga dama ki biyoni".
"gani h'aka yasa inna cewa babu komai kutafi kawai tunda inanan' Hjy dake gefe saida taji wani iri"
"da sauri Aisha ta bisa zuwa mota' shiko goga zama yai a mota tana jiranta' tana shiga yana tada mota suka nufi g'ida' suna cikin tafiya ne Aisha tace gskya zhrdee baka'kyau ta"..
" Dan Allah kada ki fadimi mgnr bazan"
"wani irin dadi ne ya lullube Aisha sbd gani abinda zhrdee yaiwa Zainab'amma a fili tace amma dai baka kyauta ba"
"tsaki yai be tanka taba har suka isa g'ida'
" bayan goma ne yya Shamsudee yaje ya dauko Hjy' inna kawai ta rage' bayan tafiyar Hjy ne inna ta tada Zainab zaune ashe tun shigowar su Aisha ta lura da halin da Zainab ke ciki' bayan ta zauna ne inna take tambyar Zainab abinda ke damuta"
"shiru Zainab tai taci gaba da kuka' gani ba lfy ne da'ita ba yasa inna bata matsa mata da tambaya ba hkr kawai ta bata"
"satin Zainab biyu a hospital inna ke kwana da'ita' ita k'uma uku gani yanzu Aisha na tafiya yasa bata cika zuwaba' saidai tatura su Amatullah suje tareda Aisha' idan basuda lecture ranar har dare suke kaiwa' idan zhrdee yana dawowa daga kasuwa sai yabiya ya daukosu"
"Aisha na zuwa gun Zainab ne kawai amma badason ran zhrdee ba'dan dai bashida yadda zaine kawai ya hanata"
"inna har g'ida tarako Zainab saida ta dan jima snn takoma g'ida"
"da yamma bayan zhrdee yace dawo kasuwa ta tarasu a parlour su' ga Zainab ga Aisha snn kuma ga zhrdee"
"snn Hjy ta fara da Zainab'ke Zainab"
"me kika akan jikinki?"
"a'a dama cewa nayi bazan iya girki ba' sbd koda tafiya nayi kafata zafi yakemi' kamar zai fashe'y yanzu tafiyar danayi daga daki zuwa parlour ba karami zafi naji ba"
"to kai kaji abinda Zainab tace".
" to Ai Hjy ni bansan yadda akeyi ba"
"to ke Aisha aike kin zauna da kishiya".
" Eh " h'aka ne"
"to ina sauraranki".
" Eh dama idan abu yazama h'aka tunda lalurace aba sauke mata girki"
"bayan h'aka fa?"
"shiru Aisha tai"
"Ina sauraranki Aisha".
" still shiru"
"to tunda abu ya zama h'aka' ita k'uma lalura tana kan kowa' ke Zainab daga yau na sauke maki girki' k'uma miji bazai kwana a d'akin kiba sai lkc lkc zairinka shigowa dubaki' ke Aisha kici gaba da girki har Allah ya dauketa lfy"
"to Hjy"
"ke Zainab kin amince da h'akan?"
"eh na amince".
"to shikenan k'uma Dan Allah kurinka hkr da junanku"
"duk suka amsa to"
"ke Zainab idan kina bukatar wani abu a marmari ki sanarmi ko Aisha sai a dafo maki"
"to Hjy ngd"
"k'uma ki kula da magani sosae"
"bayan Hjy ta koma bangaren su ne Aisha da zhrdee suka koma daki' itako Zainab saida ta juma a parlour snn takoma d'akin ta"
"tun daga lkcn Zainab ta daina girki duk bayan sati biyu Hjy kesa zhrdee ya kai medata hospital kamar yadda doct yace' bayan suyi bincike da zasuyi su gama sai ya dawo da'ita g'ida snn ya tafi kasuwa' ko parlour bata fita shiyasa duk safe Aisha ke shiga su gaisa hakama da yamma' wani lkc kamar da safe kafin yafita kasuwa idan Aisha zataje d'akin zainab sai yahana ko k'uma yace tatsaya ta kare masa abin breakfast idan yafita sai taje tayi abinda zatayi tunda Zainab tafishi".
"jin h'aka yasa masu yawanci lokaci sai bayan yafita kasuwa take zuwa ta dubata' mgnr abinci kuwa duk da Aisha tana samata amma be hana Hjy samata ba' mundun tai abinci da kwaryan Zainab a ciki' mgnr kayan murmari kuwa inna da kanta take mata miyar nama ko kaza ko k'uma kifi tace akawo mata' tunda bacin abu me gishiri takeyiba sbd kunburin da tai' koda ankawo saidai tace Aisha ta dauka tunda zhrdee ba shigowa yakeyi sosae ba' sai yakai kwata uku be lekataba' banlema tunda tace bazata iya girki ba shikenan kakarsa ta yanke saka sai yaga dama yake lekowa"
"wani lkc saiya kwana uku wani lkc k'uma kwana biyu snn ya lekota' Aisha kuwa duk safe take lekawa' mgnr abinci shima h'aka duk lkcn da tai saita sa mata koda babu yawa saidai ba kasafai takeyi ba' saida yamma sbd lkcn ne mijinta ke dawowa' a cewarta k'uma bazata shiga kitchen sbd Zainab ba"
"ita Zainab h'akan be dameta ba sbd baci takeyi sosae ba sbd gishiri' shima abbanta kamar yasan halin da take ciki yasashi siye mata kayan tea manyan gwangwanaye ya aiko mata dasu' mgnr rashin shigowar zhrdee gunta wani zcy tace jeki ki sanarwa Hjy' wani zcy yace a'a kidai bari idan tashigo' wani zcy yace kyaleshi da halinshi kawai"
"zama a b'akin gado tai taci gaba da kukanta' taiga zhrdee yai sallama' ganita yai tana kuka' kusa da'ita yazo ya zauna kusa da'ita a b'akin gado h'ade da cewa lfy koda jikine?"
"bazan tai dashi taci gaba da kukanta' kome yagani oho jawota yai jikinsa ya rungumeta yana lallashinta ya'isa haka kinji' Dan Allah kidaina kuka haka hannu yasa yana share mata hawaye h'ade ta jijjigata alamar rarrashi"
"saida yaga ta daina kukane ya tashi ya dibo mata ruwa h'ade da dauko ledar magani daya shigo dashi"
"menene wnn?"
"maganiki ne Wanda doct ya rubuta asiye' bansamu na siye bane sai yau"
"shiru kawai tai tana kallonsa' da kansa ya bare magani ya ciro yasa mata abaki snn ya dauko cup d'in ruwa yasa mata tahade' saida yameda cup d'in ta'ije snn yasa hannu ya ciccibeta ya kwantar da'ita ya gyara mata kafa' shima hawan gadon yai yafara yimata tausa".
"da sauri tace zafi' h'ade da janye kafarta"
"ohhh!! srry' bansan akwai zafiba"
"dawowa yai ya kwanta kusa da'ita h'ade dasa hannu yana shafe mata ciki' Zainab najin h'aka takara lafewa a jikin zhrdee'ita kanta batasan lkcn da bcc ya dauketa ba"
"Aisha nacan na jiran dawowar zahradee' shiru da taji kamar tabishi d'akin taga ko lfy' can k'uma tace baridai takara jiransa tagani"
"zhrdee yana can gun zhrdee shima kansa besan lkcn da bcc ya daukesa ba' Aisha tayi jira har tagaji bcc ya dauketa' koda zhrdee zai falka ji kawai yai ana kiran asalatu' yana duba agogo 4-30 itama Zainab lkcn ta falka koda ta b'ude ido gani zhrdee tai yana rungume da'ita'jin ta motsa yasashi cewa kina bukatar wani abu?"
"a'a"
"OK"
"gani biyar yakusa yasashi mikewa ya sauka daga gadon snn yasa hannu ya dagota ta mike' dauko mata zani yai zai daura mata' a'a bashi kawai"
"hannu tasa ta amsa ta daura zhrdee ya rike mata hannu suka shiga toilet da kansa yai mata alwala tana yana gamawa yai nasa snn yasake kamota suka dawo bedroom' sallaya ya dauko ya shinfida mata snn yaje ya dauko hijab da wani zanin da zata canza da kansa ya canza mata zani h'ade da sanya mata hijab' dayake a zaune take sallar kamota yai ta zauna shikuma ya nufi masallaci"
Zainab na idar da sallah takoma ta kwanta' shima zhrdee yana dawowa d'akin Aisha yashiga lkcn ta idar da tana sallar' kallo daya yai mata yasan tana cikin fushi' bebiye tataba yace ina kwana Aisha ta?"
"can karkashi ta amsa da lfy"
"kintashi lfy?"
"karamar tsaki kawai tai masa"
"murmushi kawai yai sbd yasan kishine ke damuta"
"Dan Allah hadami tea nasha"
"wa!!! Allah ya sauwake' kajecan inda ka kwana tabaka tea kada"
"ta'iya kwana da miji banle h'ada tea ne zaimata wuya?"
"zhrdee najin h'aka ya mike yakami hanyar fita' gani har yakai b'akin kofa batace dashi komai ba'suna h'ada ido ta hurga masa wata uwar harara' fita kawai yai zuwa d'akin zainab' koda yashiga tana kwance tace kadawo?"
"nadawo' yajikin?"
"ina kwana".
" lfy klau ya jiki"
"jiki da sauki"
"Allah ya kara sauki".
" amin ngd".
"b'akin katifa ya zauna kusa da'ita' ita k'uma yunkurawa tai zata tashi"
"da sauri yace mezaki"
"wanka nakeso nayi"
"to tsaya' mikewa yai ya cire jallabiyar dake jikinsa yarage dagashi sai gajeran wando snn yasa hannu ya dagota ta zauna' cire mata bes d'in dake jikinta snn ya dauko towel ya daura mata yasake riketa ta tashi tsaye yacire ragowar kayan cikin'suka nufi bathroom' suna shiga ya cire mata towel d'in da take daure dashi ya cire nasa saida ya gama cudanyata da sabulu snn yai nasa yana gamawa ya ije sosan yana rike da'ita ya sakar masu ruwa akah"
"zhrdee na rungume da'ita ruwan yagama wankesu tass snn yakashe dauko towel yai ya daura snn itama ya daura mata' karamin k'uma ya goge masu jiki dashi' yana gamawa ya kamota zuwa bedroom tana zaune a b'akin gado zhrdee yana duke a gabanta yana shafa mata mai"
"itako Aisha tanacan tayi fal kamar zata fashe sbd fushi' a zcyrta tana f'adin manafuka alguguma dama ciwon karyane tunda har ta'iya kwana da miji' zaune take ita kadan tana faman cira"
"zhrdee yana gama shafawa Zainab shama ya shafa nasa yakwashi mai yameda kan mirrow' ido kawai Zainab ta xubawa zhrdee h'ade da mmkin anya kuwa zhrdee d'in data sanine? kodai wanine ba shiba?" idan ko shine Ashe dama akwai rana irin yau zaizo nagani' lalla ashe kuwa mijina yana sona idan ko hakane dole na sake dan tse na nunawa mijina soyayya k'uma nayi hkr da duk wata kalubalen da zaizo ya shiga tsakanina dashi"
"wani irin sanyi taji ya ziyarci zcyrta yau kam babu ciwo dan jama take tawarke garau' k'uma a yau take kara jin so zhrdee' shiru da tai batasan lkcn da hawaye na dadi suka zubo mata ba"
"ji kawai tai ana cewa subhnalallah lf"
"da sauri ya kariso gunta ya duka a gabanta yana f'adin lfy?" kodai jikin ne"
"a'a"
"to menene?"
"babu komai"
"idan jikin ne kiyi mgn sai mu koma hospital"
"a zcyrta tace duk da ciwon dake damuna amma ciwon sonka yafi wanda ke damuna'a fili k'uma tace a'a babu komai"
"gani har a lkcn six thirty ne yace to zo mu kwanta' kamota yai suka kwanta yana rungume da'ita yana f'adin Dan Allah Zainab
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 38