da yake cikin wani hali, bayan wannan a tunanina abinda ya shafi Mah ya shafe ki, ko da kike kiransa yayanki a Niger dan dadin zance ne baki bashi wannan darajar ba?"
Muneerath ta yi tsai tana kallonta
Saudat ta ce" me zai hanna ki je kusa da shi ki bashi baki?"
Muneerath ta zarro ido ta ce" kin fa ji irin fadan da suka yi da mahaifinsa, idan na je ya karyani fa garin shishigi?"
Da sauri Saudat ta ce" Ko ya karya kowa banda ke, ba zai iya koda yi maki mugun magana ba plz my freind ki dube shi, ya gaji da yawa zuciyarsa ta gaji"
Wani iri Muneerath ke ji da kalaman Saudat
Haka kawai take ji a cen kasan zuciyarta dole ne ta je gareshi dole ne ta rarashe shi
Sai take ji wata damuwa irin wace ya dace ta ji idan wani na jinninta ke cikin damuwa a kansa
A hankali ta saka dubanta cikin nasa wanda gaba daya ta ringa jin dukan wani kuzarinta da da karfin jikinta na barinta
Idannuwansa masu launin ja suka ringa yi mata kaikayi a cikin nata duda irin nisa da suke da junna
A hankali ta cire dubanta sakamakon kasa jure kallon da ta yi
Iman ce ta zauna a gefenta tana ta sauke ajiyar zuciya tana amsa waya da harshen larabci wanda da alama danginsu ne na saudiya suka zo aman sun samu cewar ba wanda zai shigo hakan ya sa ta fada masu su je cikin Palace su yi ta adu'a har yanzu shiru ba'a fito da ita ba
A hankali ta mike daga zaunen da take tana jan mayafinta ta nufe shi
Tun kallon da yake tsareta da shi sai yanzu ya iya dan sasauta dubansa a kanta yana mai dan sada idannuwansa daga kanta sakamakon bugawar da zuciyarsa ta karra kaimi tana yi da dukkan karfinta
A hankaki ta zauna daf da shi sosai hakan ya sa ya kuma dagowa a hankali yana kallonta
Idannuwanta ta lumshe kafin ta kuma budewa a hankali ta dago hannunta ta nufi kusan idannuwan nasa a hankali ta ringa karra matsawa har ta isa sosai ta kai yatsar nata tsai har kusa da kwayar idannuwansa kafin yake kiftawa da dan sauri ya kuma budewa da wani saurin yana kallonta har kamar da ruwa ruwa a cikin idannuwan
A hankali ta budi bakinta har iskar bakin nata da bata fitar da wari bale kanshi ta dan daki gefen fuskarsa muryarta cen ciki ta ce" Me yasa kake min kallon nan?"
Idannuwansa ya kuma lumshewa ya karra kureta da duba muryarsa cen ciki ya dora hannunsa saman nata , da sauri ta janye tana dan turo bakinta , a sanyaye ya ce" Dan kin fi mini kowani abin kallo dadin kallo "
Da sauri ta dago tana kallonsa itama, a hankali ta ce" idan Mah na cikin halin rashin lafia sai ka zama wani iri, bana son yannayin nan naka, sai ka ringa fadin maganar da baka sani ba"
Lebensa na kasa ya dan danne da dan karfi yana fitar da wani numfashin ya kalli kofar bloc, ya maida dubansa a kanta a hankali muryarsa na crking ya ce" Bana so ta sha wahala, koma me zai sameta bana so ta wahala"
Muneerath ta dane irin abinda ke taso mata ta rintse idannuwanta, wannan karron ita din ce ta samu kanta da dora hannunta a bayan hannayensa a hankali ta jimke , irin jimkar nan dake fitar da labarin dake zuciya, muryarta a sanyaye ta ce" Mah zata tashi In Sha Allah, u see ta sangartaka da yawa sai ita zata iya lalaba shagwababenta, idan ka ci gaba da wahalar mata da kanka Allah ya tasheta zata bata rai, idan ka ci gaba da wahalar mana da kanka Hanja zamu yi ta shiga dam.............."
Shiru ta yi da maganarta sakamakon wani kure mata baki da ya yi da kallo, sai a lokacin ta ringa tariyo abinda ta fada hakan ya sa da sauri ta dan zarro ido tana cire kanta gefe idannuwanta suka sarku da na Iman
Irin kallon da Iman ke yi mata sai da ta ji gabanta ya fadi
Watau wani irin kallo ne da ta kasa fasara shi
Irin kallon nan na idan idannuwan mutun sun yi ja kuma ya hada da kallon kyama ko jin haushi
A hankali ta kai nata idannuwan itama kan inda Iman ta sauke nata duban
Fitowar likitar da ta yi ja gaban tiyatar, babar likitar da ta sauka daga saudiya dan aikin nan ya saka Muneerath saurin mikewa tana kallon yannayinta
A hankali ya juyo kan likitocin da gaba daya suka bayana a irin wannan lokacin,
Irin yannayin da fuskarsu ke nunawa shi ya saka du wani mai rauni fara zubar da hawaye
Wanda yake da juriya kuwa sai ya zamana ba baka sai ido
A hankali ya ahiga daga kaffafuwansa still hannunsa rike da na Munnerath ya......
Kamar yadda na fada cewar in sha Allah Litinin da alhamis zai ringa zuwa maku sakamakon litafina na kudi da na fara posting dinsa yau Litinin mai sunna WATA KOKOWAR
. Shin kina son sannin me ya kunsa? Sunnansa ya dace da shi?
Ba zaki gane hakannba sai kin karanta yar uwa
Dari biyu ne kacal my hajia ki tuntubeni ta number wayana kamar haka+22793811618
11/14/21, 12:53 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
5锔忊儯8锔忊儯
Kokarinsa karasawa gabansu, inda gaba dayansu suka sada kawunnansu wanda ke nuni da jimamin da suje ciki na halin da Gimbiyar kasarsu ke ciki
Dakatawa ya yi a lokacin da ya kusa isawa ya tsaya da tafiyar da yake yi
Ji yake idan har ya isa kusa da mutanen nan tabas numfashin da yake ja da kyar na iya barin gangar jikinsa
Karan sautin kukan Iman ya saka shi sauke mata dubansa da kyar kafin ya mika hannunsa na hagu dake dan rawa ya riko hannunta na dama ya janyota dan kusa da shi kadan
A hankali Muneerath ta sauke kwayar idannuwanta a kan hannun nasa wanda bata san dalili ba
A hankali ta shiga dan son gannin ta janye nata hannun dake cikin tafin hannunsa na dama , ba tare da ita kanta ta ankara da abinda ya sakata hakan ba
A hankali ya sauke dubansa a kanta, irin nauyin da kansa yake da shi, irin halin da yake ciki du dishi dishi yake ganni
Pah da ya karaso sakamakon kiran da akai masa ya iso kan yaronsa
A hankali ya saka hannunsa a kusa da fuskar Hanja
A hankali ya dora hannun nasa a gefen fuskar ya dan shafa, sai kuma ya saka hannayensa ya janyo Hanja din ta hanyar rike kafadunsa gareshi
Da karfi suka rukunkume junnansu idannuwansu rintse wanda har jikinsu rawa yake
A hankali Muneerath ta juya wannan karron ba zata iya gannin abubuwan nan ba
Abinda bai cika damunta bane ya sakota gaba lokaci daya ta ji wani irin kuka na son kubce mata mai karfi bayan ba haka take ba
Bata san me yasa take irin barancin nan ba
A yau ta yi kokarin fashewa da kuka mai ihu fiye da irgen yan yatsunta
Labewa ta yi ta hade kai da gwuiwa ta fashe da matsanancin kuka
Tana kukan ta ji an dafa kanta hakan ya sa ta dago a firgice ta sauke dubanta a kan Oga
Da sauri ta shiga kokarin son gannin ta share hawayenta inda Ogan ya zauna shima a kasa yana kallonta jikinsa a mace ya ce" Ta mutu hala?"
Da sauri ta girgiza kai ta ce" kai innalilahi Oga har gabana ya fadi, ni dai ban sani ba ko da ran ko babu, na dai baro su a cen ne, walahi tausayinsu ne ke neman kasarani "
Kansa ya langwabar gefe ya girgiza kai ya ce" yau na ga dukiya kuma na yarda dukiya bata iya yiwa mutun maganin damuwa, kai subahannalahi na fada maki ni ina takamar makaranci ne izub dina talatin da bakwai irin na yi ja gaba na so na dauki ragamar saukar da zo rarabawa sai na ga iyayena, ke na raina kaina kuma walahi muna komawa makaranta zan shiga, Allah na tuba sarkin garin nan da ya dauki karatu sai na ce ashe ni wawa ne ban sani ba?, Kin ga ma zo a talauce zan koma a Allah koro, ban san fari ba ban san baki na, ga masu rike da kasar ga mulkin sun san zasu tsaya gaban wanda ya halice su , kudinsu da mulkinsu bai hanna su karatu ba, sai mu dan shirme da rashin rabo da hauka irin na talaka wani dan nema ne zai hanna mu cikar buri na karatun islamiya da sannin addininmu da bautawa wanda ya yi mu, Gaskiya idan wuta ta ci naman talaka ya zama dan iska!, Watau ya zo a rakiya zai koma a ala koro"
Muneerath kan kanta ta kuma sadawa tana jin so take ta kara barewa da wani kukan, gaba daya ba koshi ta yi da kukan ba
Oga ya dora da fadin" Na yi mamakin gannin mai jan kune da janyo ayar Allah, ina gannin harda sarkin makkah yau mun gaisa, abinda dai bai min ba da na ga kafuraima sun hade kai sai muimui suke da baki sunna karyar da suka saba, kai gaskiya bai dace ya bar wannan iskancin ba sai dai in raba kafa ya yi"
Muneerath ta turo baki sosai ta ce" Oga dan Allah ni dai ka bari bana so "
Oga ya tsura mata ido, kamar wanda aka tsikara ya ce" Kai, yauwa ke yar oga dan Ubanki me kike a jikin kato? Muneerath yaushe kika zama yar iska ban sani na? A gabana a gaban uban saurayinki a gaban mamanki , uwarsa na kwonce rai a hannun Allah kika yarda aka yi badalar nan da ke? Me kike so ubansa ya yi tunani da tarbiyar da na baki tsakani da Allah ? Wannan ai iskanci ne karara walahi"
Dama a daf take da katon tankin ruwan hawayenta, sai kawai Oga ya idasa hankadata ramin ihun kukan da ya kireta da iskanci bayan ya san ita ba yar iska bace, kai yaya zata yi da zuciyarta dake zafi da son ta koma ta ga halin da yake ciki? Sai kawai ta bare baki ta mike kafafu ta riko hannun Oga ta fashe masa da kuka tana kallonsa
Ido ya zarro yana waige waige, shi fa yanzun tsoro yake ace ya taba Muneerath walahi, ya kula kamar tana da daurin gindi a garin nan , kar a je kafin a gane shine ubanta sai an harbe shi tukunnan bayan matarsa bata yafe masa ba ya koma ya hadu da walakiri da sandunna, gwara dai ya kyaleta har su shiga kasarsu sai ya mata fadan wannan sabon halin, sam ba halinta bane, bai dace ita da kanta ta fara irin halin nan ba
_____________________________
Muryar Pah da ta shake sosai ya bude a sanyaye ya ce" Son, I'm sorry "
Da sauri Hanja ke girgiza kansa yana karra rike Pah ya ce" Pah i'm sorry, ka yafe min a kan komai, Pah ka yafe min na roke ka, ban san me yake damuna ba, aman dukan abinda ka fada gaskiya ne, ban san ko dan kana saurin dago abinda zuciyata ke ciki bane nake jin haushinka, dan Allah ka yafe min ka ce kar su ce min Uwata ta rasu"
Idannuwansa ya karra lumshewa shima yana tapping din bayansa a hankali kafin ya ce" Ka ga wani abu?, Idan ta tafi ta barmu Son ina so mu yi abinda ma'aiki ya koyar, dan Allah kar ka ruguza ni"
Hanja kam baya tunanin in zai iya, hakan ya sa ya yi shiru har uncle dinsa watau cousint din Pah ya karaso ya shiga basu baki da yaren turanci kafin ya umarce su kan su fuskanci likitocin dake jiransu , a kasan zuciyarsa kuwa Allah Allah yake ya ji me likitocin zasu ce dangane da Mah, ya tabata faduwar matar nan daidai take da faduwar iyalanta, domin sakarar soyayar da suke yiwa junna baya tunanin in daya zai iya babu daya, so yake kawai ya ji an yi mai yiwuwar ya taka rawa!
A nutse likitar ta fara bayani kamar haka" Alhamdulilah, dukan halin da bawa ya samu kansa a ciki ya godewa Allah,
Mun yi aikinmu, mun yi kokarinmu, aikinmu ya tafi daidai sai dai wata matsala da ta bijiro ta harkar jinnin da ya ringa fesowa cikin cikin
A yanzu maganar da nake mak....."
Hanja ne ya dubeta a hankali ya ce" Dan Allah ki sanar mana amsa daya cikin biyu, ta rasu ko tana raye!"
Da sauri ta sada kanta ta ce" Ka yi hakuri, bata rasu ba, aman tana cikin mawuyacin hali tsakanin rayuwa da mutuwa, wanda muke so ku saka hannu a sakata a cikin Coma, domin muna so mu dauke hankalinta baki daya dan mu bata kyakyawar kulawar da ta dace"
Gaban goshinsa ya dafe a rikice ya ce" Coma?"
Pah ya shiga maimaita" Innalilahi wa ina ilaihi raj'une "
Uncle dinsa ne ya share zufa ya ce" Menene pourcentage din tashinta da mutuwarta a halin comar?"
A sanyayenta ta ce" Kamar yadda kowace coma ke ciki haka wannanma, tana iya bude ido ta motsa a gobe, kamar yadda tana iya daukan shekaru inji na bata numfashi da komai, haka kuma tana iya tafia a kowani lokaci, sai dai abin dadin shine farkawar na iya zuwan mata a kowani lokaci"
Hawaye ne mai dumi ya shiga gangarowa daga gurbin idannuwan Pah, a rikice ya siga fadin" Ta shamace ni, ba haka bane abin zai kasance, nine nake da cancer ita dan ciwon ciki ne ke damunta da bashi da wani hatsari, ita ke ce min dan ciwon ciki ne sama sama da bashi da wata damuwa, me yasa zata min haka me yasa?"
Da sauri ya rike shi yana dan girgiza shi muryarsa a sanyaye ya ce" Haba ya shugaba, ka nutsu ka daina irin maganar nan, kaine fa zaka talafa masa ya samu karfin jure halin da yake ciki, kar ka gaza a gabansa , idan ka yi haka ina zai saka ransa ne?"
Pah ya sada kansa hawayensa na zuba sosai
Uncle Joeil ya ce" Ka yi hakuri, ku yi hakuri kar a jona mata inji a hadata da fama, bamu san halin da take ciki ba, may be mutuwarta ta fi wannan wahalar sauki a gareta, ku mu barta ta tafi, ku mu barta ta huta"
Sai a lokacin Hanja ya dube shi,
Duba ya masa mai tsauri kafin ya cire a kansa yana kallon likitar ya ce" Ku jona mata, idan da chance din Mahna ta tashi koda na 0,1% ce ina so, ku jonna mata komai ku shiga bata kulawar da take da bukata, daga yau daga ni sai Pah zamu ringa shiga wajenta,"
Ya juyo ya fuskance shi da kyau da wata kakausar muryar da ta saka shi jin shayin yaron fiye da da ya ce" Ba zan birne uwata ba har sai babu wani sauran numfashi a jikinta!, Daga yau zan saka hannuna a takardar yarjajeniyar da zarar Ubana ya tashi sauka a kujerar sarautar kasata ni dansa rayaye mai shekaru isasu zan maye gurbinsa!"
Daga haka ya juya ya amshi takardar hannun likitar ya saka hannu sannan ya juya da wani irin saurin da ya saka Pah saurin mikewa yana zarro ido hawayensa suka dauke , kukansa ya tsaya tsit ya bi kakarfan yaronsa da kallo gaba daya tsigar jikinsa na tashi, kafin ya lumshe idannuwansa ya juya a hankali ya nemi son gannin iyalinsa inda ya bar Uncle Joeil tsaye cike da mamakin abinda ya faru da tashin hankalin furucin HANJA cewar zai hau mulki bayan shi ya fi kowa sannin irin tsanar da yaron ya yiwa mulki wanda da wannan damar yake karra sakin karinsa dan ya gama sannin cewa mutuwar Pah a kusa take, yana shekawa shi zai hau abinsa
A birkice ya zo ya wuce HANJA baima kula ba ya fita a asibitin
Ba zai yiwu ba, shi da ya gama sannin lagonsu ba zai yarda su masa sakiyar da ba ruwa ba
Zai taba wajen da zasu rasa sukuninsu, karfinsu, dabararsu ta haka zai shige su ya lalata dukan wani motsi nasu
Turus ya yi yana kallon ikon Allah,
Kukanta take kashirban , Oga ya yi ban bakin ya yi rarashin ya zauna ya zuba mata ido ta rike masa hannu taf sai birgima take da kafafu tana fadin" Ko wani ya ce maka ni yar iska ce ai ka karyata shi bale kai da kanka?, Ina zan kai raina na ji sanyi? Walahi Oga tsoro nake ji Allah"
Idannuwansa ya lumshe ya dan jingina yana ta kallonta da irin abin da take yi
Oga ne ya ankara da shi dan haka ya ce" Yauwa dan girman Allah rabani da ita kar ta jaza min balaki a kasar mai jan kunne, yau na ga ikon Allah yar gidan oga dama yar shari ce ke?, A Allah ba taki ba, a Niger za'a birne ni in sha Allahu !"
Da saurri ta kalli wajen da yake tsaye
Sai da gabanta ya fadi haka kawai, hakan ya sa ta hadiye kukan tabarar da take zubawa tana kallonsa kamar yadda yake mata mayatacen kallon nam masa
A hankali ya shiga takowa inda take
Ido ta dan zarro dan ta gama wanye cewa yanzun bashi da cikakiyar lafiyar kwakwaluwa gaskiya, dan haka gwara ta yi ta kanta
A hankali ta ce" Oga ka boye ni dan Allah "
Tsili tsili ya yi da ido, in ba iskanci irin na Muneerath ba yo in ya boyetan bata kula wannan mutumen ya fi shi girma bane? Tsaf zai maida shi gefe ya kamota walahi, shi kam yau ya ga abu a gabansa ana masa abu da y'a
Abin ai na Allah ne budurwa da jika馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀 ga wani page din馃ズ馃ズ馃ズ馃ズ馃ズ馃ズ馃ズ
11/14/21, 12:53 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
5锔忊儯9锔忊儯
Tsayuwa suka yi suka saka Oga a tsakiya wanda yake cicira ido zucoyarsa cike da tunanin irin hukuncin da zai yiwa Muneerath idan suka samu kansu a kasar Niger inda ake jin yarensa idan ya furta cewa shi mahaifinta ne , ta yadda za'a taya shi cin ubanta la'ada waje idan aka ji irin dibar albarkar da ta masa a kasar mai jan kunne, wai shi Muneerath ta saka tsakiya da saurayinta tana kukan tabara salon yayi tunanin shi ya daketa ya maka masa hannun nan nasa mai tuwo ya summar da shi
A sanyaye yana kallon irin kamanin da Muneerath ta dauko na mahaifinta wa'inda in ba tsayawa ka yi ka masu kallon tsaf ba wani iya ganewa zaka yi ba ya iya budar bakinsa ya ce" Kukan me kike yi Muneerath ? Kin san da Mah ba zata so ki yi kuka dan bata da lafia ba "
Muneerath ta dan leko tana kallonsa
A hankali ta ji tsoron nasa da take ji na kawarwa daga zuciyarta hakan ya sa ta iya fitowa a bayan Oga wanda ya yi fittt ya tafi yana mai ayana 'Yan iska kawai, gaskiya gwara na ga ubansa idana aure za'a masu a masu ba sai mun tsinci yan amaye amaye da tashin zuciya da barcin rana ba mu ahiga uku, su su sha murnar hakan ni kuma bakin ciki ya kashe ni a banza ba'
Muneerath dake kallonsa a hankali ta ce" Ina Mah?"
Yan kafadunsa ya iya dagawa a hankali ya ce" Tana cen kwonce, za'a sakata a koma "
Ido ta zarro hakan ya sa ya kurawa idannuwan nata ido a hankali ya ce" Fada min, kina tunanin zata tashi kuwa?"
Bata san lokacin da ta ce" Yo ni na sani ne ka ga kar ka fara kukan ka ji?, Gwara ka je gida ka cenza kayanka ka dan nutsu ka ci abinci ko yayane, a yanzun adu'a zamu yi ta yiwa Mah in sha Allah zata tashi"
Ajiyar zuciya ya sauke zai yi magana su Iman da Saudat da masu masu rakiya suka karaso wajen domin Pah ya salami kowa ya ce kowa ya tafi gida ya huta ya mata adu'ar tashi idan da rabon hakan
Iman na zuwa, sakamakon gannin a dazuma ya rike mata hannu sai ta samu kanta da riko hannunsa tana kallonsa tana hawaye a bayane kafin ta fashe masa da dan kuka marar sauti sosai tana kallonsa
A hankali ya janyota jikinsa ya rungumeta dan ya rarasheta, Iman fa itace kanwarsa da yake manta cewa ba wai jinni daya suka fito ita da shi ba
Iman na cikin halin rudu na rashin Lafiyar Mah kamar yadda yake ciki shima
Iman y'a ce a wajen yayun Mah wada suka rasu sakamakon accident din mota
Tun tana karama take hannunta har zuwa yau
Bata san wata uwa sama da Mah ba, idan a yau ta rikice da koke koke kan abubuwan da suke faruwa da ita tabas ta cencenci a dubeta a rarasheta, abin kaunarta na nuna kulawa ga watanta a bayane, sai ko mamanta wace take yiwa kauna irin ta mahaifiya na kwonce a halin rayuwa ko mutuwa? Dole ta so a rungumeta, bale su a wajensu rungumar fa ba laifi bane , sam ba wani abu bane, su da ko a gaisuwa suke rungume junnansu bale a haka?
A hankali Muneerath ta ringa jin wani irin zafi na ziyartar dukan jikinta har zuwa kofofin hancinta
Idannuwanta ta cire a kansu ta sauke kan Saudat wace ta kula kamar murmushi Saudat din ke yi hankali kwonce harda rungume hannaye
A hankali ta ce" Kai Saudat zafi nake ji hancina kamar iska ta masa kadan mu tafi inda a maida mu"
Da yaren hausa ta yi maganar tana yawo da idannuwanta da take aon kauda su daga duban bangaren yan iskan nan!, Sai dai kamar gam aka ringa dawo da dubanta har a kuma duban hannunsa dake saman bayan Iman yana dan dadabawa a hankali
A hankali ta kai dubanta saman fuskarsa, idannuwansu suka sarke da junna
A hankali yannayin fuskarta na innocent girl ya ringa nuna halin da take ciki na bacin ran rike wata a jikinsa , sai dai sam bakinta bai nuna ba hakama aikinta bai nuna ba
A hankali ta cire dubanta ta juya wannan karron ba tare da ta jira Saudat din bama dan ta kula Saudat din na son zaman ta kalli iskanci karara
Sai ta kama hanya a kafarta tana tafia, du kuwa da irin nisan wajen gaba daya sai ta manta take tafiyarta a kafarta inda gaba daya ta samu kanta da tunanin rayuwa irin ta HANJA
Tsaki ta ja a bayane tana fadin" Kai kowama sai ka rungume? Kowama sai ka rikewa hannu, baka da zabi a matan da kake iya rikewa hannu? Baka da zabi a irin macen da zaka nunawa kukanka? Kowace bola da sharama sai ka rungume ka nuna mata kanna cikin wani haki na bacin rai? Wannan ai sallon yada iskanci ne a doron kasa, anya kuwa yaron nan ba ya gama watsa kansa ba kuwa ?"..
Bata shirya jin muryar ba ta ji daga bayanta Saudat da ta gama shan dariyar yannayin Muneerath din , wace tana bada baya HANJA ya saki Iman cikin gagawar maganar da bai san yana da ita ba ya ce da ita" Autan Mah, ki daina kukan nan haka kin ji? Saukin kennan muka samu daga Allah, domin da yanzu gawarta aka turo mana , kuma haka zamu dauka mu je mu birne, mu tafi mu yi mata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 42