"to zasuji".
"zahrdee be dade da fitaba Zainab ta fito ita da inna Hulaira' bayan Zainab ta fitane Huaira ke tanbayar Alhj dama wnn shine yaro da kakegaya mana?".
"Eh" shine".
"Allah sarki' gskya nayaba da hnklinsa Allah yasa ayi damu.
"amin Alhj yace".
"duk sa Hjy Saratu mmnr Zainab taji dadin abin amma saita matse.
"zahrdee yana fita komawa mota yai ya zauna'be dade da zama ba Zainab ta fito'da sallama ta kariso gun.
"kusa da motar taja ta tsaya' gani h'aka yasa zahrdee fitowa daga motar ya zagayo.
"jikin motar ya jingina suna fuskantar juna' Zainab tace sannu da zuwa".
"yawwa'snnu 'yar mata.
"kina lfy?"
"lfy klau".
ya kike ya g'ida da hutu k'uma' tunda angama karatu ko?".
"Eh"h'aka ne result kawai muke jira".
"to Allah ya taimaka".
"amin'ngd".
"yah!! sunar malamar nema namance?".
"zainab".
"OK" srry h'aka fa akace".
"to zainab nasan basai nace komai ba' sbd duk wata abinda zanfadi anriga da ansanar dake daga g'ida ko?".
"Eh" h'aka ne".
"to yah!! kika gani nayi maki?" idan kinsan banyi makiba Dan Allah zafi kowa jin dadi sbd bazanso ayi maki doleba".
"ba badamuwa Zainab nayi maki?".
"saida Zainab tasa mayafi ta rufe fuska snn tace eh".
"wani irin bakin cikine yai kululu ya tokari zcyr zahrdee.
"to shikenan tunda kince nayi maki ngd'".
"nima ngd".
"zantafi amma Dan Allah kiyi hkr sbd bazan samo dawowa cikin satin nan".
"to sai yaushe zaka dawo".
"uhmmm!!" to maybe nest upper week.
"babu damuwa' ubangiji Allah yasa mukai.
"amin ngd".
"ni zabshige ciki".
"to zainab amma Dan Allah minti daya".
"komawa yai cikin mota ya memo h'ade da pen yadawo' gashi Dan Allah ki rubutami number wayatane babu caji shiyasa amma idan naje gida nai caji zakiji kirana.
"to shikenan".
"amsa Zainab tai ta rubuta masa snn ta mika masa.
"zainab ngd saikin jini".
"shikenan".
"ga sako Dan Allah".
"tsayawa tai taga wani sakone".
"ledar shoping din da yai ya dauko ya mika mata snn sukai sallama.
"zainab na shiga ije ledar tai a gaban Hjy hulaira snn tashige dakin su'dama lkcn Alhj Musa baya gun' budewa Hjy Hulaira takeyi tana fito da kayan daya bayan daya tana sambarka.
"gani Hjy Mmn Zainab batasa hannu ba yasata dibo kaya ta zuba mata a jiki' murmushi kawai tai batare da mgn ba.
"zahrdee yana isa gida dakinsa yashige' har Aisha tafara bcc shigowar shine yasa ta tashi hade da yimasa sannu da zuwa.
"bayan kwana biyu Abba yaje gidan su Alhj Musa suka daedaeta aka yanke masa sadaki hade da rana 16 October ranar jumma'a kenan yafito masu.
"Alhj Kailani yai murna sosae.
"tunda zahrdee yabar gidan su Zainab be kirata ba banle anyi mgnr zuwa.
"mmki sosae Yakama Zainab wani lkc sai taji kamar ta sanarwa inna Hulaira' amma dai sae tace bari takara daga masa kafa zuwa kwana biyu tagani.
"Abba ya hada Shamsudee da Nurudee yace saedai sufito da matar da zasu aure idan ba h'aka ba da kansa zai samo masu' shidae Shamsudee cewa yai yarinyar da yakeso a wnn shekarane zata zana weac din' ayi masa uzuri har takare.
"amma yace kai fa Nurudee shikuma yace habiba yakeso 'yar gidan Alhj sani shima koda yaje da mgnr aure cewa yai bayaso yaita bawa mutani wahala yafiso ayi gaba daya da sauran yaran gidan wata kanin habiba kenan suma wnn shekarane zasu kare karatu idan su kammala sai ayi mgnr auren kawai tunda gidan mazansu ma har sukai komai.
"to yanzu muma so suke mukai kenan?".
"a'a" Abba kabari dai lkcn yai tuku.
"to kenan amma Dan Allah kuyi kokari sbd banaso wann shekara takare batare da munada mata ba' kuna gani kaniku kenan har zaije ga nabiyu amma Ku dakuke manya ace bakuda ko daya.
"duk dariya sukasa.
"bangare Hjy kuwa sai faman shirye-shirye takeyi babu kama hannu yaro binni da kauye ta aika ba kamar lkcn bikin Aisha ba wanda ma suke binni ba kowane yasani ba banle na kauye.
"anko kuwa anyishi yakai kala biyar ko wacce rana da nata.
"kan Aisha ya daure sbd mafi yawanci lokuta takan sacijin kamar ana mgnr biki k'uma sunar zahrdee ake ambato.
"wani tunani daya zomata tace kodae na tambayesa ne?" can k'uma tace bari kawai na barsa idan yai ra'ayi dan kansa zai sanar dani tunda baya boyemi komai.
"zahrdee be kira Aisha ba saida yarage saura sati biyu bayan ta idar da sallar azahar tana zaune kan sallaya saiga kiran zahrdee yashigo' gani bakon number yasa taki dagawa har wayar ta tsinke.
"har ta mike saega wani kiran yashigo'gani kiran bame karewa bane yasa ta daga danjin wake damuta da kira h'aka.
"tana dagawa da sallama taji duk da bata gane muryaba amma besa taki amsawa ba.
"nasan kina mgnr ne batare da kingane dawa kike mgn ba ko?".
"wlh kuwa"Dan Allah dawa nake mgn ne?"
"zahrdee ne".
"eyya Dan Allah kayi hkr wlh bangane muryanka bane?".
"Eh" nasan da h'aka Ai".
"bayan sun gaisa zahrdee yace dama bugowa nai na tambayeki abinda kike bukata".
"murmushi Zainab tai hade da cewa bani bukatar komai".
"to shikena tunda baki bukatar komai gani number na idan bukatar yataso saiki kirani'idan k'uma kunya kikeji saiki bawa kawayenki nasan bazaki rasasu ba.
"to kawai Zainab tace".
"snn sukai sallama'bayan ya kashe wayar ne Zainab ta zauna shiru tana tunanin wann hali irin na zahrdee.
~~~ ~~~~ ~~~~
"Nasir tunda aka kaiaa Egypt dayake Akwai kwararron docts su bashi kyakykyawar kulawa jiki kam alhadumllh yanzu kusan komai da kansa yakeyi batare da yabawa Fatima wahala ba.
"sae dae docts din suce yana da'kyau yarinka zagawa yana exercise sbd dadewar da yai a kwance.
"Nasir ya samo wnn cutar ne a gun zuwaira daya aure batare daya san tana dauke dashi' ita kanta batasan tana dauke dashi ba sakamakon auren wani mutum da tai shima kusan irinta ne harma zan'iya cewa yafita sbd duk shekara yake zubi' ma'ana kowani shekara yake auren mata hudu kafin wani shekara duk ya sakesu ya dibo wasu.
"shine sanadiyar da yasa zuwaira tasamu wnn cutar' bayan rabuwarsu dashi Nasir ya aureta a nan ne shima ya dauki cutar'abinda yasa ma be cutar dashi h'aka ba Nasir mutum ne me kulawa da kansa wajan shan maguguna.
"ko'a lkcn da yaji canji a jikinsa yaje dan gani doct' doct kamal yace infection ne amma idan yana kulawa da magani babu abinda zaisameshi.
"da h'aka Nasir yaci gaba da kulawa da kansa wajan shan maguguna' inda ya godewa Allah ma jininsa (O) shida Fatima' a nan ne Aisha ta dauki cutar dayake ita jininta bekai nasu karfiba yai affecting dinta har mahaifarta.
"amma ita Fatima ma batasan ana yiba sbd bata dashi' shima Nasir yanzu yasamu sauki sosae' a cewar doct zasu iya komawa gida idan yaso yarinka zuwa chickcup' koda Fatima ta sanarwa abbansa sai yace aa sutsaya yakara samu sauki tuku.
"shima Nasir din gani yasamu sauki yasashi daukar Fatima suna yawo sauran kasashe suna shan iska..
~~~ ~~~ ~~~~
gida yashake fal da jama'a na binni dana kauye har babu masaka tsinke.
"bagaren maza kuwa duk sun shirya zuwa daurin aure.
"jikin Aisha yai sanyi sosae sbd duk halimu ya nuna mata zahrdee ke aure'amma wani abu daya daure mata kai ko jiya tare suka kwana dashi amma bece mata komai ba.
"daki takoma ta zauna bakin gado hawaye ne kawai takeyi wani nabin wani.
"gidan su Zainab ma duk sun shirya daurin aure gidan su zahrdee kawai ake jira.
"zahrdee Shamsudee nurudee duk kaya irin daya sukasa sbd Abba ne ya dinka masu sai dai na zahrdee da malum-malum ne' duk su uku suka shigo cikin gidan abokiyar wasansune mai suna Hajjo ta rangada guda hade da cewa zahrdee ango' kaga ta inda kafi yayyinka kenan har kakaiga mata biyu ga yayyinka marasa zcy dayan ma ya gagaresu.
"Aisha dake daki tanajin h'aka tafashe da kuka ashe dama zhrdee zai'iya yaudarata h'aka zai'iya cin amanata h'aka ya boyemi mgnr aurensa.
"fadawa tai a gado taci gaba da kukanta.
"around ten O'Clock shap aka daura auren zainab da zhrdee.
📖🖊
☘☘
☘
AURE IBADA NE
FASAHA ONLINE WRITERS F.O.W.☘.
(IMPACTING VALUABLE KNOWLEDGE AND ENTERTAINMENT IS OUR CINCERN)
STORY WRITENNG
BY
MMN USWA
SAKON GAISUWATA GAREKI SISTER MARYAM A.I. GITAL WLH INA YINKI SAHEBATA BABU ABINDA YA SAUYA ALLAH YA BARMI KE HAR ABADA TARE DA LAFIYA MAI DOREWA AMEEN INA YINKI TAWA UP UP UP DA YARDAN ALLAH.
3⃣2⃣
"ana gama daurin aure sukayo gida.
"ko kafin su dawo anriga an shirya walima'suna isowa aka fara walima.
"ango zahrdee yasha wa'azi sosae hade da fatan Allah yabashi ikon adalci a tsakanisu.
"bayan la'asar gidan amarya sukakai kaya daya daga cikin gidajen da Abba ya gina ne bangaren da tun farko Abba ya gina masa a nan ne Zainab zata zauna.
"tunda bayan dauri aure zahrdee yaso kiran Aisha kodan yai mata bayani amma besan ta inda zaifara ba.
"sbd shima kansa yasan be'kyauta ba kamata yai tun kafi lkc yai tasani tunda gaba daya gidan babu wanda ya sanar da'ita' k'uma koba h'aka ba shine ya kamata ya sanar d'aita tunda zamansa takeyi amma be sanar d'aita ba sbd yana gudun bacin ranta.
"shiru kawai yai yana tunani sbd besan wani Aisha take ciki ba a wnn lkc' gani duk irin tunane-tunane ga bazai kaisa ba wayarsa ya ciro daga aljihu yai dialling number Aisha zahrdee yayi kira yakai eight miss call Aisha na kallo amma batai picking ba' gani zaidameta takashe wayar daya baya.
"jin takashe wayar hnklin zahrdee yakai matuka gurin tashi' kai kawai yasa yashige cikin gida Allah yasa snn babu wasu mutani ta bangarensa hakan yasashi samu damar shigewa dakinsu hade da sa key yarufe dakin.
"yana shiga gani Aisha yai kwance sharbe-sharbe a kan gado kamar wanda akaiwa duka' da sauri ya karisa kan gadon h'ade da sa hannu ya dagota jikinshi yana cewa Dan Allah Aisha kiyi hkr ki yafemi' nasan nayi maki laifi amma Dan Allah kiyi hkr wlh ba laifi bane nima kaina bansan mgnr wnn auren ba wlh Aisha.
"fisge jikinta tai daga nasa' katashi ka bani gu zahrdee banaso ganika Dan Allah kafita kawai zahrdee' zahrdee banasonka banason ganika zahrdee katafi gun amaryanka kawai.
"haba Aisha wacce irin mgn kikeyi h'aka? wlh babu inda zani inanan tare dake Aisha ta..
"zahrdee kafita min a daki".
"babu inda zani".
"kafita min a dakina".
"wlh babu inda zani' sai dai duk abinda zakimi kiyi amma wlh ina tare dake.
"hannu zahrdee yakai zai rikota'juyawar da zatayi tasa ta igijeshi ya f'adi ta baya a kasa a guje Aisha ta sauka dan dagoshi.
"hannu tasa ta taimaka masa ya mike yana tashi tajada baya' binta yai da karfi ya riketa yana f'adin Dan Allah Aisha ki saurareni kiji mgnr da zanfadi maki Aisha.
"cikin galatse tace ina sauraronka.
"dukawa yai a gaba rike da hannayenta bibbiyu' snn yace Dan Allah Aisha Dan annabi ki saurari abinda zanfadi maki' wlh Aisha anyi aurenga ne kawai amma wlh kwata-kwata bada amincewa ta bane' su Abba da Hjy ne suka shirya h'aka amma na rantse maki da Allah Aisha bana sonta ko kadan wlh Aisha kece nakeso dake ne zcyta take rayuwa.
"nasan ba lalla bane idan na f'adi maki ki yarda ba amma wlh wlh Aisha tunda nake a rayuwata ban taba jin dindinon son wata mace ba bayan ke' Aisha kece rayuwata da sonki nake kwana nake tashi' idan har kika koreni kika rabani dake bansan inda zansa kaina ba' k'uma koba komai kinga kibawa duniya kofar shigowa rayuwarmu kenan su tarwatsa zaman damuke dake.
"Dan Allah kiyi hkr ki rungumi wnn aure a matsayin kaddara' ni zahrdee nayi maki alkawarin bazan taba canza makiba ko dede da kwayar zarra.
"idan ma banda abinki Aisha wlh bafa sonta nakeyi ba' kece kekadai tawa na mallaka maki kaina halak malak.
"murmushi kawai tai.
"hannu tasa ta dagosa sama' gani h'aka yasa zhrdee rungumarta.
"around 8-30 yyar Hjy da kanwar Abba da sauran da baza'a rasaba suka tafi dauko amarya.
"motocine lafiyayyu guda biyar masu bakike glass suna biye da juna' koda suka isa inna Hulairane da sauran jama'a suka taresu cikin girmamawa bayan sun gaisa batare da bata lkc ba aka fito da amarya' Kai tsaye bakin abbanta aka kaita yai mata nasiha sosae snn yabasu ita hade da cewa beyarda kowa ya kwana a gidan ba' ana kaita adawo.
"duk suka amsa tare da godiya' snn yace wa Hulaira ta kira masa Hjy umman Zainab tana zuwa yace ko kinada abin cewa?"
"a'a" alhjy Allah ubangiji ya basu zaman lfy?'.
"amin" kefa Hulaira?".
"a'a" Alhj duk abinda zamuce kariga da kafadi' mudai fatanmu Allah ya hada kansu ita da abokiyar zamanta.
"amin' tashi kuje".
"a lkcn ne Zainab tasa kuka' hade da kiran inna Hulaira.
"da sauri Hjy tabar dakin sbd hawayen da suke zabo mata.
"ana daukar amarya kai tsaye sai gidan su zhrdee' har dakin Hjy aka kaita snn aka tuwa daya daga cikin bakin da sukazo baki ta kira Aisha.
"koda yar'aike taje bakin kofa tanata sallama babu wanda ya amsa mata sakamakon Nisan da sukayi.
"Aisha naji tayi kokarin ture zhrdee dan tasamu mikewa amma ina zhrdee ya hanata dole yasa ta hkr.
"yar'aike ko da taji shiru komawa tai tace tariga tai bcc' yyan Hjy tace saida aje a tada'ita sbd idan ba'a hadasu yau anmasu fada ba sbd Allah wani lkc ne za'a hadasu.
"har tamike da sauri Hjy tace a'a abarta kawai.
"Aisha najin shiru tacewa zhrdee kagani ko' da kabarni naje naji kiran da akemi' wata kilama Hjy ne ke kiran.
"idan Hjy ne sai me' Dan Allah kizo mu kwanta.
"kamo mata hannu yai suka koma.
"bayan kowa yai nasa jawabin ne aka dauki amarya zuwa gidan ta".
"koda suka isa dakinta aka sauketa kanwar Mmn zainab ce ta dauko wasu maguguna tasake bawa zainab tasha hade dana shafawa a jiki' bayan ta gamane ta dauki bokitin ragowar magugunar ta bata da k'uma nuna mata yadda zatayi anfani dasu' ko wnn da lkcn shansa.
"Zainab ta amsa sukuma suka mike h'ade da sallama' drive ya medasu gida' gani za'a watse a bar gida babu kowa gashi har lkcn ango bezoba yasa yyar Hjy ta buga gida ta sanarwa Hjy akan har yanzu zhrdee bezoba ita k'uma gida takeson dawowa sbd bcc takeji.
"Hjy najin h'aka taje ta sanarwa Abba abinda ake ciki'murmushi kawai Abba yai hade da daukar wayarsa ya kira zhrdee.
"zahradee yana gani number Abba amma be daga ba sbd yariga da yasan kiran da ake masa.
"Abba yai kira har yagaji amma zhrdee be daga ba' tun ran Abba be baciba har yakai ga yabaci.
"himm Alhj kaga abinda nake fadi maka ko?" tun yanzu kenan yaronga yana niman zuba mana kasa a ido.
"mikewa Abba yai batare sa yai mgn ba yana gaba Hjy na baya' bagaren Aisha Abba ya nufa da kansa yake knocking jin muryan Abba ne yasa Aisha mikewa da sauri hade da cewa zhrdee tashi Abba nefa da kansa.
"a lkcn har bcc ya fara daukar zhrdee jin ance Abba ne yasashi mikewa da sauri ya dauki wandonsa yasa snn yaje ya bude kofar".
"yana budewa Abba yace fito kawuce".
"to kawai zhrdee yace hade da komawa cikin d'akin' toilet yashiga yaje yai wanka snn yazo yasa kaya yafita' yana fita Aisha tasa kuka.
"zhrdee na fita Abba yasashi a mota da kansa yakejan motar tafiya suke amma babu wanda ya tankawa wani har sukakai gidan.
"suna isa zhrdee ya bude kofa ya fita a lkcn ne Abba yace son saida safe' idan ka karisa ciki kakirami yya tafito.
"to kawai zhrde yace snn yakarisa ciki.
"yana shiga Hjy tai masa sannu da'isowa h'ade da cewa saida safe.
"Allah ya bamu alkairi.
"tana fita yarufe gida ko'ina kai tsaye wani extra room yanufa koda yashiga dakin babu komai empty ne ko katifa babu dawowa yai parlour ya dauki pilon cushion yaje yai pilo dashi rigarsa k'uma ya shinfida a kasa ya kwanta.
"Zainab shiru-shiru ango zaishigo amma shiru' gashi har bcc ya fara daukarta' shiko zhrdee yana can bemasan tanayiba.
"Abba yana isa gida Hjy ta taresa da yya dai Alhj?".
"murmushi kawai yai batare da yace komai ba.
"gani 1C-lock yayi k'uma har yanzu zahrdee be shigoba mikewa tai tanufi parlour a hankali take tafiya sbd tsoron daya kamata a tunaninta ita kadaice a gidan.
"koda ta jijina kofar parlour jinshi tai a rufe gam da key' dawowa da baya tai tafara dube-dube gidan' duk inda taduba babu wanda tagani wani Sabon tsoron yasake kamata da sauri ta juya zata koma daki sai nepa suka dauke wuta' gida yasake rufewa da duhu.
"hankalin Zainab yayi matukar tashi a hankali take laluba tana niman hanyan zuwa daki dan kunna light din wayarta.
"duk juyin da Zainab zatayi saita bige sakamakon rashin light garin lallabawa tana niman hanya yasa duk ta rikito da jeren banga da akai mata glass din suka faffashe.
"da sauri Zainab taja da baya' taje ja dabaya ne Glass ya soketa a kafa' a take tasa ihu tana kuka.
"duk abinda Zainab keyi a kunni zhrdee amma besa ya fitoba.
"da h'aka tai tayi tana karo da bango har ta'isa d'aki' ga bigewar da goshinta yai' da h'aka har tasamu tashiga d'akin.
"Zainab najin ta dafe gado ta fashe da kuka tana kokarin daukar waya ta kuna' bayan ta kunnane taje ta rufe kofa a gefen gado ta rakube taci gaba da kukanta.
"ga waya a hannunta amma batai tunani kiran zahrdee ba'da h'aka har safe yai.
"jin kiran sallar farko zahrder yamike yabar gidan' itama Aisha mikewa tai taje tai alwala tazo sallah' bayan ta'idar da sallah ne taji bcc ya kamata pilo ta jawo ta kwanta akan sallaya taci gaba da bcc.
"zahrdee bedawo gidan ba sai around 11AM koda ya dawo parlour ya zauna' bayan ya zauna ne yake gani barnan da Zainab tai.
"mikewa yai ya tara kayan gefe glass din da suka fashe k'uma ya sharesu ya zubar snn ya dawo ya hade da kunna TV yana kallo' be dade da zama ba su Amatullah da Amatulrahman sukai sallama dauke da kayan abinci a hannu' zahrdee da fara'arsa ya taresu bayan sun gaisa amatullah tace Hjy ce tace akawo maku abin karyawa.
"Allah sarki kice mata mugode.
"yya ina amaryan taka?".
"tana ciki tana bcc".
"jin haka yasa basu sake mgn ba suka mike hade da sallama.
"har bakin kofa zahrdee yai masu rakiya sann yadawo.
"zama yai dirshan ya dibi abinci yafara ci' yana cikin ci kenan yar'uwan Zainab sukai sallama suka shigo.
"da fara'arsa ya karbesu' suka gaisa bayan sun gaisa ne yace dasu tana cikin daki.
"gani su tsaya basuda niyar shiga yace bismillh mana.
"ido suka sake hadawa suna kallon junasu' da yake duk yar'mata ne mace daya ne me aure a cikin su.
"mikewa zhrdee yai ya fita ya bar masu g'idan.
"yana fita idon su yakai gun kayan da zainab ta barnatar da sauri har suna h'ada baki suna cewa lahhhh! duk abinda sukai kamar wasu yara".
"to mema ya kawosu parlour?".
"a'a kekuwa kila garin wasane.
"h'aba wani irin wasa?" wasa yabar bedroom sai parlour.
"k'uma dai da wani irin tunani wlh' jiya-jiya da daurin aure shine har zasuyi wani abu?".
"kekuwa rai da marmari' rai dangin goro".
"yanzu dai duk kumubar wnn mgn kuzo muje cikin d'akin muganta.
"duk su hudun duguma sukai zuwa cikin bedroom'koda suka shiga ganita sukai kwance kan sallaya tana bcc' shigowarsu ne yasa ta b'ude ido' tana cewa su walida har kunzo sannuku da zuwa.
"duk Zainab na mgnr ne a kwance bata tashi ba.
nusaiba dake kusa da walida tace Zainab amarya to tashi zaune mana.
"to"kawai tace".
"da kar zainab ta laluba ta mike zaune' snn tace da wani lkc ne kuka shigo.
"bamu dade da shigowa ba' mushigo musamu angonki a parlour yana karyawa amma ganimu yasashi fita.
"himm kawai zainab tace' gani gado a mutsutsuke ko gyara shi ba'ai ba yasa walida cewa zainab meyahanaki gyara d'akin tunda safe sbd Allah' yanzu inda bakin kunya ne suka shigo mezakice?" Dan Allah kitashi ki gyara gadonki tun kafin jama'a suyi yawa.
"to kawai tace".
"saida Zainab ta kamo katakon gado snn ta mike.
"h'ada ido suka sakeyi suna murmushi.
"gani takasa daga kafa sakakoman ciwon dataji garin yai mata tsami.
"nusaiba tace me k'uma ya samu kafar zainab?".
"yankewa nayi".
"yankewa k'uma?".
"Eh" wlh".
"garin yaya?" k'uma da me?".
"dauke light akaji nikuma naje mikewa ban saniba na bige da katakon friend dake parlour shine glss dinsa ta yanke ni.
"to fa' Allah ya sauwake".
"amin".
"jawo zani gadon da Zainab zatayi taga Ashe shima jini yabata bata saniba' suma suna gani suka sake h'ada ido.
"kwashewa Zainab tai ta zuba a gefe har ta daga kafa kenan tanaso taje wadrop ta dauko wani zanin gadon taji kafarta ya rike mata' tsayawa tai tai shiru h'ade da matse baki.
"walida tace yah?" dai Zainab?'.
"kafa nane yaimin tsami".
"to!!! koma ki zauna".
"koma gefe tai ta zauna.
"nusaiba da walida suka gyara mata gadon tas' zani gadon daya baci da jini suka kai bathroom suka ije sbd a nasu tunanin najasa ne a ciki yasa basu wanke ba.
"walida tace Zainab kinyi wanka?".
"a'a".
"sbd me?".
"himm kawai tace".
"h'aba Zainab sbd Allah da saniki da komai kike zama da najasa har wnn lkc?".
"shiru Zainab tai bata tanka ba".
"amma kinyi sallah ko?".
"nayi".
"to shikenan yanzu tashi kije kiyi wanka daga nan ma saiki gargasa jikinki da ruwan zafi.
"to kawai tace".
"mikewa Zainab tai gani yadda takejan kafa yasa walida riketa zuwa bathroom bayan ta fitone suke mgn nusaiba ke cewa walida kodai na karfi yai mata?".
"me kika gani nusaiba?".
"ke baki gani yadda taji jiki' k'uma ga barna da sukai har parlour fa sbd Allah' wann wani irin abune h'aka?".
"gskya kam"da alima".
"matar aure dake tare da sune mai suna SAMEENRAT tace a'a basai yai mata na karfiba dama dole asamu h'aka tunda ba taba sani namiji taiba'amma idan ta daure kafin nan da sati tasaba.
"duk baki suka h'aka suna cewa ko 🤔 ?"!!!.
"Eh" mana amma kuce mata tarinka amfani da ruwan zafi wajan tsarki".
"duk suka hada baki da cewa to".
"fitowar Zainab daga toilet ne ya katsesu.
"Su walida da nusaiba yaran yyan Alhj Musa ne Uwa daya uba daya' ita k'uma SAREENRAT matan yayan su walida sai dayan da suka shigo tare mai suna Rahma ita k'uma da bbnta da Alhj Musa uba daya ne duk suna karatu a nan bauchi university ne.
"aiki suka taya Zainab sosae harda abinci saida sukai mata suka zubawa zhrdee nasa a kula snn sukai wanke wanke gam da sallar magrib suka tafi gida' bayan fitarsu ne zainab tashiga wanka tana gamawa tai alwala saida tai sallah snn tai kwanlliyarta shikin sket da riga na material light blue tayi matuka dawowa parlour tai ta zauna tana kallo.
"koda zahrdee yabar gidan can wata uguwa yaje ya boye inda babu wanda yasan yana gun' saida ya daidaici magrib yayi kowa yatafi masallaci mata k'uma maybe suna daki suna nasu sallar snn ya saci jiki yazo gun Aisha' Aisha na sallah kamar daga sama taji anfado dakinta.
"h'akan yasa tai kananu sura sbd ta'idar da sauri' bakin gado zhrdee ya zauna yana jiran ta'idar' tana sallama tace lfy?" me yakawoka kaida kake da amarya?".
"gani zata daga masa murya batare daya tanka taba 🤫 yai mata daga snn bata sake mgn ba.
"mikewa yai ya tube h'ade da cewa jeki ki hadami ruwan wanka.
"Aisha tace wankan me zakaimi anan? inda kaje kai abinka daban inda zakai wanka daban' babu wani ruwan da zanha maka.
"ko kallonta beyiba yace ta kanki akeji' snn yashige bathroom yaje yai wankansa h'ade da alwala yazo yai sallah snn ya kwanta.
"Aisha dake tsaye tana kallonsa har ta b'ude baki zatai mgn kenan zhrdee ya jawota gado ta fada jikinsa' Aisha na kokarin tureshi da karfi ya danneta yana cewa h'aba Aisha ta Dan Allah meye kikeyi h'aka?"
"dama Akwai ranar da zaki iya korata daga gareki?".
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 38