saida yarane?"
"idan NA barsu kuka sukeyi"
"to suyi mana' idan suyi su gaji zasu bari' amma sbd Allah dan fitarwar da zakiyi gashi k'uma darene shine SAI kin fita dashi' to wlh kada ki karami h'aka"
"shiru Aisha tai bata tanka ba'
" zhrdee yana rungume da shahida ya koma mota yaje ya dauko dayan ledar yazo mata dashi ya baya h'ade da kudi "
"amsa kawai tai h'ade da ngd"
"snn yace kiyi hkr ban sanar dake akan lkc ba"..
" babu komai"
"jibi nakeso kukoma keda Zainab' abinda yasa bazaku koma gobe ba sbd feti nakeso a sake maku kinjiko"
"babu komai Allah ya kaimu"
"ni zantafi sbd sauri nakeyi' to shikenan' yanzu dai fara komawa dashi kiji kidawo"
"to kawai tace' daukar ledar tai tashige ciki ta'ije snn tasake fitowa' lkcn zhrdee ya koma mota' har mota ta bisa ta dauki shahida snn sukai sallama' sake fitowa yai ya rakata har ciki h'ade da rungumeta snn sukai sallama yatafi"
"wani irin dadine ya ziyarci zcyr Aisha' har zai shiga mota da sauri yasake dawowa h'ade da kwanda mata kira' tana juyowa yace kiyi hkr fa' idan Allah ya kaimu jibi Dan Allah kafin la'asar nakeso kudawo"
"to babu damuwa Allah ya kaimu' iji Aisha kenan"
"snn suka sake sallama yatafi"
"yana hanyane ya kira Zainab ya sanar mata da lkcn da yakeda bukatar tadawo' itama bata nuna damuwa ba"
"zhrdee' yana isa g'ida bangaren Hjy yashiga' bayan su gaisa take tambyarsa ina yatsaya da bedawo g'ida akan lkc ba"
"gidan su Zainab naje da Aisha' lfy?' eh lfy klau jibi zasu dawo dakinsu"
"alhamdllh naji dadi sosai Allah ya kara hkr' k'uma kaima Dan Allah akiyaye"
"insha Allahu Hjy"
~~~~ ~~~~ ~~~~
"bayan sati uku Alhj AMINU suna zaune da Hjy Mariya a lkcn yaso f'adi mata amma k'uma yarasa ta'ina zai bulo mata' k'uma gashi a gsky idan ba f'adi mata yai ba' in har yace zaibar Fatima taci gaba da zama a hotel Akwai cutarwa' tunda yanzu Mariya tafara ganosa shiyasa yanzu ta rike masa wuta kota ko'ina"
"h'akan yasa koda ranar da Fatima ne kada girki baya kwana idan yaje da safe zuwa 4PM yake barin g'idan ta sai k'uma gobe' gani haka zai iya jefasa cikin halaka da kuma gudun kure ita fatiman tunda bata nuna masa damuwa akan hakan ba' yasashi shima ya yanke shawarar sanarwa Mariya"
"bayan kwana biyu suna kwance da Mariya bayan sallar asuba yace Mariya"
"na'am Alhj"
"Dan Allah Akwai wata mgnr da nakeso f'adi maki amma besan yadda zaki dauki mgnr ba"
"Alhj kenan kada kaji komai kafadi kawai"
"himm Mariya kenan' kisan duk cikanke musulmi ansansa da rungumar kaddara me kyau ko akasin h'akan ko?"
"kwai da gske Alhj na shiyasa a kullum nake alfahari dake a matsayinka na megidana' ubangiji Allah ya barni dakai"
"murmushi kawai yai"
"Alhj bakace amin ba"
"kina jina Mariya"
"ina sauraranka tunda kaki cewa Aminci"
"Mariya kenan a nawa tunanin muriga mu wuce wnn guri kum' sbd yanzu muzama daya keda' amma tunda haka kikace to amin amin matata ta kaina Allah ya kara dankon kauna da soyayya ya kuma kara mana hkr da juna"
"amin me gidana na kaina Allah yabar min kai"
"amin"
"yanzu ina sauraranka Alhj"
"dama ba wani abu bane Mariya kin dai San tsawon shekaru da muka diba dake babu wanda ya taba jin mu dake to dan Allah ina rokonki a yanzu ma koda na f'adi maki banaso ki daga hankalinki wlh duk abinda zai shige cikin rayuwarmu ni AMINU nayi maki alkawari inash Allahu bazan taba juya baki baya ba' Allah kafin na f'adi maki koma menene Mariya inaso kiyi min alkawari"
"Alhj kenan ni wlh duk NA koda naji ko menene' amma alkawarin me kakeso nayi maka"
"Mariya kafin muyi aure dake shine besan waye keba amma tun bayan aurena dake a kullum nake daga hannanye sama nakewa ubangiji godiya daya azirtani dake'' wani abu da baki sanida Mariya a kullum idan nayi sallah saina daga hannu sama ina rokon ubangiji daya barmu tare har mutuwa' Mariya ina sonki kuma ina alfahari dake ba sbd komai ba sbd kyawawan halayenki wlh Mariya koda cikin a bokaina nake idan kowa yana fadin laluran gidan sa abin har mmki yake bani sbd ban taba samu haka dake ba' kuma nasan ba komai ne jawo haka ba sbd tarbiyan da kika samune daga gidan ku' shiyasa ka aure mace yar'babban g'ida ma yanada kyau" *_idan akace g'ida mafi yawanci al'umma sukan dauka kudine' basusan ba haka abinya yakeba' idan akace babban g'ida ana nufi gidan tarbiya' gidan da idan ka auri daya daga cikin zuru'ar g'ida bazakayi da kasani da aurensu ba' sbd tun farkon asalin gidan su Riga so dora jini gidansu akan turba me'kyau ne. amma yanzu ba haka bane duk Wanda yaji akace babban g'ida zakaji ana tambyar waye ubanta' ko k'uma YAR' gidan waye' ba'a dubi da tarbiya' nasaba' tsatstsasu gidan ta tafito, al'ummar yanzu idan suna niman aure basu duba irin wnn abubuwa, idan uban yarinya yanada kudi' tofa angama samu tarbiya a wnn gidan' tunda dama shine damuwarsu ba tarbiya ba. ya ubangiji Allah ka hure mana ta hanyar halas_* wlh shiyasa a kullum nake alfahari da aurenki h'ade da zabgawasu Alhj da Hjy addu'ar akan irin tarbiyan da suka baki "
"Mariya naji haka jikinta yai sanyi tace babu komai Alhj nayi maka alkawari insha Allahu koma wani irin maganane bazan taba nuna maka damuwa ko bacin rai akansaba"
"saida ya tashi ya jingina bayansa da gado snn yace Dan Allah Mariya kiyi hkr sbd nasan ban kyauta ba Dan kamata yai NA sanar dake kafin na aikata amma h'akan besamuba sakamakon yadda abu yazomi"
"Mariya najin haka zubawa AMINU ido tai jikinta har rawa yakeyi h'ade da son jin abinda zai f'adi mata' ita kanta batasan lkcn da hawaye suka wanke mata fuska ba"
"Alhj yace nasan za'ayi haka Mariya amma Dan Allah kiyi hkr' hkrin nan Dana sanki dasu inaso ki kara"
"cikin kuka tace dama kenan idan kace zaka gidan Nigeria ba nan kake zuwaba?"
"nan nake zuwa Mariya"
"ka Dade kenan da auren?' k'uma aina take?"
"a'a ban Dade da auren ba' idan bekai wata ba' k'uma muna tare da'ita anan London"
"batare data sake mgn ba mikewa tai tafita tabar masa d'akin' koda yake kwada mata kira besa ta tsaya ba' gani haka yasashi binta da sauri"
*_TO HAUSAWA SUCE KISHI KUMALLON MATA_*
~~~~ ~~~~ ~~~~
"zhrdee yana fadiwa Zainab lkcn da yakeso su koma ta sanarwa innarta' itama inna tunda taga an daidaita ta hadawa Zainab hadandun maguguna nasha Dana matsa take amfani dasu"
"yau ne ranar da zata koma gidan zhrdee' sbd ita keda girki yasatace Zainab ta shirya akan lkc' duk wani shirin da zatayi tayi ana sallar azahar inna ta sata gaba ta rakata' Zainab tai kuka kamar yaune farkon zamanta da zhrdee"
"suna isa saida tasake kaita gun Hjy sukai mata f'ada sosai snn suka koma bangaren su' itama inna takoma g'ida' gani yamma yayi yasa Zainab shiga kitchen tai abinci ta zubawa zhrdee nasa a kula ragowa kuma ta barsa a tukuya' tasake wanka tasha kwalliyarta takoma d'aki ta zauna sbd itadai tayi abincine kawai amma batasan me girki a cikinsu"
"Aisha bata dawoba sai bayan isha' sbd su tsaya jiran kanwar bbnta itace zata rakata' suna shiga gidan zhrdee shima ya shigowa' bece dasu kalaba yashige bangaren Hjy har saida masu rakota suka fita snn ya dawo bangarensa"
"a parlour ya zauna Zainab najin motsinsa ta fito ta kawo masa ruwa da abinci har zata zauna yace taje takira Aisha' tare suka fito da'ita Zainab ce tafara gaidasa snn Aisha itama ta gaishesa"
"zhrdee dake zaune yace to Allah ya kawomu Dan Allah ina rokonku da ku zauna lfy a tsakaniku zamane na gsky da amana nakeso muyi daku' dukkanmu a cikinmu babu wanda baya kuskure amma idan h'akan yafaru da ko waye Dan Allah kada kaji komai kafadiwa mutumi da yai kuskure sbd gyara"
"duk suna zaune sukace inash Allahu"
"abu na biyu k'uma bazan zauna daku baku gani iyayena da daraja da mutuncin ba' sbd duk wani mataki da zantaka a duniya sune sila Dan haka kuga albarkaci nakeci ba ni kadai ba harda ku' Dan haka duk meso zama dani dole tabi abinda nakeso' dokane naso idan kutashi da safe kafin kuyi aikin komai aje a gaidami iyayena' koni ban yarda a gaidaniba batare da angaida su Abba da Hjy ba"
"NA biyu kuma wlh wlh wlh koda da wasane naji wata taima wata gori a b'akin aurenta' koma jina ko"
"duk sukace eh"
"snn ya juyo kan Aisha' ke danace kudawo kafin la'asar meya zaunar dake har wnn lkcn?"
"su ummata ne tace natsaya inna Asiya tazo ta rakoni"
"yayi kyau' inna Asiya ko' yanzu abinda za'ayi kinga Zainab taji mgnta ta dawo a lkcn dana bata gashi k'uma harda abinci tayi kinga yanzu idan nakwana a dakinki banmata adalci ba' yanzu hkr zakiyi zuwa jibi' ke Zainab dauki abinci muje daga ciki"
"shiru Aisha tai' zhrdee yace tashi kije ki kwanta saida safe"
"to saida safe"
"mikewa tai tashige dakinta' Aisha na shiga ta rusa da kuka' sbd a nata tunanin yau a dakinta zhrdee zai kwana"""
📖✍
☘☘
☘
*AURE IBADA NE*
FASAHA ONLINE WRITES. F.O.W.☘.
🌳 *impacting valuable knowledge and entertainment is our concern* 🌳
*story written by Mmn uswan*
vote me on Facebook
gmail:hauwaszaria@gmail.com
*JIJINA*
*_A gaskiya banida kalaman da zanyi amfani dashi wajan nuna farin cikina a gareku' nagode nagode sosai ubangiji Allah ya kara girma da daukaka ya kara budi ya albarkaci mana zuri'a' ya shirya manasu shirin addinin musulci' yasa masu yiwa musulumci hidimane' ameen ya allahHAJIYA ZALIHAT YOLA (mmn ahamed) .HAJIYA HANNA. Abdulrahman Hafsat Hausa Nvl H2 and Muhammed Allah yabar kauna da zumuci amin_*
*_YAN'UWA RAKIN JIKI' IDAN AKWAI WANI KALMAR DAYAFI HAKAMA WLH KUNFI DA HAKA GARENI UBANGIJI ALLAH YABAR ZAMAN TARE' YA ALBARKACI RAYUWAR YA"YA"MU' YASA MASU JIN KANMUNE YA MASU YIWA UBANGIJI BIYAYYANE MUMA SUYI MANA BIYAYYA' YAKARA BUDAWA MAZAJANMU WAJAN NIMO MANA HALIS YA KARA MANA HAKURIN ZAMA DASU HAJIYA AMINAT KABEER KIRU. HAJIYA ZULAIT YOLA MMN AHAMED_*
*_~WRITES~_*
*_manya magani kananu' jagaba kun riga kunyi gaba' saidai ta Allah amma bata mutum bakiba' sama da ikon Allah' hasken garin wata sha kallo tautari tsaya gaban makiyinku_*
*UP*
❤ *UP UP* ❤
*UP*
*_~DA ALBARKAN ME MANA RUWA DA ISKA~_*
*RAHMA RUFA'I NALELE*
*BATUL ADAM JATAU*
*AMINAT KABEER KIRU*
*REAL DANBU CE (MMN WALEED)*
*SAFIYA MUSA A HUKUMA*
*ZAINAB IBRAHIM (MAHABEE)*
*CIKI DA GASKIYA*
*ANTY RUKKY(MMN ABDUL JALAL)*
*UMMUSULEMAN*
*MARYAM L.I. GITAL*
*ZAINAB MAKAWA*
*FASMA NIGER*
*HALEEMA AUWAL*
*HALIERMIER AMEEN*
*ZAINAB SHU'AIBU*
*KING BOY*
*_jijina gareku masoya na' hakika kun cika cukankun masoya na gaskiya shiyasa a kullum nake alfahari daku a duk inda kuke' ubangiji Allah yabar kauna da zumuci. amin_*
*_especially my momcy Aisha magaji taki da ban ne uwata ta kaina ina yinki wlh Allah yabar kauna da zumuci_*
*THE*
🔚
6⃣5⃣
"suna shiga d'akin gani Abba kwance kusa da Islaha zhrdee yace a'a Abba har bcc ne?"
"eh' ina gama masa wanka yai bcc"
"bari na kaisa d'akin Hjy ya tayata hira' hannu yasa ya daukesa zuwa dakin Hjyn da sallama ya shiga' tana amsawa yace ga Abbana yazo tayaki hira"
"murmushi kawai tai masa' snn ya shinfidashi sukai sallama yakoma dakin Zainab' ko kafin ya koma tun tashiga badroom ta h'ada masa ruwan wanka snn tafito"
"yana dawowa zama yai yaci abinci snn ya mike ya tube' yana tubewa Zainab tana ninke kaya saida ya kare snn ta h'ada kayan ta zuba a wardrobe shikuma ya shiga wanka' yana fitawa suka kwanta....
" yau ko masallaci zhrdee bejeba a g'ida yai sallarsa shida Zainab suna idarwa suka sake Zainab ta mike har takai b'akin kofa' zhrdee yace Zainab ina zaki? "
"zanje na gaida Hjy ne"
"OK amma kada ki Zainab kidawo yanzu ki h'ada mi tea"
"to kawai tace snn ta fice daga d'akin' mikewa yai yakoma ya kwanta yana jiranta"
"gani bata dawowa da sauri ba yasashi mikewa zuwa dakin Aisha' yana shiga ganita yai tana zaune kan sallaya' itama tana gani yashigo tai sauri ta shafe addu'arta dama tariga ta kare' mikewa tai h'ade da gaidashi ina kwana"
"lfy klau' kutashi lfy?"
"lfy klau"
"Aisha na mikewa ta haye gado ta kwanta kusa da yaranta' gani haka yasa zhrdee cewa tashi kije ki gaidasu Hjy snn kidawo ki kwanta"
"batare da musuba ta mike ta fita zuwa bangaren su Hjy' yana zaune yana jiranta har saida tadawo snn shima ya mike yafita ya koma dakin Zainab' yana shiga yaga har tadawo rike da tea a hannu' karisawa yai h'ade da tambyar dalilin dadewarta"
"koda naje be sameta a dakinta bane tana d'aki Abba har najuya zanfita sai gata ta shigo to kawai yace h'ade da amsar tea d'in yasha"
"a zcyrsa yana f'adi Ashe kenan Aisha bata tsaya su gaisa da Hjy ba tadawo?"
"yanasha yasake kwanciya' duk yadda Zainab taso daurewa amma saida zhrdee ya kureta har yakai ga ta nuna gazawarta snn ya barta ta huta' yau kam zhrdee be fita kasuwa ba sai around 12PM snn yaje kasuwa"
"bayan kwana biyu Aisha ta amshi girki' dayake tasan yafi son towun masara da miyar kuka ko kubewa yasa tai masa' koda zhrdee ya gani yaci sosai yana gamawa ta kwashe kayan ta meda su kitchen yana gamawa wanka yashiga' suna kwancene zhrdee yace aishata"
"tana makale a jikinsa tace na'am zhrdee dina"
"Dan Allah Akwai wata mgnr da nakeso na f'adi maki amma Dan Allah banaso haka ya tada maki da hankali' da banyi niyar fadiba amma gani nayi barin kashi a ciki yaba magani yuwa k'uma ya kamata ace kinsani tun a lkcn to dayake Akwai Dan abubuwan da suka shiga shiyasa"
"ido Aisha ta zuba masa tana kallonsa"
"zhrdee yace amma kiyi hkr k'uma insha Allahu h'akan bazan sake faruwa ba' shiru yai yana jijina lamarin snn k'uma yace akwan sati daya daya shiga tsakaninmu.....
" a gigice Aisha ta fisge jikinta daga nasa tasa kuka'tana salati h'ade da nashiga uku"
"kamota zhrdee yasakeyi ya jawota jikinsa yana bata hkr' cikin kukan Aisha take tambyer saki nawa yai mata' dayane kawai' k'uma in Allah ya yarda h'akan bazan sake faruwa ba' a lkcn Aisha taso tambya ita kadane h'akan yafaru da'ita ko harda Zainab' amma gudun kada ta kunna wa kanta wani wutar da bazata iya kashewa ba yasa tabar tambyar"
"tayi kukan har tagaji' shima zhrdee be bantaba har saida yaga ta daina kukan ta hkr"
"tun daga lkcn taka tsantsan takeyi a zamansu' yanzu kam alhamdllh domin zhrdee yana iya kokarinsa wajan gani yamasu adalci a tsakanisu' shiyasa suma yanzu komai nasu tare sukeyi babu mejin tsakanisu' duk da dama Zainab bame damuwa dace sbd ta dashi taga gidansu da kishiya' shiyasa koda taga wani abu yazo mata yakan zama ba sabon abune a guntaba' aishane ma take nuna damuwarta akai' sbd yanzu idan iskanci zhrdee ya tashi dukkansu yake masu' Aisha ce kecewa zata masa mgn' Zainab ke hanata ranar a d'aki suke niyi' shima sbd yariga ya saba da f'ada ko kasuwa baya fita akan lkc yana zaune a parlour niyi yakeyi yana masifa ko yaran dake g'idan susan da zamansa"
"tuda kida ya canza dole rawa shima ya canza' kuma inda zhrdee ya godewa Allah matarsa duk suna shakkansa gashi dai karami ruwa ne dashi amma tsiyarsa yafi na babban. *_shiyasa hausawa ke karin Hausa da fankan fanka bata kilishi' wani lkc azabar karami mutum har yafi na babba' snd daga aisha har zainab suna shakkansa koda mgn ne suna shakkan meda masa' babu duka balle zagi' sbd tun bayan dawowarsu yadaina dukan su amma ido kawai ya ishesu sunan abinda yake nufi. kuma ba komai ya jawo masa haka ba sbd zhrdee ya tsare gidansa raina biyar babu wacce zatace ta kara masa a cefane gidansa' duk da dai d'an adam tara yake be cika goma ba' amma yana Iya kokarinsa wajan gani ya kyautatawa iyalinsa' hakama iyayensa. Shiyasa yanada kyau namiji ya tsare hakkin da Allah ya dora masa' rashin h'akan kuwa shikesa aita samu matsaloli a zaman takewar auratayya ga rashin gani girmansa sbd duk hakkin da Allah ya dora masane ya kasar maka. Allah datta damu masu irin halinma ubangiji Allah ka ganar dasu, ameen ya Allah_*
~~~~ ~~~~ ~~~~
tun daga ranar da Alhj AMINU ya sanarwa Mariya mgnr aurensa bata sake kulawa ba' koda mgn yai mata tanka masa har tsawon kwana biyu"
"gani h'akan ba shine mafita a garetaba tun aikin gama yariga ya gama' aurene dai yariga yai' kuma koda beriga yayi ba ban isa na hanasa ba' idan ma nace zan hanasa badai zarginsa nakeyi amma kada wajan kokarin hanasa yasashi yaje ya f'adawa halaka yakoma niman matan bazan' kaga garin niman gira na rasa ido kenan' k'uma bansan matsayinta a zcyrsa ba"
"ballema me afkuwa ya riga ya afku wata kilanma tana nan da ciki tunda da alama auren ya dade' amma koma menene daurewa zanyi na kuma rumgumi aure h'ade da kwantar da hankalina na rungumi mijina' sbd idan har na daga hankalina nasan karsheta dai shine ya mikami jan takarda' tunda Alhj ba meso damuwa bane.
"idan kuma na kuresa nasan karshanta ya sakeni' idan har kan ya kasance yaya zanyi da yarana haka kawai wata Wanda bansan irin tarbiyanta ba tazo ta rusami nawa tarbiyan da naiwa yara' gara kawai nayi hkr na sanyaya zcyta' ta hahakane ma zanji komai akan auren amma idan na tada hankali babu abinda zanji sbd abinda hkr be bakaba rashinsa bazai bakaba.
" mikewa tai ta bisa hat d'aki inda yake kwance daidai lkcn idonsa biyu da sallama tashiga har kan gadon tabisa ta zauna h'ade da cewa Alhj har katashi daga bcc ne? "
"cikin taushin murya take masa mgn"
"Alhj AMINU dake kwance mmki Mariya ne kawai ya kamashi' duk da yasa tun da Allah yasa ya aureta wani abu makamancin haka betaba hadasu ba' tun suna Nigeria abokansa har mmkin irin zamansu sukeyi' shiyasa koda tai masa haka yai mata uziri sbd yasan ba laifinta bane harda kishi h'ade kuma da jin zafin auren da yai batare daya sanar da'ita ba' kuma ba itaba kowaye dole zaiji haushin h'akan"
"shiru da yai yasa Mariya cewa lfy Alhj tunanin me kakeyi haka?"
"lfy klau Mariya' yaya dai?"
"babu komai' ido kawai ya zuwa mata yana kallonta' gani irin kallon da yake matane yasata cewa h'aba Alhj wnn irin kallo h'aka?
" himm Alhj kenan' kace kai aure kuma matar tana nan amma bantaba ji koda da wasa neba kace zaka gunta';kodai dama wasane kakemi?"
"h'aba Mariya tunda nake dake nataba f'adi maki h'aka?"
"a'a haka taba ba"
"to amma meyasa baka zuwa kwana a gunta' kake kwana anan' baka tsoron Allah ya kamaka da laifin h'akan?"
'shiru yai kamar bazai bata amsaba can k'uma yace kae AMINU bari kwai na f'adi mata koma menene hausawa suce ranar wanka ba'a biyan cibi' ina zuwa mana"
"kamar yaya bangane ba' sbd tunda nake dakai koda da wasa bantaba ji kace zakaba' amma yanzu k'uma kace kana zuwa"
"tun Mariya tana dabarane Dan bugun cikin Alhj AMINU"
"shima daya gano haka yasa yake kokarin wayance mata"
"Alhj da kaefa nakeyi"
"nima tunanin da nakeyi kenan"
"shiyasa sbd tsoron kada Allah ya kamani da laifin h'aka'
" yanzu tunda ka aureta babu wani alaka daya shiga tsakaniku' gaskiya baka kyauta ba"
"da gefen ido ya kalli Mariya h'ade da cewa uhmm"
"yanzu a aina take?"
"yawwa ko kefa abin son ji kenan"
"ehhh' tooo' tana gidan yan'uwanta"
"h'aba Alhj sbd Allah tsawon wata daya mutum yai aure amma k'uma tana gidan yan'uwanta' gsky haka beyiba' idan har ka amince yau din nan zata tare anan g'idan"
"ehhh' too' way dah haya naso kama mata"
"h'aba Alhj hayafa kece duk dakunan dake gidan nan' a'a wlh babu komai tazo mu zauna tare';menene duniyar' menene a ido idan ba ruwa ba?
" Mariya tai hakane sbd bataso Alhj AMINU ya rabasu' tafiso su zauna gu daya sbd duk abinda zasuyi ayi akan idonta' daga gani yadda yakeyi da ido da alama Akwai wani abinda yake boye mata' amma idan ta tare anan Ai karyansa yakare idan ma satar jiki yakeyi yana zuwa gunta to tazo karke"
"yanzu bari naje na h'ada masu kausar da halif kayansu gu daya' idan yaso SAI amaryan naka ta zauna a daki dayan ko yaya kagani?"
"eh to babu damuwa' amma da kinbari kawai na kama mata haya"
"a'a wlh kabari kawai wnn ma ya'ishemu mu zauna' kudin da zaka kama mata haya ya'isa ka kara mana wann abu a g'ida' tunda abu da yawa"
"baridai naje na gyara daki idan yaso da yamma saimuje na dauko amaryata ko...
" da sauri Alhj AMINU yace a'a kibari kawai basai kinjeba"
"h'aba Alhj...
" nace dake a'a ko ban'isa bane"
"daga abin arziki' tunda bakaso shikenan' fita tai zuwa dakinta h'ade da juyayin lamarin mijinta anya kuwa babu abinda yake boye mata?"
"tana fita taje yasawa kofa key snn ya kira Fatima' bayan su gaisa yace da ita ta h'ada kayanta anjima zaizo ya dauketa tadawo gidansa da zama"
"Fatima tai murna dajin haka sbd itama ta gaji da zaman hotel d'in da takeyi kamar wata karuwa ko Mara gata' ita kenan saidai idan yazo ya biya bukatarsa ya tafi ya barta bazai kara zuwaba SAI wani ya ka masa' amma yanzu ne zatasan tai aure' mikewa tai tashiga h'ada kayanta dama ba wasu kayane masu yawa tazo dashiba tunda tasan yadda zaman London din yake"
"Mariya na kare tunaninta ta mike taje ta kwashe kayan ta hadasu daki daya snn ta share ta kankabe' yamma nayi Alhj yaje ya dauko Fatima suka dawo g'ida Mariya dake zaune a parlour tana zaman jiransu jin sallamarsu saida gabanta yai mummunar f'adi' injalillahiwainnailaihijlraju' kawai take f'adi a zcyrta"
"duk da haka a lkcn ta dane zcyrta tai masu kyakykyawar karba harda abinci ta kawo masu' duk da Alhj yaso mgn a lkcn amma hanasa Mariya tai tace in Allah yai dare gari zaiwaye' dan haka suje su kwanta idan yaso da safe sai suyi mgnr da zasuyi"
"haka suka mike yana rike da jakarta suka shige cikin d'akin' itama tashi tai taje nata d'akin' tana shiga ta rusa da kuka' Mariya tayi kuka sosai saidai bcc barawo da yazo ya dauketa"
"tunda Alhj suka kwanta babu abinda ya shiga tsakanisu da Fatima' sbd gani yake kamar idan ya kwana da'ita ba nata bane hakkin Mariya' Dan tunda aikai aure yake kwanciya da'ita saidai idan lkcn da yaje tana period ne' gani k'uma babu halin fadiwa Mariya h'akan sbd yace mata be taba kwana da Fatima ba' yanzu idan yafafi yai zama masa matsala' shiyasa kawai zai kwana a dakin Fatima"
"da safe kuwa Mariya ta h'ada masu abin breakfast ta kai dinning table snn taje ta sanar da Alhj ta waya suka fito harda ita suka hadu suka karya' a lkcn ne Fatima ta kare mata kallo taga ba komai bane Mariya sbd ta zauna da kishiyoyin da suka fita komai k'uma su buga da'ita su bari balle ita"
"bayan su gamane Alhj yai gyara murya snn yace Mariya ga Fatima' Fatima kenan ga Mariya' idan bakusan juna ba yanzu ne zakusan juna k'uma kusan halayyar junanku' nasan dai duk a cikinku babu yaro duk kusan ciwon kanka to Dan Allah ina rokonku da Ku zauna lfy da junarku' idan laifin daya taima daya zaifi dacewa da kusabarwa junarku d'an samu warware matsalar ba karike mutum a raiba' dan Allah"
"duk suka h'ada baki da insha Allahu"
"Fatima dake zaune tace ina yaran gidan ne?"
"Mariya tace duk su tafi sch"
"yawwa Mariya kiyi hkr na mance ban sanar dake ba' itama Fatima tana da yara biyu Khadijat da Jabeer"
"Allah sarki' ina suke?' ko kinbarsu a gun bbnsu ne"
"a'a ai rasuwa yai?..
"Allahu Akbar' ubangiji Allah ya jikinsa da Rahma"
"amin Mariya"
"Alhj da kabari ta taho dasu kasan d'an sai uwarsa balle mawuyacin lkcn ga da muke ciki' duk da bangansu ba amma wlh har naji tausayinsu"
"himm Mariya kenan' ai nima ba laifina bane' babu yadda banyi da'ita akan tazo dasuba amma taki' amma tunda hakane duk lkcn danaje g'ida tare zamu dawo dasu"
"gsky kam da yafi' ai rike maraya ba karami lada bane' SAI kaga sanadiyar haka Allah ya kara buda maka"
"kan Fatima na kasa tace ngd sosai"
"tun daga lkcn Alhj
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 38