An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
1锔忊儯
_
_*Darasinmu na yau, hadisin da ke da ala'ka da hali 01 cikin 46.*_
掳
掳
_*Manzon Allaah(锓 )* *ya ce:{WANDA MUSULUNCIN SU YAFI KYAU DAGA CIKINKU SUNE WA'DANDA SUKA FIKU KYAWUN HALAYE, IN SUN FAHIMCI ADDINI.}*
```[Sahihul Adab;285]```
_Wannan hadisin yana nuna mana cewa a cikin musulmi, wanda halinsa yafi kyau to shine kuma musuluncinsa yafi kyau. Ai kyawun hali shine mutum, shine dottaku. Allaah Ya azurta mu da halaye masu kyau. Allaahu aalam. )
A hankali ta lumshe idannuwanta cike da wani irin mad'aukakin shauk'i, leb'unnanta ta d'an cije sai kuma ta bud'e tana kallonsa a sanyaye cike da wata irin k'aunar jar rigar dake jikinsa mai had'e da wani shar shar sai rawanin da gaba d'aya ya rufe masa gaban goshinsa.
Cike da shauk'i tace "Dogarina, ina sonka, ina sonka kamar na mutu, ka ganni a nan tsabar k'aunarka ya sakani a kullum sai na je wajen hanyar ficewarka, sai nai ta ganninku ku dayawa kuna wucewa ashe dai kai d'in har an d'aura mana aure oh dad'i kasheni."
Wata murya marar dad'i ya bud'a yace " Ke yi min shiru, ni bana son hayaniya ni nan da kika ganni sai dogariya nake iya so dan haka ki min shiru."
Hannayenta ne ta had'e cike da tsoron ganin suturar jikin nasa na son komawa irin ta mutane sak sak ta had'e hannayen da kyau tana girgiza kai cike da hawaye take fad'in " A'a, a'a kar ka b'ace, kar ka saka irin kayan al'umma sak mutuwa zan yi idan baka zo min a mutun ba na ganka gani gaka kar kar ka min haka dan Allah!"
Marin da aka kwad'awa fuskarta ne ya sakata bud'a nanauyan idannuwanta da suka gama rinewa suka gama macewa suka tafi duniyar mafarki, a firgice take kallon mutanen da suka zagayeta kafin ta ringa jin dariarsu sama sama sunna yi da dan karfinsu
A birkice ta kuma zuba masu ido kafin ta kai dubanta kan hannayenta dake rawa ta kara jimke su da wani irin karfi a bayane ta sauke wata irin nanauyar ajiyar zuciya kafin ta ji muryar kawarta na fadin " Sai ki tashi mu tafi, an tashi fa kina barcin asara"
Da sauri ta kuma kai dubanta kan allon rubutun kafin ta mike tsaye daga bajewar da ta yi tana duba jikinta cike da tsoron kar a je ta kwala fitsari sakamakon marin da ta sha, ita bama wannan ba shin kawarta ce ta kwada mata shi ko waye?
Da sauri ta suri jakarta ta juya ta bi bayan kawar tata tana kara hararar du wanda suka yi ido hudu da shi har suka fito tsakiyar titi sosai
Ba wada ta yiwa yar uwarta magana sai cen kamar an tukota ta nisa ta ce" Abin da mamaki, yadda kika san a gaskene haka na ganshi kai jama'a ko dai mahaukaciya ce ni?"
Juyowa kawar tata ta yi da dan bacin rai ta ce" Ai in dai a da ke ba mahaukaciya bace a yanzu zaki ja a maki irin mugun kallon nan, haba dan Allah kin ga yadda kike makyarkyata kina magiyar kina sonsa? Kina son waye ne? Ke haka zaki yi ta yin abin nan?"
Tsayawa ta yi jikinta ya yi mugun sanyi muryarta a sanyaye ta ce" Ko dai na haukace din ban sani ba?,
Juyowa Amina ta yi tana kallonta, irin yadda idannuwan nan nata masu kwayar ciki mai blue mai duhu da dan baki tsakiyarsu suka tara ruwa suke wul wul da su ta tabe baki kafin ta cije bakin nata ta kara fara tafia
Da sauri ta kamo hannunta a sanyaye ta ce" Amina, dan Allah ki fada min ko dai alamu ne na ciwon hauka ya kama ni? AMINa ni ko dan aiken gidan sarki ne a aura kin ina so, da na tsaya a dogari dan na ga a duniya idan kana son gannin wanda ya fi kusanci da sarki to dogari ne, dogari fa shi ke gyarawa Sarki zama a saman doki, ya gyara masa babar rigarsa ya saka masa lema ya rikw masa, a duniya sirrin sarki sirrin dogari an ce fa har bayi yake raka sarki, idan Allah ya amshi adu'ata da na jima ina yi na kasancewata yar uwar sarki ya bani dogari na aura ai na gama zama dangin sarki"
Galala Amina ta yi tana kallonta kafin ta janye hannunta da sauri ta ce" Walahi ki nutsu , kulun ina fada maki ki fa nutsu, ba dai sirrin sarki ba shine matar sarkinma! Wannan abin na tabata baki da lafia a kan maganar sarauta ke kam a nan kika kare, a duniyar nan du labarin wata masarauta a tafin hannunki take, idan ana history na sarakai har lumshe ido kike , kai ina kwakwaluwar nan taki da sake walahi!"
Kanta ta ringa gyadawa kafin ta tabe lebenta na kasa ta juya kwayar idannuwanta da yannayi na dan fada fada irin ta ji haushin nan ta ce" Sai me? Inace ke a duniya dan wake ko a gaban waye akai maki tayi zaki ci? To kowa da irin jarabawar da Allah ya dora masa, ni tawa ta dogari ce idan ana budar kaini dakinsa ki fadi ki mutu don Allah!"
Itama bakin ta tabe kowace ta juya cike da bacin rai ta kama gabanta
Jira nake na ga ta nufi wani lalatacen gida duba da yannayin suturar jikinta, jira nake na ga ta shiga wani gidan namu na yaku bayi duba daga makarantar da ta fito, sai dai wani rantsatsen gida mai shegen kyau ta kutsa kanta kai tsaye ba tare da shayin mai gadin dake zaune yana busar tabar sigarinsa ba, shi din kansa sai na ga bai wani yi yinkuri na dakatar da ita daga kokarin shiga gidan da yake ba nasu ba wanda ga dukan alamu aikota aka yi
Kai tsaye ta zagaya ta gefen da yake kamar madafa ne , mace biyu ta wuce sunna zazaune sunna cin abinci ko ci kanku basu yiwa junna ba har ta karasa madafar nan ta shiga da sauri ta shiga bubuda kwanikan da ta tabata a nan ake saka mata nata kason abincin da sam mutun ba zai yi tunanin a gida irin wannan ana rabon abinci irin haka ba
Gannin wayam babu ya sakata fitowa rai bace ta kare masu kallo kafin ta girgiza kanta ta koma cen hanyar shigar ta buda tankameman falon da yake falonsu ne
Ja ta yi ta tsaya tana karewa falon kallo bata san lokacin da ta saki jakarta ta makaranta a nan ba ta janyo wani ashar ta dire tana kallon falon ta ce" Kai uban kowa ya fito daga wajen da ya shiga ya labe yau a yita ta kare a gidan nan"
Ba wai maganar a fito din ba, ko wa'inda ke zaune wani shashakai suka kaleta suka juyar da kansu
Kanwarta ce ta zo wucewa da roba a hannunta ta ce" Ke kauce zan shige"
Hannunta ta saka ta janyota kiiii baya ta yada sai da ta yi tangal tangal kafin ta juyo da yannayi na tashin balagar rashin kunya ta buda baki zata yi magana maganar ta makale mata sakamakon shako wuyanta da ta yi tana firfito mata idannuwa ta ce" Ke yaushe na zama sharar da zaki bangajeni ki nemi wucewa ko tunani kike kin fara tara mazaunan da suka kai nawa da zasu iya bangaji a bakin hanya? Bama wannan ba uban wa ya bata falon nan da na tashi tunda safe na share dan na ji dadin zama idan na dawo?"
Muryar maman wace aka shake din ce ta fito tana zarro ido cike da mamaki tana tafa hannu ta ce" Ke ke ya haka, yaya zaki kama min y'a ki makure haka salon ki saka fatar jikinta ta yi birdi bayan yar ja ce ba bak'a ba?"
Da yannayin jin haushi ta hankadata tana kallon kishiyar maman nasu da kuma kanwar tata dake gudu tana ihun sai ta halakata tana neman mabugi ta ja wani uban tsaki ta ce" Dan Allah mama kin ga ni ba wannan ne ya tsayar da ni ba, idan kin tuna tun da safe na gyara dakin nan aman shine dan rashin tarbiya yaren nan suka lalata kuma ba zan san waye ba dan na hukunta shi?"
Maman ta gyada kai tana kallonta ta ce" Ke yanzu banda jarabar tsafta me kika iya da har zaki tisa mutane a gana daga dawowarki ki shakar min yarinya ne, wai ko dai kin manta yadda aka haifeki da jinni a gidan nan haka na nakudo yar nan na haifi abina ko wani shegen ne ya rada maki a daki cewar kin fita iko da gidan ubanta? To ki shiga taitayinki, ki je ki ja tsuman rayuwarki ta kamaceceniya da namiji sannan ki iya da rashin lafiar dake damunki na haukan son dogari ki barmin yata ta wala son ranta a gidan ubanta, waje ne idan kin yi niya ki gyara idan baki yi ba ki matsa abinda ke ajiye ki zauna ehe!"
Tana gama fada ta ja hannun yarta suka yi waje tare, uta kuwa ta kuma bin falon da kallo kafin ta girgiza kanta cike da takaici ta dauki jakarta ta nufi dakin mahaifiyarta
Tana zuwa ta tura kofar ta ja ta tsaya tana kallon maman nata du wannan hayaniyar barci take kashirban a irin wannan lokacin da aka yi salar la'asar aka gama har duhun magariba ya fara shiga
A hankali ta karasa bakin gadon ta tsaya a sanyaye ta shiga dan kiran sunnanta tana kallonta
A firgice ta farka suka yi ido hudu da yar, da sauri ta maida idannuwanta ta rufe tana girgiza kanta ta kuma budewa a kanta ta ce" kai subahannalahi wannan ido naku na gado ba dai abin tsoro ba, ke wai ban ce da ke ki ringa barina ina barcina idan ta kama ba yanzun da kika tasheni muka hada ido da ke da magagin barci yaya kike so na yi ne? Idanfa na firgita na zo ina mafarkinki kai ku dai kun dauki jinnin wahala walahi gashi tun kina jaririya nake kaiwa sarkin mayu ya duba min kar a je mayu ne ku ban sani ba aman amsar daya ce ku din ba mayi bane kuna dauke da baiwa ce idon mage ba kowa ke samu ba domin idon wanda ya fi kowa daraja ne a cikin masu daraja mafi kusancin Allah, to ama nakin nan ya girma da yawa ga wani shegen dogon hanci uwa zanen cartoon!"
Du cikin yannayin jin haushi ne ta fadi magangannun nan ga y'ar cikinta , wanda na so gannin mutuwar jiki da bacin rai a bayane a fuskar yarinyar, sai dai ga mamakina hankali kwonce ta ce" Abincina ne ban samu ba, gashi bani da cenji komai a jikina ki dan zuba min madara da garin cen na sha na kwaso yinwa yau mafarkin dogari na yi a aji."
Hannunta ta saka ta talabe habarta cike da mamakin yar tata, kafin ta girgiza kai ta ce" To a kan me zan baki garina bayan kin san ina ajiye da shi ne dan shegen koma bayan tayan ubanki na sai an gama raba abinci su dawo su cinye nasu kuma su cinye na mutane, ke dai bara in lalubo maki hamsin a cikin kudin da kika banin nan, ni an kwana biyuma baki bani komai ba Allah dai ya sa ba daina kula saurayin naki mai bamu kika yi ba dan haukan da ake kadawa cewar kina fama da shi?"
Wannan maganar ma sam bata wani d'ad'ata da kasa ba, saima kallonta da ta yi na maganarta ta karshe da ta sanyayar mata da gabai ta ce" Yanzun kema kallon mahaukaciyar kike min kennan oan maganar dogari? Ku dukanku zan baku mamaki ne a kan maganar dogari, sai na kawo dogari har gidan nan ya aureni mun koma kusa da sarki sai na ga mai k'yamata dan Allah."
Tana gama fad'a ta juya zata fita ta kuma juyowa tace "Kuma ma rik'e garinki, kuma shima mai banin zan kore shi yau tunda dai kema baki yarda cewar ni ba mahaukaciya bace ba, kuma kin ga insha Allahu karatun matuk'iyar jirgi sai na cinma burina koma menene ni da Allah na dogara."
Tana gama fad'a ta kuma juyawa ta yi tafiarta ranta a b'ace, hakan ya saka uwar rakata da kallo kafin ta yi hamma da mik'a tana girgiza kai tana d'an shafa dokin wuyanta da take ji ya d'an rik'e mata a bayane tace "In ba hauka ba ina kalar fatarki ina zama ko kalar shiga jirgi ne bale zama matuk'iyarsa? Kaf a afrikama mace nawa ce take tuka jirgi? Bayan wannan ko a karuwan jirgin nan ai babu bak'ak'e bale a d'auke ki , kawai b'ata lokaci nasarun da suka bud'a wannan makaranta sune yan iska, ke dai kawai ki auri masu zuwar maki, suma na tabbata wannan k'irar taki ce ba wani abin ba, bari dai na mik'e na d'an watsa ko na jini garas."
___________________
Tana shiga d'akin da yake mallakinta bayan ta bud'e da ky d'inta ta jefar da jakar makarantarta kafin ta cire hijab dinta ta k'arasa bakin katifarta ta zauna tana kallon waje d'aya.
Abinda take tunawa irin kayan da aka ce lalle lalle shi za suna sakawa gabanan dan fara d'aukan darasi na wa'inda suke da ra'ayin aiki irin nata, ita fa babar damuwarta shin oga dogari zai yarda ta yi aikin jirgi? A duniya burinta biyu ne auren dogari ne na farko sai ko kasancewa matuk'iyar jirgi, wannan buri ya shiga ranta ne daga ranar da ta ga farar banasariar dake matuk'iyar jirgi, daga ranar ta gama yankewa kanta hukuncin a duniya bata da wani aiki sama da shi, aman fa idan dogari ya yarda.
Kuma d'aga kanta ta yi tana duba 'yar k'aramar agogon d'akinta, yunwa take ji sosai fa, irin sosai d'in nan, gashi ba abinci
Dolema ta yi zance yau idan tana son kwana lafia ba tare da ana yak'i irin na sambisa a cikin tumbinta ba.
馃尵 my alkalami
A pages na gaba in sha Allah..........
*WACECE ITA?*
*MEYE LABARINTA*
*SU WAYE DANGINTA?*
*WAYE MAHAIFINTA?*
*WAYE DOGARI?*
*MENENE TAKAMAIMAN MAFARKINTA?*
.................RAI DA LAFIA DAI IN SHA ALLAH...
DAGA ALKALAMIN SAJIDA YAR MUTAN NIGER.
11/14/21, 12:43 PM - Allah Akbar: 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
*膼 挪 泞 搂 茝*
2锔忊儯
An haifeta a shekarar 1997 a jamhuriyar Niger
Ita din y'a ce ga Elhaji Yunusa mai sari da kuma Rukayatu. Ta taso cikin gida mai tarin y'aya domin mahaifiyarta nada kishiyoyi har uku kwarara da suka san da su
Ahalin gidan elhaji Yunusa wasu irin ahali ne masu wuyar kwatance, sun kasance sakaku, bodararu, mararsa kunya da tarbiya, lamarin ya kasance abin tsoro domin ko a tsakanin iyayen da y'ayan ba jin kai da soyaya da ja a jiki bale tsakanin yayun da kannan.
Gida ne ginane mai shegen kyau, gida ne da ya gina shi dan ya yagawa makota da makiyansa, ya dage ya faso gari ya yi ginnin kece raini ne dan kawai ya keta raini a anguwa da jama'ar gari.
Yawancin y'ayan Elhaj Yunusa sun kasance masu girman kai, fadim rai, jiji da kai ko dan suna gannin gidan da suke fitowa a ciki ne? Sam basu dauki halitarsu ta dan adam a matsayin kasa wace gobe ana iya wayar gari su tsinci kansu a nanage a cikin kabari
Rayuwa ta yanci ce ake yi a cikin gidan Elhaji Yunusa, ba abinda ya dame shi da biyan karatun yaro na islamiya ko na gwamnati, idan kana so kar ka yi karatunma ba abinda ya dame shi, sannan idan mace na so kar ta yi aure ta yi ta zamanta a gidan matsalarta ce da ta uwarta, shi dai ba zai kori kowa ba, ba kuma matsalar wani zata saka masa ciwon kai ba, shi din kansa yana rayuwa ce tamkar ta marar adini, shi ba mai zage zage bane, sannan ba mai daurewa yaro gindi bane, shi ba mai yiwa yaro nasiha ko fada bane haka zalika idan ya ga ka matsawa yaronsa yakan ce da kai wai ina dalili ka yi rayuwarka ka sakarwa yaronsa mara shima ya yi fitsari son ransa.
A takaice rayuwa ce marar tsari, a cikinta ta taso mace daya tak a cikin yayunta maza uku, yayun da sai su tashi basa yiwa junna magana bayan ba fada suka yi da junna ba, ba wanda ya damu da dan uwansa, ba wanda yake da ra'ayin damuwa da dan uwansa domin mahaifiyar tasu kanta da ta haife su bata nuna masu mahinmancin hakan ba, a wajenta ita kanta bata damuwa da wani a cikinsu sai idan yana anfanar mata wani abin, sam bata damu da lamarin wani ya kula wani a cikinsu ba, bata tunanin wannan din matsalarta ce, ita dai ta yi mai wuyar tunda ta haifa idan sun ga dama su yi zumunci idan sun kiya su kashe kansu matsalarsu ce!, domin ita a rayuwarta ko kokowar ajiye masu abinci gaskiya ba zata iya ba, wasu iyayen zuwa suke su dibarwa y'ayansu dan kar su dawo su rasa abincin, ita ta fada masu gaskiya idan sun zo da wuri su samu idan basu samu ba su nema su ci a waje itama ta kanta take bata son damuwa
A duniyarta wanda take iya zabura a kowani lokaci ta biya masa bukatarsa mijinta ne, gyara take yiwa kanta na mamaki wanda hakan ya sa shi din kansa baya dadewa bai je mata ba, wannan kawai ya isheta farin ciki domin bata rasa na kashewa in dai zai zo inda take.
Sai dai du iya gyaranta a banza ya tashi domin y'ar da ta haifa da cikinta ba abinda ta iya na fannin gyara, ko girki bata iya ba, abinda kawai ta iya a rayuwarta shine tsafta, bata gajiya da shara da wanke bayi da wanke tufafinta da abin shinfidarta, takan share falonsu a kowani lokaci hakan baya hanna daga ta gama shararta su lalata mata su dawo su yi ta masifa a tsakaninsu tamkar zasu cinye junna danye
*MUNEERATH* ta taso a cikin rayuwa mai duhu, tun Muneerath na da shekaru goma sha daya da ta taba cin sa'ar gannin irin hawan sarki ta dawo gida cike da bege da wani irin tunani, tashin farko ta sanar da mahaifiyarta magana kamar haka" Mama, na ga kwaliya, mama ina burin na auri sarki"
Sai dai amsar da ta samu ita ta saka gwuiwowinta da mafarkinta cenzawa nan take a lokacin da mahaifiyarta ta yi daria tana fadin" Ke mumunan namiji mai kudi kyawawan mata ke wawa, mace bak'a mai muni irinki ai sai dai ki dan lalaba da rokon Allah ko Allah zai sa a cikin bayin gidan wani ya ce yana so, idan kin taki sa'a Dogaro ya yaba kuma shikenan ko ba komai sunnanku yan kusa da sarki!"
Daga wannan rana ta ringa kokaron sannin shin wai wanenema shi *DOGARI* din nan?, meye kusancinsa da sarki? Shin akoy dogari a duniya? Domin sam batama san menene dogari din ba.
A hankali ta gane meye hakan kuma waye hakan, sannan ta ga haza cewar dogari yana da kusanci da sarki har ya taki mukamin rike lemarsa, hakan ya saka ta sauko daga burin da ta ci na sarki ta dawo dogari.
To abin ne yake ta hauhawa, a hankali lamarin yake neman yin kamari da wuce tunanin bawa, ta saka abin a ranta ta yadda ya zamo burinta na biyu a cikin gidan duniya, wanda na farkon kuwa mahaifinta da kansa ne ya yi mata daria kafin ya girgiza kansa ya barta nan tsaye a lokacin da take sanar masa burinta na karatun da take bayan ta kawo masa sakamakon makarantar gwamnatin da take wanda tunda ta shiga makaranta itace ke cin ta farko a kowace jarabawa ta dadage ta ce" *Pa*, da ka ga ina kokarin nan burina na biyu a duniya shine na zama *HOTTEST* "
Da matukar mamaki ya tambayeta " Hottest fa? Na jirgi? "
Cike da kwarin gwuiwa ta gyada kanta tana kallonsa
Idannuwanta dake da color blue mai duhu ya kala da kalar datar jikinta , Muneerath dai ba fara bace ko daya bata da hasken fata aman kuma ba bak'a bace lut, fatarta kalar fatar hausawa ce mai kyan gaske domin a fatarta babu wani waje fari wani waje bak'i, ta yi uniform ne gaba dayanta ta yadda take ba ko fararen sha'a, ba a nan abin yake ba, ba wai matsalar fatarta ba duda a yanzu an waye ba sai farare kawai ake dauka a matsayin hottest ba dan kuwa yanzun
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 42