adu'a ki daina kukan haka ya isa kin ji autan Pah ?"
Yana fada ne ya shafa gefen fuskarta da sauri ya kama hanyar fita, sai dai kafin ya idasa fitan muryar Pah ta dawo da shi
A kan dole ya dawo yana waiwayen kofar kamar ya ce yana zuwa zai bita ne sai dai ba halin hakan domin ya tabata tataunawa ne zasu yi da mahaifin nasa, kuma ya tabata hakan baya wuce a kan maganar da ya yi cewar zai dauki sarauta
Dan dole ya umarce au da su tafi, Har saudat zata wuce ya samu kansa da cewa" Dan Allah Munee ta ci abinci kar ta manta da cikinta "
Wannan ya sa ta ki ahiga motar da Iman ta shiga ta taka a kafa, domin ta gama hardace wacece Muneerath, idan ranta ya baci ta fi kaunar ta tafia a kafa ta dan jajantawa kanta ta dan dudura ashar daidai gwargwado sai ta ji ta huce abinta
A hankali ta ce da ita" Waye ke yada iskanci a doron kasa kawata?"
Da sauri Muneerath ta dajata ta juyo zata bata amsa aka zo aka wuce da Iman
Da ido ta bi motar da iman ke ciki riiiii har ta shige mata kafin ta juyo, zata kuma yin magana aka wuce da mamanta da Oga wanda yake murmushi yana daga mata hannu mamantama ta mata murmushi
Dan murmushi ta masu ta dawo hankakinta kan Saudat ta ce" Wai ni oga yau ya cema ina iskanci, tsakaninki da Allah saudat da muka zauna da ke na taba yarda aka yi rungume rungumen nan da ni a cikin hayacina? Wa'inda suka samu a da ai a rashin sani ne na fada kansa, a yanzu fisabililahi ke ba shaida bace shi ya warto ni? Oga sannin ko waye Hanja ne bai yi ba da bai daukeni a yar iska ba tunda dai ni ai da sauki tun da aka haifeni har zuwa yanzu shi kadai na rikewa hannu , shima dan na hanna shi kuka ne, aman shi fa? Kowace shara rungumowa yake kai tsaye"
Saudat ta dan cije lebe tana gyada kai kai tsaye ta ce" Kika san ko sonta yake?"
Gaban Muneerath sai da ya ruguje ya fadi wanda ta san da babu fatar dake tare da kirjinta da a kasa warwas za'a tataro kirjin nata
Gummm ta yi bata bata amsa ba dan haka kawai ta ji Saudat din tama gama raina mata wayo, Kaf duniya babu wanda ya rainata irin Saudat din, dan Allah ina mahadin Hanja da Iman? Iman laso laso din nan da ta gama talata kirjinta a facebook tana dora hotunna kamar tsirara? Duda shima ta fara tunanin anya ba kwarto bane aman kuma ai sam basu dace da Iman ba, kai iman fa kanwarsa ce fa, yanzu haka rungumetan da ya yi dan ya lalasheta ne, ai Hanja akoy tausayi fa
A hankaki suke takawa suma har suka iso wata kujera inda sojojin gadinsu ke barbaje ta ko'ina haka kuma drnnn na saman kansu yana yawo ba daya ba ba biyu ba
HANJA ya kuma duban hanyar tafia palace , zancen zuci yake a tunaninsa ya ce" Ko a kafa ta tafi ko a sama? Allah dai ya sa ba haushina ta ji ba dan na dan rungume kanwata ina rarashinta"
Pah ya yi murmushi yana jin sanyi har kasan zuciyarsa, dama burinsa ya samu wada zata kasance mai kishin da zata hanna masa kallon matan nan da kwonciya da su, burinsa ya haukacewa wace idan ya kula wata zata iya barinsa, sai gashi ya samu a ruwan sanyi
A hankaki ya kalli fuskar Pah
Sai a lojacin ya gane ya ji shi ne fa, dan haka sai ya samu kansa da sada dubansa yana jimke hannunsa a hankali ya ce" Anya zata so ni?"
Ya dago ya kurawa fuskar Pah ido a sanyaye ya ce" Sai nake gannin kamar bana gabanta "
Pah ya kawar da idonsa shima a sanyayen ya dan dage kafadu ya ce" A gaskiya a yanzu baka gabanta, wanninka yake gabanta"
Idannuwansa ya rintse saboda wani irin abu da ya ji ya sokar masa kahon zuciya, bai san menene ba, bai san me yasa kalaman Pah suka so su bata masa rai ainun, bayan ya san gaskiya Pah ya fada masa iya gaskiya
A hankali ya ce" Aman me ya fi ni da zata fi dubansa?, Me yasama ka ce min wani ke gabanta? Sai nake ji kamar an zageni"
Pah ya yi murmushi yana kauda kansa ya ce" Abinda zaka gane a duniyarsu daidaikun mata ke iya nunawa saurayi sunna sonsa, suma kamar wa'inda suka aikata laifi idan aka ji hakan kamar zubar da kima ne a wajensu, ba kamar wajenmu bane da yin hakan ba wani abu bane nrml ne yadda namiji zai nuna maka so hakama mace, Son koda tana sonka ba zata taba nuna maka ba, idan ka nuna mata fine, idan baka nuna ba sai dai ta auri wani ta barka"
Ido ya zarro ya ce" wannan ai kashe kai ne"
Pah ya yi murmushi a bayane wanda rabonsa da yi tun da Mah ta fadi , a yanzu da ya shiga ya ga Alhamdulilah sai yake jin sa'ida a zuciyarsa, a hankali ya ce" Idan ka yi wasa....kamar da wasa.....zaka ga wasa, Now tell me a kan maganar Tronne"
Ido Hanja ya lumse a sanyayen da yake taintar kansa idan sunna maganar Muneerath ko tsakaninsu ne shi da Mah ya ce da Pah" Haka na yanke hukunci, ina fatan kasantuwar hakan"
Daga haka ya mike tsaye yana nuni da a zo a dauke su
A lokacin da suka shigo falo suka tarar da Iman kwonce idannuwanta lumshe sai Muneerath ta yi turus tana kallonta da kare mata kallo, wollah yarinyar akoy rama ko me yasa ita kuma kamar ta karye?
Saudat kuwa da ta gama shirya shirin shakawa Muneerath ta dan karkace kai ta ce" Aman sun dace, wannan saima ranar auren idan ta sha farar rigar nan tasu da dan magenta a hannu fari tana murmushi ya rikota ya rungumota"
Muneerath ta juyo tana kallonta, sam bata san me Saudat din ke yi ba , aman ta shirya fada mata abinda take yi ba daidai bane, sam ba hali bane, ta yaya zata ringa haka Hanja da Iman? Me yasa take haka ne? Ita bata ji abin na bata haushi ne? Haba dan Allah a ringa yin abinda hankali zai dauka mana, Hanja ai sai dai ya samo mata mai karfin hali in ba haka ba kulun a matsala zayana kasancewa, Iman din da daga an yi mata abin haushi take wuni tana kuka? Har fa kusan haukatata ta yi da ta kula motsi kadan sai ta yi kuka sai take taokanarta ba dare ba rana
Tana kallon saudat din a kausashe ta ce"
Barkarmu da warhaka yan uwa馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ
11/14/21, 12:53 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
6锔忊儯0锔忊儯
Muryarta a sanyaye tana kallon saudat ta ce" Sai ina jin gaba daya magangannunki basu dace ba, yanzu tsakani da Allah ina hadin wannan tsigigiyar yarinyar da a jikinta hancinta da farinta da idannuwanta sai shagwabarta ne kadai abin so?, Ke kin kuwa taba gannin Hanja da kyau? Kai ina ga baki taba kure masa kallo mai sunnan kallo ba wollah, Saudat Hanja sai da mace daidai shi, gaskiya ni bana son hade haden nan da kike masa"
Saudat ta saki murmushi tana kallonta ta ce" Wace mace? Ke baki san nasarun nan, bale masu kudin nan, na kai maki karshe sarakin nam, masu kyan nan, masu farin nan, masu daukan karfen nan sun fi son mace yar sharshara irin wannan ta kwoncen ba?, Yaya kike maganar basu dace ba bayan a gabanki da ya bata runguma ta shige jikinsa gwannin kyau tamkar indiyawa ba?"
"Ke itace fa ta rungume shi ba shine ya rungumeta ba, ke baki san kanwarsa bace?" Ta fada a dan zazafe dan gaba daya ji take abin na bata haushi har a kasan zuciyarta
Saudat ta kebe bakinta ta nemi ratsawa ta gefen Muneerath din ta shige, sai dai bata bata damar hakan ba ta dakatar da ita da hannayenta tana fadin" ki tsaya ki fada min dan Allah mana, ki tsaya ki yarda da maganata dan kar ki sa hakan a ranki bayan ba haka bane, kin ga fa yarinyar cen kanwarsa ce, shi kuma yayanta ne, kuma a zamantakewarsu Mah ita ce mamansu Pah kuma abansu ko? Ina maganar soyaya a nan in ba shirmen irin naki ba saudat"
Saudat ta ringa danne dariyarta a ranta tana fadin ' walahi sai kin kawo kanki da kanki in dai soyaya ce, idan ta barki kika gama haukan boyen zata falasaki ne, mu dai je zuwa ni da ke ma ga mai taurin kai' a bayane kuma sai ta ce" kin ga inace cewa aka yi du mu je mu yi sallah mu sakata a adu'a ba zaki wani tsayar da mu a nan muna maganar da ba ita ba?, Yo in ba abinki ba Muneerath dan kawai tsakanin ya zamo haka to ko Mah ta haifeta ta zo gidan da ita ai akoy soyaya tsakaninsu bale kin manta yar riko ce ita din? Yo kema Pah din da Mah din ai iyayenki ne, yanzun idan aka ce kece budurwarsa sai ace ba kyau?"
Zuwa yanzu so take kawai su yi balaki da Saudat, Allah ma kuwa haka zuciyarta ke fada mata Saudat ba mai kaunarta bace sam, to me yasa zata ringa neman fada da ita? A kan me zata tsaya gata ga ita tana son rikita mata magangannu? Me yasa ba zata bar maganar a yadda ita ta barta ba?
Tana shirin yin magana ta ga mota bak'a na karasowa sojoji na gudu da kafafuwansu haka droon na yawo a saman kan motar, hakan na shedar Hanja na cikin motar
Gabanta ne ya yanke ya fadin mata a lokacin da suka yi ido hudu da shi ya kureta da duba , duban da ba zata ce na meye ba sam
A hankali ta samu kanta da sakar masa harara mai zafi cike da jin haushinsa, wai shi dama gaba daya a nan ya tile? Soyaya da Iman , lallema
Bakinta ta murguda bata iya tsayawa ta ga fitowarsa ba, hasalima bata kula da Pah suke tare ba, shi kadai idannuwanta suka nuna mata ta juya rai bace ta shige ciki tana hada matatakalar ko kula cewar akoy wasu hakimtatum mataye larabawa a dayan falon na kusa da baban falon gidan bata yi ba ta shige lft ta danna tana ta cika tana batsewa
Oga da matarsa da suke zaune suma a falon gefen matayen nan da sam basa jin wani yare face larabci da turanci shi yasa ake zaman kurame dan kowa na son kauce zargin kar wani ya yi tunanin yine ake yi da shi ya kalli Matarsa a hankali ya ce" Kuma yanzu komawa zamu yi hala? Tunda an ce da sauki ko?"
Kallonsa ta yi, irin kallon nan na tsarewa da ido hakan ya saka shi shima kureta da duba, ba irin duban nan na balaki ba, ba kuma irin duba na raini ba, wani duba ne ya mata wanda duda jan idannuwansa sai da ta ga rauninsu
A hankali ta sada kanta muryarta sanyaye ta ce" Nima ban sani ba, yar ogan ce tunda ta bace mana ban ganta ba sai dazun nan a hanya ita da kawarta, ni kam abin na yar oga ya fara bani tsoro, ban san yaushe ta zama haka ba"
Oga ya karra kallonta yana son gane wai ta kula ko da wa kuwa take magana har ta masa a sanyaye haka? Rabonsa da gannin ta masa magana a sanyaye tunda ta dawo hayacinta
Yana shirin yi mata tambayar wani tafkeken soja ya shigo ya tsaya muryarsa sama sama ya shaida shigowar sarkin da Yaransa hakan ya sa larabawan nan mikewa gaba dayansu du suka daidaita hannayensu suka sada dubansu
A hankali Oga ya ce" Toh fah me hakan ke nufi kuma?"
Mamansu Muneerath da bata gane ba itama ta ga shigowar HANJA
A hankali ta karra kallonsa da kyau cike da mamakin yannayinsa
A yanzu jikinsa sanye ne da wandon suit din kadai sai riga ruwan toka mai duhu wace ta dan rike shi daga sama har zuwa kasa kasa kusa da abdo din da ya ninninke ya nuna kansa wajen cikinsa
Hannayensa dake da kauri wajen damatsunnan da jijiya birde birde da irin yadda kasa kasa wajen jimkaken hannun ya nuna kakarfan jiki irin nasa, har zuwa baki sidik din gashin kansa da yake caje gaba gaba ne kadai ya nuna ya dan fara hargitsewa kadan irin cajewar da akai masa ta fara hadewa kadan , har zuwa idannuwansa da jajayen lebunnansa
Da sauri ta cire dubanta a kansa gannin bayan ya gaba gaisar da larabawan nan da yaren larabci radau a bakinsa kamar wajensu ne ya juyo, gabanta na faduwa cike da tsoron me ya kai Muneerath jikin dan sarkin kasar nan?
Pah da ya gama amsawa mutane masu tambayar jikin matarsa yan uwanta na kusa sosai da suka fantsamo dan gannin jikinta da kulawa ya shigo shima ciki wajen Yayar matarsa, da mahaifiyarta, da kuma dayar matar mahaifinta marigayi sarkin Makkah
Cike da mutuntawa ya gaishe su, kafin a nutse ya basu bayanin komai bayan sun yi gaisuwa irin ta larabawan nan
Oga da yake kallon komai sai ya samu kansa da fadin" Nana, inaga wannan runguma da aka yiwa Muneerath ba komai bace, tunda dai kin ga da farko da shi wannan katon ya rungume mutanen nan jira nake ace su dinma yan matan nasa ne? Dan kuwa kin ga su Idan sunna soyaya ba ruwansu da shekaru, sai kuma ga ubansa ma ya aikata, garin nan so suke au karar min da man kaina kaf, walahi so auke du hargitsa min tunanina ta hanyar nunan idan iskanci nake ji su a rubuce suka shanye shi, kin ga mu yake nunowa uban kardai muma su rungume mun mun shiga uku"
Harare ta so sakar masa, sai dai gannin sun nufo su har matan ya sakata mikewa tsaye tana jan lulubinta da tunane tunanen ta yaya zasu gane yaren junna? Ko dai ba'a zama a nan suka zauna?
A mutunce Pah ya fara magana, ga mamakinta sai ta ji Freinch radau a harshen Hanja a lokacin da Pah ya shiga gabatar da su yana dan murmushi kan cewa iyayen yarinyar da suka dauko ne a africa wace Aleesa ta daukota , tana son yarinyar sosai
Sannan ya gabatar masu da matayen suma yana murmushin inda Mamansu su Muneerath ke kara fasarawa Oga wanda freinch din nasa sama sama ne ba wai ya kware bane
Pah ya yi wani murmushin yana fadin" Yarinyar itace yaronku ya haikace a kanta"
Wannan kam sai Hanja ya samu kansa da kasa fasarcewa su mama dukda ya kula fasarar suke jira sai kawai ya dan sosa keyarsa ya dan juya a hankali ya nufi hanyar ficewa yana ayana' Ai fa na shiga uku tunda na ba Pah amanar haka ne, sai ya kuncen wando a ko'ina'
11/14/21, 12:53 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
6锔忊儯1锔忊儯
Da murmushi Pah ya raka shi, ya tabata zai je ya nemi ganninta ne, aman bai san ba ko zai iya kuwa? Burinsa idan Allah ya yi Aleesa ta kawo hankali ta tarda su a hade, bai san irin farin cikin da zasu yi ba gaskiya
Ba shi ya bar wajen ba sai da ya saka aka kai su Oga baban waje na alfarma, aka gabatar masu da komai sannan aka basu wayar da zasu iya samun yarinyarsu da number dakinta
Oga kam ya gama ajiye komai zuwa yanzun ya kara baje kolinsa dan ya kwashi gara daidai gwargwado, wannan marar lafia kuwa yana fatan ta tashi har kasan zuciyarsa
Maman Muneerath kanta sai ta samu kanta da binsa da kallo a dukan motsinsa
Irin yadda komai zai yi sai ya hankalce da ita, irin yadda yake kafa kafa da ita, sai abin ke son birgeta har yake son samun waje a zuciyarta , kamanin da yaronta baba ya dauko na bata mamaki, babu abinda ya bari nasa sai dai ya yi hasken fatarta, Muneerath kuwa ta tsakuri cen ne, ta tsakuri nan
______________________________
Dare ne ya tsala
A irin lokacin nan du yan matam kowace na abinda ya zame mata malati, watau wata na fama da waya a kunne, wata na fama da ita tana cikin social media, watan kuwa na kallo ne da wayar, gaba dayansu dai su ukun da suka hade a daki daya sakamakon rashin dadin zuciya da kuma da gaya Saudat ta gayato iman cewar ba zasu barta ita daya a dakin cen ba, sai suka hade a dakin Muneerath su dukansu inda Muneerath din take wani shasha masu kamshi bayan ba abinda sukai mata tana wani hura hanci abinta ga kuma waya a hannunta tana ta aikawa sir attahir message wanda yake zaune gaban tea yana sha yana cike da kewar muryarta, da kewar fadanta, da kewar komai nata aman ba yadda ya iya, maman Sir bata fito a mutun ta fada masa komai ba aman a irin yadda ta nuna shi ba mahaukaci bane, ya san kokowa ce da ta fi karfinsa, hakan ya sa yake nesa nesa da komai nata dan shi kam ya san abokin kokowar nasa ba sa'ansa bane, da ya hada kansa da ciwok zuciya gwara ya ba kansa hakuri
A hankali ya shiga whatsup din kamar yadda ta bukata yana dan girgiza kansa yana son sannin me take so kuma? Idan aike ne sai ya je yanzu yanzu ya yi
Zuwa lokacin ne ta aika masa da kira ta WhatsApp ta kanga a kunnenta
Yana dagawa ta shiga tambayarsa abinda yake damunsa
A sanyaye ya ce" Wani abu kika gani?"
A hankali ta ce" Gani na yi yanzun baka min irin kalan nan na soyaya da sauransu"
Dan murmushi ya yi na gannin wannan ai wulakanci ne take son yi masa kafin ya ce" Kin damu da su ne? Ko tunda na fara fada maki su kin taba bani amsar kema kina so na?"
Zuwa lokacin ne aka dan buga kofar nasu a hankali
Idannuwanta ta kai wajen kofar kafin ta cire ta dora kan yan matan
Gannin ba wace ta sanma an bugan ya sakata mikewa a hankali ta nufi hanyar budewar ta kama ta bude tana fadin" Freind, aman ai mun yi maganar nan da kai ko?, Nice da bakina na ce maka zan fada maka irin haka da zarar lokacin ka ji ya matso, ka sani b......"
Idannuwanta ne suka sauka a cikin nasa ya wani kuretan nan da kallo baya ko jin wahalar irin kallon nan
Maganarta ta samu ta katse mata a kan lebenta tana kallonsa
A hankali ya langwabar da kansa yana son cire abinda ke son damunsa na wayar da take yi duda bai san ko da waye ba, a hankali ya samu kansa da furta" Yinwa nake jihhhhhh"
Muneerath ta kurawa lebunnansa idannuwa ta kasa motsin kirki har sai da ta so jin kamar Attahir na magana a hankali ta ce" Zan tabo ka idan na gama , ana kirana"
Daga haka ta katse kiran tana kallon irin yadda ya bi wayar dake hannunta da kallo har ya karanci mai kiranta
A hankali ya tsareta da idannuwansa yana jin wani irin abu na tafarfasa masa zuciya
A irin wannan lokacin? Tsakiyar dare ne fa, shine ya yi kiranta?
Muneerath ta ce" To ni dai ai ka san ba iya girki na yi ba HANJA tsakani da Allah in dai ba cake zamu je na maka ba sai dai in su saudat zan taso su taya ni mu dafa ita da i........... Ita da , ita daya" ta samu kanta da karasawa tana wani hararan gefe guda wanda shi kuma gaba daya a tsayen nan ta inda zai bilo mata ya fi tunani domin sam baya jin dadin zuciyarsa, hakan ya hanna masa gane inda indar da ta yi kafin ta bashi amsa
A hankali ta juya dan kiran saudat din yana nan tsaye
Ta fada mata ta dawo tana rike da hijan dinta da kuma wayarta , Saudat din na bayanta infa Iman ta dago ta raka su da kallo gaba dayansu ta koma ta kwontar da kanta tana sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta zabura ta mike tana dan sauri ta biyo bayansu tana ayana ai sai dai a dafa da ita
A lokacin da suka fito su biyun ne yana nan tsaye
Singileti ce a jikinsa fara sai wando da ya zarce gwuiwarsa
Har yanzun yar tsoro tsoro ce tsakaninsa da Saudat hakan ya sa tana gaishe shi ta sada kanta ta yi gaba fa dan sauri
Muneerath ta karasa gefensa tana jin damuwar jin yinwarsa a ranta da tunanin bawan Allah idan da ace Mah din ta mutu shikekan ya shiga uku da rayuwa ta sangarta shi komai ita ke masa
A hankali ta budi baki zata yi masa magana ya rigayeta ta hanyar fadin" Ki rufan asiri ki daina tada min hankali"
Ido ta zuba masa tana son yi masa magana iman ta karaso da kula ta ce" Prince me zaka ci na kama masu mu dafa? Ka san Muneerath cake kadai ta iya"
A hankali Muneerath ta lumshe ido daga kallonsa
Wayar dake hannunta bata san lokacin da ta yi mata nauyi ba ta saketa kasa
Bayan ta fadinma sai ta ga idan ta tsaya dauka ta shiga hakin masoyan, a hankali ta juya jiki a mace da niyar komawa daki, tunda ga babarsa ta biyu ita kuma meye nata na yi masa girki? Ai sai ta koma ta saurara
Hannunta na dama da ta ji ya riko ya sakata ja ta tsaya
A hankali ta nemi juyowa sai dai wata bakuwar jaraba sai take jin idannuwanta sun cika da kwalah, hakan ya sa ta nemi janye hannunta dan ta je ta samu iyayenta ta fada masu yanzun bata san me ke damunta ba, kadan kadan sai ta ji magana na bata mata rai har kamar ta yi kuka
A jinginen da yake jikin garu ya janyo hannun nata ta yada zata juyi gaba dayanta ta taho da wani irin karfi ta fada san fafadan kirjinsa inda ya saka hannunsa a hankali ya dafe bayan nata yana shafawa idannuwansa a lumshe ya kai hancinsa daidai kunnanta wanda gashin kan nata ke ta hanna masa hadewa da kunnen naga, muryarsa cen ciki ya iya budar bakinsa da kyar ya ce" My Munarah........."
Gaba daya mutuwa jikinta ya yi, haka kuma ita da kanta ce ta samu kanta da makale kirjin kato a gaban al'uma
Wara yar shashekar kuka ta ja tana sauraronsa
Muryarsa cen ciki bayan ya dan gogi kunnen nata ya ce" Walahi, kasheni zaki yi....................ba zan iya ba, kar ki saka na yi kisa na tada hankalin iyayena, ...........kin ga har na gama hango da irin bindigar da zan dauke kansa na huta, ban san me yasa ba"
"Wayo Oga.......". Ta samu bakinta na son kurma ihu ta kirayi abanta ya talafa ya rabata da yaron nan tun kafin ya kasheta
Wa yake son kashewa?
Me yasa ba zai fada mata gwa da gwa ba sai ya raba hali
Ya Allah, ya Allah me yake damunta ne da yaron nan????????
Oho馃槀
Sorry 2 days na yi tafia ne
Domin samun labarinki, mai sunna WATA KOKOWAR wanda nake kan rubutawa ki tumtubeni ta number wayana kamar haka +227 93 81 16 18 sai kun zo
11/14/21, 12:53 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 42