da su cewar idan sun shiga su tabatar bayan yin wanka sun daura alwallah, sannan kar hira ta shagaltar da su har su cika dare dan kar su kasa tashi sallar asuba a kan kari, sannan kar su manta da adu'a kafin su yi barci
Har sun kama hanyar tafia Mah ta bukaci kan Muneerath ta bata wayarta zata yi wani abin da ita
Ai kuwa da murnarta ta bata suka yi tafiyarsu ba tare da tunanin komai ba
A wannan daren bayan Mah ta gama kula da mijinta wanda tafiyar gagawa ta taso masa du yadda ya so ya kaucewa tafiyar hakan bai yiwu ba aman sai ya nemi alfarma a wajen matarsa kan ta boyewa Hanja domin ya tabata idan ya sani zai fito kai tsaye ya hanna ne,
Ita din da kanta ta samu kanta da yarje masa ba fan komai ba sai dan tana matukar jin dadin irin yadda yake dan haba haba da jikinsa da lokacinsa bayan a da ya zubar da komai maganar fatar bakinsa daya biyu zancen mutuwarsa ne, duda ta san haka din abu ne mai kyau dukan musulmi ya kasance ya rayu da sannin yana iya mika ran aro a kowani lokaci, a kowani lokaci sai dai kuma mugun zurfafa tunanin mutuwar na iya hadasa cuta, hakan kuma na iya kasancewa cutarwa ga bawa domin da ace hakan ba komai bane da Allah bai boyewa bawa ranar mutuwarsa ba sannan da bai saka hijabi a tsakanin mala'ikan mutuwa da dan halita ba
Dan haka ta bashi dukan kulawa ta yi masa rakiya har wajen motar da zai bi boyayiyar hanya ba tare da media ta san da fitarsa ba sukai kyakyawar salama ta dawo cikin dakinta
Kai kawo ta ringa yi a baban falonta da byro a hannunta tana dan wasa da shi ta hanyar juya shi a hannunta
A hankali ta kai zaune saman bed ta mika hannu ta dauko wayarta cikin nutsuwa tare da ta Muneerath wace ta amsa
Number ta dauka ta kwafa a wayarta ta danna kira tana mai kai dubanta wahen agogo wace ta nuna mata karfe kusan biyu ne na dare, sai dai ta tabata wanda ta kirayan zata same shi koda a karfe nawa ne, kuma bata tunanin zata iya rintsa idannuwanta idan har bata daidaita wannan abin ba
Ba ita ta kwonta ba har sai da ta gama komai kafin ta dauro alwallah ta taho saman bed dinta tana mai adu'aa dukan motsinta ta haye saman gadon
A hankali ta rintse idannuwanta sakamakon murdawar da cikinta ya fara yi mata
Sannu a hankali ta ringa adu'a a irin tsugunin da ta yi a saman gadon tana rike da hannunta tana beman sauki a wajen ubangijinta wanda ta tabata shi kadai ke kawo mata agaji a irin wannan ciwo nata
Ciwon ciki ne da take yi , wanda yake taso mata wani sa'in sai ta kusa shekara biyu bata yi shi ba
Wani irin ciwon ciki ne dake gagabowa tun daga mararta ya yi sama gaba daya ya rikitata ya yi ta juya mata ciki tana birgima du hakurinta da girmanta kuwa, da jyar yake sakar mata amai kafin ta samu zuwa bayi ta zubar da datin dake taruwa wanda yake bata tsoro a dukan lokacin da ta samu yinsa domin shi ba gudawa bane sam, hasalima tauri ne da shi kuma ba tare ba, haka dai take fitar da shi mai mugun warin dake juya mata kai
"Hasbunnalahu wani'imal wakim" shine abinda take maimaitawa tana kallon agogo gannin har hudu ce ta gota ta tabata a yanzu Son baya kusa ita kuwa du abinda zara tsinci kanta a yanzu ba zata iya kiran mijinta da ya fita dan hidimar kasarsa ta dawo da shi ba, haka kuma ba zata kirayi Iman kururuwar iblis ta tara mata jama'a ba
Hakan ya sa a hankali ta ringa murkususunta tana ambatar sunnan Allah tana karra gyara daurin dan kwalin da ta dora a saman doguwar rigar barcinta fara mai dogayen hannu mai laushi domin sam bata wani lafe mata a jiki ba
Wankin hula ne ya nemi kaita safe, tun Mah na gane yaren ciwonta har ta dawo ta fita a hayacinta, har lokacin salar asuba ya shige bata san inda kanta yake ba bayan ita din mace ce mai bi kofar du wani yaronta da ya kwana ya wuni a gidan ta tashe shi sallar asuba , dan kuwa ko anfani da waya bata yi ta fi gane ta je da kafafuwanta
...............................................
Jiki mai rike abin sabo ya maimaita shi da karfin gwuiwa, sabawa da ta yi da tashin asubar ne ya sakata tashi a kan lokaci harma ta tashi Saudat suka daura alwallah suka gabatar da sallah bayan sun yi wanka domin tsaftar nan ta Muneerath ita kadai ce abinda bata taba barinta, tsafta akoyta ta jikanta da kuma mugalinta, du inda zata zauna koda na minute daya ne sai ta yarda da tsaftarsa
Bayan sun gama sallar suka gaishe da junna
Shiru Muneerath ta yi tana duban agogo kafin ta kalli Saudat dakr Hamma ta ce" To yanzun ai ya dace mu bashi amsa ko?"
Saudat ta katse hammarta tana dan zarro ido kafin ta yi yar dariya tana talabe kumatunta ta ce" Anya kuwa sir mai sanyin haki zai iya da rigimarki?, Kin san menene idan har bai zama kazar kazar ba ina tsoron ki mayar da shi solofiyon namiji"
. Muneerath ta yi yar dariyar itama tana cire hijab dinta a hankali ta shiga dan motsa wuyanta kafin ta kwonta ta ta shiga dan motsa kafafuwanta tana jim na sasafe da take dan yi dan ci gaban rike lafafen ciki kamar yadda aka koya mata ta yi murmushi a karro na biyu ta ce" kin san menene?, Attahir na nunin shima wani zaki ne, harma ya ce zai iya saka rigar dogari dan na so shi...................wannan wasan da ya buga ya saka ni a tunaninsa........................aman;;;;;;;;;;;;;;' ta dan yi shiru tana kikifta ido alamun wani tunani ne ya shigo kwakwaluwarta hakan ya sa saudat tabo hannunta tana fadin" Aman me?"
Muneerath ta yi murmushi ta juyo tana kallonta ta ce" Ni fa bana tunanin idan har namiji laso laso zai iya rayuwa da ni lafia, kin ga meye anfanin namiji idan zai maka magana sai ya sanyayar da murya? Ni fa gani nake to wane ka bara min kennan? Kin ga aka ce mace ita ce yar kwalisa, yar sanyin murya, yar lalashi, yar yar yar yar..........., Ki duba ki ga Attahir idan zai yi magana fa fari yake, na taba tambayarsa ko ciwon idannuwa yake ko kuma haka aka haife shi ne? Sa ce min ya yi aa wai akoy abinda ke saka shi cikin shauki irin haka, shi kuma haka Allah ya halice shi bawan Allah"
Wata irin daria ce ta kubcewa Saudat har tana rike ciki a saman salayar tana kwonciya, ya subahannalah wai shin wace iri ce Muneerath ? Yanzun yana mata irin kashe idon nan dan ya saka ta afka a soyayarsa wai ta masa tambayar ciwon ido yake?
Bata karasa wannan ba Muneerath ta girgiza kai tana zama ta mayar da gwuiwar hannayenta baya ta gyara kwinciyarta ta daga kafafuwanta kadan ta tsayar da su tana ta sauke ajiyar zuciyar wahaka dan wannan yana bata wahala duba da mazaunan nata idan ta yi haka wani bajewa suke abinsu ta yi murmushi ta ce" Allah ya daina baki daria wannan abin, to sai na ga ni me namijin ya bara min dan Allah?, Haba ai ya dace nakiji kawai ya kasance mai kaza kaza,mai balaki da tashin hankali, dan rikici na mamaki, wanda idan na masa zai daga ni sama ya nunawa shirwa ni ya nana da kasa............a haka zan fi jin tsoronsa, ke ogama cewa ya yi wai akoy kura wai kawai in ya kula ni din wannan an so a yi tabi tabi sai dai aka gyara min aka zari hamsin a dari, wai a haka zai barni ko dan idan ya min aure ya ci daria, dan ya san wai ko a yadda idan namiji ya ce irin wai ina da ko manyan kaya ko me? Nake fada masa in ce masa ya daina dinka min manyan kaya, ke ni dai da abin ya ishe ni sai na koma siyan gwonjo da kudina na kari, yo shi kamar wada ya tsane ni a cikin y'ayansa kulun kulun sai ya sa a min baban dinki, mai dinkin nema munafuki sauran ai dinkin motsa da karfi ka yage yake masu sai ni yake yiwa buhu dan kawai an tsane ni"
"Innalilahi" shine abinda Saudat ta fada tana karra wara dubanta a kan Muneerath, walahi ita bata taba gannin mutun mai faranci irin Muneerath ba, yanzun babanta take cewa an ce tana da manyan kaya? Haba haba dole ya ce an zari hamsin, kuma tsakaninta da Allah ne take maganarta ,
Sai kuma tausayin Muneerath din ya tsargun mata a zuciyarta, shin menene musababin wannan hali da take ciki? Munnerath bata taba zama ta bude mata sirrin cikin gidansu ba, idan ta kamata wani sa'in tana hawaye ko ta zurma a tunani idan ta tambayeta ba'asi tun tana ce mata ba komai har wani lokacin ta fashe da kuka ta dora kanta gefen kafadarta tana fadin Saudat, kin ga fa iyaye ne da ni, da ransu da lafiyarsu, idan na ga asabar ko lahadi ta gabato na ga iyayenku na kawo maku ziyara, wa'inda suke nesa da kasa sai na ji zuciyata ta tsinke, shin wai anya baki daya y'ayan gidanmu su suka haife mu?, Sam basu damu da mu ba, mahaifiyata na raye ina nan bata neme ni ba, shin me yasa ba shakuwa ba soyaya sai kiyaya nake karanta a tare da su?, Idan kina so ki ga ana sonki a gidanmu tabo fada a waje yanzu zasu ringa yiwa kansu kirarin su an gwada masu rashin mutunci? To wannan fa an tabo waje watau zasu nuna maka su din sun iya masifa mai sunna masifa wace bata da hadi, abin bakin cikin ba dan a nuna maka kauna ake maka hakan ba, sai dan a nunawa duniya in masifar take nema ta tardo gidan, shi yasa ni bana kai masu fadana, idan na ga an fi karfinama sai in yi Allah ya isa walahi,.......aman abinda yake bani mamaki Saudat shiru ba Oga ba Mamanmu ba kowa nawa harda shi mai son na yi karatun ko bai san bana gidan bane?
Daga wannan ranar ta ringa yiwa lamarin Muneerath uzuri, daga nan ta ringa fahimtar dukan wani abin na gabonci, irin na mamakin nan idan Muneerath ta aikata daga mahaifiyarta ne, iyaye mata sune masu koyar da y'ayansu lamarin rayuwa, uwa mahaifiya ita ce zata bambancewa yarta komai , ciki kuwa garda karatun da ake basu a rufe a islamiya, yawanci malamanmu ba zasu fito maka a mutun dan su ganar da kai wane ake nufi ba, hakan kuma ya dauko asali ne daga irin yadda y'ayan na yanzu kyar sun san me ake nufi dan an basu magana a rufe to fa tabas sun san ina ta nufa sai dai a kalli junna, aman kuma sunna mance cewa akoy masu hali irin na Muneerath, inda Allah ya taimaketa ita Muneerath din, ya kasance yarinya ce mai masifar tsoron harkar D'a namiji, kai ko fadan fa Muneerath ba wani karfi ne da ita ba, ita dai barta a wajen harkar kin tsoron waje, kai magana fa idan ta yo niyar fitar da ita fitarwa take ko a gaban waye!
Munnerath da ta mike tana juya kugunta shima duka a cikin yannayin dan motsa jikin da take ne ta dakata da sauri ta ce" Ke ban fada maki abinda Mah ta ce ba, ta ce walahi talahi du yarinyar da ta yarda namiji ya zo mata sai ciki kawai, na ce wai wani iri sai Mah ta ce ko hannuna na yarda ya taba, kin ga yaron nan nata ko? Sau biyu yana rukunkume min jiki, dan Allah dan na tsorata na yo wajenka ai sai ka wankan mari na ankara namiji ne kai, sai kawai na duba da kyau sai na ganni a jikinsa, Allahma ya sa Mah ta ce sau biyu kawai ba abinda zai samu aman ina yarda na uku ya faru an kare"
Zuwa yanzu tsakani da Allah tausayin kawar tata take sosai , duda idan ta dauki wani wajen kasantuwar Muneerath a haka shi ya fi daidai da rayuwarta duba da irin kirar da Allah ya yi mata da ace ita din mai kwaramniya ce da maza sun gama sukuta a kan dokin nan nata sun kara bude shi ta yadda zata zama dokin yan duniya, domin namiji karya kake ka ce zaka iya zagaye shi, idan ka ci riba a kan wani, a kan waninsa ba zaka kai labari ba, sai dai kuma idan ta bi wani bangaren na idan fa akaiwa Muneerath aure aka kaita a haka mijin ya nuna manufarsa da abinda zai kai hannunsa wanda ya zarce runguma za'a kwashi diyan kallo, may be ta sume masa ta yadda ba zai iya anfani da ita a haka ba, ko kuma ta haukace gaba dayama da kuka, ko a zaman gidan horon Hosteesss da suka yi irin tsakaninsu yan mata wani lokacin baka jin kunyar cire rigarka ka saka wata a saman bra dinka, ita bata taba haka ba, saima kowa ya bar dakin take cire nata kayan a labe ta cenza, to ina da namiji ya ce ga abinda zai taba?
Kallonta take tana ta kokowa da tunaninta, shin ta sanar mata abinda yake faruwa asalin meye yake iya faruwa da ita a lokacin da ta auri namiji ko kuma ta barta idan aka ce yau an daura aurenta koda tana nesa ne ta sanar mata? Ko kuma a yanzu take zaunar da ita ta yi mata ainahin karatun fari fari ta yadda zata san me ake nufi da kalmar *YA ZO MIN?*
Tana kallonta ta ce" Muneerath zauna mana mu yi magana?"
Muneerath ta juyo ta ga yadda Saudat ta yi kala irin na serieus tana kallonta watau jira take su yi magana da alamu mai mahinmanci ce
Kokarin zama take aka yi knowkng din kofarta
Da sauri ta juya tana murmushi ta ce" Yau dai Mah ta makara, kin san tun dazu idan na kalli agogon cen mamaki nake har yanzu shiru? Mah ba dai sabko ba yau ta makara zan kuwa yi mata daria na ce Mah na yi sallahta a kan lokaci, ian zuwa Saudat sai mu yi maganar"
Tana fada ne tana karasawa ta bude kofar
Abinda aka fada mata ne ya rikitata, ko dakatwa ta yiwa Saudat magana bata yi ba ta shiga bin Likitar doctern mace suka nufi ainahin asibitin dake Palas din wace take nan domin kula da lafiyarsu
Har gani take sun kasa karasawa duda a mota aka dauketa, gaba daya ta rikice Tambaya take yaushe ? Wa ya kaita asibiti ? Pah ya dawo ne? Kwata kwata Muneerath ta manta shigar dake jikinta ta kayan barci na roba masu bin jiki masu kananan gannaye kanta kuma ba hula a kame a tsakiyar kai sai takalmin dake kusa da bed dinta wanda yake kafarra wanda Mah ta hannata taka tiles din gidan nan ba takalmi, sai farar safar dake kafarta wace yanzun saka safa ya zame mata jiki sam bata zama ba safa a kafarta
Tambayoyi take ma likitar tana bata amsa har suka isa suka fita
Iman ta ganni zaune tana hawaye hancin nan ya yi jajir hakan ya sa gabanta ya yanke ya fadi da gudu ta nufi iman tana tambayarta ina Mah din ne? Ko ta mutu ne take kuka haka?"
Rai bace ta mata nuni da dakin da manyan dakarun sojoji ke tsaye wa'inda ita bata taba kula da su a gidan ba wa'inda har ga Allah sai da ta ji gabanta ya fadi na tsoronsu da ta gansu , aman da yake a yadda iman ta fada mata bata mutu ba da haushi ta ce" Shine kike yiwa mutane kukan iskanci a nan, ki yi mata adu'a mana Allah bata lafia haka kawai ki saka ni faduwar gaba karfe tara na safe ko karyawa ban yi ba?, "
Sai kuma ta sasauta muryarta ta ce" Iman dan Allah raka ni mana na ganta wa'innan na tsayan da alama basa son iskanci, kin gansu kar na he su mareni su kurumtani kin ji?"
Iman ta kauda kanta tana gunguni da tunanin lale Muneerath ta raina mata wayo, Bodyguard din na HANJA na dare ne bata sani ba? Mutanen da idan dare ya yi ko Pah basa bari ya shigo kai tsaye bangaren Hanja sai sun tabatar da Pah din ne ita da take tafia da shi kusa da kusa har sunna fada zata nuna bata sansu ba?
Munnerath gannin dibar akbarkar ta iman ta tashi sai ta kebe bakinta ta mike tana kade gefen cinyarta ta kale su ta yi adu'a ta nufe su dan ta tabata Mah na ciki idan kuwa tana farke ba zata so ace ta zo bata shiga ba, ta ga damar ana sakinta ta kama yi mata nasihar zumunci da kula da kwadaita mata lada a gannin marar lafia
Da ta tsaya a gabansu sai da ta raina tsayinta da kibarta, 'kamar yan tagwayen d'an Mah' haka take fada a zuciyarta
Sai da suka dubata da wani abu a hannun su har fuskarta da kyau kafin su bata hanya ta shiga , dama Iman ce ta bada umarnin a daukota domin itama da ta shiga ta tarda Mah a haka shine fa ta sanar da Hanja kafin ta sanar da likitocin , a yanzu da aka gama treatmen din Mah sai ta saka a kawota dan ta tabata idan Mah ta farka bata ganta a tare da su ba tana iya bata rai
Tunda Muneerath ta sanyo kafarta ya dago kansa daga zaunen da yake dare dare a saman bed din asibitin mai daukan mutun har biyu domin yana da fadi gaskiya ba irin matsatsen bed din nan bane , ya yi irin zaman nan kan Mah a saman cinyarsa hannunta kuma a cikin nasa , kanta sanye da hular mararsa lafiyan mai hade da kayanta, jikinta kuma rufe da bargo sai wajen fuskarta da kanta ne suke bude, ga dukan Alamu barci take yi
Da farko da dan karfi karfin tafiyarta ta shigo wajen, sai dai cikin ikon Allah daga bakin lokacin da ya dago da idannuwansa masu duhun haske ya sauke a saman fuskarta ya tsayar da dubansa kyam a cikin nata idannuwan da fuskarsa da ta yi ja, wace ta kula da zarar hankalinsa ya dan tashi daga fari tas sai ya dawo ja , sai ya zamana tafiar tata na rage sauri, har ta dawo tamkar an zare mata lakhah ne take neman tabulewa ta rufta kasa dan gaba daya sai ta nemi karfin jiki ta rasa kuma dan wani balaki ta ki cire duban nata a cikin idannuwansa har ta idasa kusa da su daf da daf tana mai kai hannunta na dama ta rike abin gadon dan ji take kamar wace ake jijigawa anai mata juwa , yannayi dai kamar na wace ta kurba bayan ita din nan ko goro bata ci
A hankali ta cire nata duban daga nasa dan ta kula HANJA mutun ne mai irin kallon nan da ake cewa ba kyau, watau haramtacen kallon nan da aka hanna a musulunci, irin kallon nan na a kafe mutun har a gano muninsa, kai in ba hanja ba ni kuma munina ai a bayane yake kau? So dai yake ya samu na cewa na masa bayan mamanshi ba lafia, koda yake ai aibun sangarta yaro kennan, sai mutun ya sangarta yaro yanzu haka kuka ne yake dan mamansa bata da lafia da ya ji motsina ya fuske, a banza bayan na gama sannin kai din dan akoke ne a gaban Mah da Pah'
A hankali kuma a lokacin da ta shafa gefen fuskar Mah ta ji ba zafi jikin ta kuma ga yadda take barci, ta kasan ido ta kuma lura da fa ita yake kallo walahi sai ta samu kanta da tunanin me yasa ya cika kallo?, Du abinta ta gane cewar shi din mai yawan kallo ne uwa namijin karuwi!
Dan neman magana irin nata, ba sam take mance shi din mai gigita rayuwarta ne sai ta samu kanta da yin kasa kasa da kuryarta sosai tana dan sata kallonsa ta kasan ido kafin ta dan gyara bakinta a hankali ta ce" Ka san cika kallo bashi da kyau a musulunci, a gayancema ba kyau a kurema mutun ido, ko kuma ka sani take sanin ne zaka yi mr HANJA?".............
Ku mu bata amsa sisters馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀
Barama ku ji, more cmmnt mr pstng ah tam馃ズ馃ズ
Kumama kumama ba edditing馃槖馃槍
11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
4锔忊儯9锔忊儯
Sarai kunnayensa sun jiye masa dukan abinda ta fada, sai dai ga mamakinta shiru tamkar ba kowa a dakin, hakan ya sa ta yi tunanin kawai bai jita bane dan haka sai ta kara gyara tsayuwarta sosai tana kara dan shafa gefen fuskar Mah da hannunta na hagu dake kusa da shi, da dayan hannun kuwa na dama tana dan susar gefen duwawunta irin na ka rasa me zaka yin nan kana neman fitinar nan a hankali ta ce" Cewa na yi cika kallo ba halayan mutanen kirki bane, kai kuma sai ka wani tsatsare mutun da ido ko me yasa kake haka? ?"
Wannan karron ma shirun ne hakan ya sa a hankali ta dago zarra zarran eylach dinta ta sauke dubanta a kan fuskarsa dan ta fara tunanin ko dai barci ya yi yana jinta tana magana ya wani shareta bayan ta san ba halinsa bane barin sai ta kwana?
Ga mamakinta kallon nata yake, kuma dai a yadda ta fahimta ba suma ya yi ba domin ai yana numfashi, hakan ya sa ta dan yi gaba kadan ta dawo, ta kuma yi gefe kadan ta dawo, gannin kwayar idannuwansa na binta ya sa ta kuma yarda cewa ba a sume yake ba
A kasan zuciyarta kuma ta ce' Na shiga ukunna , to ni yanzun yaya zan yi da shi kar dai ya fashe min da kuka a wajen nan dan mamansa ba lafia, to wai dama shi Pah yana zuwa yawo ne gashi sun shagwaba yaro sun barshi a gida bata da lafia zai haukace min? In ba mutane ba yanzun du kudin nan na Pah kuma yake neman wasu kamar wada zai shiga kabari da kudi?, Wani lokacin sai na kasa kasa gane son kudi irin na masu kudi walahi' a bayane kuma sai ta yi kalar tausayi tana dan kallonsa aman sai ta cire dubanta daga ta hada ido da shi domin sai kawai ta ji kamar zata kifa masaa kansa, a sanyaye ta ce" Ka yi hakuri ka ji? Ka ga fa cuta ce ai ba mutuwa ba kau?, Nawa suke yi sunna tashi mai lafiyar kuma idan lokacinsa ya yi sai ka ga ya mace murus har lahira ba wanda ya isa ya hanna, ka daina yi mata kuka ka mata adu'a ka ji? Kuka ba magani bane, idanma baka iya ba mu je na kokoya maka ka dawo ka ringa mata dan walahi ni din nan a islamiyarmu har jira ake na fara kira'a, yanzunma sauke mata kanta a samanka kali fa ai sai ta kage baiwar Allah"
Abinda ya gama sani game da wannan yarinya shine ba zata taba daina bashi mamaki ba, ya rab wai irin idan aka ga yaro na rigima na mamansa da ake masa wayo a rarashe shi ne take son masa wai ya bar kuka ko a ina ta ga yana kuka??, Sai dai wani al'amari sai haka din ya rage masa kuncin zuciya, haka kawai ya ji yana son yin abinda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 42