Share this page
ne a yane a zagayen lakausan dogon gashin kanta mai cika daga gabam goshi sosai, sai yar siririyar agogo fara A sanyaye ya ce" Ka zo ka dauki Tgr " Daga haka ya katse kiran yana kallon lokacin da ta kalli Saudat a dan zabure wanda ga dukan alamu a yanzu ta fara gane tare yake da tgr din A hankali cikin dabara ta ringa kallon kasa kasa har idannuwanta suka sauka a kan Tgr dake zagaye shi tana kada bindi Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke a bayane kuma kasa kasa sosai ta ce" Wayo Allahna, ta yau dinma ta kirkin ce, kuma gashi ba Mah ba Pah a kusa, ga yar mutane tana tare da ni , gashi inaga haushina yake ji dan sai hararena yake..... innalilahi Saudat Zaki.........." Ta idasa maganarta da dan daga murya wajen ambatar sunnan Zakin da hausa tana kwalalo ido ta nunawa saudat da idannuwanta.......... Saudat gaba daya ji ta yi tamkar zata suma, haka jikinta ke rawa ta rasa yaya zata yi daga tsayen da take A hankali ya dagakafarsa ya kara taku daya dan karra kusanta kansa da Muneerath, sai dai abin daria yana yin taku dayagaba tana yin daya baya idannuwan nan kuwa tamkar zata dauke shi da su Sai da ya gama murmushinsa na yannayinsa a cikin zuciyarsa kafin da hannayensa ya nuna masu wajen zama da yatsarsa daya ya kuma nuna cewar su zauna , ya kuma dan nuna alamun idan ba haka ba........ya karasa da dantse lebensa, daidai lokacin kuma mai kula da bangaren Mah ta same shi ta waya da tambayar idan har yanzu su Mah zasu sauko su gaisa da bakin?, Ya shaida mata lokaci kafin ya kara sauke masu kakausan kallo a kansu wanda ya saka a birkice du suka samu matsugunni suka tsuguna duwawunsu A hankali Muneerath ta saka hannunta tana ture dan kwalinta da hannayenta kuwa tana firfita tana satar kallon yadda Saudat ke share hawaye kanta a sade baiwar Allah Karasawa ya yi ya ja kujera ya hau ya zauna kafin ya shiga shafa bayan Tgr dake daf da kafarsa yana hankalce da yadda Muneerath ta nade kafafuwanta kawarta kuwa sai hawaye take Dan gyaran murya ya yi ya nuna mata abincin da idannuwansa sannan ya nuna plat olat din dake ajiye A sanyaye ta ce" Toh " Ta mike tana sarar kallon Tgr ta bubude abincin Bata tsaya tambayarsa ra'ayinsa ba ta zuzuba masa abincin ta ajiye da cokali sannan ta tura masa mg din jus din ta koma ta zauna tana sauke ajiyar zuciya Da gaya, da neman fitina, da ba bawa wahala ya ringa takalar abincin kadan kadan su kuwa sunna zaune zuciyoyinsu na dukan tara tara inda Muneerath ke bin hannunsa idan ya dauko abincin a kasan zuciyarta tana ta ayanna dama ba Tgr a kusa Allah yau da sai ta kwaba masa abincin nan idan yana so ya yankata!, To dan dai Tgr dai daba ce, daba kuma mai cinye mutun murus wace ita nama shine abincinta danye ba dafafe ba, hakan ya sa ta nutsu ta yi shiru tana sauraro har daidai lokacin da wayarta ta dauki ringin cikin wakar hausa mai taken tatausan lafazi A hankali ta kai hannunta ta dauki wayar tana duba sunnan dake sama baro baro an rubuta Freind Dan murmushi ta saki hade da sauke ajiyar zuciya a hankali ta daga idannuwanta a kasa kafin ta dan dago da dubanta ta sauke a gefen da yake A karro na hudu idannuwansu suka kuma sarkewa da junna, da sauri ta cire dubanta a cikin nasa ta sada kanta tana shafa gefen wuyanta a hankali ta ce" Sir zan tabo ka idan an jima zan yiwa Mah maganar zuwanka abinda tace sai na fada maka" A hankali ta kashe kiran ta ki kallon wajensa, gaba daya ji take bata iya kallonsa bata san me yake ji a tsatsare mutun da ido ba A hankali ta ce" HANJA, yaushe zaka mayar da ni gida? " HANJA da gaba daya ya ji abincin ya tsaye masa a kirjinsa ya cinkushe masa, gaba daya ya ji zaman wajen ya fara isarsa maganarta sai ta diro masa a wani baibai Me take nufi da yaushe zai maida ita Niger?, Me take nufi da shi?, Shi wai sa'anta ne ko meye? Mai kula da Tgr dake tsaye yana jira shima a kadan ya yi minti arba'in a tsayen ya kai dubansa kansa, yana shirin masa nuni da ya tafi da shi su Mah suka sauko Turus Mah ta yi gannin a yan taron harda su Tgr ga kuma y'ayanta da alamu an tsatsare su ne , sai itama ta ki idasawa har sai da ta ga an ja Tgr an tafi da ita kafin ta karaso tana murmushi Jikinta ya yi sauki sosai, saman kujera ta zauna tana zama ta dan daga murya ta ce" Abinci ake ci ne? Wanda ya gama ya zo na ganshi, Son harda kai a cin abincin?" Muneerath yanzun ta samu kanta, an tafi da Tgr haka kuma ga Mah a gefe dan haka sai ta dauko dan mayafinta ta kade abinta ta yafa sannan ta mike tsaye da kyau tana gyara rigarta ta kalli Saudat, yar daria ta yi da yannayin na Saudat ta ce" Sai ki taso mu karasa cen yau mun tsira Allah dai ya sa mu rabu da kasar nan lafia, taso kin ji" Tana fada tana kamo hannun Saudat ta mikar da ita hankali kwonce ta jata suka yi wajen Mah Wata shakar ya yi, harma ya ki ya motsa daga yannayin da yake Daga inda yake yana ji dan rashin kunya yarinyar nan na fadawa Mah zata kawo kato gidansu, ta karashe da tambayar Mah yaushe za'a maida ita Niger? Tana missing din iyayenta fiye da tunanin dan adam, sai ya ji kawai shi take nema da fitina dan haka ya mike tsam tare da daukan tissu ko ruwa bai tsaya ya sha ba ya juyo ya sauko da sauri sauri ya karaso Yana tsayawa su Pah na shigowa da baban Minister da matarsa da y'arsu yar kwalisa sai rangaji take abinta Bai tsaya da niyarsa ba yana zuwa rai bace ya ce" Ke!, An ki ba'a mayar da ke Niger din!, Kuma dakike maganar zaki gayato wani sakaran saurayinki marar aikin yi sai ki gayato shin mu gani tunda ke bakya jin magana sai neman rainawa mutane wayo da batawa mutane rai da kika fi kwarewa a ciki, ba zaki je din ba kuma ba zai zo nan ba!" Ikon Allah ne kawai gaba daya al'umar dake wajen suka tsaya kallo, ciki kuwa harda Iman da yar gidan Minister wada tunda take bata taba sannin yana doguwar magana haka ba, itama sai kai dubanta kan wace yake yiwa ihun, Iman kuwa da gaba daya kwanakin take dan fuskantar ya cika zakewa a lamarin Muneerath jin ba zai maida ita ba ba kuma zara gayato saurayinta ba sai ta yi mutuwar tsaye tana dane kukan dake son fasowa ya fito daga bakinta Kallon kallo suke kafin Munnerath tsam ta mike ta koma datan gefen Mah ta shirya tsaf koda ta kwana ta ce" To kuma ni yanzun dan Allah me na maka, kai kawai ka tsane ni?, To a kan me zaka ce ba zai zo ba bayan saurayina ne kuma Mah ta san da zamansa?, Bayan wannan Niger din nan fa ba anguwa ba nake nufi sunnan garinmu ne garin iyayrna inda ka dauko ni, ko zan iya sannin a kan me ba za'a maida ni ba? Ni wollah Mah kin gani haka fa ya hayo cem wajen da zakinsa ya hanna mana cin abinci karshe harda hawaye kawata take na ta gama sarewa cewar mun mutumun lalace, kuma dai ai ni na daina yi masa rashin kunya shine zai ce yanzuma ba zan je Niger ba?, To ni dai sai na je ko a tayar jirgi ne koa kafa!" Hargowa da rigimar da ta shiryawa din ne kam ya gama hadawa kala kala, fitina tashin hankali fada shine abinda iyayensa suka gama karanta a tatare da shi wanda yake kiris ya fashe da su Lokaci daya ya daga kafarsa zai zagaya ta dayan Bangaren, hakan ya sa Saudat ta duke jikina bari cike da tsoron yannayinsa ta rufe ido ta dora hannu a kai tana dana sannin zuwanta gidan ta gama sannin cewa tasu ta kare hakama sun gama rasa aikinsu kennan ko wa ya tsaya masu,sam bata san Muneerath rikakiyar mahaukaciya bace sai yanzun da ta baiwa sir Hanja amsa a haka, in ba kasada irin tata ba idan yace ba zata je ba ta yi hakuri a lalaba shi mana sai ya mayar da ita a hankali idan ya yi niya duda bata san dalilinsa na cewar ba zata koma garin iyayenta ba, haka kuma ita da kanta ta ga gangancinta na cewa zata gayato sir Attahir gidan nan , ita a tunaninta yadda ya zamo waje mai saukin shiga a wajenta hakama kowa ? Gaba daya ta tsorata da jan da fuskarsa ta yi shi yasa ta duke dan ta san har ita yau sai ta dauki duka! Da gudu Muneerath kuwa ta dafe rigarta ta juya wajen matakalar benen ta fara haurawa da dan ihun neman ceto tana kiran sunnan Mah da Pah Gogon kuwa ko idannuwansa basa gane masa da bakin fuska a wajen, ko lamarinsa ya yi daukakan da baya iya hakuro har su tafi?, Ya aniya bin bayan nata da nasa kalar salon bi da gudun dan so yake ya damketa ya yi mata shakar mutuwa sai ta fara bambance raini tsakaninsa da banza Attahir din da duk a cikin abin ya fi bashi haushi ba tare da ya san dalili ba Pah dake yar daria ne ya yi maganar da ta saka jinnin kowa kusan hawa a wajen nan, kama daga iyayen budurwarsa masu neman iri, da shi gogan dake neman kasara yar mutane, da kuma Iman mai fama da nata miki cikin shiru, da Saudat da bata san abinda ake ciki ba, da Mah wace ke kokarin taro shi kar ya aikata haka dan bata san a yaya zasu kare ba ta tabata ba iya tsere masa zata yi ba duda ta fala a guje abinta a lokacin da ya ce" Ts 's my dghter in low " Shi dai turancin nan ba yarena bane, idan ban yi daidai ba ku daidaita馃槀 11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 5锔忊儯2锔忊儯 "WHAT?" shine kalmar da ta fito daga bakin budurwar da dukan karfinta haka kuma idannuwanta a waje Iman dake tsaye bata san lokacin da kafafuwanta suka kasa daukanta ba HANJA da ya ja birki daga niyarsa na son bin bayan Muneerath ya juyo a hankali ya tsaya da wani expression a kan fuskarsa na son sake jin karrin bayani daga mahaifinsa da ya fuske ya maimaitawa Yar gidan minister abinda ya fada Juwa ce ta kwasheta daga tsayen da take, juwa ba ta karya ko ta gayya ba Juwa ce ta makata da kasa wanda hakan ya saka du wani dake wajen nufarta banda Iman da ta hade kai da gwuiwa da kuma Saudat da ta mike tsaye tana wuki wuki da idannuwanta , sai kuma ahi gogan da gaba daya ya tsayar da du wani tunani nasa a kan mahaifinsa Saman doguwar kujera Mahaifinta ua kwontar da ita, Pah ya nufi wajen Wayar tafi da gidanka ya dauka ya shiga buga kira wa likitocin palace din Mahaifiyarta na shafa gefen fuskarta tana ambatar sunnanta , MAh na gefenta tana afkin yi mara sannu Karasowa ya yi tsakiyar falon ya zauna saman kujera ya dan ringesa hannunsa na dama ya dora kafa daya kan daya yana dan kadawa yana kallon ikon Allah domin ba suma ta yi ba kuka ne take sai lalabata suke yi ana bata baki da hakuri a haka har likita ya zo ya dubata ya tafi Pah na zaune yana kallon su Mahaifinta ne ya sauke ajiyar zuciya cike da ladabi ya dan saki dan murmushi ya ce" Honorabl, ka yafe mana wannan hargitsin, maganar nan ce ta rikitata duba da soyayar da take yiwa sir HANJA" Cike da isa irin na saraki Pah ya kai dubansa kan Hanja dake zaune yana kallon kowa cike da miskilanci kafin ya fyskanci minister da datako iron nasa ya ce" Soyaya suke da yarinyar wajenka? Tun yaushe fa?" Minister ya kalli yar tasa dake ta hawaye a yanzu ta daina kukan tun karfi ya ce" Hassy ki sanar masa" Sai da ta ja numfashi sannan ta ce" ya kai shekara biyu " Mah ta kalli Hanja da sauri tana bukatar karin bayani aman abin haushin ya ki ya furta komai sai tsatsare Hassy din ya yi da ido To shi gaba dayama gannin ranar nan yake kamar a wani mafarki, Pah ya masa aikin nan ga kuma wata na yi masa wani , to wai a me aka dauke shi dan Allah, idan soyayarma yake yi ya rasa da wa zai yi sai da yarinyar cen kuma ya kasance shi bai sani ba har sai an fada masa? Pah ya dan dage kafadunsa yana kallon Minister ya ce" Zan waiwayeka a kan maganar"......yana fada ya cire kansa yana basarwa ba tare da ya kalli gefen da Hanja yake zaune ba Su da suka zo gannin marar lafia sai ya kasance ziyarar tasu ta samu takaituwa harma suka bar gidan da wuri ba tare da sun samu kan yarsu ba hakama wanda yar tasu take haukan a kansa Bayan tafiyarsu da kamar minti biyar sunna zaune a yadda suke Mah ta umarci Iman da ta koma dakinta cike da tausayinta a kasan zuciyarta, sai dai du yadda ta kai da son iman da tausayinta ba zata hadata soyaya da Hanja ba idan har ba shine ya bukaci hakan ba domin ta san wahala ce zata siyan mata mai dogon zango, dan haka gwara ta kyaleta ta yi ta gama Sai da ta shige Tare da Saudat Hanja ya fuskanci iyayensa tare da neman karrin bayani a kan furucin Pah Pah ya dube shi da kulawa ya ce" Me yasa ba zaka ba kanka lafia ka samawa kanka nutsuwa ka hannama kanka faduwar gaba da shiga tashin hankali sakamakon abinda kake so na ambatar maka wani a gabanka?, Dama an yi namijin da zai ringa shiga bakin macen da jinina ke so bayan kana raye ba mutuwa ka yi ba? Girman kai da jiji da kai fa ba wannan bangaren ake yiwa ba, mai ilimi yana nan soyayar mace ta lalami ya saye zuciyarta a lokacin da ita kanta bata shiryawa hakan ba, ko har yanzu kana kan bakanka na kai baka ce kana sonta ba?" Hanja ya dafe gaban goshinsa kafin ya ciro ya ce" Me ya kawo maganar so a tsakanina da ita ?, Rudani ke iya rudata a kan lamarinta ko meye?, Ba maganar so bace Pah" Pah ya gyada kansa kafin ya mike ya nufi wajen lft a kasan zuciyarsa yana ayana idan ka san wara baka san wata ba! Yana bacewa ganninsa sukai ido hudu da Mah, mikewa ya yi da takun gagawa ya bara mata wajen danma karma ta dora masa da wani ciwon kan ya bar gidan gaba daya ya nufi gidansa domin yana son kebe kansa dan ya yi tunani a kan rayuwarsa da sokoncin da yake bazawa a kowani lokaci a gaban wannan yar yarinyar Sosai ya dauki lokaci a gidansa yana ta auna magangannun iyayensa, inda ta amsa kiran yarinyar gidn minister ya bata lokacinsa yana sauraronta yana auna yannayinsa da dukan wata tafia dake iya sada shi da maganar abinda ke cikin zuciyarsa Me yasa take masa magana kamar wata marokiya? Kamar wace ke maula a wajensa? Me yasa idan ya mara gardama a abu sai ta shiga wani lalaminsa ko ita ta yi biyaya kai tsaye? Tsaki ya ja bayan ya kashe wayar ya daura alwallah ya shiga gabatar da nafila domin ya kula idan ba sallar ya yi ba ba zai samu sukuni ba Cika daren da ya yi shi ya saka shi makara, domin ba shi ya kwonta a jiya ba sai da ya gabatar da sallar asuba ya yi barci a saman salayarsa hakan ya sa sai sha daya na safe ya farka daga barci kafin yake shiryawa a gurguje ya nufo gidansu dan ya ga a wani hali yake ciki Baban abinda ya tarar ya saka shi jin juwa na neman maka shi da kasa wace bai san dalilinta ba Labarin da ya samu a wajen Mah dinsa da ya tarar vry sad ya saka shi juyawa ya nufi bangarensa ba tare da ya furta komai ba A lokacin da ya zame a bangaren nasa sai ya samu kansa da maimaita sakon mahaifinsa wajen karfe daya na dare ta voice note inda yake shaida masa ya neme shi bai same shi ba gashinnan a a茅roport ya zo da kansa ya saka an tashi jirgi za'a kai Muneerath Africa dan ta je ta ga iyayenta Ya kuma shaida masa tafiar harda Mah a yan rakiyar ga Mah dinsa da Muneerath sunna hawaye wai munneee ta ce ta fasa tafiyar wollah sai take ji ba zata iya barin Mah ba Idannuwansa ya rintse daga zaunen da yake a hankali ya danna Vidio din da ya turo masa wanda yana dannawar ya yi daoloding da gagawa ko dan karfin ntwrk ne A hankali ya shiga vidio din ya tsurawa abinda ke wakana a ciki ido yana kallo A hankali ya samu kansa da lumshe idannuwansa kafin ya bude a sanyaye ya dora yan yatsunsa wajen kuncinta da hawaye ke zubar mata ta dage tana rusa kukan rabuwa da MAH Dan murmushi ne ya kwace masa kafin yake dan kausasa dubansa a sanyaye ya ce" Karya ne, karya kike ko?, Kukan nan na farin cikin zaki yi tafiyarki ne ko? " Sai kuma ya rintse ido a kasan zuciyarsa ya shiga ba kansa amsa' Hanja ba shikenan ba kaima ka huta?, Ka huta da ihu da take saka ka, ka huta da bata maka rai da take yi, ka huta da tunanin kar aje muguwa ce ta cuci iyayenka da suka yarda da ita, ka huta da faduwar gaba, ka huta da tunanin akoy wata halita dake iya kallonka ido cikin ido ta ce da kai sai an yi, ka huta da tunanin me take yi da wa take yi , ta je din Hanja, ta je din, idanma Pah ya yi haka ne dan ya daga maka hankali ba komai bai yi wng ba' A kadan ya dauki lokaci mai yawan gaske yana kuma kallon vidion, karahe dai sai ya ajiye a kan vidion ya mike ya shiga kokarin shiryawa dan ya tafi wajen aiki, ya tabata da irin abubuwan nan ke shigar masa cikin tunani sunna hanna masa sukuni _______________________________ Tamkar a mafarki take ganni Sosai take jin ciwon rabuwa da iyayen goyonta duda an bata takarda da numbobi prvt nasu wa'inda kai tsaye ko wani ta aiko yana iya zuwa ya shige cikin palace da sunnanta bale ita da kanta, sannan Pah ne da kansa ya ja mata gargadin idan kafarta ta taka kasar ingila bata da masauki sai gidansa Sai dai duda haka wani irin baban gurbi take ji ta baro a ingila Wannan gurbi kuma ba komai bane face Mah, Mah itace macen da ta fara ganar da ita abubuwa masu mahinmanci na rayuwa Mah itace ta koya mata cake Mah itace ta jata a jiki ta koya mata soyaya irin ta d'a da uwa Bata san irin adadin soyayar da take yiwa baiwar Allahn nan ba, bata san irin adu'o'in da zara bi baiwar Allahn nan da su ba duniya da kiyama, abinda ta fi sani shine ta hadu da mutane masu halaci, kuma zata dawama mai halaci a tare da su Wayar ma'aikata aka bata da shaidar cewa a koda yaushe tana iya samun kira dan tafia, Mota ce aka basu kowace da tata sabuwa dal Gaba daya bata lura da irin yannayin da Saudat ke ciki ba, zumudi da tsoro da son ganninta gaban iyayenta dan ta jero masu tambayoyin dake cikin zuciyarta wa'inda ta yi ta tarawa tsakanin zaman nan nata na dogon zango a nesa da su ya hanna mata gannin irin halin firgici da yawan kallonta da Saudat ke yi har zuwa yanzu da ta bude gaban motarta ta shiga tana kallon motar tana murmushi da jakarta mai dauke da AtM dinta wada ita kanta bata san adadin kudin dake cikin banki na nan niger da sunnanta da kuma wanda aka bude mata na ingila da sunnanta ba A zabure ta kalli bangaren da Saudat ta bude ta shiga ta rufe kofar da karfi A dan zabure ta ce" Aushhh saudat ki rufe a hankali mana ji kin rufo da karfi har kaina ya amsa walahi!" Saudat dake binta da kallon mamaki ta ce" Muneerath me yasa kike kamar baki baki sani ba? Ni zaki boyewa irin wannan abin?" Kasakai ta yi da mamakin yannayin Saudat din da kuma irin abinda take fada Da sauri ta karra waigawa bayanta ta ga motoci uku biyu ta sojoji daya ta police kamar wa'inda suke jira ta basu waje su wuce Da sauri ta kunna motar tana fadin" Tsaya na basu waje su wuce ki fadan me na boye maki ni kuma?" Saudat ta karra cika da mamakinta ta ce" Su wuce ina bayan su din daga bakin yanzu har ki bar niger zasu kasance da ke masu baki tsaro ne a matsayinki na sarakuwa sarkin Ingila?" Kamar jinta ne ya dan dauke na dan lokaci kafin ta maimaitawa kanta maganar, hakan ya bata dariya ta kalli Saudat ta ce" Hala a jirgin aba buga maki kai da wani waje kika haukace?" Itama da takaicin yadda Muneerath ke son raina mata hankali ta ce" 11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 5锔忊儯3锔忊儯 Ta ce" Me yasa kike son saka wasa a dukan lamarinki?, Me sarkin garin ingila yake nufi da maganar cewa ke din SARAKUWARSA ce? Meye fasarar karamawa da muka samu irin wannan?, Abinda muka malaka a yanzu ni kaina da sanadiyarki na malaka ko sir da ya yi shekaru a matsayin ma'aikaci baba mai horar da hostess bai malakesu ba duka hakan a kan wani dalili?, Da aka yi maki accct na kasar ingila da takarda ta shaidar da aka baki damar zama na dindindin a kasar ingila wada kike iya shiga ba tare da visa ba kai tsaye ki shiga wajen da ya maki ki kama gidan da ya maki da dukan isa irin ta haifafen kasar me suke nufi? Meye fasarar fadan da kuke yi ke da Princ HANJA?, Me yake hasala shi a kan maganar da ta shafe ki?, Me yasa a ranar nan ya yi maki tambayar me wani namiji ya fada maki , ke kuma kika dubi tsabar idannuwansa kika bashi amsa kai tsaye ba tare da kin ji dar din abinda ka iya zuwa ya zo?, Shin inai maki kallon marar wayo kina mani na shahsasha ne?, Soyaya kuke da magajin kujerar garin ingila ko me?" A firgice Muneerath ta ce" Dan Allah sasauta da magangannun nan naki Saudat kina neman tarwatsa min kwakwaluwa, me hakan yake Nufi ? Me magangannunki suke nufi dan girman Allah?, Wacece ni? Me ya hada ni da irin wannan kokowar? Koda na kasance mai aiwatar da lamurana kai sake na san wajen wasana, kin ga tunda Allah ya hadani da shi na fahimci ya tsane ni, Saudat mutumen nan da ba dan mamansa na gefe ba da ya karya ni, kina gani fa ba laifin tsaye

Chapter 30 of 42