Share this page
suga niman Rukky' sbd idan ba kawo Rukky sukai ba ba basu bill yan'uwarsu za'ayi ba' k'uma kusan ace shine g'ida *head of the family bafa na girman shekaruba' kusan yanzu wata yanayine muka shiga idan har Allah ya b'ude kama ya k'uma hore maka abin hannu to fa kaine babba a g'ida me f'ada aji' Allah ya rufa mana asirin duniya da lahira amin* dole duk inda zasu shiga zasu dan ceto yan'uwarsu daga halin dayake cikin' kowa a family nasa advance d'in' daya daga cikinsu mai suna Bb Habu yace tunda abu ya zama h'aka me zai hana baza'a tambyi tsohon mijinta ba ko Allah zaisa a dace" daya daga cikinsu yace ta yaya za'a kirasa bayan irin labarin da mukaji akan abinda data aikata masa' ko so kake allura ya tone galma' to wlh koda wasane wani ya sake ya kirasa nidai babu hannuna a cikin abinda zaije ya dawo" "duk jama'ar dake zaure babu Wanda ya tanka' bcoz Alhj isa shine me kudin g'idan' k'uma idan ba shiba babu wanda zai'iya jada Honorable' dan h'aka kowa ya shiga juyayin ta'ina zasu bolewa lamarin?' "a h'aka dai metting ya tashi babu wata mafita da suka samu" "zhrdee a hankali jiki yananan yana sauki shida Aisha' duk da ba wani sauki yaji sosai ba amma baya sauraran Aisha' koda safe yayi tana kwance idan tace masa ina kwana' lfy kawai yake cewa daga snn bazai kara amsawa ba' idan ko har ta tanka mata tofa lkcn duk yan'uwa su hadune anata faman hira shine yake sa baki';shima jifa jifa yake sawa" "duk da iskancin Aisha amma a wnn karo tayi sanyi sosai' kome tagani Ohooo?" "tunda Honorable yasa aka rufe Rukky besake lekawaba' itama kanta tasan dai a station take amma batasan wanda yasa yaka kamotaba sbd kwanta kwanta bata kawo tunanin Honorable zaiyi mata h'aka ba' a tunaninta yariga ya yafe mata" *waye Honorable* *_Alhj imran_* _haifanfen garin gwambe ne tun farkon rayuwarsa besan kowani irin sana'aba idan ba siyasaba tun yana concilor har ya kai ga chiaman' bayan ya dauka daga chiaman ne jama'ar gari suka siye masa takardan dan majalisan dattawa gani su samu progress a local government nasu yasa suka sake siye masa masa wata takardan na *house of rep* (Dan majalisan ta raiya) wata rana yana dawowa daga abuja to gwambe ne ya hadu da Rukky duk da a lkcn kanta be waye kamar yanzu ba' sbd a lkcn secondry kawai takare' daga sann mgnr aure ya shiga tsakanisu' koda ya aureta yanada mata daya da yara biyar dan h'aka ita ya barta a gwambe kowani weekend yake zuwa' yaban saukarsa yai parking ya dawo g'ida gaba daya' wata shekara da yazo yafito niman senator' duk uban kudin daya kashe beciba' sakamakon matsala daya samu anhada baki da abokinsa aka manaficcesa' k'uma gudumuwar Rukky sbd abokin Honorable tunda ya lura Rukky yarinyace meso kudi yasashi amfani da wnn damar ya yaudareta da kudi duk wasu sirikan mijinta tana bashi' daga hakane suka koma farka da junarsu' ko kafin Honorable ya falka suriga suci gari' a lkcn da yaso hukutata Rukky ta nimin kasheshi akan idan ya mutu saita kwashi dukiyar taje ta auri abokinsa' Allah ba arzalumin bawansaba asirinta yatonu' a lkcn da yakeda shirin kamata Rukky ta kwashe masa dukiya tabar garin_ "bayan sati biyu da kwanciyar zhrdee a hospital Bbn Zainab ya matsa mata adole sai taje ta gaida zhrdee' a yau kam babu yadda zatayi sbd abbanta ya sata gaba' ciki ta koma tai kwalliya cikin riga da sket na material pink colour h'ade da mayafinta snn taiwa *Islaha* itama kwalliya cikin Dan kanti duk suyi kyauta abbanta ya sata gaba yace suje *Islaha*na hannunsa suka shiga mota' saida zaiyi driving ne ya mikewa Zainab yarinya" "suna isa yasake daukarta suka nufi d'akin da zhrdee ke kwance' Abba na gaba Zainab na baya suka shiga da sallama gun zhrdee kawai suka nufa lkcn yya Nurudee ne kawai a d'akin' cikin girmamawa ya gaida Bbn Zainab shima ya amsa' Zainab suna h'ada ido da zhrdee ya sakar mata murmushi' ita kuwa daure fuskanta tai babu alamar wasa a cikinta" "kujeran da yya Nurudee yake zaune ya mike yabawa Bbn Zainab ya zauna' *Islaha* NA gani bbnta ta mika hannu ya dauketa murmushi zhrdee yai h'ade da mika hannu" "Abba na gani h'aka ya ije kasa yarinyar kusa dashi' juyawar da zaiyine ya tuno Aisha na d'akin' suka gaisa h'ade da gaisheta ta jiki" "gani har a lkcn Zainab batace kala ba' kallo daya yai mata ta fahimci abinda yake nufi snn ta gaida zhrdee da jiki" "b'akin zhrdee har kunni ya amsa' juyawa tai ta gaida Aisha itama' a cikin zcyrta tana f'adi sbd Allah' matsawa zhrdee yai yace tazo ta zauna' ko kallo be Ashe taba tamkar bada ita yakeyi ba" 'gani h'aka yaci gaba da wasa da yarsa' saida suka juma snn Abba ya mike sukai sallama' yaso daukar yarinya amma gani yadda zhrdee ya riketa yasashi fita a d'akin' hannu Zainab tasa zata dauki yarta zhrdee ya rike mata hannu' Aisha dake kwance tana gani h'aka ta juya masu baya" "ido kawai ya zuba mata yana kallonta cikin ido h'ade da murmushi' fisge hannunta Zainab tayi ta dauki yarta tafice daga d'akin" "shiru shiru da police sukaji akan Rukky tunda Honorable ya basu ita besake waiwayarta ba' sukuma yan'sanda suna niman guri ije wasu yasa suka kaita kotu' daganan aka wuce da'ita pirizi"""""" ☘☘ ☘ *AURE IBADA NE* FASAHA ONLINE WRITES. F.O.w☘. 🌳 *impacting valuable knowledge and entertainment is our concern* 🌳 *story written by Mmn uswan* _*Dan Allah kuyi hakuri na rashin jina kwana biyu'mahaaifin mai g'ida nane Allah yayi masa rasuwa shiyasa'duk da nasan Mmn ahamed ta sanar amma ba lalla bane ace kowa ya sani' ngd sosai Allah yabar zumuci*_ _~*masu kirana suma ngd Allah ya kara kauna da zumuci amin*~_ 6⃣0⃣ "bayan kwana biyu da kai Rukky prizi'bbn Habu kani mahaifin Rukky ya yanke shawaran kira Honorable ya tambyesa ko yaji labarin ta' amma k'uma kada allura ya tono galma' wata zcy tace kirasa kawai' idan ma yaji ko allura ta tono galma menene?' Ai dama ba'a gane maci tuwo sai miya ya kare' k'uma inda ba kasa Ai nan ake gardaman kokuwa' indama Allah zaisa a ganta a sakomi dan uwana ita ba damuwana bace' kowa yadibo da zafi bakinsa" "wayarsa ya ciro daga aljihunsa ya lalibo numr Honorable kira biyu a cikin na uku ne ya daga wayar gani numr Bb Habu ne yasashi kwantar dakai h'ade da sallama' dama dabi'ar Alhj imran ne akwai girmama na gaba dashi'balle k'uma ace sirikinsa" "Bb Habu yaji dadin irin amsawar da Alhj imran yai masa dama yasa wala kanci ba halin Alhj imran bane amma dan adam yana iya canzawa a kowani lkc' shiyasa yai shayin kiransa' jin yanayin yadda ya amsa sallamar yabawa BH Habu karfin gwiwan mgn' bayan su gaisa cikin shakku h'ade da nuna kunya ta Hausa Fulani Bb Habu yace dama!!! dama!!!" b"dama me?" "murmushi ya karayi snn ya sake da dama' yana susakansa kamar yana ganisa" "baffa idan akwai wata matsala ce kayi ngd kawai kada kaji komai" "dama Dan Allah wata tambya nakeso nayi maka amma bansan yadda zaka dauki abinba" "babu komai baffa isha Allahu' Allah k'uma yasa nasani" "dama mgn ce akan Rukky?"... " wacce Rukky k'uma baffa?' ai ni yanzu banida matsala da'ita" "eh musan da h'aka' amma Dan Allah koda labarinta bakajin?" "a'a baffa banaji" "Ohooo!!! innalillahiwainnailaihi raju'un' mukan mushiga uku da wann yarinyar?" lfy baffa kake irin wnn salati da salallami" "kaidai Alhj bari kawai' wlhy wata matsalace ta taso". " wacce irin matsala haka baffa?" "hiimm wlhy dai to" "a'a baffa Dan Allah kayi mgn mana" "to wlhy dai matsala ce wacce tazama dole sai da Rukky agun snn matsalar zata warware" "wacce irin matsalace h'aka wacce baza'a iya warwareta ba saida Rukky" "amma baffa idan baka mance ba lkcn da muka samu matsala da Rukky ban boye maku komai ba a matsayinku na magabatanta sai dai k'uma mmkin da kuka bani baffa bazan boye maku ba k'uma ni kaina nasan Rukky tana tare daku kuka boyeta kukace bata tare daku' inaji ina gani h'aka na tafi na kyaleku' badan kufi karfin naja daku ba a'a sbd alkawari nayiwa kaina idan bera na yawo mage na yawo wataran za'a hadu' shiyasa na tafi kawai" "eh h'aka ne amma wlhy ba laifina bane' indama anbi tawa wlhy tun kofar da bahaka ba" "amma Dan Allah kayi hkr ka taimakemu idan har kasan inda take ka sanar mana' badan mu ko ita zakayi ba Dan Allah zakayi" "toni baffa yanzu bansan abinda kake bukata a guna ba" "eh to tunda abin tazama h'aka kasan hausawa suce ranar wanka ba'a boye cibi' abokin kuka ake fadiwa mutuwa inda kasan zaka tsira nan zafa rabe' ba komai bane yasa nake rabe rabe amma tunda abin yazama h'aka dole na sanar maka da komai' ko lkcn da kazo niman Rukky bazan boye makaba Rukky tana cikin g'ida amma abinda yasa banyi mgn ba sbd kada ace Dan bani na haifeta ba' kasan yadda mgnr duniya yake yanzu kaji dalilin kenan" "himm baffa kenan' bayan haka k'uma?" "eh bayan wasu lkcn shine tasake wani aure' bari na yanke maka labari bayan watanni da aurenta suka samu matsala da maigidanta ta sokesa da wuka k'uma ta soke abokitar zamanta' tana aikata h'aka ko g'ida bata zoba barin garin tai tunda ta tafi babu lbrinta' hukuma tasa aka kama ubanta' yanzu da h'aka ubanta yanana a rufe bazasu bada belinsa ba sai ankawo Rukky' wlhy babu inda bamujeba amma batanan" "ikon Allah yanzu bbnta yana rufe?" "wlhy kuwa" "baffa kenan' bazan boye maka ba' Rukky tana tare dani' yanzu da h'aka tana hannu hukuma' a nan cikin garin gwambe" "Allah me iko' to yanzu Alhj babu yadda za'ayi?" "eh to bazan iya cewa eh' ko a'a ba' sai abinda hukuma suka yanke akanta" "to shikenan Alhj mugode" "bayan suyi sallama ne Bb Habu yaje cikin family hause yake sanar masu yadda sukai da Honorable' daga nan suka kwashi zoga zuwa g'idan Alhj Kailani Bbn zhrdee' da fara'arsa ya amshesu bayan su gaisa ne bba Habu yace dama Alhj Dan Allah muro cin wata arziki ne a gunka" "murmushi kawai yai sbd yariga yasan abinda ke tafe dasu' saidai ya matse h'ade da cewa ina sauraranka" "akan mgnr d'an Uwa nane Alhj' Dan Allah Dan annabi Dan soyayyar da kakewa shugabanmu annabi muhammadu ( S.A.W.) d'an soyayyar da kakewa iyayenka Alhj" "murmushi Abba ya sukeyi snn yace to yanzu me kukaso ayi maku ne?" "Alhj Dan Allah ka taimakemu kasa b'akin a sako mana d'an Uwa' wlh Alhj duk lkcn da Rukky ta dawo garin nan ni da kaina zankawo maka ita" "himm Malam Habu kenan' yanzu sbd Allah idan danka akaiwa haka zakaji dadi?' kashin kaifa taso yi Dan ma Allah ya takaita abun da kilan duk su rasa ransu" "eh duk musan da h'aka mudai Dan Allah hkr kawai zakayi' tunda ma Allah ya takaita abu" "Malam Habu kenan nifa har yanzu ban fahimceka ba' nasa hannu a sakota ni k'uma jini dana yatafi a banza kenan' shine ban fahimtaba' yarinyar banza kawai ni wlh tun farko banso auren ba d'an dai kawai lekewa da yai ne amma idan ba h'aka ba me ake da yar'daba" "uhmm Alhj adaiyi hkr wlh kasan yadda yaran zamaniga suke sarai ka haifi mutune baka haifi halinsaba' k'uma nima kaina banso abari Rukky ta sake wani auren ba' tunda ba'ariga an gama kashe wacan wutar ba' to amma babu yadda na'iya" "kamar yaya ban fahimceka ba Malam Habu?" "ina nufin tunda ga case din g'idan tsohon mijinta ba'ariga an kashe ba" dama kusan da h'aka ne kuka bari dana ya aure?" "to mudai Dan Allah hkr zakayi" "tambya nayi baka bani amsata ba Malam Habu?" "eh to dama'''' daga nan ne Malam Habu ya zare ya fadiwa Alhj Kailani komai akan Rukky' babu abinda ya boye masa" "shiru Abba yai yana jijina lamarin h'ade da Allah ya kyauta snn ya mike h'ade da cewa tashi muje' suma mikewa sukai zuwa station d'in" "suna isa bayan ya shiga daga ciki ne police da suka tsare da *Alhj isa* suka gaisa snn police sukace Alhj lfy?' Abba dasu tsaye yace yanaso gani *D P O* daya daga cikin police mai suna Anthony ba Hausa ne yakeji sosai ba *duk da dama minority not majority ba wani ilimine dasu a akwai qua(means dakikai) wanda koda statement basu iya rubutawa* yace daga ciki but before yau enter late me tolk to him" "Abba dake tsaye yace OK *Sr* " yana shiga ya fito yacewa Abba yashiga' Abba yana shiga suka gaisa bayan su gaisa ne Abba yace dama akan case d'in nan ne shine nazo a badashi beli" " *DPO sa'eed* yai murmushi snn yace amma Alhj kasan koda kai kayafe government suna da nasu hakkin ko? " "eh *DPO* nasan da h'aka amma d'an Allah kuyi hkr sbd Allah idan yarinyar tadawo garin nin ni da kaina zankawo maka ita insha Allahu" "to *Alhj Kailani* dama duk wnn fineting d'an kai mukeyi da k'uma kare hakki a matsayinsa na d'an kasane amma tunda h'aka kace babu damuwa" "shiru Abba yai be tanka ba' *DPO Sa'eed* yabashi wasu file ya cika h'ade da *SING* snn yasa aka fito dasu'da sauri Malam Habu yaje ya rungume d'an uwansa' ko kallonsu Abba beyiba yai ficewarsa" ~~~~ ~~~~ ~~~~ "bayan fitar dakaban Fatima zarawara sai faman tururuwa sukeyi zuwa gunta' wasu suzo Dan Allah suwa k'uma d'an abinda Nasir ya bari mata" _*wata yanayine yanzu Allah ya kawomu mundu Allah yaiwa mijinka rasuwa balle yanada abin hannu ko nace rufan asiri' to fa zawarawa saika turo' badan sbd komai ba' sbd kwadayin abinda aka barmaka" Idan suka samu wawiya k'uma shikenan sai abinda Allah yayi' sbd zasuyi iya kokarinsu wajan gani su aurenka' bayan aure da d'an kwanaki ko watanni daga lkcn zasu fara tunanin yadda zasu shawo kanka wajan gani su cinye d'an abinda miji ya bari maka' ba damuwarsu marayun da aka barki dasu ba ko k'uma kedin a'a damuwarsu dukiyar da mijinki ya bari miki' da zaran su yayi dukiyar shikenan dama abinda yakawosu kenan' Allah yasa mudace' ya karemu da sharrin irin su amin*_ _*shiyasa yana da'kyau mu mata mukula da'kyau Dan Allah a duk lkcn da h'akan ta samesu' muyi kokarin kai hakalinmu nisa da k'uma yaki da zcyrmu wajan gani mu yaketa' sbd ba lalla bane ka gane na Allah' tunda abin ba'a goshi yake rubuce ba balle kace ka gane na k8rki' a lkcn da idan kac3 kanada marayu zakaji zawarΓ wan suce babu komai su amince' bayan anyi auren suna kwashi dukiyar shikenan' idan k'uma h'akan be samuba sai kaga rawa ya canza' da zaran kida ya canza dole rawa shima ya canza' daga lkcn sai kaga ayi ta dauki ba dade kakoma kana yaya zakayi kana dakasani' Allah ya rabamu da aikin danasani duniya da lahira amin*_ "gani h'aka yasa mahaifin Fatima ya sameta har daki lkcn ta idar da sallar isha tana zaune kan sallaya tana lazumi abbanta yai sallama' ya shigone yasa Fatima shafawa snn ta amsa da Bb kaine da kanka h'ak?" "wlh kuwa Fatima dita' sallah kikeyi ne h'aka?" "eh Bb amma na'idar" "Allah ya karba" "amin Bb" "Fatima dama guki nazo" "ni k'uma Bb?" "eh wlh" "Allah yasa dai lfy" "dama ba wata mgn bace Fatima mgnr zawarawankine Fatima a gskya banajin dadin yadda kike walakansu Fatima'idan baki sonsu be kamata kina walakanta su' idan kisan zcy ko b'akin wani Ai bakisan na wani ba' k'uma ke ba abin alfahari bane ace baki dade da fita takaba ba kika samu manimi ba' ki duba fa sbd Allah yadda *Alhj AMINU* yake ta ziriya a kanki"... " wani *Alhj Aminu* k'uma bba? " *Alhj AMINU* mana wanda yake aiki a *ministry of foreign affair* amma yanzu yana zaune a London ne shida matarsa" "himm kawai Fatima tace" "wlh Fatima ya kwana biyu yanami mgnrki yanason zuwa amma yana tsoron yadda kikewa masu zuwa shima kizo kimasa shiyasa yazo ta hannuna yai min mgn" "nidai gskya Abba kayi hkr kawai" "nayi hkr dame Fatima?' h'aba Fatima wacce irin yarinya kikeso ki zama ne sbd Allah yanzu kin gwammaci ki zauna h'aka babu aure?" "kuka Fatima nata f'adin nidai wlh babu wani auren da zanyi' sbd Allah d'an mijina ya rasu akace dole sainayi wani aure aini ba h'aka mukayi dashi". " shiwa k'uma Fatima. *Alhj AMANU* kowa? " "a'a shidai Nasir d'in". " h'aba Fatima kanki daya ne kuwa yanzu har wani alkawari kuka tsakaniku ke dashi?" "eh Abba k'uma ni bazan iya cin amanarsa ba" "to wlh baki isaba Fatima aure k'uma dole sai kin yita" "Fatima najin h'aka tasa ihu h'ade da kiran wayyo Allah na Nasir katafi ka barni Nasir wayyo mutuwa nashiga uku na lalace" "gani irin kukan da Fatima keyi yasa Abba cewa Fatima kukan ya'isa h'aka d'an Allah nifa ba cewa nayi dole sai kinyi aure yanzu ba balle ki nimi ki tarami jama'a kina jina Fatima" "cikin kuka Fatima ta daga masa kai" "to ya'isa h'aka banaso ina gani hawaye suna zubowa daga fuskanki' kina jini na bar mgnr tunda bakiso' amma sai kinbar kukan nan da kikeyi' hannu Fatima tasa ta guge hawayenta' daga snn bbnta yaita janta da hira har tasaki jiki sukai hira sosai" "mahaifin Fatima yai mata hakane sbd a rayuwarsa bayason gani ranta ya baci balle har shine yasata kuka da kansa' yanzu ya kyaletane zuwa wani lkc snn yasake tutubarta da mgnr' k'uma yasan babu wani alkawarin da sukai da Nasir tsabar soyayyar da sukewa junane kawai yasa Fatima take f'adin h'aka" "tun daga lkcn Bbn Fatima besake tutubarta da mgnr *Alhj aminu* koda yazo iya kacinsa gun bbnta kawai' a kullum hkr abbanta yake bawa *Alhj aminu* shima dayake wayayyene cewa yake babu komai kada ya damu yarinya ce wataran sai labari' *Alhj aminu* ya f'adi h'aka badan abin baya damusa bane a'a saidan darajan soyayyar da yake yibata" " *Alhj AMINU da matarsa mai suna MARIYA haifanfun yan' bauchi ne shida matarsa tun bayan samu aikinsa a cikin garin abuja ne ya dauki matarsa da yaransa suka dawo abuja da zama da yaransa guda hudu dayake rayuwar turawa ne sukayi' daga snn aka turasa London tun daga lkcn acan yake zaune shida iyalansa' Alhj AMINU dan kimani 45-50 years ne matarsa kuwa saidai suzo sa'a da Fatima' Mariya macce me kirki da mutunci kusan halaiyansu daya da me g'idan ta' saidai kash mutum tara yake becika goma ba' sbd Hjy Mariya macce ba meso alkairi ba k'uma bataso mijinta yai shima daya gane h'aka koda abu zai baka saiya duba idan batagun sbd a zauna lfy badan tsoro ba' amma bayan h'aka batada kowani matsala* ~~~~ ~~~~ ~~~~ "a yau ne 17- 5- 2018 za'a shiga kotu da Rukky da honorable karfe ten o'clock shapp suka shiga kotu bayan aalkali ya shigone duk jama'ar dake zaune cikin kotun suka mike tsaye' bayan alkali ya zauna ne suma suka zauna alkali ya bukaci Honorable ya gabatar da kansa' bayan Honorable ya gabatar da kansa snn itama Rukky ta gabatar da kanta alkali yace ina lauyanlauyan dake kare Alhj imran *barrister al'kasim* yace gani" "snn alkali yace ina lauyan dake kare Rukky?" "Rukky batadashi" "alkali yace governing zata baki lauya' alkali ya umarci *Alhj imran* yai mgn h'ade da rantsuwar zai f'adi gskya' ni *Alhj imran* ina zargin tsohowar mamata Rukky da cin amanataamanata amanata" "amana kamar yaya?" "tanabin maza da aurena akanta h'ade da kwashemi dukiya ta" "alkali yace ke Rukky kinajin abinda tsohon mijinki yace yana zarginki dashi ko?" "eh najisa amma abinda yake zargina dashi bansani ba" " *Alhj imran* to kaji abinda tace" "wlh karya takeyi idan ta musa h'akan inada sheda" "shedar yananan ne?" "a'a bayanan saidai abani lkc nazo dashi" "alkali yace andaga wnn shari'a zuwa 7-6-18' daukar Rukky akai aka medata zuwa g'idan maza" "yau ne aka sallami zhrdee da Aisha su Abba da yya Shamsudee da Hjy suka kwashi kaya zuwa mota' har su h'ade dana Aisha zhrdee yace acire nata kayan g'idan su zataje" "Abba da Hjy har suna h'ada baki wajan tambyarsa kamar yaya' itama aishan dake tsaye jikinta amace yake idanunta duk su ciko da kwalla" "fuska a daure yace nace tatafi gidansu ko yayane?" "son kanka daya kuwa?" "klau nake Abba aurene da'ita banayi" "Aisha najin h'aka tafashe da kuka" "zhrdee wai menene h'aka ne' ke Aisha shige muje" "na rantse da Allah idan kika shiga motar nan idan ban maki dukan masifa faba kice me?" "wani irin duka k'uma zhrdee idan ba kasheta zakayi ba?" "gara yar'banza tamutu kowa ya huta ni ba kasheni taso ayiba?" "wlh Hjy ta tafi kawai tun kafin na yanke alakata da'ita kwata kwata muguwa alzaluma mara jin mgn kawai' wlh Aisha na tsaneki banason ganiki kwata kwata k'uma sai Allah ya sakami nida Zainab" "shiru Abba da Hjy sukai'aisha dake tsaye dukawa tai a gaban zhrdee h'ade da rike masa kafafuwarsa tana kuka tana ambaton kayafemi d'an Allah" "duk da a rike yake amma behana zhrdee sa kafa ya tokare Aisha ba tafadi kansa tana kuka" "har ya sake daga kafa zai kaimata wani da sauri Abba yazo ya rikesa aka sashi a mota" "Abba yace Hjy taraka Aisha g'idan su kawai" "zhrdee yana zaune yana faman huci' duk da azabar zafin da yakeji amma be hanasa bala'i ba" "Hjy ta kama Aisha zuwa mota' su Abba sukai hanyar g'ida' ita k'uma Aisha da Hjy sukai hanyar g'idan su Aisha""""" πŸ“–βœ ☘☘ ☘ *AURE IBADA NE* FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.☘. 🌳 *impacting valuable knowledge and entertainment is our concern* 🌳 *story written by Mmn uswan* 6⃣1⃣ "suna cikin mota suna tafe Abba yace gskya son banji dadin abinda kaiwa Aisha ba"... " h'aba Abba bakaji dadi ba kace?' to wlh kadan nayi mata' inda ta sake ta biyoni g'idan nan Allah kadai yasan irin abinda zanyi mata' wawiya kawai dakikiya mara jin mgn" "is OK son kaga bakada lfy ko?' kayi hkr h'aka" "himm Abba kenan' sauran itama Rukky wlh har g'idan ubanta zantura a kamota" "wacce Rukky k'uma?" "Rukky mana Abba" "yanzu son duk abinda nayi akanka baka gani ba kenan?" "kayi hkr Abba bansan kayi wani abu akai bane shiyasa" "h'aba son a aikata maka danya danyar aiki irin wnn ace ban dauki mataki ba?' kaima kasan sai inda karfina ya kare" "h'aka ne Abba ngd" "tunda aka shiga mota Aisha kewa Hjy kuka' Hjy tayi lalashi har tagaji Aisha batai shiru ba' gani h'aka yasa tafita harkanta har suka isa g'idan su' bayan yya Nurudee yai parking Hjy ta taimaka mata ta fito daga motar snn ta riketa har cikin g'ida' Bbn Aisha da ummata tayi mmki gani sudawo da Aisha g'ida' sbd basu lkcn da akayi sallama'bayan Aisha ta zauna ne suka gaisa cikin girmama juna abbanta Aisha cikin kosawa yace yaya naga Aisha kindawo da'ita nan ba g'idan mijinta?" "Aisha najin h'aka tasa kuka' dama dan tutuben harshe suka samu ita sa maigidan nata amma insha Allahu idan komai ya daidai anjima zanzo na dauketa mutafi" "to Allah ya kyauta" "amin Hjy tace h'ade da mikewa sukai sallama tafita" "su Abba suna g'ida bayan Abba ya fito snn yarike wa son hannu shiga yafito suna shiga bangaren zhrdee yya Shamsudee yace Abba bekama a barsa nan ba tunda babu kowa" "eh k'uma hakane' to yanzu abinda za'ayi mukaisa dakina kawai' d'akin ka k'uma Abba?' eh dakina kaga ku yanzu ba g'ida kukeba balle nace zanbarsa a bangarenku' bangarensa k'uma babu kowa a gun' to shikenan Abba" "d'akin Abba suka shiga da kayansa sukuma suna zaune a parlour Hjy tai sallama' ganisu a parlour ne yasa itama ta zauna' duk mgnr da sukeyi akan su Aisha zhrdee be tanka masu ba har sukayi suka kare" *Rukky* "a yau ne Rukky da zhrdee zasu koma kotu' bayan alkali ya zauna snn ya umarci Honorable ya fito bayan ya fito ne akace Rukky itama ta fito duk saida suka fito snn akace idan shedan da Honorable yace zai kawo yazo yafito" "jin haka Honorable yace eh yana kusa" masinja yace ya shigo dashi' bayan Bb maigadi ya fito ne alkali ya ke tambyarsa alakarsa *Bbn idi maigadi* yace nidai gadi nakewa

Chapter 33 of 38