musa masa ba' bakace ka'iya zirya g'idan mu ba' to wlh bakae ba kowa zaka tura na hakura dakae na har abada Nasir.
"h'aba Fatima kinsan abinda kike f'adi kuwa? Fatima kifi kowa sani banaso naje na aikata zina ko kinfi son H'aka ne Fatima.
" babu abinda ya dameni Nasir nidae aurene bazakayi saba.
"to naji shikenan amma wlh Fatima baki isa ki hanani holewata ba.
" Nasir kaje ka aikata duk abinda kai niya' nikuma wlh subma tallahi daga lkcn da kafara na haramta maka kaena har abada bakace kae ka'iya jaraba kamar bakin bunsurune ba.
"Fatima ni kike fadiwa haka?
" na f'adi Nasir' Nasir me narageka dashi Nasir?.
"Shikenan Fatima naji na amince amma da sharadi.
" f'adi naji.
"daga yau a koda yau'she idan nazo da bukatata zaki biyami' idan har nasamu h'aka daga gareki ni Nasir nayi maki alkawarin wlh wlh wlh bani ba sake aure k'uma kema a matsayinki na matata ina bukatar addu'arki Allah yabani ikon jurewa h'aka.
" wlh Fatima nima na gaji da barnan kudin da nakeyi wajan aurarakin da nakeyi.
"naji zantayaka amma kaima saeka taimaki kanka kafin Allah ya taimakeka.
" himm Fatima kenan' yanzu dae abani kayana na dana ko.
"duk dariya sukai.
~~~ ~~~ ~~~~
" yau tsawo sati uku kenan da zuwa Aisha g'ida a yanzu da h'aka hankali Abbanta da ummanta yafara tashi' sbd duk wani karyan da Aisha ke masa dan kare Nasir yanzu dae yakae karke sbd kowa yasan dae akwai lauje cikin nadi.
"h'aka yasa da dare Abba ya tsare Aisha akan saedae tafadi masu gskya abinda ya hadata da Nasir da har ya kotota g'ida k'uma yaki zuwa.
" Aisha tai rantsuwa har da kukanta amma Abba yaki yarda' gani kukan da takeyi yasashi kiran Nasir.
"lkc Nasir yana kwance jikin fatimarsa suna wasa gani kiran bbn Aisha zai takira masa yasashi kashe wayar gaba daya.
" Fatima na gani h'aka tace waye? kafin ta karisa tuni Nasir ya toshe mata baki da nasa.
"abban Aisha yace lalla akwai matsala.
📖🖊
☘☘
☘
AURE IBADA NE
FASAHA ONLINE WRITES. F. O. W.☘.
MMN USWAN
2⃣3⃣
"tun daga lkcn abban Aisha yake kiran Nasir' Nasir na gani amma bazai daga ba' har saeya gaji d'an kansa ya hkr.
"itama Aisha tai iya lokarinta wajan kiran Nasir amma duk a banza, umma tace a gskya Alhj Akwai matsala sbd idan lfy klau babu yadda za'ayi yaturo Aisha har na tsawon mako uku tana niman shiga na hudu amma bece tadawo ba' ni dama wlh tunda Aisha tazo nake lura Nasir betaba kiranta amma a lkc kodae
nai mata mgn cewa tai yana kira amma yanzu da gskya tai halinta bagashi kowa ya gani ba.
"Alhj yace gskya ne amma yanzu menene abinyi?.
" abinyi kenan akirashi aji wani irin leifine tai masa da har zaiturota g'ida batare da ya biyota ko yakira yasanar damu ba abinda tai masa ba' idan ma yana gudun ya dauki mataki da kansa kenan.
"h'aba Hafsatu wani irin mgn kikeyi h'aka kwata kwata guda nawa Aisha take da har zaiji tsoron ya hukutata, idan tun yanzu yana tsoron yai mata hukunci to gaba fa?.
" Aisha na jin h'aka tasa kuka tana f'adi banlema ni babu abinda nai masa kawai ina zaune yashigo yace na h'ada kayana zaikaini tasha yasani a mota nazo g'ida.
"salati umma tasa tana cewa kajiko Alhj.
" shiru Abba yai sbd ya kasa mgn, gaba daya kansa ya daure.
"Allah ya'kyauta kawai ya ambata.
~~~~ ~~~~ ~~~
" Alhj Kailani mahaifin zahradee ba karami alfahari yake da yiwa ubangiji godiya da azirtashi da zahradee ba sbd a yanzu da h'aka arziki yaci uban na dah! duk yadda yasan zahradee adah ba lalla bane yanzu idan ya gansa ya ganesa ba sbd canzawar da yai ga fari ga'kyau da k'uma raina gashi yaro d'an kwalisa' duk wanda yasan me ake kira raina akaga zahradee tofa anga raina.
"h'akan yasa Abba ya siya masa fankareriyar mota ta alfarma h'ade da kujeran hajji da umra.
" h'akan yasa yan'mata suke ta kawo masa hari' text message yan'mata kuwa ba'a mgn wani ya karanta yai dariya wani k'uma baya karantawa sae dae idan su ishesa a waya sae yagoge' h'aka mafi yawanci lkt idan suna zaune da Abba dauko wayar yakeyi ya nunawa Abba hotunan harda karanta masa text d'in shida Abba sui ta dariya.
"cikin wasa Abba yace to son wacece sarkuwar tawa a ciki?..
" zahradee yace wa🤔 d'an Allah Abba karufami asiri d'an baso kake su kashe maka son d'in kaba.
"Abba yace a'a Allah ma ya kare.
~~~ ~~~ ~~~~~
"Nasir na zaune shida Fatima a d'akin' ta bayan yara sun tafi school' idan tunda aisha tabar g'idan Nasir becika zuwa aiki ba' Fatima tace Nasir.
"na'am matata.
"dan Allah na tambaye ka?.
"tambayeni Allah yasa nasani.
"ina fatan ka sanarwa Aisha mgnr sakin da tsakaniku ko' kodae kanada ra'ayin ci gaba da zama da'ita ne? kae koma kanada ra'ayin ci gaba da zama da'ita amma kasan yana d'kyau tasani ko..
" himmm!' Fatima kenan tunda nake dake kintaba gani narabu da mace k'uma nadawo da'ita aini bana kome' idan ma zandawo da'ita ne to gara nayi wani auren zaifimi.
"amma Aisha ai tatafi kenan.
"Tunda h'aka ne gskya yakamata ka sanar da'ita dan tasan matsayinta.
"Eh" zansanar da'ita ko ba yanzu ba.
"har tsawo wani lkcne zaka sanar da'ita Nasir? gara tunda wuri kasanar da'ita Dan tasan matsayinta.
" ko k'uma fa h'aka ne gskya kinkawo shawara mai'kyau.
"Nasir kenan kai dae Allah ya'kyauta ma halinka.
"Ai ya kyauta min tunda ya barni dake.
~~~ ~~~ ~~~~
"kwanaki sae tafiya sukeyi tun Abba yana hana umma mgn har yakai abinda yafara damusa yan' uguwa har sufara rade radin kodae sakota akayi? itama kanta Aisha abinda duniya duk yabi ya dameta.
" idan tafita uguwa har zunde ake mata' masu cewa maganin masu kwandayi kenan shidama a rayuwa idan mutum be gogewa rahamar da Allah yai masa zai godewa azabarsa.
"gashi kenan aure ko shekara be h'ada ba ya mutu.
"duk mgnr da akeyi a gari yana zuwa kunni umma' hakama da akai rasuwa kwabtansu umma tace Aisha ta tashi suje gaisuwa' babu musu Aisha tasanya hijab d'in ta suka tafi' zamansu kenan aka fidda gawa zuwa gun sallah duk mutani dake gu suka mike h'ade da salati can wata matar dake gefe ta hango Aisha suna tsayen take tabo yar'uwarta h'ade da cewa dubi Aisha Ashe dama da gske ne auren nata ya mutum?
" kedae bari kawai h'aka nima naji lbr' amma fa basu sanarwa kowa ba.
"Allah sarki wlh har taban tausayi' dubi yarinya salbebiya akirata da suna bazawara' gskya maigidanta be'kyauta ba'idan ma wani abu tai masa ai sae yai dubi da kuruciya amma ba ya sakotaba.
"Ohooo koma menene ai su suka sani' ba sunce yar' mai kudi bazata auri d'an talaka ba' sai yar' mai kudi irin sa' ai gashi auren maikudin yayi kyau.
"Nifa tsiyana dake kenan Hulera ke a rayuwarki abu betaba samu mutum ba ki tausaya masa' banle ni banga aibu Alhj Muhammed ba sbd a layinga idan bezo na daya ba zaizo na biyu wajan dukiya' ga k'uma sani hakkin talakawarsa kema shedane sbd koda rabo yakeyi kafin yazo guna sae yazo gunki' idan ma lkcn fidda zakkansa beyiba ni da kaina nasha gananki kinfito maula....
" Too talatuwa kada kimin tonan silili maulanna dae kowa na zuwa.
"duk mgnr da sukeyi umma da Aisha suna jinsu' Aisha dake gefen umma batasan lkcn da tafashe da kuka ba' gani h'aka da sauri taja hannu Aisha suka koma g'ida.
"washe gari da safe around eleven saega ubaida tai sallama Aisha da fara'arta ta tareta' bayan ta gaida umma suka shiga d'akin' ta.
" Ubaida tace Dan Allah Aisha kiyi hakuri wlh naji abinda ya faru' naso zuwa Allah Bbn Abba yahana' kinsan tunda suka samu matsala da amaryarsa ya koreta g'ida ya shiga min wani sabon kunle ko g'idan mu bayaso yaji nace zanje sae ya muna bacin ransa' kinji dalilin rashin zuwana amma Dan Allah kiyi hkr.
"murmushi Aisha tai h'ade da cewa babu komai ubaida.
" Ke Aisha garin yaya h'akan yafaru?.
"wasu kwallane masu zafi suka zubowa Aisha snn tace kenan ubaida bari kawai' daganan ta kwashe tun daga lkcn da take amarya har izuwa wann lkc ta fadiwa ubaida tana kuka.
"Ubaida tace Allah sarki Aisha to ya'isa h'aka kodae na kuka' kefa musulmace k'uma me imani Dan h'aka ki dauki wnn a matsatin jarabta.
" nan dae tai ta bawa Aisha mgn har ta dae na kuka ta saki jiki sukae hira sosae.
"Ubaida tace wlh Aisha tun ranar saurin aurenki da Nasir da suka shigo godiya bayan daurin aure a lkcn ne naga Nasir ni kadae a zcyta nace tab di jam ina Aisha zata kai wnn mutumi' a cire jikinsa ko tsayinsa aka barki dashi aikuwa anbarki da aiki banle ga tsayi da jiki' lalla Aisha kinshi fama inama da gari daya muke washe gari nazo naga yadda kika koma.
"Dariya Aisha tai snn tace ubaida kenan koma menene kafin nasan shi kin rigani.
"Eh nasan da h'aka amma kinfi kowa sani Bbn Abba guda nawa yake da har zanji jiki.
" amma yanzu Aisha aina kuka tsaya dashi?
"himm wlh ubaida nima kaina bansan makomata ba' bansan abinda Nasir yake nufi dani ba' Abbana da kansa yasha kiran sa amma baya dagawa' nima da umma musha kiransa duk da h'aka baya dagawa.
" ni k'uma har ga Allah nasan ba f'ada mukai dashi ba banle nace ko dan h'akan ne ya turoni g'ida h'aka kawai nefa ubaida.
"kwallane suka zubowa Aisha.
" da sauri ubaida tasa hannu ta sharewa Aisha hawayen snn tace to yanzu kinsan abinda zakiyi?
"a'a".
" Ina wayarki?.
"gashi.
"Amsa ubaida tai snn ta shiga gun text tafara da
( Assalamualaikum Barka da warhaka da fatan kana lfy Allah yasa h'aka amen, abban Khadijat nayi ta kiran wayarka baka daga amma nai tunani ko baka kusane shiyasa, Gani nayi yau tsawon watana uku kenan da zuwa g'ida bakazo ka daukeni ba k'uma baka turoba Allah dae yasa lfyne.).
" snn tai sending d'in text d'in.
"yana shiga daedae lkcn wayar tana hannu Nasir' gani text yashigo ya b'ude bayan ya gama karantawa har ya'eje wayar a gefe sae k'uma ya dauko ya rubuta kamar h'aka.
" ( Karkiji komai lfyta klau ki kwantar da hankalinki ko banzoba zakiga sako) snn ya tura mata.
"yana shigowa suka b'ude ubaida ne ta karanta wani irin ajiyar zcyne Aisha tai.
"Ubaida tace kingako Aisha Dan Allah kikara hakuri har Allah ya kawosa kikoma dakinki.
" amin ubaida ngd sosae.
"ni zantafi Aisha saena sake dawowa.
" nan sukai sallama Aisha ta rakata har b'akin kofa.
"tun daga lkcn idon Aisha kullum a kan hanya yake ko zataji Nasir yai sallama' gashi koda ta kirasa baya dagawa idan tai masa text baya biyota' h'akan yasa tasake shiga damuwa sosae kullum cikin kuka take.
"Sbd kuka zazzabi ya kamata ga zafin da takeji a gabanta batare da tasan dalili ba' wasa wasa kuragen da tatabayi a g'idan Nasir ne suka dawo mata' tun tabasha amfikulos a boye har yakai ga saeda umma tasani' bayan ta sanine da sanarwa Abba' Abba da kansa yake siyo mata amma duk a banza.
"Tun Aisha na daurewa tana tafiya har abu ya gagara takoma a kwance komai saedae ayi mata kusan kullum umma ke wanke mata ta shafa mata mgn' duk lkcn da umma zata wake mata sae ta daure sbd ihun da Aisha keyi.
"Gani abu yaki ci yaki cinyewa yasa Abba d'aukarta zuwa hospital suna zuwa da doctor ya duba h'ade da yimata tambayoyi gado yabata' ko riga bata sawa sbd kullum s'au biyu ake wanke mata.
"Gani wayarta babu caji k'uma hospital basu kuna generator ba yasa Abba daukar wayar Aisha zuwa g'ida yaje daga nan yai mata caji.
" suna cikin tafiya Abdul ke drive saega shigowar text wayar Aisha.
"Abba kamar bazai b'ude ba amma gani number Nasir NE yasashi budewa.
"Gani yai kamar h'aka.
( Assalam Aisha kiyi hkr wlh mancewa nai kamar nace zakiga sako' to ba komai bane sakon dama takardankine gashine nan kamar h'aka, Ni Nasir guduma na sakeki saki uku sae anjima)
INNALAILAHI'WAINNAILAIHIM'RAJU'UN
KAWAI ABBA YAKE AMBATA.
tofa jama'a Allah ya'kyauta
📖🖊
☘☘
☘
AURE IBADA NE
FASAHA ONLINE F.O.W.☘.
MMN USWAN
KAE KAE KAE WANI KAYA SAI AMALE BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE MURUCIN KAN DUTSE BAKI FITOBA SAIDA KIKA SHIRYA INA MIKA SAKON GAISUWATA GAREKI Mrs G'IDADO MOM ABDUL JALAL KINA GABA MUNA BIYE DAKE JA GABA MANYANMU ALLAH YAJA DA NISAN KWANA YA KARA LAFIYA.
2⃣4⃣
"Abdul dake driving yace Abba lfy? wlh Abdul Mijin Aisha ne ta aiko mata da takardan saki.
"Innalallahi'wainnailaihim'raju'un.
"sakifa Abba kace?.
"wlh kuwa Abdul.
'"wlh Abba ni dama tun farkon da yazo niman aurenta hankalina be'kwanta dashi' kawai Dan babu yadda zaiyi ne.
"hakane Abdul kasan ance matar mutum kabarinsa' babu damuwa Allah yasa haka yafi alkairi.
"amma dan Abdul inaso kabar mgnr ga anan yatsaya gani sae kae.
"Abba ko zansan dakikin biye mata?.
"Eh" ba komai ne yasa sbd yadda take cikin irin wnn halin kaga be kamata a sanar da'ita irin wnn zancen ba.
"Eh" k'uma mgnr ka gskya ne Abba'to shikenan fatanmu dae shine Allah yabata lfy.
"Ameen' Abdul.
"Kwanan Aisha bakwas a hospital safe da yamma sae an wanke mata kurajan' duk lkcn da za'a wanke mata idan har su umma da Abba suna gun' tashi sukeyi suyi nisa da gun sbd ihun da takeyi su k'uma hankalinsu tashi yakeyi.
"gani ciwo yaki ci yaki cinyewa yasa Abba zuwa office d'in doctor bayan sun gaisa ne Abba yace a gskya doctor be'raina da yinkaba amma dan Allah inason zanyiwa Aisha canji hospital sbd banga wani progress da ake samu anan ba.
"mirmushi doctor yai snn yace Alhj kenan laluran Aisha be d'anganci rashin kwarewar aikin mu' tunda kana gani kamar laifinmune to bari na f'adi maka gskya laluran Aisha ba karamin lalura bane' dama inason kashigo nai maka bayani sae gashi Allah ya kawoka.
"a gskya Aisha tana bukatar kyakykyawar kulawa sbd wani cutar ba'iya waje ya tsaya ba can cikin jikinta yake shiyasa sae ammata gwaje gwaje sosae snn musan irin magani da zamu dorata akai.
"to doctor yanzu me kake gani za'iya?.
"abinyi yana gunka.
"kamar yaya?.
"to a gskya irin wnn lalura ba karamin kudi yake ciba' ba nan ba duk hospital da zaka kaita mgnr dae kenan.
"yanzu kamar nawa kake gani zataci?.
"A yanzu kam bazan iya f'adi ba sae yadda muka gani' abin nufi sae mufara mugano wacce irin lalurane snn k'uma mu abinda magani daya dace tai amfani dashi'zamuyi kokarin bata kyakykyawar kulawa wajan gani cutar besake dawowa ba.
"to doct babu damuwa nidae fatana Allah yabata lfy.
"Amin Alhj'.
AFTER 2 DAYS
"dict ya h'ada takardun duk wata gwaje gwajen da yaiwa Aisha da k'uma results d'in da yabayar' da Abba yazo kai tsaye office d'in doct ya nufa baya su gaisa sae da dotc ya gyara zama snn yace to Alhj gskya a iya binciken da mukai akan Aisha result na farko da yafara bamu shine a gskya dae Aisha tasamu matsala a mahaifarta wanda ba lalla bane ta mahaihu.
"na biyu k'uma shine tana bukatar kyakykyawar treatment sbd cutar da take dauke dashi..
"A gigice Abba yace badae HIV bane doct?.
"murmushi doct yai snn yace a'a Alhj.
"ba HIV bane' wnn wani irin cutane wanda k'uma ina kyautata zaton tasamune a gun maigidanta sbd a iyan tambayoyin da nai mata da k'uma gwajin da mukai ya nuna mana cewa adah batadashi sae bayan auren ta.
"to ni k'uma a Iya sanina da Aisha ba maza takebi ba banle nace daukowa tai gun biyebiyen maza.
"ita k'uma irin wnn cuta daukarta akeyi.
"maybe yana niman matan banza ko k'uma auri sakine sanadiyar h'aka ya dauki wnn cutar wanda har itama tasamu.
"da alama shima kansa besan yana dauke dashi ba' sbd duk wanda yake dauke da irin wann cutar dole ya samu nakasu a harkokin lfyrsa' ma'ana ta hanyarne yake iya harbawa wani.
"Amma zamuyi iya kokarinmu akan Aisha mgnr haihuwa k'uma maybe maybe zata iya samu nan gaba' amma dae anya kuwa" himmm!!.
"to nidae doct abinda yafi damuna shine naga Aisha tasamu lfy' shine babban matsala ta.
"karka damu Alhj insha Allahu zata samu lfy nan bada dadewa ba' tunda yanzu mugano cutar da take dauke dashi.
"to nagode doct.
"nima nagode".
"tun daga lkcn aka canzawa Aisha maguguna' mgnr kaikayi da zafi da suke hanata bcc duk tafara samu saukinsu shiyasa yanzu h'aka koda doct yazo wanke mata gun batajin zafi kamar yadda da takeji' sbd doct yana shigowa da kanta take b'ude masa gababta ya wanke snn ya shafa mata magani'.
"In day!! ne kuwa sae yazo da masu riketa' duk da h'aka be hana Aisha ihu da shure shure' hatta makwabtanta sae sun san ana wanke mata ciwo sbd ihu.
"tuni zahradee yaji labarin Aisha tadawo g'ida' tun kafin Nasir ya aiko mata da saki tun anriga ansanarwa zahradee da cewa Aisha batada aure' da k'uma sanar masa halin da take ciki na rashin lfy.
"Zahradee yai matukar tosaya masa amma a yadda yakeji a zcyrsa ba zai'iya zuwa gaidata ba.
"sae dae a matsayinsa na masiyinta zaitayata da addu'ar samu sauki.
"Cikin hukunci ubangiji a hnkli Aisha tafara samu sauki' yanzu har zama tanayi k'uma tana iya tashi ta d'an zaga d'akin.
"Abba da umma suji dadi gani 'year"su tafara samu sauki.
"Yau ma da ubaida tazo dubata har waje suka fita can wajan wani gidin bishiya suka zauna' ubaida tace niko Aisha kinsanarwa Nasir kamar bakida lfy?
"a'a ubaida bansanar masa ba' niso na nasar masa amma wayar bata hanuna' tun ranar da Abba ya amshi wayar yace zaije g'ida yasamu caji shine besake dawomin dashi' koda na tambayesa cewa yai ina ta kainane ko inata waya.
"ni k'uma tun daga lkcn besake tambayarsa ba.
"To Allah ya kyauta' amma ai yakamata ki sanar dashi koda bazaizo ba' tunda zamansa kikeyi yanada'kyau yasani.
"Eh" nima nayi tunani h'akan ubaida amma babu yadda zanyine.
"Abinda yafi damunama shine besan halin da yake ciki ba' sbd nasan inda lfy klau ne Nasir bazai barni na zauna a g'ida har tsawon wnn lkcn ba.
"kowani haline yake ciki oho Allah ne masani.
"Aisha na mgnr ne tana kwalla.
"To Aisha Allah ne masanin komai' duk ma halin da yake ciki dae addu'a ne naki insha Allahu Allah zaikawo masa mafita.
"Amin ubaida ngd.
"sun jima suna hira ubaida natabawa Aisha hkr da cewa Nasir yananan zuwa gateta insha Allahu' da h'aka har yamma yai snn ubaida ta tafi g'ida.
"Sae da Aisha ta shafe wata daya da kwanaki snn suka koma g'ida mgnr sauki kam ba'a mgn sae dae ramar datai.
"da h'aka Aisha taci gaba da kula da kanta'shima Abba kusan kullum idan yana dawowa daga kasuwa saeya siye mata kayan marmari h'ade dasu frue a hankali Aisha tafara maida jikinta.
"mgnr waya kuwa kusan kullum sae tayi amma Abba yaki bata k'uma yacewa umma kada tabari Aisha tai amfani da wayarta wajan kiran Nasir.
'"mmki ya kama umma'umma tayi tayi da Abba akan ya sanar da'ita dalilin h'akan yaki.
"shiyasa tun tana mgn har tagaji ta hakura' da mgnr' h'akna yasa tai tunanin zuwa g'idan ubaida sbd tai amfani da wayarta takira Nasir idan a yanzu da h'aka kewar Nasir takeji.
"tana matukar son gsnisa koda bazai mata komai ba' amma k'uma kash!!!.
sae tai rashin sa'a koda ta tambayi umma' umma kin yarda tai a cewarta wai abbansu yace kada abari tarinka fita ko nan da kofar gida ne.
"babu yadda Aisha zatayi dole yasa ta hkr.
"Tunda Aisha taji tasamu sauki tasawa iyayenta kuka ita zata koma g'idan mijinta' duk yadda umma takai ga lallashinta amma Aisha taki hkr h'akan yasa da yamma bayan Abba yadawo daga kasuwa umma ta sanar masa.
"Abba yace ta kira masa aishan' mikewa tai taje dakinta ta kirata sukazo tare.
"Da sallama Aisha ta shigo dakin bayan sun gaisa snn tace Abba gani' Abba yace Aisha.
"na'am Abba".
"naji sakonki a gun ummanku' h'akane?.
"jiki a sanyaye tace eh'Abba.
"Amma ke Aisha meyasa kikason komawa g'idan Nasir baki gani akwai tutarwa a zamanku? yanzu sbd Allah me sonka tsakani da Allah kenan zai turoki g'ida tsawon wata hudu babu ko waiwaiye? yadda sbd Allah kina gani yai maki adalci kenan?.
" h'akace nima nasan be kyauta ba amma Dan Allah Abba kuyi hkr' babu mmki wasu uziririkane suka shamasa kai da yazo amma Dan Allah kayi masa hkr Abba.
"Aisha kenan bafa ba mgnr hkr nakeyi ba.
"eh"to Abba inaso na koma.
"ina Aisha?".
"Aisha kiyi hkr babu inda zaki..
"kuka Aisha tasa tana f'adin Dan Allah Abba kayi hkr.
"Aisha kiyi hkr Nasir baya sonki' ni k'uma bazanso 'yanta taje inda ba'a sonta ba'.
"a'a Abba wlh baka fahimcesa bane yasa.
"himm" Aisha kenan".
"Aisha kinfi kowa sani kukalai keda kaniki Allah yabani a rayuwata Dan h'aka bazanso naga abinda zai tabamin Ku na kyaleba.
"ko aurenki da maigidanki Allah ne kawai yai da k'uma namu gudumuwar na rashin bincike sbd a lkcn dukkanmu idanumu ya rufe' Aisha a gskya kinban mmki sbd a rayuwata da k'uma irin tarbiyan dana baki banta tunanin zakimin h'aka ba.
"bayan aurenki da Nasir labari yazomi duk irin rashin mutunci da rashin adalci irin naki dan Allah ma shedane banmaki irin wnn tarbiya ba' shine bika juyawa zahradee baya' ke a ganiki kinmasa adalci kenan?.
"Allah ya gani bankasa da komai a g'ida naba banle ace rashine yasa yai maki duk irin hidimomin da yai maki' amma ni nasan so da kauna ne yajashi ga h'aka.
"Aisha nasan ba rokonsa kikai ba' amma kodan darajar soyayyar da yake maki wlh be kamata ki masa haka ba.
"tunda Abba yafara mgn jikin sisha yai sanyi" kukanma da takeyi ya gagara.
"Abba yaci gaba da cewa bazan boye maki ba Aisha tun bayan tafiyar wlh kasa h'ada ido da Alhj Kailani nayi sbd bansan da wani ido zan kallesa ba.
"duk da shima bezo yaimin bayani ba amma banyi blimey nashiba sbd tun bayan tafiyarki zahradee yashiga matsanaciyar hali na rashin lfy wanda dakar mahaifinsa yasamu gano kan d'an sa.
"duk halin da suke ciki lbr yana zuwamin naso naje amma matsalar shine bansan da wani ido zan kallesu ba.
"yanzu dae koma menene Aisha gashi nan kin gilbi kayanki' rashin hakkinkine da bandashi shiyasa' sbd kin nimi kibani kujya a idon duniya ki zubarmi da mutunci k'uma ki hakani f'ada da jama'a to ta Allah bataki ba' sbd yanzu da h'aka ina me tabbatar maki Nasir ya aika maki da sako tun ba yau ba'ga salon nan.
"mika mata wayarta yai snn yace b'ude ki karanta sakon.
"jikin Aisha har rawa yakeyi wajan budewa.
"koda Aisha ta bude bata karisa karantawaba ta sulale ta sume.
📖🖊
☘☘
☘
AURE IBADA NE
FASAHA ONLINE WRITERS F.O.W.☘.
MMN USWAN
2⃣5⃣
"Umma na gani Aisha ta sume tasa ihu h'ade da kuka' Abdul dake zaune a gefensu a guje yaje ya d'ibo ruwa' yana dawowa jikin umma na rawa ta amsa ta yayyafa mata.
"duk abinda sukeyi Abba na kallonsu amma be tanka masu ba" duk da shima d'in ya razana amma ya matse yanuna ko a jikinsa.
"umma ta kuka h'ade da kiran suna Aisha.
"Aisha na farfadowa h'ade da sauke wani irin ajiyar zcy.
"daga umma har Abdul sae faman sannu suke cewa Aisha.
"Aisha na dawowa normal tasake fasawa da wani kuka.
"tsawa Abba ya daka mata h'ade da cewa rufemin baki" yarinyar banza kawai.
"a'a" Alhji"...
"rufemi baki' ko kema nadawo kanki.
"dama duk wani irin abinda yaranga zasuyi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 38