Share this page
wani kara mai karfin gaske muryarsa a kausashen nan ya ce" Kamar dole nake karanta a furucinka PAH! Me maganar da na karanta a page na Facebook din Royal Familly cewar ni HANJA na ajiye tukin jirgi baki daya?" Pah ya kuma Fuskantarsa shima da nasa jinnin dake gudu a jikinsa da kuma karfin hali da sannin cewa hakan na iya faruwa dama ya shiryawa hakan ya ce" Eh dole ne kake karanta, kuma ya zama dole ka bar bauta wa kasa ta wannan fannin ka kama naka bautar da Allah ya haliceka dominsa!, Lion 馃 u'r a king!, Plz ka yi aiki irin na saraki!" Gaban goshinsa ya dafe ya yi tafia baya kadan ya dawo gaba kadan Hannayensa ya hade ya jimke yana kallon mahaifinsa, fuskarsa ta yi ja hakama idannuwansa, hannayensa du sun tada jijiyoyi irin na bacin rai hakama gaban goshinsa ya tada wani irin jijiya dake bugawa dal dal dal muryarsa a cinkushe ya ce" Abui, ka sani daraja na mahaifina kake, hakan ba yana nufin zaka ringa min irin haka ba!, Ka dauke min ita dan ka hasala ni, ka nesantata da ni dan ka birkita ni, shin dan Allah ya baka dama a kaina ta uba shine kake son halaka ni?, A yanzu ka saka ni shiga abinda bana ra'ayi, sarauta ka ba dan uwanka mana? Idan yana so ya kona kasar matsalarsa ce muna iya bara masa kasar!, Shine zaka yi magana da sunnana kan cewa ni ne na yi wannan d茅cision din?, Sannan ka saka a rufe min kofa ina ihun a bude min sun labe banma gansu ba bale su bude min?, Plz tell me so kake ka ga na fadi kasa?, Tell me so kake ka halakani?" Pah ya lumshe idannuwansa shima da suka yi jan ya shiga fadin" Yaya kake magana kamar wanda yake aiki da son zuciya?, Yaya kake aiki da kalamai irin na jarumi bayan ka sako son zuciyarka gaba da komai?, Kana min maganar ya kona kasar watau idan na bara masa kasar ya gyarata ko ya konata baka da damuwa da hakan bayan kai shaida ne konatan shine abu mafi sauki da zai aikata daga bakin lokacin da zai wayi gari ba ni ba bayana?, Yaya kake acting kamar wani mai karfi kamar wani mai juriya bayan ka kasa fuskantar barazanar rayuwarka nutsuwarka duniyarka ka iya janyota ka ganar da ita halin da kake ciki?, Yaya kake son min rashin kunya bayan ni ubanka ne kuma ban baka tarbiya irin ta mai jan kunne ba duda na kasance mai jan kunnen?, HANJA ya zama dole ka hau kujerarka!" Da karfin Murya HANJA ya budi baki ya ce" Ban zan hau ba!, Abui ba zan hau ba!" A hankali juwa na kwasarta, cikinta na murda mata ba ji ba ganni da wani irin karfi, numfashinta na dauke mata tana janyo shi da karfi da kyar ta iya karasowa tsakaninsu mayafin abayarta na faduwa daga jikinta, zufa ta wanke mata gaban jiki, jikinta yai mata nauyi sosai da kyar ta iya budar baki cen ciki tana rike rigar Pah da dayan hannunta da dayan tana son kamo hannun Hanja domin a kusa da kusa suke sosai tana fadin" Please, i bg u da sunnan mahalincinmu plz ku saurara min haka, dan Allah ku daina fada a tsakaninku, Khalb nd Habiby ku....................." luuuuuuuuuuuuuuu ta tafi gaba dayanta ta fadi a kasa domin a tsakanin su biyun ba wanda ya kawowa ransa cewa kokarin shiga tsakaninsu da take ba dan ta raba su kawai bane , a cikinsu ba wanda ya san cewa a yau tun safe tana dan fama da ciwon cikinta A cikinsu babu wanda ya gane halin da take ciki wanda suke ciki ya fi dauke masu hankali har sai da ta kai kasa kan cikinta da goshinta gaba daya da karfi ta yi wata muguwar faduwa ya saka su juyowa a firgice inda wayar dake hannunta ta silale ta fadi kasa daidai lokacin da Muneerath ta rintse ido sakamakon jin karar faduwar wayar sai jin muryoyin dakarun mazajen da suke fada tamkar zasu ciji junna sun shiga kiran sunnan mace daya kwal dake saka su nishadin rayuwa cikin ihun murya inda daya ya ce" ALEESA!," dayan kuwa ya furta " MAMAH" A DAKE KUMA TA JI WANI RATS RATS RATS sakamakon saukar kafar daya a cikinsu a kan wayar sai daukewar kiran ya biyo baya wanda ya sakata sakin tata wayar daga tsayen da take ta fadi kasa lokaci daya tana jin wani irin faduwar gaba da ya ziyarceta wanda ta ji wata irin juwa ta kwasheta ta aniya yin luuuuuuu zata kifa da sauri Mahaifiyarta ta tarota tana ambatar sunnan Allah da sunnanta tana girgizata da tambayar meye menene ya faru? Duka a firgice hakama kawarta aminiyarta a rude ta dauki wayarta ta shiga maida kiran aman cikin ikon Allah a swt offf take amsa amo hakan ya karra rikita su domin kuka ne ta saka ta shiga fadin ta tabata wani mugun abu ya faru, kuma a kan Mah ya faru, kar dai a je ciwonta ne? Ko kuma fadansu ya saka ta summa ? Sosai yamnayin da ta shiga ya ba mahaifiyarta mamaki sannan ta dauki soyayar da yarta ke yiwa matar nan da girma da mahinmanci A saman kujera suka taimaka mata ta zauna gaba daya jikinta na wani irin rawa na tsoro da firgici, Gaba daya sai ta ji idan ba ganninta ta yi a Palace ba ba zata iya samun nutsuwa ba, harma ta furta hakan inda mahaifiyarta da mamaki ta ce" Muneerath, Ingila fa kika ce?, Waye zai baki damar zuwa Ingila a yanzunnnan ke kuwa?, Awani ake yi na tafia fa, bayan wannan duda kin ce kina da Visa kuma ke din Hostesss ce ai ba koda yaushe ake da jirgin tafia Ingila ba, sannan ni gaskiya kin ga aikin nan naki har yanzu ba wai na yarda da zan iya barinki komawa bane, kuma ba zan iya barinki tafia Ingila ke kadai ba, me zai hanna ki yi ta yi mata adu'a na tabata koma menene zasu kire ki domin da alama su dinma sun damu da ke tunda har MATAR ta kiraye ki" Daidai Oga ya shigo kennan daga anguwa da manyan kayansa ya karaso yana kallonta yana son tambayar lafia ita kuma wannan?, Sai ya ji Munnerath din ta riko hannun Mamanta ta ce" Mamanmu, dan Allah ki bani dama na je na gani ko zamu samu jirgin da zai tashin, dan Allah mamanmu ki taimakeni kar zuciyara ta buga, walahi na san yanzu sunna cen wani abin ne ya faru dan Allah ki bani dama mamanmu idan akoy jirgin sai mu tafi tare gaba daya har ke harma Oga idan kina so, akoy kudi a acct dina kuma ina da damar gayatar du wanda nake so domin takardar yar kasa ce da ni, ina da alfarma na masarautar Ingilar, ina iya kai tsaye na sa a min takardar gayata na je da ku" Saudat dake ta gwada kiran layin ne ta shiga kiran layin sir Attahir Ringin take ta yi aman bai daga ba hakan ya sa ta dauko wayarta ta shiga kiransa da wayarta domin bata san me ya hada shi da Muneerath ba kwana biyu kennan ba kabarinsa kwata kwata Ta ci sa'a ya daga, hakan ya sa a dan gagauce ta shiga sanar masa cewa Muneerath ce na waya da Mah ta ji alamun kamar wani abu ya samu Mah din ko Sir Hanja, shine gatannan tana ta kuka wai ko zata samu jirgin da zai tashi to Ingila?, Walahi muma muna jin alamun ba ma dadi bane ka san kuma irin karamcin da sukai mata shine nace bara na tambaya ko akoy damar hakan?" Sir ATTAHIR ya lumshe idannuwansa cike da jin wani abin da yake ta yaki da shi kwana biyun nan dan ya nisanta kansa da ita , da kyar ya iya hadiye abin yana sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Subahannalah to ta kirayi number HANJA din mana ba sai ta ji ba idan bata samun Mah din, bayan wannan baki san tana da damar sakawa a tashi da jirgi da ita ba koda kuwa ita daya ce? In dai akoy jirage a kasa ko na wata kasar ne tana da wannan damar ku je a茅roport din kawai bara na yi kira na daidaita maku komai" Da sauri Muneerath ta mike jin abinda ya fada, ta kai dubanta kan iyayenta da mamaki ke neman kashe su Oga ya ce" Wai tsaya Jirgi fa na ji an ce?, Ingila dai ingila ko wani gari ne ake yiwa kiranyen nan?, Shi wannan din da kuka yi maganar da shi waye shi?, Kuma waye Hanja da Mah?" Maman su Muneerath ta girgiza kanta tana kallon Muneerath din da ta matso da sauri ta rike hannunsa tsakaninta da Allah kuka take tana fada masa cewar su din iyaye ne a wajenta , Hanja kuwa tamkar yaya yake a wajenta Baki ta tabe ta ce" Ya damu da sannin me hakan yake ciki ko kin ga alamun ya damu da damuwar wani ne a duniya bayan tasa?" Oga ya ce" idan kuwa kina jin tsoron Allah ba zaki ce ni oga ban damu da kamarin yar oga ba, koda na yi rashin damuwa da rayuwar wani banda ta yar oga, ki ci gaba da min irin wulakancin nan, duniya ce" Da sauri mamansu ta ce" In sha Allah alkhairin duniya zan tainta na kuma gama da ita lafia tunda ban cuci dan kowa ba!" Da sauri Muneerath ta fashe masu da kuka ta ce" Dan girman Allah kar ku yi, yau dai kar ku yi fadan nan, ku taimake ni ku raka ni, idan bakwa zuwa ku bani dama na je na gani, walahi ina cen ta yi rashin lafiyar da ta daga hankalin kowa har sai da Hanja ya yi kuka du rashin imaninsa kuwa !" Mamanta ta hae girar sama da ta kasa tana fadin" Je ki shirya bara na sa yayanku ya kai min y'ayana gidan yayana kar kafin mu dawo na tardo sun bar kasar sun tire!" Oga ya kankance ido ya ce" Da alamu kin manta ni ne ubanta kuma ke kuwa a karkashina kike, dan haka ba inda zaku" Muneerath ta riko hannunsa kanta na sarra mata a hankali ta dora kanta a gefen hannunsa tana murzarwa zafin da kanta ya dauka na shiga hannun nasa muryarta a mace tana fadin" Oga dan Allah ka barni ka ji aban Muneerath ?" Hanci ya ringa bugawa yana hararen gefen Mamansu da ta yi gaba ta shiga kimtsa y'ayanta da hada masu kayansu dharda na islamiyarsu sannan tana neman layin danta dan ya zo da motar da ta siya ta sakar masu ya kai mata y'ayanta cen a kula mata domin ba zata iya iya barin Muneerath ta tafi ita kadai ba walahi, kuma da ace bata ji irin kalaman da suke fadawa junna da irin tada hankalin da yarta ta yi a daidai gabar nan da suke kaunar junna take jin son yarta tamkar ranta da ba zata barta ta wani je ba, sai dai a yanzu suke karra sannin junna dan haka ba zata bar abinta ba gaskiya zata je kafarta kafarta Sun yi tafia mai nosan gaske, mai daukan lokaci Sunna sauka Sir Attahir ne da kansa ya saka aka dauke su sannan ya shaida zuwansu Palace din dake rikice wanda gaba daya da kyar ya iya samun damar a barsu su shiga da adadinsu Gaba daya jikinta karra yin sanyi yake a lokacin da suka durfafi palace din Bayan sun samu shiga sam ba ta iyayenta da suka rude da kasar da gidan da matakan tsaro take ba Da gudu gudu ta shige motar palace din ta umarci a kaita asibitin palace din ta bar Oga na kiran sunnanta A lokacin da ta saka kafarta baban filin idannuwanta suka yi arba da abinda take iya kira baban tashin hankalin da bata taba kawowa ranta ba Da karfi ta rufe idannuwanta ta kuma budewa a kan gadon da ake son turawa da mutun sama rufe da farin abin rufa wanda Pah dake tsaye a gak da HANJA suka zubawa gadon ido haka kuma Iman dake tsaye gaba daya ta yi jajajir dan birkicewa itama ta bi gadon da ido har aka tura shi aka shige wani dakin dake hanyar coridor din watau daki ne na tiyata ko na meye oho A hankali take daga kafarta, jikinta sanye da atamfa mai ruwan ja mai dan duhu an yi mata dinkin riga da sket wanda ya mata dasss a jikinta ya kamata sosai a jikin nata ya fitar da dukan wani yannayi na kyau da tsarin halita a jikinta A hankali ta tsaya a gabansu idannuwansu suka ringa sarkuwa da na junna har ta sauke dubanta a kan HANJA wanda suka tsaida dubansu tsai ido cikin ido sunna kallon junna A hankali ta motsa lebenta dake naturel baya dauke da ko man lebe tana kallonsa cikin ido ta ce" Me yake faruwa ?" Idannuwansa da yake ji sun gama kyekuashewa ya lumshe a hankali ya kuma budewa a kanta Dukan da zuciyarsa ke masa da halin da mamansa ke ciki na rayuwa ko mutuwa da kuma ganninta da ya yi a irin wannan lokacin na ba zata a gabansa sai ya ji zuciyarsa na kakaryewa Dukan da zuciyarsa ke yi da kuma irin yadda yake neman jin wani sa'ida da ganninta ya saka shi daga kafarsa a hankali ya matso daf da ita daidai lokacin da sojan da doreban da ya rako su Oga suka karaso daidai lokacin HANJA ya aikata aikin da ba wanda ya kawo haka a ransa, domin ita kanta wace ya aikatawa hakan bata taba tunanin haka daga gareshi ba a daidai lokacin da ya mika hannunsa ya damko nata ya janyota da karfi ya bata wata wawar rungumar da ta cuje dan kwalin kanta ta saki yafar da ta yiwa jikinta da mayafinta fari kal ta yi kasa kasa dan firgici da tsoro ta yi baya baya aman duka ya tarota a jikinsa ya kara rukunkumeta da rukunkumewar nan mai neman karya kashin bawa inda su OGA, da MAMA, da IMAN, da PAH , da dukan wani dan adam din dake wajen ya zarro ido kafin da sauro sojojin wajen su aniya neman kare hakan da tare Oga da ya zarro ido a zuciyarsa ya ayana' Kuturu uban meye wannan kuma' yana neman karasawa ya raba wannan garjejen jan mutumen da yarsa, a daidai lokacin da itama take mutsu mutsun son kwatar kanta idannuwanta duka a waje muryarta har tana rawa tana son ambatar sunnansa aman bugun da zuciyarta ke yi ya tsananta ta yadda ta kasa fitar da koda kalma daya ce saima jin lalausan sajensa na gogar gefen fuskarta muryarsa cen ciki sannan yana fuzga haka kuma yana goga mata sajensa ba da wata manufa ba sai dan neman inda zai saka ransa ya ji sanyi ya furta" TSORO NAKE JI, I'M AFRD MUNE..................... MUNEERATH ...........MU...... MUNEERATH MAH, MAHNA MAH............. " SAKAMAKON LABARINA NA KUDI MAI TAKEN *WATA KOKOWAR* DUTSE ZAI RINGA ZUWAR MAKU LITININ DA ALHAMIS KADAI IN SHA ALLAH.......... .. .... KI GARZAYO KI YI RGST YA UWA DAN SAMUN NAKI CIKIN AMINCI IN SHA ALLAH........DAGA ALKALAMIN SAJIDA 11/14/21, 12:53 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 5锔忊儯7锔忊儯 Wasu zafafan hawaye ne suka shiga saukowa sunna gogar masa a gaban rigarsa, kanshin turaransa na dukan hancinta, gaba daya jikinta na rawa da bakon yannayin nan, irin yadda a yau ta ga faiblesse din HANJA sai ta kasa rike kukanta, tsoronta ya tsananta A hankali muryarta na rawa rawa ta budi baki ta ce" Hanja, plz numfashina, ka sasauta min rikon" Baya jinta ne? Ko ya yi nisa ne? Zuciyarsa ta gaza ne? Ko bai gane cewa ta yi ya sasauta mata ba kunnayensa suka jiye masa kara matse ni? Sai gata ta ja numfashi wannan karron ta hade da kirjinsa sosai muryarta ta kasa fita sai kawai ta lumshe ido tana sauraron bugun zuciyarsa da kuma yadda yake karra riketa tamkar wani ne zai kwace masa ita a hannunsa? Aman rikon da ya mata ba na wasa bane, wanda ya saka Iman fashewa da wani kukan infa Pah ya cire dubansa a kansu ya dora kan Iman sannan ya maida wajen da ake kokowa da tsohon nan ana kwasar ba dadi tsakaninsu A rikice Oga ya daga murya ya ce" Ke yar oga dan ubanki me kike a jikin kato? Waye wannan din da ya riko ki haka na shiga uku" Da sauri ta ankara ta dan daga murya tana mutsu mutsu muryarta a dan dage ta ce" Hanja ka saka ni abana zai dakeni menene wannan abin dan Allah" Pah da ya gama gane a wajen Yan africa fa musulmai ba'a haka , wannan ba wasa bane a wajensu ya samu da kyar yana fama da tasa zuciyar da damuwar ya dafa gefen kafadar yaronsa a sanyaye ya ce" Please ka sakata kar ta rasa numfashi, ko so kake itama a kwontar da ita ne?" Kwontar da itan da ya ji shi ya tashe shi a duniyar da ya afka, da sauri ya sasauta mata rikon hakan ya bata damar wartar jikinta cike da wata kinyar da bata san ta uban mecece ba da kuma tsoron Hanjan da bata taba ji ba, da wani irin tausayinsa da bata taba ji a zuciyarta ba ta ringa jan mayafinta tana lukube jikinta har kanta Shi kuwa kallonta yake da irin kallon nan tamkar zaka dauke mutun da ido sam baya so ko ido ya kifta Bangaren su Pah kuwa yana karasawa suka bashi dama ya isa kisa da su Oga wanda Pah na isowa kusansa sai ya samu kansa da sada kai gaba daya dan walahi wani irin gwarjinin mutumen da yake tunanin ko christane ya dirar masa da shayinsa , hakama Mamansu da ta gama cika da hali da mijin nata ke rabawa tana kallonsa da kuma tsoron rungume mata y'a da ta hango an yi itama ta samu kanta da sada kai a gaban wannan jan mutumen da ya tsaya a gabansu tsayinsa du ya kere su sannan ya kura masu ido Murmushin karfin Hali Pah ya sakar masu kafin ya mikawa Oga hannu a sanyaye ya furta" Asalamu alaikum " Sai da oga ya kalli matarsa da Saudat kafin ya iya ba Pah hannu yana mai amsa salamarsa da saurin kuma kallon hannunsa jin wani irin laushin abu ya rika a hannunsa Pah ya dubi Saudat ya sakar mata murmushin itama ya nemi da ta masu translate kafin a nutse ya shiga yi masu barka da sauka , ya dora da fadin ya san su din iyaye ne kowasu makusantan Muneerath, su yi hakuri sun zo a irin wannan lokacin basu samu sauka mai kyau ba, sunna cikin hali ne na rashin lafiyar matarsa watau Mah wace har sun shiga halin kukan rashinta domin sai da ta yi doguwar suma ta kusan awa biyar kafin take dawowa duniya, yanzu haka dai itace aka shiga da ita dakin tiyatar gagawa wace likita ya ce a tiyatar nan kila wa kala ne, rabon rashin tashinta ya fi rabon tashinta karfi, dan haka dan Allah su yi hakuri da irin halin da suka same au, yanzu shi zai je masalacine ya yi alwallah ya zauna a cen har a fito da ita, yana da bukatar adu'ar su da duk wani makusantansu, su taya shi da adu'a ya san Allah baya barin wani dan wani ya ji dadi , su taya su da adu'a idan lokacinta ne ya yi Allah ya sa ta cika da kalmatu shahada, ta samu kyakyawan karshe sannan mutuwarta ta zamo hutu ce a gareta, suma iyalanta Allah ya basu ikon jure rasa masoyiya abokiyar rayuwa a karro na biyu, domin wannan itace matarsa ta biyu KHADIJA shine sunnanta na kirki anai mata kiranye ne da ALEESA Gaba daya jikinsu ne ya yi wani irin sanyi, Saudat take fasara masu kuwa sai share hawaye take hakama Mamansu da kyar ta iya rike kukanta tana kallon Pah cike da tausayi Oga ya sauke ajiyar zuciya ya girgiza kai ya ce" Jikina du ya yi la'asar, kai jama'a mutuwa mutuwa, kawai dai sai ta karar da mu innalilahi wa ina ilaihi raj'une" Saudat dai bata fasara wannan ba sai da ya kuma budar bakinsa ya ce" Cuta ba mutuwa bace Elhaji, Allah ya bata lafia idan ba laifi mu je masalacin kawai nima ai ba karamin makaranci bane mu je kawai mu yi ta karatu Allah ya bata lafia ka ji?" Murmushi Pah ya yi yana gyada kansa ya juyo yana kallon yada HANJA ke zaune saman abin zama irin na jikin ginin nan kansa a jingine jikin garu still idannuwansa a kan Muneerath dake face da shi itama a zaune a kusa da Iman ta riko hannun iman din tana dan murzawa kanta a kasa Ajiyar zuciya ya sauke ya shiga yiwa jami'an tsaron magana kan a barsu su kadai watau su Muneerath da yan tafiyarta da Hanja da Iman, daga nan kar a bar wani ya kuma shigowa domin gari ya dauka du wani makusanci ya garzayo so suke su layu a wajen bayan shi baya so a karra rikita Hanja din Saudat da mama suka karasa suma suka zauna kusa da Muneerath wace kanta ke kasa gabanta na faduwa tana cike da tsoron abinda zai biyo baya na abinda wannan dan na Mah ya wani mata a gaban iyayenta, ita kam bata san dabi'ar iskanci a me ya dauketa ba walahi A hankali tana kallon kasa muryarta cen ciki ta ce" Mamanmu, walahi rikicewar da ya yi ne aka yi katari nice a kusa da shi haka ta faru, walahi na rantse maki a zamana a gidansu ba aikinmu kennan ba, kuma yanzu hakan shi kansa daga ya dawo a hankalinsa zai fara hararata kin ce na fada maki, ya ga damar ya ce nicema na rukunkume shi, abinda da muka zauna ma da shi ba wani shiri muke yi b..........." Muryar mamanta a sanyaye ta ce" Muneerath ina so na daura alwallah a nunan alkibla kaina ya kule tunda muka shigo, so nake na rokarwa baiwar Allahn nan sauki na Allah da ita da mu baki daya" Muneerath ta kaleta da sauri da dan mamakin jin furucinta, shin bata ji me tace bane ko kuma bata ga abinda ya faru bane.....kai da ta ji dadinta da bata gani ba walahi dan ita ta ki jinnin a mata kallon yar iska tunda ita dai ba yar iska bace Iman ce ta mike bayan Saudat ta fada mata bukatar Mama jikinta ba kwari kamar zata kifa ta ja mama suka nufi cen ciki dan ta bata gyararan wajen da zata yi ibadarta a nutse Kan Saudat a sade da yaren Hausa ta ce" Muneerath, dan Allah ki dube shi, ya dace ki karasa gefensa ki raashe shi" Ido Muneerath ta zarro ta dan saci kallonsa a hankali ta ce" Saudat ni gaskiya na gaji da rarashinsa dan Mah bata da lafia, adu'a ya dace ya zauna ya yi aman kina ganni ya rungumeni a gaban Oga , Oga fa ya ganni aman ina ga mamanmu bata gani ba , hakan wancen karron kuka ya sha ni tsoroma yake bani kin ji karfinsa kuwa?" Saudat ta lumshe idannuwanta cike da tausayin lamarin nan dake cikin duhu , a yanzu idan ta kai dubanta kan Hanja sai ta ji tamkar ta rushe da kuka, gashi zaune tamjar DUTSE, ya kura mata ido tamkar BAKUWAR HALITA, kallonta yake da SO da KAUNA da BEGE , wanda harshensa ya kasa yin FURUCI a gareta A sanyaye ta ce" Muneerath kin dai san lada irin na wanda ya taimaki mutumen

Chapter 33 of 42