gaisa take sanar da'ita mgnr zahrd.
"ubaida tai murna sosae da fatan Allah yasa ayi a sa'a".
"amin ngd ubaida"
"amma Dan Allah na tambayeki mana Aisha".
"Allah yasa nasani".
"Dan Allah Aisha yaya kikaji a lkcn da zahrd yazo a matsayin yadawo gareki?".
"him ubaida kenan".
"a rayuwata ubaida babtaba tsammani zahradee zai dawo gareni amma wani hukunci na ubangiji yau way nine zahradee zai aura.
"him" Aisha kenan"
"wlh dama tun farko banso aurenki da Nasir ba' kawai dae dan naga yaddau kika zake kika nuna kinfi sonsane akan zahradee shiyasa' k'uma kinsan ance matar mutum kabarinsa koda na yini daya Allah yariga ya rubuta zaki zauna da Nasir.
"h'aka be ubaida' wlh bantaba tsammani Nasir zaimi h'aka a rayuwa ba' shiyasa har yanzu nake kwankwanto Nasir din dana sanine kuwa"
"a'a" Aisha ba shibane wanisa ne".
"Aisha idan zaki kwantar da hankalinki ki rungumi masoyi dae da yafi maki".
"Nasir d'in me Nasir din bazan' idan yana soki da bazai turoki g'ida ya mance dake h'aka ba'daga mgn sae ya'aiko da takardan saki.
"Ni wlh idan banda ina gani girmansa dako gaisawa bazamuyi ba.
"ba mmki dama tun farko ba sonki yakeyi ba' sha'awace tasa ya aureki' yanzu k'uma da kika daina bashi sha'awar ya koroki.
"wlh Aisha duk da kinki f'adiwa kowa irin zaman da kikai da Nasir amma duk wanda yasan menene jin dadi Aisha baki tare dashi sbd jikinki ya nuna.
"ke idan bandama abin ubangiji da yake dauke mana nawin mazajanmu kawata ina zakikai Nasir' mutum ga girma ga tsayi kamar basamude.
"amma ke dubeki kamar akama a karya".
"dariya Aisha tai".
"Aisha idan zaki kwantar da hankalinki ki kwantar kibada kai biri ya h'au.
"a rayuwa idan ka auri me sonka wlh kagama komai koba komai ke kuruciya shima h'aka kinga sae kumore kuruciyarku banlema ke da kika taba aure kinga kenan sae yadda kika juyashi sbd yanzu kinfishi sani kan duniya.
"amma kinsan yakamata kiyi gyara ko".
"gyaran me k'uma?".
"keko kigane mana".
"shewa sukai h'ade da tafi".
~~~ ~~~ ~~~
Gskya Nasir ya kamata muje g'ida kano' sbd mudade bamuje ba".
"h'aka ne Fatima amma kinsan na f'adi maki banida lfy ko?" baki gani ko fita banayi?".
"h'aka ne' Allah ya baka lfy".
"amin Fatima".
"Nasir kodai hospital ne zamu?".
"a'a" kibari mugani tuku kin dict kamal yana zuwa har g'ida ya dubani idan muka tafi hospital zaice banyaba da kokarin da yakemi bane.
"h'aka ne kam"
"amma kibari mugani zuwa gobe".
"gobe k'uma?"
"Eh"
"to' Allah ya kaimu".
"amin"
"amma yanzu ya kakeji jikin naka?"
"wlh Fatima ni kadae nasan abinda nakeji' cikin jikina kamar wuta ake huramin".
"a'ahhhh!"
"kashi magani rana?"
"a'a" ban shaba"
"bari to na dauko maka kasha".
"a'a" dibomi ruwa nayi addu'a kawai sbd nafi jin dadinsa".
"to tace h'ade da mikewa".
"daga nan ki kirami su Jabeer da Khadijat.
"Fatima na dibo ruwan tare suka dawo dasu Jabeer.
"amsar ruwan yai yafara addu'a' saeda yadade yanayi snn yasha ragowar k'uma Fatima ta amsa ta shafa masa a jiki.
"bayan ta gama bayansa taje ta zauna gab dashi h'ade da dora hannayenta a kafadarsa tana masa tausa" musmushi yai alamu nuna jin dadin abinda take masa".
"gani su Khadijat da Jabeer suna kallonsa bude masu hannu yai alama suzo.
"a guje sukaje jikinsa".
"h'aba Khadijat meyene kukeyi h'aka?" baku gani beda lfy ne".
"a'a kyalesu kawai' basuda inda yanan.
"amma gani nayi bakada lfy ne ai".
"kamar ki damu".
"Nasir nace kodae a sanarwa g'ida ne?'.
"me fa".
"a'a barsu kawai".
"himm Nasir kenan".
"tun daga lkcn Fatima bata sake mgn ba.
"cikin dare around 12AM jikin Nasir ya tsanata'gani yadda yake hasa-hasa Fatima ta kira gateman ya taimaka mata suka dauki zuwa mota.
"Da sauri tai rushing dinsa zuwa hospital din doct kamal' suna isa emergency room aka kaisa doct kamal ya bashi taimakon gaggawa h'ade da samasa drip da allurai snn yasamu bcc.
"Tunda Nasir ya sa bcc be falkaba sai bayan allar asuba snn ya falka' yana falkawa daidai lkcn Fatima na zauna a gefen kasan' gani ya bude ido yasata dagowa da sauri tana f'adin sannu Nasir yaya jikin?".
"kai ya daga mata alama da sauki".
" a hankali yake kiranta amma batajiba sai dai kawai gani bakinsa tai yana motsi' hakan yasa ta kara kunnita a bakinsa snn taji abinda yake cewa.
"Ashe yara yake tambaya.
'"Fatima tace suna gida.
"da hannu ya nuna mata alama taje gunsu.
"Fatima tace aa Nasir babu damuwa kaidae kaji da kanka kawai.
"duk da h'aka Nasir yaki yarda gani ya nace yasa Fatima taje ta dauko su.
"anan su Khadijat suke yini da yamma Fatima ta medasu gida ita k'uma ta dawo hospital.
"a hankali Nasir ya fara samu sauki dan har mgnrsa yafara fita ba kamar da ba.
"da Bilyaminu yazo bayan sun gaisa da Fatima Nasir yace Fatima tafita ta basu gu zasuyi mgn.
"h'aka ta fita dan babu yadda zatayi' bayan ta fitane suka sake gaisawa da Nasir snn yai masa mgnr da yakawoshi.
"Nasir yace babu damuwa bari yanzu nai kama transfer a account dinka idan yaso sae kaci gaba da aikinka.
"Okay kawai yace".
"bayan ya fitane Fatima ta tare Bilyaminu tace Dan Allah Bilyaminu inaso nai maka wani tambaya?".
"Allah yasa nasani".
"Dan Allah bilyaminu waini me kuke kullawane kaida Alhj Nasir?".
"haba Hjy me kike tunanin zamu kulla kuwa".
"humm bilyaminu kenan' kasan dae ni matan Alhj ne k'uma bazan so ace yau ya aikata abinda zaije ya dawo ba ko?"
"haka ne but Dan Allah kiyi hkr sbd alkawari naiwa Alhj akan koda wasan bazan bari wani yasani ba..
"haba bilyaminu wani irin abu kuke aikatawa ne da bakuso wani ya sani.
"babu komai sai alkairi'amma tunda kin matso kiji zaki iya tambayar Alhj idan yafadi maki da kansa fanilabihamduli.
"to shikena ngd".
"Allah ya kara sauki"
"amin ngd".
"bayan Fatima ta koma daki gu tasamu kusa da Nasir ta zauna hade da dora hannayeta akan kirjisa' snn tace Nasir Dan Allah na tambayeka mana?"
"Allah yasa nasani'.
"Dan Allah Nasir mekuke kullawane kaida bilyaminu?"
"na mefa?"
"kusan lkt da dama idan yazo zakuyi mgn bakason yi a gabana".
"Eh" h'aka ne'be shafeki bane yasa".
"yanzu sbd Allah Akwai abinda zakayi kace be shafeni ba?"
"amma kinsan a rayuwa babu abinda nake boye maki idan zanyi me'kyau ko akasin hakan ko?"
"h'aka ne".
"to kiyarda mi beshafeki bane".
"himmm"
"Fatima abinda nakeso kigane wnn Abu inayine dan ni dake da k'uma yaranmu fa"
"to shi abin beda suna?".
"yanada suna amma kibari idan lkc yayi zaki sani.
"Allah yasa a aikata alkairi".
"alkairi nema Fati na".
~~~ ~~~~ ~~~~
Allah ya kawomu yau daurin aure Aisha da zahradee' gidan su Aisha kam babu wasu mutani sbd ummata tace bazatayi taroba sbd ba'a dade da taron farko ba yanzu k'uma ace ana wani taro' ita gskya bazatayi ba.
"hakan yasa babu wasu mutuni sosai' saidai wanda baza'a rasaba.
"goga zahradee kuwa yaiwa Aisha dike dike na ban mmki' h'aka shima kanshi.
"gidan su suma Alhj bata sanarwa abokanar arziki ba'sai dangi kawai suna yakama dole ne yasa.
"karfe goma daedae aka daura aure.
"zahradee najin anshafe wani irin kabbara yai wanda shima kansa besan lkcn da yai ba.
"bayan sallar magrib aka kai amarya gidan mijinta.
"ya kumbo ita ta kai Aisha dakin uwar miji bayan sun gaisa matan dake dakin kowa ya tofa albarkacin bakinsa da fatan zaman lfy.
"fuska Aisha a rufe da kyale ta mike kenan zasu fita kyalen yai santsi fuskanta ya bude.
"da sauri taja ta rufe.
"a lkcne daya daga cikin matan dake zaune a dakin ta karewa Aisha kallo.
"mikewa tai h'ade da kiran Hjy su shiga daga cikin bedroom' duk matan dake zaune su baza kunni suji abinda zatace.
"suna shiga matan tace ke Hjy dama wnn aishan ne zahradee ya aura?"
"Eh ita ce".
"amma kika yarda".
"kamar yaya menene da'ita?"
"hmm" Hjy kenan".
"lfy?"
"yanzu sbd Allah zakice bakisan komai a kanta ba".
"kamar yaya?".
"kodan tabata aure?"
"aure me?" idan sbd aurene Ai me sauki ne".
"to menene?".
"na tabbatar maki Aisha dai HIV ne da'ita k'uma ance ba'a gun kowa tasamuba sai gun tsoho mijinta.
"HIV fa kikace"
"kwarai da gske".
"kan ubantan uban nan' Ashe da kasa.
"yau za'a yita".
📖🖊
☘☘
☘
AURE IBADA NE
FASAHA ONLINE WRITES F. O. W.☘.
MMN USWAN
2⃣8⃣
"me za'ayi Hjy?"
"Dan Allah duk sbinda zakiyi bazan hanaki tunda d'anki ne' k'uma lfyrsa tafiye maki komai amma kibari idan jama'a saragu duk abinda za'ayi sai a yisa.
"yanzu dae d'anne zcyrki mukoma gun jama'a tuku.
"batare da ta saurari abinda Hjy zata ceba ta jata zuwa parlour.
"bayan su Aisha sun shiga daki' kanni Hjy dana Alhj sukakai masu abinci' masu ci sukaci bayan su gama drive daya dauko amarya ya medasu g'ida.
"around 11-30 duk yan'biki su tafi masu kwana kuma suyi bcc' yarage Hjy da kannita a d'akinta suna ta hirarsu.
"abokan zahradee suka kawoshi' Aisha na zaune a bakin gado' jin sallamarsu yasata rufe fuskata.
"duk suka shigo Ruslayni ne yafara b'ude taro da addu'a snn kowa yafadi abinda baza'a rasa ba.
"zahradee baki har kunni yana godiya.
"snn sukai sallama' bayan ya rakasu ya dawone ya matso kusa da Aisha' duk a lkcn kanta rufe yake hannu yasa ya yaye mata mayafin dake kanta.
"gani tai face-face da hawaye yasashi cewa subhanalillahi Aisha me zangani h'aka? kuka k'uma a rana irin ta yau' wanda idan a f'ade ne banida kalmomin ko lafazin da zanyi anfani dasu wajan furtasu ba' to dan Allah kiyi hkr ki dae na kukan nan kinji Aisha ta.
"jawota jikinshi yai ya rungume ta'yasa hannu yana share mata hawaye' ita k'uma manna kai tai a kirjinsa.
"saida yaga ta daina kuka snn yace to yanzu tashi muje muyi alwala muzo muyi sallah mugodewa ubangiji ko?".
"mikewa yai h'ade da kamo hannunta suka shiga toilet saeda tafarayi bayan ta gama ne shima yai nasa suka fito.
"zahradee ya jasu sallah raka'a biyu suna idarwa zahradee ya dora hannu a kanta yai addu'ar da ibangiji ya umarci ango da yayishi.
"yana idarwa duk da dai ba wnn ne na farko a gunta ba amma koda zahradee yai mata tambayoyi h'aka ta amsa masa tsaf snn yace alhamdullh.
"mikewa yai ya dauko ledar daya shigo dashi ya dawo bayan yau zauna ne ya bude ledar snn yace bismillh.
"musmushi kawai tai".
"har zahradee yakai na biyu Aisha batasa hannu ba' gani taki sa hannu yasa zahradee dibawa da kansa yake bata' Aisha taso taki amma gani yadda ya nace mata yasa ta amsa.
"suna gamawa yace suje suyi brush' bayan sun gama brush suka fito sbd kunya zahradee kasa cire riga yai saida ya kashe light snn ya tube' jin yazo ya rungume ta yasa ta kankame jikinta duk abinda yake mata' kasa meda masa tai.
"shiko zahradee be dameshi ba' h'aka yaci gaba da aiwatar da nufinsa.
"da h'aka yasamu ya rabata da kayan jikinta zahradee yana gab da zai aiwatar da nufinsa kenan yaji knocking kamar bazai tashiba amma jin knocking d'in yaki karewa yasashi mikewa saida ya meda dogowar wandonsa snn yaje ya bude kofar.
"gani Hjy ne yasashi komawa ya dauko rigansa yasa snn yafito' yana fitowa Hjy ta jamasa hannu sukai nisa da d'akin snn tace kaje d'akin su Shamsudee ka kwanta.
"cikin rawar murya yace lfy Hjy?"
"bana bukatar tambayarka dalilin h'akan' kawuce kawai.
"jikin zahradee yai sanyi' tsayawa yai ya zubawa Hjy ido.
"bazaka wuce ba?"
"wlh zahradee idan kaje ka kwana a dakin ban yafe maka ba'sa kai kawai tai tabarsa tsaye a gun.
"babu yadda zaiyi' h'aka yaje d'akin su Shamsudee ya buga masu sbd suma sunriga suyi bcc.
"Nurudee ne yaji knocking d'in da akeyi' da sauri yace waye?" nine yaya" kai wa? zahradee.
"da sauri yaje ya b'ude kofar h'ade da tambayar lfy?" ba tare daya tamkaba yashige d'akin' dakai fa nake".
"Hjy ce tace nazo nan na kwanta".
"ka kwanta?" me yafaru?"
"wlh yya nima bansani".
"kai Shamsudee tashi dan Allah".
"cikin magagi yace lfy me yafaru?'
"Dan Allah katashi"
"b'ude ido da zaiyi yaga zahradee da sauri yace lfy kazonan?"
"shiru yai be tamka ba".
"Shamsudee ne yace Hjy ce tace yazo nan ya kwanta.
"ya kwanta k'uma?"
"to Allah ya kyauta" koma menene da safe maji".
"matsa masa sikai ya kwanta".
"shiru shiru Aisha bataga zahradee ya dawoba mikewa tai taje ta leka bataga kowa ba' dawowa tai ta zauna a bakin gado mmki ya'isheta can ta tuna da waya da sauri ta d'au wayarta tai dialling number yana shiga taji ringing kusa da'ita dole yasa ta hakura da kiran.
"mikewa tai ta dauki kayanta ta mayar snn ta kwanta.
"da asuba lkcn Abba yafito zuwa masallaci yaje tadasu Shamsudee sutafi'dama dabi'arsane duk asuba tare suke zuwa masallaci yana knocking duk suka fita sbd dama duk sun riga su tashi.
"gani sufito harda zahradee yasa Abba cewa son meya kawoka nan k'uma?"
"murmushi yai h'ade da cewa Abba muje masallaci tuku kada mu rasa sallah.
"to kawai yace amma mmki ne ya isheshi.
"bayan su idar da sallan ne suka fito sallamaci Abba ya jasu gefe yake tambayar yadda aikai.
"Shamsudee ne ya f'adiwa Abba h'ade da cewa amma muma bamusan dalili.
"to shikenan kuzo muje.
"kai tsaye d'akinsa ya nufa'yana shiga ya dauki wayarsa ya kira Hjy" da sauri Hjy tazo a ladabce gaidashi' bayan su gama gaisawane yace Hjy meyasa kika hana son kwana a d'akin matarsa?"sbd wasu dalilaine da nakeso naji bancike akai.
"bincike k'uma?"
"Eh" bincike".
"ko zan'iya sani?"
"Eh" zansanar dakai koda ba yanzu ba amma Dan Allah kayi hkr a matsayinka na maigidana kadan ban lkc har na kammala.
"to shikenan babu damuwa' amma duk abinda zakiyi banaso ya dauki lkc Dan gudun kada mushiga hakkinsu.
"babu damuwa ko yau ne na kammala bincikena zai'iya shiga d'akin matar.
"shikenan amma Dan Allah banason yawan bincike sbd banason abinda zaije ya dawo.
"za'a kiyaye insha Allahu.
"k'uma Dan Allah ina niman izini".
"na mefa?"
"inaso zanje hospital nida Aisha.
"asibiti k'uma?"
"Eh"
"himm" Hjy manyan gari kenan"
"Allah ya tsaye".
"amin ngd".
"zahradee yana gama wanka ya shirya cikin captan orange colour yayi kyau matuka bayan ya gama shiryawa ne yashiga cikin g'ida'kai tsaye d'akin Abba yashiga da sallama cikin girmamawa ya gaidashi.
"my son kenan ango kaga yadda kai kyau kuwa".
"himm Abba na kenan".
"amma dae kashiga kaganemin kwana sarkuwata ko?".
"a'a" banje ba Abba".
"a'ahhh! mazan tashi kaje".
"to yace h'ade da mikewa"
"saida yabiya d'akin Hjy yabiya suka gaisa bayan su gaisa ne yautar su Hjy wacee bata wuce 25 years ba tace ango ango ina zuwa h'aka?"
"karaf yace Abba ne yace naje naga kwanta Aisha.
"wani irin dariya tai masa'' hade da cewa lalla zahradee har yanzu Akwai kuruciya a tare dakai.
"yayar Hjy dake gefe tace aike kinfishi kuruciya' a matsayinki na uwa kitsaya kina tsokanar d'anki.
"murmushi yai kawai ya fita' yana fita da sauri Hjy ta bishi h'ade da kiran sunasa.
"zahradee na tsayawa Hjy tace ban hanaka zuwa gun matarka ba amma wlh kada ka kuskura wani abu ya shiga tsakaninku.
"shiru yai be tanka ba"
"kana jina ko baka jina?"
"naji Hjy"
"to" k'uma idan kashiga kace tashirya zamu fita.
"to kawai yace".
"da sallama yashiga daedae lkcn tana fitowa daga wanka daga ita sae towel daure a kirjinta wanda bewuce gwiwa ba.
"tsayawa yai sakaka kamar dolo yana kallonta' da sauri ta d'au wani zani ta kara a jikinta' snn tace kariso mana' dan murmushi yai h'ade da shafe kansa alamar kunya.
"snn yazo ya zauna a bakin gado.
"Aisha tace ina kwana".
"lfy klau kintashi lfy"
"klau"
"dama na shigo na sanar dake ne Hjy tace kishrya zaku fita".
*"fita k'uma?"
"Eh*".
"to shikenan".
"mikewa yai ya dauki wayarsa da sauri yabar d'akin.
"Aisha nason mgn dashi amma gani yadda yakeyine kamar yana tsironta yasata kyaleshi kawai.
"Hjy na gamawa ta aiki Amatulraman ta kira Aisha ta fito su tafi.
'to tace hade da mikewa taje da sallama tashiga bayan sun gaisa tace Hjy tace kifito kutafi tana jiranki.
"batare da ta tankaba mayafi kawai ta dauka suka fita tare.
"tana fita ta hadu da Hjy dukawa tai har kasa ta gaida ta' da fara'arta ta amsa'bayan sun gama gaisawa ne Hjy tace muje.
"suna shiga Shamsudee ne ke drive suna cikin tafiya yace Hjy ina zamu?
"hospital".
"hospital k'uma?".
"Eh".
"A take gaban Aisha yai mummunar fadi' innalillahiwainnailaihiraju'un' kawai take fadi a zcyrta.
"shima kansa Shamsudee dake drive yashiga kokoto a zcyrsa.
"general hospital suka fara zuwa' suna shiga doct yace Hjy meke tafe daku?"
"doct yarinyata ce nakawo inaso ka gwadami ita kaf idan da wani lalura da take dauke dashi inaso nasani.
"Hjy zarginta kikeyi ne?"
"a'a ba zarginta nake ba".
"idan ba zargiba to menene' buduwarce ko tanada miji?"
"tanada miji amma sun rabu' k'uma zarginsa ake yana dauke da cutar HIV shiyasa na kawota a gwadata sbd nasan ta inda zanbulowa lamarin.
"Aisha dake zaune idanuta suka ciko da kwalla' a zcyrta tana cewa dama Ashe kallon da akemin kenan.
"doct yace gskya kinji dabara' bari a hadata da masu gwajin.
"tunda akaje da Aisha dakin gwajin habanta ke fadiwa' babu abinda takeyi sai salati a zcy.
"duk gwaje-gwajen da zasuyi suyi amma basuga komai ba' dauko result din sukai suka kawowa doct.
"yana budewa ya karanta snn ya sanarwa Hjy.
"Hjy bata nuna damuwa ba amsan result din tai hade da godiya.
'itako Aisha alhamdullh tai.
"a zcyr Hjy ko bata yarda ba.
"suna fina wani hospital suka tafi' nan ma duk dai result din iri dayane.
"a hospital na uku da suka jene garin bincike doct yagano Aisha nada matsala a mahaifa k'uma sanadiyar h'aka bazata haihuba.
"kuram baka kawai tai ta amshi result suka koma gida' suna isa dakin Aisha suka shiga tsayawa Hjy tai akan Aisha' ita k'uma Aisha ba duke gwiwa bibbiyu a gaban Hjy.
"mika mata result din tai tace karanta da kanki.
"jikin Aisha na rawa ta amsa ta bude tana karantawa tana kuka.
"dama kinsan da wani laluran ko baki sani ba?"
"nasani"
"harda shi zahradee?"
'a'a"
"meyasa kika boye masa?"
"kiyi hkr Hjy".
"kibani amsata".
"Dan Allah kiyi hkr".
"a fusace ta fisge result din hade da cewa almura mana fuka wlh nidake ne a gidan nan.
"Hjy na fita Aisha ta fadi a kasa ta fashe da kuka.
"da yamma bayan Alhj ya dawo daga kasuwa Hjy ta shiga suka gaisa'bayan su gaisa na ta dauki wayarta takira zahradee yazo dakin Alhj ya sameta.
'"tana kashe wayar tamikawa Abba result din' Abba yace na menene wann k'uma?.
"kaidai karanta gaka abinda yake ciki' budewa yai ya karanta' mmki ya kama alhj sosae" ke dama Hjy ta yaya akayi kikasan da wnn matsalar?"
"Hjy ta kwashe komai ta sanar masa' kan Alhj ya daure sbd betaba zaton h'aka ba.
"suna cikin mgn saega zahradee yai sallama ya shigo % ganisu da yai h'aka yasashi cewa lfy Abba?"
"Abba be'iya cewa komai ba mika masa result din yai.
"wnn na menene k'uma Abba?"
"shiru Abba yai".
"budewa yai ya fara karantawa' batare daya kareba yake what??????
"Aisha fa"
"kwarai da gske"
"zahradee"
"na'am" umma".
"bazan boye maka ba wlh banji dadin h'akan ba'amma yanzu ni bazance komai ba sai abinda kayanke".
"kamar yaya Hjy".
"ina nufi har yanzu kana sonta?"
"Eh"ina sonta".
"kana sonta fa kace".
"Eh"inaso"
"to shikenan' amma da sharadi.
"na mefa?"
"zaka kara aure...
"aure"k'uma?"
"Eh" aure".
"Abba!!!!! "a'a son ni banidana cewa' mgnrta gskya ne.
"Dan bazan boye makaba son har ga Allah inason gani jikokina' idan k'uma kaga shekarunka bekai na ije mata biyu ba to fa saedae ka saki Aisha..
"haba Abba meyakawo mgnr saki?"
"zabi yarage gareka son dan ni nagama shawara".
"to shikenan Abba na amince".
📖
☘☘
☘
AURE IBADA NE
FASAHA ONLINE WRITERS F. O.W.☘.
MMN USWAN
INAMA DAUKAKIN'YAR UWANA MISULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH ALLAH UBANGIJI YA MEMETA MANA AMEEN.
2⃣9⃣
"shikenan son Allah ya baku zaman lfy".
"amin"amma Abba...
"amma me?" banason ji komai tashi kaje kawai".
"mikewa yai batare daya sake cewa komai.
"bayan fitarsane Abba yace amma wlh Hjy Alhj Muhammad yaban mmki".
"name fa Alhj?".
*"Hjy kenan a iya sanina da Alhj Muhammad ban taba zaton zai buyemi wani Abu ba.
"Eh" abinda yasa bazai f'adi makaba kada ya sanar dakai kazo ka hana zahradee auren Aisha...
"haba Hjy kamar ba musulmi ba".
"h'aka ne mana".
"himm Allah ya'kyauta.
"amin" koma menene gashi musani Ai.
"da sallama zahradee ya shiga d'akin Aisha' duk da sallamar da yai besa ta amsa ba, sbd kikan da takeyi.
"a sanyaye ya karisa inda take zaune ya duka a gabanta h'ade da cewa h'aba Aisha kukan me kikeyi h'aka kamar wanda akaiwa mutuwa?".
"Dan Allah ki daena kukan nan h'aka".
"tamkar ba da'ita yakeyi ba".
"gani h'aka yasa zahradee mikewa h'ade da sa hannu ya dagota tsaye' dakar yasamu ta mike snn ya kamota zuwa bakin gado ta zauna' hannu yasa yana goge mata kwallar dake gangarowa a fuskanta.
"da zaran ya goge sai wasu su sake gangarowa gani batada niyar daina kukan yasashi jawota jikinshi ya rungumeta akan kirjishi.
"Aisha najin h'akan kwanciya tai a kirjin zahradee ko motsi batayi.
"a take zahradee yaji yanayinsa ya canza sbd sabon yanayin da yaji jikinsa.
"da sauri ya mike zuwa toilet yai wanka a nan cikin toilet din ya tsaya ya meda kayan jikinsa snn ya fito batare daya h'ada ido da Aisha ba wayarsa ya dauka da sauri yabar dakin.
""itako Aisha tana kwance kallonsa kawai takeyi h'ade da mmkin zahradee'a zcyrta tana cewa dama ashe h'aka ma'aurata sukejin fadi bansani sai yanzu kodai zahradee ne kawai yakeda irin wann ni'imar h'aka?".
"zahradee yana fita d'akin su Shamsudee yanufa yana shiga daidai lkcn Nurudee zaifita kasuwa sbd yau befita da wuri ba' gani zahradee a hanzarce yace lfy kuwa zahradee?".
"murmushi yai hade da cewa klau.
"kai kawai yasa yashige cikin dakin ya kwanta.
"juyi yakeyi kawai a kan katifa a zcyrsa k'uma yarasa yadda zai kwatanta irin dadin da yakeji a zcyrsa' wani bangare k'uma yana cewa ashe dama h'aka aure yakeda dadi bansaniba? ko dai Aisha ce kawai takeda dadi h'aka? kai idan ko Aisha ne gskya nayi dace.
"mikewa Aisha tai taje toilet ta tsaftace h'ade da alwala sakamakon kiraye-kirayen sallar da'akeyi.
"tana fitowa daga toilet Amatullah tashigo da abinci tace iji Hjy".
"to ngd"
"bayan ta'idar da sallah zama tai ta dibi abinci iya wanda zai'isheta ta barwa zahradee nasa.
"shiru2 Aisha bataga zahradee ya dawowa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 38