ta fada, magangannun nata sai suka samu muhali a cikin kwakwaluwarsa harma ya samu umarni daga kwakwaluwar tasa kan ya sauke kan na Mah kar a je ta kage din ne, dan haka a hankali ya saka hannayensa biyu ya sauke kan Mah ya mike ya karra gyara mata kwoncinta sannan ya mike gaba dayansa hakan ya kasance fuskar Muneerath na daidai kirjinsa ya kuwa tsaya mata kikam a saman kanta, hakan ya sa dan dole ta kauce kadan tana lumshe ido dalilin kamshin nan nasa da ta rasa shin wani irin turare ne mai irin sansayen Kamshi da naci haka a jikinsa
A hankali ta kai zaune a wajen da ya tashi kanta a kasa tana jin yadda hancinta ya karra cika da kamshin turaran nasa
A hankali ta dan dago dan kallonsa, sai ta ga ita yake kallo hakan ya sa ta karra tura bakinta aman kuma ta kasa furta masa komai
Idannuwansa ya lumshe kafin ya juya ya kama hanyar fita
Har ya kusa fitar ya juyo yana kallonta , hannunsa na dama ya dago a lokacin da suka yi ido hudu ya kai wajen lebunnansa
Cikin yannayi na sanyin jiki da iya sarafa karatun kurma ya yi mata alamu na zif wa bakinta, sannan ya nuna mata Mah dake kwonta ya kuma maida hannun wajen bakinsa ya yi mata alamu da kar ta mata hayaniya kafin ya lumshe ido ya kai hannayen biyu gefen fuskarsa ya mata alamun ta barta ta huta, sai kuma ya dan fitar da idannuwansa da yannayi irin na ta fahimta? Kafin ya kai wajen kunnensa ya dan ja sai kuma ya dantse hakorinsa a kan lebensa na kasa wanda Muneerath dake bin dukkan motsinsa a saman lebenta take fasarawa kanta abubuwan da yake nunawa da yarenta watau hausa har ta dire kan' Idan kika ki zan cije maki lebe'
Ido ta dan fitar, a nata fahimtar kennan kafin ta yatsina fuska ta cire kanta shi kuwa ya juya da dan sauri ya fice dan amsa kiran karamar wayar da Pah ke kiransa da ita
Yana tafia ta bi bayan kofar da ya rufo da kallo
Ajiyar zuciya ce ta kwace mata kafin ta mike ta kara dan yaye bargon Mah ta tataba jikinta
Jin jikin ba zafi, ga kuma karrin ruwanta na tafia daidai sai kawai ta yi bismillah a hankali ta haye saman bed din na Mah ta kwonta daga saman bargonta kasancewar lubukeke ne, ta dora kanta a kusan gashin na Mah a hankali ta ce" Kin ga, kece mamana fa, ke ce Ogana a garin nan, kin ga Allah ne gatana kuma ke ce gatana a garin nan, dan Allah ki rufa min asiri ki mike daga cutar nan taku ta yan gayu kar ki sheka yaronki ya sheke ni ya ba zakinsa ya cinye banza ya yarda kasusuwana kin fa fi kowa sannin irin tsanar da ya yi min kau? Ban san me na masa ba ko yanzu nunan ya yi zai cije ni, wai ko dai maye ne shi? Mi ya kawo cizo a lebe?"
Ta dan yi murmushi ita kadai ta ce" Wai shi mai leben nan uwa na jarirai da wasu hakoransa masu laushi yana tunanin zai iya karawa da hakorana ne?, Yo idan na dantsa masa cizo ba sai a asibiti za'a iya bambareni daga jikinsa ba?, Da wasu girarsa kamar na yan gayun yan matan garinmu, namiji da shi yana aske gira"
Sai kuma ta lumshe idannuwanta a bayane aman kuma kasa kasa sosai ta shiga yiwa Mah adu'ar da duka ta zo bakinta tana tofa mata ta bayanta, ta yi dare dare a saman bed dinta sai ga barci ya kwasheta mai dadi irin na safiyar nan gata a saman lalausan bargo abinta
Rike yake da hannun mahaifinsa, sosai yake jinjina soyaya irin ta iyayensa, a yanzu haka sai da ya jajirce ya rintse ido ya tsaya gaban mahaifinsa ya shaida masa bata da lafia ne, cikin ikon Allah ya yi luuu zai zube masa domin juwa ce ta kwashe shi da hanzari ya rike shi a jikinsa yana mai yi masa magana da dan karfin da zai wartsake ya nuna masa cewar rashin lafiyarta ne ciwon cikinta ne, kuma a yanzun baya bukatar su zube masa su biyu, idan suka zube masa yaya suke so ya yi ne?,, Hakan ya saka Pah ya jure ya daure ya ringa sauke ajiyar zuciya har ya samu nutsuwa kafin ya kama hannun HANJA su nufo wajen da aka rike Mah din watau dakin hutunta
A lokacin da suka shigo dakin, abinda ya gani ne ya saka shi yin turus da mahaukacin mamakin da ya saka shi bude baki da ido yana kallonta
Mah da ta buda idannuwanta ta samu kanta da sakin murmushin yannayinsa, a hankali ta mikawa mijinta hannu da ya nufeta da sauri stlll tana murmushin Hanja din da ya yi mutuwar tsaye a wajen shigowar yana kallon Muneerath dake barci a saman gadon Sarauniyar ingila a bayanta a irin wannan lokacin da take rashin lafiya, ta wani lafe abinta har an luluba mata bargo gashinta dake daure ya karra yin lumbuk a jikinta
Da kallon mamaki yake bin Mah da ta kama hannayen Pah ya taimaka mata a hankali ta sauko kafafuwanta ne masu sanye da dogon sakaken wandon asibitin da kuma safa dinta kafin ta maida hannunta a hankali ta gyara mata rufarta ta juyo tana murmushi ta dora tafin hannunta a gefen fuskar Pah da idannuwansa suka tsumu da kauanar da kuma tausayin matar tasa a sanyaye ta ce" Khalb, yaushe ka dawo?"
Maimakun Pah ya bata amsa sai ya yi gagawar rungumeta a jikinsa tsam idannuwansa a rintse yana jin yadda zuciyarsa ke kadawa
A hankali take dan tapping din bayansa itama nata idannuwan a rintsen a hankali ta ce" na ji sauki fa "
Pah ya dan girgiza kansa a sanyaye sannan muryarsa cen ciki ya ce" sai da na matsa ciwon ya motsa?, Wani irin ciwo ne wannan da ba zai barmin mata ta huta ba? Da ace na ga wannan dan aiken ciwon da na kama shi ban san yaya zamu kaya ba, ALEESA lafia fa na barki"
Murmushi ne ya kwace mata, sai kuma wani irin tausayin kansu ya kamata, a hankali ta ce" haba khalb, idan da karar kwana kuma fa?"
Da sauri ya ringa girgiza mata kai tamkar matashin saurayi yama rasa me zai ce mata, sai da ya nisa kafin ya ce" Kin manta wa aka fadawa sauran kwanakin da suka rage masa a duniya?"
Murmushi kai ciwo ta yi ta ce" Ka manta ba su ke da wannan ikon ba?, Sai wanda ba'a gane masa wani ciwon dake iya kaishi ga kushewar ba ya mace ya bar marar lafiyan"
Hanja dake jingine yana kallonsu dukkan bayanansu a cikin kunnayensa duda a hankali suke yi aman dakin kai amsa amo ne komai kankantar magana kunnayenka na iya ji
So yake ya karasa ya ce da su dan Allah su daina wahalar masa da zuciya, shin me yasa suka dauki maganar mutuwa hira mai dadi a tsakaninsu? , Sai dai haka kawai kafafuwansa sun masa nauyi , jima yake kamar idan ya matsa kusa da gadon cen akoy abinda ke iya kama shi
Daidai lokacin Muneerath ta farka a barcinta,
Murginawa ta yi dan yaye bargon da aka luluba mata tana cuno bakin an hanna mata jin sanyi bayan yanzun ita din nan ta rigaya ta saba da sanyi
Hannayenta ta daga sama ta bankarro kirjinta tana mika tare da adu'ar farkawa a barci
A hankali ya janye dubansa daga kanta yana mai jin gabansa na dukan tara tara daidai lokacin Muneerath da farin cikin gannin Mah ta farka da kuma Pah ya dawo ta ce"
*ALHAMDULILAH, ALHAMDULILAH YA RAB*
11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
5锔忊儯0锔忊儯
Da matukar farin ciki ta dirko ta karasa kusa da su sosai ta ce" Lah Mah da ranki, dama na san zaki tashi ciwon ba wani bane dan jikinki ai ba zafi, Pah yaushe a gari?"
Pah dake murmushin yar shiriritar yar dake nan haukata masa yaro ya dan kama kuncinta ya ce" Ke da kike jinya ce kika yi barci?"
Muneerath ta yi murmushi tana dan jin kunyar an taba mata kunci ta ce" Pah, gwara ni, ka ga Walahi Hanja kuka ya yi ta shekawa da kyar na lalaba shi ya tashi a nan"
Ido ya kwalalo daga inda yake yana mai karra kallonta, da kallon yadda iyayensa ke dariar abinda ta fada
A ba zata, a yannayi na rashin tsamani wani sansanyan murmushi ya wadaci saman lebensa, wanda ya sauka a kan fuskar Mah dake satar kallonsa tana mai jin dadin irin yadda du yada ya so kin kallonta abin ya gagare shi
A hankali ya kuma juyar da kansa yana shafa sajensa kadan kadan kafin ya taka ya karasa har kusa da su sosai
Muryarsa a rage sosai ya ce" Hutu, likita ya ce hutu take da bukata"
Pah ya gyada kansa ya mike yana fadin" Ba zata huta a nan ba sa a turakar mijinta"
Muneerath ta fito daga labewar da ta yi a bayan Pah tunda ta ga ya nufo wajen tana dan murmushi gannin bai kulata ba ta sake abinta ta karasa kusa da gadon ta yayo bargon ta cuimuimuye ta dora a kanta ta yi gaba tana fadin" Sai kun zo Mah bara na je na gyara maki gadon tunda an sake mu"
Gaba dayansu da kallo suka bita cike da sha'awar lamarin yainyar, ko dan a gabansu basu san mutun mai hali irin haka ba?, Irin rayuwarta na matukar saka su nishadi na debe masu kewa na saka su a shauki a koda yaushe, bata da wata damuwa ita sam a rayuwarta, tabas zaku yi mamaki idan har kuka fahimci rayuwa irin ta Muneerath ta zamo abin mangari a wajen sarki na ingila da matarsa, rayuwarta bata fa kowa a saman kanta, bata da kowa a cikin zuciyarta ita din lafiyarta kalau ras take haka take lamarinta ba tare da ta jira wani ba
Tun kafin ta kulewa ganninsu suka cire dubansu a kanta suka dora kan HANJA
Gaba daya hankalinsa da nutsuwarsa sun rakata da kallo ne
Kallo ne mai shige da kamar baya so ta tafi a wajen
Kallo ne kamar wanda zai dawo da ita kar ta yi masa nisa
Yannayin da fuskarsa ta nuna kamar Hanja na son ya dakatar da ita ne
Ba shi ya san halin da yake ciki ba har sai da ta bacewa ganninsa kafin a hankali ya ankara da halin da yake ciki, sai ya samu kansa da kasa juyowa kai tsaye domin bai san yaya iyayen nasa suke ciki ba duba da sun yi shiru ya tabata hankalinsu a kansa ko kuma Pah na taimakawa Mah ta mike
Sai da ya rintse ido yana mai tambayar kansa menene dan Allah ya saka shi bin yarinyar nan da kallo? Me hakan yake nufi? Salon ya janyowa kansa ko?
A hankali ya juyo sai kuwa suka yi ido hudu da Mah wace sunna hada idon ta sakar masa lalausan murmushinta mai sanyaya zukatansu
Sai dai ga mamakinta nan da nan sai ya hade rai yana mai cire kansa ya karasa ya kama dayan hannunta Pah na dayan hannun suka taimaka mata ta idasa mikewa tsaye kamar yadda suke mata kafin su kamo hanya a hankali su nufi kofa fuskar nan tasa a hade shi a dole kar a masa maganar bin yarinyar nan da kallo, koda yake a shiryema yake da basu amsa daidai da tambayarsu, zai fada masu ne haukan yarinyar nan na karra girmama duba fa ta dauki bargo ko me zata yi da shi?
A hankali suke tafia har suka karasa bangaren Mah din
Kasancewar ta ce tana son zuwa ta dauki sako a cen wanda ba wani sako dan dai ta salami yan matanta ne dan ta tabata sunna cen din duba da Muneerath ta dauki bargo ta ce zata je ta gyara mata gado
Ai kam sunna nan din, kuma su suka gyara dakin da kansu wanda Iman da kyar ta iya wani kokari a guaran tana kallon yadda Muneerath ke mika injin shara kasan bed tana son sharo dati bayan ba wani dati ko daya yau dinma abinda ya hanna masu gyarawar dan mai wajen bata nan, idan bata nan kuwa ba shiga suke yi ba
Murmushi Mah ta saki a lokacin da Muneerath ta matso tana mata murmushin itama ta ce" Mah me zamu dafa maki?"
A kasan zuciyarsa sai kawai ya samu kansa da mamakin furucinta, wai me za'a dafa , yar dake kona shayi? Ta kona wainar kwai ta ce ta fi vitamine?,
A hankali Mah ta zauna bakin Bed tana mai godiya wa abubuwan kaunarta watau Pah da kuma Hanja
Pah ya ce" Bara na je falona na dawo dan na saka a kimtsa maki komai"
Yana tafia ya yi sauran su hudu a dakin,
Mah na murmushi tana shaa kan Iman dake gefenta tana jikinta sosai tana sauke ajiyar zuciya, Muneerath kuwa tana tsaye a gabanta tana kallonta, Hanja kuma yana cen kusa da mirror dinta yana duduba turarukan dake ajiye kamar wanda hankalinsa na kan hakan bayan gaba daya hankalinsa ba a wajen yake ba a kan su Mah yake
A sanyaye Mah ta ce" My Munee, wannan kayan na fita ne?, Kin ga yadda wandon nan ya maki a jiki kuwa? Ba hula a kanki fa?"
Muneerath da sauri ta bi jikinta da kallo, lokaci daya ta zarro ido tana fadin" La hauli, tashin hankali da a haka naie yawo ko hula babu? Allahnma da ya sa a gaban Hanja ne da Pah, wollah Mah ni du rikicewa na yi da aka ce baki da lafia kuma ina zuwa na tarda shi yana kuka sai ya karra rikitani"
Wannan karron sai ya kasa rikewa, ya juyo ya karaso wajen yana hararanta a dake ya ce" Ke a ina na yi kuka da zaki ringa yadawa cewar ina kuka?"
Iman dake jikin Mah a hankali ta dago dubanta tana kallonsa tare da mamakinsa da ya ki ya daina kokarin kasheta, wai me yarinyar nan ta fita ne da har ta fita samun alfarmomin nan a game da mutumen da ta rayu da sin gannin sakin fuskarsa a gabanta?
Muneerath ta kama baki ta ce" Lah, Ka rantse da Allah ba sai da na rarasheka ba ka daina kukan, ji fa dan ka ga ta tashi ne zaka karyata ni?"
Wata daria ce ta kubcewa Mah lokaci daya tana dafe cikinta tare da dafe kafadar Iman
Da sauri suka nufeta, lokaci daya suka rufun mata a tare suka kai hannayensu gefen kafadarta da nufin rikota dan talaf mata duba da dan tarin da ta dan fara sakamakon dariyar ba zatan da ta sarketa
A hankali idannuwanta suka sauka a kan fari kal din hannunsa dake saman bayan hannunta mai duhun haske wanda ta ji tamkar an dora mata gashin mage ne mai laushi a bayan hannun nata sannan a hankali aka dan murza bayan hannun hakan ya sa gaba daya ta ji gabanta ya fadi
A hankali ta cire duban nata daga kan hannayen nasu ta dan fara kokarin zarewa cikin dabara tare da dago duban nata ta sauke a kansa dan gannin idan tunaninta na baima san ya taba mata hannu ba haka ne
Ido hudun da suka yi, da idannuwansa masu launin ja wa'inda tun tashin hankalin rashin lafiyar na Mah da suka dauki launin har yanzun bai hadu da abinda zai saka su cenza kala ba suka shiga cikin nata masu hasken gaske da kwayar cikinsu masu kala daban da ta mutane sai ta tsinci kanta da bugawar zuciya a karro na biyu wanda shima abinda ya ziyarce shi kennan harma ya shagala da kallonta har sai da ta cire hannun nata da sauri tana kallon yadda Iman ke mikowa Mah ruwa tana mata sannu ita kuwa tana nuna ba komai fa
Gaba data rasa me zata yi ta yi,baki daya daburcewa ta yi ta rikice hakan ya sa da sauri ta juya tana fadin " Mah bara na dauko hijab "
Hannunsa na hagu ke rike da Mah dinsa, ya rintse idannuwansa yana jin yadda yake fitar da numfashi tamkar mai ciwon huka
A hankali ya bude duban nasa ya kurawa hannunsa ido, wannan tabawa da ya mata itace tabawa ta farko da ya yi mata ba da niyar fada ba
A gaskiya bai san me yake damunsa ba, abinda ya fi ajiyewa a kasan zuciyarsa shine Bashi da lafia
Gaba daya jikinsa sai ya mutu Iman kuwa Muneerath na tafia itama ta bar wajen, dama karfin zamanta dan ta ga Muneerath din ne a yanzu da bata nan bata isa ta yi dogon zama a wajen da yake zaune ba, shi kuwa bai bar wajen ba har sai da Pah ya dawo ya dauki matarsa ya yi bangarensa da abinsa yana ta riritata tamkwar kwai
11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
5锔忊儯1锔忊儯
Bayan kwana biyu
Kula ta musaman, jinya mai girman daraja Mah ke gabatarwa a gefen mijinta, hakan ya saka Hanja fita dukkan wasu taro na Pah da kuma jagorar da yawa a cikin Palas a baban dakin taro
Wannan al'amari ya dauki hankalinsa sosai harma ya yi kwanakin nan ba tare da ya saka kafarsa a filin jirgi ba, hakan ya matukar bashi mamaki da tunanin dama akoy abinda zai hanna masa leka tsuntsu marar numfashinsa?
Sai dai wani abin ya fi gaban wani, watau a yanzu da ya tsaya ya fuskanci mecece matsayin gadon da ya tabata ko ba dade ko ba jima idan dai da ransa da lafiyarsa ko da ran mahaifinsa ko babu ya zame masa dole da karfi da yaji ya mulki kasar sai wani dari dari ya kama shi
Shin yaya Pah yake yi yake walwala?, Kai gani yake da shine harta walwala rasawa zai yi, ko dan shi din farin shiga ne?
Yaya Pah yake yana samun time isashen da yake ganninsa zaune a falo?
Yaya Pah yake har yake gane iyalinsa nada matsala ko sunna cikin farin ciki harma ya basu lokacinsa?
Tabas a yanzu ya yarda cewa shi din bako ne kuma yaro ne karami a duniyar nan wanda yake da bukatar a kama hannunsa
Gefe guda ga wannan nataciyar yarinyar da tunda sunnansa ya fara yawo kan Media a matsayin wanda yake gabatar da aikin babansa harma sunnan da ake kiran mahaifin nasa maimakun prnc kamar yarda ya saba ya hau kansa aka fadi dalilin cewa yana cikin hutun kula da lafiyar matarsa ne take aiko da takardar neman izinin samun damar shiga Palas din dan ta ga jikin Mah da ita da iyayenta
Ba dare ba rana sai an sanar masa da nata sakon a cikin sakwani hakan ya sa yau ya yi croi samanta dan ya gama da tata matsalar kafin ya fuskanci yan hutun nan su amshi kasarsu su rufa masa asiri, tsakani da Allah tunanin da kwakwaluwarsa da zuciyarsa take cikima ta fi komai adabarsa a irin lokutan nan
Tunda ya sauko daga matatakalar gidan tare da Tgr dake tafia ta kasaita yake jiyo muryarsu da yar dariyarta
A hankali ya jinginar da bayansa a jikin garu ya samu kansa da saurin lumshe idannuwansa yana mai bin hirar da take yi tana gaurayawa da yarenta da bai iya ba domin a yanzun tana french ne da kuma ainahin hausa tamu gangariyarta abinta sunna labaru irin na tsegumi da kuma hirar dangi ita da aminiyarta a saman table sunna cin ganima sunna kora jus , iman kuwa na kwonce a saman doguwar kujerar Falo tana sanye da earpc a kunne tana sauraron wata tsumamiyar wakar larabawa tana lumshe ido
Sai da ya gaji dan kansa Tgr kuwa tana kai kawo a daidai wajensa kafin ya sauke dubansa a kan Tgr
Haka kawai ya samu kansa da sakin murmushi yana mai son gannin tsererenta idan ta ga Tgr
A hankali ya ci gaba da takawa ya idasa fitowa gaba dayansa direct ya nufi wajen Dinern hankali kwonce
Sansanyan kamshin turaransa ya saka an lumahe idannuwanta kafin ta dago dubanta a hankali, sai dai abinda ta gani ya sakata saurin maida kan nata jikinta na rawa ta yi shiru tamkar gawa danma kar a ji motsinta a wajen har suka wuceta suka fara taka yar matatakalar hawa wajen table din
Yar shewa Muneerath ta saki tana kai hannunta kusa da kafadar Saudat ta ce" Ke dillah ki bari, yanzun dan zai zo zance sai ya shigar da takarda?, Ai yau yau zan saka a kawo shi zance gidan nan ya kuma shigo har falon nan mu zanta mu fafata abinmu, ai dai zaki zauna a kusa da ni ko?"
Saudatma ta yi yar dariyarta ta ce" ai kece fafatawar, kin ga a yadda ya damu kan yana so ya ganki gashi kwana biyu cif tunda muka shigo bamu ga waje ba ya dace mu dan sama masa dan time dinsa , kin ga fa soyaya ciyar da ita ake ba mantawa ake yi da ita ba fa"
Muneerath ta dan talabe habarta ta yi luuuu da idannuwanta a hankali cikin yaren turanci wannan karron ta ce" Ban san zan so wani halitar da ba dogari ba Saudat, wani sa'in sai na ji ina son Sir sosai bale idan kina koda min shi sai na ga ai shima da nasa ikon a inda yake, ya Allah ka yaye min matsalar sarauta dake zuciyata na fuskanci abin sona mu so junna mu yi aure"
Saudat ta girgiza kanta da dan kari kari ta ce" Dogari?, Wai dan girman Allah su rasa ina zasu sauko ki sai nan?, Dogari mutun ne mai daraja aman a kan me zasu sauko maki burinki na son zama sarauniya?, Ai ba'a sacewa bawa gwuiwa komai kaskancinsa domin ba'a san meye Allah ya boye a tare da shi ba, waye ya san gobe ne?, Kin wani damu dogari dogari kin kuwa gane ainahin aikin dogari? Dogari irin na kasarmu?"
Muneerath ta mike daga zaunen da take, hakan ya sa doguwar rigar dake jikinta fara ta idasa sauka tana rawa a jikinta ta dan watsa hannayenta ta ce" Ba zaki gane ba, ni fa ba wai kudinsa ko wani yannayin rayuwarsa bane damuwata, Saudat buri ne da mafarki da na tashi da shi yake bani wahala, ki duba ki ga irin wh....................."
Katsewa maganarta ta yi a lokacin da idannuwanta suka sauka a kan fuskarsa
Sajen fuskarsa mai kyalin baki da lebunnansa zuwa uwa uba fitinanun idannuwansa masu kallon wuce ka'ida da ya zuba mata
Sanye yake da suit ash color masu farar riga a ciki mai duhun haske
Gashin kan nan nasa ya sha mahaukacin gyara sai kyali yake
Da farko a kansa dubanta ya tsaya, ta yi ta yi ta cire ta kasa aiwatar da hakan , hakan ya sa ta samu da kyar ta lumshe idannuwanta tana jin wasu kwala sun cika mata su masu zafin da suka hadasa mata jin ciwon ido kafin kunnayenta su jiyo mata amon muryarsa ba ihu ko kadan cen kasa kasa ya amsa kira a wayar dake hannunsa ya ce" Ka sanyo su baban falo nan da awa guda idan na gama karyawa"
Yana gama wannan ya danna wani kiran wanda yana dagowa ya kuma saukewa a kan furkarta da yannayinta kafin ya saci kallon Saudat da ta mike itama ta sada kai jikinta na dan bari tamkar yadda suke mada a wajen aikin nan, ya kuma maidawa kan Muneerath wace bata taba yin barin nan dan yana waje ba ya karra zuba mata ido, dan siririn dan kwali fari
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 42