gida.
"ko sauraran Nasir batayi taja yaranta banle tasan abinda yake fadi tai tafiyarta.
"kwanan Aisha biyu suka koma gida' abinka da mara jiki sai takara ramewa sosae sai tsayin.
"kafin sati biyu Aisha taji sauki sosae kamar ba'ita ba sai dai ramar da tayi' yau Nasir a g'idan ta yake da safe ya shirya yatafi office sbd har yanxu E. F. C. C. suna bincike a kansa.
"Hakan yasashi fita da sassafe' bayan ya fitane Aisha ta kwashe kayan daya bata ta kai kitcher taje ta gyara parlour snn takoma bedroom ta gyara sai da ta gama gyara ko'ina snn tashiga wanka.
"kafin ta fito taji motsin anyi parking din mota da alama kuma Nasir ne yadawo' amma kuma lokacin Dawowarsa beyiba sbd yanxu karfe gomane.
"hakan yasa tai saurin wanke sabulum dake jikinta towel kawai ta daura h'ade da sa hijab tafito parlour dan gani ko waya.
"tana isa parlour motar Nasir ta hango a gefe kuma bashi a parlour a take taji gabanta yai mummunar fadi.
'"juyawa tai tanufi dakinsa' koda taje tana knocking Nasir yana jinta amma yaki bude kofar' Aisha tai knocking har tagaji amma Nasir be bude ba' gani haka yasa ta fasa da kuka h'ade da kiran sunansa.
"jin kukanta ne yasa Nasir bude kofar tashiga cikin dakin' suna hada ido taga gaba daya ido sa yai jazir kamar garwashin wuta.
"Sake fashewa tai da kuka' shima Nasir kuka yakeyi' Aisha tana fadin dan Allah Nasir ka fadimin menene ke faruwa.
"shima zama yai dirshin a gabanta yaci gaba da kuka' gani bashida niyar fadi mata yasa Aisha kwanciya akan carpet tana birgima.
"Hannu Nasir yasa ya dagota ta zauna a gabansa snn yace Aisha' kinaso kisan abinda ke faruwane? Yace to zan fadi maki amma sai kimin alkairi nasan zanrasa komai a rayuwata amma inaso ki zamomi daya daga cikin abinda bazan rasaba.
"Cikin kuka tace insha Allahu nayi maka alkairin hakan.
"Snn yace Aisha E. F. C. C. sunyi bincike a ministry namu ana zargina da haddame kudi ta biliyoyin naira wanda nima kaina bansan iya adadinsu ba' yanxu da haka Aisha nimana sukeyi su kamani.
"babu abinda yake fitowa daga bakin Aisha sai innalailahi'wainna'ilaihim'raju'un.
"Nasir yace Aisha ba taba lokaci zamuyiba ki tashi nasa bilyaminu ya medaki garin kuma nima barin garin zanyi.
"Cikin kuka Aisha tace babu inda zani sai dai mutafi tare dakai.
"Nasir yace a'a Aisha.
"ihu Aisha tasa ta fada masa a jiki tana fadin Nasir wlh bazan iya rabuwa dakai ba sai dai mutuwa.
"Nasir yace a'a Aisha.
"Itama Aisha tace a'a Nasir
TOFA KUBIYONI KUJI YADDA ZATA KAYA TSAKANI NASIR DA AISHA
📖🖊
☘☘
☘
AURE IBADA NE
FASAHA ONLINE WRITES F. O. W ☘
MMN USWAN
I'm wait 4 ur cmm
👆
Hafsat Hausa Novel H2 fcbk A Gaskiya bani da bakin godiya a gareku sai dai Allah ya bar kauna sbd nvl din na idan bakuzo na daya ba to ko zakuzo ba biyu dan haka Allah yabar kauna da zumunci amin.
0⃣8⃣
"Nasir yace Aisha inaso ki saurareni d'kyau wlh Aisha bazan iya barinki a garin nan ba.
"Aisha baki da kowa saini' ni k'uma yanxu da h'aka da kike gani barin garin zanyi Aisha k'uma kinga be kamata natafi na barki a garin da bakisan kowa ba' shiyasa nace kibi bilyaminu ya medaki gun yar'uwanki.
"Insha Allahu idan komai ya lafa zanzo da kaina na daukoki mudawo' kinji Aisha.
"Aisha dake kwance jikinsa tasake fasawa da kuka tana fadin wlh babu inda zani.
"Nasir yace a'a Aisha katafi kawai.
"Aisha tace nifa na fadi maka.
"yace wlh Aisha nima na sukeyi ido rufe sutafi dani' idan har sukasan ina nan g'idan wlh zuwa zasuyi su tafi dani' shiyasa nakeso kibar nan kafin suzo kamani.
"kuka Aisha tasa tana cewa wlh sai dai su kamamu tare dakai amma bazan iya tafiya na barka cikin irin wanga halinba.
"Cikin fushi Nasir ya egijeta gefe ya mike h'ade da cewa ke wacce yarinya ce me shegen nacin tsoya' meyasa abinda nake duba maki baki dubawa kanki ne.
"Ana guje maki wahala baki guje wa kanki.
"Idan har suka kamani kikasan iya adadin shekarun da zanyi a prision tunda ni dai a yanxu da haka har ga Allah banida kudin da zanbiyasu' ba kudi bama ko duk abinda na mallaka a duniyar nan ne zasu kwashe wlh bazai biya kudin da suke tuhumana ba.
"Amma tunda kince nacine dake' k'uma ban'isa dake ba ni kinga tafiyata.
"Da sauri Aisha ta mike tana kallon Nasir' gani yasa kai be saurareta ba yai tafiyarsa babu ko waige.
"ihu Aisha tasa tana kiran ummata a guje tabi Nasir tasha gabansa h'ade da kankameshi taci gaba da kiran umma' hannu daya Nasir yasa ya fisgota daga jukinshi ya hurgata a tsakar parlour yaci gaba da tafiyarsa.
"Buguwar da Aisha tai da cushion yasa takasa kuka sai faman shure-shure takeyi da kafa.
"Har Nasir yakai bakin gate ko me yatuno kuma oho yasashi komawa da baya yashiga cikin parlour yadda yabarta haka yadawo ya sameta a gun kwance' hannu Nasir yasa ya dagota snn yace Aisha' Aisha daga ido tai tana kallonsa.
"Nasir yace kin amince zaki zauna dani a h'aka? Kai kawai Aisha ta daga masa' Nasir yace banida komai da kika sani a dah' Aisha da h'aka zaki zauna dani?
"Aisha tace eh' zan zauna.
"Nasir yace a'a fa Aisha ' kinga kinada ragowar kuruciyarki' be kamata na tauye maki hakkinki ba' a matsayinki ta yarinya mai kuruciya da jini a jika' ina tabbatar maki idan har kika rabu dani zaki iya samu wanda yafini Aisha.
"Cikin kuka Aisha tace a'a ni ina sonka a haka' k'uma zan'iya zama dakai koda kafi haka ne talaucewa.
"ido kawai Nasir ya zuba mata yana kallonta har takare' Bayan ta karene Nasir yasa hannu ya jawota jikinsa snn yace Aisha nagode da Allah ya azirtani da mace tagari irinki Allah yai maki albarka' yanxu kinga babu lokaci zomuje ciki duk wani acceses da kikasan nakine kikwaso mutafi.
"Aisha tace ina zamu? Nasir yace g'idan Fatima ne zankaiki ku zauna tare' ni kuma zan kauce zuwa wani lokaci' ko bazaki zauna da'ita ba.
"Aisha tace zan zauna amma dan Allah koda cikin dare ne kadan rinka lekowa kana dubamu kaji".
"Nasir yace naji Aisha ai dama bazan barku haka kawai ba ' idan banzo dan kuba ai zanzo dan yarana.
"Aisha tace to shikenan' tare suka kwashe kayan' gaba daya zibarenta ya kwashe mata da kayan sawarta ya zuba cikin wata karamar kit snn kaya kuma cikin karamar jaka ya zuba mata yaja zip ya rufe' hijab kawai ta dauka shikuma yana rike da jakar sukabar g'idan.
"Lungu Nasir ya dunga bida Aisha har sukabar cikin gari snn ya yanka ta daji' sakamako tsakani g'idan Fatima da Aisha akwai tazara sosae' hakan yasa Aisha tai tafiya har tagari amma da haka sukai ta tafiya har sukakai g'idan Fatima.
"Gani sun shigo Nasir na gaba Aisha na baya yasata cewa har abu yazo amma dai anji kunya' Nasir najinta amma be tanka mata ba' kai tsaye dakinshi ya kaita' bayan su shigane Nasir yace Aisha ga dakin da zaki zauna.
"Aisha tace to' snn yace zomuje na nuna maki lungu da sakon g'idan ko' to kawai Aisha tace' Nasir na gaba Aisha na baya ya nuna mata ko'ina snn suka koma daki' gani lokacin sallah yayi yasa Aisha cewa bari nayi sallah.
"Nasir yace Aisha nima zantafi akwai kayan abinci a kitcher' Aisha ta fasa da kuka h'ade da cewa yanxu ina zaka? Nasir yace nima bansan inda zanje ba Aisha' amma ina Allah ya yarda koda sau dayane a sati zansan yadda zanyi naxo na ganku.
"Ni inda ma zasu kwashe duk wata abinda na mallaka su barni cikin iyalina wlh Aisha yafimin kwanciya hankali.
"Aisha naji haka ta fadi kasa taci gaba da kuka.
"Fita Nasir yai h'ade da daga mata hannu yana mata bye bye' a guje Aisha ta bishi' gani haka yasashi fita da sauri h'ade da jan kofar ya rufeta a ciki.
"Fadi a kasa Aisha tai taci gaba da kuka.
"Nasir na fita daga dakin Aisha sukai karo da Fatima tace an dai ji kunya wlh' Nasir najin haka ya daure fuska snn yace Allah yasa dai kinsan ko ni waye' idan na kara jin bakinki wlh saina kwantar dake a nan.
"Fatima najin haka bata sake cewa komai ba' Nasir ya shige gaba h'ade da cewa zaki biyoni daki muyi mgn ko yaya?
"Batare da ta tanka masa ta bishi' sun kusan minti talatin a ciki snn yafito yai tafiyarsa.
"Itako Aisha da tai kukanta ta gaji tashi tai taje tai alwala tazo tafara sallah.
"Da yamma Aisha ta fito zata shiga kitcher dan girki' da sauri Fatima tace me zakiyi? Aisha tace abinci ne nakeso na dora.
"Fatima tace ba haka mukai da maigidanba' cewa yai idan nadafa na rinka sa maki iya bakinki' tunda ba dan kowa ne dake ba.
"Aisha tace shine yace maki haka?
"Bazan Fatima tai da'ita.
"har Aisha ta juya zata koma d'aki sai Fatima tace akwai abinci ki a kalla yana kitcher' k'uma idan kika cinye ke kika sani sbd harda na dare nayi' sbd ke bazansa wani sanwa a g'idan nan ba.
"batare da ta tanka mata ba shiga kitcher din tai taje ta dauko abincin tana tafe tana hawaye ta shige d'akinta.
"Tana shiga eje abincin tai a gabanta ta dauko wayarta d'an kiran Nasir' sai dai kasa!!! Koda tai trying sai tajishi swech off.
"medawa tai ta eje shi a gefe taci gaba da kukanta.
"washe gari da safe Fatima ta aiki yara sukai wa Aisha abin karyawa' na rana kuwa cewa tai harda na yamma ta hada' dan haka idan ta cinye to harda na darenta kenan.
"Aisha tace to.
"Da haka Aisha taci gaba da rayuwa a g'idan Nasir bata kula Fatima sbd damuwar rashin mijinta ma kawai ya'isheta' kuka kuwa dashi take kwana take tashi' shiyasa tabi tai rama sosae sbd yadda tasa damuwa a ranta' ba kamar Fatima ba' duk da yaran dake tsakani su amma ko'a jikinta.
"Bayan sati biyu cikin dare misalin karfe biyu saiga Nasir yashigo kai tsaye dakin Fatima ya shiga duk da tana gani dhigowarsa amma tai banza dashi kamar bata ganshiba.
"Nasir yai mgn har yagaji amma Fatima bata tanka masa ba' gani haka yasashi fita daga dakin ya koma d'akin Aisha' sallamar da Nasir zaiyi sai kunni Aisha' a birkice ta tashi' gani Nasir ne a guje taje ta rungumeshi h'ade da fashewa da kuka.
"Gani irin kukan da takeyi yasa Nasir daukarta kamar karamar yarinya har kan gado ya kaita snn yafara lallashinta.
"Cikin kuka Aisha tace ina ka shigane nake nimarka a waya amma baya shiga? Nasir yace eh ga wayar nan' hannu yasa a aljihu ya fito mata dashi ya nuna mata snn yace na kashene sbd kada su nimeni ta waya su sameni.
"Shiru Aisha tai tana jikinsa.
"Nasir yace Aisha ba komai ne ya kawoni cikin dare ga illa na sheda maku naji labarin gobe zasuzo bincike a g'idan nan' sbd duk abinda kika sani na wancan g'idan sun kwashe.
"Aisha tace Innalillahi'wainna'ilaihim'rahu'un' Allah umma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan.
"Yanxu yaya zamuyi? Nasir yace wlh nima Aisha bansan yadda zaiyi ba' shiyasa ma naxo na sanar daku duk wasu abubu naku masu mahimmaci ku boye.
"Aisha tace toni ina ne zankai sarkokin da kasiyemi? Nasir yace kefa macece kiyi dabaran nan naku na mata mana.
"Aisha tace a'a bari na baka katafi dasu ka boyemin kawai a inda kake idan komai ya lafa saika kawomi.
"Nasir yace a'a Aisha.
"Aisha tace katafi dasu kawai.
"Sai da yai shiru na dan mintoci snn yace to Aisha.
"Aisha na makale jikin Nasir har karfe bayan asuba' gani biyar tayi da sauri ya mike yaje yai wanka yadawo ya meda kayan jikinsa Aisha ta mike ta dauko sarkokin ta bashi' har Nasir yakai bakin kofa sai Aisha tabiyoshi snn take sanar dashi yadda sukai da Fatima akan mgnr girki.
"Nasir yace eh shine yace kada tai abinci da kanta sai dai ayi a bata sbd aikin g'idan da yawa ba lallane ta'iya ba' shikuma bayaso ta wahala.
"Shiru Aisha tai.
"Nasir yace ni zantafi saina sake dawowa.
"Aisha tace to shikenan' komawa tai ta shiga toilet tai wanka h'ade da alwala tazo ta fara sallah.
"Nasir yana fita dakin Fatima ya shiga ya sameta zaune akan sallaya tana lazumi' duk da shigowar da taga yayi besa ta yanke ba cin gaba da lazuminta tai.
"gani h'aka Nasir yace ni dai zantafi Fatima' a lokacin ne ta shafe addu'a snn tace yanxu dan Allah alhj abinda kakeyi ya dace kenan? girma fa kakeyi ba komawa baya ba' k'uma abinda kake aikatawa baka tsoron wataran a aikatawa yar'uwa?
"Nasir yace Fatima kenan yanxu sbd Allah me k'uma na aikata? ke kullum baki rabuwa da zargi' idan kina tunanin wani abu na kawo mata wlh ina shiga g'idan nan d'akin kine na fara shiga snn naje d'akin ta....
"shigawar yarane yasa takasa meda masa mgn' rungumeshi sukeyi suna baba oyoyo baba' baba ina katafi bamu ganka ba bb?
"murmushi Nasir yai snn yace doughter kenan wani aiyukane suka shami kai amma in Allah ya yarda nakusa kammalawa ina kammalawa zandawo mu zauna tare kinji ko...
"kafin ta b'ude baki tai mgn Fatima tace ke fita kinaba gun.
"Nasir yace nima tafiya ne zanyi saena sake dawowa.
"Banza dashi Fatima ta mike h'ade da tada kabbarar sallah taci gaba da sallarta' shima dayaga h'aka fita yai yai tafiyarsa.
"Itako Aisha tana idar da sallah alkur'ani ta dauko tafara karantawa' saida ta dade tana karantawa snn ta'eje tafara kwararowa mijinta addu'a h'ade da iyayenta snn ta shafe addu'a komawa tai gado ta kwanta amma ba bcc takeyi ba.
"Tunanin iyayenta ne ya f'ado mata a zuciya'ita kanta batasan lokacin da tasaki wani kuka ba' cikin kukan ta dauko wayarta ta duba ko akwai kudi a ciki' tana duba gani tai babu ko sisi' medawa tai ta eje kai da gwiwa ta h'aka taci gaba da kuka.
"Misalin 10AM Fatima na zaune a parlour taji shigowar mutani g'idan' da sauri ta mike d'an mekawa taga ko su waye.
"Tana lekawa wasu mutani ta gani turkaka duk mazaje ne su biyar' salati tai ta sanarwa ubangiji' kafin tarufe baki har su shigo cikin g'idan.
"Titsiye Fatima sukai a parlour h'ade da tambayar ina maigidanki? Cikin rawar jiki Fatima tace bayanan.
"Daya daga cikin su yace ina d'akin sa yake? Da hannu Fatima ta nuna masu' sukace da'ita muje' suna gaba tana baya suka shiga d'akin' suyi bincike iya bincikensu amma basuga komai ba' sukace muje naki d'akin a nan ne sukaga sarkokin zinare da sauran kaddarorin da baza'a rasa ba.
"bayan sun gama kwashewa suka koma d'akin Aisha' Aisha na gani sun shigo tace innalallahi'wainna'ilaihim'rahu'un' snn tace daga ina k'uma? ID Card d'an E. F. C. C. Suka nuna mata daga snn bata sake cewa komai ba.
"Suma suka fara seaching d'akin a d'akin ta kam basu sami komai ba' sbd tariga tabawa Nasir ya wuce dasu' sunyi bincike iya bincikensu amma basuga komai ba' ita ko Aisha tana gefe inba kuka ba babu abinda takeyi' Gani basuga abinda suke bukata ba yasasu fita subar g'idan.
"Suna fita Aisha ta fashe da kuka sbd yadda suka walakanta mata d'aki' itako Fatima bala'i tasa tana f'adin wlh sisi bazaiyi ciwon kai ba' idan sai anbiyani.
"Su iyayen sai faman nimanta sukeyi amma basu samuta k'uma koda sun kira wayar maigidanta shima baya shiga h'akan yasa hankalinsu ya tashi sosae' amma sai bbnta yace tunda anji shiru lfy ne' sbd lfy ne ke buya inda ba lfy da tuni anji.
"umma tace h'aka ne alhj' Allah ya tsare ita a duk inda take' alhj yace amin' komai menene tunda AURE NE insha Allahu bazata tagaiyara ba ' himm kawai umma tace.
"Bayan zuwan E. F. C. C. g'idan Nasir da sati daya misalin 12AM dai dai sai gashi ya shigo kamar daga sama' komada ya tabi kofa yaji a kulle yake gam da key'gani h'aka sai ya zaga ta dai dai window Fatima yana kwada mata kira' a gigice ta falka' jin muryar Nasir yasa taja dogon tsuki ta koma ta kwata taci gaba da bccn ta.
"Gani h'aka yasashi komawa gun window Aisha kira daya ta mike Nasir yace nine Aisha da sauri ta mike taje ta b'ude masa kofa ya shigo cikin d'aki' bayan ya zauna ne ta b'ude frg ta dauko ruwa ta bashi h'ade da cup' koda ta xuba masa ruwan a cup k'adin kawai yasha snn ya'ije cup din.
"Har kasa Aisha ta duka ta gaidashi' amsawa yai babu yabo babu fallasa snn ta zauna' karewa d'akin kallo yai snn yace ya naga d'akin kamar a birkice.
"A lokacin ne Aisha ta sanar dashi mutani da sukazo bincike' Nasir yace nasan za'ayi h'aka amma ni dai banida abinda zance sai Allah ya kyauta.
"Aisha tace amin' ni inda zasu kwashe komai su barmin kai wlh zanfi kowa murnar h'aka amma sbd Allah wanga wacce irin rayuwane h'aka' mutum da g'idan sa da iyalinsa amma ya gagaresa zama.
"murmushin yake yai h'ade da cewa Aisha har yanxu ke yarinya ce' ko zan kwana ina maki bayani ba lallane ki gani ba' amma Allah ya naganki wani iri kodai bakijin dadin zama da Fatima ne? Ko k'uma wani abu take maki.
"Aisha na hawaye tace babu komai'kewarka kawai ke damuna'da k'uma kewar su yar'uwa na.
"Nasir yace shiyasa nace bilyaminu ya medaki garinku idan komai ya lafa ni da kaina zanzo na daukeki.
"Da sauri Aisha tace a'a ni babu inda zani na barka' ni nafiso na zauna dakai' Nasir yace to ai yanxu ba tare muke ba' sai lokacin dana samu hanya nake zuwa inda kike' Aisha tace eh na yarda a h'aka inda har zaka rinka zuwa lokaci - lokaci ina ganika.
"Shiru Nasir yai na dan wani lokaci snn yace Aisha kina sona?
"Kai kawai ta daga masa alamar eh.
"Nasir yace gobe duk yadda zanyi sai nayi na nimi kudin mota da zai kaiki garinku' ki shirya kayanki da safe cikin dare daidai wanga lokacin zanzo na daukeki mutafi na saki a mota kafin safe insha Allahu nasan kin isa garinku.
"A sbd yasa zansaki a motar haya sbd duk wasu yaran aikina da kika sani yanxu da h'aka babu kowa' kowa ya kama kansa sbd nima yanxu da haka ta kaina nake dan mafaka nake nima.
"shiyasa zan saki a motar haya ki tafi gida.....
"Cikin kuka Aisha tace ni babu inda zani' zan zauna a h'aka idan har zaka rinka lekowa ina ganika.
"Gani irin kukan da takeyi yasa Nasir dagota yai ta zauna akan cinyarsa snn yace waya kukan ya'isa h'aka banaso na sake gani wanga hawayen' hannu yasa ya share mata tass snn yaci gaba da cewa yanxu Aisha kin zabi ki zauna h'aka? Aisha baki tausayamin kada hakki yai min yawa Aisha.
"Aisha manna kai tai a kirjunsa tana ejiyar zuciya' shima rungumeta yai a jikinsa kamar yaramar yarinya' snn yaci gaba da cewa ni dama ba wani abu nake dubawa ba illa zamanki ke kadai gani nai kamar baki saki jiki a g'idan nan bane shiyasa' duk da nasan ko waye Fatima bazata cutar dake ba' amma kinsan halinku mata banlema ace kishiya dole wataran sai a hankali' k'uma kinga ba zaune nake a cikin ku ba banle idan naga wani abu zai shiga tsakaninku na kwaba yanxu duk da haka kin amince zaki zauna?
"Aisha tace eh.
"Nasir yace to shikenan' da haka ya lallaba yai ta bayan bukatarsa.
"itako Fatima gani 2AM yayi mikewa tai taje tai alwala tazo tafara jera nafiffilinta kamar yadda tasaba.
"Nasir yana tare da Aisha gani 4AM ya mike h'ade da dauko towel ya daura yashige wanka' bayan ya fitone yana meda wandosa ya mika mata towel din ta daura snn tashiga wanka.
"bayan ta fitone daga wanka ne tasa kayanta Nasir yace Aisha ni zantafi' shiru Aisha tai kanta na kasa' sbd tanaso ta tambayesa amma kuma takasa' Nasir yace yan'mata na yah! dai?
"A sanyaye Aisha tace dan Allah kanada dari biyu kabani? Nasir yace Aisha me zakiyi dashi? Aisha tace ummata nakeso na kira sbd munyi kwana biyu bamuyi waya dasu ba.
"Nasir yace Ayya wlh gashi dagani sai naira dari k'uma idan nabar nan bayanki dashine zanyi amfani na hau napep na karisa' Aisha tace dan Allah Yallabai ina kasamu gun fakewa? Murmushi kawai Nasir snn yace kada kisamu yan'mata na kimin ko.
"yanxu ga darin idan yaso ni saina hakura' da sauri Aisha tace a'a katafi dashi kawai ni na hakura.
"Nasir yace Allah kuwa ki karba' sbd bansan mgnr da kikeso kuyi dasu ba.
"Tace a'a ba komai bane dama gaisawane kawai zamuyi dasu' tunda hakane babu damuwa wani lokaci sai muyi.
"Nasir yace to shikenan Aisha nagode Allah yai maki albarka yasa kici gaba da wanga hali naki ta gari.
"Murmushi kawai Aisha tai masa' Nasir yace ni zantafi saina sake dawowa.
"Aisha tace Allah ya tsareka ya kareka aduk inda kake.
"Nasir yace amin mugode snn yafita d'akin Fatima yaje koda yashiga ganita yai tana sallah ' hakan yasa betsaya bata lokaci ba yai tafi yarda' har yakai bakin kofar parlour zai fita saiga Fatima tasha gaba na h'ade da hankadeshi ya koma da baya.
"Nasir yace Fatima menene h'aka k'uma? Fatima tace ina sarkokina da katuro aka amsawa? Da mmki Nasir yace sarkoki k'uma Fatima wasu sarkoki kike mgn akai? Fatima tace kafi kowa sani' kuma wlh bari kaji sisina bazaiyi ciwon kai ba' tunda ba kai kasiyemin ba ubana ne yasiyemin' idan haka kafitomi dasu kawai.
"Nasir yace Fatima kanki daya kowa?
"cikin tsawa Fatima tace kaina biyu ne ba daya ba.
"Nasir yace ubanwa kike ma tsawa? Wlh idan kikai wasa saina maki dukan masifa kafin nabar g'idan nan.
"Fatima tace bance bazan dukuba amma wlh in har kadukeni saina rama' Nasir yace ok ba kinada karfi ba?
"Fatima tace kada ban'iya ramawa da kaina ba wlh sai kudina ya ciremin ta kaici' domin wlh biya zanyi a ramami.
"Nasir yace ok bari na dukekidin k'uma kafin nabar g'idan nan inaso naga wanda zasu rama maki.
" Fatima tace bismillah...
"kafin ta karisa Nasir ya dauketa da mari wanda yasa ta f'adi' kafin ta dago yasake kai mata wani' ihu Fatima tasa h'ade da kukan kura ta shakeshi.
"Gani h'aka yasa yaci gaba da dukanta harda tokari' jin hayaniya yaki karewa yasa Aisha fitowa daga dakinta' gani halin da suke ciki yasa Aisha fashewa da kuka.
"Duk uban dukan da Nasir kewa Aisha besa ta karaya ba' Yana kai mata kafin ya sauke take ramawa' da Nasir yaga haka wani irin nushi ya kaimata h'ade da shaketa a bango.
"Ihu Aisha tasa h'ade da tafiya ta shiga tsakiyatsu tana kokarin cire masa hannu ya wiyar Fatima' cikin fushi Nasir yace Aisha ta tashi a gun Aisha taki.
"Hannu daya Nasir yasa ya fisgo Aisha yai hurgi da'ita akan cushion din dake parlour.
"A guje Aisha ta tashi tasake zuwa gusa taci gaba da kokarin cire masa hannu a wiyar Fatima' sbd shakar da yaiwa Fatima zata iya suma koma tarasa ranta.
"Gani haka yasa yai hurgi da Fatima yakoma kan Aisha' itama ya hauta da duka kamar mahaukaci' Aisha sai faman ihu takeyi' amma besa Nasir ya kyaleta ba' gudu kada ya cutar da yar ' mutani da yawa yasa Fatima ta rarrafo tazo ta haye jikin Aisha dukan yakoma sauka a kanta.
"Aisha zare jikinta tai a guje tashige dakinta h'ade da rufe kofar da key' kan gado ta fada tasa kuka.
"Gani yara sun fito gada dakinsu ne suna kuka sukayo kan mmsu yasa Nasir egijeta h'ade da tokari snn yafita.
"Fatima na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 38