ne idan ba sama ya daga kansa ko ya kai dubansa waje da zai nuna masa cewar dare ne
Yana fitowa daure da tawul kadai a kugunsa ya nufi wajen da suturarsa take,
Iya gajeran wando ne ya saka kafin ya muke tsaye yana lumshe idannuwansa ya kai dubansa wajen agogon dakin dake kafe
Kuma lumshe idannuwansa ya yi ya dauko wata jalabiya fara ya saka kafin ya nufi wajen da yake kebance a cikin wannan tankamemen falon ya mayar da gabansa gabas ya tayar da sallah
Kwarai na yi mamakin ganninsa yana sallah, a irin wannan gari a yannayin halitarsa, irin shigarsa, irin yadda yan mata suka shige gidansa wa'inda na kasa gane mene dinsa ne, wace ya yiwa magana irin shigarta, kai lamarin da yawa, sai dai a irin yadda ya gabatar da ibadarsa ya tabatar min cewa idan ya tsinci kansa gaban mahalincinsa bashi da wani abin daban a gabansa sai shi, ya dukufa ya gabatar da sallarsa kafin ya yi adu'o'i sosai ya shafa ya kuma mikewa ya cire wannan jalabiyar ya mayar da ita wajenta
Ido nake rinrintsewa, kai shi haka yake ne? Wane Wardugu (Na cikin Bak'a ce) a kirar diraran jiki, ginanen jiki, mai sanka sanka, shin karfe yake dagawa ko menene?
Saman lalausar shinfidarsa ya haye a hankali ya lalubo commande biyu dayan fari dan karami dayan kuwa bak'i
Daga kwomcen da yake ya gyara kwonciyarsa da kyau ya kara gudun AC sannan ya danna na labule suka rufe kansu su dukansu kafin ya karra rike bargon nan a jikinsa yana lumshe idannuwansa kasan zuciyarsa yana adu'a dan samun barci cikin tsari da amincin Allah
Saman ta cira ta haye kusa da kafafuwansa ta kwonta saman lalausan bargon wutsiyarta cen gefe kanta ta kai ta shigemar da shi wajen kirjinta ta kwontar da kyau itama ta shiga neman barcin hankali kwonce
A kalla ya yi barcin kusan awa biyar kafin ya ringa jin yadda take ta goga masa gashin wuyanta da ta karra buda shi sosai tana ta son juyo da shi tana ta cinninsa kan dole sai ya tashi
Manyan idannuwansa ya dan buda da mayen barci da jan da suke dauke da shi ya juya a hankali a kasan makoshinsa kuwa cike yake da jin haushin yannayin jikinsa a cikin ransa fadin yake"Ya rab, yanzun kuma ina zan samu mace?"
Dan tsaki ya ja a dan bayane, ita kuwa zakayar nan sam ta ki ta barshi sai kara cinashi take kan sai ya tashi domin gari ya waye ita yinwa take ji, shima haka
Mikewa ya yi ya kuma nufar bayi dan yin wani wankan
Sai da ya kimtsa jikinsa tsaf sannan ya fito ya yi gaba tana biye da shi
Sai da suka zo wajen cin abincinsa ya zauna kanna ta juya ta shige gaban mai ciyar da ita suka fita suka yi bangaren cin abincin da manyan cinyoyi na manyan saniyoyi ke jiranta ta shiga dandatsa
Sai da ya ga tafiarta kafin ya mike da sauri da goran madarar nonon saniya da aka yi masa sabon tatsa aka tace shi sosai ya nufi PALAS watau baban GIDAN SARAUTAR dake ake kira da BUCKINGHAM
A nutse yake tafia bayan sun karaso doguwar tafiar yana duba time din sallah gannin da saura sosai sai kawai ya yi kwana ya karasa wajen da ya tabata ba zai rasa wace ta kawo kanta dan hakan ba
Yan mata uku ya tarar a bangarensa dake cikin gidan wanda yake malakinsa, wa'inda idan zai rantse ba zai yi kafara ba dayar a kadan ta yi sati a wajen tana jiransa, biyun ne dai bai san yaushe suka zo ba
Ido hudu suka yi da junna gaba dayansu kafin ya cire dubansa ya ja ya tsaya yana dan kare masu kallo a fakaice
Kai da ba dan abu daya ba da ya hadda su ukun nan ko kishirwarsa zata mutu, da yawan lokuta yakan ji haushin aikinsa ne ba dan komai ba sai dan irin jarabar nan da suke fama da ita, shin ina dalili? Dan kawai kana Pilot kamar a kanka aka halici Jaraba?
Bai ce da su komai ba ya wuce ya shige baban dakin da a nan yake baje kolinsa da ire irensu, dakin da ko sallah baya yi a ciki
Umarni ya ba yaron dake biye da shi kan a shigo masa da daya a cikinsu sauran su tafi, dayar kuwa ya bada yannayinta domin Allah yana gani shi ko sunnanta bashi da shi
A lokacin da ta shigo a zaune yake bakin gadon, da idonsa yake biye da ita da kallo har ta gama tube dukan wani abu mai sunna sutura a jikinta kafin ta shiga jujuya jikinta tana son lalle sai ta birge shi har ya amsa gayatar da take masa
Idannuwansa ya lumshe, domin ya amsa, ya fa amsa a yanzun yana iya sukuwa har tsakiyar dare danma kar ya ce har gobe i warhaka ne ya yi karya?
Yana kokarin saka hannunsa dan ya janyota gaba dayanta jikinsa ya mata tashi daya ta yarda idan ya mata murza daya sai ta ji ba zata iya kaiwa gobe ba ya ji an turo kofar an shigo da yannayi kamar da dan bacin rai
Da sauri ta juya kafin da gudu ta fada saman gadon tana son janyo abu ta dan kare gabanta domin shi kadai ne abin rufewar a jikinta
Irin kallon da take binta da shi ya sakata jin kamar fitsari zai sako mata dan haka da gudu ta mike a yadda take din ta fice a dakin gaba daya
Kansa kasa yake kallo, bai iya dagowa ya kaleta ba, ba dan komai na sai dan ita din mai daraja ce a duniyarsa, kuma yana matukar jin kunyar ita da kanta ta kama shi a irin wannan hali, aman me yasa ta shigo kanta tsaye dakinsa da yanzun sunna harkar nan ta same su fa?
Muryarta a sanyaye ta ce" Khalb?"
Kansa ya kasa dagowa ya kaleta dan jin kunya
11/14/21, 12:43 PM - Allah Akbar: 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
5锔忊儯
A hankali ta karasa inda yake zaune, lalausar alkyabar dake jikinta ta Veloor mai ruwan baki da duwatsu farare kal kal kal ce ta jata sosai a jikinta ta gyara ta zauna tana kara kallon lalausan gashin jikinsa kafin ta saka hannayenta ta janyo shi jikinta sosai ta dora kansa saman cinyarta
Gashin kansa take ta shafawa a hankali kafin ta ci gaba da fadin" Haramun ne aikata zina, Allah ya yi alkawarin azaba ga mazinaci idan bai tuna ya daina ba, ina matukar mamakin kasarku da ake yinta a bayane, harma gidanku gida mai daraja, shin baku da kyankyami ne?"
Idannuwansa dake lumshe kamar ba zai taba buda bakinsa ya yi magana ba da kyar ya iya budawar a sanyaye ya ce" Me na yi?"
Ajiyar zuciya ta sauke cike da kwarin gwuiwar son gannin ya cenza ya dawo mutun sak irin na kowa ta ce" Abinda na tarar da kai kana shirin yi"
Lebensa na kasa ya cije a hankali ya ce" Khalb, i'm sorry to say ts aman yaya zan yi ne? Aikina ne "
Muryarta still a nutse ta ce" Aikin da ba kowa ne yake sonka da shi ba? Wai yanzu du darajarka ka gwamace ka je ka yiwa wasu karti aiki? Kai fa Allah ya haliceka ne da darajarka , HANJA kana kwonce sai a yi maka komai, ka bar aikin nan ka yi aure ka dauki lamarin sarautar dake rataye a wuyanka"
Idannuwansa yake lumshewa ya mata shiru bai bata amsa ba hakan ya sa ta dora da fadin" Zina mugun aiki ce , mai cinye alkhairi, Zina na hanna sukuni tana saka bakin fuska komai hasken mutun, zina na bin dangi , idan ka yi da y'ar wani sai an yi da taka, idan da matar wani ne za'a yi da taka, aya ce, shin yaya zaka yi da ranka idan ka wayi gari ka ga ya faru da matarka?"
Still idannuwansa a lumshe suke cen kasan makoshinsa ya ce" Khalb, idan ta zabi bin wasu bayan gani ba shikenan ba ai yancinta ne sai ta je ta yi dan kanta"
A dan rikice ta ce" Baka da kishi ne? "
Kansa ya dago yana kallonta, a hankali ya saki dan lebensa da ya cije a sanyaye ya ce" Ta ina ake jinsa? Ni na kasa ganewa, kin ga fa kika ce idan na yi budurwar da nake so na ganta da wani nan dina za yana min zafi na ji kamar zan kama da wuta dan azaba, ai nan na zo na ce maki na kama su Rozario a hotel sunna hvng sex aman ni komai ban ji ba, da ta bani hakurima nu mantawa na yi sai dai na bara masu soyayarsu ita da shi dan na ga ya fini sonta ko? To wai ko dai ana haihuwar mutun ba kishi ne? KHALb ni ban ga abin damuwa a irin abin nan ba, abu ne na ra'ayi, ka yi da wace ya kama ka ji kana ra'ayin, kuma ni ban taba zuwa na kwata ba, su suke zuwa sunna rawar jiki su kawo min, sannan maganar aure ni yanzun idan na ce zan yi aure har ba zaki hanna ba? Kin fa san meye yake jira, jira yake na ce ai zan yi aure ya nemi sakani a harkar sarautarsa, ba zan iya ba, na fada maku idan har na zauna to fa babu jirgi a duniya!"
Shirun da ta yi a hankali tana ta shafa gashin kansa dan ta ga ya fara caza ne ya saka shi kara komawa a hankali ya kara kwontar da kan nasa kafin ya ringa sauke ajiyar zuciya wata na korar wata har yana jin makogwaronsa na masa zafi dan maganar da ya zuba mata
Bata karaya ba a sanyaye ta ce" Sai na ji tsoro na kama min zuciya, sai na ji kamar zan fashe da kuka, ka kuwa san meye rashin kishi? Du namijin da baya kishin iyalinsa ba zai shiga aljana ba, Khalb me yake damunka ne? Ko dai a gaba ka san shi ainahin kishin kansa ne?
A hankali ya ce" Kamar yaya?"
Itama a hankalin ta ce" Ina nufin a gaba ka samu wace zaka yi kishinta "
Da dan murmushi ya dago gaba dayansa ya mike tsaye kafin ya dan rankwafo a hankali ya rike hannunta na dama ya manawa bayansa kisss a sanyaye ya ce" Na kula yau horon da kika yi niyar bani shine hadani da ciwon kai, zan he office now plz ki ce masa na yi tafia kin ji? "
Yana gama fada ya juya ya yi gaba ita kuwa ta raka shi da kallo kafin ta dan dafe habarta ta yi wani yannayi na tagumi a hankali ta ce" Ya Allah, ka karra jadada rahama ga abokiyar zamana mahaifiyar yaron nan, ka shiryar min da shi"
Mikewa ta yi ta gyara gadonsa da kanta ta dauke rigar da yarinyar ta cire tana girgiza kanta cike da jin tausayi da kuma haushin tarbiyar yarenmu, shin ina zamu je? Ta sani a wajenta wannan ba wani abu bane domin ba musulma bace ita yarinyar, aman duda haka shin ina akida?
Jikinta dai a sanyaye ta fito nan aka amshi abin hannunta ana rike da kayanta suka juya suka shiga watsetsiyar motar da ta kawota nan din suka kama hanyar baban bangarenta
A lokacin da ta fito bayan an bude mata ana ta gyara mata hanyar wucewarta suka yi ido hudu da kanwar tata
A kasan zuciyarta take ayana.....' Lalle ita kanta zata so gannin yarinyar da zara motsa zuciyar yaronta, wace kala ce bata kawo bukatarta da harinta ba, farar ce, yelow din ce, fararenma irin mai dau din nan ba wai sama sama ba, kai ba'a maganar kyan aman cikin ikon Allah cikin biyu ne ki zabi daya ko ku ga walen junna ko ki kama gabanki ba abinda ya dada shi da kas, shin wacece? A ina take? An halitota ko a gaba?.......'
................................................
"Kwana biyun nan kina cikin yannayi na rashin karfin jiki Muneerath, me yake damunki ne dan Allah? Kin ki ki fada min gashi ana ganninki za'a gane cewar kina cikin damuwa, me yasa kike da zurfin ciki mai tsanani a gareni? Ko kamar yadda kika saba ce min ba zaki taba fada min abinda ya shafi cikin gidankun bane?" Amina ta karasa fadi tana kallon Muneerath
Murmushi mai ciwo Muneerath ta yi tana kallonta ta ce" Ba zaki gane bane Amina, ina cikin tsaka mai wuya, na tambayo nawa ake koyar da iya ruwa na garin nan an ce du awa daya jaka uku, Amina idan na ce zan saka kaina a wannan sha'ani ai sai a yi tunanin ko na fara rashin jin magana ne, waye zai bani kudin nan? Ta ina zan samu na cika burina?"
Amina ta zauna kusa da ita itama jikin nata ya yi sanyi sosai da wannan lamari na kawar tata, dunia na fadar abubuwa a kan gidan nasu, ana fadar lamari marar dadi, fadi ake ko a wajen cin abinci kowa ta kansa yake yi, ana fada cewa komai na gidansu tamkar na mutanen da kowa ke ikon kansa, irin gidan yan barikin nan, gida ne da iyayen kansu basu da tarbiya bale y'ayan, aman ita sam bata yarda da wannan magangannun ba domin kawar tata ko kudi ta bata bata amsa, ko wajen cin abinci idan ta zo gidansu in sukai mata tayi bata ci kiri kiri take nuna ta ci a gida, bale a rayuwarta ta ki jinnin ta yi hirar gidansu, mugun zurfin cikinta baya iya barinta ta budi baki ta yi bayanin damuwarta, wani lokacin haka kawai zaka ga ta fashe da kuka mai tsanani idan an taru anai mata tambayar lafia? Sai ta ce mutuwa ta tuna, daga haka kuma waye zai ce wani abu? Mutuwa ai ta isa idan aka tunata a yi kuka ga mai tunanin makomarsa
A sanyaye ta ce" Me yasa irin naki ra'ayiyikan suka kasance masu tsauri ne? Me yasa idan Allah ya cida mu muka samu bac din nan mu je mu karanci fannin likitanci ko fannin koyarwa ko abubuwa da yawa gasunan wa'inda mun tabata koda iyayenmu basu da karfin talafa mana idan muna karatu a Niger zamu kai ga ci har mu zama wasu gobe? MUNEERATH ni bana hangowa mace musulma mai tunanin yin aure da haihuwa a kusa yin irin aikin nan, bama wannan ba ki duba fa ki gani ko a y'ayan masu kudin da suka samu damar shiga makarantar nan sai masu gagarumin ilimi da kuma tsari kamar an zana su, Muneerath ba raina halitar da Allah ya maki ko nasabarki na yi ba, ko daya matakan da ya dace a taka a hau a kai wajen da kike so din nan ne ya fi karfinmu nesa ba kusa ba, waye zai tsaya maki? Ta ina zaki samu shiga makarantar da ko ka shiga ba yana nufin ka samu bane aa yana nufin ka je ka sha gwagwarmaya ne idan da rabonka ka wuce idan babu kima ka bata shekaru ka dawo gida?"
Muneerah ta mike daga zaunen da take tana kade sket din dake jikinta mai ruwan blue budade da ta siya a wajen gumama ta ce" Amina, zan je na ci gaba da fadawa Allah, zai tsaya min, na tabata alkhairi ne domin du idan na yi sallah fada masa nake idan ba alkhairi bane ya cire min a raina, aman kasancewar kulun karuwa yake a cikin ran nawa inaga idan na zauna na zuba ido zan kasance cikin masu fada nan gaba ina karkata kai cewar a da fa burina shine na zamo hottest, idan akai min tambayar shin yaya aka yi ban zama ba, cike da mutuwar zuciya sai na tabatarwa wanda ya tambayenin cewa dan ya fi karfina banma kwatanta ba!, na fi son na fadi cewa ban zama bane dan haka Allah ya hukunta domin na gwada dukan damata Allah ne bai yi ba"
Cike da tausayi Amina ta rakata da kallo har ta yi gaba
Shigar Muneerah ba shiga bace ta y'ayan masu kudi, domin a jikinta riga ce bak'a ta gwonjo da blue din sket shima na gwonjo wa'inda ta siya da kudinta abinta, sai blue din mayafi tamkar matacin koko da ta yane kan nata da ita, sai jakar tata ta gado ta zuwa makaranta wace bata rabo da ita koda yaushe tana bayanta
A sanyaye take tafiarta a yauma domin bata da kuzari ko daya baki daya tunanin yarda zata fitowa matsalarta ta gama cike mata kwakwaluwarta,
Sam bata ji tsayuwar motarsa a gefenta ba sai kalmar Dogari da ta sakata juyowa tana kallonsa a sanyaye
Sani dake tsaye jikin motarsa, matashin saurayi mai jinni a jika mai nema da karfinsa dan kasuwa ne ginane sannan dan bayan layin su Muneerath ne, kuma a da kawance suke na kud da kud da junnansu aman daga bakin lokacin da ya nuna shin zata iya aurensa? Ta nuna masa aa, ita kawancensu shine ya sa take kula shi ai ya san wa take so dan Allah kar ya kawo mata wannan maganar, shi kuwa Sani a duniyarsa yana son macen da bata bleating, irin rayuwar da Muneerath ke fuskanta a gidansu bai dame shi ba, ai lowani gida da nasu irin kwamacalar, gwara su ba a munafurce suke rayuwar ba, a bayane take ita cema bata son a yi maganar gidansu shima kuma ba dan tana karyata rayuwarsu ba, Muneerath ta masa gaba da baya da zata lamunce masa da ya je gidansu ya yi birgimar ko a aura masa ita ko ya fasa fita kasuwa, kasancewar shine ci da shan gidan baya tunanin zasu yi saken ya ajiye nema ah tam
Dan murmushi ta sakar masa a hankali ta karasa inda yake tsaye ta ce" Lah, Sanini ban ganka ba, daga ina haka? Ina yini ya kasuwa "
Murmushin ya mata shima yana fadin" Alh Muneerana, daga kasuwa nake zan koma gida nake kiran Munee, munee shiru sai da na ce ta Dogari, hop kina lafia yaya dogari?"
Dan sakai ta yi da bakinta kafin ta watsa hannunta a sanyaye ta ce" Nima ban san yaya yake ba "
Sani ya dan zarro ido ya ce" Ba dai har yanzu baku hade ba?"
Kanta ta dan sada cike da jin ciwo a zuciyarta , sai kuma ta watsar tana zagayawa gefen daya ta bude motar ta shige gaba tana fadin" Oya direban Munee karasani gida mana "
Daria ya yi cike da jin dadin da alamu zata dawo masa irin na da yarda suke zumuncinsu ba wani kwane kwane ya shiga motar yana fadin" Daga nan har wucin gari zan kai Muneerar dogari"
A lokacin da ta shiga gidansu dai yannayi ne irin na kulun, da alamu kuma tsohon gidan na nan dan kuwa yawancin zaman nan da suke na yama kowa a wajensa yana tsula mai gyara shi idan uban gidan na falon ne, ba wai dan su bashi waje ya huta ba fa suke haka, no iyayen kowane ke koro shi waje da dan cin hanci dan ya samu zama kusa sa ogan gidan ba dan tana ranar girkinsa ba, aa , dan kawai a samu na fafatawa a tashi a yi ta masifa har makota na samun jifan marfin kwano
Bata yiwa kowa magana ba, duda wasu cikin yayunta yan matan sunna kugin kiranta da *Ta Dogari* da sigar neman fada dan ta biye masu a yi masifa, aman sai ta share kowa abinta ta yi shigewarta ciki dan a yau so take su zanta da shi mai gidan, tana son su dan tatauna ko yayane
Da salamarta ta shiga a bakinta, sai dai abin haushin daga matan har mijin ido suka dago suka zuba mata an rasa mai amsa mata salamar da ta nemar masu amincin Allah ya tabata a gare su cikake
Bakinta ta dan yatsina tana kallonsu kafin ta karasa kanta tsaye ta shiga ta zauna a gabansu baki dayansu hakan ya sa suka yiwa junnansu kallon kallo ciki kuwa har abokan zaman majaifiyarta suka kamu da jin dadin ga ta inda zasu jata fada ya fado masu a banza
Ido hudu suka kuma yi da mahaifinta kafin ya dan yi murmushi yana kada kansa ya ce" Ruky, duba ki gane min kyankyasata, in ba dan ni kaina ina tsoron kwakwaluwar muneerath ba ai da na ce na samu jari, kin san fa akoy mazan da dan sakarci su kawai bak'sr mace ta masu a rayuwa, wai har fadi suke su idan suka samu bak'a a wannan zamanin da bata shafe shafe ko nawa zasu batar dan ita basu da bakin cikin hakan, kuma fa manyan masu kudi fa, sai na yi mamaki sosai har na ringa tunanin su kuwa ko magaya ne basu da shi?"
Ya karashe yana dauko wayarsa lokacin da matarsa Ta budi bakinta irin da yannayin kisar nan ta ce" Shine ai boss abin ke damuna, ka ga yarinyar nan mace har mace, eh lale bakinta ya yi yawa sosai aman duba ka ga kafma a cikin yaren wa ya yi fitowar gashinta da kirarta?, aman ka ga a banza tunda ba zamu anfana da shi ba, y'a kamar wace aka zara a cikin taran?, duba ka ga tana tafe tana mafarkin dogari...." ta karashe tana kilkilewa da daria
Dayarma ta ce" Ni du ba wannan ba, du kyan bakin mutun ai ba abin yabawa bane da zaka yaba kyanta, kuma tun kyanta ai a banza tunda a bayane take Muneerath mahaukaciya ce"
Mahaifiyarta dake zaune cikin shiga ta atampa an mata wani shegen dinkin da ko y'ar a yanzu da wahala ta saka irin rigar nan haka ta fita da ita tana dan gyara farcenta tana kallon kowa tana girgiza kafarta daya dake saman dayar tana kallonsu bata ce kun ci kanku ba, domin ita a yau ta yi niyar sai ta caji oga ba zata kula ko wani shege ba
Zamanta ta gyara a sanyaye ta ce" Baba, dan Allah wajenka na zo ina son ganawa da kai"
Wayar da yake dannawa ya dakatar yana kallonta , sai kuma ya ce" Ba dai a kan maganar Dogari da kuma son zama Hottest bane? "
Sai da ta hadiyi yawu marar dadi da jin ciwon irin yadda suka dauketa kafin ta lumshe idannuwanta a hankali ta gyada kanta a lokacin da ta samu wata idea ta gyara zamanta ta ce" Ba su bane, ina so ne ka bani kudi ko yayane na nema na karra na je na shiga clob din da ake koya ruwa, ina son na iya ruwa"
Wannan karron mamanta ce ta ce "TO FAH" tana kallonta
Lishiyar mamanta ta fashe da daria tana fadin" Yau mun yi abin kanmu mun karra kankaro wulakanci mun samu buri na uku, sai yar Oga naki salon daban ne"
Muneerath da ta tsare shi da ido ba irin adu'ar da bata janyowa tana kallonsa tana tofe shi a kasan zuciyarta, ita bata iya karya ba da ta yi masa dan ya bata yan cenji, yana basu kudi fa ba baya basu ba matsalarsa ba zai yi asarar kudin makaranta ba a cewarsa dan ya tabata ba karatun zasu yi ba wai basu da takaici
Da daidaya ya ringa bin matan da kallo kafin ya ce" Ni ina mamakin matan gidan nan, yanzu da kuka tsatsaremu da y'ata ta kawo magana mai mahinmanci na farko a rayuwarta so kuke na zageta ko me? Kai ban taba gannin yan bakin ciki irinku ba, ai ni abin alfaharina ne a ce daya cikinsu ta iya ruwa, baki ga wani abokinmu da dansa ya iya ruwa ba yadda motsi kadan zai ce wane ya ciyo gasar kaza a gari kaza dan tsabar kwarewa, dama haushinsa nake ji idan yana irin maganar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 42