dauki a kalla second ashirin tana kallonsa kafin ta bude gaban motar ta shiga ita kanta gabanta na faduwa kuma jikinta tamkar an zare mata laka, abu daya ne ta sani zata so ko a tarihin rayuwarta ta fadi ga yadda katangar makarantar yan hottest take
Shiru ne ya dan ratsa mktar kafin ya kara kallonta ya shiga yi mata tambayoyi dangane da shin inda zasu ina dinta ne? Kwata kwata sai ta ki bashi gamsashiyar amsa, kai daga baya sai ta daina fahimtar mema yake fadi, ta afka tunanin hanyar cike da begen wajen a kasan zuciyarta
Sun dauki lokaci sunna tafia a kadan sun kusan awa biyu har sai da ta fara tsarguwa gannin anguwar kamar sun fita daga gari kafin suke hawa wata shinfidadiyar kwalta
Lumbuk take a saman hanyar, tamkar a yau aka yita domin sai walwali take, bata da tudu bata da rami rami a mike take ziryan
A hankali suka hango wani gini mai tsayin gaske sai afkin camarori ta ko'ina, ga ginnin ba dai tsayi ba na andur ya dauki kalar gidin ruwan kasa lasho din
A dan firgice ta kale shi jin ya ce" Wace hanya zamu bi kuma? "
Karra kallonsa ta yi ta kuma maida dubanta wajen, a sanyaye ta nuna masa wajen muryarta na cracking ta ce" CiCiki zamu je "
Karra kallonta ya yi ya ce" Ciki kuma? Ta yaya ? Ina Baje dinki ne?"
Karra kura masa ido ta yi kamar yana mata yaren shainanci,
Hannayensa ya watsa ya ce" ai in aiki kike a ciki kina da baje dinki na shiga, idan ba haka ba ai kin san ba zaki shiga ba ko? Ina fatan dai ba gannin wani bane kika zo dan bafa sa bari a shiga"
Muneerath muryarta a sanyaye ainun ta ce" Yanzun sunna nan ciki? Da su din da masu basu horon harma da jiragen?"
Birki ya ja a lokacin da suka kusa isa yana kallonta, sai ya fara yi mata wani kallo daban domin tambayarta ta bashi mamaki ainun da kuma shaku a kan kwakwaluwarta, waye bai san makarantar nan ba? Waye kuma zai yi tambayar idan har mutanen da masu basu horon na nan ciki?
A hankali ya ce" Ina fata dai mai lafia na dauko ba ruwa biyu ba "
Sai a lokacin ta dan gane abinda ta fada din, dan haka sai ta sakar masa dan murmushi ta ce" Dan Allah mu zagayeta mana makarantar mu ganta da kyau?"
Fuskantarta ya yi da kyau ya ce" Yar budurwa, kin ga ko sunnanki ban sani ba, ni walahi kin yi min ne soyaya ce nake so mu yi da ke idan har ban takuraki ba, ina fatan kina fahimtar yarena?"
Murmushi abin ya bata dan a yadda ya yi maganar zaka gane ya fara tsorata ne da ita, hakan ya sa ta masa murmushi na kirki kafin ta ce" Ka san meye, na jima ne ina son gannin makarantar nan, shine yau na samu mai kawo ni, bayan shi ba komai fa, dan Allah ka zagaya da ni sai mu zauna mu yi zancen fahimta da junna"
Haka kawai ya ji ya yarda da ita dan haka ya kunna motar tasa ya tayar ya juya da ita a hankali sunna tafe tana kallon yannayin ginnin da irin camerar da ba'a yin doguwar tafia ba'a ga wata camerar ba
A hankali ta kurawa wani waje ido, ba komai ya sakata kurawa wajen ido ba sai gannin wannan wayar mai kayoyin tsini a jikinta ta nan ta dagu sosai, kuma an yi wani irin katari da irin abin ginnin nan irin mai hawa hawa waje waje haka
Kara kurawa wajen ido ta yi kafin ta ce" Dan tsaya a nan mu gani "
Tsayawar ya yi kuwa yana kallon inda take kallo, sai gani ya yi ta bude ta fita daga motar
Kara gyara zama ya yi yana bin bayanta da kallo a lokacin da ta juya ta nufi wajen katangar nan
Kara gyara zamansa ya yi da kyau irin ya samu abin kallo din nan, sannan yana gannin irin yadda take ta aune aunenta shi dai bai kawo komai a ransa ba sai a lokacin da ya ga ta dauko wani busashen ice dan dogo haka sannan ta nufi wajen abubuwan nan kamar matatakala
Dan kwalin kanta ta cire ta kara daure jakar dake bayanta a jikinta da kyau sannan ta kamo kasan rigar nata ta sakota ta tsakiya ta hade ta yarda cinyoyinta suka kusan bayana sosai ta daure su da kyau ta ci damara da shi sai ya yi kamar wandon indiyawan nan burkumeme
Kara zubawa kwaurinta da wajen cinyarta da ya bayana ido ya yi lokaci daya yana shafa wajen kansa a hankali ya ce" Ke ko mahaukaciya ce zan yi manage, sai na auri biyu tashi daya da mai hankali da mai kayan kwonciyar hankali"
Lokaci daya kuma ya shiga zarro idannuwansa sakamakon abin al'ajabin da idannuwansa suke gannin masa
Da sauri ya bude motar a tsorace ya ce" Ke baki da hankali ne? Baki san sojoji ke gadin gidan nan ba idan fa suka zo harbe ki zasu yi kamar barauniya, sannan baki san karafunnan nan sunna hade da wutar lantarki bane? Yana taba ki fa sai dai gawarki a nan ko bakya ji ne?" Ya karashe da taratsun ihu gannin bata kula shi ba kara hawa take
Bata kula shi ba da sauri ta kara kaimin hawan nata, wannan busashen icen ta saka ta shiga ture karfen nan, a firgice ta dan tsaya sakamakon kukan jiniyar da gaba daya wajen ya dauka sannan motocin da ta juya ta hango suka kara tsoratata, aman bata tunanin zata tsaya dan motocin nan da sauri ta karra ture shi sosai sannan ta haye saman katangar ta kuma juyowa tana kallon yadda dan saurayin buzun nan ke tafa hannu yana ta nuna masu yana magana aman cikin ikon Allah neman tsatsara shi da bindiga suke
Da sauri ta zarro idannuwanta gannin an tsare shin sannan wani rufcece ya durfafo inda take da yaren freinch tun karfi yake fadin" Tsaya a inda kike, ki sauko ko na harbe ki!"
Idannuwanta ta rintse cike da firgicin gannin kamar an zo kama gagarumin barawo ko za'a gabza yaki tsakanin yan boko haram da sojoji? Ihun da ake mata ya sakata rintse ido da baya baya ta juya ta shiga kokarin dirawa ta bayanta
Da wani irin karfi suka kuma kwala kiran ta sauko hakan ya sa ta saki garun gaba daya tana ambatar Allah a ranta ta tafi ba tare da tunanin zata dira da ranta ko a mace ba
Wani wahaltacen ihun ta saki a lokacin da ta ji wani irin abu shi ba wutar nepa ba shi ba wutar kiyama ba ya hade an jona mata a wajen wuyanta kiiiiiiiiii gaba dayanta karkarwa kafin ta zube kasa warwas tana wani irin abu tamkar ana jan wata jijiya a jikinta
Ribom din dake kanta ne ya kwonce gashin kanta ya bayana mai baki sosai da kuma tsayi lumbuk da shi , ta kasa kasa take bin manyan takalman sojojin da suke nan tsaitsaye da kallo gaba daya kwakwaluwarta take jin zata tarwatse mata , bata taba jin azaba irin wannan ba, bata taba jin muguwar azaba irin ta yau ba, ta rantse da Allah ta saki fitsari mai zafin gaske dan bata san abinda ke jiranta kennan ba
Bata shirya ba ta ji an kwasheta kiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii an saka a bayan motar nan sannan an kwace jakarta an saka abin detecten bom da dukan abu na cutarwa an tabatar babu a ciki sannan suka yi ciki da ita
Tafia suka yi mai nisa kafin suke isawa office din nasu na bincike
Kuma fitar da ita suka yi suka yi wani janta janta tafia tafia da ita suka kaita wani daki mai duhu suka jefata ciki suka rufo
Da sauro ta dukunkune kanta cikin cinyoyinta gaba daya jikinta na bari ta kasa katabus sai karkarwa take kamar zata mutu
A firgice ta dago kanta jin motso kamar a kusa da ita,
Shiru ta yi sai kuma ta ji muryar namiji yana fadin" Walahaula wala kuwata ila bilahi yau me na aikata na dauko mahaukaciya yau na mutu na lalace Annata batama san na dauko motarta ba, wayo Allahna"
Da sauri ta kai dubanta wajen duda duhun da dakin ya mamaye da shi , a hankali take ta ambaton sunnan Allah kafin da kyar ta ji wasu hawaye sunna fitowa ta cikin idannuwanta
Wani dan haske ne ya bayana mai ruwan blue, wanda mutanen dake tsaye gaban Computer kama tun daga shugaban makarantar , da shugaban masu bada tsaron, da shugaba mai kare hakkin yara, da mai kare hakkin mata, da dai sauransu suka zubawa Alon madubin da ya raba dakin da inda suke sannan sunna sauraron amon muryoyin dake tashi
Ido hudu Suka yi Muneerath da saurayin nan, da sauri ya ja baya cike da tsoron ganninta kafin da muryarsa sama sama ya ce" Ke wacece ke? Me na gaba maki da yau kika zabi shiga motata na kawo ki nan, cewa suke wai wa ya aiko ki dan girman Allah ki fada masu ni dai ban sanki ba a sakeni na tafi gidanmu wajen Annata"
Ya karashe yana hade hannayensa yana fashewa da kuka tamkar ba shine dazun ya dauko yar mutane cike da shakiyanci da mugun nufin son samun lagonta dan ya far mata
A tsorace itama take kallonsa kafin ta ce" Walahi walahi ni babu wanda ya turo ni, ka ga tun ina karamata burina na zama HOTTEST, ko a yau ni kaina ban yi tunanin zan shigo gidan nan, nama fa hakura da zama domin iyayena basu da halin biya min, kai ko kudin da zai kawoni nan ni bani da shi dan ka ce kana iya kawoni ne na biyoka muka zo, ashe haka gidan yake?"
Da karfi ya ce" Kin kuwa kashe mu, wayo Allahna na shiga uku to kin san baku da halin biyan uban me ya kawo mu nan din? Gashi yanzun banma san a me suka dauke mu ba!"
Kallon ogansu daya daga cikin masu bada tsaron ya yi ya ce" Oga wannan fa ina ga shirya abinsu suka yi, ka barni na shiga na jigata su ta yadda zasu yi bayani da kansu!"
Ogan nasu ya dan daga masa hannu yana kallon itin yadda suke maganar , a hankali ya kai dubansa wajen shugaban makarantar da ya tsura masu ido su dukansu ya ce" A jikinsu babu mai dauke da wani micro komai kankantarsa a kowani irin lungu ko sako na jikinsa dan mun duba, sannan ga takardun bayannan ko su su waye nan yanzun aka miko daga dakin bincike na computer bango, inaga da gaske ba turo su aka yi ba dan cutar da kowanmu, dan karrin bayani kuma muna iya zuwa cen gidan iyayen nasu su duka biyu, idan kuwa kun yarda da maganata ban ga wani abu mai duhu ba kawai a sake su "
Malamin Psychologist ne ya juyo da byro a hannunsa yana dan cicijewa ya ce" Ban karanci wani yannayi na munafurci a kallonsu ba, ga yadda computerna ta nuna min aman zan so na shiga koda na second goma ne na gansu gani ga su dan karrin yarda, aman koda ban shigan ba na yarda da irin abin nan da nake gani na computerna dan ban taba aiki da ita na ga ba haka ba, ana iya korarsu su tafiarsu"
Shugaban mai kare hakkin mata ce ta dauki magana tana fadin" Na tausaya mata, aman dan Allah ku bani jakarta ina son gannin meye a ciki ?"
Sai a lokacin suka dauko jakar suka budeta, baki daya abubuwan dake ciki suka zazago saman table din
Su dukansu ido suka zubawa kayan kafin su dauke takardun su raraba wa junnansu suka shiga karantawa dan gannin ko na meye? , takardunta ne kama tun daga na Entrer en 6eme, na Brevet dinta da na Bac dinta wanda yake hade da yar takardar dake nuna ko wace ita a bac dinma, takardunta na jarabawarta kaf sunna ciki, sai wani turare na fesawa sai litafi na rubutu kamar kwaya uku da byro kalar ja da blue, sai dala ashirin
Junnansu suke kallo gaba dayansu kafin ta kara gyara tsayuwarta ta tausasa muryarta ta ce" A wannan zamanin da wahala ka ga budurwa irin wannan ba ja gira ko jan baki da madubi harda su pant a cikin jakarta ba, tabas ni na yarda da kalaman yarinyar nan, ina kuma rokon oganmu da ya duba wannan lamari ya taimaketa ya saka hannu ya kai maganar ga gwamnatinmu mai adalci a zuba mata ta samu horo ta fito a cikakiyar ma'aikaciyar Hotteste "
Daya daga cikin sojojin ne ya dauki magana da dan zafi zafi ko kuwa dan muryarsa ce mai gautsi ko meye oho ya ce" Eh ban ki ba, kuma tana iya zama haka idan aka tsara ta zamo hakan, abinda nake nufi a nan shine ba zamu saki mu yi gangancin da zamu dauki wada zata cutar da y'ayan mutane ba, ku fa tuna irin yanda duniya ta rikice, lale yarinyar nan tana iya zama innocent mai tafe da buri na son zama hottest kamar yadda kuma take iya zama makashiyar dake da burin kashe mutane da kanta"
Mai kula da yannayin yan matan wajen, watau mai tsaban tsarin halita, tsarin fata, tsarin yannayin jiki da irin gogewar mutun ta sha sket dinta damame fuskarta dauke da farin gilas na gayu ta sha madaidaicin jan bakinta ta ce" Bama wannan ba, in ba shirme irin nata ba a Niger kasa mai dauke da buzaye, filani, kyawawan hausawa , kyawawan yan mata na kabilu daban daban ne zata saka irin wannan ra'ayi a ranta? Ta kuwa san menene girman kalar da ake so a hotteste? , Bakinta ya min yawa sannan bani da tabacin idan kaf jikinta ne haka, hausarta wata gatse gatse ban ji ko kadan ta sako turanci tsaftatace ba, eh lalle takardarta ta nuna tana da ilimi aman ai ba shi zai tabatar min ba sai idan na gani a aikace, duwawunta sun yi girma da yawa mu da bama daukan masu katuna katunan duwawu?, idannuwanta sun wani lumseh sosai ta haka zata ringa yiwa pasinga magana? So kuke a fara samun matsala ne da zaki ce a duba lamarinta ? Bayan an rufe dauka kuma yanzun ita aka dauketa yaya zamu yi da iyayen yaren manyanmu da suka kawo muka kiya?"
Da sauri mai kare hakkin yara ya dauki magana ya ce" ina da magana, ni kuwa mai zai hanna a duba irin yadda take da motivation? Ku juya ku gani har yanzu kuka take tana kuma jadada masa , idan har ta samu aiki irinsu ne masu aiki da zuciya daya, ya dace a ringa duba yayan talakawa, da yaran da suke da burin aman ana dane masu dan son zuciyar iyayensu"
Dukan wannan tataunawa sa suke shugaban makarantar matashin datijo dan ba zai fi shekara arba'in ba mahaukacin iliminsa ne ya kawo shi matsayin da yake kai yanzu yana tsaye ne yana bin kowa da kallo sannan yana marantar dukan abinda suke fada, a wannan makaranta a nan dukan wani shugaban kare kare da rikice rikice yake , hakan ya sa basa daukan decision kai tsaye sai a jima ana rigima a kan abu
Sai da wajen ya nemi rikicewa kafin ya yi gyaran murya da takardun da aka yi bayanin ita din wacece da makarantar da ta yi ya ce" Takardunta sun nuna shaidar ita din yar kasa ce, haifafiyar kasa kuma girman kasa, da farko dai dukan bayanan takarda ba su kadai ke gamsar da ni ba, dole zan baza yara kasa a min bincike a kanta, idan ta fita ina take zuwa? Me take yi? Da su wa take? A bincikar min malamanta na makaranta, a duba min gidansu yar ciki ce ko sunnan tana haifafiyar gidan ce? Ina nufin barci ke kawota ita din ko kuwa sai ta yi kwanaki bata ciki?, koda ta kama sakin nata ta koma gidansu ne sai mun yi hakan"
Dan jim ya yi ya kuma kallonsu baki dayansu ya tsaida dubansa a kan mai zaben yannayi da sauransu ya ce" Da ace abubuwan da kika zana za'a bi kafin a dauki mutun da wannan wajen bai dace da ke ba domin kina kan dogon takalmima tsayinki bai fi 1m 60 ba"
Ya maida kan wanda ke maganar a koreta ya ce" Da taka ce zaka fadi haka? Ko ka san naka da suka fito a yanzun me suke aikatawa a cikin gari?"
Sai kuma ya ja gabansu gaba dayansu ya ce" Muna haihuwarsu ne mu zubar, idan na ce mu zubar ina nufin ba mu ke binsu waje dan gannin me suke aikatawa ba, su din sunna tashi da burikansu, da yawansu sukan dauki hanyar lalacewa dan neman samun cikar burinsu, shin idan muka dubi lamarin daya cikin dubu muka tsamo muka talafa matsala ne? Maganar nan zata iya mutuwa a tsakaninmu na sai ta hau sama ba domin mu ke basu horo mu ke kaisu kampani ya zaba, idan har ita din ta cencenci zama hotteste abin a talafa mata ne ta zama ba mu koreta ba!"
Ya dora da fadin" Ku kun san menene aikinmu, shin wannan ta iya ruwa? Idan bata iya ba ba mu zamu koya mata ba!, shin ta iya Inglish kamar ruwa? Idan a takardarta satar amsa ta samu ta rubuta ta cuci kanta dan koda mun zauna a nutse mun baiwa kanmu amsar riketa mu talafeta dan talafawa yara su zamo wani abu ya kasance bata iya ba dole zamu saki hannun junna, Aikin Hotteste ba aikin direban mota bane ko kwondastan mota ba, sai ka zauna a table ka kuma kawo sakamakon jarabawa koda zaka samu ci!"
Karra dubansu ya yi da kyau ya ce" Ba zamu koreta ba, ba kuma zamu riketa ba"
Shugaban mai bada tsaron da kwarai ya ji dadin hakan a ransa a bayane ya ce" Yaya zamu yi da ita kennan sir?:
........sorry yan uwa馃槃
11/14/21, 12:44 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
1锔忊儯2锔忊儯
Wajen madubin ya kai dubansa, ba komai yake gani ba sai jaruma, ba komai idannuwansa ke gane masa ba sai mai baban mafarkin rayuwar dake shirin rushewa, ba kowa yake gani ba sai yar yarinyar dake neman zama wani abu da karfin zuciyarta bayan tana da abubuwan da take iya zuwa ta banzatar dan samun kudaden aman ta ki yi sai ta fi kaunar ta rufe ta nemi na kanta, kwarai ya yarda da kalamanta bayan a yanzun mutun ba abin yarda bane, haka kawai yake gannin darajarta bayan baima san ko wacece ita din ba! , hannunsa ya dora saman madubin yana kara jin magangannunsu ita da buzun nan da ya gama fahimtar yanzu suka san junna yana ji a ransa idan suka katse mata tafiarta sun shiga hakkinta, yana ji a kasan zuciyarsa dukan yaran matasa masu tsaye a kan burinsu na alkhairi kamarta basu cencenci a katse masu shi ba, idan da halin a kama masu za'a iya kama masu ne, a yadda yake tsayen ya gama hasaso mutanen da suke aiki da su wa'inda yake sama da su aman kuma suke da damar dole sai an shawarci junna dan aiki ya je a tsare ba tare da tangarda ba
A cikinsun wace ta fi zama da Hotteste din ta nuna rashin amincewarta da hakkan,
Sai dai kamar yadda ya kasance mai talafi da jajircewa ba zai saki hannun yarinyar nan ba, dan ya tabata da wani wanda ya daure mata gareta da shi zai kawota su shigo ta babar kofa sunna takama da daga kai ko dan iliminta da kuma kudinsu su zo su nuna ko dan dukiyarsu a dauki yarsu, da yawansu idan ba'a dauki y'ayan nasu ba sukan nuna mune da asara ba su bafa馃し馃徎鈥嶁檧锔 , aman a wannan yarinyar sai yake gannin ba haka ba
Juyowa ya yi ya harde hannayensa , sai da ya dauko yannayinsa na jajirtacen matashin saurayi ko nace matashin datijo ya ce" Kamar yadda nace da ku da farko zamu tabatar da magangannunsu, sai option ta gaba zamu hada conseil, a cen zamu gabatar da matsalar wa syndicat, sannan zamu yi Vote! Wa'inda suka fi yawa a kan *A KORETA* ba zata karra koda second daya a gidan nan ba zamu sakata a mota a maida ita gidansu, wa'inda kuwa suka fi yawa a *BARINTA* ta zama HOTTESTE a tare da mu zamu karbeta da hannu bibiyu mu hadu mu bata horo ba hantara, ba kyara, ba zagi, ba cin zarafin halitarta, ba komai na wulakanci har ta fito a matsayin Hotteste horon kampaninmu, na tabata komai muninta ba zata rasa kampanin Jirgin da zai dauketa ba!"
Dan kus kus kus ne ya dan tashi kasa kasa kafin du su bada amanarsu duda ita mai alhakin daukan yannayin mutun din ta gama daukan hakan a wani abin daban dan ita gani take zagayeta zai yi da wuya ta iya kayar da shi, aman duda haka itam zata gwada nata chanc din dan gannin ba'a dauki yarinyar nan ba, ita kawai bata yi mata bane! (Rayuwa kennan, ba mai ba in baka nan, rayuwar kennan ka hadu da mutun yau bai taka maka ba, bai kashe maka ba aman sai ka ji ka tsane shi iya tsana kamar zaka kashe shi dan jin haushinsa.....Allah ka sa mu ki mutun domin ka, sannan mu so shi domin ka)
.....................wannan kennan
Murginawa ya yi daga kwoncen da yake a bed din dakin hotel din da ya sauka a Europe
Dakin yana bada wani dumi mai dadin gaske wanda du wanda ya fito daga waje cikin kakausan sanyin mai ratsa kashi mai saka bawa ya yi kiskirim ya kamo wata tashar bayan ba abinda yake tunani sanyin ke neman kasara tunaninsa dan tsabar karfi idan ya samu wannan dumi na dakin da yake kwonce inaga kafin ya fito sai an hada da motar yan sanda a ciro shi da karfin tsiya
Dan dakin ya samu chaufage watau na'ura mai dumama daki da dumi, ga kuma wutar garwashin rushi mai zafin gaske da aka hura ake kuma kulawa da kara masa gawayin marar kauri da kama daki a kai a kai, ga sanyayen kanshin turaran ruwan da na'urar watso kanshi ke watsowa a hankali ba da yawa ba tana jone tana aikinta wanda shine ya gama dakin ya kasance zaman dakin ba zai gunduri wanda ke cikinsa ba
Dan Blutouphe din dake kunnensa na iPhone original fari ne ya dan haska haske blue mai haske halan ke nuni da dayan biyu ko yana sauraron wani abu daga cikin wayarsa ko waya ce yake yi, aman irin shirun da ya yi yawa sosai din nan ya saka ni tunanin ba waya ce yake yi ba, domin waya a garin nan tsadar balaki ne da ita koda a cikin garin zaka yi in dai ba irin wayar cikin gida bace watau ta jikin bango ko ta ajiye telephone, sai ko idan whatsup ne, idan kao tsaye ne ba zaka iya jimawar nan haka ba zaka kashe ko kudin wayar taka ta katse kanta ba
A hankali ya yi dan murmushi ya mika hannunsa ya dauko byro da Bloc note din gefen bed din ya bude a hankalo ya shiga rubuta adu'ar da take karanto masa cikin harshenta na jinnin larabawa da nutsuwarta ta nutsatsiya, da kauna irin ta uwa a gareshi kafin ya budi baki cen kasa kasa ya ce" Mah, na rubuta ki kwonta ki huta plz dare fa ya yi a wajenku "
Kamar jira take ta ji ya mata magana sai ta ji wata hamma ta zo mata, a nutse ta rufe bakinta ta yi tana adu'a kasa kasa
Murmushi ya yi dan sarai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 42