Share this page
tasan meke ciki" "hankalin zhrdee ba karami tashi yai ba akan abinda Zainab keyi masa' gashi babu hkr duk abinda take masa saiya sanarwa Hjy' ita dai saidai tace kakara hkr watan sai labari' amma a zcyrta ba karami dadi tajiba yadda Zainab ke gara zhrdee" "idan yakira yaga numr busy yai kamar zaiyi hauka sbd kishi""" *Allah kenan shiyasa me hakuri yana tare da rinjaye a rayuwa* 📖✍ ☘☘ ☘ *AURE IBADA NE* FASAHA ONLINE WRITES. F.O.W. ☘. 🌳 *impacting valuable knowledge and entertainment is our concern* 🌳 *story written by Mmn uswan* *kuyi hkr da jina shiru wlh sai a slow ne' h'akan yasa bansoyi posting amma sbd masu yawan tambayane yasa kuka jini a yau* *_~masoya nagode da bibiyar littafin AURE IBADA NE da kukeyi Allah yabar kauna da zumuci~_* 6⃣2⃣ "h'akan yasa zhrdee ya kasa hkr' zuwa yamma bayan la'asar zhrdee ya shirya zuwa g'idan su Zainab' zhrdee yana isa Zainab na dawowa daga uguwa g'idan kanwar innarta taje gaidata sbd zazzabi da tai yasa taje gaidata" "zhrdee yana isa kofar g'idan su Zainab' Zainab itama tana isa tadawo uguwa' wani mutum ne ya sauketa daga mota' ashe zhrdee yana can akan titin area dinsu yana kallonta' da sauri yai parking ya fito daga motarsa' itako Zainab batasan yana kallonta ba' tana sauka ta dauki yar' ta h'ade da sallama har tajuya zata shige g'ida *Islaha* dake hannu mmnta tasa kuka zata bisa' sbd yadda tagansa kamar zhrdee ne a tsaye" "farine sal ga hanci har baki gashi beda jiki kamar d'an Fulani saidai tsayi' h'akan yasa tunda suka shiga motarsa *Islaha* ta makale masa sakamakon ganisa takeyi kamar bbnta" "gani kukan da tasa yasa mutumi fitowa daga motarsa yasa hannu ya dauketa yana dariya' yana daukarta tai shiru' dagashi har Zainab d'in dariya suke mata' a guje zhrdee ya kariso gun h'ade da fisge yar'sa daga hannu mutumi yana f'adin bani yan'ta d'an rainin hankali kawai' waya baka izini tsayuwa da matata?' ko an f'adi maka sakinta nayi' to idan itace wlh daga kai har ita karya kukeyi' manafuki algugumi wanda besan darajan aure ba" "duk mgnr da zhrdee keyiwa mutumi besa ya tanka saba saidai ma murmushi har ya kare snn mutumi yace h'aba Malam da hankalinka da k'uma tunaninka kake dabi'a irin ta marasa hankali' kamata yai ka tamb"... " d'an Allah Malam kaimi shiru wlh na rantse da Allah idan nasake ganika da matata kotuce zata rabamu dakai " "Zainab dake tsaye mmkin zhrdee ya kamata gani rashin mutuncin da yakewa mutumi h'akan yasata cewa d'an Allah kayi hkr d'an makwabcinmune k'uma yanada matsala a kwakwalwarsa shiyasa" "jin h'aka yasa zhrdee fusata hannu yasa ya fisgo Zainab zuwa cikin g'idan' mutumi dake dake tsaye ya dauka da gske ne mgnr da Zainab tai na rashin hankalin yasashi tsalle yashiga tsakiyar su yana kokuwa da zhrdee akan saiya saki Zainab' duk kokuwar da zhrdee keyi *Islaha* na hannunsa yaki sauketa' *Islaha* na gani h'aka tasa kuka duk kokarin zhrdee kada mutumi ya taba masa Zainab' shima dayake me addini ne duk da besan tsakanisu ba beyi tunanin rike Zainab din ba' duk kokuwar da sukeyi hannunsa yana kan na zhrdee ne" shikuma zhrdee kokarin sa yaga Zainab ta shige cikin g'ida idan yaso duk abinda zasuyi sai suyi" "Zainab na gani yadda *Islaha* ke kuka hannu tasa ta fisge yar'ta daga hannu zhrdee snn tashige cikin g'ida' ko juyowa batai ba balle tasan abinda suke ciki' zhrdee yana gani ta shige yakama mutumi da f'ada' da yake bamafadacine ba' be tankawa zhrdee ba zagawa yai ya shige motarsa yabar gun' sbd tsabar kishi da takaici zcyr zhrdee kamar yakama da wuta yakeji a fusace yaje ya shiga motarsa yabar gun' g'ida yanufa kai tsaye yana shiga dakinsa yaje ya kwanta h'ade da ijiyar zcy' a zcyrsa yana fadin bazai kara zuwa g'idan su Zainab da sunar rokon tadawo g'idana ba' to k'uma idan nayi haka ai ban nuna mata kuskutenta ba' kamata yai ya kirata koda a wayane na f'adi mata abinda ke raina idan yaso daga lkcn saina fita harkanta' tunda har tana sauraran wani banza ba niba' harma cewa takeyi banida hankali' lalla Zainab saina nuna mata kuskuren yin h'akan' k'uma daga snn na kwashe yarana da suke hannunta" "shiru yai h'ade da rufe ido kamar me bcc amma ba bcc yakeyi ba' wani irin zafi yakeji a zcyrsa wanda shima kansa besan dalilin h'aka ba' daga nan har bcc ya daukesa' bcc yai nisa da zhrdee har akai magrib da isha be saniba' kiran Aisha ne ya tadashi daga bccn dayakeyi a gigice ya tashi h'ade da daukar wayar yaga ko waye' gani Aisha ne yasashi tsaki yai hurgi da wayar" "gani after eight yasashi mikewa yaje toilet yai alwala yazo yai sallolinsa bayan yai addu'ar sane ya shafa yasake dauko wayar batare daya tashi daga kan sallayar ba yana dauka bayan ya kare dube duben da zaiyi b'ude data dinsa yai yashiga fcbk yaita karance karancen da zaiyi bayan ya kare yakoma kan WhatsApp yana hawa yaga Zainab da Aisha dukkansu su biyun kowa idan yashiga nasa sai yaga suna tp' be tanka masu ba ije wayar kawai yai ya zuwa masa ido" "Aisha na ganisa a online tai sama SLM' zhrdee yana kallo be amsa ba' tasake cewa SLM" "tsaki kawai yai yafita a gun' yakoma gun Zainab' Zainab tana kallonsa a online amma batai masa mgn ba' taci gaba da harkan gabanta' gani bazai iya hkri ba yai mata sallama da assalamu' alaikum?" "koda taga sallamarsa banza tai dashi' duk da h'aka be daddara ba yasake sallamar' gani zai dameta yasata blocking nasa snn taci gaba da abinda ke gabanta" "batare daya luraba yace Zainab ninefa zhrdee' yanzu har kece da kanki kike walakantani Zainab' ninefa mijinki k'uma uban ya"yan" Zainab' Zainab Zainab" "duk da haka bega antanka masa ba" "himm walakanci ko Zainab?' babu komai kici gaba' sauka yai ya rufe data dinsa ya'ije: wayar a gefe' can k'uma me yagani yasake dauko wayar ya kira numr Zainab' tunda yafara kiranta Zainab tana kallo amma bata daga ba' da taga zai dameta ije wayar tai a gefe tasa a slint snn ta kwanta" "tana kwanciya bcc ya dauketa' duk uban kiran da yakeyi tana bcc batama saniba' miss call kuwa yakai *30* gani wayarsa tana nuna masa betttery low yasashi hakura amma badan yasoba' ranar ko abinci beciba h'aka ya kwanta da yunwa" "da safe suna dawowa daga sallar asuba shida Abba' Abba yake tambyarsa su Aisha da Zainab' zhrdee yace duk suna lfy" "eh nasan suna lfy' hausana kana lekasu k'uma yaushe zasu dawo" "eh to Abba a gsky mgnr Zainab dai har nafara fidda rai da'ita' sbd duk yadda zanyi nayi amma taki yarda ma ta saurareni balle taji abinda naje dashi' rannan fa harda wani nadansu ya dauketa daga mota' da alama nimanta yakeyi" "a'a son' kada kabari zcy ta bata maka auren ka da'ita' kasan aure da zargi babu aure ko" "wlh kuwa Abba" "a'a son' nasan su waye iyayen Zainab' ni nafika sanin waye *Alhj Musa* wlh ko da da wasane bazai bari Zainab ta saurari wani ba da aurenta' kilan dai wani Dan' uwarta ne' Wanda ba lalla bane ace ka sansa" "himm Abba kenan" "da gske son k'uma kaje ayi bincike kaji" "to shikenan Abba" "to son yaya mgnr ita aishan?" "tana lfy itama" "nasan tana lfy kana zuwa dubata ita da yara?" "a'a Abba" "sbd me son? " ita da bance Zainab daban? " "to a gsky son idan har haka zakayi ina me tabbatar maka bazamu shirya ba' idan har kanaso mu shirya kaje ka dubosu' ni bazan matsa maka akan saika dawo dasu ba tunda baniike zama dasu ba' kai kasan halin kayanka amma kaje ka dubasu k'uma kada kaje hannu kawai" "to kawai zhrdee yace snn suka karisa cikin g'idan" "yana gama breakfast yai wanka ya shirya snn yazo ya sallami Abba da Hjy yafita' supmkt yaje yai siyayya ba laifi snn yakarisa g'idan su Aisha' tagama shirya yara kenan zhrdee yai sallama ya shigo cikin g'idan' *shihid* yana zaune akan cinyar umma' ita k'uma *shahida* tana gun mmnta' Aisha na gani zhrdee da sauri ta mike cikin doki da murnar ganisa' umma take zaune hijab tasa h'ade da gyara zama" "Aisha taje suka shiga tare har kasa ya duka a ladabce suka gaisa snn umma ta fice daga d'akin ita kuwa Aisha kitchen ta shiga ta hado masa tea sbd a lkcn safene ta jere masa a tre ta kawo zhrdee yana dauke da *shahid* Aisha ta shigo da sallamarta har kasa ta duka snn ta'ije masa a gefe bayan ta'ije tace ina kwana" "fuska a daure tace lfy klau' ya kuke?" "lfy klau" "daga snn besake mgn ba" "yawo tre d'in tea tai zata zuwa masa a cup' zhrdee a'a a koshe nake ngd" "batare komai ba ta meda ta'ije" "gefe ta koma ta zauna h'ade da baza kunni ko zai wani abu' shima bebi ta kantaba yaci gaba da wasa da yar'sa' gani su kwashi mintoci bece komai ba' ji tai kamar tai masa mgn amma k'uma batari sbd kada ya rainata' sun kwashi kusan thirty minutes babu Wanda yaiwa d'an uwarsa mgn amma duk abinda yakeyi idanu Aisha na kansa' da zhrdee ya lura da haka yakara daure fuska snn ya mike h'ade da mika mata yarinya yace zantafi dama nazo na duba yara nane" "jin haka ran Aisha ya baci' ta kasa hkri tace dama sbd yaranka kazo badan niba kenan?" "duk yadda kika dauka hkne" "haka kace zhrdee" "ta kanki akeji' ni kinga tafiya ta' fice warsa yai batare da sallama ba" "Aisha na f'adin wai zhrdee me kake nufi da nine eyye zhrdee" "ko juyawa beyiba balle yasa tanayi' Ashe duk abinda suke ciki ummata na jinsu' kuka Aisha tasa tana kuka tana masifa' ummata ne tashigo d'akin ta hauta da f'ada' duk yadda Aisha taso meta mgn umma ta hanata d'an batason jin abinda ke tsakaninta da mijinta' dole yasa Aisha ta hkr da f'adin' tai kukanta har tagodewa Allah Dan kanta ta hkr" "zhrdee yana fita kasuwa ya wuce koda suka hadu da Abba a kasuwar yake tambyar su *shahida da shahid* zhrdee yace duk suna lfy" "har zhrdee yai zcy akan bazai kara kiran Zainab ba ko yaje g'idan su amma k'uma h'akan beyuwuba d'an yakasa daurewa da h'akan' da yamma bayan yadawo daga kasuwa *around 9-30* yaje g'idan su Zainab sbd yasan lkcn abban Zainab yana g'ida" "cikin shigarsa ta alfarma babu yabo babu fallasa k'uma babu karyan arziki': ba karami kyau yai ba yaje g'idan su Zainab har parlour yashiga da sallama' lkcn mamy kanwar Zainab ce ke tana kallon wani prgm da akeyinsa a *zeeworld me suna LAALI* zhrdee yai sallama yashiga mamy dake zaune ta mike da sannu da zuwa bayan su gaisa ne yace tai masa sallama da Abba" "a guje taje tai sanarwa Abba suka fito tare' bayan ya zauna ne suka gaisa h'ade da tambyarsa lfy?" "zhrdee babu kunya yace karar Zainab na kawo Abba" "karar Zainab k'uma?" "eh wlh Abba" "murmushi Abba yai h'ade da daukar wayarsa ya kira inna yace sufito da Zainab zhrdee ne yazo" "to inna tace h'ade da sanyo hijab ita da Zainab suka fito tare" "Zainab na hango zhrdee ta daure masa fuska' itako inna da fara'arta ta kariso gun' zhrdee ya duka har kasa suka gaisa snn ya zauna" "Abba dake zaune yace surinkikine ya kawo karar yar'ki" "karar ya"ta k'uma subhanallh" "zhrdee yaya akayi ne?" "wlh inna Zainab ce nagani da wani a tsaye suna hira" "hira k'uma zhrdee?" "eh wlh inna" "ke Zainab yaushe kika zama h'aka? da aurenki zaki rinka fita kina sauraran wasu mazan Zainab' to ni wlh babu ruwana bazaki jawomi mgn ba" "ni wlh inna sharrine kawai irin tasa amma ni bantaba tsayuwa da kowa ba" "karya kikeyi k'uma' ina Wanda naganki dashi rannan" "duk abinda sukeyi abbanta ido kawai ya zuba masu kafin yafara masa" "tsaki Zainab tai h'ade da cewa *Isma'il yaron inna hasiya dine saurayina*? " Ohooo kinfi kowa sani" "a'a kae dakata' wanda kake mgn akai yaron kanwata ne fa" "eh shine' ranar da naje gaidata da batada lfy har na fito daga g'idan shine iskan ruwa ya taso gashi nariga nayi nisa da g'idan ba halin komawa' ita cikin tafiya kenan saiga *isma'il* yana dawowa aiki shinefa ya tsaya da daukoni ya kawoni g'ida' shinefa kikaji yake mgn akai" "karya takeyi inna" "wlh ba karya bane k'uma a kirasa ma a tambyesa" "kinada numrsa?" "eh!! to' gashi dai kaduba da kanka' sbd gani nake kamar nagoge wanda nake dashi" "Abba yana amsa ya duba cikin sa'a yagani' yace gashi nagani' daukar numr yai yasa a tasa wayar ya kirasa' yana pinking call d'in Abba yasa a hadfree kowa yaji' duk mgnr da Abba keyi da *isma'il* zhrdee naji har akai sallama dashi" "bayan Abba ya kashe wayar ne yacewa zhrdee kajiko' kenan dama zartinta kakeyi?" "a'a wlh Abba ba zarginta nakeyi ba' ni dama abinda yafi bakantami rai harda dariya take masa" "Abba najin h'aka yasan kishi ne kawai kecin zhrdee' snn yace amma inaso wann yazama farko k'uma yazama karke wlh koda dawasane kada nasake jin irin h'aka ya kasance' sbd bazan yarda ka shafawa yan'ta b'akin fentiba" "to Abba za'a kiyaye" "ke tashi muje mubasu gun" "suna tafiya shima zhrdee mikewa yai' gani yamike itama ta mike har ta juya zata shige daga ciki' hannu yasa ya fisgota da karfi suka fita daga parlour Zainab tayi kokarin kwacewa amma ta kasa har cikin mota ya kaita shima ya shiga cikin inda take ya zauna h'ade da rufesu daga ciki" "Zainab na kokarin turesa ta fita daga motar' dariya kawai zhrdee yai h'ade da cewa fita mana" "koda tasa hannu zata b'ude taji motar rufe gam da key' wani irin dariyar keta zhrdee yai snn yace h'aba Zainab meyesa kikemi hakane sbd Allah' ke nalura kodan kewata bakyaji ko Zainab?' dan Allah kiyi hkr kizo mukoma g'ida".. " cikin tsiwa Zainab tace wani g'idan? " "g'ida mana Zainab?" "Allah ya kiyaye' nida gidanka har abada na barsa kenan' haka kawai naje na zauna da wanda besan mutunciba duk kokarin da nake masa d'an gani na kyautata masa amma begani' dani da baiwa babu maraba, " gashi duk iya kokarin da nakeyi d'an gani na kyautata maka baka gani k'uma baka ragami' ita kuwa Aisha dayake ta fini mutunci a gunka duk da rashin biyayyarta da rashin sani darajan su basu Hjy da Abba' amma baka gani laifinta sbd YAR" lu'u'lu'uce"!!!! "lalllilahaillahu h'aba Zainab waya f'adi maki h'aka?" "h'aka ne mana" "wlh ba h'aka bane Zainab" "hakane mana' shiyasa ni yanzu nan zanje na auri wanda nakeso k'uma yake sona' wanda ba cusani ai a gunsa ba balle naje g'idansa matansa suzo sunami gori cewa aurena da mijinsu cushene"... " da sauri yasa hannu ya toshe mata baki h'ade da cewa h'aba Zainab waye yake f'adi maki h'aka sbd Allah? " "aikafi kowa sani tunda a gabanka ake komai' k'uma nayi imani inda baka f'adi masu hakaba babu wacce ta'isa ta f'ada h'aka a gabanka" "wlh Zainab ba h'aka bane kawai dai"..... "a'a basai ka rantse ba' karike rantsuwarka kawai kaje Allah ya h'ada kowa da abokin azikinsa" "h'aba Zainab kinsan abinda kike f'adi kuwa?' kinsan yadda nakeji sbd rashinki a tare dani kuwa?' kinsan yadda soyayyarki take wahalar dani babu dare babu safe harfa kasa bcc nakeyi sbd zafin rashinki kusa dani Zainab amma shine zaki iya kallon tsabar idana kina fadimi h'aka' kodan bakisan yadda nakeji bane Zainab" "koma me kakeji Allah ya yaye maka" " daka mata tsawa yai hade da cewa to wlh baki isaba Zainab da raina da lfy ta' bafa sakinki nayi ba balle kice" "Zainab najin h'aka tasa kuka tana f'adi nidai wlh babu inda zani h'aka kawai na koma kuzo kuna walakantani kaida Aisha"... " h'aba Zainab aishan me wlh na rantse maki da Allah bata iya ta walakantami keba Zainab' idan ma baki saniba yau zansanar dake wlh sbd ke nakori Aisha g'idan su' kinga ko su Abba da Hjy banbari susan dalili koranta ba".. "nidai kadaina cewa sbd nine ka kori Aisha"... " wlh sbd kece' tun daga ranar bankara zuwa g'idan su ba' idan banda Abba yaimi mgn shine naja' wlh Zainab alkawari na daulawa kaina idan baki komaba itama Aisha bazata koma g'idan ba" "kai kasani da dadin bakinka" "wlh Zainab ba dadin baki bane idan kina gani kamar karyane bari na ciro maki wayarta daga aljihu kiga text da kiran da takemi" "hannu yasa a aljihunsa zai ciro wayar' Zainab tace a'a ni babu ruwana wann tsakaniku ne" "to kiyi hkr Dan Allah Zainab wlh nayi maki alkawari insha Allahu bazan kara aikata kwatankwaci abinda da nake aikata maki a baya ba' kinji Zainab?" "naji". " yawwa Zainab dinta' amma fa banji kince kin yafemi ba?" "Allah ya yafe mana" "a'a Zainab h'akan yana nuni da ba'a yafe maka ba kenan'/idan har da gske kin yafemi cewa zakiyi ni Zainab na yafewa mijina zhrdee duniya da lahira" "ita kanta dariya mgnr yabata" "h'akan yasashi jawota ya rungumeta shima yana dariya' " gani yadda ta kwanta a jikinsa yasashi cewa yawwa ko kenan yanzu abinda za'ayi jeki ki dauko yara mutafi g'ida"... "da sauri Zainab ta cire jikinta daga nasa tana fadin wani g'idan k'uma?" "h'aba Zainab meyasa kikeson meda hannu agogo baya' bayan mugama mgn k'uma' na lura dake Zainab yadda nake sha'awarki da d'akin gani mu kasance tare ke bakyayi' idan ba haka ba yanzu fa kusan wata biyu bamu tare dake kina g'idan ku'idan banda abinda ke ko gajiya da zaman gidan bakiyi' naga wasu mata idan aka sake su har kuka sukeyi sbd basuson zama g'ida amma banda ke Zainab" "su ai kace' su k'uma daban nima daban" "to yanzu dai tunda bazaki bini yau ba zanzo na daukeki mutafi?" "nima bansani ba" "shikenan tunda hakane bari yanzu na shiga na tambayi inna da Abba" "a'a kabari kawai zan tambayesu da kaina" "yawwa ko kefa har naji dadi my Zainab' amma d'an Allah idan so samune inama gobe kidawo" "a'a wlh saidai nanda sati biyu" "na shiga uku sati biyu fa kikace' Ashe kinaso natare anan gidan kenan" "himm kawai Zainab tace' snn zhrdee yace ina wayarki?" "yana cikin g'ida" "gobe zan aiko da sako idan beyi makiba sai kiyi mgn" "Allah ya kaimu tace' nan sukaci gaba da hiransu zhrdee bebar g'idan su Zainab ba sai around 12AM snn sukai sallama h'ade da daukar kudi yabata ko zata bukaci wani abu" "washe gari zhrdee yana fita kasuwa waya yasiye d'an karere h'ade da zannuwa masu kyada tsada yabawa yaron shagonsa ya kaimata har g'ida" "Zainab ta nunawa innarta kayan' Inna tace Allah ya amfana" "tun daga lkcn kira da chat akai akai wani lkc har gajiya takeyi da zhrdee" "tun daga lkcn zhrdee besake zuwa gun Aisha ba' itama da rashin hkri koda ta kirasa baya dagawa k'uma besa tayi fushi' ta daina kiran ba' kullum cikin kiransa take tai kuwa baya kirguwa duk zhrdee yana tarasu batare daya krantasu ba" "duk da ba fita takeyi ba amma saida Aisha tasamu labarin Zainab zata koma gidan zhrdee' shiryawa tai ta musanman tacewa ummata zata g'idan ubaida' Aisha na fita bata tsaya ko'ina ba sai kasuwa shagon zhrdee" "duk da mmkin ganita da yai amma sai ya matse sbd kada yaran shagon sa susan halin da suke ciki' da fara'arsa yace har kin kariso?' kawo *shahida* sbd itace ke rike a hannu' yana daukarta suka shige cikin shagon' inda yake zaune yace ta zauna" "tunda suna zauna babu wanda ya tankawa d'an uwarsa' saima daure fuskan da zhrdee yai mata' jin motsi za'a shigone yasashi mikewa da fara'arsa yace tashi muje g'ida' yaran shagon a ta waje yatsaya yai sallama' tare suka fita daga cikin dakin karami dakin ganisa yasa zhrdee cewa bari naje na dawo" "a motarsa ya dauketa koda suka shiga be sake mata fuskaba har suka isa kofar gidan su' bayan yai parking har ta b'ude zata fita yace dakata" "tana tsayuwa yace da iziniwa kika fita' k'uma waye yace kibini kasuwa' yaushe muka fara haka dake?" "Aisha ja gani h'aka tasa kuka' ba kuka na tambayeki ba' amsa nakeson ji daga gareki" "cikin kuka take cewa d'an Allah kayi hkr sbd binka kasuwa danayi' amma k'uma abinda yasa na bika sbd koma na kiraka baka dagawa k'uma idan nayi mata text bana gani reply" "shine akace ki biyoni kasuwa?" "a'a ji nayi ance Zainab zata koma shine nazo na tambyeka har danine zankoma?" "idan inada bukatar ki koma da ban sanar dake ba?" "ko akace maki ita Zainab d'in gaban kan tayi batare da izinina ba?" "h'aba zhrdee meye haka sbd Allah? laifin me nayi maka h'aka?" "wlh Aisha idan ta nine babu abinda kikai mi' saidai Zainab" "ita tace nayi mata wani abu?" "wlh Zainab batace komai akanki ba' amma kinsan idan Zainab bata yafe manaba Allah ma bazai yafe mana bako?' wlh Aisha ba karami cutar Zainab mukeyi ba nidake' a lkcn soyayyarki ya rufemi ido bana gani kowa sai ke Aisha' kekuma kikai amfani da wnn damar kike yadda kikeso' Aisha tunda na aureki koda da wasane bantaba gani safiya yayi kinje kin gaida Hjy ba balle Abba' Aisha bakisan mutunci iyayena ba da yan'uwana' kinfi kowa sani banida wani gata a duniya face su' duk wani mataki da zantaka sune sila amma besa ki dubesu da wnn darajan ba' wnda nayi imani ida iyayenkine bazaki iya masu haka ba' wlh Aisha sbd ke yasa na daina jin mgnr iyayena' na daina masu biyayya duk sbd ke' wlh Aisha nayi nadamar aurenki".... " toni ina ruwana?" "wlh idan bakimin shiru ba a yadda nakeso yanzu saina rubuta maki takardanki".. " tunda Aisha taji haka bata sake mgn ba" "zhrdee yaci gaba da cewa wlh Aisha kinban mmki asanadiyar najasa yiwa iyayena biyayya' sbd soyayyar dake tsakani da da Uwa ko uba yasa suka nimamin auren Zainab amma sbd soyayyar ki nakasa rike amanr da suka bani' inda ace su mutu kafin na rokesu gafara ba' yaya kikeso nayi" "Aisha sbd soyayyar ki har sabawa ubanagijina nakeyi na dauki hakkin wata nabaki baki taba nunami h'akan da nakeyi ba daidai ba ne' na lura dake Aisha idan za'a bakanta ma wata ke a faranta maki ba damuwarki bane" "to wlh bazan yarda ba Dan bazan yarda sbd ke ranar lahira natashi da barin jikina a shanye ba' idan har zakibi yadda Allah yace kofa a b'ude take idan k'uma ba hakaba Allah ya h'ada kowa da abokin arzikinsa' wawiya mara kunyar banza kawai' wlh Aisha dukan abinda kikemi inda Zainab ce bazatayiba' sbd Zainab tafijin mgn ta' gashi sbd rashin jin mgnrki zakisa abanza kawai" "to bari kiji nagaji da irin wnn halin taki' idan bazan yarda Allah yakamani da laifi ba" "kuka kawai Aisha keyi har zhrdee yakare mgnrsa'ga yara a hannunta da suke bcc" "bayan ya karene tace to yanzu wani hukunci ka yanke akaina?" "idan har kinason zama dani saikinje kinbawa Zainab hkr' dan ita muka zalunta k'uma kece sila ga duk abinda na aikata" "naje nabawa Zainab hkr kace fa?" "kwarai da gske' ko ban'isa bane?" "ka'isa amma bazani ba saidai idan sanadiyar haka yazamo itace silar rabuwarmu dakai" "alhamdllh' tunda ke kika zabi haka' Allah ya h'ada kowa da abonki arzikinsa" "Aisha tace amin" "fitami daga motata" "batare da musuba tabude ta fita rungumeta da yara a hannunta" "ina zaki kaimisu?" "shiru Aisha tai ta zuba masa ido" "ko kallon ida take beyiba yace zubami yarana" "Aisha dake tsaye tasake fashewa da kuka" "da kefa nakeyi ko bakiji abinda nake fadi bane?" "Aisha najin h'aka ta zuba masa yaransa a mota' hannu yasa ya jawo murfin motar yarufe snn ya fisgi motarsa yabar layin" "ihu tasa tashige cikin g'ida tana kuka" ☘☘ ☘ *AURE IBADA NE* FASAHA ONLINE WRITES. F.O.W. ☘. 🌳 *impacting valuable knowledge and entertainment is our concern* 🌳 *story written by Mmn uswan* 6⃣3⃣ "Aisha tana shiga cikin g'ida da ihu tana kuka' jin kukanta ne yasa umma fitowa a guje daga dakinta h'ade da tambyar lfy Aisha?" "cikin kuka Aisha ke cewa umma zhrdee' zhrdee umma" "zhrdee' me yasamu zhrdee d'in Aisha?" "zhrdee ummata wayyoo zhrdee" "mutuwa ne zhrdee d'in yayi komai Aisha?" "kukane yaci karfin Aisha yasa takasa mgn" "gani h'aka yasa umma ta kama Aisha zuwa d'aki' bayan su shiga dakine umma ta dauki waya ta kira Abba bbn Aisha a kasuwa' yana gani kiran hafsatu ya daga sbd yasan ba kasafai take kiransanba idan yana kasuwa sbd

Chapter 35 of 38