ya ji hamma ce ta yi aman kuma ba zata kwonta ba sai ta gama yi masa nasiha , muryarta tausashe ya ce" Yanzun sai kun kara kwana nawa? "
HANJA ya kai dubansa kan agogon dakin kafin ya ce" Uku "
Kai ta gyada, sosai take son ce masa dan Allah a kwana ukun nan ya tsare kansa da aikata zina, sai dai kasancewar ba a kowani time take masa irin maganar nan ba sai ta wayance ta ce" A duk lokacin da ka ji zuciyarka na ingizaka ga aikata aikin da ubangijinka ya hane ka da aikata shi komai kankantarsa, ka yi gagawar hasaso amsar da zaka bashi a lokacin da ka zamo daga kai sai shi, ka saka zuciyarka koran shedan ta hanyar sakata furta A'UZUBILAHI MINA SHAIDANIN RAJIM, ita da kanta ba a kan lebenka ba, a haka zaka ji koma menene yana kasa da son kauce fushin wanda ya hakiceka, shi kuwa du wanda ke yinkurin barin sabon Allah ana masa kyakyawan zaton zai daina kwata kwata wata rana"
Murmushi ya yi har cikin zuciyarsa yana lumshe idannuwansa bai yi magana ba, Murmushin nasa shine amsarta wanda ta ji dadin jin murmushin dan alama ce ta ya dauki maganar
Da kyar ta katse kiran shima sai da barci ya farra daukanta kafin ta katse dan kanta ta silale saman bed dinta , dama dan ta masa nasiha ne ta yi masa dogon kiran nan
Murmushi yake da byron a hannunsa
A hankali ya dora ya rubuta *MOTHER* a saman farar takardar, kafin ya dora a kusa da sunnan MOTHER din kalmar *I LOVE YOU*
Wayarsa ya janyo ya bude ya dauki hoton hakan sannan ya tura mata ta whatsup dinta ya ajiye wayar yana dan murza gefen wuyansa daga zaunen da yake
Knocking din da aka yi ya saka shi kai dubansa wajen kofar
A hankali ya mike tsaye daga kwoncen da ya koma ya yi ya ja ya tsaya
Kaffafuwansa ya dan wara ya mike hannayensa sama ya yi mika da salati a kan labansa kafin ya nufi wajen kofar kasancewar rufeta ya yi da ky
Bai wani leka dan gannin ko waye ba, murdawa ya yi ya bude
Ido ya zuba masu, yan mata ne biyu tsala tsala sun dau wanka cikin shigar kananun kaya watau dayar na sanye da dogon wando dayar kuwa da riga doguwa aman bakin tsayinta gwuiwarta kuma a gwuiwarta tana da tsaga, irin dai an gama damewa iya damewa
Idannuwansa ya lumshe ya kai dubansa kan yaron da shi da kansa ne ya saka shi dauko masa gidan hutun nan
*Ka sani kora ka yi nisa ka boyewa ganina wanda ya halice ni, ya haliceka, ya isa da ni mamanka ba kai ba yana kallonka, shin baka tsoron a taba ni mamanka?* da sauri ya buda idannuwansa yana kawar da dubansa a kansu , kwata kwata ya ji abin ya fice masa a rai duda idan jikinsa za'a buda za'a ga ba haka ba, aman a hankali abin ya fice masa a ransa
Kofar ya mayar ya rufe ba tare da ya ce da su komai ba ya koma saman bed sin yana dafe kansa da yake jin ya masa nauyi ya kwonta a hankali yana lumshe idannuwansa
Kallonsa suka yi, mai sanye da doguwar rigar ta dan watsa hannayenta ta ce" Yaya haka ?"
Shima gaban goshinsa ya dan dafe ya ce" hakan na nufin baya ra'ayi"
Mai sanye da wandon ce ta juya kwayar idannuwanta ta ce" Ban gane ba, ba shi ya saka ka kawo masa mu ba? Shine ka sa muka ajiye du wani costomanmu na yau muka biyoka ka mana alkawarin in dai kudi ne damuwarmu zamu samu isasun da sai mun ji dama mun bishi?"
Kalonsu ya yi daya bayan daya ya fara tafia yana fadin" Mu je ku amshi kudinku dan ba sune damuwarsa ba!"
Da wannan ya yi barci, aman a mugun jigace, irin mugun barcin nan da kana yinsa ne kawai aman farkawarka zata fi zame maka alkhairi a kan rintsa idannuwan naka, tun karfe hudu ya farka a jigace ya samu da kyar ya yi wanka ya dauro alwallah ya fito
Saman darduma ya hau ya mayar da gabansa gabas ya tsaftace tunaninsa, ya tsayar da dubansa, ya dorawa harshensa ambaton wanda ya isa ya bashi ko ya hanna masa, wanda ya isa ya karre shi , wanda ransa ke hannunsa, mai dora cuta mai kuma bada magani, gagara misali sarkin sarakuna
Sai da ya gabatar da azhkar dinsa cikin nutsuwa kafin ya mike
Kayan gudu ya saka ya fice a dakin jikinsa ba kuzari sosai dan mararsa ta masa nauyi
Bai samu ya yi gudun yadda yake so ba ya koma dakin hotel dinsa ya zauna sai hada rai yake dan bai fa ci abincinsa ba, ko yinwar dake cikinsa bata kai damuwar da yake ji ba
Kasancewar pc dinsa a kunne yake, sannan connexion ba saukewa ake yi ba vidio calll ya shigo masa
Ya jima yana kallon sunnan kafin ya dauko ya daga yana kallon screen din
Kallon junna suke da hakimtacen mutumen da ya bugo masa wayar,
Da dukan alamu a wajen wannan kamilalen ya gaji wannan shariya da iza irin ta sarauta
Kamar ba zai yi magana ba ya kalli agogon hannunsa ya kuma kallonsa ya ce" Ina kwana "
Kansa ya dan sada ya sosa girarsa sannan ya dago yana kallonsa
Kuma gimshe fuskarsa ya yi ya ce" Abinda ya gani a takarduna ba su ba zai fada min? Meye laifinsa dan ya fadan cancerta ta kai stade na karshe har da zaka kore shi a kasa? Wannan fa shine likitan mamanka a hannunsa ta rasu, kuma nima shine likitana tun ban san zan haifeka ba, meye laifinsa? Ko dai tsoron kujerar da ta zame maka dole hawanta ne ya saka ka korar shi?"
Idannuwansa ya rintse cike da jin zuciyarsa na tsintsinkewa, kuma budewa ya yi ya sauke a kan fuskar mahaifin nasa kafin ya saka hannunsa ya rufe computer ya jinginar da bayansa a jikin garun dakin yana jin kansa na juya masa......da ace shi din mai magana ne da ya budi bakinsa ya sanar da su abinda yake ji a cikin zuciyarsa, ba zai iya fasara masu ainahin me yake ji a zuciyarsa a yanzu ba, baya tunanin harshe zai iya sanar da abinda ya dane masa zuciyarsa ba, shin ina zai shiga? Ta ina zai fara? Me zai rika?.......
Kukan da wayarsa ke yi ne ya saka shi kuma bude idannuwansa ya dauko,
A nutse ya daga da salama a kan labansa
Sama sana yake jiyo muryarsa yana fadin" Ki fadawa yaronki ni ubansa ne ba yaronsa ba, ni zai rufewa call? Bani shi"
Sai da ya saki murmushi a sanyaye ya ce" Mahhhhhhh "
Tsai ta yi jin yannayin muryarsa, a hankali ta ce" Son lafiyarka? Baka da lafia ne? "
A sanyaye yana fatan idan ya budi baki ya rushe mata da kuka ya ce"
Ya Allah ka amshi ibadunmu, ya rab ka yafe mana zunnubanmu馃憦馃憦馃憦
11/14/21, 12:44 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
SADAUKARWA GA : *SIS MUNEERATH MARUBUCIYARMU BABAR MARUBUCIYARMU LIKITARMU KUMA HAJIARMU*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
1锔忊儯3锔忊儯
TASO DA NONO
Ki samu ayaba (plantain) ki yanyanka ta ta bushe sannan ki daka ta ta zama gari, saiki samu aya ki wanke ta ki saka gyada ki markada sai ki tace ruwan kina diban wannan garin plantain din kina zuba madara peak kinasha kamar sau biyu arana kafin sati daya zakiga canji sosai nononki zasu tashi su ciko..in shaa Allah.
Sannan ki samo APKI ki dake shi sosai ki tankade shi ya yi laushi sosai ki kawo garin Hulba ki hade da Bulanga (Man kade) ki cakude su sosai ki ringa shafawa mama da hips, su maman ki ringa daure su cikin bra dan idan sun dauko cikowar su dauki yannayon tsayawa ciirrrrrr a kirjinki ki yi ta yi har su tsaya iya yanda kike so hajia, sirri ne wanda aka gwada鈽猴笍
A hankali ya kuma maimaita sunnanta yana lumshe rinanun idannuwansa
Mahaifinsa da ya dauki zafi sakamakon kashe masa kira da ya yi ne ya tsaya a gaban matarsa uwar gidansa kwalin kwal yana kallonta gabansa na faduwa
Tamkar kurma ya shiga yi mata nuni da tambayar bashi da lafia ne?
A hankali ta kai zaune dan jin zuciyarta na luguden kida da tsoro fal a cikinta ta ce" Fada ya maka ne? Menene? Ka ci abinci?"
Da kyar ya iya sakin lebensa da ya cije da karfi muryarsa cen ciki ya ce" Wai likita ya ce masa ya kusa mutuwa, kin sani? "
Idannuwanta ta rintse da dan karfi sakamakon tabo mata abinda ke sakata kwana da tashi tana kuka , takan wuni zuciyarta cinkushe, takan so zama da shi su yi maganar da zasu tsayar da maganar zama tare daga ita sai shi sai mahaifinsa aman kwata kwata ya kiya, ashe gudun maganar ne yake? Ashe abin na masa ciwo ne?
A hankali bayan ta aro dukan jarumta ta ce" Na sani "
Idannuwansa ya buda da sukai masa ja muryarsa a sanyaye ya ce" Yaya kike iya shanyewa? Yaya kike iya walwala?"
Idannuwanta da suka kawo kwallah ta bude ta sauke a fuskar mijinta dake zaune yana kallonta, da wani irin yannayin da ta kasa gane shin shirin fashewa yake yi da kuka ko murmushi ne kwonce a kan fuskarsa?
A hankali ta ce" Dan na yarda cewa dukan mai rai mamaci ne, dan na kwana na kuma tashi da sannin cewa du daular nan da muke ciki du irin girman sarautarmu , du gatanmu, du masu tsaronmu bamu isa mu ja da wannan kakarfan lamarin ba, idan lokacin ya zo babu tsumi babu dabara dole zamu mika wuya"..........dan sasautawa ta yi hawaye na zirarowa ta kurmin idannuwanta, muryarta ta yi rauni ainun ta ce" Dan na san kuma cuta ba mutuwa bace, ta yiwu shi aka ganowa haka aka fada, hasashen kennan, wanda babu wanda yake tsaye a lokacin da Allah ya hukunta bale ya tsaya ya fadi cewa ga rana, ko boka, ko malan, ko likita ba zai ce wane ga ranar da zaka mutu ba, komin zafin ciwo, Son mun san da ciwonsa...........cancer, ya ki a yi treatment dinsa.
Son na kwana da sannin shi mai wannan ciwo yana iya murjewa ya tashi kalau wanda yake tafe da lafia ya zama gawa, idan na tuna haka idan na tuna cewa idan ba lokacin bawa ya yi ba ba zai mutu ba, sai na dan ja numfashi na sauke,
Son ka fa sanshi ina fada maka ka zauna mu yi maganar kana gudu, Son sai na zabura na farka na fashe da kuka idan na tuna yar uwata ....."
Ta karashe tana fashewa da kukan da ya saka HANJA mikewa tsaye yana cakuda gashin kansa a hankali ya ce" Plz , Mah, plz li bar kukan "
A hankali ta ringa rage kukan nata tana ta shasheka, idannuwanta ta lumshe ta kuma budewa tana kallon yadda mijin nata ya bude mata hannayensa yana nufin ta zo gareshi
A hankali ta karasa gareshin tana karra rike wayar da kyau ta shige jikinsa ta dora kanta saman kirjinsa, muryarta cen ciki ta ce" Bana so ka mutu "
A hankali yake tapping din bayanta a cen ciki ya ce" SHIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIT "
A hankali Hanja ya kashe kiran ya kai zaune saman bed dinsa
Dubansa ya kuma kaiwa wajen agogo kafin ya mike ya yi bayi
A gurguje ya shiga shiryawa yana duba time din da jiragen zasu tashi dan zuwa gari gari
Idan ya ce a yau zai tafi ya tabata sai ya sha yawo, zai sha wahalar zaman jirgi da cenza jirgi, aman kuma zai je din dan zuwan shine abinda yake ji a gaf da zuciyarsa, zai je ya fuskanci mahaifinsa a yau su zauna su tatauna, ya hanna mamansa kukan nan da ta dauka take yi, ashe shi yasa kwanakin nan bini bini ta zo wajensa ta zo ganninsa? Ya rab
...............................................
Barkarmu da wannan rana
11/14/21, 12:45 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
1锔忊儯4锔忊儯
Ta jima Kanta sade tana kallon takardar da kwaro kwaro sa hannun mahaifinta da na mahaifiyarta suka bayana kafin ta dago kanta ta kuma danna recodern da akai masu dan ta tabatar ta kuma yarda da maganar da aka fada mata
Zuciyarta ce ta ji ta mata rauni, a hankali ta kai dubanta kan Buzun da ta jaza masa yin kwararan kwana biyu a cikin gidan nan, du ya firgice ya fita a hayacinsa, gaba dayansa ya firgice, a sanyaye ta ce" Baka daina kukan ba? "
Dubanta ya yi, shi yanzun tsorontama yake har ga Allah, bai san wani irin damuwa iyayensa suka shiga na rashinsa ba
Shugaban makarantar ne ya dube shi ya yi murmushi ya ce" Mahaifinka na waje, kai kawai yake jira ku juya gida, mahaifiyarka kuma ta ce bata yi fushi da kai ba "
Muneerath ya kali shugaban makarantar, gaba daya sai ta ji ta karra muzanta, ita bayanan nata iyayen banda tsabagen turewa da nuna halin ko in kula da nuna kai gwarama da ta tafi dan mahaifiyarta cewa ta yi Allah ya sa su su gane bata da lafia su bema mata magani kafin su dawo da ita, babu wanda ya nemi zuwa ya ganta, oga daria ya yi ya ce kai aman yar oga an yi nataciya, to idan so take ku bata mana ni ai bana hanna yarona yin aiki ko wani iri ne, ai gwara ita aikin nata a bayane yake idan ta samu kuma zan fi kowa daga kai da tunkaho a gari, wasun fa ba'a san ko me suke so takamaimai ba gasunnan shagu a zube sai kwarewa a iskanci!
Ko da akai masa tambayar zai je ya ganta ? Dan idan aka rufe aka fara masu horo ba wanda zai shiga , cewa ya yi kai ina akoy inda zai je kawai a gaisheta
A hankali ta hade hannayenta ta dora kanta saman table din dake gabanta ta dora hannayen nata saman kanta watau saman gashin kanta da rabonsa da abin daurewa dan kwali tun da ya kwonce ya fadi a wajen da aka jona mata chok din nan,
Kunnayenta ke jiyo mata takun tafia da budewa da tafia da kuma rufewa
Shiru ne ya dauki sal din, kanta a saden nan sanyin wajen na ratsa gabai din jikinta baki daya
A hankali ta karra jan shashekar kukan da take ta danewa, jin shirun ya karra ratsa wajen sosai ya sakata dan dagowa a hankali
Ido hudu suka yi da shi, a hankali ya sada dubansa sakamakon yadda gabansa ya fadi na hada idon da ya yi ido cikin ido da ita
Kuma juyowa ya yi yana kallonta a hankali cikin yaren turanci ba freinch ba, gogagen turanci dan ya fara gwada ilimin nata ya ce" Me yasa kike kuka "
Gashin kanta ta ture da hannunta a hankali ta karra cije lebenta na kasa ta hade gashin girarta mai bakin gashi sosai wanda tamkar an mata gyaran gira irin gyaran girar nan mai shegen kyau , hannayenta ta hade wajen kirjinta ta kara busa iska wajen gashin da ya kuma zubowa gaban goshinta
A hankali ya zauna saman kujerar yana kallon iya fuskarta da lebenta ya yi ja , kasancewar tana da baiwar lebe mai ruwan pink na kasan nan sannan ko yaya ta dan dantse shi sai ya dan karra kumburi ya kuma dauki shekin dan yawun dake gogarsa sakamakon takan fitar da harshenta ta dan lashi leben nata ta mayar
Fuskar nata sai ta masa kama da shekarun da ba nata ba, tamkar bata kai shekarunta ba, fuskar tata ta masa kama da fuskar yara kanana irin fuskar mage, gaba daya a yanzun da idannuwan ke cika da hawaye sunna zuba shar shar shar yadda ka san a mayar da ita TV abin kallo
A hankali cikin yaren turancin ya ce" Bakya son aikin ne ?"
Kanta ta girgiza tana kallonsa , a nutse ta budi bakinta cikin wani irin kalmasashen turancin da idan ba fada maka aka yi ba zaka yi tunanin yarinyar au tunda ta budi baki da shi ta buda, ko kuwa shine kadai yaren da ake mata a makaranta kuma ta kasance mai maida hankalinta wajen iyawa dan a yanzu da yawa sun amsa sunnan yan makaranta aman kuma cikin ikon Allah ko yaren da ake masu a makarantar ya zama aiki yinsa daidai, ko su yi magana mai dan tsayi da shi, a hankali ta ce" can you introduce yourself plz? " ( 馃檮 saura ku ce na yi kwabar ni ba iyawa nabyi ba ah toh馃樋 )
Da mamaki ya karra kureta da ido kafin ya dan yi gyaran murya yana gyara igiyar cravatte din dake wuyansa yana shirin yin magana aka yi knocking
Kafin ya bada damar a shigo aka shigo
Fuskarta a hade hannunta dauke da wata leda
Da kallo ta bishi irin zaman da ya yi kafin ta kai dubanta kan Muneerath
Kayan ta ajiye mata saman table din sannan ta ajiye mata wani dan litafi mai dauke da sunnan makarantar kafin ta dora hannayenta biyu saman table din da yaren freinch ta ce" ina fatan kin fahimci wajen da kika sako kafarki, a yanzu zaki tashi ki je ki yi wanka, ki cire dukan dattin nan na jikinki , ki cenza pant da bra ga kayan da yan makarantar ke anfani da su nan ki saka, a cikin dakinki akoy turare, akoy komai na bukata ki gyara jikinki kafin ranar shigarku saloon ta zagayo, ki fito ki same ni a wajen piscine zaki shiga mu ga irin yadda kika iya ruwa"
Shugaban makarantar ne ya ce" Aman ai ba haka aka tsaida maganarta ba ko?"
Da yannayin ladabi mai hade da jin haushin mutun ta sada kanta ta ce" Ka yi hakuri Sir, gani na yi sun mata nisa ina so ku bani damar da zan horata da sauri ta yadda zata kamo su, wannan formation din kai ka san idan mutun na wasa nan da shekarama ba zamu iya yayeshi ba bale a wata uku"
Fuskarsa ya fara hadewa dan yana son gane kamar tana da wata takakiyarta da ita ya ce" Idan bata iya ba zaki saka yar mutane cikin ruwa ta sha ruwa ne?"
Zata bashi amsar da zata yi convincd dinsa suka ji muryar Muneerath da yaren hausa yanzun ta dago dubanta sosai tana kallonsu su dukansu ta ce" Kuna magana bayan ban san ko su wanene ku ba? "
Da sauri ta juyo tana kallonta, irin yadda ta tsare su da maganisun idannuwanta masu lu'u lu'un kore mai ruwan ruwan tafki wanda yake da haske aman mai dauke da shukokin kainuwa ga gazar gazar din gashin idannuwanta da ruwan hawaye suka jika su suka yi luf su kadai suke hade junnansu sai ta ji wani irin dar dinta, aman kasancewar ta san dole ta sada mata ta mata biyaya dan itace mai gidanta a nan sai ta wani kausasa yannayinta ta kara rage tsayinta ta hanyar kuma dora hannayenta saman table din ta yadda iskar bakinta zata doki fuskar Muneerath din idan ta fara magana a kausashe ta ce" Wani irin rashin hankali ne zaki mana tambaya haka kai tsaye tsakaninki da mu baki da kunya ne? Sannan wannan ya zama na karshe da zaki yi magana da yaren hausa a cikin gidan nan idan kika kuma yi zaki fuskanci punishment "
Muneera dake zaunen nan bata tunanin wai akoy macen da zata wani yi mata ihu a kai haka kawai batama san ko wacece ita ba zata zuba mata hauka a wajen nan bayan zuciyarta a cinkushe take so take ta je ta sha kukanta na irin rayuwar da iyayanta ke gabatarwa wace bata ga irinta ba har yanzu, ace wai ta kwana biyu a wani wajen ba abinda ya dame su, bakin fuskar da basu sani ba sun zo masu da wasu zanceceku mararsa tsari dan ba sannin komai suka yi a kan maganar ba aman ba bincike ba komai suka nuna hakan ya fi masu zamanta a kusa da su, shine wannan mai sket a tsagen kusan pant a waje ta wani zo tana mata maganar ta saka pant sabo a gaban wannan gardin harda su maganar bra tsabar rashin kunya kuma ta wani fara yi mata ihu an yi hausar ba punishment ba ta yankata dan kaniya hausar ai ba ta uban wani bace! Ido cikin ido ta ce" idan fa shi kadai na iya? "
Ji ta yi kamar ta gaura mata mari, kan balaki wannan fitsarariyar ce zasu kawo mata ta hora? Ko freinch bata iya ba? Bale turanci?
Rai bace zata fara magana ya daga mata hannu ya karra kallon Muneerath dake zaune tana kallonsu kafin a nutse ya ce" Ki yi hakuri, ki je waje ina zuwa "
Kallonsa take tamkar zata hadiyi zuciya ta kuma kallon Muneerah da mugun tsanarta ta yi kwafa ta juya ta fita ta tsaya gak da kofar tana jijiga
Zama ya yi ya aro jarumta ya hade ransa sosai ya bude litafin dake gabanta yana kallonta ya ce" Kamar yadda kika san kowani enterprise na dauke ne daga sama zuwa kasa, idan na ce kasa ina nufin harta mai goge gogen gidan nan, kamar yadda a kowani gida akoy baba, mama, yaya, har zuwa auta, wanda ya dace ka yi respectin din du wanda ya girmeka haka ne....."
A sanyaye ta ce" kar dai ita ce mai wajen? "
Irin yadda ta tsakure dan tsukeken bakinta ya saka shi karra shagalta da lamarinta kafin ya tunawa kansa ko waye shi a gabanta da dan sauri ya kawar da dubansa ya ce" nine mai ja gaban wajen, nima ba wajena bane "
Ido ta kwalalo ta rufe bakinta da hannunta tana kallonsa ta ce" Wayo Allahna, ka ga da na sani da ban maka tambaya kai tsayen nan ba, kuma fa asalina ni din ba fiysarariya bace ko daya, an samu akasi ne a rikice nake na kwan biyu ban sadu da iyayena ba na san hankalinsu a tashe gashi ni sata na yi ba an rufe ni a nan....."
Sai da ta gama fada kuma ta tuna shi fa ya kunna mata abinda iyayen nata suka fada hakan ya sa ta shiga murza hannun nata tana fadin" Ba ainahin wa'inda suka haife ni ba, makotanmu "
Kansa ya gyada a dai yannayinsa na ya dauki yannayin serius Ya ce" An yi accepting dinki a wannan makaranta bayan an yi vote masu son ki zauna suka fi masu son ki tafi yawa, sai da na je da kaina na samu amanar mahaifanki kafin na zo nan, daga yanzu har zuwa lokacin da zamu yaye ku a nan zaki zauna da mu, ya zamana dole a gare ki ki girmama du wanda yake gidan nan shima kuma zai girmama ki komai karantan shekarunki dan kece mafi karama cikin yan uwanki, ya zama wajibi ki bi du wani dokoki na gidan nan dan ki samu zama lafiya da masu koyar da ke harma ki samu fitowa a cikakiyar HOTTESTE "
Da wani irin madaukakin emotion tana kallonsa ta ce" Kana nufin kun yarda zaku bani formation? Wa ya biya min? Wa ya saka ni? Wayo Allahna"
Irin yadda madaukakin farin ciki ya bayana a fuskarta ya tsaya kallo ko amsa bai bata ba, lokaci daya ta mike tsaye da hannunta tana nunawa ta ce" Ka ga na iya ruwa, na iya turanci
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 42