Share this page
nasan a yanxu da h'aka Aisha bakasan komai akan soyayya ba' k'uma banaso ta sani sbd banaso ta raba hankalinta biyu. "nafiso ta tsaya kawai tayi karatu' sbd shine kawai gatan daya dace na bata a duniy. "zahradee yace h'aka ne baba. "alhj muhmmed yace to kaji dalilina na hanata tsayuwa da samari. "zahradee yace to bb yaushe zandawo? "murmushi muhmmed yai h'ade da cewa yaro kenan' yanxu duk mgnr da nai maka baka Fahimta ba? To kaje ko gobe zaka iya zuwa mu gaisa' aikai d'ane a guna. "zahradee yace nagode bb' mikewa yai h'ade da sallamarsa. "yace to a gaida g'ida' idan ka'isa kace ina gaida alhj' kace masa alhj muhmmed na yan'wake na gaida shi. "zahradee yace zaiji in Allah ya yarda. "zahradee na tafiya alhj muhmmed ya kwashe da dariya h'ade da cewa yaro kenan' idan banda jarabar duniya kamar wanga yaron mai yasani akan aure? ☘☘ ☘ AURE IBADA NE FASAHA ONLINE WRITES F. O. W.☘ MMN USWAN FANS NAGA ADDU'OINKU NAGODE SOSAE ALLAH YABAR ZUMUNCI YA KUMA AMSA ADDU'ARKU AMEEN. 1⃣1⃣ "Alhj muhmmed yana shiga cikin g'ida gani yadda yake dariya yasa Hafsatu tambayarsa lfy? "Sae da ya zauna snn yake sanar da'ita yadda sukai da zahradee' Hafsatu tace Allah me iko yanxu da kansa yazo da mgnr ga alhj? "Alhj yace wlh kuwa nima kaina abin ya bani mmki. "umma tace to yanxu yaya kukayi dashi? Alhj yace aa kawai dae cewa nai ba yanxu zai aurer da'ita ba. "umma tace to ma alhj koda yanxu ne zaka aurer da Aisha sai a dauketa abawa yaron da besan ciwon kansa ba banle yasa nata. "Alhj yace kema dae kyagani. "zahradee yana isa g'ida parlour ya sami iyayensa zaune suna hira da yayyinsa h'akan yasa shima ya samu gun ya zauna kusa da abbansa. "Gani shi cikin nishadi yasa hjy cewa zahradee yah! dae? "Cikin zumudi zahradee yace himm hjy nibaki labari. "hjy tace bani nasha Allah yasa alkairi ne. "zahradee yace alkairi ne ma hjy' hjy tace to ina sauraranka' cikin doki zahradee yace hjy kinsan daga ina nake da kika gani h'aka? Hjy tace a'a saeka f'adi. "zahradee yace g'idan su yarinyar da zan aure. "duk parlour suka sa masa dariya. "zahradee yace Allah kuwa hjy da gaske nake. "Nan hjy ta haushi da f'ada tana f'adin kai zahradee kanka daya kuwa? Kasan abinka kake f'adi? Zahradee yace Allah hjy da gaske aure nakeso. "hjy tace idan kasake irin wanga mgnr anan saena mareka. "A take zahradee ya canxa fuska. "Gani yadda zahradee ya canxa fuska yasa alhj cewa xonan my son' bani labari nasha' kace dae zanyi sarkuwa. "hjy na gani haka mikewa tai ta shige daga ciki ta barsu a nan. "zahradee yace wlh abba wata yarinyace na dade ina sonta tun ina secondry lokacin batayi girma ba' haka nabar wa zuciyata har Allah yasa tai girma shine yau naje da kaina har g'ida su na sanarwa mahaifinta. "Alhj yace eye kacedae na girma tunda gashi har zankai ga sarkuwa. "zahradee yai dariya h'ade da cewa dan Allah abba kaje g'idan su Aisha kayi mgn da mahaifinta dan Allah abba wlh abba ina son Aisha sosae. "Alhj Kailani yace zahradee kasan mgnr da kakeyi kuwa? Kwata2 shekaruka nawa a duniya da zakayi mgnr aure zahradee? In ma banda abinka baka gani yayyinka ga suna ko mgnr auren basu' shine kai zakace kanaso aure zahradee. "Nurundee da shamsudee suce ato abba kowa ma ya gani' dan Allah kafita har kansa sauraransa da akeyi ma shine yasa yakewa mutani mgnr banza. "Jin h'aka yasa zahradee dukawa a gaban abbansa gwiwa bibbiyu h'ade da rike gwiwar abba yace dan Allah abba dan annabi abba ka taimaka min kaje g'idan su Aisha ka nima min auren ta abba' abba ni koda ba yanxu za'ayi auren ba inaso ta zauna a matsayin nine mijin da zata aure sbd ko secondry bata kareba k'uma abbanta yace sae tayi karatu snn zai mata aure. "Tunda zahradee yafara mgn abbansa ke kallonsa har ya kare' snn yace waima yarinyar da kakeso yar ' g'idan waye? "zahradee yace yar ' g'idan alhj muhmmed ne dake kasuwan yan'hatsi. "Alhj yace wani alhj muhmmed kake mgn akai? "zahradee yace alhj muhmmed dake zaune a doruwa mana abba' shifa ya sanka har cewa yai ma na gaidaka. "nan alhj Kailani yace ohooo ayya yanxu na tuna' Allah sauki aiko mutumin kirkine. "yanxu sbd Allah zahradee bataji kunyar tunkararsa da irin wanga mgnr ba? "murmushi zahradee yai h'ade da shafe kansa snn yace to ai abba mutumin hanata tsayuwa da samari yakeyi wai sbd kada a bata masa tarbiyar yarinyar sa' ni k'uma da gana h'aka shiyasa naje gunsa direct na sanar dashi manufata. "mmki ya kama alhj Kailani sosae' shiru yai yana kallon zahradee har yakare snn yace to da kaje gunsa ya kukai dashi? "zahradee yace cewa yai wai sae tai karatu snn zai aurer da'ita. "Nima kaina abba inaso Aisha tai karatu sbd yarinyar mai hazakace tana da ilimi sosae' amma inda so samune da tana kare secondry sae ai mana aure idan yaso a gidana sae taje gaba.... "amma ya dakatar dashi da cewa haba zahradee wanga irin zance kamar saeda kai haddansa snn kazo guna. "Snn abba yace zahradee lalla hakan ya nunamin ba karamin so kake wa Aisha sha sbd tunda nake dakai baka taba fitowa gaba da gaba ba ka nunamin bukatarka haka sae yau' sae da alhj Kailani yasa hannu ya dafe kafadar zahradee snn yace zahradee. "Nagode da h'akan dakai koba komai nima ka siyemin girma da daraja a idon sa' amma ita yarinyar tasan kana sonta? "zahradee yace a'a bata sani ba abba. "Alhj Kailani yace ina me baka shawara da kaje ka nimin soyayya a gun yarinya idan har ta amince tana sonka nikuma nai maka alkairin nima kama aurenta a gun mahaifinta. "tsanle zahradee yai h'ade da rungume mahaifinsa yana godiya' sae da ya zauna snn yace to abba itana zanfara? "Duk su uku sukasa dariya shamsudee yace shege dama ashe karyan rashin kunya kake mana' ko iya zance da budurwa ma baka iya ba. "Sae da zahradee ya daure fuska snn yace abba kaganshi ko. "kamo hannunsa abba yai h'ade da cewa xonan my son fadimin me kake bukata? "zahradee yace dama kudin da zaiyi mata siyayyane na kai mata shine bandasu. "dariya abba yai snn yace zahradee waye yace maka zuwan farko gun budurwa ana bata kudi? Zahradee yace to abba me zankai mata wanda zataji dadi itama? "Alhj Kailani yace zahradee. "zahradee yace na'am abba. "abba yace tattaro hankalinka ka miko min su nan. "zahradee yace to abba na. "Gani irin abinda sukeyi su kamar abokan juna shamsudee da Nurundee yasa su tashi subar gun. "bayan sun tashi ne abba yace zahradee. "zahradee yace na'am abba. "Alhj yace inaso ka natso da kyau ka saurari abinda zan f'adi maka' nasan yana mstukar son Aisha' sbd yadda ka nuna min' amma inaso kasan da cewa ita mace kamar wahainiya take tana iya chanzawa a ko wani lokaci. "Idan h'aka a matsayina na mahaufunsa ina baka shiyasa kada ka sake Aisha tasan kana sonta h'aka' bance kada ka nuna mata so ba amma kayi da kadada sbd gudun yin dana sani. "kai na mijina k'uma duk namiji ansansa da karfin hali da juriya ba komai ne zaka nuna zakewa akai ba' banle akan mace. "idan har kabari Aisha tasan kana sonta haka tabbas kana tare da wahali' k'uma ita rayuwa da kake gani ba lallane abinda kakeso ka samuba' idan yau Allah yasa Aisha ba matarka bace yaya zakayi? Shiyasa nakeso kabi komai a hankali. "mgnr abinda zaka kai mata k'uma da kake mgn akai' zahradee banaso tun farko ka fara budewa Aisha ido da kudi' bawai banaso kai mata alkairi bane ko dan baka dashi ko k'uma kayi tunanin banaso na baka ne a'a wlh ko daya zahradee kafi kowa sani duk cikinku nafi sonka dan h'aka banga abinda zaka bukata a guna na hanaka ba sae dae idan bandashi ko yafi karfina. "Amma idan tun yanxu kafara b'ude mata ido da kudi in har Allah yayi ita abokiyar rayuwarka ce baka tunanin yadda zamanku zai kasance. "idan h'aka nafiso kaje ka hureta da soyayyarka tuku idan yaso komai sae yabi baya'idan har kanaso ka bata kyau kabari kaje kamar sau biyu kaga irin karban da zatai maka snn in katashi komawa sae kai mata shatara ta arziki ka kai mata. "Amma idan tun yanxu kafara zuwa da mata da kudi ko wasu abin duniya ba lallane ka tantance irin son da take maka ba' dan Allah ne take sonka ko dan abin hannu kane' amma idan kaje babu komai ta nanne zakasan irin son da take maka na Allah ne ko kuwa. "ni kuma nai kama alkairin insha Allahu da kaina zaje na nimo maka auranta. "zahradee yace hakane abba na' tafawa sukai suka sha hannu. "zahradee yace Nagode abba na' shiyasa nake matukar sonka' Allah ya barmin kai. "nan dae sukaci gaba da hiransu' zahradee nabawa abba labarin Aisha suna dariya. "Alhj Kailani duk cikin yaransa yafison zahradee' sbd Zahradee yarone mai biyyaya k'uma baya tsanlaka mgnr mahaifinsa duk cikin yan'uwansa yafisu sa hankali akan kasuwancin abbansu sbd su shamsudee da Nurundee tunda sukai girma suka san dadin kasuwanci kowa kama nasa yai' kasan yasa abbansu daukar yaran shago yana biyansu'amma tunda Zahradee yakawo karfi yashiga har kasuwancin mahaifinsa gadan gadan' koda yaran shago sun so yin cuwa- cuwa amma ganisa yanasa su rage wani abu. "duk da dae bazai hanasu yi kwata2 ba amma zaiyi sauki' shima kansa abba yaga canji sosae' duk da karatunsa amma be hanasa xuwa kasuwa ba' h'akan yasa abbansa yake matukar son sa fiye da sauran yan'uwansa. "duk da nuna masu babbancin da yakeyi be damesu ba sbd sufi kowa sani dalilin da yasa yake masu hakan. "tun daga lokacin Zahradee yake zariya g'idan su Aisha' tun bbn Aisha yana kin kulasa har ya gaji yaci gaba da kulasa' mafi yawancin lokuta batare da abbansa ya sani ba idan Zahradee zaije g'idan su Aisha yakan siyewa su abdul sweet da chocolate da ice cream yakai masu. "su abdul suma har sun saba dashi sosae' amma duk a lokacin be yarda sun fara tsayuwa da Aisha ba' shima beyi fushi yasa ya daina zuwa ba. "A lokacin Aisha na SS2 wata juma'a da zahradee yazo shida abokinsa Russlayni suna tsaye a kofar g'ida ga hadari ya taso gadan gadan haka ruwa yai masu dukan tsiya' shiko Russlayni da yake mai zuciya ne nan yahau masifa inda yake shiga bsnan yake fitaba. "in banda hakurin da yake bashi babu abinda Zahradee yakeyi. "Russlayni yace badae zan rantseba amma ba lalla bane na sake rakoka g'idan ga' sae kace yar'gwal' ko ita kadae ce macen da tarage a duniya da zaka rinka wahala h'aka a kanta. "Wai ma na tambayeka dame suke takama kudi ko mulki? Nidae naga ba yar'kowa ne ba' k'uma ubanta ba finku kudi sukai ba amma sae sa wani uban doka' to wlh idan kai zaka jure ni bazan jure ba ' k'uma bazan sake rakoka ba. "Sae kace wata gwal kai idan gwal ne daga yau ka yage inaso su dauketa su daura a wiya su rinka yawo a gari sbd asan suna da kaya mai tsada da daraja' amma ita ba gwal ba banle ace. "Duk mgnr da Russlayni keyi shiru Zahradee yai yana kallonsa har yakare. "Ashe duk mgnr da Russlayni keyi alhj muhmmed yana jinsu' shiru yai har Russlayni ya kare' shima kansa yasan be kyauta ba' sbd tun kafin ruwa ya dauko suke tsaye a kofar gida shi bace su shigo daga ciki ba kuma bace su tafi ba gashi kenan ruwa yai masu dan banzan duka. "hakan yasa shi matsewa yace Zahradee dan Allah kuyi hakuri wlh kafin na iso gunka ne ruwa ya sauko amma insha Allah idan na shiga cikin g'ida yau d'in nan zansanarwa Aisha komai a kanka k'uma in Allah ya kawoka ko zuwa gobe ne zanbata izini fitowa ta saurareka. "Zahradee yace ba komai bb Allah yasa mukai. "Russlayni da yake yariga ya fusata ko kallo alhj muhmmed be'ishesa ba jan hannu Zahradee yai suka bar gun' ko sallama be bari suyi ba. 📖🖊 ☘☘ ☘ AURE IBADA NE FASAHA ONLINE WRITES F. O. W. ☘. MMN USWAN Allahamdulillah masha Allah. It's a great pleasure for me to be able to make the most important decisions in my life and I am very thankful to almighty for the opportunity and the previllage of my life to be in a good health condition. 1⃣2⃣ "Alhj muhmmed yana shiga cikin g'ida umman su Aisha dake kwance a kan gado gani yadda ya shigo a jike sharkam da sauri ta mike h'ade da tambayarsa daga ina h'aka. "Alhj yace gani nai baku da bread ya kare shine ya fita siyowa sbd yara duk sun yi bcc ga k'uma dare da yai shiyasa nsje da kaina. "umma tace shine kabari ruwa ya dukeka h'aka? "Alhj muhmmed yace to yaya za'ayi' mikewa tai ta taimaka masa ya cire kayan snn ta dauko masa bargon da yake rufe jikinsa dashi idan sun zo kwanciya ta bashi ya rufe jikinsa dashi snn suka kwanta. "suna kwance ne alhj muhmmed yake sanarwa umma cewa yanxu su zahradee ya tafi g'ida k'uma gashi ruwa yai masu duka'umma tace Allah sarki Gaskiya alhj yaronga ba kasamin so yakewa Aisha ba' idan ba kana gani zaizama matsala ba' mai zaihana kabara umurnin tsayawa dashi' tunda kaga yanxu ta mallaki hankalin kanta' k'uma shima yaron a iya nazarinsa da nai yanada nasha. "Alhj muhmmed yace himm Hafsatu kenan nan kullum ku mata tunaninku irin daya ne kina gani yaro karami wanda be gama sani ciwon kansa ba banle na wani' ta yaya zanbari Aisha ta tsaya dashi' umma tace sbd me alhj? Kodae baka sonsa da'ita ne? "Dariya alhj yai h'ade da cewa wlh ko daya Hafsatu nidae kawai tsorona daya ne kada nazo na saki jiki dashi yazo ya kaeni ya baroni' in banda rayuwa yariga ya zamo abinda ya zama kamar yarona ina yasan wani kalmar so' himm Hafsatu wlh idan bakine ranar da yafara zuwa guna ni da farko ma na dauka aikensa akai ashe aike kansane. "Babu ko kunya wai yazo niman auren Aisha. "Tsayawa tai ta barshi sae da ya kare snn tace alhj kenan ni k'uma a nawa tunani yanada hankali sbd inda wani yaron ne yadda kake mgnr yayi karami to wlh ba lalla bane yazo ya sameka sai dae kawai kaji a gari ace Aisha tana hira ko k'uma ace tanada samari suna zuwa gunta. "amma tunda har kaga yayi haka ya nuna maka shi dan babba g'ida ne' k'uma in Allah ya yarda abinda kake tunani in Allah ya yarda bazai faruba' k'uma idan banda abuka hanata sauraranro samari bashi ne zai shiryar maka da'ita ba' idan Allah yariga ya shiryar maka da yaro to ka gode Allah. "Alhj yace hakane amma ai Allah da kansa yace tashi na taimaka ko? "Hafsatu tace hakane amma inaso kasan cewa Allah shike shiryarda da wanda yaso ko. "Alhj yace hakane to Allah ya kara shiya mana' musan ba wayanmu bane k'uma ba dabararmu bane. "umma tace abinda nakeso ka gane kenan. "Nan dae sukai ta hiransu. "Tun a hanya zahradee yake tunani kala-kala akan Aisha' anya bbnta yana sosa dashi kuwa? Duk tsawon lokacin daya diba yana zuwa g'idan su amma har yanxu bbnta bebari ya fara tsayuwa da'ita ba' kodae akwai wani abu a zuciyarsa ne? Da yake boyesa k'uma ya kasa fitowa ya sanar dashi. "Sae dae kullum idan yazo yai ta jansa da hira bayan k'uma ba gusa yazo ba' shifa Gaskiya yafara gajiya da irin wanga abu da bbn Aisha yake masa' idan yasan bazai bashi bane kawai gara tun farko yafadi amma ba yaita ja masa rai ba. "Russlayni ne ya katse masa tunaninsa da tabansa yace zahradee. "yace na'am Russlayni' Russlayni yace tunanin me kikeyi? Murmushi kawai zahradee yai h'ade da cewa babu komai. "Suna area d'insu kowa ya shige g'ida da yake dama layinsu daya ne. "zahradee yana shiga g'ida d'akinsu kawai ya nufa' da yake anyi ruwan sama shiyasa parlour babu kowa. "koda zahradee ya kwanta yai kokarin bcc amma abu ya gagara'sae faman juyi yakeyi' zuciyarsa na saka masa abubuwa kala-kala zahradee be samu bcc ba sae asuba. "bari yai sae da yai sallar asuba snn ya kwanta. "washe gari da safe da yake yau weekend ne k'uma dama duk ranar end alhj muhmmed baya su Aisha da kannita suna karyawa bbnta yace Aisha idan kin gama inaso ganiki. "to kawai Aisha tace. "Aisha na gani karyawa taje jin kiran bbnta' da sallama ta tashi dakin har kasa ta duka snn tace abba gani. "sai da alhj muhmmed yai gyaran murya snn yace Aisha dama ba komai bane yasa na kira ki' inaso na sanar dake wata mgn ne ina yaron nan zahradee da yake yawan zuwa? Ba kince kin sanshi kuyi mkrnta daya ba? Aisha tace eh' yace dama niman izini yazo a guna sbd duk ganisa da kikeyi a g'idan nan ba zuwa yakeyi ba' guki yake zuwa abinda yasa kike gani yana zuwa guna sbd naki bashi bakine a kanki. "Amma yau nayi masa alkairin zanbari kifita idan yazo shiyasa nace bari na sanar dake' sbd kada kice baki da masaniya akai... "Aisha tace to abba ni mezan masa da yake zaizo guna? "abba yace nima bansaniba amma idan yazo zai sanar dake da kansa manufarsa. "Aisha tace to shikenan abba. "Alhj muhmmed yaci gaba cewa dan Allah Aisha inaso ki kula sosae kada kiga nabaki izini tsayuwa da samari ki nimin ki zubarmin da mutunci' wlh Aisha idan kikaimin h'aka bazan yafe maki ba. "Aisha ban amincewa zahradee ba sae da naga natsawarsa' amma kasa dan'adam ta yake be cika goma ba' dan Allah Aisha kada kibari shedan ya rinjsyeku ku aikata abinda zaisa mutunci na ya zuwa a uguwa kinjiko Aisha. "Aisha tace naji abba k'uma in Allah ya yarda zankiyaye. "Alhj muhmmed yace Allah yabada iko. "Aisha tace ameen. "Da yamma bayan an idar da sallar isha'i gani garin da hadari yasa zahradee zuwa da motar bbnsa' itama Aisha bayan ta idar da nata sallar duk da abbanta be sanar da'ita ita nufin zahradee a kanta ba amma be hanata rangada kwalliyarta ba' da yake dama ma'abociyar kwalliyace. "kwallliya tai cikin doguwar rigan shadda wanda abba ya dinka mata ita da kanita abdul irin daya green ba kasamin kyau tai ba. "bayan ta gama gun tasamu ta zauna kusa da abdul suna hira' ita k'uma ummansu tana gun alhj tana bashi abinci' dama dabi'ar Hafsatu ne bata barin mijinta ya zauna shikadae dan zaici abinci' koda bazataci ba zama takeyi kusa dashi yanaci suna hira har ya gama. "sallamar yarone ya katsesu da sauri umma ta leka h'ade da tambayar waye? Bayan yaro yai gaisuwa snn yace wani ne ya sikoni wai yana sallama da Aisha. "umma tace jeka kace waye? "komawa yai snn ya dawo yace yace wai zahradee ne. "umma tace jeka kace tana zuwa. "yace to. "komawa cikin dakin tai ta sanarwa alhj' alhj yace kice taje amma minti talatin nabata' kuma tasa hujab idan zata fita. "umma tace to. "kiran Aisha tai dakinta sae da takara gyara ta h'ade da sanya mata hujab snn tace taje ana sallama da'ita. "Cike kunya ta kami hanyar fita sae k'uma ta juyo' umma tace lfy? Aisha tace abdul nakeso ya rakani. "murmushi umma tai snn tacewa abdul yasashi suje. "Aisha na rike da hannu abdul suke fita gun zahradee. "zahradee dake zaune a mota hangosu yasashi fita da sauri ya kariso gunsu h'ade da kiran malama Aisha' murmushi kawai Aisha tai snn tace ina yini. "Cikin doki da murna zahradee yace lfy klau Aisha' ya g'ida dasu umma da abba? "Aisha tace lfyrsu klau. "juyowa yai gun abdul dake tsaye ya tsaresu da ido snn yace abdul bako gaisuwa? "murmushi abdul yai snn yace ina yini. "zahradee yace lfy klau malam abdul. "juya akalar kallonsa yai gun Aisha h'ade da cewa Aisha ina tafan abba ya sanar dake komai ko? "Aisha tace a'a. "juyawa yai gun abdul snn yace dan Allah abdul din bamu gu muyi mgn kaji. "to kawai abdul yace snn ya kauce ya basu gu. "bayan kaucewarsane zahradee yai wani gyaran murya snn yace Aisha nayi tunanin abba yariga ya sanar dake ne' amma tunda kince be sanar dake ba babu damuwa ni da kaina zan sanar dake abinda yake tafe dani Aisha. "zahradee yace kina kayrarona kuwa Aisha? Aisha tace ina sauraronka. "Ba komai bane ke tafe dani Aisha sae so da kauna danake maki Aisha' Aisha ba dade ina sonki shekara da shekaru h'aka naci gaba da rainon soyayyarki har izuwa wanga lkcn Aisha' shiyasa yanxu bace lokaci yayi da yakamata na sanar dake kudurina akanki' gani abba baya barinki tsayuwa da samari yasa nazo gusa direct dan niman izinin zuwa guki. "Shiru tai tana sauraronsa' gani shirun da tai ne yasashi cewa Aisha kina jina kuwa? Murmushi kawai tai masa. "zahradee yace shiru da kikai tabani amsa sae dae kashhh! Bazan iya babbance kalar amsarki ba sbd fasara biyu tabani wakau eh ko a'a' Aisha kina sona kuwa? "murmushi tai h'ade da sa hujab dinta ta rufe fuskanta. "wani irin dariya zahradee yai h'ade da hamdala snn yace Aisha nagode da amsar soyayyata da kikai yi' Allah yasa kinaso kamar yadda nake sonki Aisha' Allah kuma ya barmu dare har karshen rayuwarmu. "Cikin jin kunya Aisha tace zantafi abba yace kada na dade. "zahradee yace Aisha hakan ma nagode' ban sbd tunda nake zuwa g'idan ku ban taba tsabar kaina cikin farin ciki irin yau ba. "Bari na barki ki tafi gida haka kada abba yai maki fada kinga ba zanji dadi ba ko? "Shiru Aisha tai. "zahradee yace Aisha ki gaida abba da umma saeda safe. "juyawa tai h'ade da kama hannu abdul suke shige cikin g'ida. "zuba mata ido yai har saeda yaga ta shige' wani irin tsalle yai yana murna snn yashige mota yaja yabar uguwar. 📖🖊 ☘☘ ☘ AURE IBADA NE FASAHA ONLINE WRITES F. O. W. ☘. MMN USWAN ALLAHAMDULILLAH MASHA ALLAH. INA TAYA DAYA DAGA CIKIN MEMBERS DINKU MURNAR AURE. HAPPY MERRIAGE LIFE SIS KHAIRAT UP. Marubuciyar Takaicin d'a namiji Fatima zara Aisha Humaira Kai nake so Da sauransu. Allah ya bada zaman lfy yakawo zuri'a na gari yasa nayi kenan mutu ka raba. 1⃣3⃣ "yau zuciyar zahradee cike yake da farin ciki fal baya musaltuwa. (Ya Allah Ka HADAMU DA MASOYAN MU KO A LAHIRANE AMEEN Ya RABBI). "zahradee yana isa g'ida' bayan yai parking direct parlour ya nufa sbd bare banyi ba banle ance su abbansa su kwanta. "Da sallama ya shiga parlour' su hjy da yayyansa suka amsa' bayan ya duka ya gaida iyayyensa da yayyinsa snn ya mike kusa da alhj Kailani yaje ya zauna' gani yadda yake cikin farin ciki yasa alhj Kailani cewa my son yaya dae? Yau na ganka h'aka? "zahradee yace himm abbana ban baka lbr ba' alhj Kailani yace son bani nasha. "zahradee yace yau bbn Aisha ya bari ta fito ta saurareni na bayyana mata abinda ke raina k'uma ta amince tana sona. "Alhj yace wow son na tayaka murna. "zahradee yace nagode abba. "Gani irin abinda sukeyi yasa hjy tace dan Allah alhj menene kukeyi h'aka? koda auren aka daura nasan iya kacin murnar da zakuyi kenan. "Kailani yace bazaki gani bane shiyasa. "mikewa tai ta bar masu gun. "su shamsudee da Nurudee da suke gun h'ada ido sukeyi snn shamsudee yace a dae yi a hankali. "Nurudee yace kasan JJC( july just come) ne that is why. "duk suka sa dariya. "su Amatulrahman da suke zaune a gefe'Amatullah tace yy anty ne zaka kawo mana? "Tsawa abba ya daka masu yana cewa waye yasa bakinku a mgnr? shiru sukai h'ade da mikewa su bar gun. "abba yace my son yanxu kasan me za'ayi? Zahradee yace a'a abba. "Sae da alhj Kailani ya gyara zama snn

Chapter 6 of 38