dauko computer Muneerath din wace bata anfani da shi sam dan ita batama san aikinsa ba gaskiya, ta zauna ta shiga opperath a nutse ta hada connxion bayan ta saka cod din masarautar sannan ta kuma hada layinta ta hau google
A nutse ta dora harafin sunnan Dogari tare da danawa kan africa ta shiga kallo
A hankali take kallon hotonsu da irin shigarsu da matsayinsu a fadar sarki
Da mamaki ra juyo tana kallon muneerath da yanxun yar riga ce a jikinta daidai gwuiwarta kanta a hade waje guda , dan mak up din da ta yi mata ya fitar da tsarin kyanta, yarinyar ta bada kala irin ta manyan hannu ce aman ta mace a son irin wannan? Sai ta samu kanta da bushewa da dariya tace "yanzu daman muneerath baki taba haduwa da dogarin ki ba, aman kike maganar mijinki dogari meye meye ki ishemu da zancen dogari ? Ta karashe tana wata dariyar ............. muneerath ko ta cika fam sabida dariyar da iman din ke mata
A hankali Muneerath ta cire kanta, seriusly itama abin na damunta, a hankali ta juyo gannin Iman ta dawo gefenta tana kallonta
Iman ta dafa hannunta ta ce" Ina iya taimaka maki har ki samu soyayar dogari mai kyau mai tsari wa ke kadai"
Muneerath ta ji zuciyarta na dan bugawa tana kallon iman ta ce" Allah zaki min haka?, Aman ta yaya ke zaki iya min haka ke da kike nan?"
Iman ta yi murmushi ta janyo computer ta ajiye ta cire wayarta kirar iphone ta gyara zamanta ta shiga Facebook tana kallonta ta ce" Baki san yanzun duniya ta yi ci gaba na mamaki ba?, Daga nan da kike zaune kina iya malakar zuciyar dogari harma ya haukace sai ke ba? Kin ga ta facebook yanzu har aure yake haduwa a kuwa sha shagalin biki a tare, kin ga abu mafi sauki kennan a yau yau ki fara hira da dogari, a hankali ki tura masa hotunnanki ki mike a haka ki karkato bombom din nan naki na maii hotuna masu masifar kyau ki karkato mamanki ki rike su ki bankaro su sosai ki yi yannayi na yarinya mai fuzga wace zata tada sha'awar namiji daga ya kaleta irin haka...." Iman ta mike ta rike mamanta ta wani gantsare ta turo lebunnanta ta cije daya ta wara kafafuwanta takashe ido daya inda Munnerath gaba daya baki da hanci bude tamkar sabon kamui take kallon iman har ta gama ta zauna ta dora da fadin" mu dora shi saman dp dinki na facebook mu ringa matsa masa har ya amshi invitation dinki daga nan mu ringa masa hira kala kala idan yana son sannin wacece ke mu fada masa ki fada masa irin son da kike masa, na tabatar maki cewa nan da yan kwanaki zai haukace maki sai kin ga dogari a kasar nan koda a kafa ne"
Gaba daya Muneerath sai ta ji kanta na sara mata, wani irin takaicin iman ne ta ji na shiga zuciyarta, muryarta a shake ta ce" Ki ce karuwanci zaki koya min?"
Iman ta tsaya da maganarta tana kallonta da mamakin jin furucinta domin ita dai a nan bata ga meye ya kawo kalmar nan ba
Muneerath ta girgiza kanta gwuiwarta a sage ta ce" Yaushe mata suka yi arha har haka? Yaushe muka yi zubewa har haka? Yaushe musulunci ya zama abin wasa har haka? Yaushe rashin sannin ciwon kai ya cika matan duniya har haka? Anya kuwa maganar ta al'adu ne ba iskanci bane duba da koyarwar litafin daya ne?? Anya kuwa mace na anfani da karancin shekaru irin nata kuwa? Dole a ambaci mazinaciya kafin a ambaci mazinaci domin du iskancin namiji malamarmu ta pc ta ce da mu ba zai kai hannunsa kan mace ba sai ya kula cewar itama lalataciyar ce! Yanzu iman ni da ke Mah ta ce da mu ko tabamu namiji ya yi zamu dauki ciki, a nan ta ce da mu koda kowa na yawo kansa bude mu mu kasance masu lulubewa domin suturar mace mutuncinta.... aman shine kike irin wannan abin? Anya ba tambayar mah zan yi ba kuwa ke ba yar iska bace?"
Iman showwwwwwwwwwwwwwwwwww
11/14/21, 12:51 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
3锔忊儯6锔忊儯
Iman ta zaro ido da sauri tana kallonta ta ce" ke wai me kike fadi haka, ba ke kike haukan sonsa ba ni kuma me ya hadani da iskanci wannan ai ba iskanci banr!"
Muneerath ta mike rai bace ta ce" Walahi ke yar iska ce kuma sai na jadadawa mah kar ki yi cikinki ki goga min! Nan nan ake yiwa yar gidan idi gorin ta yi cikin shege nan da nan babanta ya koreta , dan na ce maki ina sonsa ai Ogama ya sani kuma shima ya ce ya san ba dogari ba ko baban dogari ne zai so ni shine ke kike cewa ni Muneerath na tarbi namiji nace ina sonsa? To bari ki ji, walahi dogari idan ya ga dama ya ce yana sona zan fadawa aminiyata amina mu ja masa rai na kwana biyu kafin na bashi amsar eh ina sonsa, idan kuea bai ce ba ya jima bai so nin ba sai me? Sarki ne dai ko? Yau ina hostess dolema zai zama dan uwana dan ina komawa zan kai gaisuwa kai tsaye gaban mai Damagaram, ko sarkin maradi!"
Tana gama fada ta juya cike da bacin rai tana kallon iman da mamakinta ta fita da wayarta tana girgiza kai a ranta tana ayana 'dama ai da ganninku kwartaye ne ku, ni dai ba kwartuwa bace!'
Iman mamaki, kunya, dana sani suka kusan sumar da ita, bata taba tunanin zata zile mata haka ba, yanzu du irin bata lokacin nan da ta yi tana mata surutu ya tashi a banza? ........mamakin furucin yarinyar kuwa ya tsaye mata a rai, bata gane ba, meye a ciki dan ta nunawa namiji tana sonsa? Tsaki ta yi tana girgiza kanta a bayane ta ce" Bagidajiya kawai, tunda dai ba zaki furtawa namiji kina sonsa ba bani da damuwa da ke dan na san ko ya yar gwal ce ba fai MY PRINCE ya fara nuna so a kanta ba, baka kirin mai katon bombom!"
Bayan salar isha'i
Hanja ne ya shigo da dan hanzari kamar yadda tafiyarsa ta kasance , idan ka gansa yana tafe da lako lako to bashi da lafia ne
cikin parlon mah ya shiga da salama a bakinsa cen kasa kasa
Mah na zaune tana dan nazari ya karasa kusa da ita sosai ya zauna dauran kanshi yayi a kafadun ta a hankali yake sauke wata irin ajiyar zuciya mai zafi yana yi yana fan lumshe idannuwansa
Kallon fuskar shi tayi a hankali ta jimke hannunsa dan tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa, a sanyaye ta ce" Me ke damun zuciyana?"
Idannuwansa ya lumshe yana jin zafi a kasan zuciyarsa a hankali ya ce" Ina jina ba karfi a gabanku, ina so na kasance mai faranta maku, ina so na cire maku damuwarku"
Idannuwanta ta lumshe tana murmushi a sanyaye ta ce" Bamu da damuwa khalb bayan wace bawa baya iya cirema kansa sai yadda Allah ya yi da shi, you see farin cikinmu kuwa na tare da mu tunda kana gefenmu, yanzun yaya maganar dawowar naka? Ina so ka dawo kusa da mu"
Dan murmushi ya yi a hankali ya ce" Tigre fa?"
Mah ta dago tana dungurar kansa ta ce" Ka kaita gidan zoo mana?"
Ido ya kwalalo ya ce" Sai na mutu za'a kaita mah, idan na mutunma a barta ta ci gadona in ban haihu ba, in kuwa na haihu na tabata my Princ zai rike min ita"
Mah ta dan shafi gefen fuskarsa a hankali ta ce" ka zo da ita, ka sakata a dakinta na nan, aman gaskiya karta ringa zuwa gaishe ni na yafe"
Yar dariyar da bai shirya ba ya yi yana kallonta kafin ya saka hannunsa ya buda alkur'anin dake ajiye a gefenta ya budo wajen bakara ya gyara zamansa ya tankwashe kafafuwansa a hankali ya buda muryarsa ya yi bismillah ya fara karanta mata ita a sanyaye wanda take gane dukan kalaman ciki idannuwanta lumshe tana idasawa a kan lebenta shauki na dibanta tana cike da farin cikin yannayin
Na su su tashi ba sai da dare ya yi sosai Hanja ya yi mata salama shima zuciyarsa sakai nauyin ya sauka hakama bacin ran da yake ciki ya age sosai ya nufi bangarensa inda itama ta shige dan yin wanka ta tarda nata mai gidan
____________________________
Karfe takwas da rabi ta gota
A hankali take tafia tana bin matatakalar gidan cike da dana sannin biyowa ta matatakalar sai dai haka kawai ta ji ra'ayin saukowar ta nan yau dan ta irga ko hawa nawa ne, sai dai abinda bata sani ba mugun wahalar da kanta ne ta shiga yi ta sauka a hawa na hudu bayan ta gama hada zufa ta duka ta cire takalmin dake kafarta cike da dana sani ta daga kanta ta kalli saman da ta baro tana tunanin ko dai komawa take ta biyo ta lft din?
Cijewa ta yi a hankali ta ci gaba da saukowa a bayane ta ja tsaki ta ce" Mutun shi ke kashe kansa dan neman fitina irin tasa! Yanzu da suka yi wannan hawan dan a ce masu me? Yanzun tsakani da Allah waye zai iya hawan nan a cikin gidan nan? Kawai kwaliya da barnar sumunti? Wannan ai almubazaranci ne na tabata wannan bulon zai iya yin wani gidan aman aka ajiye shi a matsayin na hawa a taka kawai....."
Tana mitarta ta idasa saukowa kasa ta daga kanta tana ajiyar zuciya a hankali ta ce" ni da matakalar nan sai a kiyama idan na je aljana na tarar da matakala mai sunna matakalaba wannan ba!"
A hankali ta idasa shigowa pankamemen Falon bakinsa sake gannin an cenza labulayen dake ciki an saka farare kal kal masu girman gaske da daukan ido
A hankali ta daga kanta tana bin dakin da kallo yana fitar da kanshin turaran wuta mai sanyin kanshi , ga sanyi yana ratsa ko'ina na falon kafin ta sauke kanta a kan sababin kujerun da aka zuba a tsakiyar falon suma farare kal kal kal, da irin yadda aka ajiye wasu dima diman po da flower a cikinsu jifa jifa su dinma kalar fari ya fi yawa a tare da su sai dan ratsin kalar blue mai duhu
A hankali ta dora kafarta saman kafet din da yake tsakiya wanda yake da girma sosai tana kallonsa mai wasu abubuwa a sama masu shige da kwai harma idan ta zo takawa sai ta kauce kafarta kar a je kwon ne aka jejera ta taka ta fasa dan yanzun ita ta dawo daga rakiyar masu kudi da yan gayu , ta gane cewa ba abinda ya gagare su, da kudinsu suke shagalinsu, barikinsu kuwa aljihunsu
A hankali ta juya wajen katon madubin dake ajiye
Idannuwanta ta lumshe a hankali ta dora hannunta a gefen fuskarta tana kallon kanta tamkar ita dince a ciki
Wajen idannuwanta ta tsurawa ido itama tana mamakin kalar idannuwanta, a cikin yam gidansu du haka idannuwansu suke tamkar na mage, na wasun su kuwa tamkar na aljanu domin ya saka ja mai haske kamar na mayu
Rigar dake jikinta ta bi da kallo, a hankali take sauke ajiyar zuciya ta kai hannunta ta shafa shafafen cikinta da yanzun yake bata mamaki a shafe tamkar bai tana tasawa ba, sai irin kirarta da sanadiyar shafewar cikin ta karra bayanar da kanta tamkar wata niki minaj ta bayan, blue din riga mai duhu sosai ce a jikinta , bata da kwaliya ko kadan sai dai budadan wuya ne da ita sanann hannayenta a dan bude suke kuma har kusa fa tsintsiyar hannunta, rigar ta bi lafiyar jikinta sosai ta kwonta mata har kasa sai yar tsagar da ta bata haushi ta ringa mitar du yadda ka yi da nasara sai ya nuna maka shi dan iska ne, sai da ya miko da dinkin zarensa ya kare?
Sai hular da ta saka mai haske a kanta wace ta haska kalar fatarta
Bata yi wani dogon kwaliya ba, dan lips kadai ta shafa a kan lips dinta sai kwalin da ta furta da kyar tana share kwallah da ta tarun mata, sai turaren da ta shafa sosai a jikinta wanda ya ratsata sosai
A hankali ta kai hannunta ta jikin madubin zata dora dan ta shafa madubin da yake birgeta sosai , a lokacin ta jiyo muryar Iman da Mah ta turo ta kirayeta ta ce" Munee aka ce ki zo deening"
Muneerath ta juyo da sauri gannin har tara ta yi su kuwa da suke kari tun takwas a tunaninta har sun gama sun haye sama shi yasa ta tsaya shiririta
Da dan sauri ta zagaya ta nufi deening din ,
Dan saurin da take ya saka lamarin bada kala sai ya zamana kafarta na motsawa wajen na yin hanyar da Kafar ta nufa, sai kaeai ta ringa aikata sitin saba'in ba tare dama ta san tana yi ba
A hankali ta dan rage tafiarta gannin Pah zaune, gefensa na dama HANJA, sai Mah sai iman
A dan sanyaye ta yi masu gaisuwar jimula bayan ta kara binsu da kallo a ranta tana ayana' yanzu Mah ta saka ni gaisuwar rungume rungumen nan ni kuwa walahi kunya nake ji'
Har zata zauna Mah ta ce" Hi girl, baki gaishe mu ba fa?"
Muneerath ta hadiyi yawu a hankali ta karasa kusa da Iman da ta fi kusa da ita ta dan rage tsayinta ta mana mata kiss a kuncinta tana yatsina fuska a ranta tana ta aibata gaisuwar nan ta zagaya ta yiwa Mah, lokacin ne kuma Hanja ya rike cokalin dake hannunsa da wani yannayi yana jin hankalinsa na tashi dan sam baya so ta masa wannan gaisuwar shima haka kawai baya so!
Sai dai ga mamakinsa ko Pah bata yiwa ba ta koma ta zauna da yaren hausa tana dan murmushi ta ce" Ai dai banda gardawa"
Mah dake kallonta ta yi dan murmushi dan bata san me tace ba aman da bata yiwa hanja haka ba ta ji dadi ainun har cikin ranta
Pah da ya gama ne ya fara mikewa yana fadin cewa meeting ne da shi tare da ministocin kasar , dama a shiryensa yake cikin suit dinsa ruwan ash mai duhu
Mah ta mike da dan sauri cikin shigarta na abaya ta fita a kujerar ta mayar da kujerar ta rufe ta bi bayansa da dan sauri, sai ya yi sauran Hanja dake zaine fuskarsa a hade da Iman da ta kasa tashi duda ta kare, sai Muneerath da ta gama hada dan abinda zata taba ta zauna abinta ta saka cokalinta tana dan ci, .....sai dai irin cin nan ne mai bayar da haushi domin tana ci ne tana dan buga cokalin a farantin hakan yake bada sauti
Da dan sauri Iman ta kureta da ido tana mata alamun ta bari, domin idan ana saman table ba kasafai ake surutu idan yana waje ba, uwa uba irin cin abincin nan na bashi haushi domin ya tsani idan kana cin abinci cokali na yawo a cikin plat dinka kwata kwatama cin abincin na dan lokaci ne da yake gannin babu fa'ida bata lokaci ana yi, shi da kansa dan shayin da yake surfing ne ya zaunar da shi
Muneerath da gaba daya take sha'aninta a ranta fadi take" Wannan mutun ba dai fari ba, kuma sai yana saka kaya baki , yanzu jalabiyar nan dama nasaruma na sakawa?"
Idannuwansa ya rintse dan tunda ta zo shi dai bai kaleta ba, ta kara bashi haushi da bata kawo gaisuwarta ba, da bata masa gaisuwa irin yadda ta yiwa su ba da farko yaji dadi aman daga baya sai ya shiga mamakin yaya aka yi bata yi gagawar yi ba bayan a kulun har haushin iman yake ji kamar mai jira safiya ta yi idan yana gidan ta rukunkume shi ba, sai kuma yanzu abin nan da take yi da cokali har tsakiyar kansa yake hawa kamar ya buga kanta da table din nan ta suma ya huta
Mah da ta dawo ne tana kallonta ta ce" Muneerath daina wasa da abinci ki ci ki gama, yayanku baya son ana hada cokali da plat kukan hakan na tayar masa da hankali"
Da mamaki muneerath ta dakata tana kakkon mah, kai, ya ilahi ta fada a kasan zuciyarta, dama maza na aljanu hala? Domin a gidansu akoy yayarta da ba'a wasa wuka idan tana wajen, ba'a gurza galan a kasa kuma ba'a gurza kwano a kasa, sannan ba'a cakal cakal da cokali a kwano idan dai ka mata haka yanzu zata fadi ta shigo bori irin na masu aljannu ta sume idan aka yi wasa a wajen
A hankali ta dubi Mah da yaren turanci ta ce" MAH HALA ALJANU NE DA SHI?"
A tare Iman da HANJA suka dago suka sauke dubansu a kanta
Kallon da Hanja bai mata ba na yana hanna kansa ya samu idannuwansa tsumu tsumu a cikin nata a lokacin da ta dubi tsabar idannuwansa take tambayar shi hanja Aljannu ne da shi?
"Innalilahi ya salam ya rab" shine abinda ya fito daga bakin Mah tana mai kai duwawunta saman kujera tana kallon Muneerath kafin da sauri ta kai dubanta wajen Hanja da ya mike rai bace ya.........
Sai fa ta haukata ka馃ぃ馃ぃ馃ぃ馃ぃ馃ぃ馃ぃ馃ぃ
11/14/21, 12:51 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
3锔忊儯7锔忊儯
Da sauri Mah ta mije tsaye gannin wajen ne yake nufowa ta juya gaba dayanta ta dora hannayenta saman kirjinsa ta tare da dukan karfinta tana kallon fuskarsa ta ce" Khalb me zaka yi?"
Hanja da zuciyarsa ke kunna yana kallon Mah ya datse lebensa na kasa yana tsaye kikam ya ga Yadda Muneerath ta zabura ta mike tana wuki wuki da idannuwa rai bace ya ce" Mah dan Allah ki miko min ita "
Muneerath ta zarro ido da sauri ta labe a bayan ta ki ta fito gaba dayanta duda labiyar ba wai ba'a ganninta bane domin Mah bata da baban jikin da zata iya boye na Munnerath a hankali ta ce" A miko masa ni kuma? Yo me na maka?"
Da sauri Mah ta kama hannunta ta bayanta ta dan matsa dan ta mata alamun ta daina magana idan yana yi, Muneerath ta dan saka kara tana kallon hannunta tana kallon yadda ya wani irin zuba mata idannuwan san nan ta turo baki tana kunkuni a kasa kasa
Mah ta kama hannayensa a hankali ta zaunar da shi saman kujera ya kasance sun sakata tsakiya shi da Muneerath din da sai da ta ga ya zauna kafin take maida duwawunta saman kujerar tana sauke ajiyar zuciya cike da tunanin to shi kawai haka yake? Ta kula kiris yake jira ya ringa hararanta ko dai haka kallonsa yake? Yanzun daga tambaya ai in ba haka bane sai kawai ya ce mata ba haka bane kau? Mtsssssss halaya sak irin na marar wayau!
Mah dake maida numfashi a hankaki ta karra dora hannunta saman hannun Hanja dake ajiye saman table din nan a sanyaye ta ce" Me yasa kake saurin hawa a kanta? Me yada maganarta kadan ke hasalaka??"
Hanja ya lumshe idannuwansa a hankali bai bata amsa ba , shi da kansa tambayar kan nasa ne yake a kan lamarin yarinyar nan, shi dai ya san a ba sa'arsa bace , nesa ba kusa ba,
Abinda yake bashi mamaki da yainyar nan ba wani dogon karatun da ya kamo nasa tayi ba na farko, na biyu ba wata mai shekaru ba, na uku ita ba wani irin yan matan nan masu tsaida numfashi ba bale ta ce dan kyanta take masa iya shege da shiga hanci da dukunkune, haka kawai ya sauka a kungurmin jeji ya kwasota ta zo ta hanna masa zaman lafia? Ya kula ko kallo bai isheta ba kamar wata tsiya! Shi kam ya shiga uku yana zaman zamansa sun dauko mahaikaciya
Muneerath dake dan bubuga yatsanta a hankali ta dago ta kale shi da kuma mah
Bakinta ta tabe ta kuma maida kanta kasa
Iman dake zarro ido cike da mamaki tana kallonsu gaba daya ce ta kai hannunta ta dafe kuncinta tana mai ci gaba da kallon nasu
Hanja ya kai hannunsa wajen gashin kansa a hankali ya ce" Yau za'a kawo tgr"
Mah harda su ajiyar zuciya kafin ta gyada kanta ta kuma sauke dubanta a kansa a hankali ta ce" Na mikk maka tea din ka gama sha ne?"
Bai kai ha bata amsa ba Muneerath ta mike abinta tana ayana bara dai ta shiga kicin ta da kokoya hakananma dan ta ga su a nan ba fadan ta bata suke yi mata ba
Kasa kasa ya bita da kallo har ta juya ta nufi hanyar kicin din sai kuma ta ja ta juyo da dan sauri tana kallonsa ta juyo ta taho da dan sauri hakan ya saka shi jin gabansa ya yanke ya fadi
Tana zuwa facing din Mah ta ce" Mah na manta ban fada maki ba, walahi ki binciki wannan yarinyar yar iska ce"
Ba Mah ba , shi da kansa da ya lumshe ido sai ya samu kansa da budewa tar yana kallonta
Iman kuwa cikinta ne ya bata wani irin kululu da sauri ta kalli Muneerath gabanta na dukan tara tara
Mah yannayin hankalinta ya nuna hankalinta a tashe yake tana kallon Muneerath ta ce" Daughter me yada kika ce haka? Wani irin iskanci kuma?"
Iman da sauri ta zabura ta mike tana kallon Muneerath ta ce" Mah walahi karya take min wannan yarinyar fa inaga bata da hankali fa Mah"
Wata uwar Harara da Hanja ya sauke a kanta ta yi gagawar zama hannayenta na bari hakama jikinta cike da tsoro da tashin hankalin ashe yana zaune ta yi magana muryarta sama sama har haka, da kuma tsoron abinda Muneerath din ta fada da yannayin da fuskar Mah ya nuna
Muneerath ta tafa hannu ta ce" Kai mutane, yanzun nice mahaukaciyar? Kin ga ban so nuna mata abinda kika ce na yi ba aman tunda ke ba yar kirki bace zan nuna mata ba sai kin kwaso cikinki ba ta kare a kaina ina daki......"
Cike da shiririta irin abinda ya sha kanta kaeai take son isarwa ta bar wajen ta juyo wajen Mah a sangarce ta ce" Mah, daga ce mata ga wanda nake sa ran ya zamo mijina muna magana ni da ita watau Dogarina ta ce meye Dogari? Ni dai na ki fada mata sai ta dauko computer ta tambayeta, computer ta fada mata sai cewa ta yi xata taimake ni, ni dai ina kallonta du ban gane ba Mah ba sai ta shiga wani abu irin na kwartaye ba?"
Mah da hankalinta ya tashi da yannayin da Iman cike da tsoron kar a je yarinyar wani mugun abu take aikatawa da bata sani ba, cike da tsoron kar a je ta dauko yar mutane tarbiyarta ta kakace bata sani ba a sanyaye ta ce" Wani abin take yi Muneerath ?"
Muneerath ta gyara tsayuwarta ta ce" Cewa ta yi wai na bude facebook a yi hotona na turo sama da kasa a dauka a turawa dogari"
Mah dake kallonta a hankali ta ce" Meye sama da kasa?"
Cike da jin kunyar Mah din Muneerath ta sosa gaban goshinta idannuwanta suka sauka a kan fuskar Hanja da gaba daya ya zuba mata ido da kallon hararan da bata san me ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 42