Share this page
burin aure watau sarki da mamana aka wuni ana min daria ana cewa mahaukaciya ce ni, daga karshe suka ce gwara na kama dogari marar galihu idan Allah ya tsaya min ya ji tausayina sai ya aureni, dan kuwa ba wanda zai so kirtitinar bak'a irina!, Saudat a dayan burina da na nuna ina son zama Hostess kishiyar mamana ta ce sai dai na zama karuwar yan gugan gidan jirgi idan na yi daraja, walahi a gaban Mamana ta fada sai kawai maman nawa ta yi daria tana fadin wa ya ga yar baka kirin, gaskiya Oga ya yi haihuwa a nan, a wannan ranar ce da abin ya min ciwo muka kidime da fada a gidan nan da yayuna domin aun samu abinda suke so, oga na zuwa ya raba mu aka fada masa komai ya ce du ubanda ya kara shiga harkata walahi zai iya yin komai, a ranar ne ya dauke ni ya biya min kudin koyon iyo, sannan yake bani yan kudade a kai a kai dan na yi yan bukatocina, ya ce koda ban zama ba na gwada" Muneerath ta dago da idannuwanta da suka cika da kwallah sosai tana kallon Saudat dake hawaye ta ce" Ashe nima zan ga ranar da mahaifiyata zata daga hannu ta dake ni dan gyarana? Ashe zan ga ranar da Umana zata titsiyeni kan na fada mata daga ina nake?, Ashe zan riski ranar da mamana zata daga dan yatsarta dan ina cikin damuwa?, Saudat a nan ake fada ni da fada mutun fiye da bakwai tana tsaye tana kallo ba zata yi magana ba bale ta shigar min , ashe dai mamana na cikin duhu ne ya sa na ga rayuwa irin wadda na gani.....? Ta karashe maganar da fashewa da kuka mai zafin gaske tana dora kanta a gefen kafadar Saudat har tana jijiga gaba dayanta dan abin daga kasan zuciyarta yake fitowa, daga cen kasan zuciyarta take jin wuyar abinda ke damun nata wanda take jin yana sakinta a hankali a hankali Karar bude Kofar ya saka su yin tsit da sauri Muneerath ta dago kanta Ido hudu suka kuma yi da mahaifiyarta dake dauke da wata babar jaka shake da dinkunnan atampopi da ta ringa dinkawa Muneerath din a lokacin da bata nan Cire dubanta ta yi a kansa ta karasa kuda da gadon Muneerath din ta yaye shinfidar sama domin ta yi dati sosai ta juyo wajensu muryarta a dan dake ta ce" Ku tashi ku yi wanka ku dauro alwallah ku gabatar da sallar la'asar kafin lokacinta ya shige, idan kun gama ku fito dakina ga abinci ku ci, so nake kuna gama cin abinci ku gyara dakin nan sosai ku wanke bayin ku cenza katifar Abdul ya tafi ya siyo sabuwa sai ku cenza wadinnan wandunnan dake jikinku ga atampa nan ku saka maza mu je saloon a maku kitso, kar na dawo na tarar da ku zaune a nan" Tana gama fada ta juya ta fice inda Muneerath ta bita da kallo cike da wani mamakin da ya kusa kasheta da farin ciki marar musaltuwa har sai da saudat ta ce" Kin ga tashi wollah kar ta dawo ranta ya baci kina zaune uwa sakarai".................................... RAYUWA KENNAN BAYAN KWANA SHIDA KASAR INGILA A tsakanin kwanakin nan sun gabatar da rayuwa cikin wani yannayin da basu saba ba sam Yaronsu dake gefensu ya zama gashi a cikin gidan aman kuma tamkar baya nan A tsakanin kwanakin nan ya yi tafia sau uku wace yake yin zuwa da dawowa bai kwana ko daya ba HANJA na acting tamkar ba abinda yake damunsa sakamakon abinda mahaifinsa ya yi masa, sai dai abinda bai sani ba bai taba gabatar da rayuwar nesanta kansa da su ba irin wannan Mah ta yi nacin bin, ta yi nacin kiran, ta yi fadan da tambayar shin lafiyarsa?, Sai dai a kulun amsar daya ce abubuwa sun sha kansa bashi da time Yakan kwatanta yin hira da Tgr sai ya samu kansa da mamakin kansa da tunanin to amsa zara bashi ko me? Sau biyu yana yarda da haduwarsa da yar gidan minista sai dai abin takaicin yarinyar sam bata da ra'ayi nata na kanta, ko zance suke abinda ya gabatar shine gaskiya koda da gangan ya gwada nuna mata akasin tunaninta takan zubar da nata tunanin ta dauki nasa, a haka ya nuna mata yana da butakar kwonciya da ita abin mamakin ita ta kama masu waje ta gyara komai sannan ta ringa zumudin irga lokacin da ya rage ya kwonta da ita Wannan lamarin ya daure masa kai, sai kawai ya girgiza kai yana saka nimbobinta a black list yana jin takaicinta tare da tuna yarinyar da koda wasa ya nemi taba mata hannu ko a cikin malagigin wuya na tsoro take in dai hankalinta na jikinta sai ta bige masa hannunsa tana jaraba Kai koda da gangan take yi hakan na birge shi, hakan na nufin ba zata iya gagawar yarda da namiji ba koda kuwa saurayinta ne Aman ita gashi soyayar bai rigaya ya furta mata ba, yana dan kulata ne yana auna magangannun soyayarta da take nuna masa aman a haka ya nuna mata zai kai keyarta kasa ya yi wasan kura a jikinta ta aminta harma take zumudi? Walahi sai KYANKYAMIN HALAYA IRIN NA MAZINATA ya darsu a zuciyarsa, watau su basa kyamar wutsiyar kowa kuma basa auna da wa zasu kasance da irin lokacin da ya kama a gabatar da abin? Burinsu a taba su kadan su bude sket kowani kazami ya danna kansa a ciki? Su basu da fid茅lit茅 ? Kowama nasu ne, a kan yan kudade sai su yi, haka kuma a kyauta sai su yi? A yanzu da yake zaune saman bed dinsa karfe bakwai ne na dare yana kallon waje daya ba tare da ya san wa yake kallo ba Tunani ya yi masa yawa, ya kasance mai yawan tunanin abinda bai san dalilinsa ba A hankali ya dauki katuwar wayarsa ya shiga wajen vidio dan ya yi kallo ko zai samu abinda zai dauke masa damuwarsa duda shi din ba mutun bane mai son yawan kalle kalle Vidio din da ake ta turo masa sunna bude kansu ta whatsup ya shiga bi daya bayan daya wa'inda ba wani mahinmanci sai kawai ya goge A haka har ya sauka kan vidion birthday dinsa da Mah ta yiwa su Muneerath ta tura masa A hankali yake kallon abinda suka yi, wani lalausan murmushi ya samu damar sauka a kan lalausan lebensa a lokacin da suke dirkar rawa , inda rawar ta fi yawa a kanta Wajen da ta kykyace da dariyatana shafawa sauda crem ya samu kansa da maidowa koda ya wuce A hankali ya ringa murmushin shima yana dafe daidai zuciyarsa Idannuwansa ya lumshe yana tunanin idan bai ganta suka yi rigima ba ba zai iya rintsawa ba Zai iya rantsewa bai taba jin missng din mutun irin yadda yake missing din yarinyar nan Ba shi kadai ba har a wajen aikinsa sunna missing din yarinyar bale a nan gidansu Da murmushi ya yi a bayane ya ce" kanwar da nake son samu ce ta fito min daga africa, me take yi? A ina take kwonci? Me take ci? Da wa take hira?, Ya zama wajibi na saka a sakata cikin masu tahowa zuwa indonesia" A hankali ya mike daga zaunen da yake da wayarsa ya fito Yana saukowa ya hango su zaune saman diner, a kan dole ya nufe su domin sun rigaya sun ganshi Da kallon kula suke binsa har ya zauna a gefensu Fuskarsa ba fara'a a yanzunma haka kuma da Mah ta gabatar masa da abinci sai ya nuna a koshe yake Pah da yannayin taurin kan yaron nasa ke damunsa tamkar wani DUTSE yana jin duka ya ki ya rugurguje ne ya ce" Dazun mun yi vidio call da Muneerath" Da sauri ya dago da dubansa, cikin gagawar magana ya samu kansa da fadin" yaya take, a ina take, me take, su waye suke tsaronta, tare da su wa take, Attahir dai yana kasar nan shin yana damunta da kira ko?............." Sai kuma ya yi zuru zuru yana kallonsu , sai da ya gama magangannun ya ringa aunawa a ma'auni Jikinsa a mace, idannuwansa sun dauki launin ja ya samu kansa da furta" NA SHIGA UKU" 馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀 *SAKO ZUWA GAREKU MAKARANTAN DUTSE, IN SHA ALLAH POSTING ZAI DAWO SAU BIYU A SATI, WATAU LITININ DA ALHAMIS SAKAMAKON NOVEL DINA NA KUDI MAI SUNNA WATA KOKOWAR DA ZAN FARA POSTING RANAR LITININ IDAN ALLAH YA AMINCE, NA GODE SOSAI DA KULAWA.....DOMIN SAMUN NAKI KO NAKA KA TUNTUBENI A NUMBER WAYATA KAMAR HAKA +22793811618, A FARASHI MAI SAUKI NAIRA DARI BIYU 200...... IN SHA ALLAH ZAKA SAMU NISHADI DOMIN SALON NA DABAN NE* DAGA YAR MUTAN NIGER sajida馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ 11/14/21, 12:53 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 5锔忊儯5锔忊儯 Murmushi ne kwonce a kan fuskar Pah, inda damuwa ta bayana a kan fuskar Mah A hankali ta kamo hannunsa tana kallonsa da kula ta ce" ba fa faduwa bane dan ka yarda cewar kana cikin soyaya, Son ba faduwa bane dan ka yi kokarin gyara soyayarka, sam bana so ka zamo mai wasa da damarka , Son idan ka yi sake da maganar Muneerath bana tunanin in ta juyar da muradinta ta yarda da shi a kan wani in zaka iya karkatota ta dawo gareka, ka ga , ga number mamanta wace na samu tun a daren da na yi rashin lafia da kuma number mahaifinta, numberta ta cen ce a wahen Pah dinka na yi na yi ya bani ya kiya ya ce sai ka nuna kana so da kanka, plz Son kar ka rikita ni , damuwarka na damuna fiye da tunaninka" Idannuwansa dake lumshe yana jin gaba daya magangannun mamansa na samun matsuguni a cikin zuciyarsa kafin ya kaleta a hankali yana karra karantarta Kansa ya maida kan mahaifinsa da ya ga shi yake kallo kafin ya dan yi gyaran murya a nutse ya ce" Pah, maganar taron nan naku da Allah ka halarci abinka, ka ga inada tafia a satin nan mai yawa plz" Hankalinsa ya bashi kacokam duba da magana ce mai mahinmanci wace yake so ya halarta taro ne na manyan sarakai da matansu da zasu halarta a cikin satin nan , tunima sunna kasar shine bai basu lokacin zama da su ba, kuma so yake a yi zaman da Hanja aman yake son kara zile masa kamar yadda ya saba, shi kam bai san dalilin da ya sa HANJA ke zilewa sarauta ba, wannan abin na hadasa masa ciwon kai da zafin kai mai tsanani, Hanja shine kadai gareshi kuma da shi kadai yake takama, shin yaya zai yi ya taro shi ne? Dukkan hanyar da zai bi dan ya ginar da shi ita yake bi, ko ba maganar rashin lafiyarsa dole zai bashi kujera ya hau ya gabatar da nasa zamanin, shi yasa daga ranar da ya ga yarinyar nan ta saka shi magana ya ringa farin ciki A yanzu haka idan abu ya shafeta irin yadda yake magana fiye da misalin yadda ya saba ke saka shi tunanin tabas wannan itace wace zata budi bakin birkitacen yaronsa ta koya masa magana da kowa , ba halaya na yadda ya ga dama ba bayan ahi din sarki ne wanda dole zai saurari al'uma, a yi mulki a yi isar a kuma tausayawa talakawa Dan haka yau zai cenza masa ya fara zuwar masa a kaisashe dan ya ga kuma yaya zata bada, dan haka sai ya kure shi da duba a kausashe ya ce" Saurara Hanja, wannan tarron ba shawararka nake na ba, umarni ne na baka kan kai zaka halarce shi! Dole ne kuma kai zaka halarce shi, idan kana so ba a satin nan ba kana iya saka rana ka halarce shin, fa wayata nan ka cire numbobinsu su hudu ne, idan ka saka rana sai ka sanar masu da wajen da kake ra'ayin ku yi tarron!" Yana gama fada ya ajiye wayar ya mike fuska a hade ya yi gaba Da kallo suka bi shi su dukansu kafin Mah ta dubi Hanja Sai da gabanta ya fadi gannin irin bacin ran dake kwonce a saman fuskarsa Ta budi baki zata yi magana ya mike a fusace ya juya ya nufi kofa hakan ya sa ta mike tsaye da sauri tana kallonsa har ya bar falon gaba daya A hankali ta zauna tana dan dafe cikinta dake mugun murda mata kasa kasa sai kuma ya saka tana lumshe idannuwanta A hankali ta bi hanyar da Pah ya bi da kallo tana mai tunanin Me ya yi haka? Me yasa bai bari ta lalaba shi ba kamar yadda ta fada masa cewar ya barsu ta lalaba abinta zai halarci tarron? Me kuma ya sa ya ce da ita tare zasu gabatar kuma yanzu ya nuna Hanja kadai zai gabatar? Kanta ta sada tana dan barin jiki na irin murdawar da cikinta ke yi har ya lafa kafin ta mike a sanyaye tana jin yadda jikinta du ya mata wani irin nauyi Hannunta ta mika ta dauki wayar mijin nata a hankali ta shiga contact dinsa Sunnan da ya yi svng din number Muneerath ta kuma maimaitawa tana murmushi watau shi har ya ganta a matsayin matar yaron nasa ko? Domin da Wife LION ya saka sunnan A hankali ta dannawa number kira ta karra a kunnenta Maimakun ta bi ta lft sai kawai ta bi ta wajen matatakalar tana takawa a hankali har aka daga kiran Salamar da Munnerath ta yi ya saka Mah dan zarro ido tana murmushi ta ciro wayar daga kunnenta ta kuma maidawa a sanyaye ta dakata ta amsa salamar kafin ta ringa sakin murmushi na irin murnar da ta ji Munnerath na yi tana ta tambayarta yaya gidan me suke yi? Tana missing dinsu, sai dai sam bata ji ta tambayeta mutumen da take so ta fara tambayarta shi kafin ta tambayeta kowa A sanyaye Mah ta ce" My baby, yaya gida, ina mamanki, ina Abunki da yan uwanki? Ina kowa da komai? Yaya garinku?" Muneerath dake kallon mamanta tana murmushi wace ta tsaya a kanta da muciya kan walahi idan bata murje miyar yodon da ta kada mata ta kadu da kyau ba sai ta muka mata muciyar nan, inda Saudat ke kwasar dariyar scene din, domin a yau a kicin din mamansu Muneerath din suka kusan wuni a kan girkin tukakiyar shinkafa da miyar yodo, ana yi ana sakewa ta sha dunguri da rankwashi, ta sha wani irin daurin zani sai zufa take tana ihun ta kone maman nata kuwa tana tsaye ta yi murmushi ta sha murrr sunna girkin su uku , sai yan kannenta yan mata biyu da aka saka barar tafarnuwa ne, gyaran daki da wankin bayi Amsawa take tana cewa mamanta " Mamanmu Mah dina ce " Murmushi ta saki tana kallonta, domin labarin Mah , da Pah, da Iman, da HANJA har gajiya take da sauraro ba dare ba rana Wayar ta mika mata sai dai ita bata iya turanci ba, Mah kuwa french din nata ba mai tsayi bane hakan ya sa sai gaisawa kawai suka yi a rarabe kafin Munnerath din ta amsa Mamanta na cike da mamakin wai dama da gasken da sarauniyar ingila suka gaisa? Da gaske sunne suka rike mata yarta haka? A hankali Muneerath dake daria ta dan fara ragewa tana sauraron Mah A hankali yannayin tashin hankali ya fara bayana a kan fuskarta a raunane ta ce" Mah, dama Pah bashi da lafia aman na zauna da ku ban taba fahimtar hakan ba?, Mah dama kuma kunna da damuwa bayan kun malaki komai na rayuwa dama kunna iya neman wani farin ciki ku rasa?" Mah ta yi dan murmushi tana lumshe idannuwanta domin ji take cikin ya fara motsa mata Sai da ya sasauta mata a hankali ta ce" Muneerath kowani bawa da tasa irin kadarar, You see my baby a haka da muke ciki da za'a ce mu miko komai mu wayi gari Pah ya samu lafia, my boy ya ajiye aikin tukin JIRGI ya dawo ya yi aure ya haifa min yan jikokina da zan iya rantse maki ko baya ba zamu duba ba zamu saki sarautar Ingila" Da wani mamakin Muneerath ta ce" Mah, dama bakwa So sir na tukin jirgi? Tukin jirgi fa mafarkinsa ne, abu ne da ya fi kwarewa a cikinsa, aiki ne wanda idan yana yinsa yake cikin farin ciki, idan ya bar aikin nan wane kuke so ya kama?, Kuma aure yana da yan mata fa ku masa jan ido ya fitar da mace ko ku masa na dole" Mah ta yi murmushi a sanyaye ta ce" Baby kin san wanenen HANJA?, Allah ya yi shi mai daraja a cikin bayinsa, domin sarakai sunna da daraja sosai yarinyata, HANJA shine yaro daya kwal da ahalin sarautar babar masarauta ta duniya watau Ingila ta malaka, babu maganar tirsasa Hanja a aikata komai sai dai mu rarashe shi, Hanja yana da dama , yana da mulki mai girma wanda ubangiji ya halice shi a cikinsa, Tuki, aikin karfi ko wani iri ne dan nema ko dan sha'awar hakan ba na HANJA bane, HANJA yana da obligation na al'umar kasarsa, Hanja yana da abubuwan da suka zame masa tilas wa'inda suka daki burinsa, da sha'awarsa suka shigo a duniyar dolensa, My girl HANJA bashi da zabi yana aikin tukin jirgi ne dan mahaifinsa na so ya cakudu da al'uma ya koyi rayuwa da su, Sai dai kashhhh a yanzu haka maganar da nake maki mahaifinsa a yau ya taka da kafarsa ya je ya buga takarda da tambarin masarauta da sunnansa a matsayin wanda ya saka hannu dan dakatar da shi aikinsa, ba zai kuma yin aikin da ba nasa ba, komai sonsa da tuka jirgi ba zai iya fita daga gidan nan ba, baby i'm afrd, ina cike da tsoron abinda ke iya faruwa a yai a cikin gidana, Pah dinku ya dauki zafi sosai ya dadauki matakai masu tsaurin gaske wa'inda na so ya barni na lalashi Son na dora masa nauyin da ba zai iya zubar da mu ba, sai dai bai bani damar ba ya karra dora masa wani hawan jinnin wanda nake cike da tsoron abinda ke iya faruwa, kina gani wai fa ya bada dokar kar a bar Son ya fita daga PALACE" Muneerath dake saurare kanta ya daure, ta kasa gane me yasa Mah ke mata hira irin wannan ta sirrin gidansu kai tsaye, ta rasa gane me yasa mahaifinsa ke son tirsasa shi, lalle ta ji bashi da lafiya shi yasa yake aon hora ahi zama sarki aman a ganninta a barshi ya yi tukinsa mana?, Lalle yau akoy rigima a gidan nan, ita da kanta ta sani, aman kuma maganar sai ta mata nauyi sosai ta kasa tantance ita me zata ce a nan? Aman kula da ta yi cewar kamar Mah na mata hirar ne dan ta ji sanyi sai a sanyaye ta ce" Mah, in sha Allah ba zai tada hankalinsa ba" Mah da ta ci gaba da tafia ta fara zufa sosai na irin murdawar da cikinta ke yi mata a hankali ta ce" Dole zai yi fushi, dama yana cikin bacin rai da rudani na zuciya, Baby he is in love but ya kasa admettre harma ya kai ga abin sonsa" Haka kawai ta ji jikinta ya karra yin kalau tana kallon yadda mamanta da Saudat ke kallonta domin tun cenzawar yannayinta mamanta ta rage gaz sosai suke kallonta sai kuma irin maganar da ta yi cewar Pah ba lafia ya saka Saudat fahimta ta dan kwatantawa mama a sanyaye shine suke jira ta gama wayar A hankali Muneerath ta kuma cewa" Mah da me zan iya taimaka maki?, Idan ina yin koma menene dan na taimaka maki ki sanar da ni ba tare da jin wani abu ba, domin a rayuwata kin min rana, Mah kin ga kafin na hadu da ke ban san dadin uwa ba, ban san komai na mahaifiya ba, Mah a kanki na fara sannin kula, da nasiha irin na uwa, Mah a dawowata na tarar da mamana ta dawo hayacinta har yanzu nima wai nice na iya dafa shinkafa na iya abubuwa irin na mata? Mah kin ga.........." Sai kuma muryarta ta sarke ta dan fara shashekar kuka ta ce" A dawowana mamana ta ce min Haba Muneerath ki ringa adu'ar samun dace da miji na gari ba wai ki ringa adu'ar Allah karkato da hankalin dogari a kanki, Mah a da fa ita ce ta ce min dama dama dogari ko zai so ni?, Daga ranar nan na san cewa bawa baya yanke rai da rahamar ubangijinsa" Mah ta lumshe ido tana sakin murmushi da bayanan Muneerath, a hankali ta ce" Ina murna da murnarki my Daughter, ina matukar farin ciki da farin cikinki, plz ki daina kuka kin ji?" Muneerath ta gyada kai tana ta murmushi a hankali tana jin yadda Mah ke shasheka kamar ta yi gudu ta ce" Mah wai motsa jiki kike?" Mah ta ja numfashi ta sharce zufa da kyar ta idasa hawa gaba daya ta kara dakatawa tana lumshe ido kafin ta nufi dakin Pah a hankali muryarta ta yi kasa sosai ta ce" Baby, zaki min wata alfarma?, Plz zaki taimakeni ki min wata alfarma?" Muneerath ta amsata tana sauraron tana dan kwankwasa dakin Pah, sai kuma ta ji shiru da dan mosti kadan Dan jim kadan sai kuma wani bugawar da karfin gaske ya shiga kunnenta wanda ya sakata saurin cire wayar a kunnenta Mah da ta juyo a figice ta sauke dubanta a fuskar yaronta ta gansa da wani irin bacin ran da bata taba ganninsa da shi ba kafin ta ankara ya daga hannunsa rai bace ya kuma mugun doka kofar mahaifinsa wanda ya zo zai bude jin bugawar da karfi ya saka shi budewa a hanzarce dan sannin cewa lafia ba wanda zai matsa mugun bugu irin haka Da sauri ya bude yana bayana gaba dayansa yana sharce ruwan alwallar da ya dauro ya sauke dubansa a kan yaronsa wanda sai da ya ji gabansa ya fadi da yannayin yaron nasa da kuma matarsa dake gefe wada ya kasa fahimtar halin da ita take ciki Rai Bace HANJA ya dube shi ido cikin ido a kausashe ya ce" A kan wani dalili zaka dauki irin matakin nan da rayuwata?" DOMIN SAMUN NAKI LABARINA MAI SUNNA WATA KOKOWAR KI TUMTUBENI TA NUMBER WAYATA KAMAR HAKA +22793811618. A KAN FARASHI MAI SAUKI IN SHA ALLAH 200 DARI BIYU TA TRANSFER KO KATIN MTN.........na gode masoyana sai kun zo 11/14/21, 12:53 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 5锔忊儯6锔忊儯 Da sauri Muneerath ta zarro idannuwanta tana saurare da sauri ta gyara tsayuwarta tana karra nutsuwa Pah ya fuskance shi a dake ya ce" Dan ni na haifeka, kuma dan na isa da kai, haka kuma dan kai din SARKIN kasata ce ya zama dole ka dauki mulkinka!" Wani irin duka ya kaiwa kofar dake bude hakan ya sa ta bada

Chapter 32 of 42