Share this page
da kanka ka dauko ni a garinmu?" Hanja sai kawai yake bin yannayin da take maganar da kallo Lebensa na kasa ya cije da tarin haushi ya ce" Dubi haukan da ake dorawa wai ni Hanja wai ke budurwata ce ko matata? Sai nake ji kamar na yankaki na birne a wajen nan na huta" Jikin Muneerath ne ya kuma daukan bari da sauri ta dauki wayar tana dubawa kafin ta ahiga girgiza kai ta kuma hade hannayenta ta ce" Kayya, kayya, aman wanda ya yi wannan munafuki ne kuma ba zan yafe masa ba koda kabarinsa zai kama da wuta balbal, dan Allah kai ai ka san ba wannan tsakanina da kai, maganama ni da bana maka tun ranar da ka shakeni ina zaman zamana? Ka min rai kar ka kasheni Oga bai ganni ba, ka yafe min wannan gangancin da aka ce wai ni din nan budurwarka, ka ga fa da saurayina walahi nima ba zan taba yarda da wannan maganar ba wa'indama suka dora basu da hankali ne, aman dan Allah kar ka yi maganar kasheni a kasar nan ka maida ni kasarmu na tarda iyayena na rayu da su, ko yau na bar aikin Hostess na ci riba domin zan fada cewar aikin nan na taba dandanawa " Tana magana ne tana dan kusanto shi da daga yan yatsotsinta masu dauke da faratuna farare tas ba digon abinda yan matan kasarsu ke sakawa farce musulman da kafuran, hakama hannun nata baya dauke da dogayen faratuna, sanann sai ta hade hannayen nata ta kuma rungume a kirjinta Fuskarta da furucinta gaba daya sai suke masa nuni da yarinyar is innocent, tamkar yarinyar da bata san komai ba Idasa zama ya yi a saman cafet din wanda shi da kansa bai san ya yi hakan ba A sanyayen da bai sanuryarsa har ta kai haka sanyi ba ya ce" Kin tabata idan nace zan maida ke kasarki daga nan zaki yarda? Na saka ki a wani jirgi ya kaiki?" Muneerath ta koma dan nesa da shi ta zauna tana ta ahiyar zuciya a hankali ta gyada kanta kuma tana kallonsa ta ce" Wanda zai tashi idan ya taka biredi ai ya rage, bale har ya samu hawa bene? Walahi ko a yanxu aikina ya tsaya alhmd zan koma na cewa mamanmu mafarkina ya tabata, na samu biyan bukatana, zan cewa kishiyar mamanmu nice na taka kasashe hudu na duniya ina aikin da ya zamo burina, sannan zan nunawa oga da ya ce ya san ni ba mahaukaciya bace kuma yana tunanin idan na yi kokari ina iya zama wani abu a yayansa cewar lale na je na taka jirgi kuma na yi aiki, ka ga sai na dauko takarduna na ci gaba da karatuna a university" Lebenta da take hadawa tana dan warewa idan tana maganar yake kallo , sannan yana dora kowani furucinta a kan ma'auni yana aunawa A hankali ya cire dubansa a kanta cike da mamakin kansa So yake ya hanna kansa ci gaba da yi mata magana dan yana so karfi da yaji ya karyata cewa yana jin dadin yin hira da ita a wannan lokacin harma yana son sannin dukan amsoshin tambayoyinsa dan a ganninsa a kan meye zai ci gaba da magana da parfait inknow haka ba gaira babu dalili, sannan yarinyar da a tunaninsa du dunia babu wanda ya raina shi irinta, yanzu haka ya tabata dan ta ga daga ita sai shi ne yana iya karya mata wuya har take mada magana, da ace a kusa da Mah ne da bai san yaya zasu kwashe ba A hankaki ya juyo ya ga kamar zata dauke shi da ido, duba ne na tana son karantar a wace suke ciki, zai mata ilan ne ko zai sasauta mata A hankali ya cire dubansa yana fadin" Ki daina tsareni da ido " Da sauri ta cire idannuwanta a kansa, a kasan zuciyar Muneerath adu'a take tun karfinta kan Allah ubangiji ya rufa mata asiri ya rabata lafia da mutumen nan, ita dai ta san bata taka masa ba, bata karya masa ba, aman ya tsaneta kamar wace ta masa wani mugun abu, A hankali ta kara juyowa zata kuma kallonsa ta ga ita yake kallo hakan ya sa gabanta ya fadi ta juyar da kanta Walahi ba zata taba mantawa da wata bugawa da yayarta ta mata wani lokaci da aljannunta suka tashi, watau tsayuwa ta yi sunna fada sai ta ga ta kureta da kallo ashe ashe abu na kusa tana kyarara ihu sai ta warci Muneerath din ta doka da kas....kafin dai ta ankara ta gudu ta kara balata, wannan shi ya sa a yanzu ta ji gabanta na dukan dari dari Idannuwansa sun yi ja kamar ba nasa ba, hakan na mata nuni da abin na kusa Inahu sulaimana wa inahu bismilahi rahamanin rahim, Allahu la'ila ha ilahu, alhayul kyayum....... "haka mamanki ke cewa baki da hankaki dan kina son zama Hostess?".......maganar da ya ji yana fada kennan, wanda itama ya sakata daina adu'ar da take a kasan zuciyarta da sauri tana kallonsa Kanta ta sada lokaci daya tana tunano iyayenta A hankali ta dago tana murmushi ta dan matso kusa da shi sannan ta juya tana kallon inda yake kallo a hankali ta ce" Ko kaine sai kace bani da hankali, ka ga ni ban iya girki ba, ban iya ruwa ba a lokacin, ban iya komai ba fa....bani da hanyar shiga makarantar nan dan kudin da ake biya Oga ba zai biya min ba, a haka kuma nake ikirarin ni Hostess ce" HANJA ya juyo gaba dayansa wannan karron yana kallonta, a yanzunma a tsanake ya kuma cewa" Yaya aka yi kika samu kanki a ciki?" Muneerath ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Abinda na fara rikewa shine Allah, na san cewa shi kadai ya isa ya tsaya min, na san da cewa ikonsa na kan kowa, kuma yana iya yi min a lokacin da ban aune ba, shi yada kawai na dukufa ba dare ba rana ina fada masa....Ya Allah ka bani DOGARI sannan ka bani damar zama Hostess" Dan dakatawa ta yi tana kallonsa kafin ta kara sada kanta tana wasa da hannunta ta dora da fada masa irin yadda aka yi ta koyi ruwa, irin yadda ta fara koyan girki aman kulun abin na gagararta, kamar an kunna redio tas ta kwashe masa yadda ta tsinci kanta a wajen horon Hostess Ta idasa da dafe habarta tana yarfe hannunta ta ce" Wannan labari nawa akoy abin mamaki ko baka gane ba kai?" HANJA bai taba gannin mutumen da yake hira a sake a gabansa irin yarinyar nan ba , ciki kuwa harda Mah dinsa, domin Mah tana magana da shi ne da sigar rarashi da yannayi na son ta lalaba shi, aman yarinyar nan hira ne take da shi kamar na sako da sako, kanta tsaye hankalinta kwonce ta gama bashi labari da sunnayen mutane kala daban daban da a ciki bai san meye Oga, meye hajia baba watau hostess dinsu baba, sunnaye dai kala daban daban da ta ambata da hausa ba da turanci ba ta krashe da koda labarinta irin abin dai a ranta yake Sannan bai taba gannin yarinyar dake magana zuuuuuuuuuuuuuuu kamar wata redio abinta daki daki har sai a ta dasa aya ba sai wannan yarinyar Kansa ya cire a kanta a hankali yana jin kamar zai saki murmushi a bayane sai dai ya hanna kansa hakan Muneerath ta kuma rafka tagumi ta ce" Yanzu ko yaya makomata take? A islamiya ake cewa karmace ta yarda da namiji ya zo mata idan ba mijinta ba, idan ta yarda da haka har namiji ya tabata to fa ta aikata zina....... hakama Mah ke cewa namiji na taba mu muna iya daukan ciki,shikenan mutuncinmu ya zube idan har muka yi wasa da suturarmu.......Dan girman Allah yanzun hannuna ka riko ka kuma riken jikina fa? Da wani irin mamaki yake kallonta, kai shi kwata kwatama sai ya ji ya rasa me zai yi tunani da yarinyar nan, gashi dai yanzu sunna maganar fahimta kuma tana son fara sako masa rainin wayon, ko me yasa take irin haka? Ko a tunaninta shi HANJA zai iya wata mu'amala da ita ne? Bata san cewa a cikin tsarinsa shi yana da haram bane? Bata san cewa baya zuwarma macen da bata fito ta nuna sana'arta bane? Bayan wannan bata san cewa baya haikewa yan shila bane? Dan tana ganninta bukekiya ai girman jiki ne ko a tunaninta shi zai iya wani abu da abinda bai nuna ba? Kansa ta cire yana dan girgizawa kafin ya mike tsaye ya ce" Kin ga magana nake so na maki ina so ki fahimce ni kin gane?" Muneerath ta yi gagawar gyada kanta tana binsa da kallo, willah kamar wani balarabe Allah, kawai shi kuma haka farinsa yake fas? Kamar mai shafe shafe ita mamakin laushin fatarsa take, yanzun dai dan tana tsoron a wajen nan ya hada mata jinni da kwakwaluwa ya sa bata kireshi da sunnan da ya dace da shi ba, kai tsaye ya ringa tabata dan yana dan......... "kin ga, a gabanki ta ce wai ga amana nan na rike mata yarta, ban san yaushe ta min kishiya take kiranki kai tsaye yarta ba, abinda na sani ita din mutun ce mai kafa kafa da mutuncinta, kin ga idan halinki ne kuka kowani namiji ki bari idan kika fita daga gaban Mah sai ki dora daga inda kika tsaya, aman a yanzun ki kula, ki kiyaye, ki ajiye komai ki yi hakuri da komai, Bani da damuwa da MU'AMALARKI da MAZA, domin ba hurumina bane, aman inada da damuwa da damuwar mamana.......Shin zaki kiyaye harkar maza a zamantakewarki a kusa da ita kafin ta bani damar na mayar da ke gaban iyayenki?". Ya fada da yannayi na serius, ya fada yana kallonta tare da tsatsareta da idannuwansa yana jiran amsarta a kusa dan ya kara gaba Cike da mamaki Muneerath da ta fara jin haushin maganarsa tana tunanin to a mema ya dauketa ne kwata kwata tunanin kar ya ilatata ya shige mata ta turo baki ta dan saki harare ta ce" To tsakani da Allah a mema ka dauke ni? Hala ni yar iska ce? Inace kai ka rike min hannu da nan dina kau?".......ta karashe tana mai nuna kugunta cike da jin haushin furucinsa "Ikon Allah" shine abinda ya kubce daga bakinsa yana kallonta Fara tatare naman gaban goshinsa ya yi yana hada rai dan fa ya kuka yar nan ba'a zaman kalau da ita sai ana rashin mutunci da ita, yanzun ko dan wannan dogon sharhin da ya mata ba dan yana tsoronta ba ai ya ci ta masa biyaya, maimakun ta amsa shi sai ta shiga fadin wannan kalma tata ta rainin wayo? Wata tsawa ce ya sakar mata wace ta sakata zabura tana kiki fiki da ido tana kallon ,yama karra hade fuska ya ce" ( *AKOY SU, WALAHI AKOY SU, YAN MATAN DA SUKE TAFIA ISLAMIYAR SUKE KUMA TAFIA BOKO DIN AMAN BASU SAN AINAHIN ME HAKAN YAKE NUFI BA KUMA BASU GANE MEYE AINAHIN MANUFAR ABIN BA, A WAJEN MUTANEN DA YA DACE TA SANI SUNE KAWAYENTA, IRIN KAWAYEN NAN NA ZAMANI MASU ABIN TSORO WA'INDA IDANNUWANSU KE BUDE TARRR SUN SAN KOMAI, TO IDAN NATA KAWARMA NA HAKAN TA SANI BA SAI A KARE A TUTAR BABU, YA KASANCE A ANGUWA TAKAN JI AN CE WANCE TA YI CIKIN SHEGE, WAYE YA YI MATA? WANE NE YA LALATA TA.........IDAN BA HADUWA TA YI DA LALATACIYAR DA TA FEDEMATA BIRI DA ABAWA CEWAR GA NUFIN LALATAR BA ZATA GANE BA, ABINDA DAI ZATA GINU A KANSA SHINE TSORON KAR A MATA CIKIN SHEGEN, SAI NA GABA TANA IYA KASANCEWA IRIN HALITUN NAN DA U MAGANA IDAN BA KARARA AKA FITO MASU DA ITA BA, BA GANEWA SUKE YI BA SHI YASA TAKE TAFE A BAIBAI KUMA KOMA ME AKA CE MATA TAKR YARDA, IDAN KUN KULA TANA RAYUWA NE A TSAKANIN GIDA BIYU, GIDAN SU KAWARTA DA TAKE MANGARIN RAYUWARSU HAR TAKE FATAN ITAMA TA ZAMA IRIN HAKA BALEMA IDAN SUNNA MAGANA DA ITA DA KAWAR TATA TANA FADA MATA MAMANTA TA HANNA SU ZAGI A GIDANSU, SAI ABIN YANA BATA MAMAKI DUBA DA NASU GIDAN ASHAR BA KOMAI BANE! SAI UWA UBA KARIYA IRIN TA UBANGIJI, ALLAH SHI KE KAREWA ......SAI KA RAYU A ANGUWA TA BADALA AMAN IDAN ALLAH YA TSAREKA BA ABINDA ZAI FARU DA KAI HAR KA YI KA GAMA RAYUWARKA A TARE DA SU........................abinda baya kasancewa cen dama ba kasamracen bane watau baya cikin rubutacen al'amari* ) 11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 4锔忊儯2锔忊儯 Sorry ba eddtng Ya hade fuska ya ce" Look, abinda nake so da ke daga nan har mu koma kar na kuma gannin shirmen biye biyen nan! Wannan din Umarni ne na baki ba shawara ba, idan kuma kika ki bi zan bi da ke !" Yana gama fada ya kama hanya ya dadana numbobi a wajen wani allon waya kamar lap sannan kofar ta bude ya wuce ya fita kwata kwata a dakin Da gudu Muneerath ta mike dan bin bayansa sai dai gannin ya rufo kuma ya yi cikin motarsa ya sakata fara yin dan baya baya kafin ta hantsila gaba dayanta Ihu ta saka mai hade da kuka tana rinrintse ido dan du a tunaninta wani abu ne ya fito zai kamata A haukace ta buda idannuwanta a rikice tana ta waiwaiga cikin dakin idannuwanta suka sauka a kan wani makeken zaki kansa na kallon sama kadan kamar yanna son kallon jaririn zakin dake saman wuyansa Zakin irin na felush ne, an mahaukacin bata lokaci dan yinsa kama daga kalarsa har gashin jijinsa da irin tsayuwarsa da komai A guje ta yi bayan kujerar dake falon ta tsuguna tana mai saka hannayenta ta toshe bakinta danma kar ya jita ya halakata , lokaci daya kuma cikin nata na juyawa dan azabar tsoro Gaba daya gumi take, haka kuma jikinta rawa yake, ta daina ihun kukan sai zuru zuru da take da kwayar idannuwanta masu shegen kyau cike da ruwan hawayen dake sauka a saman hannayenta da ta rufe bakin nata da shi Shikennan, shikenan, tata ta kare, dama wannan mutumen dake biye fa rayuwarta shine ajalinta domin du hafuwarsu da harare suke rabuwa ita da shi Gaba daya ta gama hautsinewa , ta kuma dauki lokaci mai tsayi ba tare da ta dani ba, kwakwaran motsi ta kasa yi haka kuma gwuiwoyinta sun sage sun yi tsami , Zuwa yanzu kanta a hade yake da bayan kujerar tana ta sauke ajiyar zuciya mai zafi baki daya ta gama sarewa ta saka a kasan zuciyarta cewa jira zakin nan yake ta yi wani motsi ya ankara da ita ya cinyeta hakan ya sa baiwar Allah ko cikinta ya yi irin murdawar nan sai ta rintse ido dan kar kukansa ya ankarar da zakin cewa da mutun A haukace ta juyo jin an taba kafadarta, a zabure da niyar kwala ihu da wani kukan har kamar zata sike, sai dai mikewar da ta yi tsaye idannuwanta suka sauka a kan fuskarsa yana kallonta cike da mamakin yannayinta A haukace ta fada kirjinsa tana mai fashewa da kuka jikinta kuma na rawa, rukunkumeshi ta yi tana jan numfashi da kyar hakan ya sa gaba daya ya yi kasakai cike da mamakin yannayinta a hankali ya shiga fadin" Hey, menene haka? Meye? Me kika gani haka?". Domin ba zai manta a jiya ne ta sume masa a kirji bayan ta masa irin rikon nan dan kawai ta ga tgr Muryarta cen ciki tana kukan ta shiga fadin" Zaki ne, zaki ne, shine ka kawo ni wajen zaki? Dan Allah me yasa kake son kashe ni? Me na maka? Inace yanzu muka shirya? Dan Allah ka daina hadani da zaki haka ka ji?" A hankali ya dan juya da ita gefen da felush din nan take a hankali ya kurawa Felush din ido yana jin wani abu daba dangane da felush din wanda ya kasa bambance tausayinta ne na ta tsorata da tgr ya sa ta ji tsoron wannan abin ko menene? A hankali ya shiga tafisa da ita inda ta kara rukunkumeshi tana girgiza kai hawayenta bai tsaya ba har idannuwanta na mata zafi ga muryarta har neman disashewa take tsabar ihun da take ta ce" Kar ka kaini mana, kai kuwa kar ka kaini dan Allah, ka min rai kar ka kaini na tuba " Saman kujerar nan ya fara zama kafin ya rintse idannuwansa sakamakon irin yadda ta biyo shi gaba dayanta idannuwanta rintse ga gumi na karra tsatsafo mata du da irin sanyin garin domin ko AC babu a wannan wahe dan gari ne mai sanyin gaske wanda idan ka fito daga kasa mai rana zaka wahala sosai da saka kayan sanyi domin har kankara ke zuba watau neige a garin, gashi bata da rana hakan ya sa a kasar suke fama da saka kayan sanyi da kuma anfani da abin dumama dakunnansu idan sunna ciki A hankali ya dora hannunsa saman kanta ya dan shafa kadan muryarsa cen ciki ya ce" Ki daina kuka da ihu, kaina zai rabe biyu!" Muneerath ta kara kankame shi ta ce" To to, kukanma sai na daina aman idan ka fitar da ni dan Allah ka fitar da ni ka ji?" Ajiyar zuciya ya sauke domin a yanzun ba da ihun ta yi maganar ba da rada rada ta yita a saman kirjinsa kafin take barkewa da kuka tana karra rike shi A hankali ya kuma kallon zakin, walahi so yake ya ce da ita cikin mahaukaciyar tsawar da zata firgitata cewar KE tada ni , ba zaki bane kin wani haye min jikina kin rikeni kina giga min hawaye da majina a jiki! Aman haka kawai sai ya ringa jin idan ya yi haka zai iya firgitata bayan bata da laifi a tunaninta har yanzun zakin da ya tsoratata ne, sannan haka kaeai yake ji a ransa baya so ta kuma sume masa duda koda sumar ta yi yana iya bata taimakon gagawar da suke koyar da ma'aikatansu saboda halin tafia a cikin jirgi babu abinda ba'a haduwa da shi A hankali ya ce" To ki daina rike ni mana, kin ce ba kyai taba mutun fa" Muneerath ta karra rike shi tana girgiza kai tana ta sauke ajiyar zuciya jikinta har ya dauki zafi Sai da ya ga dama dan kansa kamar an kwato maganar daga bakinsa ya ce" ke Felush ne, bafa mai rai bane" Dif ta yi na dan sakwani kafi ta dn dago da fuskarta wajen sagensa da tsinin karran hancinsa da jajayen lebunnansa a hankali tana kallonsa tana kuma hangen zara zaran gashin idannuwansa muryarta cikin rada aman dumin furucinta na dukan habarsa hakan ya sa a hankali ya samu kansa da rintse idannuwansa ta ce" Kana nufin wancen abin ba na gaske bane aman har yake da faratunna da fatar kafa irin na mai rai?" A hankaki ya bude idannuwansa da suke da yannayi irin nasu yannayi kamar mai dan kurba eh yane ya dan duko da duban nasa a saman fuskarta hakan ya sa lebunnansa suka dan zarto kusa da hancinta, hancinsa na gugan gashin idannuwanta idannuwansa na kallon goshinta ya yi mata shiru ba tare da ya bata amsa ba kawai ya kura mata ido irin kallon nan na rashin kunya wanda ka ga ana kallon kana kallon mutun aman ba zaka daina kallon nasa ba dan ba tsoronsa kake ji ba Hancinta dake shakar kamshinsa ya fara ankarar da ita irin zaman da ta yi dare dare a saman kan kato ta hanyar shaka mata kanshin jikinsa sosai a jikinta har ya kasance kwakwaluwarta a yanzun ta faa kai mata sakon halin da take ciki Wani irin hantsilawa ta yi baya jikinta na rawa tana zarro ido ta mike tsaye da sauri tana kallonsa cike da mamaki da tsoron abinda ta aikaa wanda a yanzun ta gama gane ita Muneerath yar oga itace ta ara rungume jikin kato Da sauri ta dora hannunta na dama a saman bakinta ta zarro ido kafin ta saki hannun nata ta tafa tana girgiza kai a hankali ta ce" Ashe nima yar iska ce? Yanzun shikenan nice na yi wannan abin shi kuma ya kyale ni har ya zauna da ni a samansa? Yanzun wannan gabjejen katon sau hudu kennan yana zuwar min? Innalilahi wa ilaihi raj'une" A hankali ta karasa kasa ta zauna ta rafka tagumi tana kallonsa. Sai ta ga kamar barcima yake, sai ta ga kamar ko a ka bai dami da abinda suke ciki ba, yanzun ina zata dosa? Ina zata kai wannan abin? Iman bata yi ba ita ta yi? Walahi ba laifinta bane! To ai zakin nasa ne kuma a cen gidanma jiya zakinsa ne, a nanma kuma zakinsa ne, sannan kafin zakin ai shi ya fara rikota ya zo nan da ita Wayarsa dake ajiye kuda da kalin Pizza ce ta fara ringin, ringin take ta hanyar kida irin na Iphne Da sauri ta rarafa dan daukowa hakan ya sa Hanja dake a zaunen nan kuma rakata da lumsasun idannuwansa dan gannin meye kuma zata aikata da zai idasa halaka shi a zaunen nan da yake , gaba daya sai ya ringa tunanin yarinyar nan ba abinda bata sani ba rainin hankali ne irin nata da salon nata a haka, Abin haushin maimakun ya yiwa rainin hankalin nata kwakwaran hukuncin da zata kama kanta ta kula ta daina neman haike masa sai kawai yake son karasa fahimtar irin nata rainin wayon Juyowa ta yi ta karaso ta mika masa wayar saman cinyarsa ta koma ta zauna ta rafka tagumi tana tunanin tata wayar a dakin cen da aka sauketa ta saka a caji sabuwar wayarta dal da Mah ta bata a jiya kafin su taso, sun yi whatsup da Mah cewar sun sauka rabonta da ita tun da safe har gashi yama na kokarin sanyo kai, ga wata yinwa dake kwakularta har ta fara shedata dan ta fara sakata juwa Wayar yake bi da kallo gannin sunnan Mah na yawo kwado kwado aman ya kasa daga hannunsa ya dauka har ta tsinke, sai dai tana tsinkewar aka kuma bugowa hakan ya sa ransa yake ayana' Aya sai yanzun hoton ya kai inda kike Mah?' Muneerath ta ce" Hanja ka daga mana ana kiranka" Da sauri ya wara idannuwansa a kanta yana kallonta gannin ta mike tana kakabe kakabe bayan ba kurar komai a jikinta aman sai dube dube take kamar ba ita bace ta gama haukan ihu da kuka yanzu yanzun nan kafin ta karasa kusa da dan kwalinta ta duka ta dauka tana kadewa ta zabgawa zakin nan harara a bayane ta ce" Asarare kawai! " Ta dawo ta zauna tana kale kale a dakin A hankali ya daga kiran , blootoof din dake kunnansa yana ta haska wuta blue hakan na nufin magana ake a ciki A hankali ya kai dubansa kanta kafin ya cire muryarsa kuma cen ciki ya ce" Lafiyarta kalau " .... . 11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 4锔忊儯3锔忊儯 Ci gaba da magana Mah ta yi wanda shi kuma ya yi shiru yana sauraronta gaba daya bakinsa ya masa nauyi yana tunanin anya zai iya dogon bayanin a yanzu kuwa? Muneerath kam idannuwanta a kan kwalin Pizzar nan da ta kula biyu ne da kuma kwalba dake dauke da jus irin na yan gayun nan A hankali ta kuma satar

Chapter 24 of 42