nishi tace Allah ya'isa ban yafe ba' mugu kawai.
"suma yara zuba sukai a jikin mmsu suna kuka.
GA TAMBAYA KUMA A GUNKU NAKE BUKATAR AMSAR READERS
1
Duk wanda yasan doka kuma yasan me ake kira gamnati kuma yasan menene E. F. C. C ta yaya za'ace suna nimanka har kazo gida ka kwana ka kuma biya bukatarka da matarka hankalinka kwance?
2
Duk mutani da akace ana nimansa ina yakeda lokacin tsayuwa fada da matarka????
Amsa tana gareku saina jiku READERS
TAKU HAR KULLUM MOM USWAN
📖🖊
☘☘
☘
AURE IBADA NE
FASAHA ONLINE WRITES F. O. W. ☘.
MMN USWAN
0⃣9⃣
"Gani irin kukan da sukeyi yasa Fatima tsaida nata kuka ta koma lallashinsu.
"mikewa tai ta rike masu hannu sukai d'akainta.
"Itako Aisha gani irin dukan da Nasir yaiwa Fatima da sabadiyar haka itama ta sami nata' yasata tsorata tai data sani rashin tafiya garinsu da batai ba' kamar yadda ya umarceta da taje.
"Zama tai taci kukanta har ta gode Allah' dan kanta tai shiru sbd babu me lallashinta.
"Gani har gama yayi Fatima bataji motsin Aisha ba yasa Fatima bin Aisha har d'akainta' da sallama tashi d'akin' Aisha na zaune a bakin gado ta amsa da shigo anty.
"Fatima na shiga a bakin gado ta zauna' Aisha tace ina kwana anty' Fatima tace lfy klau Aisha ' Fatima taci gaba da cewa dama dana zuwa nai na baki hakuri akan abinda ya faru dazu da asuba' Aisha tace babu komai anty' snn tace dan Allah anty na tambayeki mana.
"Fatima tace Allah yasa nasani.
"Aisha tace dama h'aka alhj yake dukan matarsa h'aka?
"murmushi Fatima tai snn tace a'a wanga ma bacin ranane' amma ba h'aka yake ba.
"himm kawai Aisha tace.
"Gani h'aka yasa Fatima dafa kafadan Aisha snn tace Aisha ki yarda dani duk abinda zanyi bazan cutar dake ba' sbd na daukeki tamkar yar'dana haifane.
"Aisha kinga yarinya nan ko bayan rai nane bazanso ta auri namijin da zai cutar da'ita ba' shiyasa na daukar wa kaina alkairin duk matar da Nasir zai kawo g'idan nan insha Allahu bazan cutar da'ita sbd nima inaso yarinyata Allah ya bata sbokin zama na gari.
"Cikin kuka Aisha tace nagode' amma dan Allah ku daina irin wanga fadan h'aka dan Allah.
"murmushi Fatima tai snn tace menene Aisha?
"Aisha tace wlh har kunsa tsoro ya kamani' dariya ne Fatima tai sosae snn tace Aisha ke yarinyace shiyasa.
"mikewa tai h'ade da cewa zomuje ki karya' tare suka fita zuwa kitcher Fatima da kanta ta dibawa Aisha abin karyawa tabata' hannu bibbiyu Aisha tasa hannu ta amsa h'ade da godiya.
"D'akainta ta koma ta zauna zubawa abincin ido tai tana kallon abincin tunani kala2 takeyi a zuciyarta.
"Tunda Nasir yabar gida yau tsawon satinsa biyu kenan amma be likitan Aisha tai nimansa ta waya har tagaji wayar a kashe yake' h'akan yasa Aisha kuka kullum dashi take kwana take tashi.
"Wani tunani yazo mata tace kodai naje na tambayi anty ne ko ita tana samunsa a waya' wani zuciya tace me zaisa kije ki tambayeta bayan kina gani irin rabuwar da sukai...
"Tana cikin irin wanga tunani - tunani kenan taji ana knocking da sauri ta mike taje ta b'ude kofar yarinya ta gani tace Aisha tace ubaida lfy?
"Ubaida tace mamy ne tace kizo kici abinci.
"Tare suka tafi zuwa dinning' Fatima tace Aisha ta zuba masu' Aisha tace to anty.
"Mikewa tai ta zuba masu snn ta zauna suka fara ci' suna ci suna hira' khadijat tace mamy' Fatima tace na'am ubaida' khadijat tace wanga ma anty mune?
"Fatima tace eh' itama anty kune' k'uma daga yau sunanta anty.
"Khadijat tace to shikenan mamy' kani khadijat dake gefe yace yaya kullum kullum sai dady ya kawo mana sabuwar anty ko?
"Jabeer ya karisa mgnr ne da kallon khadijat.
"khadijat tace kai dan Allah kai wawane wayan nan ba dady ya koresu ba.
"A gigice Aisha ta yarda spoon din dake hannu ta.
"Gani h'aka yasa Fatima ta daka masu tsawa.
"mikewa Aisha tai da sauri ta koma d'aki' gani h'aka yasa Fatima mikewa ta bata d'akin' tana shiga gani Aisha tai ta zabga uban tagumi.
"Fatima tace Aisha lfy? Aisha tace anty dama alhj yana auri sakine? Da sauri Fatima tace me kika gani? Aisha tace mgnr dasu khadijat ne sukai yasa nai zargin h'aka.
"Fatima tace a'a duk mgnr yarane' idan ma yanayi ina ruwanki' shifa na mijine yanada ikon auren mata hudu idan h'aka ni banga abin damuwa ba.
"uhm kawai Aisha tace.
"Fatima tace dan Allah Aisha kada ki damu kinji' wlh duk mgnr yarane.
"Aisha tace babu komai anty nagode.
"mikewa Fatima tai ta koma ta sami su khadijat da Jabeer f'ada ne tai masu sosae' h'ade da jan kunni akan surutu.
"Da yamma Aisha tazo ta sami Fatima a kitcher tana aikin abinci' Aisha tace anty wani aikine zantayaki? Fatima tace ki barshi kawai.
"Aisha tace Allah kuwa anty.
"Fatima tace Allah kije na yafe maki.
"Aisha tace to shikenan' komawa daki tai.
"Nasir watarsa biyu kenan da barin g'ida ko lekowa bayayi' Aisha tai nimarsa har tagaji' kuka kuwa kusan shine abincinta babu dare babu safe' rama kuwa ba'a mgn koda wanda ya kwanta jinya sai h'aka.
"Tabi ta rame ta kara baki' duk wanda ya santa ada ba lalla bane idan ka ganta ka ganeta ba' dama ba kiba ne da'ita ba sai tsayi h'akan yasa takara fitowa doguwarta sabbal.
"Can ko gun iyayenta hankalin ummata a tashe yake' sbd munanar mafarkai da takeyi akan Aisha' mafi yawancin idan ta kwanta bcc da dare cikin mafarki take gani Aisha a zaune tana faman kuka' wani lokaci k'uma ganita takeyi cikin duhu mai tsananin baki tana fama ihu' A gigice umma ke tashi h'ade da salati
"Tana mikewa toilet take shiga tai alwala tazo ta fara nafila h'ade da addu'ar nima wa ya'ta sauki a duk halin da take cikin.
"Gani duk irin nafiffili da sadaka da takeyi besa ta daina gani Aisha a cikin irin wnn halin matsawa alhj bbn Aisha tai akan zataje ta dubo ya'na sbd jikinta yana bata Aisha tana cikin wani hali.
"Alhj ya kara ya tsare yace babu inda zata' sbd Aisha ba karamar yarinya bace' k'uma inda babu lfy da maigidanta ya sanarwa ya'uwa' bayan h'aka inda ita Aisha har yanxu tana tare da kuruciya aishi maigidan nata ba yaro bane' dan h'aka babu wanda zaije banlema insha Allahu tananan cikin koshin lfy.
"Tunda alhj yace h'aka umma bata sake cew komai ba' mikewa tai taje taci gaba da aikinta.
"Alhj yaci gaba da cewa kawai dan anji shiru sai afara wasu irin tunani na banza' to inda daukarta yai sukabar kasan fa yaya zakiyi?banlema kuna kasa daya da ita' kawai dai kila dan wasu uzuzukane sukasha gabansu banlema shi namiji mai iyalai ga k'uma lokaci da Allah ya kawomu.
"Duk maganganun da yakeyi umma na jinshi amma bata tanka masa ba har yakare mgnr sa yai shiru.
"Gani goma saura yasa umma shigewa d'akainta tai alwala tazo ta fara nafila ta walha.
"Sai da Nasir yakai wata hudu currr da rana bayan sallar azahar sai Nasir yai sallama lokacin Aisha tana d'akainta kwance' shima yana shiga g'idan d'akin Fatima ya nufa' itama tana toilet shiyasa batasan shigowarsa ba.
"Bakin gado ya samu ya zauna yana jiranta' Fatima na fitowa ta ganshi yadan shingida akan gadon' kamar bazata tanka masa ba' sai dai tace sannu da zuwa.
"Nasir ya mike da cewa yauwa uwar g'ida rai g'ida har kin fito? Gani yadda yake mata mgn tasan da bayani' h'akan ya sata daure masa fuska.
"Nasir yana gani h'aka ya mike yazo inda take tsaye' hannu ya mika yana kokarin rikota' da sauri taja da baya' gani taja da baya yasashi binta itama bata daina komawa da baya ba har saida takai bango.
"Gani takai bango ne yasa Nasir kwashewa da dariya h'ade da sa hannu ya riketa' Fatima tai kokarin tureshi amma takasa' cikin dariya Nasir yace tureni mana idan zaki iya.
"Shiru Fatima tai tana kare masa kallo' baki Nasir yakai yana kokarin yimata kiss' da sauri Fatima ta kauda fuskanta' duk da kauda fuskan da tai behana Nasir abinda yai niyaba.
"bari tai sai da yai nisa snn ta tureshi zata gudu' hannu yasa ya riketa da karfi yana f'adin h'aka Fatima yau k'uma rowa ne za'aimin h'aba matata ta kaina uwar ya'ya'na abin alfaharina kace jiya k'uma kace yau a kullum jinki nake tamkar buduwa' ke ko budurwanma bazata gwada maki komai ba a guna' daya kike tamkar da duhu.
"Murmushi Fatima tai h'ade da cewa a d'adin baki irin taka ba.
Nasir yace wlh kuwa Fatima' Fatima kada ki mance irin soyayyar da mukewa juna tun muna yara h'akan ne yasa koda mukayi aure' muka samu matsalar rashin haihuwa babu yadda iyayena basuyi dani ba akan saina kara aure sbd ke baki haihuwa' ni k'uma nakeyi sbd wlh Fatima har gobe bantaba so wata mace a duniya irinki ba.
"Fatima ba lallane kisan irin son da nake maki ba' soyayyar da nake makine yasa nabar iyayena nabar yar'uwana na nimi transfer na aiki na dawo nan garin sbd lokacin da muke garinmu gaba daya ya'uwana sukai miti akan idan na fita aiki zasuzo sui maki duka su koreki a cewarsu wai kin mallakeni ni k'uma basusan cewa ba haka bane.
"wlh Fatima ba haka bane tsatstsar soyayyar da nake mikine yasa suke gani haka' jumai kanwata itace tabini har gun aiki ta sanar dani abinda aka shirya maki' kinji dalilin dayasa mukabar g'ida kenan.
"Cikin shagwaba Fatima tace to meyasa tunda mukazo nan kaketa aure-aure? Dariya Nasir yai h'ade da shafe mata fuska yace Fatima kenan' kinfi kowa sani tun kafin muyi aure na sha sanar dake alkawari na daukawa ubangijina bazan tanayin zina ba.
"Fatima tace to hakki fa? Tunda idan ka auresu ko shekara basuyi a gunka kake koransu.
"Dariya Nasir yai h'ade da jawota jikinsa yana cewa Fatima ta manta da wann mgnr' Fatima tace baza'a manta ba Nasir' Nasir yace menene abin damuwarki tunda kina tare dani' kefa mutu karaba ne' kinriga kinsha gaba su.
"Dariya Fatima tai h'ade da cewa Nasir kenan' shima dariya yai h'ade da kara mannata a jikinsa' da haka Nasir ya samu ya biya bukatarsa' bayan ya gama ne ya wanka ya meda kayan kijinsa yadawo bakin gado ya zauna' Itama Fatima zaune take a bakin gado daure da towel Nasir ya jawota kijinsa snn yace Fatima.
"Fatima tace na'am Nasir.
"Nasir yace inaso ki fahimceni dan Allah.
"Fatima tace ina sauraranka.
"ido ta zuba masa tana so taji abinda zaice.
"Nasir yace wlh Fatima duk auren da kikaga inada ba dan naci maki fuska bane yasa nakeyi' kawai kinsan ance matar mutum kabarinsa ko.
"wani irin kallon banza Fatima tai masa h'ade da cewa hakane.
"Snn yace wata yarinya na gani kuma wlh yarinya tayi saima kinganta....
"Da katar dashi Fatima tai tana cewa bashi na tambayeka ba' karisa zancenka.
"Nasir yace wlh Fatima yarinya tayine shiyasa naji ta biyamin rai' wata muguwar tsaki Fatima tai masa.
"Nasir yace nakarike maki zance dai har nakai kudin aurenta har iyayenta sun sa mana rana.
"Fatima tace yayi kyau' ita kuma wanga da ka'ije ta fa? Nasir yace wafa? Fatima tace Aisha mana ko ka mance da'ita ne.
"Nasir yace ok' Aisha ai ba wata matsala bace a guna' Fatima tace sbd me kace haka Nasir? Nasir yace kinga takardanta a nan.
"Fatima tace mugani' hannu Nasir yasa a aljihu ya ciro takardan ya mika mata ' Fatima tana amsa ta yage takardan h'ade da cewa wlh baka isa ba dan kayi kadan.
"Cikin wasa da dariya Nasir yace Fatima idan kika hanani aure so kike ace ga maigidanki nan yana zina ne' kinfi kowa sani yadda nake.
"Fatima tace bagani ba' tunda nake dakai kataba zuwa da bukatarka na hanska ne? Ko k'uma ance duk matar da suke duniyane saika sansu'
"hannu Nasir yasa ya jawota jikinsa snn yace haba Fatima ki tausayamin mana' fisge jikinta tai daga nasa snn tace baza'a tosaya dinba' kuma wlh babu inda Aisha zata' kai meyasa bakada tsoron Allah meyasa baka tunanin haduwarka da ubangiji kane Nasir.
"Nasir yace Fatima kenan duk abinda nai bafa zina nai ba' aurensu nakeyi.
"Fatima tace idan aurensu kakeyi sai me to na tambayeka Nasir.
"Nasir yace Allah yasa nasani.
"Fatima tace kai Nasir baka gajine? Nasir yace dame? Fatima tace da kwanciya da mace' Nasir bayan aureni dakai yar ' matan da ka aure kasaka sukai goma kai Nasir meyasa bakada tsoron Allah ne? Meyasa kake meda ya' ya' mutani zawarawane Nasir' meyasa bakada tausayine Nasir? Wlh Nasir da badan so ba babu abinda zanyi dakai' bakai bama duk me hali irin naka.
"hannu Nasir yasa yana toshe mata baki.
"tsawan da Fatima tai ne wajan cewa sakanmin bakina yasa Aisha ji.
"Da sauri tazo tana knocking.
"tura Nasir gefe Fatima tai snn tazo tasa hijab snn taje ta b'ude kofar h'ade da cewa Aisha yaya akai ne? Aisha tace a'a ji nai kamar kuna hayaniya.
"sai da tai murmushi snn tace a'a babu komai maybe karar TV ne da kikaji.
"rufe kofar tai da key snn takoma taci gaba da cewa yanxu dan Allah bakaji kunya ba ace kana yaudarar yar ' cikin ka Nasir.
"daure fuska Nasir yai h'ade da cewa menene abin yaudara k'uma Fatima? Fatima kinfi kowa sani inba keda wlh babu matar da itasa ta tsaya a gabana tana fadimin mgn h'aka kawai dan kace.
"Fatima tace oho kai kasani ' yanxu sbd Allah menene Aisha tai maka da har zaka saketa? Nasir yace wlh batai min komai ba' nidai kawai gajiya ne nai da'ita sabo nakeso.
"Fatima tace to wlh baka isa ba' bari kaji Aisha babu inda zata zama daram.
"Nasir yace idan zamanki takeyi basai nagani ba'ai ko ba zamana takeyi ba ' tunda kai kaje garinsu ka daukota ka rabata da iyayenta ka kawota nan to wlh tazo kenan sai dai mutuwa' mgnr aure k'uma kayi na karke kenan.
"Dariya Nasir yai h'ade da cewa kace Allah kenan.
"Fatima tace ba nice Allah ba amma in har ina raye kayi na karke kenan.
"Dariya Nasir yai snn yace Fatima kenan shiyasa kike birgeni' ni zantafi.
"Fatima tace na mance ban sanar dakai ba abincin mu ya kare.
"Nasir yace kedawa da naji kike cewa abincin ku' Nasir wlh tsorona daya ne kada idan Allah in yasashi sakawa yaran mutani ya saka masu ta hanyar yaranka....
"wani irin tsawa Nasir ya dakawa Fatima h'ade da cewa wlh Fatima duk irin bakaken maganganu da zaki f'adi a kaina zan amince amma banda yarana idan kike sake sainayi mumunar saba maki.
"K'uma na fadi na saki Aisha taci gaba da zama a g'idan tunda g'idan ubanta ne' mgnr abinci k'uma tunda kin iya eje Aisha a g'idan na tabbata kinada kudin ciyar da'ita ai.
"Fatima tace idan bazaka bawa Aisha ba' to nida yara fa.
"Nasir yace ni tabbata kudin da aka sallameki aiki Sunnan basu kareba.
"Fatima tace idan kudin sallamana aiki yananan fa sai me? Kai ni wlh bazan yarda ba.
"Gani tana kokarin rikesa da sauri yafice yabar g'idan.
"Itako Aisha tana can cikin dakinta batasan abinda ake ciki ba.
"itama Fatima tana dakinta ta rasa ta yaya zata fita ta sanarwa Aisha sakin da Nasir yai mata' gashi k'uma tana bata tausayi' shiru tai tana tunani ta ina zata fara' wani zuciya yace kyaleta kawai har ranar da Gaskiya zaiyi halinsa' sbd idan kika sanar da'ita sai tafi ganiki da baki akan wanda yai saki.
"A nan tabar mgnr sukaci gaba da zamansu Fatima bata taba nunawa Aisha wani abuba koda wasa.
"Yau kam umman Aisha da kuka ta tashi tatasa bbnsu Aisha a gaba da kuka a dole zataje gun Aisha taga halin da take ciki.
"Gani tashiga damuwa sosae hakan yasashi cewa tanari gobe zai tura kannita suje su dubata.
DAN Allah FANS KUYI HAKURI NA RASHAN JINA DA ZAKUYI KWANA BIYU SBD EXAM NAKEYI MAYNE NO MONDAY MUHADU
NAGODE
☘☘
☘
AURE IBADA NE
FASAHA ONLINE WRITES F. O. W.
MMN USWAN
1⃣0⃣
"Washe gari da safe alhj bbn Aisha da kansa yakai abdul tashar mota' din union yana hango su da kaya da sauri yaje ya amshi abdul dake rike da jakan snn suka kariso gun motar.
"din union yace bb ina zaku? Alhj yace motar birni kebbi mukeso.
"din union yace gashi nan sai dai gun mutum dayane ya rage.
"alhj yace ba damuwa dama dhikadai ne zaije.
"abdul yana shiga mota alhj ya biya kudi din union ya kwashi kayan da umman Aisha ta siye mata na tsaraba aka xuba a but abba bebar tasha ba saida yaga tashin su abdul.
"abba shima ya juya ya koma g'ida.
☘☘ ☘☘ ☘☘
ASALIN AISHA
"Aisha yar'asalin garin bauchi ne' itace babba a gun iyayenta sai kaninta abdul basek sai kanwarsu nafeesat wadda Allah yai mata rasuwa shekaru hudu da suka wuce.
"Aisha ta taso tun tana yar'karamarta yarinuace mai ilimi na addini dana zamani' tun tana yar'shekara goma da watanni a duniya tai saukan slkur'ani mai girma' a lokacin daidai da takare primary' bayan walimar saukan alkur'ani ne abbbata ya kaita secondry school' duk da ba mai kudi bane amma yana iya kokarinsa akan yaransa' hakan yasa daga ita har kannita prvt school sukeyi.
Alhj muhammed da matarsa mai suna Hafsatu duk yar'asalin garin bauchi ne a cikin karamar hukumar ningi' hakar budiness din sa ne ya dawo dashi cikin birni bauchi.
"Alhj muhammed din kasuwa ne' ta fannin kayan masarufi'k'uma ya kware sosae a harkan ta hanyan ne ya siye g'idan sa da motarsa' bana karya bane amma bazaka raina masa wayoba.
"Da Allah ya kara buda masa duk su biyun suka sauke farillah shida matarsa' sakamako Allah yaiwa iyayensu rasuwa.
"lokacin da Aisha tafara secondry school a snn ne abdul yake primary 5 sakamakon prvt school aji 5 biyar aka tsayawa' ita k'uma Nafeesat na primary 3' sbd tsakani Aisha da abdul be wuce shekara biyu ba' Itako nafeesat shekara uku abdul yabata.
"Aisha da iyayenta suna rayuwarsu ne cikin rufin asiri dan baza'a sasu cikin jerin masu kudi ba k'uma bazaka ce dasu talakawa ba' sbd duk wani abin ma da mai kudi bazai iya yiwa ya'ya ' sa ba bbn su Aisha yana masu' ga k'uma kyautatawa makwabtansa masu laluran rashin lfy ko halin yau da gode daidai gwargwado da befi karfinsa ba.
"H'akan yasa duk makwabtansa suke gani girmasa.
"lokacin da Aisha ta fara JSS1 lokacin zahradee yana SS2 goying to 3 k'uma shine head boy a school din' dayake boys and girls ne' mafi yawancin lokuta Aisha tana makara sbd jiran kaninta da takeyi' sai ta rakasu nasu makarantan su shige snn takarisa nata.
Zahradee yasha kama Aisha late tun yana dukanta har yagaji ya daina dukanta' a bangaren g'ida kuwa ummansu tana kokari wajan gani sun bar g'ida akan lokacin sbd koda su makara' amma abinka da yara da yara tsayawa takeyi tai ta biyewa su abdul da nafeesat' gashi k'uma rules din school din su duk kansu su biyu before 7-30 anaso aga kowani student a class sbd eight dult uncle yake fara leason.
"ita kuma Aisha bata shiga school sai koter after eight.
"tun zahradee na dukan ta har yagaji ya kyaleta' suma kansu teachers din uzuri daya sukewa Aisha sbd yarinya ce mai kokari abune mai matukar wahala uncle or anty suyi tambayar bata amsa masu ba' koda ko ba'ita aka tambaya ba.
"Tun daga lokacin zahradee yafara son Aisha' duk da a lokacin ba girma ne da'ita ba' sbd natafi 11 years ba dan ma Allah ya yita doguwace shiyasa ake gani kamar tafi h'aka.
"h'aka zahradee yaci gaba da raino soyayyar Aisha a zuciyarsa babu wanda yasani dagashi sai abokinsa mai suna Rsslayni' zahradee yana zani weac din sa resutl dinsu yana fita mahaifinsa yaje kaduna ya samummasa addmno na H.N.D. dake kaduna' babu yadda alhj Kaelani beyi da zahradee ba akan yaje kaduna karatu amma zahradee yaki.
"A cewarsa koda diploma ya samu yai wanda ke cikin garin bauchi ma kawai ta ishesa' gani yadda zahradee ya kasa ya tsare yasa mahaifinsa yabiye masa da k'uma sonda yake masa' sbd zahradee shine na uku a gun mahaifinsa yana da yayyi a gabansa' babbnsu shine Nurundee sai na biyu shimsundee zahradee sai kanninsa biyu mata dake binsa Amatunrahman da Amatunkaree dayake haihuwar kunikane tsakanisu shiyasa komai tare ake masu' yanxu da h'aka suna JSS3 goying to SS1.
"H'akan alhj Kailani ya samanwa zahradee diploma dake cikin garin bauchi ya karanta ACCOUTING' dayake bamai dadewa bane karatun nan danan zahradee ya kammala' duk a lokacin Aisha bata kare secondry ba yasa zahradee shiga univesty( Sr AHMADU TABAWA BALEWA) dake bauchi nan ma yaci gaba da karanta ACCOUTING d'in sa.
"tun lokacin da Aisha ta shiga secondry suka h'adu da wata yarinya mai suna ubaida komai tare sukeyi sbd ita ubaida yarinya ce mai kokari kusan ince GG suke da Aisha' akwana a tashi Aisha tafara girma a mamomin balaga sun fara baiyana a gun ta' ma wankin yan'mata yafara wanketa".
"Tana SS1 samari suka fara kawo mata hari' amma mahaifinta yahanata sauraran kowa sbd a cewarsa karatu yakeso tayi' k'uma mafi yawancin samarin babu wadda zakace dashi yafito ayi AURE sbd suma kansu basu gama rike kansuba balle su rike mata.
"gudun kada su batawa yar'sa rayuwa k'uma su hure mata kunni yasashi dakatar dasu gaba dayansu' itama ya hanata sauraran su.
"Duk da h'aka basu kyaleta ba ' idan zata school ko na islamiya sai sun tareta' Duk da ba area d'aya suke da zahradee ba amma yanajin labarin komai a gun Rsslayni'g'ani H'akan yasa zahradee xuwa g'idan su Aisha kai tsaye yaje tsayawa yai a kofar g'ida yai sallama' Allah yasa lokacin akwai alhj muhammed a g'ida' jin sallamar da yakeyi ne yasashi mikewa yaje ya dubo mai sallamar.
"Gani yarone d'an matashi wadda ba zai wuce shekara ashirin da biyu zuwa da uku ba ' yasashi cewa yaro lfy? Murmushi zahradee yai h'ade da susa kansa.
"Dukawa yai har kasa ya gaida shi' gani natsowar yaron yasa alhj muhammed ya amsa da fara'arsa' snn yace lfy yaro wa ya aiko ka?
"Cikin jin kunya zahradee yace a'a bb aiken kainane.
"alhj muhammed yace Allah yasa dai lfy.
"Murmushi zahradee yai snn yace dama mgnr Aisha ce.
"Da sauri alhj muhammed yace wani abu tai maka ko?
"zahradee yace a'a dama naga Aisha ne inasonta shine nace bari na fara sanar dakai.
"Murmushi muhammed yai snn yace so fa kace yaro? Toma wani irin so kake mata?
"zahradee yace bb sonta nake da aure.
"Sae da alhj muhammed yai dariya sosae snn yace yaro kayi Gaskiya amma kai baka gani kayi karami da aure?
"Shiru zahradee yai be tanka ba.
"alhj yace wai ma ya sunnaka?
"zahradee yace su nana zahradee baba.
"muhammed yace Allah sarki zahradee nagode sosae da gurmamani da kayi k'uma koba komai ka nunamin kai d'an babban g'ida ne' A Gaskiya bazan boye maka ba zahradee Aisha tayi karama da AURE k'uma koba komai nafiso sae tayi karatu koda diploma ne snn nai mata aure k'uma kaga yanxu da h'aka ko secondry bata kareba...
"Da sauri zahradee yace eh bb nima nafiso tayi karatun sbd koba komai zatasan encin kanta' nima yanxu da h'aka karatun nakeyi bb.
"bb id'an har zaka bani Aisha aure wlh zan'iya jiranta bb.
"Dariya muhammed yai h'ade da cewa Allah me iko' zahradee dan Allah kai daga wani g'ida kake ne?
"zahradee yace ni daga almadina queaters suna mahaifina alhj Kailani.
"muhammed yace a'a! Kardae ace Kailani me atanfofi?
"zahradee yace shifa.
"muhammed yace a'a lalla kafito daga babban g'ida ne domin duk zari'ar alhj Kailani sae son barka.
"jin h'aka yasa zahradee jin dadi a ransa.
"muhmmed yace zahradee yanxu abinda za'ayi kaje tuku' zahradee yace bb bangane ba? Alhj muhmmed yace zahradee ni dae
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 38