Share this page
abinda ya faru ya zama dole ya ziyarci wajen nan dan ya dauki wa鈥檌nda zasu maye gurbin wace ta rasun Daga cikin motocin ne manyan sojojinmu na niger manyan da ganninsu sai a TV, wa鈥檌nda suke kusa da shugaban kasa , sai baban sarkin Niger tare da manyan dogaransa suka fito suka bude bangaren da sarki yake Idannuwa Muneerah ta zarro a lokacin da ta yi arba da dogarai Jikinta ne ta ji ya fara rawa rawa a dan rikice cen kasan makoshinta tace" Dogari " Bata ankara ba ta ga sarki ya fito cikin shigarsa ta alfarma gefensa wani datijo mai shigar costume bakake kansa aske tas tas ba gashi ko dis a jiki fari ne kal fuskarsa dauke da yalwataciyar fara鈥檃 ya kara mikawa mai girma sarki hannu wanda shima ya amshi hannunsa fuskarsa dauke da yalwataciyar fara鈥檃r A hankali Muneerath ta ce" Wayo Allahna dogarai ne birjik yau a gaban idannuwana tare da sarki? " Saudat ce ta riko hannunta ta ce" wai da gaske abinda ya fada ko menene? Me yakawo sarkin ingila kasarmu ? Me suka zo yi nan wajenmu? Ikon Allah" Ameerah ce ta yi saurin kallon yan matan ita kanta bata gaskata abinda kunnayenta suka jiye mAta ba, abinda dai ta sani mutanen nan da suka fito daga cikin mota na kasarmu manyan mutane ne da haka kawai ba zasu tashi su tako su zo nan ba koda kuwa makarantar babar makaranta ce da ake ji da ita a niger baki data dan tana daya daga cikin manyan abubuwan dake shigo da gunduma gunduman kudade a kasarmu, aman abu daya ne ta sani "Prince" din ingila da aka ce shine baban ogansu a cen baban kampanin jirgin air peace, shine baban matukin jirgin da kampaninika da dama ke kokowar son gannin ya zama nasu, yana daya daga cikin masu kwakwaluwar kera wannan abu mai shegen nauyin dake tashi a sararin samaniya tamkar leda, shi din nan shine mai jiran gadon mahaifinsa, ko dan aikin gidansa ka samu gani kai din kanka ka zama cele bale shi da kansa, kai baima taba saukar da jirgi a africa ba , koda ya saukar a yanzun bata tunanin idan zai dauko passinger niger, bale har a yi tunanin ganninsa a wannan waje kamar a mafarki, kai da suma sun zama cele, makarantarsu kuwa da ta gama zama babar makarantar da a gabanan gaskiya har yan kasashen ketare zasu dauko , Kasancewar sunna sanye da kayan girki ne kowace wando da riga mai dan tsayi har kusan gwuiwa da abin girki a daure a gaban rigarsu da farar hula ba komai a hannayensu bale a yatsotsunsu dan idan zasu yo girki komai cirewa suke dan samuwar tabataciyar tsafta a wajen aikin abincim nasu, da dan saurin magana ta ce" kowace ta koma dakinta ta rufe ta yi connectd ta yi abin karuwa mun yi baki idan sun tafi zan kiraku mu je wajen Sir kan maganar yarinyar nan, du wace ta so rufa mata asiri ko ta yi niyar kareta dan kar na ci galaba a kanta a koreta sai dai a kore su su biyu dan na rantse maku sai na jaza maku matsalar da ba zaku taba fitar da kanku a ciki ba! Sai na maku shari da ba zaku tana samun lafia a cikin duniya ba dan kuwa sai na saka ku a ukun da baku taba zato ba! Bale ke Saudat kin san ni ma saka hannu aka dauke ki ba dan kudin papanki ya isa ba sai dan muna mutunci da shi, a yanzuma na saka ki koma masa abu me mafi sauki a wajena idan kika min rashin mutunci!" Muneerath na kallonta hawaye aun cika mata idannuwanta muryarta a sanyaye ta ce" ke bakya taimako domin Allah? A cikinmu shin kowa ne ya iya komai yadda ake so? Da yawa sunna da matsaloli a wurare daban daban, me yasa ba zaki taimaka min na iya ba? Me yasa ba zaki talafa min na samu cikar burina ba?" Sai da Ameerah ta yatsina fuskarta kafin ta juya rai bace tace" Dan baki yi min b.........," bata kai ga karasa maganarta ba ta tsaye mata a saman harshe sakamakon gannin abinda idannuwanta ke gane mata Shin shi din ne da take gani a jaridu ko mai kama da shi ne? Dan bakin dan kwalin dake jikin mamansa yake gyara mata sai wata zukekiyar yarinya a gefensu matashiya da zata kai shekara ashirin da bakwai haka danma yannayin dadi ya boye yawan shekarunta balarabiya ce sak sai shinning take yi A bayane ta shiga fadin" what? HANJA? " Kamar a mafaki suke kallon wannan lamari, daga inda suke ba zasu iya cewa ga kamaninsa ba dan ya yi nisa da su sosai sa dai irin yadda haskensa ya kawo inda suke da irin yadda gaba daya aka aniyar kokarin kakare shi kamar wa鈥檌nda suke tsoron kar kuda ya taba masa lalausar fatar jikinsa sai dai ina tsayinsa ba zai basu wannan dama ba uwa uba irin yadda ya daure fuskarsa kamar wanda yake daf da fashewa da kula mai tsanani dan kuwa ba karamin takaici ya ji a zuciyarsa ba a lokacin da mahaifinsa ya matsa sai sun gana da sarkin garin harda fadi da babar murya cewa ai tun yanzu ya dace ya saba da sarakai dan kuwa babu sarkin da zai ce ya isarma kansa sai wanda ya halici sarakai, wannan shi kadai ne ya isarma kansa A dake sannan cen kasa kasa yace聽" Mah, ku koma cikin mota mutane sun yi yawa, ba wani zama zan yi ba zan amshi wata ne a nan da zata mana rakiya har zuwa cen din plz聽禄 Aleesa ta yi murmushi tana girgiza kanta ta ce" Tunda ka li yarda cewar ko bamu dauki wata ba muna iya ci gaba da tafiarmu nima sai ka barni na ga yadda kuke daukan yan matan cikin jirgin nan聽" Murmushin yake ya yi da idannuwansa ya zabgawa budurwar nan harara ya mata nuni da motar da idannuwansa ba tare da ya buda bakinsa ko ya yi anfani da hannayensa ba Da sauri ta juya har kamar zata kifa ta yi gagawar shigewa cikin motar da aka bude mata tana sauke ajiya zuciya kafin ta hangi bayansa ta kura masa ido tana kallonsa Karasawa ya yi wajen mahaifinsa, muryarsa ya rage sosai kafin yace" ya dace ka ja matarka ku koma mota sir " Mahaifinsa ya kale shi ya tabe baki ya ce聽" idan aka ki fa? " Dan murmushi ya yi a hankali ya ce" na sanma ba zaka ki ba, ina son na gana da su ne aiki ne fa?聽" Murmushi ya yi yana kallon matarsa yadda take kallon mutanen wajen cike da admiration shima ya rage muryarsa sosai ya ce" ka ga kaunarta ta gama mamaye min kaf jinnin dake gudana a jikina, tun daga lokacin da zamu taso take cewa kafarta kafarka, kawai ku je ku yi aikin tare mana dan ba zan iya bata mata rai a dan lokacin da ya rage mana da junna ba聽" Kallon mahaifin nasa yake nan da nan ya yi kici kicin da fuskarsa rai bace yace" bamu dora dokar ba zaka ringa min maganar nan ba?聽" Mahaifinsa ya sakar masa murmushi ya ce" sorry " HANJA ya ce" ka sha maganinka?" Mahaifinsa ya kai hannunsa eajen gaban goshinsa ya sara masa ya ce" Yes sir " HANJA ya dan girgiza kansa yana kallonsu suka juya suka yi gaba tare da sarkin da dogarai kama daga masu rike lema da masu tafe sunna kirari abinsu suka nufi cen ciki dan zagayen makarantar Magana ake yi mata aman har ga Allah kunnayenta basu ji ba, a gabanta Saudat ta tsaya da sauri da murya mai amon gaske sannan tana jijiga hanayenta ta ce" Muneeraht ki wuce mu je dakin taro sun tafi sun barmu ta baya tun dazu" Firgigit ta yi cike da zabura a tsorace da jin ihun a kanta tana kallonta ta ce聽" Lafia?" Saudat ta juya ta fara tafia tana jan hannunta ta ce" ki wuce mu je ciki kina gannin sn shige gaba dayansu!" Biye take da ita dan janta take da sauri sauri har suka bude kofa ta baya suka sanyo kansu Muneerath tace" Saudat baki ga dogarai ba? " Kasancewar kawancensu sun san sirrin kowace wanda take da burin aure sai hakan bai ba Saudat mamaki ba , ita dai janta ta yi suka zauna a layin kujeru na biyu dan na gaban yan matan sun cike su sai Ameerah da sir da sauran manyan ma鈥檃ikatan gidan da suka halarta nan da nan Daga gaba kuwa wajen kujerun alfarma sojoji ne a tsaitsaye du sun zagaye dakin taron ta yadda idan mai rabon daukan ba dadin zara iya sauka akansa Kasa kasa Muneerah ta ce聽" Saudat, mu yi mu tashi mu je wajen su kafin su tafi dan Allah na gaishe su" Saudat itama kasa kasa ta ce" Da alamu fadan Ameerah baya zuciyarki ko? Kina ji fa abinda ta ce maimakun mu yi tunanin abinda zai raba mu da ita lafia ke ta wani dogarim cen kike dogain banza dogarin wofi!" Muneerath ta ce " ranki ne ya bace ban sani ba? Ki yi hakuri Saudat kin ga ameerah babu abinda zan yi na birgeta, na tabata Allahn dake tsaya min shi zai tsaya min, kuma kin ga idan freind ya ji abinda ya faru in sha Allahu ba zai kore ni ba, ni na tabata yadda na samu kaina a gidan nan Allah ba zai bada damar a wulakanta ni ba, aman tsakani da Allah shin zaki ce dogarin banza ? A da fa du wanda ya ce da dogari banza ne walahi sai infa karfina ya kare fa" Wani irin abu da aka busa ya saka su baki dayansu tsorata kafin nan da nan a bude wajen su shigo Shigarsa ce ta kaki irin na matuka jirgi, a yau bakake ne a jikinsa sannan galolinsa na jikinsa Gashin kansa gaba daya baya yake dan ya mayar da shi baya , yannayinsa na ingarman namiji ya karra karuwa a tare da shi, idan ka kale shi dole ka ji gabanka ya fadi dan mutun ne tsayaye ga fuskarsa a hade take tamkar bai taba yin daria ba Baki dayansu tsayawa suka yi, dan kuwa da hannu Sir ya masu nuni kan su mike, su din kansu sun nutsu dan kuwa nutsuwar da suka ga uban gidansu ya yi ta fi basu mamaki Kujerar da aka ja masa bai je inda take ba, daga tsayen da yake a tsakiyar dakin taron kowa yake bi da kallo kafin yabudi bakinsa kasa kasa ya ce聽" Asalamu alaikum " Baki Muneerath ta hangame jin ya yi masu salama kasa kasa ta ce聽" Ke saudat kin ji salama fa ya yi cikakiya, ko dai musulmi ne?" Saudat gannin ya masu nuni da hannayensa kan su zana kuma Sir ya nufo inda yake yana masa bayani da wasu file file a hanayensa Ameerah na gefe ita kanta ta wani nutsu tanamikowa sir yana mikawa HANJA sai ta rag muryarta sosai duda hankalinta ba a kwonce ba tsoron mutumen take haka kawai a zuciyarta ta ce聽" Muneerath bakya karanta jaridar da ta shafi manyanmu ne?, wannan fa sarki ne kuma baban matukin jirgi ne wato pilot, sannan da kika ganshi a nan ya iya kera jirgi" Muneerath ta mata galala da ido jin wani rainin hankali kafin takai dubanta kansa zuwa lokacin ya tsaya kikam a gabansu yana karewa na gaban kallo balema wa鈥檌nda ameerah ta yarda da kwarewarsu a aikin, da tsarin kyansu da komai da komai tana karra yi masa bayani Tun daga kasa har sama ta karra debowa ta sake binsa da kallo kafin ta ji wani irin tashin hankalin da baa tana tunanin zai sameta a irin lokacin nan datake tsaka mai wuya ba, walahi ba kowa ya cuceta ba sai Saudat da ta kaleta ta kalli wannan mai kirar yan dben yaro karamin mai taa gashi irin na yan iska, ga gunduma gunduman hannaye soja sak ta ce wai sarki, fisabililahi sarautar iskanci ta zama ko dai rabon karshen kwananta ne ya zo mata a haka a yau? Ko dai irin ta ga samu ta ga rashi ne zai idasa samunta a aikace ba labari ba, a lokacin da ta ji wannan dariar da sai an hannaka yinta take cizo ka, irin dariar nan da bata zuwa sai wajen jin kunya, wannan dariar marar mutunci da bata tashi zuwarma bawa sai ta ga wajen kumya ko wajen ya shiga uku ce ta kubce mata hade da yannayi mai karra neman fitina ga mai lafiama bale wanda yake jira a daku, ta dubi Saudat da ta ji fitsari ya faa zubo mata sakamakon gannin ikon Allah da bakar rana gannin idannuwanta da kawancenta da Muneerath ke shirin janyo masu shiga uku da tashin hankali marar musaltuwa, lokaci daya ta ji dama summa ta yi da wannan idannuwan da suka zubo maa riiiiiiiii tamkar mujiya ciki kuwa harda masu ja uwa gauta uwa uba malamin dake tsaye wanda ko uban gidansu na tsaye a kusa da shi ne jinni a akaifa shine Muneerath ta budi bakinta ta saki yar iskar dariarta a irin wannan lokacin da take bakin kofa Bata idasa tsurewa ba ta zube kasa kan gwuiwoyinta hannayenta saman kanta ba sai da ta ji Muneerath ta budi bakinta ta cenza garshe zuwa gogagen turancinta ma hade da hausarta gogagiya da french dinta gogage ta ce" Ke lear ko? Wannan mai kama da yan damben ne sarki?" Rabon a yi, baban rabon a yi, a hankali ta yi maganarta bata san wa ya murda waje karin volume din makogwaronta ba sauti ya fito ba Kukan da Saudat ta fashe da shi tana fadin mun shiga uku mun lalace, da irin yadda Sir ya aniya rike igoyar wandonsa wato belt tamkar wanda za zuba da gudu ya je ya zuba zawo ba, da zaburar da Ameerah ta yi ta nufo su ramta bace tana zuwa bata yi wata wata ba ta daga hannunta ta Da kyar wollah馃槦 Sorry d errr typng 11/14/21, 12:47 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 2锔忊儯0锔忊儯 Tana zuwa bata yi wata wata ba ta falawa fuskar Muneerath mari wace sai a lokacin ta dawo cikin hayacinta gaa dayanta ta kurawa kowa ido A yanzun ta gama yada cewa tata ta sameta, idanma suka koreta ta komawa oga mutun cikakiya ai sun masu mutunci A hankali ta lumsheidannuwanta daga jin yadda juwa ke neman dimata da kasata sauke dubanta a kan Ameerah tana dane kanta da daukan hannunta ta kwada mata marin idan ya so a yi wace za鈥檃 yi dan kuwa darajar kanta ta sani ba zara kyale yar iskar nan ba "Ya salam, me yake faruwa harda mari? Yaya haka da saurin mari a fuska waje mai daraja, Son me yasa ta mareta?" Aleesa ta fadda da muryata a sanyaye aman kuma kalamanta na nuni a hankalinta a tashe yake Da sauri sir ya hade hannayensa biyu shima da yaren turancin ya ce" dan Allah ku yi hakuri sir, yarinya ce bata san abinda ake ciki ba aman zan mata fada sosai ita da kanta tana baka hakuri " Ameerahma ta dawo da sauri tana hade hannayenta tace" wani hakuri zata bada? Sir yarinyar nan bata da kunya, sam bata san girman manya ba, tunda muke bata formation ta kasa koda dafa tea mai kyau ne, bata iya tafia da dogon takalmi ba, bata iya kwaliya ba, ko kitso bata so a mata sai shirme da raina mutane bayan ko sisi bata biya a nan!" Sai da ta gama fada kafin kuma ta tuna cewa idan ruwa ne ta balo ta balo harda ita a ciki, domin kuwa vote aka yi da tawun bakinta Muneerath ke gidan, bandama wannan ba zata taba son wani abu ya samu aikin Sir ba, dan ita kanta tana zaune ne da taimakonsa domin kuwa da farko gaba suka sakota sosai Da ido yake bin kowa, irin yadda dakin taron ya rikice kowa ka kalla sai zarro ido yake sannan du sunna nunata irin ta dai daukowa kanta ruwan dafa kanta Bakinsa ya tabe ya kama hannun mamansa dake ta kokarin ta karasa wajen Muneerath yana karra yatsina fuskarsa a sanyaye ya ce " ina zaki je Mah? " Mamansa ta ce" kuka fa take kana gani ta mareta kan me? Dan ta yi daria? Dama haka aikinku yake da tsauri?" A hankali ya dawo da ita kusa da shi kafin ya juya da ita ya kaita wajen kujerar da aka janyo masa dan ya zauna ya janyota da kyau ya zanar da ita yana kallonta a ransa yana ayanna鈥 ta yaya zaka iya aiwatar da aikinka idan Mah na nan, ba zata taba bari ba 鈥 A hankali yace" zauna bara na je na ji a kan me ta mareta " Kanta ta gyada tana kallonsa ya sauko daga wajen ya nufo inda suke Da hannunsa yamasu nuni kan su karra matsawa kusa da yan matan A lokacin da suke matsowa Muneerath sai a lokacin ta ji kafafuwanta sunna neman tona mata asiri ta hanyar yi mata tawaye, domin sau uku tana gwada daga kafarta dan ta arta a guje aman sai ta ji an riketa a wajen mugun rikon da ta kasa tsawatarwa kafafun nata har suka cin mata A dake sannan kasa da muryarsa sosai ya ce" du wata dake min kuka ta hadiye haukanta a wajen nan kar ta tadawa mamana hankali, sannan kowace ta matso sosai ku saurare ni!" Kasancewar da ainahin inglish ya yi maganar kwararen inglish tatace a cikinsu idan ka cire sir da Ameerah sai Muneerath sai ko Saudat da ta tsinci dan abinda ba鈥檃 rasa ba Yana hankalce da su da sauri Ameerah ta tatabo su da hannayenta ta daidaita su, sai dai Saudat da Muneerath da kansu suka matso din suka bada hankulansu A dakensa ya ce" ina son a bani bayani dala dala na abinda yake faruwa a gidan nan! Wani irin abu ne kuke kwabawa? Wace irin tarbiya ce kuke bawa dalibanku? Meye maganar ba sisi da kuma maganar komai baa iya ba? Ina so maganarku ta kasance kasa kasa ta yadda ba zai kai kunnan mahaifiyata ba!聽" A dake ne ya yi magangannun nan, sannan a cicire ne ya yi su, haka kuma tsayuwarsa ya yi wace zata kare Aleesa da gannin komai, haka kuma yana yin maganar ne yana karra dunkule hannunsa dake nuni da da ace babu wani shigen dake hanna masa rawar gaban hantsi da koda bai iya ashar ba da an ji duka irin mai gigita bawan nan Sir ne ya dauki magana da sauri sauri da inda inda kafin ya karasheta yana mai sadda kansa cike da firgicin ranar da nan da Muneerath ta aikata aikin nan, zai iya cewa a yau ya yi nadamar kafafiyar zuciyarsa da ta nace kan sai an dauketa, shi din da kansa ya san ya gama yawo A kausashe ya ce" wani irin banzan zance ne kake fada min haka? Baka ga takardunta na shaidar ta yi karatun girki ba, baka ga na shaidar ta iya ruwa ba, a kasashenku da ake kawo maku hare hare, idan har da gasken turota aka yi ta ilata ku?聽禄 A sanyaye ta budi bakinta ba tare da ta jira an bata damar magana ba, ita fa hasalima gani ta yi normal magana ce ake yi da kowa ta yadda kowa ke fahimta kuma tana iya karre kanta daga kokarin da ake a hadata da yar ta鈥檃da ta fara magana da tsadadan turancinta wanda bata yi wasa wajen iya shi ba ta ce" walahil azim ni ba yar ta鈥檃da bace, ban san menene kalmar nan ba, ban rayu da wannan a zuciyata ba, alfarmar Allah nake ci, ni ba yar kowa bace dan ko iyayena basu waiwayeni a nan ba, abinda na sani na rayu da burin zama HOTTESTE shi yasa na dage ma yi karatu da dukan karfina da nutsuwata, ban zo nan da na lalata komai ba sai dan na ga yaya gidan yake na fada a tarihin rahuwaa cewar na yi yaki da son zama hotteste na kuma fadawa Allah kan ya datar da ni na zama mafarkina ne bai cika ba ba laifina bane, ban kasance mai zubar da burina da sauki ba shi yasa kulun nake tare hanya dan na kalli dogari, ni ba mahauk..,,,,,,,,,," Da dan daga murya Ameerah dake jin kamar ta rike makogwaron Muneerath dan haushi ta ce" zaki mana shiru a man uban wa ya baki damar yin magana ko dan baki da tabiya?" Wani mugun kallo da ya watsawa ameerah sakamakon daga muryar da ta yi na uku kennan tun da ya zo wajen nan har tana neman hadasa masa ciwon kai ya sakata yin shiru tana rage muryarta sosai ta ce" ka yi hakuri sir, wannan yarinyar sam bata da yannayi da tarbiyar hottes, caractere dinta ba na irin aikinmu bane, wannan tana iya zubawa pasinger tea mai zafi a jikinsa ko ta tsoratar da shi " Muneerath kam yanzun ta shaka , ranta bace sannan kasa kasa sosai ta ce" akoy marar tarbiya irinki ? Shin kin tsane ni ne domin na kasance mai taka dokokin Allah ko kin tsane ni ne dan bakya son kalar fatata? Ke wai Allahn da ya yiki ya maki albishir din a haka zaki gama da duniya ko tunaninki ke zaki zauna a wajen nan har duniya ta nade? Kafin ki zo wata ke wajen haka kuma zaki bar wajen du nacinki wata ta hau dan babu abinda ke zama dindindin a duniya ita dukanta karya ce! Kuma idan takamarki ke wata ce ni nan zan auri dogari kwana kusa zan zama yar uwa sarki kwana kusa zaki dawo talakata zan zo nan na hanna ki wulakanta mutane! Ku rike Hotteste dinku haka Allah yahukunta min ba wani ba!聽Takai dubanta kan ameerah da gaba daya ta gama tsurewa da kuma yarda cewar muneerah fa mahaukaciya ce ta ce" ke kuwa da kika mareni Allah in dai tsautsayi ya hadani da ke a waje sai na nanaga keyarki a kasa, idan ba haka ba kuwa na barki da Allah wuta balbal!聽". Wato Allah na yin bayin Allahn da sam basa tsoron budar bakinsu su fadin abinda ke cikin zuciyarsu ko a gaban waye, bale rayuwar Muneerath ta yita ne cikin ihu a makwontai, watau tana magana ne tun tana tsoron fadi har ya zamana fadi take tun karfinta kuma s take dole a saurareta Walahi bai taba gannin fitinaniya, fitsarariya, tsayayiyar yarinya irin wannan ba, a yau da ace Mah bata dakin taron nan da sai ya tsiyayewa yarinyar nan kaf man dake kanta! A yanayinsa na nutsuwa koda ransa a bace , sannan muryarsa cen kasa kasa dan kar ya masu ihun da gaba daya za鈥檃 shiga uku ga mamansa ya zaunar da ita a cen bayansa a tunaninsa bai san ta taso tuni tana bayansa tana saurare da kuma bin kowa da kallo ba a hankali yana kallonta yadda ta tsafe abinta ita ta san korarta za鈥檃 yi kennan ko wace wace ya ce"Hey" Ga mamakin kowa na wajen nan juyoea ta yi ta ce" tsaya in gama sai ka kore nin kai kuma!" Ta dora da fadin" Saudat ba abinda ta yi, kuma ita ta iya girki, ta iya ruwa, ta iya tafia saman dogon takalmi na tabata ko dan kar ranmahaifinta ya bace zata jure wulakancinku na adadin kwanakin da kuke son tafka mata, ku rufa asiri dan soyayarku da fiyayan halita kar hukuncina ya shafeta! A kore ni ni ita a barta ta yi abinta, ga dukkan alamu aikin Hottest din nan karuwanci ne dan gashi dan ban iya tafia da dogon takalmi ina karairaya ba za鈥檃 kore ni!" Baiwar iya yarensu da Allah ya bata ne ya sakata zagewa ta fadi komai da turanci kafin ta juya da niyar tafiarta tunda ta gama fada zuciyarta

Chapter 11 of 42