cewar shi taimako ya yi ta hanyar fadin" Da kyar aka iya rike Muneerath tana ihun kuka, inaga ta ji maganar cewa kana mu'amalantar wasu mata tamkar na aurenka bayan ba na aurenka bane, shine take fadin zuciyarta ciwo take yo mata ba zata iya zama ta kwana ba, na kwatanta rarashinta gannin dare ne a jiyan sai abin ya gagara a dole na saka aka kaisu Niger din domin idan ka ga kukan da take sai ka tsorata kar a je ta suma ko ta kamu da wani ciwon"
Tsayuwar da ya yi a gaban Darius sunna tataunawa ya ji gaba faya kafafuwansa zasu maka shi da kasa ta hanyar daukansa suka nemi zubar fa shi ba tare da ya shirya ba
Kansa sai da ya amsa na dan lokaci ya sake kurawa fuskar Pah ido yana kallonsa
Darius hankali tashe da ya riko hannunsa daya da dukan hannayensa da karfinsa dan taimaka masa yana fadin" Kula Sir kar ka fadi mana"
Da karfi ya janye hannunsa da ya fara taurara dan bacin rai yana kallon Pah , muryarsa a kausashe ya ce" Kana nufin Bata cikin gidan nan a yanzu haka?, Ta tafi kasarsu dan ta ji wannan yar maganar? Menene damuwarta da wannan maganar koda ta jitan? Inace wa ubangijina kadai nake da damar bama dalilin aikata hakan ba wani halita ba?"
Pah ya tabe baki yana daga kafadunsa ya zauna tare da sauke ajiyar zuciyar gannin bai zube din ba ya ce" Ka san dama wani lokacin ina fada maka cewa wasu matan da suka san ciwon kansu basa koda magana da masu irin halayan nan, inaga tana cikin matan ne"
Gabansa sai da ya doka da karfi hakan ya sa a birkice ya ce" TaTaTana cikin matan da basa kula namijin da ya kwonta da wata macen da ba ita ba?"
Pah da sauri yana kallonsu gannin su duka abin mamaki yake basu ya ce" Ba haka nake nufi ba, ina nufin musulma ce ita, sannan al'adunsu na tafia da adininsu ne, a kasarsu aikata hakan dati ne, mai aikata hakan kuma dan iska ne, basa ko garajen rike hannun junna tsakanin maza da matayensu, basa rungume junna da garaje, namijin da ya mayar da kansa mai biyan bukatarsa da macen da ba tasa ba su da kansu auke kyamatarsa domin sunai masa kallon wanda baya jin tsoron ubangijinsa"
Da mamaki Darius ya ce" Kai abin mamaki, saurayi dama ana kayade masa irin macen da zai yi mu'amala da ita? Gaskiya adininku akoy takura to ita ta yaya zata ce Prince na ingila zai zauna da mace daya? Lalle tana da rigima"
Pah ya dube shi, a saukake ya ce" Adinina bashi da takura, adinina mai tsafta ne, sannan bai hanna mutun auren mace daidai har hudu ba idan har yana iya kamanta adalci a tsakaninsu, kai naka adinin ai kwaya daya ya halatawa mutun, a haka kuke zaune da sunnan matayenku daya aman yan matayenku dubu wannan shine adalcin?, Darius plz ka barni na gana da yarona"
Dan risinawa ya yi kansa a kasa yana mai neman afuwa idan ya bata masa sannan ya fice da sauri cike da mamakin kai kawon da Hanja yake yi, koda yake ya san ko wacece ta yiwa kanta, ya tabata prince dinsu na iya dauko dubunta Idan yana so, aman har a yiwa prnc maganar mace wace kala ce bai fede ba? Ai sai dai kar a kuma kawai
A nutse Pah ya furta" Hanja ka tsaya waje daya mana"
Da karfi karfi ya ce" Na tsaya waje daya? Na tsaya waje daya? Ina son tsayawar na kasa ne, na kasa tsayawa Pah, Pah me yasa ni? Me na yi nake fuskantar wannan hukuncin? Dan na kwonta da mata? Na san adinina ya hanna, aman nawa al'adun basu wani hanna ba, Pah bani da aure, shikenan sai na tsaya na mutu da ciwo a cikina shine ta yi tafiyarta? Pah ni na san ba zata taba sona ba, idan kana son mutun komai ya aikata ba zaka guje shi ba, Munarah tana soyaya da Attahir ne ba ni ba, an fada mata shi Attahir din nata bai san harkar mata bane? Shine zata shiga jirgi da shi su koma kasarta ta bar Mah kwonce ni kuma ina yawo kamar dan iska?"
Pah ya sadauta muryarsa ya ce" Calm down son, ba fa abin ihu bane, ka gane ita tana aiki da hannawar Adininta, bata wasa da wannan kuma tana tsanar mai wasa da wannan, dukan musulmin kirki ya dace ya kiyate dokokin adininsa, My son Allah ya halice mu ne dan mu bauta masa fa, shin Idan ka mutu a cikin aikata zina me zaka je ka cewa ubangijin da ya maka rai, ya baka daula, ya baka lafia da hankali da dama na rayuwa? Me zaka ce masa idan ka tsaya a gabansa ya nemi dalilinka na aikata hakan bayan kana da damar ajiye macen sunnarka?"
A hankali ya yi baya ya zauna saman kujerar dake kusa da shi ya saka hannayensa cikin gashin kansa ya jimka da karfi.....magangannun da yake a cikon zuciyarsa sune 'Shikenan na rasa ta?, Shikenan na yiwa kaina ilah? Shikenan na kashe kaina da kaina? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, Astagfrullah, Astagfrullah, ya Allah ka sanyaya min wannan zafi da nake ji a zuciyata'
A hankali Pah ya zauna kusa da shi da damin flowers sunna kamshi ya kamo tafukan hannayensa ya bude ya saka masa gindinsu a nutse ya ce" Ka tashi ka je "
Juyowa ya yi da dadadan kanshin flowers din masu sirki da yelow da fari kal a hannunsa yana kallon Pah tamkar bakon Halita a gare shi
Pah ya ce" Idan ka yi wasa, ina tsoron fuskantarka na baka hakurin rashinta, ka tashi ka je za'a kaika har kofar gidansu , sai dai ka sani Muneerath ba irin yan matan dake lashe didigenka bane, ita da Allah ya halicema bai saka mata tsoronka a ranta ba bale ka yi anfani da wannan damar ka sakata dole, sannan ta san kana da kyau ta kuma yarda da hakan aman bai wani damunta, haka kuma irin sarautar garinmu daria take bata , cewa take mu da bama rawani?, HANJA ban san ta yaya zata dubeka ba, abinfa na sani Idan ka samu kanka a gabanta ka bar zuciyarka ta fadi abinda yake cikin zuciyar taka"
Lebensa na kasa dake rawa rawa ya samu da kyar ya iya furta" Pah, Mahna?"
Pah ya yi murmushi yana dan dukan gefen kafadarsa ya ce" Mah dinka, Mah dinka tana tare da Allah, nima zan koma kwana kusa da ita, my son jira ba zai kaika ga ci ba, ka yi jinkiri da yawa, kasancewarka a nan kuma ba shi zai tashi kafadun Mah dinka ba, you see ka rigaya ka balowa kanka ruwa tunda ka fadi a gaban kanina cewar zaka hau mulki, ina so ka hau shi da darajarka, daga nan garadai zasu maka rakiya, haka kuma a cen Sarkin garin ya fada min cewa ya tara dogarai da dawakan garinsu zasu yi maka jagora, sannan president dinsu ya bani maganar cewa sojawa tuni sunna shiri, Son ka dauko abinda ka je nema plz"
Idannuwansa ya sada yana jin zuciyarsa na dokawa ya kasa kwakwaran motsi har sai da Pah ya yi yar dariya ya ce" Ban taba tunanin gannin tsoronka a bayane ba sai yau, ashe kaima akoy abinda kake tsoro? Mace?"
Da sauri ya kalli Pah yana hade fuska ya ce" Tsoro kuma?"
Pah ya gyada kai yana fadin" Eh mana, dubi fa , kalli hannunka a jimke aman sai rawar lebe kake HANJA Sarkin ingila kake fa"
Ajiyar zuciya ya sauke yana cije lebensa ya mike tsaye yana rintse idannuwansa kafin ya juya da sauri sauri ya fice yana amsa adu'ar mahaifinsa a cikin zuciyarsa ya tarda taron sojawan da aka hado sho da su, sai ya ji har wani nauyi na son kama shi ya kara cin fuska ya wuce tsakiyarsu suka nufi wajen jirgin.
_____________________________________
"Wai me take faruwa a garin nan ne Nana nake gannin shiru ya yi yawa kamar an kame mutane an labe?" Oga da yake shigowa yake fada
Kishiyar Maman su Muneerath dake fama da kayan miya ta dago ta masa kallon uku biye da shi da maman Rumaisae dake ta faman hade haden turaran wutarta na siyarwa wanda ta matukar kwarewa a hada shi ta ce" Aman Oga gaskiya ka fara rashin jin tsoron Allah a al'amuranka, wai me yasa komai naka ita ce? Du motsinka ita ce? Ni fa abin nan ya fara isata walahi salon na yi magana a ce bani da hakuri, haka kuka tafi kuka yi kwana biyu a ban ina ba kuka barni da jarababun y'aya uwa haihuwar cikin wuta dafe ni ne kadai basu yi ba a gidan nan kuka dawo kana ta wani budewa kana karawa, kiri kiri sojoji a kofar gidan nan sun hanna yayata shigowa ban san dalili ba oga ko dai a wajen cacar taku ka ciyo mana jaraba bincikarmu ake a kwace gidan da muke karya da shi a kashe mu?"
Oga ya wani irin jan birki yana kallonta har ta gama
Tun dafa kafarta har kanta ya karewa kallo, ita dai irin matan nan ne masu tsayi Masha Allah ga kira mai kyau, sai dai a rayuwarta bata san meye gyara ba, kan nan nata kamar gwuiwa a gwaguye kuma bata daura masa dan kwali, kafar nan faso ta mata kanta sosai sai a hankali, a yannayinta na mace idan ta zo gitaka sai ta bajeka da warin jiki irin na gashin hamata da zaamin gyafto, haka take, haka rayuwarta take
Kawai gani ya yi walahi ba zai iya bata amsa ba gaskiya, shi kam ai yanzun yana da abubuwan tsayawa yi a gidan, bale kamshin nan da nana ke hadawa ai dole ya dan zauna a gefen yar oga da ta haukace ya daki babar rigarsa ta yadda idan ya fita zai karra ba makiya haushi
Baki ya tabe yana fadin" da na zama dan yesu idan da adinin musulunci ya hanna ka yiwa dayar matarka magana dan ba aikinfa bane, kin ga ji ba matsiyaci bane walahi da kudina a aljihuna yo haukanki ki gama"
Juyawa ya yi wajen Muneerath da ta kalli Saudat a sanyaye ta ce" Ki ce dai irin kwatancem zuwarma mutun da kika min shine yake yiwa wasu matan ko? Kai Allah wadaran naka ya lalace!"
Saudat kasa kasa ta ce" Ki yiwa Allah kar ki bari mamanki ta ji wannan maganar walahi ta hada daga ni har ke ta jinyata mu, yau na ga shirme to wai ke ina ruwanki ne?"
Oga ya karra kura mata ido ya ce" Ni kamar da kayan nan Yar Oga ta yi barci kuma sune a jikinta Nana?"
Mama ta tabr baki tana zuba kafin kafin a turarenta ta ce" Kiris nake jira na maka mata muciyar nan Abanta, ka duba ka ga yarinyar nan ta ci abinci ta ki ci tana zaune da wani wando da riga ta saki jiki kamar wata katarpila sai langwabar da kai take irin ka mutun nan ta saka ni a gaba in na yi ciki ta bi ni Idan na dawo ta biyo ni , wata sangartar ai bata da anfani!"
Oga ya wani saki murmushi na jin sabon sunna Aban Muneerath da akai masa ya juya zai nufi wajen Muneerath din matarsa ta fito daga cikin kicin tana ta ruwan hawayen hayakin itace ta rangada buda tana kama baki ta ce" Daga sweet heart an koma azamulumi mai yiwa y'ayan mutane asiri, yau kuma Aban Muneerath aka dira? Ka ga bariki kiri kiri watau mu ba haihuwar y'ayan muka yi ba ko uban Muneerath ne ita kadai?"
Oga ya kuma jan birki ya juyo yana kallon yadda take ta shirnatu abinda dan ta karro wani warin hayaki sai huci take, kai shima akoy jaraba yanzun wannan matarsa ce? Du muninsa ya fita tsari tinda shi wanka yake, a kausashe ya ce" Kin san Allah in ban yi wasan kura da ke a gidan nan ce min shege, ku ji yar bakin ciki ai ci gaba aka samu, a da bata da hankali a gaban kowa ni din nam nine swuit heart dinta, daga baya aka yi walkiya ta ganni a fili na dawo makiyinta, yau kuma ta yafe min ta kireni da sunna mai daraja zaki ji haushi dan ke kina ce min Oga? To ni du ubanda ya kuma ce min Oga ba aban Muneerath ba sai na dauke fuskarsa da mari a gidan nan ka ga iskanci ko?"
Dansa ne ya shigo da sauri yana zarro ido ya ce" Kai Oga anya anguwar nan lafia kuwa ? Dazun mun ga an zagayemu da sojoji bamu damu ba dan dai kowa ya san BAZOUM da bada tsaro a kasarsa, aka dan jima motoci suka karu abin tsoron harda sojoji da gendarmomi, to kuma yanzun laluwa ke kusanto mu Oga aka shigo layinmu abin tsoron na ga ana magana da yan anguwar ana ta mayar da su gida, kar dai a je wani ya aikata laifi a gidan nan ka fa san kaf anguwar nan gidanmu ne yan kwaya"
Dau ya dauke fuskarsa da mari yana kallonsa ya ce" Dan ubanka yanzu na dora dokar kirana da Oga sunnana Aban Muneerath, sannan ban gane ba har yanzu kana siyar da kwayar ne? Na shiga uku kar dai a je kun janyo min jaraba ina zaune ban sani ba?"
Da sauri ya juya ya fita hakan ya sa hankalin matayen da y'ayan gidan gaba daya tashi, mai iya dauko mayafi ko hijab ta warto da gudu, wada bata iyawa kuwa a haka dinta ta nufi kofa da sauri dan gannin abinda yake faruwa ciki kuwa harda Muneerath dake sanye da wandon barci wanda da kadan ya dara gwuiwarta sai rigarsa fara kal mai siraran hannaye
Tsoro ne ya darsu a zuciyoyinsu
Mita daya tak ce a tsakiyar anguwar wace ta fi kusanci da kofar au Muneerath, sai ko tarin iko watau sojoji da gendarmomi da dogarai manya manya amintatun sarki cikin sababin shiga irin tasu masu digiri da digirgir watau ko a cikin dogaran masu tsafta ne, wa'inda suke da damar zartar da hukunci idan ka yi batanci ga sarautar kasarmu, sun sha rawaninsu manya manya sababi dal, cikin shigarsu irin ta dogarai sun rike sandunna irin nasu kowane a shirye yake sun layu gefen hagu da dama gaba dayansu hakan ya sa suka yi caaa kuma suka cika ido sosai
Oga ne ya fara yin saranda a tsayen da yake inda gaba daya iyalansa suke bayansa irin sun labe a bayan wada ya fi kunar nan, watau kauran nasu
Zufar dake goshinsa ya samu da kyar ya share a sanyaye ya ce" Inaga motar cen bom ce a ciki za'a seto mu ne a kashe mu gaba daya, oh haihuwa, haihuwa? Na haifo wanda ya je ya zagi shugaban kasa ina ga an zo a kashe ubansa da danginsa, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une"
Da sauri maman su Muneerath ta riko hannunsa tana kallonsa ta ce" Aban Muneerath dan Allah ka je mana, ka je ka ji menene ka ga fa inaga mune muka yi laifin dan na kula kaf mu ake kallo"
Hannunsa ya janye yana kallonta ya ce" Kaya, kaya Nana, ba zaki gane ba, dole a kalle mi, anguwar nan waye marar ji irinmu? Dan Allah ki yafe min kar na mutu da fushinki kin ji matar aljanata?"
Muneerath dake bin dogarai da kallo cike da mamakin Dogarai ne birjik haka a kofar gidansu ta samu da kyar ta fito daga cikin yan uwanta ta matso gaba sosai tana karra kallonsu, da sojawan da suke tsaitsaye fuska a hade kamar masu jira a yi motsin da bai masu ba su harbe mutun
Daidai lokacin da Hanja dake tura mesage a wayar Pah rai bace kamar haka" Baka ce min da dogarai a tafiata ba, wadinnan sunne fa Muneerath ke haukan so, idan fa ta kore ni saboda su? Kuma baka ce min Attahir ne zai kawo ni gidan su Muneerath ba, me yasa kake min haka be?...." A hankali ya ji dukan da zuciyarsa ta masa ya yi tsanani da yawa hakan ya sa ya dakata yana dafe gaban zuciyarsa kafin ya dago da dubansa a hankali ya sauke a gaban motar
Makoloton makogwaronsa ne ya motsa ya yi sama ya kuma yi kasa lokaci daya sakamakon ganninta da ya yi tsaye tana karewa mutane kallo bata motsa ba daga inda take
A hankali ya juyo bangaren Attahir ya ga sam ba wajenta yake kallo ba, sannan ya sake maidawa wajenta
Idannuwansa ya rintse sakamakon jin takaicin shigarta da kuma mamakin kansa, wace irin shiga ce budurwa bata yi su fita da ita a matsayin budurwarsa bai taba damuwa ba sai yanzu wannan shigar ta Muneerath da take rufafiya a kan shigar yan matan garinsu, sai ya ji wani irin abu na dukan kirjinsa mai zafi da sana sannin kwaso mutanen nann, kai saima ya ji dama shi daya ya zo aka harbe shin da mazan nan su kare mata kallo
A hankali Attahir ya kara sada kansa ya ce" She love u, ta fada tarkon sonka a lokacin da ita kanta bata shirya ba, ya dace ka rike abinka domin ita din mai aiki da fadin rai ce, ta ga damar saboda fadin rai ta yarda da waninka"
Kallonsa ya yi a karro na biyu kafin ya kuma kallonta
Da sauri ya zarro ido ya samu kansa da bale murfin motar da saura yaana mika hannayensa baya ya dauko flowers din da ya zo da su sakamakon gannin ta nufi wajen dogaran nan har kamar zai bar kafar daya a cikin motar dan sauri
Da gagawa Oga ya daga hannayensa sama yana fadin" Ta zo, mutuwar ta zo "
"MUNARAH" Ya fada a hankali yana kallonta
Da sauri ta ja daga niyarta na son karasawa wajen dogaran nan ta masu tambayar shin me suka yi ne?
Juyowa ta yi a hankali ta sauke idannuwanta a kan fuskarsa
Wani irin tsale zuciyarta ta yi ta doka , a hankali ta nemi zubewa kada sai dai hakan bai faru ba saboda tangal tangal ta yi kafin ta yi gagawar kauce hannunsa da ya miko da nufin son tarota kar ta zube
Baban dogarin Fada ne ya daga murya yana fadin" Ku sada dubanku a gaban sarauniyar Ingila, Allah ya ja da zamaninki mai farin jini, tabas ke din halita ce ta Allah wace ya hada da madaukakiyar baiwa, ku sada kawunanku a duba ga cikin duban abin duban sarkin Ingila Umarni ne daga mai girma mai martaba sarkin garinmu"
Ai kam daga sojojin dake kallon mamakin dama wannan yar bak'ar ce, har zuwa dogaran da sauri suka sada dubansu, ita kuma da mamaki take kallon wanda ya yi maganar tana bukatar karin bayani
A sanyaye ya kuma furta "Munarah, plz ki kale ni"
Tsoron kallonsa take ji, wayo tsoro take ji ta juyo gare shi, hakan ya sa ta ki juyowar sai kallon gefe da take cike da tsoron abinfa ke iya faruwa idan ta kale shin
Rigar dake sama ta suit dinsa ya cire a hankali ya kara son matse mata waje
Kanshinsa da ya karra kusantota ya sa da sauri ta dube shi a haukacr ta ce" Walahi kar ka taba ni, wayo na shiga uku zai taba ni Oga, mama ku taimaka min"
Kasancewar da hausa take maganar sai ya dan ja yana kallonta domin ko yaya maganar nan dai ba mai dadi bace, hakan ya da yake kallonta har ta gama ihun
A hankali ya mika mata rigar tasa yana kallonta
Rigar ta harara sannan ta kale shi tana jan hanci ta ce" Meye hakan kuma?"
HANJA ya lumshe idannuwansa a sanyaye ya ce" Plz, ki rufe jikinki, ki rufe bana so sunna kallo"
Jikin nata ta kalla sannan ta kale shi tana karra turo baki ta ki amsa
Saudat da ta fito da gudu da hijab ta karaso a hannunta tana mika mata cike da wani irin farin ciki marar misaltuwa
Muneerath ta amsa ta bude ta saka tana riko hannun saudat kasa kasa ta ce" Tafi da ni, me ya kawo shi garinmu? Saudat tafi da ji ina jin ciwon nawa na neman tashi zuciyata ta fara kusanto bakina kaini fakina dan Allah na sha magani kin ji?"
A hankali ya kara matsawa yana nuno mata Flowers din hannunsa da suka dan fara langwabewa saboda zafin garin yana kallonta a gabanta
Flower din ta kalla ta kale shi, a sanyaye ta ce" Hanja shukar nan fa ta menene? Ni kamar baka da lafia dan Allah meye ne? Wayo Ogana zuciyata zata ballo dan Allah mu je ciki kin ji Saudat?"
Saudat ta girgiza mata kai tana kallonta ta ce" Muneerath ba inda zamu je, ki saurare shi dan Allah"
Muneerath ta warce hannunta cikin fada fada ta ce" Ba zan saurare shin ba, na ki na saurare shin na ce! Na tsane shi, na tsani halayansa, me yasa zan saurari mutumen da bashi da aiki sai aikata zina? Watau du matan da yake zuwarma ya auna masu ciki ko? Ba abinda zan saurara da mai hali irin nasa, gashi daga jiya zuwa yau ji nake kamar kiris ya rage na babale na mutu ba"
Juyawa ta yi da niyar tafia da sauri ya damko hannunta ya juyota da karfi gabansa hakan ya sa Oga zarro ido ya shiga nufo su da gagawa yana fadin" Mun shiga uku za'a maimaita a anguwa a samu na gorantawa y'ata na ci uban mutun, ke , ke Yar oga dan ubanki ba ya biyo ki ba, meye kuma kin yafe a wuce wajen mu je na bashi duniya da kiyama a daura ku tafi ni bana son bidi'ar komai, shima dama mamansa a kwonce kawai a daura mu je ciki mu je ba sai ya rungumeki a nan ba, shin kina ga yan leke ta katanga kuwa ?"
Damatsunnnan hannayenta ya rike gaba daya ya jijigata da dan karfi yana kallonta muryarsa a rikice ya ce" Kirani da dan iska, ki kireni da komai kike so, ban ki ba na aikata, kuma na yi dana sani!, Aman ba zan iya da nauyin DUTSE irin na soyaya ba, lalle soyaya itace DUTSE, bata jin rarashi, bata jin ban baki, bata jin kunya bata da kawaici sai ta halakani zata huta? Munarah I LOVE YOU.......I LOVE YOU MUNARAH"
Lebunnansa take kallo, furucinsa na sauka a cikin kirjinta
A hankali ta shiga neman numfashinta aman yana neman gagararta,
Gaba dayanta ta ringa son kwatar ganninta dan ta karra kallon fuskarsa da jin kanshin turarensa a hancinta
Lokaci daya jikinta ya saki dubanta ya rufe komai nata ya tsaya cak ya kasance ta yo gaba ta fada a jikin kirjin HANJA, watau sun aikata abinda Oga yake gudu rungume a tsakiyar titin garin malan bahaushe
Sumewa ta yi
Muneerath ta sume
Yar oga ta tafi馃槀
Yaya kuka gani??????
I'm sorry wani sa'in gaskiya na kudin kan daukan hankalina馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀
Domin samun naki ki tumtubeni ta number wayana kamar haka +22793811618 a kan farashi mai sauki in sha Allah
11/14/21, 12:54 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
6锔忊儯5锔忊儯
*TALLAH........TALLAH.....TALLAH*
Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba馃
Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali
Ina masu pimples
Tabo(spot)
Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 42