馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
6锔忊儯2锔忊儯
A hankali ta kuma dan kokarin kwace kanta tana rintse idannuwanta dan jin yadda gaba faya zuciyarta ke neman biyowa ta bakinta ta fito
"Innalilahi" ta fada tana jin ta kasa wani kwakwaran motsi a rikon da ya mata
A hankali cikin dan fada fada ta ce" Ka sakeni, ka wani rikeni kai dai kowace banza tana iya hawa kirjinka kau? Sakarni kar a shiga min zanen cikin yan iska"
Mamakin dake neman kasarashi a kan yarinyar nan sai irin karfin da take da shi a tatare da shi
Ya jima da wuce bangaren da daga ya kalli mace ya ji halitarsa ta motsa sai da ya farra ganninta
A hankali ya fara tsorata da koda son rike hannunta ne bale kafeta da yake da ido shi kadai ya san me yake son karanta a tare da ita da ta fi sauran matan da yake mu'amala da su
Ya yi tunanin ko kalar fatarta ke birge shi? Ya yi tunanin ko wannan bombom din nata ke haukata shi? A yanzu haka ba wai son sakintan bane baya yi, wollah abinda ya mike masa kamar sanda yake jin kunyar aminiyarta da Iman da sukai masa kurru gani
Hakanma sabo ne a gare shi wai jin kunyar a ga yannayinsa
A hankali ya rage muryarsa ya ce" Me yasa dan na rike wata a jikina yake baki haushi? Munarah kina jin haushin na taba wata ba ke ba , kuma ke na taba ki kina cewa iskanci ne, ni kam meye wai irin naku al'adun da ake yi da wa'inda ba'a yi"
Ajiyar zuciya ta ringa saukewa sakamakon sajensa da kuma hucinsa dake sauka a kuncinta, sajensa kuma sai sosa mata lebe suke
A hankali ta ce" Dan Allah sakeni fitsari nake ji"
Sai da ya ji tamkar jinnin jikinsa zai tsaya, a hankali ya ringa dabarar sakatan dan shima ya fahimci idan ba sakatan ya yi ba komai na iya faruwa
Yana cikata da sauri ya juya har yana jin kamar numfashinsa na gaf da tsayawa ya wuce su da wani irin sauri ya shige Lft ya sauka dan so yake ya yi bangarensa ya zauna ko zai samu nutsuwa
Ido da ido suka kalli Junna da Iman, a hankali ta so cire dubanta a cikin na Iman din, sai dai hakan ta gagara sakamakon mugun kallon da ta kula Iman ta tsareta da shi
Muryarta ba karfi ta ce" Ke kuwa me ya samu idannuwanki?, Na ga kamar hararena kike"
Iman ra hadiye abinda take ji a ranta ta ce" Ba kama bace, ba kama bace Muneerath, na gaji, walahi na gaji, me kike so da ni ne dan Allah? Dukan abinda yake nawa kin karbe, harta kusancina da Mah kin amshe bayan kusancina fa Mah ya fi kusancinta da Hanja din kansa da kike ta budewa da isar naki ne, kin kuwa san irin lokacin da na dauka ina dama da soyayarsa? Kin san irin son da nake masa?"
Muneerath dake kallonta a hankali ta ce" Ni yanzun ina hadina da maganar son da kike masa? Idan soyayarku kuke kin taba gannin na yi magana ne? In dan rike nin nan da ya yi ne ki yi hakuri, ni da kaina abin na damuna, sai ace shi musulmi ne, sai ace shi dan musulmai ne sai kuma ya ringa rike mutun a jikinsa bayan ni ba muharamarsa ba, kin ga soyayata da Mah kuma Allah ne ya hadata, ni dai ba danginta bace aman ta rikeni tamkar yar cikinta, wannan kuma ban san yaya zan yi na hanna ba, Iman me yasa kike nemana da fitina ne? Kin ga ni yanzun zazabi ne ya sauko min har rawa jikina yake, mai yiwuwa mutuwa cema zan yi dan zufa ta karyo min, zuciyata ta kusa fito min ta baki, koma menene ki yafe min Hanja kuma ki dafa ki cinye abinki"
Iman ta ce" Abinki dai, gashi kiri kiri kina son min shigar sauri a wajensa? Abin takaicina kamar makauniya, kamar kurma, kamar mahaukaciya idan kina abu kamar innocent, maganar rungumewa kuma ai Hanja kakansu yake yi, a yau idan ya yi niya sai ya kwonta da mace biyu su kwana a jikinsa, maganar adini kuma ai inaga ba ke ba ya dame kaf ahalinki ya shanye a fannin harda!"
Muneerath ta lumshe idannuwanta , jikinta ya karra mutuwa, shin me yasa Iman ba zata daina mata abubuwan da take yi mata ba? Me yasa kuma idan ta nuna mata tana cikin halin son kadaice kanta bata ganewa? Bata da lafia Bon sang!, Bata cikin mood da kowace irin magana a yanzu! Gaba daya ji take karshenta ne ya zo , tata ce ta kare, shine zata ringa fada mata maganar cewa Hanja na kwana da mata biyu? Dama haka yake? Dama haka ne halayensa? A dan kaushashe ta ce" Ban ga anfanin tarin sannin nasa da baya anfani da shi, Iman wani irin so kike ikirarin kinaiwa Hanja?, Koma wanene so din nan na tsine masa albarka, Iman , Hanja ba saurayina bane, hauka kike rabawa, shirme kike yi, kuma ina matukar tausaya maki, ke baki da zuciya ne? Namijin da kika san yana aikata irin haka da wasu matan ne har kike yiwa irin so din nan?, Ina zaki je da matsalarsa? Ina zaki je da fama da shi? Ko zaki rayu da shi a hakanma?...."
Ta hadiyi yawu tana kallon yadda Saudat ta dawo ta rike hannunta fuskarta na nuna matsananciyar damuwa , a hankali ta ci gaba da fadin" Ko kema aikin da kike na facebook ba iya nan kika tsaya ba? , Ba'a taraya sai halaya ya zo daya, Iman kema aikinki kennan?, Iman ni da ban hada jinni da shi ba, ban hada soyaya da shi ba, wannan abin da kika fada yana kona min zuciyata fiye da tunaninki, Iman ji nake tamkar na yi ra kuka da dukan karfina har sai muryata ta daina fita, Iman ciwo nake ji jin haka yake, ya fara zama abokina, ya fara zama yayana, na fara fahimtar waye shi, sai ki saka min tsanarsa a raina?, Iman halayan nan nasa har ya kai a bayane kowa ya sani? Me mamansa ta dauka mataki? Me mahaifinsa ya dauka? Ko kallon da nake masu na iyaye masu matukar kaunar y'ayansu, masu matukar tsayawa a lamarin yaronsu soyayar bata kai zuci ba?, Iman.......Im......"
Kuka ne ya ci karfin Muneerath, ur Muneerath mai karfin zuciya, Muneerath dinmu da bata san gabas ba, Muneerath dinmu da karamin abu ko nace abu mai tana zuciya baya gagawar taba tata, Muneerath dinmu da ko kukan da ta yi na faduwar Mah nan da nan ta saku da ta ganta a garin harma ta ga da sauki, itace ta fashe da kukan da bata san me yasa ba
Tun karfi ta dora kanta a saman kirjin Saudat tana rusa kukan da dukan karfinta
Muryarta a cen ciki take fadin" Dan Allah, dan Allah ku taimake ni, walahi na rasa gane kaina, dan Allah ku nisantani da kasar nan, ku kaini nesa, daga garinmu zan iya aikowa da Mah adu'a, daga inda nake zan iya yiwa Mah adu'ar samun lafia, Saudat dan Allah ki kirayi Freind a maida ni gida, ba zan iya ba, walahi zuciyata gaf take da bugawa ban san dalili ba, shi kuma ribar me yake ci da wannan abin? Saudat na tsane shi! Na tsane shi!"
Subahannalah, wannan shine ba sabanba namiji da kwontace
Tabas wannan bacin rai da ya rufe ma Muneerath ido tsabar tsagworon kishin da take fama da shi ne ya sakata irin furucin nan, ba sani ta yi ba, ba taba yi ta yi ba, lalle akoy ciwo ka ji wani da kake gannin darajarsa a irin wannan halin aman ta kasa gane cewar abinda ya sa abin nan ya taba zuciyarta har haka dan ta gama macewa a kogin son dan nasara ba tare da ta shiryawa hakan ba, kamar yadda ya gama haukacewa a sonta
A yanzu matsalarta daya ce, kuma tana gannin idan hakan ya kasance gaba dayansu farin cikin hakan zasu shiga
Taba so Na iya cenza mutun, mai mumunan hali ya dawo mai kyakyawa a lokacin da ba'ai tunanin hakan ba
So take ta yi anfani da wannan damar ta samu ta yiwa Hanja dukan da so zai saka shi daina halayansa, duda tana tunanin da kamar wuya
Aman zata kwatanta, tsoronta daya ne kar a je ya kasa zama waje daya ya kula da lafiyar mahaifiyarsa
A hankali ta ringa janta har suka shige suka sauka
Sunna saukowar bata hannata kukan da take yi ba wanda ya saka Pah mikewa da sauri domin falon yake bai jima da saukowa ba, masalaci ya fito shine ya zauna yana jan carbi yana gannin matarsa na masa gizo ta ko'ina a cikin gidan, yana fama da kewarta mai girman gaske
"Subahannalah, me yake faruwa, bata da lafia ne?"
Ya fada yana nufo su yana kallonsu da wani yannayi na tsoron jin abinda ya sajata kukan
Da sauri Saudat ta ce" Ba komai fa Pah, kawai wani dan abu ne ya sakata kukan nan har take cewa zata mutu a kaita Niger". Ta fada da sauri dan kar ya yi tunanin kukan ko na matarsa ne shi mai majinyaciya a kwonce
Muneerath ta dago tana jan hanci ta karra fashewa da kuka tana fadin" Wannan ne karamin? Ke yanzu dan Allah bakya jin kamar zaki mutu da kika ji maganar nan?"
A hankali Saudat ta girgiza kai tana kawar da kan nata cike da son dane dariyar yannayin na Muneerath
Muneerath ta ce" Baku shaku ba shi yasa, aman ni fa muka shaku dole na ji ciwo a raina, Pah wai Hanja, HANJA"
Sai ta kasa karasawa dan tana tsoron kar a je bai sani ba ta fada masa juma a samu matsala
Pah da kula ya ce" Daughter kukan nan ya isa haka , ki daina sshi ki fadan me Hanja din ya yi ne?"
Hanci ta ja tana kallon Saudat ta ce" Fada masa "
Saudat ta zarro ido tana kallonta, sai dai ba zata iya musawa baa domin a tsaye yake a kana kafafuwansa yana jiran jin dalilin kukan, sai dai gaskiya ta gama cutarta
Cike da jin kunya ta fadi abinda ya farun da dalilin kukan na Muneerath tana ji a ranta Idan suka kasance daga ita sai ita sai ta rama walahi!
Pah ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" Daughter shine kike yiwa wannan kukan kamar an yi rasuwa?"
Muneerath ta ce" Pah, wannan abin ai ba karamin aabu bane, Pah ba abin wasa bane, shin idan ya mutu a irin halin nan fa? Ni kam dan Allah kaa taimaka a kaini gida cen Niger ba zan iya ba, abubuwaan garin nan yanzun na kula so suke su kasheni"
Da mamaki yake karra kallonta , tausayinta ne ya ji a kasan zuciyarsa, yarinyar ta yi falng a love , tanaa matukar kishin abin soyayar nata, aman bata sani ba
Sosai ya so ya rarasheta ta koma ta kwonta, sai dai wani tunanin shima ya same shi
Ba tare da jan abin baa ya bada damar a tayar da Jirgin Masarauta da yake a A茅roport din bangaren Sarkin daban wanda yake taronsa da sauransu harda jirginsa a wajen , kan za'a kaita gida
Iyayenta da suka samu dan lokaci nasu na kansu suka fara fuskantar junna Oga ya ji cewar wai wani yar Oga na kukan a maida ita gida
A tunaninsa abin na wasa ne ya ga an kuma tashin Jirgi guda mai shegen kyau da sanyi an zubo au dagaa su sai su bayan sun yi salama sukai kuri a zaune a Hight class sunnaa kallon junna
Aun kusan tafiyar awa daya abin ya tuko shi a hasale ya ce" Ke yar Oga dan ubanki ba kin sa an daukomu an ciro mu bamu shirya ba kuma kukan na uban meye kike ne? Ko salon sojawan cen dake cikin baya su zo su kashemu su ce mu muka saka ki kuka? Ashe sojojin nan dake yawo a anguwarmu masu tsaronki ne? Kai mutane Allah mai iko kai kacari ka haifi sarauniya"
Mamanta taa ce" wai me yasa kai sai zagi dazu fa na ce maka ba mutunci bane zage zagen nan"
Habarsa ya rike ya ce" Yo ni nana abin ne ke karra daure min kai,, kina gannin ikon Allah fa, wai dan ta yi kuka tsakani da Allah sshi jirgin hala da batiri yake anfani ba da esansi ba da za'a ringa tayar da shi saboda kukan yar ogo?"
Muneerath da kanta kamar ya rabe biyu dan ciwo cikin kuka ta ce" Oga ka san me aka yi ne? Oga wai yanzu Hanja ashe mata yake bi? Me zai hanna ni kuka dan Allah?"
Oga ya zarro ido kafin ya tafa hannunsa ya ce" In ban dake ki ba shege nake sai dai su kashe ni, yau na ga iskanci gannin idona, dan ubanki ubanki ne shi da zaki ringa rizgar kuka dan yana bin mata? Yo Allah na tuba yau talaka fitikma ya bi mata bale mai kudi kuma sarki? Ke ina ruwanku tunda dai sonki yake kawai mu daura maku aurenku mu tarkato mu dawo , halinsa kuma ya daina ko kar ya daina idan ya mutu sai su gana da walakiri!"
Ido ta zubaa masa cike da takaici, hakama mamanta, suka rasa abin fada sai kallon kallo, inda Saudat ta mike da sauri ta nufi bayi dan ba zata iya rike wannan dariyar ba kam, kasheta zasu yi ahalin nan walahi.
_____________________________________
Yinwar da ya kwasa manta batunta ya yi sakamakon tunani da ya sako shi a gaba
Taa ina zai fara yada mata manufarsa? Dole ya hanzarta dan ya fara tsoron mai kiran nan nata shi kam, baya so su saka shi a ha'u'la'i, au saka shi yawo ba riga
Sai da ya raba dare kafin ya mike ya dauro alwallah dan gabatar da sallah kafin ya zauna ya buda alkur'ani ya shiga karatu a nutse yana lumshe idannuwansa yana tuno fuskar Mah dinsa
Tare da ita suke yi har sunna tsokanar junna idan mutun ya yi wani kuskure a wata gabar
Sosai ya roki Allah a kan abu hudun nan
Na farko gamawa da duniya lafia
Na biyu shiriya
Na uku lafiar Mah dinsa
Na hudu Allah ya bashi sa'a a kan yarinyar nan, dan ya fara tsoron abinda ta yi dan kawai ya dan rungumeta tana cewa shi sai rungume mata, to idan ta san waye shi yaya kennan? Kai ikon Allah bai taba jin tsoron a san yana aikata zina ba sai yau
Da sauri ya nemi da Allah ya rufa masa asiri kar ta ji........to amaan wai kishinsa take ko menene?
Allah Allah yake safia ta yi, sai ya saka kayan da ya san dolema ya kasheta, sannan ya fada mata cewa" MUNEERATH ina son ki, ki yarda ki zama sarauniyar Ingila taa hanyar zamowa matata"
鈽癸笍鈽癸笍鈽癸笍鈽癸笍 Ham, kak, na fada masa ko na bari ya gani?馃槀
11/14/21, 12:54 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
6锔忊儯3锔忊儯
Washe gari
Tun karfe bakwai suka nufi asibiti daga masalaci tare da Pah da Hanja
Sun jima a zaune a kusa da ita sunna tofa mata adu'ar neman sauki a wajen Allah
A hankali Pah ke shafa gababn goshinta da ya yi fes da shi a sanyaye yana mai yi mata dadadan kalamai da nunin cewa ta jure, ta daure, kar ta saka, kar ta manta sunna nan , sunna da bukatarta
Hanja kuwa hannunta yake rike da shi mai jone da wata na'urar shima
A sanyaye ya ce" Mah, ganninki a wannan yannayi na kashe dukan kuzarin jikina, Mah yau zan fuskantace ta, ban san yaya zata dauka ba, da ace kina nan ifannuwanki biyu da rai da lafia da kin tare min ita koda ta zo baude min, plz ki motsa ko yayane ta yada zan samu kwarin gwuiwar fuskantarta ki motsa ki nunan kin san ina nan, ki motsa Mah..........."
A hankali Pah ya lumshe idannuwansa cike da tausayin yaron nasa,
Wani tausayinsa ya kara shigarsa na Idan ya ji ta tafi yaya zai dauki abin?
Sai dai baya tunanin karamin rigima zata saka Hanja gane matsala ne bibiyar mata da yake, ba wai a adininsa kadai ba, harta matar da yake so idan mai adini ce zata ji kishinsa
A hankali ya juyar da kansa yana aro dukan jarumtar da yake da ita dan yaki da tausayin yaron nasa da fadawa kansa cewa idan har ya jure ya daure ya kasa falasa kansa a gaban yaron nasa dan taimakon yaron nasa ne ba dan wani abin ba,
A nutsue ya kuma hade lebunnansa da jikin kunnen Mah na dama a sanyaye ya lumshe idannuwansa ya shiga karanta mata surorin alkur'ani dan kara sama mata sukunin zuciya, ya yi imanin idan me take ciki adu'a zata sanyaya mata cutarta
A haka har suka gama ziyartar nata suka fito da zumar sai da rana domin likitocin dake tsaye a kanta sun basu lokutan ganawa da ita idan a ra'ayinsu ne, sai dai kuma ifan sunna son ganninsu wannan kuma ba laifi bane sai su zo su ganta su zauna da ita adadin lokacin da suke so, domin a cewarsu idan ana yiwa mutun magana yana ji a mafarkinsa
A falo Pah ya zauna har lokacin bai ga wulgawar Iman ba, bai san tana wajen mahaifiyarta ta labe cike da tsoron bayanuwar abinda ta aikata wanda ita da kanta ta san cewa fitina ta janyowa kanta da kanta
Kamar yadda ya yi niya, bai iya komawa barci ba , wanka ya dauki lokaci mai tsayi yana yi kafin yake fitowa da wayarsa ya zauna dan shi kam bai san wani irin kaya suka dace ya saka a irin wannan lokacin ba
Abinda bai taba yi bane ya yi ta hanyar tabo number masu shirya su na masarautar ya nemi kan su zame a bangarensa da irin shigar da take iya birge mace mai tsatsauran ra'ayi su taya shi shiryawa
Ai kam hakan ce ta faru, a cikin minti ashirin suka karasa da dukan abubuwan bukatunsu suka zame a bangaren nasa inda ya zauna daga shi sai rigar wanka suka shiga shirya shi ta hanyar sake lumde fatarsa da sinadarensu na shirya mutun, shi kuma ya zauna ya basu hadin kai idannuwansa lumshe yana tunanin ta yaya zai iya da ita ne?
Sun dauki a kadan awa daya a kan shirin Hanja, domin shirin da bai taba tsayawa ya yi bane akai masa, barta da gashin kansa sai da suka caje masa shi suka yi tsaga ta yadda wani ya yi baya kadan ya tsaya sama sama kadan
Suit ruwan baki sidik ne suka gabatar masa , da macheste, da safa fara kal kamar yadda rigar ciki take fara kal, da bakin takalmi kafa ciki, harta da gajeran wando sai da suka hadowa shigar nasa suka hada masa
Nan ya shiga ciki ya saka kayan ya fito , suka hau gyara masa mabalan wuyan rigar da komai cike da yabawa da irin kyan da kayan sukai masa, inda shima da kansa yake yabawar a zuciyarsa
Kampanin Julieta ne suka kawo flowers din da shi da kansa ya bada ordensu aka shigo masa da su rututu dan so yake Pah ya taya shi zabe aka zubewa Pah a gabansa wanda jikinsa ya karra yin sanyi sosai yana kallo cike da tunanin yaya zasu kare da yaron nasa
Kyau kam, Hanja ya yi kyau, ruwan kyau da fuzga ya yi shi, kayan sun amshe shi sosai harma ya yi masu maganar cewa idan har ta amince da maganar daje tafe da shi, lalle zasuna shiryashi kulun
A nan ya bar wayarsa ya sauko yana tambayar idan har darius ya shigo domin shima a yau ya bukaci ganninsa dan ya samu kwarin gwuiwar tunkararta da kalaman da suka dace
Pah ya lumshe idannuwansa bayan kamshin turaran yaron nasa ya fara isowa inda yake yana fatan Allah dora shi kansa kar au raba hali gashi yau mai tsawatar masunma bata nan
A gaban Pah ya ja ya tsaya yana murmushi tare da dan yin alamu irin na ya fada masa ya yi kyau kuwa?
Pah ya saki murmushi yana kallonsa ya furta" Masha Allah, my hero, my son u look lk a 馃"
Dan murmushin ya kuma saki yana bada damar Darius ya shigo ya fada masa me yake gani da kalamansa
Pah ya zauna ya karra bada hankalinsa a kansu yana murmushi
Darius cike da farin ciki ya shiga fadin" Duk matan duniya sunna son idan aka tsaya a gabansu a koda kyansu, farinsu, gashinsu, dukiyar da suka malaka da......"
A tausashe Pah yana tatare girarsa na sama ya furta" Plz Darius ka dakatar da abubuwan nan da kake fada domin na tabata idan ya yi kokarin nunawa wadda yake so wannan tabas zata nemi fada da shi ido rufe, bama irin matan da ake sace zuciyarsu ta haka bane, an fada maka kowace mace ce wannan ke rufe mata ido? Wata macen tana sonagana ta gaskiya ne, wata macen du tsakaninta da kai bata so ka yi mata magana irin ra karya"
Hanja ya dubi Pah yana murza agogon hannunsa ya ce" Pah, ban taba jin shakar duban halita na yiwa maganar kamar yadda nake jin na yarinyar nan, me zan ce mata dan ta saurareni?"
Pah ya yi murmushi yana kallonsa ya ce" Ba tsoronta kake yi ba, tsoron amsarta kake ji, bale a irin wannan lokacin ban san yaya zaku kare ba"
Yana kallin Pah ya sauke ajiyar zuciya yana fadin" Nima na kula saboda rashin lafiyar Mah itama sai kuka take bata son damu, ban san yaya zamu karre ba"
Pah ya ari jarumta yana kallonsa da kulawa ya dan watsa hannayensa ya ce" Khadija mama take a wajenta, shi yasa a rikice ta zabi ta koma daga gida ko daga cen adu'arta zata tardo Khadija da bacin ran da ta kwasa, shine abin ya daure min kai irin kukan da take a jiyan nan, anya itama ba sonka take yi ba?"
Darius cike da farin ciki ya ce" Sarkina, ko dai princesses Iman ce mai wannan sa'ar?"
Hanja da yake ta auna maganar Pah a ma'auni da sauri ya ce" Pah, ban gane ba, wace ta tafi ina? Take kuka a kan me?"
Pah ya kuma yardawa kansa jarumta ya ce" Inaga ko a cikin hira ne jiya ta tsinci labarin ka kasance mai yin taraya da wasu yan matan da ba matayen aurenka ba, ni kam ban san meye ya hargitsata har haka ba, baka ga kukan da take tamkar zata mutu, cewa take kirjinta ciwo, ji take kamar lokacinta ne ya yi a taimaka a kaita Niger, gannin abin nata da gaske ne ta kasa nutsuwa da gagawa na umarci kan a kaita gida tare da bada umarnin ATTAHIR AHMAD ya yi jagorar bukatarsu ta cikin jirgin"
11/14/21, 12:54 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
6锔忊儯4锔忊儯
A hankali ya dago dubansa da idannuwansa da suka fara dauko maganar Pah din har zuwa inda ya furta sunnan mutumen da yake jin haushinsa har ransa ya sauke a kan Pah
Muryarsa a nutse ya ce" Pah dakata, ban gane komai ba plz, wacece ta tafi dan an yi me? "
Pah ya hadiye yawu yana karra nuni da sam shi bai san me ya sa ba hasalima ya nuna
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 42