Share this page
umma ne yasata kashe wayar taje a guje. "Tun daga lokacin g'idan su zahradee suke ta shirye2 shima Alhj Kailani gani yanada wasu kudi a hannunsa yasashi tada gini gaba daya kawai' a cewarya gara ayi a huta gaba daya. "Ranar wata asabar su Aisha batada lecture tun safe umma tace zata aiki Aisha G.R.A. g'idan wata kawarta Hjy madina amso wasu kaya da tasata siyo mata idan taje DUBAI' Hjy madina tare suka tashi da hafsatu tun suna yara'shidama rayuwa ta gaji h'aka fini ubane na fiki miji' amma duk da h'aka akwai kyakykyawar alaka a tsakanisu. "Aisha ta amso sakon da ummanta tai mata' tafito kenan daga g'idan tana tafe sakamakon ba kasafai ake samu napep a street d'inba' h'akan yasata tafiya a kafa' har takusa fita daga street din kawai ji tai kamar daga sama aka janyo mata kyalen da tarufe kanta dashi. "A gigice ta juya dan gani waye yai mata irin wanga aikin. "Wani kyakykyawar mutune tagani tsaye a gabanta sanye cikin English wear blue jeans da white T.shirt yana yimata mirmushi' a sanyaye tace malam lfy? Me nai maka da zaka rikemin kyaleta. "Murmshi yai h'ade da cewa allahamdullh Allah Kaine abin godiya'gaskiya inada sa'a a rayuwata sbd duk inda naje cikin sa'a nake' yau gani a garin bauchi kuma da abin kaunata. "Yan'mata ya sunaki? K'uma wacce uguwa kike? "Shiru Aisha tai takasa mgn. "Au yan'mata tsorona kikeji? Kinga daga fuskanki kiga wani abu. "Kin dagawa tai. "Wlh idan baki daga na f'adi maki abinda zanfadiba da kaina zansa hannu na daga maki fuska da kaina. "Jin h'aka yasa Aisha tsorata' gashi area babu kowa daga ita saeshi na uku su shine Allah' k'uma yadda take ganisa tasan komai zai'iya. "Gani jikinta ya fara rawa'yashi kara daure fuskansa. "A hankali Aisha take dago fuskanta' shikuma dake tears zuba mata kwala kwalan idanusa yai' yana jira ta dago fuskanta. "Tana dagowa gani zasu h'ada ido da sauri ta dauke fuskanta daga nasa. "Wani irin dariya yai h'ade da tsalle yana kiran yan'mata ran gari' gaskiya kinada abin birgewa fa' wlh nayi sa'ar mata. "Idanu Aisha suka ciko da kwalla'a sanyaye tace Dan Allah kabarni natafi kada ummata taga na dade taimin f'ada. "Kai alhamdullh naji dadi da samo uwa ta gari irin ummata Allah ya kara mata tsawonrai da lfy mai amfani. "Shiru Aisha tai. "Bazakice amin ba. "Can karkashin murya tace amin. "Yace banji ba. "A lokacin ne tace amin a pili. "Yawwa ko kefa' h'aka kawai naiwa ummata addu'a k'uma kiki cewa amin? Yanzu f'adimin sunanki'kinji yan'mata. "Bakin Aisha na rawa tace ni banida da suna. "Juyawa tai zata tafi'da sauri ya fisgo jakar dake hannunta h'ade da cewa wlh idan baki f'adimin sunaki ba wlh babu inda zaki. "Aisha tajin h'aka tace ni sunana Amina. "Dariya yai snn yace daga gani wanga kyakykyawar bakin naki besaba da karya ba' shiyasa a yanxu ma da zakiyi karyan yake rawa. "Bazan tilassamaki ki f'adimin gaskiya ba' amma inaso kisan cewa nasan ba gaskiya kika f'adi ba. "Shiru Aisha tai tana mgn kasa kasa. "Gani yadda bakinta ke motsi yasashi cewa lahhhh! Zagina kikeyi ko? "DA sauri Aisha tace ni wlh ban zagekaba ko sa'ata bana zagi banle kai da girmanka'ni tun ina yar'karamata ummata ta hanani wasan zagi banle yanzu da nai girma. "Good kawai yace' gani yamma yayi yace bari nabarki kitafi g'idan kodan taya immata aikin abinci. "Amma kafin nabarki kitafi sae kin f'adimin uguwarku. "Gani idan ba karyan tasake yimasa ba ba zaibari ta tafi gida ba' matsewa tai tace gun central mosque g'idan mu na kallon masallacin ne. "Okay yace da saekin gani' k'uma ki gaidamin ummata. "To kawai tace a guje ta bar gun. "Gani yadda tasa gudu tabar gun yasashi dariya. "Kwanci tashi babu wiya su Aisha har ta kammala karatunta' yanzu da h'aka gun g'ida biyun shirye shirye kawai sukeyi an tsaeda rana 23 March sbd murna zahradee rasama yadda zaiyi yai. "Alhj Kailani ya gyarawa zahradee g'ida tsaf abin sae son barka komai na g'idan irin dayane da fyantin g'idan hatta furniture da labulaiyan g'idan iri daya ne. "Gun kawarta ubaida taji labari result dinsu ya fito yasata cewa itama zataje duba nata'bayan takare aiki tai wanka ta shirya zuwa school dinsu' Batare da bata lokaci ba taje ta duba'gani yadda G.P.dinta yai low yasa ranta baci. "H'aka tafito daga school din tana share kwalla'ji kawai tai ance ke yan'mata yau Allah yakaminke cikin sauki. "DA sauri Aisha ta juya'gani mutunmin ran nan ne yasata tsaki. "Durowa yai daga kan motar da yake zaune yasha gabanta. "Gani kwallane cike da idonta yace subbuhana lillahi lfy? Cikin muryan kuka Aisha tace yanzu sbd Allah duk irin kokarin danai wajan hana idona bcc nai karatu k'uma bama hakaba saeda nazo karke shine zasumin h'aka? "Mutumin yace me k'uma akai maki? "Aisha tace tunda nafara karatu bantaba samun carry over ba k'uma G.P. dina 3.1ne bayan ace yafi h'aka sbd Allah saeda nazo karewa shine zasuce yadawo 2.99 statement of result dina. "Wow! yau mean at shis your age kice kin gama diploma? Congrats" gaskiya nasarawa abbana. "Yan'mata be happy about your result, it's a good attempt. "A lokacin ne Aisha tad'anji dadi a zuciyarta' juyawa tai zata wuce batare da tace masa komai ba. "Ji kawai taji yace' Can I have few of your time pls. "Okay kawai itama tace. "Snn yaci gaba da cewa duk da nasan ba sunan ki ta gaskiya bane amma tunda ke kika bani bari nakiraki dashi h'aka. "Kunyane yakama Aisha'mayafin dake kanta ta rufe fuskanta dashi. "Yace Amina nagode sosae da wahalar da kika bani' amma abinda nakeso dake shine dan Allah kidaena karya sbd be kamaceki ba' k'uma nasan ba tarbiyar dasu abbana suka baki ba kenan. "Dan Allah kidaena sbd kada ki zubar masu da mutunci' kinsan idan yaro yai abu mara kyau akance daga g'ida yakoyo'nikuma nayi imani wann ba koyarwan su Abba da umma bane. "Jikin Aisha yai sanyi tace to kayi hakuri'in Allah ya yarda bazan karaba. "Murmushi yai snn yace to yanzu f'adimin inane uguwarku? Doruwa kana shiga uguwar hannu dama g'ida ta uku nan ne g'idan mu. "Allah yasa yau d'inma ba wata karyan aka zuba min ba. "Batare daya yatsaya tambayarta ba' ji kawai tai ya fisgo wayar dake hannunta yasa number sa anata yai plashing nasa' snn yai seving number sa a nata yasa Nasir Mai guduma' snn yamika mata wayar h'ade da cewa sae nazo. "To kawai tace snn tafara tafiya' tana tafe tana juyi tana kallonsa. "Gani zata f'adi yasashi cewa sarkin gudu yau ba gudun k'uma sae yayge yayge. "Jin mgnr da yaine yasa bata sake juyiba. "DA yamma bayan 5 PM saega Nasir a kofar gidan su Aisha ta waya yai kiranta' gani zata fita yasa umma tace Aisha Ina zaki? "Wlh umma wani mutum ne yake kirana' daga ina kuma yake Aisha? "Wlh umma nima bansanshi ba' kuma daga ganisa ba yaro bane. "To Allah ya kyauta jeki ki ganshi. To umma. "Tana fita kai tsaye gunsa ta nufa da sallama. "Cikin girmamawa ta gaidashi' shima da fara'arsa ya amsa. "Snn yace da farko dae sunana Nasir guduma Ina zaune a cikin garin argugune nida iyalina'matana biyu amma ban dade da kara na biyunba idan kin yarda inaso na kara dake ana uku'yan'mata idan har kika amince kika aureni'ni Nasir nayi maki alkaewari da tanajin jin dadi da kwanciyar hankali a gidana. "Kiyi hakuri sbd nasan a ciki zuciyarki zakice nacika dadin baki ko? Ko kuma kice natara mata bazaki samu kulawar daya dace ba a g'ida na ko? "Shiru Aisha tai takasa hada ido dashi. "Nasir yaci gaba da cewa wlh idan har kika yarda kika aureni wlh zanbaki kulawar da bazaki samu agun yaro ba' yan'mata kada kiganni h'aka kiyi tunani na girma wlh girman jikine kawai. "Amma bari banari naji ta bakinki ko. "Kan Aisha na kasa tace to naji amma Dan Allah kabani nan da jibi zanyi shawara. "To yanzu f'adimi sunanaki. "Murmushi tai snn tace Aisha. "Nice name' suna me dadi'. "Ni zantafi umma tace kada na dade. "Okay Dan Allah ki gaidamin dasu umma da Abba. "To zasuji ni nashige sae anjima. "Ngd Aisha'nan sukai sallama tashige gida'shima yatafi. ☘☘ ☘ AURE IBADA NE FASAHA ONLINE WRITERS F. O.W.☘. MMN USWAN 1⃣7⃣ "Aisha na shiga cikin g'ada'umma tace Aisha har kindawo? Eh umma nadawo' umma tace wayene yazo gunki d'in? Wani mutum ne umma' amma dae lfy ko? "Eh' kawai tace' da sauri takarisa cikin d'akinsu. "Itama umma gani yamma yayi idan tatsaya mgn zata iya makara' h'akan yasa taci gaba da aikin g'abanta bata sake bi takai Aisha ba. "Aisha na shiga d'akinsu daega kiran Nasir yashigo' koda ta daga wayar gani number Nasir yasa bata ta meda wayar ta'ije a gefe. "Duk da h'aka Nasir bedae na kiranba'gani yana niman tona mata asiri yasata sa wayar a silet yai ringing har yagaji bata daga ba. "Tana shirin mikewa kenan sbd kiraye kirayen sallar magrib da akeyi sae ga text message yashigo. "B'udewar da zatayi sako tagani kamar h'aka. "Allah ya huci ran gimbiyar tawa' da fatan ba nine na bata maki rai bako? To idan ma nine ga gwiwata bibbiyu a kasa ina niman tuba' a yafemin. "Duk da ba ganita yake ba'wani irin murmushi ta sakan ma wayar dake rike a hannunta. "Snn ta rubuta masa reply da cewa a'a babu wani kawai dan bana kusane yasa. "Snn tai sending text d'in. "Yana b'udewa'bayan yagama karantawa' alhamdullh kawai ya rubuta h'ade da saenazo jibi' snn ya tura mata. "Koda tai receiving text d'in tana gama karantawa ta'eje shi gefe. "DA yamma bayan sallar isha'i Aisha na zaune ita da Abdul kaninta suna hira saega kiran zahradee yashigo' gani number sane yasa Abdul sauri sa hannu zaidaga wayar. "Daure fuska Aisha tai snn tace kada ka dagamin waya. "Anty zahradee nefa. "Dan zahradee ne sae me? "Anty kenan' halan yau wanine ya bata maki rai? "Bazan dashi tai bata tanka masa ba. "DA h'aka zahradee sae da yai 5 miss call amma Aisha bata daga ba. "Har zahradee zai'ije wayar gani dare yayi banle yaje g'idan su aisha k'uma gashi bayajin bcc kawai sae ya h'au online d'an rage lokaci' yana h'au Aisha yagani k'uma da'alama tp takeyi. "Shima tura mata da hello. "Koda tagansa kin tanka masa tai. "Duk da h'aka besa zahradee yai fushi ba' h'aka yasake tura mata da sallama. "Karab hannunta ya d'anna gun sako daya tura mata. "Gani hello h'ade da sallama yasata hyyyy. "Zahradee yace my aisha Dan Allah kiyi hakuri na rashin zuwane kwana biyu wlh wasu aiyukane sukasha kaina shiyasa amma dan Allah kiyi hakuri'sbd nasan kiyi fushi dani na rashin zuwa kwana biyu ko. "A'a ba h'aka bane. "To menene my dear?. "Kawai dae banji dadi b'ane that is why. "Ayya my dear' I wish you quick recovery may Allah see you through, on ur healthy. "Ameen ngd tace. "tomorrow I'II cme nd check you to see hw you feel. "Aisha ta meda masa da reply da' known need of your coming I'm getting better. "Alhamdullh yace but still I'II come'bekamata ace bakida lfy banzo na dubaki ba' gobe in Allah yasa mukai zanzo. "Aisha na gani h'akan rufe data tan tai h'ade da kashe wayar gaba daya. "Koda zahradee yaji shiru bekawo komai a zuciyarsa ba sae tunanin ko caji ne ya'kare' h'akan yasashi s'auka ya kwanta. "Da safe misalin goma zahradee yaje g'idan su Aisha har ciki yashiga da sallamarsa' ummace ta amsa'h'ade da cewa waye? Zahradee yace nine zahradee' umma tace bimillah. "Snn zahradee ya karisa cikin g'idan' cikin girmamawa ya gaidata h'ade da tambayar me jibi. "Da mmki umma tace me jiki k'uma? Aina? "Zahradee yace Aisha mana. "Umma tace Aisha k'uma? Eh umma' itace tace maka batada lfy?" Shiru zahradee yai yai yana murmushi. "Kwadawa Aisha kira tai da cewa fito nan' dama itama a makale take a bayan kofa tana jin duk abinda sukeyi. "Sae tasa hijab snn tafito tace gani ni umma. "Umma tace dama bakida lfy ne shine bansani ba? Shiru tai h'ade da daure fuska' umma tace dakefa nakeyi Aisha. "Zahradee dake duke yace a'a umma kilan jikin be matsa mata bane shiyasa bata sanar dakuba' mikewa yai h'ade da cewa umma ni natafi. "Umma tace ka gaida iyayen naka. To kawai yace. "Yana gaba Aisha na baya suka fita waje' bayan sun fitane zahradee yace h'aba aisha meyasa kikeso dauko wasu dabi'u wadda bansanki dasu ba? Aisha tunda nake dake sama da shekara nawa bansanki da karyaba' amma gashi yanzu kinfara yi. "Aisha kodae akwai wani abune a zuciyarki? A'a' to f'adimin menene ke damuki? Idan yaso sae mutafi asibiti. "A'a kabari kawai nasamu sauki. "Aisha kodae wanine ya bata maki rai. "A'a". "Nine nai maki laifi? "A'a" "Su umma ne? "A'a" "To dan Allah idan ma nine kiyi hakuri' kinsan idan aiki yazo g'aban goshi yafi zafi' k'uma kinsan mundu zata aikata abin alkairi sae ka daure'sbd shedan zaiyi ta kawo nakasu akai. "Banlema kwana nawa yarage mu kasance tare na har abada. "Shiru kawai Aisha tai h'ade da daure fuska. "Gani yadda ta daure fuska yasa zahradee cewa h'aba duk cikin fushine h'aka da daure fuska? Gaskiya nidae a sakarmi fuska ko zanji dadi. "Yadda yake yimata yasata dariya. "Daedae kunnita yazo snn yace kokefa har kinyi kyau. "Murmushi kawai yakarayi masa. "Snn yace ina zuwa. "Mota yakoma yaje ya dauko wata karamar jaka yadawo snn ya mika mata h'ade da cewa gashi kiyi hakuri babu yawa. "To kawai tace. "Snn yasa hannu cikin aljihun rigarsa ya ciro kudi yace gashi wann na katine sbd nasan yanzu wanda nasa maki yakare ko? "Eh basu kare ba. "To babu damuwa ki rike ko zaki bukaci wani abu. "Shiru tai batare da tace nagode ba. "Zahradee yace ni zantafi Abba yana jirana mutafi kasuwa. "To tace'snn tace sae anjima' shigewa tai batare da tatsaya sunyi sallama ba. "Ido kawai zahradee ya zuba mata har tashige ko kibtawa beyiba. "Jikin zahradee yai sanyi sosae sbd ziciyarsa tana raya masa abubuwa kala-kala akan Aisha' can yaji gabansa yai mummunar faduwa. "Innalallahi'wainna'ilaihi'raju'un kawai yake ambata a bakin sa.. "Da kar ya'iya jan mota zuwa g'ida. "Yana isa Alhj Kailani yace son tuntuni nake jiranka k'uma kaje kai zamanka' ido kawai zahradee ya zuba masa' Alhj yace son lfy k'uwa na ganka h'aka? "Kai kawai ya kada h'ade da cewa banji dadi ne shiyasa. "Amma bayan fitarka ne ciwon ya sameka ka ko? Son kodae mutafi asibitine? Murmushin karfin h'ali zahradee yai h'ade da cewa a'a Abba nasamu sauki ai. "Shiga motar Alhj yai h'ade da cewa son jamu muje. "Zahradee yace Abba bazan iya ba' subhanallah Alhj yace snn yace son muje hospital kawai. "A'a" Abba kabari kawai idan muka isa kasuwa zankwanta' maybe idan nasamu hutu jikin zaisakeni. "Alhj yace to shikenan son Allah ya saukake. "Ameen Abba. "Koda sukaje kasuwa babu abinda zahradee yai a kwance yake. "Duk a lokacin gabansa be daena bugawa ba. "Aisha na shiga g'ida umma ta kirata zuwa tai inda umma take ta duka har kasa h'ade da cewa gani umma. "Umma tace Aisha inaso kisan da cewa idan kinji ana cewa babban mutum ba sae lalla wanda yakeda kudi ba' ko mai matsayi ko d'an siyasa ba'a'a babban mutum yana nufi mai mgn daya' nidae bance lalla inaso naji tsakaniki da zahradee ba'amma inaso kisan cewa in har kika bari wata matsala tafara kunno kai daga gunki ba kekadae abin zaishafafa harda mu' sbd mafi yawanci kafin afara zaginki mune za'a fara zaki. "Dan h'aka Aisha duk abinda zakiyi kada kibari mutuncinmu da darajanmu ya zuba. "Tunda umma tafara mgn babu abinda Aisha keyi sae kuka. "Umma taci gaba da cewa yanzu sbd Allah Aisha ace bakida lfy shine bazaki iya sanar manaba sae zahradee? Ba mmki shidinma karya kikai masa' amma k'uma Aisha bansanki da karyaba'Aisha ina kika koyo dabi'ar da bansanki da'ita? Yanzu sbd Allah h'aka zakije g'idan miji kina masa karya ko Aisha? "Kai kawai takada. "Nan umma tai ta mata f'ada h'ade da nasiha. "Da yamma Aisha taje g'idan ubaida kawarta wanda tarigata aure harda yaranta biyu' bayan sun gaisa ubaida tace amarsu ta ango wlh Aisha ba karami dace kikaiba. "Aisha tace na mefa? "Ubaida tace Aisha kenan kifi kowa sani irin soyayyar da Bbn su Abba ya nunamin amma bekai irin naki da zahradee ba' ki dubafa komai yasamu kece. "Uhm" kawai Aisha tace. "Ubaida tace yahh! Dae Aisha? Kodae akwai matsalane. "Aisha tace wlh ubaida kwata kwata naji banason zahradee ko ganisa ma banasonyi. "Dariya ubaida tai h'ade da cewa kawata kenan dadina dake akwai son tsokana. "Aisha tace wlh kuwa ubaida ba wasa nakeyi ba. "Ubaida tace Aisha kina h'auka ne? Kodae gamo kikayi?kinsan idan kikaiwa zahradee h'aka baki masa adalciba ko? Fasawa da kuka Aisha tai tana f'adin wlh ubaida bana sonsa kwata kwata. "Ubaida tace h'aba Aisha Allah yakusan rufa maki asiri shine kike niman tonawa kanki' idan kince baki sonsa ke a ganiki akwai wanda zai'iya biyan zahradee abinda yai maki? K'uma kinada wani da zaki fitarne?. "Aisha tace eh. A gigice ubaida tace lfyrki k'uwa kodae h'aukane kika fara. "Banza da'ita tai. "Gani babu wasa a idon Aisha yasa ubaida canxawa daga wasan da takeyi nan tafara tambayar Aisha" itako Aisha babu abinda ta boyewa ubaida. "A gigice ubaida tace Aisha kanki daya kuwa? Wani lokaci ma ka auri saurayi ya kakare dashi banle mai mata har biyu kije ana uku. "To wlh Aisha bari kiji kibar gani duk irin sonda nakewa Bbn su Abba lokacin da yazomin da mgnr zaikara aure har addu'a nakeyi idan nazo sallah Allah yasa yana fita mota tai ajallinsa akawomin gawarsa yafimi da nagansa da wata mace' shine zakije ki h'auko wa kanki dala ba gammu. "Aisha tace kekika sawa ranki shiyasa nidae babu abinda yadameni dasu tunda Ina sonsa. "Ni barima natafi sbd banga zansamu mafita a gunki ba. "Ubaida tace lalla kam. "Fita Aisha tai babu ko sallama. "Mmkin Aisha yakama ubaida sosae. "Da yamma saega Nasir yakirata ta wayarta' lokacin umma na parlour Abba h'aka yasa Aisha samu hanyar fita. "Da sallama ta'isa gusa' shima yana ganita da fara'arsa ya tareta cikin girmamawa ta gaidashi' shima ya amsa. "Bayan sun gama gaisawane yace Aisha nazo jin sakamako nane'ina fatan Allah ya amsami addu'ata. "Cikin jin kunya Aisha tace babu komai na amince. "Nasir yace alhamdullh Allah na gode maka. "To yanzu yaushe zanzo naga Abba? Idan gaskiya a shirye nake. "Shiru Aisha tai snn tace kabani kwana biyu. "Nasir yace to shikenan. "Aisha tace zanshige sae anjima. "Batare daya tankataba hannu yasa cikin aljihu ya dauko bandir d'in five five hundred naira note yamika mata. "Aisha tace a'a kabarshi kawai. "Nasir yace idan ba rainawa kikai ba to ki amsa. "Hannu biyu tasa ta amsa hade da godiya' snn sukai sallama. "Aisha na shiga daga lungu tsayawa tai ta boye boye kudin snn ta karisa daga ciki'kai tsaye d'akinsu ta shiga da sauri sbd umma batasan da fitataba dama. "Tana shiga d'akinsu kyakykyawar buya taima kudin snn tafito. "Da dare zahradee yaso zuwa gun Aisha amma yanayin yadda yakeji ya hanasa zuwa'sbd ji yake kamar kirjinsa zai b'ude sbd azaba. "D'akinsu ya shiga ya kwanta snn ya dauko wayarsa dama number Aisha yana dialled call ne kawai d'an nawa yai' a lokacin na kwance tana f'aman tunani ta'ina zata fara? Kawai taji wayarta yana ringing. "Koda ta duba taga number zahradee ne tsaki kawai tai h'ade da juyawa wayar baya. "Zahradee yai kira yakai sau'biyu amma Aisha bata daga ba. "Gani bata daga ba yasa ransa sake baci' zubawa wayar ido kawai yai yana kallonsa' can wata zuciya yace me zaihana karubuta mata text message ka tambayeta ko akwai wani laifin da kai mata k'uma tanajin kunyarka bazata iya f'adi maka ba. "Amma ta text tunda ba ganika takeyiba maybe ta'iya f'adi kama. "Mikewa zaune yai ya jingina da bango snn yafara da. **** ***** ***** Dear Aisha, The reason I write this letter to you I don't known what I did to you, If I call you, you did use to pick my cell, that is the reason I write this letter to ask you what I did to you? Pls tell me. **** ***** ***** "Snn yai sending d'insa. "Aisha najin shigowa text da sauri tadaga wayar' tana dagawa taga suna zahradee budewa tai ta karanta bayan ta kare tsaki tasakeyi snn tai hurgi da wayar. "Shiru shiru zahradee zaiga reply yaji shiru. "Sake rubuta mata yai yace Aisha I'm waiting for your reply. "Koda tasake karantawa kamar jiya'dan batada niyar meda masa da reply d'in' kawai bude data tai taci gaba da chat d'inta. "Shima da yaga tunani yana nima yimasa yawa hawa online yai' nan suka h'adu da Aisha. "Yace Aisha"shiru' Aisha'shiru. Bata tanka masa ba. "U don't want to telk to me ba? Himm Allah ya kyau. "A lokacin ne ta bude'gani sakonsa ta meda masa da cewa ba h'aka bane. "To menene?. "Kawai dae. "Kawai dae me?. "Look nifa ba yaro bane kada kinimi rainami hankali. "Idan kinsan da wani abu a zuciyar gara ki sanar dani. Aisha U don't care about me. "Haba zahradee' wani irin tunani kakeyi h'aka? "Aisha idan damuki nakeyi' Is better I should stop disturbing you. "H'aba zahradee meyasa kai a rayuwa bakayiwa mutum uzirine. "Babu wani uziri da zanmaki Aisha wlh akwai abinda kike kunlawa Aisha. "H'aba zahradee meyasa kace bandamu dakai ba zahradee... "Hakane mana Aisha' If you care about me let me see. Zahradee banida lokacin ka. "Iya kacin amsar da Aisha ta turawa zahradee kenan ta sauka' tana kashe data Nasir yana kira. "Sbd bugun da zcyr zahradee yakeyi mikewa yai yashiga toilet yai alwala yazo yafara nafila yanakai kukasan gun ubangiji. "Dan shine mekowa me komai me ikon yida hanawa. Allah yasa mudace' mufi karfin zcyr mu. "Zahradee yana sallah hawaye kawai suke kara kaina a fuskansa. 📖🖊 ☘☘ ☘ AURE IBADA NE FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.☘. MMN USWAN Zanyi amfani wann damar wajan mika godiya ta ga masu backing din na nagode sosae Allah yabar kauna da zuminci. Kada kudamu ba komai bane gazawane kesa ka ka dauki fasaha wani ka juya' idan har kasan kai perfect basai kayi amfani da hikimar wani. Dan haka ina rokon dan Allah duk meyi yabari pls👏 1⃣8⃣ "Bayan zahradee ya'idar da sallah yai tahhiya h'ade da sallama' snn ya dauko carbonsa yai subhanallalahi wabihamdihi, adadi khalkihi, wa rida nafsihi, wa maidada kalimatihi, wa zinati arshihi, guda 100. "Snn yai Subhanallai, walhahamdul lilla Allahu Akbar. sai salatin Annabi manzon (S.A.W.) guda 100. Snn ya karanta fatiha, Ayatul kursiyu, Amanar rasulu, Lakadja'akum. Snn ya daga hannayensa sama yana mai kaskantar da kansa da k'uma tawali'u ga Ubangijin rahma maijin kan bayijsa. "Duk a likacin hawaye basu daena zuwa daga i'donsa ba. "Yace Ya Allah ina mai tawassali da salatin manzon ka fiyayyen halitta Annabin rahma sallallahu alaihi wa sallam, tsira da aminci sukara tabbaba ga shugabanmu Annaba Muhammad (S.A.W.) da k'uma kyawawan sunayenka guda cassa'in da tara". H'aka zahradee yaita jero su tun daga Allahu har Assaburu. Snn yace " Ya Allah ubangijin sammai bakwai, ubangijin kowa da komai mamallaki mulki ga wanda yaso, kai ne kashen annabawa wanda bawani bayanka. "Allah kai ka halitceni ka halitfi Aisha, k'uma kai ka jarabceni da sonta ya Allah, Allah kafini sani abinda yake cikin zuciyarta Allah idan wani abu take shirin kunlawa a kaina ya Allah kada kabari ta cutar dani Allah, "Idan Aisha alkairine a gareni Allah ka mallakamin ita a matsayin matata, idan k'uma ba alkairi bace Allah kaimin zabi mafi alkari. "Ya Allah Kaine masani sirin dake boye' bansan abinda Aisha take nufi dani na' Allah kafi kowa sani yadda nakeji da Aisha a zcyta Allah, idan Aisha ba rabona bace Allah kada kabari sonta ya halakar dani har yakai ga sabamaka, Allah ka sanyamin sanyi a zcyta kamar yadda kasanyawa Annabi Ibrahim sanyi a lokacin da yake cikin wuta. "Allah kai nabarwa zabi kaimin zabi mafi alkairi a tsakanina da Aisha. "Bayan ya shafane ya dauki alkur'ani mai girma' ya b'ude Suratul Yasin ya karanta snn ya b'ude Suratul Rayman, da Waki'a snn ya rufe da Suratul Mulki. "Snn ya bude Suratul Ali- imran (Sura 3 Aya ta 59) INNA MATHALA "ISAA "INDALLAAAHI KA MATHALI ADAM (A') KHALAQAHU MIN TURAABIN THUMMA QAALA LAHU KUN FA YAKUUN(U). "Lalle ne misalin Isa a wurin Allah kamar misalin Adam ne, (Allah) ya halitta shi daga turbaya sa'annan kuma yace masa"Kasance" Sai ya kasance. "Yana da'kyau kowani musulmi yazama yasan wayanga SURORIN' badan komai ba kodan biyan bukatarka a gun ubangijinka. "Surorin suna cikin ( Suratul Ali-imran sura ta 3 aya ta 59) "( suratul mu'min' sura 40 aya ta 68) "Suratul yasin' sura ta 36 aya ta 82) Allah yasa mudace. "Yana shafewa wani irin sanyi yaji a zcyrsa' amm duk da h'aka bedae na ambato Allah a bakin sa ba' haka yaita tasbihi da f'adin Alhadumllah har 100' snn ya shafa yasamu gun ya kwanta. "Tun daga lokacin zahradee yaji sauki a zcyrsa' duk da saukin da yaji a zcyrsa amma da zaran zai kira Aisha sae yaji abin yadawo masa sabo a zcyrsa. "Duk kiran da zahradee zaiwa Aisha tana gani amma bazata daga ba har ya tsinke sai dae idan yagaji da kira dan kansa ya hakuri' h'aka k'uma koda sun h'adu a whApp zaiyi mgn har yagaji tana gani amma bazata tanka masa ba. "Shima tunda yaga walakancin yana niman yai yawa yasashi hakura da kiranta'kodan bacin ran da yake kamashi idan yakirata shiyasa ya hakura. "Duk

Chapter 8 of 38