cike da tunanin me zai kaita gida? Abu daya dai da ta sani shine a yau idan ta je gida yayan gidan oga sai ta fasa kan kowani shege, dan ta tabata sai sun mata dariar da suka saba
Muryarta kasa kasa ta ce" Kar ka barta ta tafi聽"
Da sauri ya juyo jin muryar mamansa gaf da su, idannuwansa ya zarro ya kuma damkar hannunta zai maida ita wajen zaman ta tirje tana kallonsa ta cenza harshenta zuwa larabci ta shiga magana a sanyaye tana watsa hannayenta ta ce" Allah fa ta ce ya tsaya mata, cewa fa ta yi Allah take fadawa ya cika mata burinta, haka fa ta ce bata wasa da buri akan karatunta, zuwa fa ta yi dan ta ga makarantar ta tsinci kanta a ciki, shin wannan bai zama babar hujar da ta isa a rike dan a kamawa yarinyar nan ta kai ga cinma burinta na son kasancewa Hotteste ko kana cikin manyan da suke da damar talafawa talakawa aman kuma suke take su sunna karra murje su dan basa son su ga sun ci gaba?聽"
A hankali ya kamo hannunta dan so yake ya zaunar da ita ko zai gabatar da aikinsa sai dai ta ki basi dama, a hankali ta fara yar gargadar murya irin hawaye fa zata masa a nan gashi yarinyar nan mahaukaciya sai ihun a bude mata ta fita take masu a sanyaye ta ce" kai ne fa uban talakawa, sarki mai taisayin talaka ne koda ba a kasarsa ba, kai ne fa Allah zai tambaya yaya ka tafiar da naka ikon? Kaine fa ya dace ka talafawa du wani wanda ya kasa ,"
A sanyaye ya ce" Mah, kar ki yi kuka mana a kan wannan, kin ga aikinmu yana da tsaurin gaske, sun taka doka ta hanyar daukan yarinyar nan bayan bata da cikakun takardun da aka saka dokar sai da su, ni ba dan tana daukan horo kyauta ba, ko daya, sai dan bata bi tahanyar da ya dace ace tana nan ba, mama bata yi makarantar hoton girki ba, bata yi ta horon ruwa ba, bata yi ta horon tafia ba, ta ina zan iya kyale haka?"
Aleesa ta dan fara daga muryarta dan ita fa so take tun yanzu ta fara tankwasa shi ta faa ganewa idannuwanta ya yi act irin na saraki a kasar da ba tasa ba dan haka ta dage kai da fata ta ce" kai zaka tsaya mata, kai zaka cike mata takarduntata hanyar sakata ta koyi girkin a makarantar daya dace"
Gashin kansa ya dan yamutsa yana dan dama bai fito da su ba ya ce" Mah ta yaya? A yanzu idan na saka kaina a wannan rigimar ina cikin matsala nima dan kuwa cewa zasu yi na take dokar da na dora, Mah ki fahimta zan bata makudan kudaden da zara tafi ta yi abinda take so da su, aman idan kika ce a yi haka ban san ta ina zan fara ba"
Mah ta juya tana kallon Muneerath da ta juyo ta nufi wajen su Ameerah da sukai tsuru tsuru ita da sir
Murmushi ta yi ta ce" Bana tunanin idan kudinka zai saka ta ajiye burin aikin nan, aman me zai hanna mu yi wani abu? Ban ki ka katanta mata maganar kudin ba, idan har ta zabi ka bata kudin a kan aikin nan bani da ja, bt idan har ta zabi aikin a kan kudin zaka yi du yadda zaka yi dan ka kama mata, ciki kuwa koda a nan ba zai yiwu ba mu tafi da ita"
Fuskarta ya kurawa ido, a duniya wannan mata tana da karfin iko da shi, tana dora abinda take so koda baya so kuma ya ji ya gani dan kuwa babarsa ce yana son abinsa baya tunanin akoy abinda zai sa ya mata rashin biyaya,
Matsawa ya yi kusa da ita sosai ya rage tsayinsa a hankali yakai lebensa kan goshinta ya mana mata kiss kafin ya ciro fari kal din papier a hankali ya shiga goge mata yan kananun hawayenta da ta fitar da rigima kafin ya jimke hannunta ya maida dubansa kansu sunna faatawa dayaren hausa shi kuwa baya jin yarensu abinda dai ya fahimta sojojin dake tsare da kofar take nunawa tana magana tana hade hannayenta
Lebensa na kasa ya cije cike da tsaa yadda zasu kwashe da su baki dayansu, dan kuwa shi ya tabata ko a kasarsa kasar arziki da wuya ya nunawa yarinya irin kudin nan ta wani zabi wai aiki bale a nan!, abinda dai zai so shine kafin ya salameta da kudinta sai ya koya mata hankali! Uwa uba masu gidan nata da suka dauketa a kan tsarin da ba shi ba, su da kansu a yau zai mayar da su terrain! Zasu koma bakin aikin cikin jirgi daga Ameerahn har sir din, dama shi mai kula da tafiar da aiyukan Hottest ne a cikin tafiar jirgi ci gaba ne ya samu aka bashi wajen nan na horo, ita kuwa Ameerah tsohuwar hoteesss ce da tayi yawon kampaninika daga karshe itama ta samu mukamin nan ta sauko kasa, horon da zai masu a yau shine ya mayar da su saman su koma su kara daukan lesson kafin su sauko su ba wasu lesson din
A hankali yake nufarsu Aleesa na biye da shi itama a hankalin , a kasan zuciyarta kuwa adu鈥檕鈥檌 take yi kan Allah ya sa kar yarinyar nan ta bata kunya, ita so take ta ga yaronta na taimako, so take yaronta ya kasance daya daga cikin manyan mutanenmu masu talafawa yaa sunna taimaka masu wajen gannin sun tashi suma sun zama wasu gobe, ya kasance mai tausayin talaka mai talafawa matasa masu zuciyar yi
Yana karasowa du suka yi cirko cirko sunna kallonsa, sai a yanzu muneerath ta bi hannunsa daa dake dunkule da kallo
Allah bata shirya ba ta hadiyi wani dunkulalan yawu kafin a hankali ta labe a bayan sir dan kuwa wani tunani ya zo mata yanzun idan ya kima mata hannun nan nasa ai ya kasheta ya kare, gwara ta labe a bayan freind duda ta ga sai fada yake mata kan kar ta kuma yin magana idan wannan na waje wai shima mai gidansa ne, in ba sir ba ai shi yake mai gidansa ita ai bata sanshi ba dan haka ba mai gidanta bane sir shine mai gidanta, baban bakin cikinta ta fita ta ga babu dogarai, kai yau da sai ta tada hankalin kowa a wajen nan walahi!
A dake ya budi bakinsa bayan ya ba kansa hakuri da lalashin zuciyarsa sannan ya jure irin magangannun da yake ta yi a yau a yanzun nan ya ce"
11/14/21, 12:47 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
2锔忊儯1锔忊儯
Ya ce聽" Zo nan "
Irin yadda ya yi maganar da sauri Sir da Ameerah suka matsa dan gabansa kadan suka wani irin nutsuwa sunna jiran jin abinda zai ce
Sai da ya kare karantar yannayinsu kafin a nutse ya ce" milliard goma ko aikin hostess " (SORRY, da yawa zasu ga ina rubuta Hotteste, da yaren faransanci haka ake rubutawa , da turanci kuwa Hostess, ina fatan kun fahimce ni duka kalmar daya ne)
Kallon junna suka yi kafin a nutse sir ya ce" ka yi hakuri sir, ban gane ba "
Shiru ya yi bai yi magana ba, sai Aleesa ce da ta shaka jin ha milliard goma ya saka dan ta bar maganar cike da jin haushi ta ce" yana nufin ta zaba tsakanin aikin ko kudin "
Ido ameerah ta kwalalo cike da mamakin furucinsu, da kyar ta iya hanna kanta doro tambayar dake kan lebenta dan ji tayi dama ita ce? Aman ko yanzu fatanta yarinyar nan ta yarda kudin su biyo ta hannunta Allah sai inda karfinta ya kare dan kuwa sai dai su ci tare
Shi da kansa jikinsa ne ya mutu, Munneraht dai yarinya ce karama, gata budurwa, yan matan yanzu da wasun a kan waya suke rasa darajarsu ta mata bale ita buri ne sama sama wanda da yawa sunna tashi da burin abu kalilan ke saka su sakinsa ya bi iska? Ya gama sakawa ransa cewa zata yarda ne da maganar kudin nan bama sai an yi jayaya ba, kai dama ba鈥檃 tura shi tambaya ba kawai a bata ta tafi dan kuwa baya tunanin zata ki amsa
Aleesama jikinta ne ya mutu, gashi ta rigaya ta zartar da hukuncin ta yarda kuma da haka, sai take ji a ranta damanma kai tsaye ta bashi umarnin da ta san ba zai taka ba, damanma ce masa ta yi ka shige gaba ta zama wani abu, aman a yanzun ita kanta ta tabata yarinyar nan ba zata bar kudin nan masu yawan da idan ta malake su ta zama sahun hajiyoyin garinmu ba ta dauki wani aikin irin na masu rabon kayan jus da sauransu a cikin jirgi ba
Hankalinsa ba a kwonce ba ya tsaya a gaban Muneerath da take kawar da kanta a duban wannan mutumen, ita walahi haske mata ido suke daga shi har matarsa da yake runguma a gaban mutane dan rashin ta ido
A sanyaye ya ce " Muneerah, sir ne ya aiko ni ya ce ki zaba cikin milliad goma da kuma aikin Hostess? "
Hankalinta ta bashi sosai ta daina hangen hanyar waje dan kar dogarai su tafiarsu baa samu wanda ya kyasa ba ta ce" Ban gane me kake nufi ba Freind"
Sai da ya hadiyi yawu jin tace masa freind a gaban su ya kara cijewa ya ce" yana nufin idan kudi kika zaba shi za baki Milliard na kudi har goma, idan kuwa aikin zama Hostess kike so zai baki"
Jinninta ne ya fara gudu hakama tunaninta, nutsuwarta ta bashi sosai kafin ta budi bakintatana nuna masa yan yatsunta ta ce" Milliard? Daidaidai har goma? Ka kuwa san me yake bada milliard? Millions dubu ne zai bada milliard, to shi din a ina zai sato kudaden nan?"
Da freinch suke magana hakan ya sa Aleesa bata ganewa aman shi Hanja yana gane dukan abinda take fadi
A dakensa yake dai yana kallon gefen da Aleesa ta bada dukkan nutsuwarta
Sir ya ce" eh haka ne "
Gaban goshinta ta dafe cike da wani yannayi shi ba na takaici ba , shi ba na neman ta fashe da kuka ba
A hankali ta ce" su din basa jin hausa ne? "
Sir ya dubi wajen da ta nuna, a sanyaye ya gyada mata kai
Bai aune ba ya ga ta nufi wajen su Aleesa dake binta da kallo, tsayuwarta ta gyara tana kallonsu ta tataro dukan turancin dake kwakwaluwarta tana dubansu ta ce" kun kuwa san shekara nawa na dauka da wannan burin a zuciyata? Ha Allah nake fadawa ba dare ba rana sai na ga alkhairi idan na kwanta da abin a raina a cikin mafarkina, a haka nake karra kwonciya ina tashi ba dare ba rana, kun san saboda na yi shi nake hanna kaina ci da sha dan na je na dauki karatu?"
Yan hannayenta ta nuno still tana kallonsu da kwayar idannuwanta irin na mage ta ce" Hannayena sun yi kunna fiye da a irga dan na koyi girki, ban samu na koya ba, kun san a ina na koyi iyo? A tafkin garin nan mai dauke da kada da manyan kifaye da macizan ruwa da komai dakomai na kasan ruwa, a haka na nutsu na sha ruwan nan kafin na iya iyo!"
Ta langwabar da kanta ta ce" shine kake son siyan burina da kudi? Ba zan iya siyar da shi ba, bana tunanin ko jirgin da nake hangowa a sama ka damka min zai sayi burina , ni burina na zamto Hostess "
Da wani irin admiration Aleesa ke kallonta, a hankali ta juya zata koma hanyar fitar dan ita fa sun gama bata mata rai, sai dai ji ta yi an rike mata hannunta raf da wani lalausan hannu
A hankali ta juyo dan gannin ko waye idannuwanta suka sauka a kan fuskar wannan mata mai kyan aljannu tana mata murmushi da hakoran makanta masu kyan gaske sai walwali suke abinsu
Gilas din dake idannuwansa ya cire ya sauke a kan fuskarta, tunda abin nan yake faruwa sai yanzu ska yi ido hudu domin itama a lokacin ta dago da dubanta dan ta kale shi suka yi ido hudu
Gabanta ne ya kwonci kwonci ya wani irin tsinkewa ya fadi da sauri ta cire dubanta a cikin nasa lokaci daya kuma ta samu kanta da karanta dukan ayar tsarin da ta Sani tana tofawa ko zata ji faduwar gabanta ya daina
A hankali ya kai idannuwansa gefen kunnenta , gashin dake kwonce tamkar na jariri ya taurawa ido shi kansa bai san me yake kallo ba,
Cire dubansa ya yi a nan din ya maida kan Aleesa da ta tsura masa ido tana kashe shi da murmushin kauna cike da matsananciyar kaunar yarinyar da irin abinda ta fada din
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya saki hannun Aleesa ya juya kasa kasa ya ce" nan da minti talatin zamu tashi destination Ingila!"
11/14/21, 12:47 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
2锔忊儯2锔忊儯
Murmushi Aleesa ta saki ta janyo hannun Muneerath dake biye da ita ba dan komai ba sai dan bata so ta janye hannuntada karfi ta yi mata sartse duba da laushin hannun matarsa ita kam ta janyowa kanau ya kashe su baki dayansu a kanta, aman in ba dan wannan ba ita ai so take ta yi ta koma ko zata dace da dogari daya
Da sauri sir ke biye da shi da takarda yana rubuta dukan abinda ya fada a rarabe ba wani a fayace ba, shi dai burinsa su rabu lafia
Sosai jikinsa ya yi sanyi a lokacin da ya ji an tashe shi a wannan waje da yake, sai dai a lokacin da ya ji cewa a gabanan aikinsa zai dawo yawo tare da hanja ne sai ya samu farin ciki maimakun bakin ciki, dan haka nan da nan ya koma office dinsa ya bugawa mahaifin Muneerath waya ya sanar masa abinda yake faruwa a ruffe, dan an shaida masa ne kawai za鈥檃 yi tafia da ita kasar ingila dan ta fara aikinta
A mamakance ya ce" wai yar ogan? To aikin ma meye kuma? Jirgi ne yar oga zata taka ta daga?"
Sir ya bashi tabacin hakan ne, mahaifinta maimakun ya zaburo ya zo ya duba, ya ga yarinyarsa sai kawai ya tayata murnar hakan ya ce a hada su a waya
A lokacin da ya karaso da gagawa ya mikawa sojan dake tsaye ya kusa da motar da Aleesa ta sakata kawai tana kallonta cike da admiration ya shaida masu cewar mahaifin yarinyar ne aka bata waya ta kanga a kunnanta , abinda mahaifinta ya fada ya sakata yin tsuru tana sauraronsa
Walahi, bilahi, rashin kulawar iyaye ciwo ne, du irin zumudinta da wannan aiki jin yadda mahaifinta ya mata magana sama sama da alamun yana tayata murnar cikar burinta da son sannin wai da gaske zata daga ko yayane? Sai ta ji gaba daya duniyar ta yi mata zafi, a hankali ta janye hannunta daga cikin na aleesa dake kallon yannayinta ta kwontar da kanta a gefen kujerar ta jinginar, muryarta na rawa ta ce聽" Oga, ina mama "
A wani shanshakai ya ce" ni dai da safe da zan fito mun hade da ita zata je wajen biki yanzu ban san ba ko a ina take gaskiya"
Wani irin zazafan hawaye ne suka shiga kokarin zubo mata a kan kuncinta, gaba daya sai ta dantse lebenta na kasa ta kasa ci gaba da magana dan tsoro take kar ta budi bakinta ta fashe da matsanancin kukan da kowa zai rasa gane kanta
Ba鈥檃 dawo amsar wayar ba a haka har sarakan suka dawo kanta a jingine da madubin mota idannuwanta lumshe bata ga lokacin da dogaran da take zumudin su hade ba suka zo kusa da motar tasu aka hanna su matsowa kusa sunna yiwa HANJA kirarin da bai san yaren da suke yi ba har ta ji motar tasu ta tashi ta buda idannuwanta da sauri tana kallon mutanen dake cikin makarantar tare da waigawa idannuwanta na karra budewa tana kallon komai wasu hawayen na zubo mata
Budurwar dake tare da su ne take kallonta, ita mamakin da take irin yadda ta ga Mamansu ta rike hannun yarinyar nan, ko dai ya sarkin garinsu ce?
A haka suka nufi filin jirgi, kwata kwata bata tare da wani zumudi ko yannayi na farin cikin tafiar nan, bata nuna komai ba koda ta zo shiga jirgin da take mafarki ba dare ba rana, iyaye ba abin wasa bane, a zuciyarta ta dauke su da wani irin daraja, a yadda take gannin y鈥檃ya da iyayensu sunna mu鈥檃mala ta kula da kaunar junna ita ba haka bane, shin iyayensu aun haife su dan dole ne ko menene? Halin ko in kula na kan mahaifinsu, ba ruwansa da abinda ka fita yi ko kake yi, shi a tunaninsa ai kauna kawai ya sakar masu mara su yi fitsari ne, ita kuwa mahaifiyarsu bata san yaya zata kwatanta irin nata abin mamakin ba, sam bata san a wani waje ya dace ta ajiye mamansu ba,
Sosai take hawaye bata kula kowa ba, Aleesa kuwa sunna shiga Hanja ya kaita wajen zamanta du yadda ta so ya kawo yarinyar ya kiya ya ce da ita ta zauna har Allah ya sauke au lafia sai ta ganta
A dakin da yake na hostess a nan Sir Muhammad ya laya su, kai yake yana kawowa yana hankalce da hawayen da ya ki tsayawa Muneerath da kuma Ameerah da gaba daya ta fice a hayacinta itama kan wannan koma baya da ya sameta domin koma baya ne a wajenta bayan matakin da ta taka yau a wayi gari ta ganta a wannan matakin kuma?
A nutsensa ya ce" tafia ce da manya, ko bai taka matsayin babanmu a wajen aiki ba shi din baba ne a duniya, ku sani biyayar da zaku yi masa ita ce ribarku, ko me ya ce kar ku daga kawunnanku har sai ta bar wajen dan ko da abokan aikinsa baya gardama bale a yi musu da shi, ku kula ku kiyaye dukkan wani motsinsa baya korar mutun a dawo da shi ko wa ta tsaya masa sai dai iko na Allah, kuma yana da damar dakatar da kai koda a tsakiyar tafia ne bale a kasa!"
Takun tafiarsa ya saka Sir M dakatar da maganarsa sannan ya koma gefe ya ja ya tsaya
Kamar yadda ya saba kai kawo haka ya yi kamar sau biyu yana karewa kowace kallo kafin ya ja ya tsaya a tsakiya
Muryarsa a dake ya ce" Aiki ya kawo kowace, du wace ta yi abinda ba aiki ba a tsayin tafiar nan ba zan iya tafia da ita ba, mahaifiyata bata cin abu mai zaki, haka mahaifina baya cin abu mai magi da sanyi a kiyaye"
Yana gama fada ya juya ya yi dakin Pilot shima dan madaidaicin daki ne mai dauke da bayi da madubi wanda suke shiga su shirya kansu kafin su dauki jirgi
Sir ne ya dawo gabansu ya shiga rabawa kowa aiki cike da kula , sai da kowa ya nufi wajen da aka bashi kafin ya maido dubansa kan Muneerath dake kallonsa tana kikifta idonnuwanta
A sanyaye ya ce" me yasa kike kuka? "
Kanta ta girgiza har yanzun hular na kanta , stil dai a sanyayensa ya ce" mu je na nuna maki dakinku, ki yi wanka ki zauna har mu sauka, idan kuwa barci zaki yi sai ki kwonta har mu sauka in sha Allah"
Kamar ta ce da shi ba zan je ba, kamar ta saka ihun a sauketa ta koma gida, ji take kamar zata hadiyi zuciya dan damuwa sai dai bata musa din ba ta bi bayansa lokacin ne kuma ta ji an ja jirgi ya fara yar tafia hakan ya sa ta ji zara fadi, sai a lokacin ta tuna ko a cikin me suke, sai a lokacin ta yi sauri ta bi bayansa cike da tsoro suka shige dakin nasu
Turus ya yi gannin sandukin da idan an yi mutuwa ake sakawa, watau a nan aka saka gawar wace ta rasun kuma aka ajiyeta a nan maimakun a kaita cen cikin da ake ajiye sandikan gawa na cikin jirgi?
Juyowa ya yi da ita ya fito da ita ya nuna mara eajen zama ta zauna ya nuna mata yadda zata daure jikinta da kuma abinda idan tana son yin baci bata son haske zata sakawa idannuwanta da na kunne da safa kafin ya juya ya koma wajen aikinsa zuciyarsa cike da damuwar halin da take ciki, kwarai ya san dAmuwar ta iyayenta ce, aman kuma ya mara uzuri dan ya kula da ake cewa Allah mai fitar da kafuri a cikin musulmi, musulmi a cikin kafiri hakan ne, su suka haifeta aman halayensu ba iri daya bane
Sun yi tafia mai nisa kafin suke sauka dan bai yi biye biyen ko鈥檌na ba ya dauro niya sai ya ajiyeta kafin ya ci gaba
Sun sauka gaba dayansu cike da gajiya, du irin halin da take ciki sai ta ringa jin idan ta daga kanta juwa zata kifata a kas, sannan ta ringa gannin abubuwan mamaki da tsoro na yannayin ginnij da idannuwanta suka iya ganni
yinwar dake cikintama ta isheta dan kuwa ta nuna cikin nata ya dan fada ga juwa na damunta
Kwata kwata bata gane komai har aka sakata a wani daki mai masifar sanyi da kyau a nan filin jirgin dauke da gado daya tak
Bata iya tsayawa yin wata wata ba ta faa saman gadon nan bayan ta cire dan sosonta dake kafarta ta kifa kanta kafin ta fashe da wani irin kuka mai karfin gaske tana karra cusa kan nata cikin matashin kan lalausa da shi a hankali take fadin" Mama, Abanmu, shin ina rayuwar nan zata kaimu? Bayan nesan cen da na yi da ku a yanzun na yi mugun nisan da ba zan iya kai kaina inda kuke ba ko a guje na fita koda wani jirgin zan shiga ba, ya Allah ka kare ni da kariyarka, kar ka bari wani ya shiga lamarina ya lalata min rayuwata, Ya Allah kar ka bari kudi ko saurayi su rude ni na bar hanyarka, ya Allah kar ka ba talauci ko kangin rayuwa damar da zasu saka ni manta ka, Allah ka shiryar min da iyayena su gane cewa amanata ka basu zaka tambaye au a gobe kiyama, ya Allah kar ka kashe ni a nesa da dangina ta yadda ko gawata ba zasu gani ba bale au salaceni, Allahna ka.....,.,"
Bata karasa ba ta ji wata ya suwaiwai din murya na yi mata magana ta hanyar kiranta da mssz,
Da sauri ta dago fuskarta cike da hawaye tana gogewa ta sauke dubanta a kan matar
Taf, sai kawai ta saki baki da hanci tana kallonta dan kuwa budurwa ce ko na ce mace ce yar gayu iya gayu sanye da dan bintilin sket da riga mai dogon hannu yan berayen mamanta sun matsu bayin Allah gashinta daure a tsakiya ta gyara tsayuwarta da kulawa tana mamakin to a ina sir ya samo wannan yarinyar da sam bata shige da yar kasarsu? A mutunce duba da wanda ya damkata a hannunsun mai kasar ne ya kuma jadada kan ta kasance kwarariya a aikinta dole zasu kula su yi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 42