Share this page
alamun nan kar a he kada ne ya cinyeta a huta Dan saurayi ne ya fito yana ta kilkila daria yana waige waige ya ce" Na rigayeki, yihu yau na rigayeki kuma gata nan tsakuwar na daukota ta cen kasa tsakanin dutse hudu na yamacin kudu da kusurwar gabai!" Shiru ya yi sakamakon ido hudun da suka yi da Muneerath da gaba daya jikinta je rawa shima yana kallonta A hankali ya ce" Baki ga Zeinab ba? " Muneerath ta matse kafafuwanta sakamakon jin fitsari zai sauko mata, yau ta ga ikon Allah yau ta yi mumunar fitowa, ita ba jaraba gareta ba yau gaba ga aljani kuma har ya ganta shima yana mata magana, da sauri ta duka ta hade hannayenta ta ce" Idan kai musulmi ne ka yiwa Allah ka rufa min asiri kar ka ilatani, ina matukar kaunar koyon ruwa dan ina da buri na karatu a rayuwata shine na zo nan yau ashe da rabon ma hade ni da jinsinku, ka yi hakuri idan lokacin wasanku ne na zo ni kaina ban san bani da hankali ba sai yau, in ba karshen kwana ba me zai kawo mutun nan shi kadai? Ka yafe min ba dan hakina ba" Daria ce ke son ciyo shi aman ya ringa rikewa sa dukan kokarinsa Zainab dake dayan gefen da basu ga fitowarta bane itama ta bushe da dariar har tana rike cikinta Da sauri suka kai dubansu ga budurwar da zata yi sa'ar saurayin, da sauri ya ce" Ke Zainab ki yi shiru kar a jiki kin san fa an hanna shiga ruwan kar sojojin cen su jimu su kama mu, waima ke Bingel ta ina kika shigo nan?" Ya jefawa Muneerath tambayar da ta kasa bashi amsa ita dai ta kale shi ta kuma kalli Wace yake kira da Zainab, gannin ta rufe bakinta da sauri tana zarro ido ya saka Muneerath yin sakalau da sanyayar murya ta ce" Aya zainab ku mutanene hala? " Zainab ta karaso kusa da ita tana daria kasa kasa ta zauna kusa da ita ta ce" Mu mutane ne bana, ni da shi tagwaye ne a nan muke wanka kulun aman idan sahu ya dauke dan an hanna shiga wai kar ruwa ya tafi da mutane, yo in ba yan birni ba mu nan ruwa wani iri ne bama shiga? Ai idan aka hanna mana shiga ruwa an kashe mu, mahaifinmu fa shine sarkin ruwa, yakan yi awa daya a kasan ruwa tun muna jarirai ake saka mu ruwa fa" Muneerath ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi tana gannin yadda saurayin yake dan zagayawa abinsa yana kallonsu sunna hirar kafin ya ce" Taso ki zo ki gani " Muneerath ta ki tashi tana kallonsa cike da tsoron girman ruwan Zainab ta ce" Idan kina so sai mu koya maki walahi " Muneerath na kallonta ta ce" Tsoro nake, kin ga zurfi ne da shi fa, kuma idan ya tafi da ni fa?" Murmushi Zainab ta mata ta kama jakarta ta amsa ta ajiye nan ta ce" ki cire hijab dinki ki daure iya kanki da shi, ki cire wannan diguwar rigar dan kar ta bace ki rasa wace zaki shiga gari da ita ko kija da wasu a cikin jakar?" Muneerath cike da mamaki ta ce" Dama ina iya shiga da wannan kayan basu yi nauyi ba?" Kai zainab ta girgiza ta mike tsaye, jikinta sket ne kasansa da dogon wando aman sket din mai budewa sosai ta juya ta kara juyawa tana wara kafafuwanta ta ce" da sket din da zai hanna kafafuwanki yin taku taya biyu a second daya ne ba zaki iya iyo ba, aman idan kayanki a bude suke komai gimansu zaki iya yin iyo dinki hankali kwonce, tsoro kuma ki cire a ranki na cire maki kadara idan hukuncin Allah ne ruwa zai ci ki ba yadda muka iya, aman idan ba karshenki ruwa bane ba abinda zai maki" Cike da jin dadin hakan Muneerath ta ajiye jakarta, ta nade gashin kanta da dan kwalin sannan ta bi bayan zainab A hankali Zainab ta riketa da kyau suka fara shiga ruwan da ta ji sulbi na kwasarta zai dimata da kasa da sauri ta yi niyar ririke zainab sai dai ina Sakinta zainab ta yi ta dimu a kas din kanta ya fara yin salama cikin ruwan ta kuwa shaka ta sha ta hancinta hakan ya sa ta gigice sosai zata fara harbe harbe ta ji an rikota an fito da kanta sosai, tuni dan kwalin ya fece abinsa a nan asirin gashin da take rufewa ya budu ya jike ya yi lub abinsa A rikice ta dan fara ihun wahala Zainab ta yi yar daria ta ce" Masha Allah kin ba sarakan ruwa rabonsu, yanzun shikenan ke da su ba zasu kuma shaka maki ba, kar ki tsorata babu wanda ya koyi ruwa bai shaka ba ko a garin nasaru ne bale a nan, kuma akoy rabo na sarkin ruwa koda baya nan idan muka koya maki bamu cire rabonmu ba akoy matsala" Tabas ta ga abu, da farko sun gigitata, sun rikitata, a hankali kuma suka shiga bin bayanta a hankali da raha, suka shiga gabatar mata da koyo irin namu na gida, koyo na kai tsaye wanda a nan take za'a yi abin kuma a tsareka da ido ka maimaita, ba tare da an maka theori ba Ke durfafar pratique hakan ya sa abin ya shigota kai tsaye ta bada dukan hankalinta tana kallo Sun dauki lokaci mai tsayin gaske kafin suka fito, cike da gajiya ta baro wajensu ta dauki hanyar gida kamar an tika mata dukan tsiya Layi take da haka ta idasa cikin gidansu, tana shigowa ta yi turus tana kallon yau kuma wani sabon lamarin Oga ne tsaye yana zuba balaki hakan ya sa ta kara kashe kunne ta ji yana fadin" Ni zata yiwa rashin mutunci , nawa na biya? Zata dawo gidan ne kai gaba dayankuma zaku fada min a me kuka daukeni ne a gidan nan!" Ido ta kikifta kafin ta yi kundunbala da du wani tsoro ta danna kai kanta tsaye ta ce" GANI MEYE? " Gaba dayansu suka juyo gareta, tun daga Oga , mahaifiyarta har karamin autansu sunna kallonta, Oga ne da bacin rai ya nufota ya budi bakinsa ya ce" 11/14/21, 12:44 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 馃敓 Da yannayin bacin rai ya nufota ya budi bakinsa yana nunata da yatsarsa ya ce " Ke yanzu dan ubanki y'ar oga yaya kuka yi da masu koya ruwan nan?" Muneerath ta kikifta ido kafin ta gyara tsayuwarta ta ce" Tarbiyarsu ce bata yi min ba " Mahaifiyarta cike da bacin rai tana zaune ta dago kanta ta ce" Muneerath lale yau zan ci yan gidanku a gidan nan, wai ke kin raina mutane ne ji menene wannan rashin mutuncin? Ba dai tarbiyarsu ba ke tarbiyar ne da ke? Shine kika min asarar wayata kuma ke baki anfana ba? " Cikin rashin damuwa Muneerath ta ce" To ai sai a amso tunda ban yi ba sai su bada kudin kau? " Kishiyar mamanta ta gyada kai tana dama tuwo da nono da siga ta ce" lale, watau idan kun kula yarinyar nan tunda ta samu Bac din nan kamar an nadata shugabar kasa, iya shege kala daban daban ba wanda ta bari a gidan nan, kowama taka shi take son ranta kuma bata daukan hukunci dan ta fi karfin uban kowa, to a dai bi a sannu danma ranar aikin uwarki ne kika ci kudin nan nata kika ci ba na wani ba da ace a nawa ne Allah sai na rike maki makogwaro ta yadda ba zaki iya mararin cin kudina gobe ba sakaryar wofi ko daga gidan ubanwa take sai tsago take?" Dayar ta yatsina baki mai sunna Huwaila ta ce" Daga gidan wa kuwa take banda yawon sakarcin nata ko dai Dogarin ya samu ne yana kwakuleta a lungu, ke yanzun in banda rashin kunya da iskanci irin naki mu zaki kalla ki ce tarbiyar wani bai maki ba, nan fa kije fita tun safe sai talatainin dare ki dawo kuma ki shige ki ci abinci ki kwonta a gado ki yi barci ki tashi ki sala wanka da ruwan pampo ki kuma fita, in ba sana'a ce da ke ba tsayayiya wai me kike yi? Ki dai bi dunia a hankali idan maza ne sai sun gama tsotseki tas zasu yar da honkon, gaki ke ba kyau ba, ke ba farin ba bale ace ko dan su a so ki duwawu kuwa akoy wadda nata ya dame naki ya shanye bariki ta gama da ita ta yar" Oga ne ya juyo cike da mamaki yana kallonsu su dukansu , kansa ya gyada ya kalli sauran yan matan su ko a kwalar rigarsu wai rigimar da ake , sam bata dada su da kasa ba, kansa ya kuma gyadawa ya dafe kugunsa da hannunsa ya ce" Yau na ga jaraba, kai wai kudinku ko nawa? Kamar wadda kuke jira uba ya bata da yarsa a gidan nan ko? Har a ringa fadin wai ranar wance ko na wane, ke huwa Huwaila da maza na karar da alheri ai da an karar da naki sai da aka gama da duk wani alherin naki fa na kwaso nima dan jaraba kamar wanda iya ke min baki walahi, to yanzu ai sai ku bari in mata tambayoyin daya bayan daya ta bani amsoshina dan kun sani sarai ba karya ba zata mini ko kasheta zan yi, dan yar nan jaruma ce kamar ubanta ko a gaban uban waye zata yi magana kanta tsaye ba da dar dar ba ko tsoron wani abin ba!, to Allah tunda na ga so kuke ku nuna min kun shanye ni ta yadda idan na yi niyar yin fada kuke amshewa ba za'a mata fadan ba, kudi kuma nawa ne ba na uban wani ba a barmin yara su sha iska!" Huwaila ta tabe bakinta da bacin rai da bambami ta ce" Ni dai ba ubana ba a zagin nan, kuma da kake cewa kudi ba zaka amso ba dama ta ina zaka iya amsowar kai da mutanenka abokannan sana'a! Ai gado ta yi na iskanci" Daga muryarsa ya yi ya ce" Ke dama yaya za'a yi na raba zagin uba da ke? Da masu uban nake ki bari in dawo layin yan layi a tudun jamus sai ki sako bakinki ki ce da ni oga du buro'ubarka kar ka zagi yan sholishow hegiya mai kirar muciya!" Jin yadda ya barowa Huwaila ruwa du sai suka ringa watsewa ba wanda ya karra sekwani ya rage daga shi sai Muneerath sai mahaifiyar Muneerath Zama ya yi saman kujera yana dafe gaban goshinsa kafin ya mike tsaye ya ce" Kai dolema na fara nema maki walahaula da su karya tambaya, dolema na fara nema maki na tsari da na yan uba a yada babarki ke maki hasada gwara in yi da gaske, ni Rukaya mamaki kike bani yar nan kamar wata kishiyarki ke kin fi shiri da kishoyoyinki a kanta, wai kina zaune ana cema yarki na bin maza kin kyale? Ni da kanwata ce ke ba matata ba sai na zane ki tas, ki gode Allah matata kike ni kuwa mai tsoron Allah ne" yana fada ne yana kamo hannun Muneerath dake kallonsa galala hakama mamanta ya turata dakinta yana fadin" Kin ga je ki labe abinki kafin in kawo na turare da wanka ki maida hankali , kai ni ko layama nake basu gaba daya yan gidan nan ko sa shafa maki lafia? Bari dai in je stade in dawo mu yi shawara da abokina idan ya ga ya dace in maka su gidan mai damagaran a mana tsakani da ke da su har ita ruky din sai na yi sauko na amso masu samaci, dan na kula so suke su idasa haukata min ke" MUNEERATH na jin maganar gidan sarki ta juyo ta kale shi da yannayi na son ta yi magana, sai dai bai bata dama ba har ya rufe kofar ya juya hakan ya sa ta raka shi da kallo kafin ta juya tana kiciniyar cire soguwar rigarta, sai da ta cireta sannan ta cire dogon wandon ta kuma cire breziyar dake jikinta kafin ta cire rigar da ta yi dan kwali da ita domin dan kwalinta ruwa ya tafi da shi Ya Allah....... MUNEERATH ban san da yaya zan kwatanta ba, dole ta rufe jikinta domin idan har ta kasance mai budewar da da karfi da yajima za'a cin mata Ya ilahi, yarinyar a cike take iya cikowa, sannan ba shafafen ciki ne da ita ba gaskiya, cikinta na tafe da yannayin da take ciki ne na halin koshi ko jin yinwa yana nunawa, abinda ya rufa mata asiri wadinan dima diman duwawu dake bayanta, irinsu ne ko sun kunso ciki sai dai ka ji haihuwarsu ba dai ba ya nuna kansa domin irinsu ne cikinsu ke bin cinyoyinsu ya lafe abinsa Wasu irin cinyoyi ne masu fadi hadi da fafadan duwawun da na yi mamakin yarda ta samu pant ya dane su daf ya kama su taf da su. Mamanta kau ba manya bane sosai domin sam basu da girman a zo a gani, aman kuma wani abu da garesu shine bakin shantu, a cike suke taf basu da ramar da za'a ga kanantarsu, su dai daidai wa daita ne daidai hannun mutun馃槍 Juyawa ta yi ta nufi wajen hijab din da take zumbulawa ta je wanka Tana sakawa ta kama hanyar bayin tsakar gida Ya kai da mutun uku da suka yi gware, ba na wani abu ba sai na raini, irin gwaren nan na ana jiranka ana jira a yi masifa da kai ana jiran tashin hankali da kai ana jin haushinka Ba wanda ta kula dan a gaskiya gajiyar da ta kwaso ta fi karfin ta tsaya ta yi wata rigima da kowama , ta kanta take yanzun so take ta rama salolin dake kantama Wankan ta yi sosai ta fito ta daura alwallah Mikewar da zata yi Rumaisa ta kifa mata mari, Mugun mari ne, gigitacen mari ne mai saka bawa ya rasa inda zai saka ransa Sai da ta kwala ihun azaba idannuwanta a rufe kafin ta bude a firgice ta sauke a kan Rumaisa A yau bata tunanin oo ogo zai iya tsayar da ita daga lalata fatar Rumaisa, bata san lokacin da ta yi kan Rumaisa idannuwanta rufe ta hankadata jikin garun kofar shiga dakin gaba daya suka rikita kasa suka zube Kamar taya haka suke juye juye a kan junna kafin Allah ya bata sa'a ta dane kan ruwan cikin Rumaisa Ihu yan matan gidan ke yi da samarin ba wanda ya yi kokarin raba su, hasalima nishadi suka samu ciki harda yan uwan Rumaisar na jinni da na Muneerath din Mahaifiyar Muneerath na tsaye ta harde hannayenta tana kallon du abinda yake faruwa, bata ankara ba sai gani ta yi maman Rumaisa ta yi kan Muneerath ta kama hijab din Muneerath din tana fadin" Walahi baki isa ba ki ilata min yarinya , ai baki isa ba ki daketa ki hannata kuka gwarama ita tana da zuciyar ta tarbe ki a kan me za'a ringa nuna mata fin karfi haka kawai?" Idannuwanta ta rintse tana jin wani irin abu na sukan zuciyarta, a hankali ta kara sauke dubanta tana gannin yadda ake son fin karfin Muneerath din domin sarkin yawa ya fi sarkin karfi ai Wani irin abu ya kara sukar mata kahon zuciyarta, da sauri ta daga kafarta tana nufar wajen duda wani irin nauyi da kafafuwan nata suka yi mata aman haka take cirawa har ji take kamar numfashinta zai bar gangar jikinta aman irin wulakancin da idannuwanta ke hango mata a kan yar tata sai ta kasa hanna kanta isawa Ja ta yi ta tsaya sakamakon gannin yayansu ya warce Muneerath din da karfi a hannun kannensa biyu da kuma matar baban nasu, da inda indarsa ya ce" Kakkkkkkkkai na fa ci...............uuuuuuuuuuuuuuwaynnnnnkkkkkku, an fada makkkkkkkkkkkkku bata da gatttttttta ne ?" Du kasa karasawa suka yi, dan shi dai sun fi kowa sannin bashi da hankalin, a gaskiya idan ya damki daya a cikinsu sai ta gane bata da wayau shi yasa kowace ta yi baya sosai Muneerath dake layi da kyar ta iya dubansa a lokacin da ya dungure kanta ransa bace ya ci gaba da magana da inda inda yana fadin" kema bakya jiiiiiiiiiiiiiii" da kyar ya karasa yana doka kafarsa ta dama a kasa ya dora da fadin" Na sha fada maki idan fada ne ki daina yi kina barin min na maki, kar abin ya maki yawa ga haukan dogari ga fadace fadace, yanzun dai jeki daki na sayi fadan kyaleni da su yau in sun rintsa shege nake" Da wani irin inda inda ya karasa maganar yana wawurar ice a gefe hakan ya sa da ihu du suka dare masu ridar daki na yi masu yin waje na yi, fadi suke kurman gidansu abin ya tashi Haka gidan su MUNEERATH yake, a kowani lokaci cikin tashin bom yake kashe wutarsa kuwa sai Allah ......................................... Kwonci tashi, Muneerath na gannin rayuwa ta kowani fanni, a kadan ta dauki wata daya tana haduwa da abokananta filani masu iyo yayan sarkin ruwa gaba da baya, sun dauki lokacinsu sun kashe aiyukansu sunna koyar da ita yin iyo da soyayar abin a rayukansu, sau kusan hudu sunna gwada nutsewa ciki da ita, na farko da na biyun kusan a sume suke fitar da ita a na ukun ba karamin mamaki ta basu ba, na hudun kuwa sai suka sara mata kawai, ya zamana har gidansu ta sani wajen da mahaifiyarta ke zama aman bata taba haduwa da mahaifinsu ba, sukan kama kifaye su kasa , nata sai dai ta je ta bayar dan ita dai ba iya gyaransa ta yi ba A cikin haka ta ringa neman wajen da zata koyi girki, sai dai abin ya gagara, sam ta kasa samu, sai a gidan su Amina ake koyar da su abinda kamar ana zubawa ana wankewa ne a kanta, du yadda amina ta kware ita ta kasa dafa abin kirki, ta kasa dafa abu ya dahu ya yi dadi sai dai ta kona ko ta cika wani abin da zai kasa ciyiwa A haka yayanta ya kawo mata journal din da aka fadi bayanin za'a dauki sababin HOTTESTE a babar makarantar da ake horar da su Ta jima tana jin juwa, makarantar tsakaninta da gidansu tafia ce mai nisan gaske wace ake cin kusan rawa biyu da rabi a mota, kuma a cikin garin take Bayan wannan irin tsarabe tsaraben da za'a kawo kafin a samu shiga, uwa uba gwamnati na biya maka rabi ka biya rabin da ta tabata ko ita aka siyar ba zata yi kudin aikin nan ba Kamar yadda ta saba kadaice kanta a gaban matsala dan ta sanar da wanda ta san shi kadai ke fitar da ita, shi kadai ke bata hanya, shi kadai ke rufa mata asiri ta yi, takan raba dare tana hawaye a cikin sujadarta ta fada masa ta sanar masa ga abinda take so, aman idan alkhairinta ne Ta mayar da yin azumi abu mafi sauki a duniyarta, ba rana kulun yi take Ta kwatanta yiwa oga zancen ya ce bata da hankali Ta tunakari Mama ta ce da ita" Munne in dai ba so kike na fita yawon banza ba na tara kudin nan, ke ko karuwanci muke ai yanzun ba tsada bale mu iya tarawa dan Allah ki raba kanki da shirmen banza , yo ni ko dudin nan gareni ai ba zan zuba ba domin abin nan ba lale ne ka samu ci ba, kana oya zuwa ka fadi shikenan an yi asara" Haka ta dawo ta kara kusanta kanta da Allah, tuni Amina ta fara karantun likitanci kuma tana jiranta ta tardota dan ko ita bata bata kwarin gwuiwar wannan shirmen Tana ji tana gani ranar da aka saka ta zo ta wuce, wace ta tabata da an yi an gama, hakan ya sa ta yi kuka, kukan rashin rabo ne ko na gannin mafarkinta ya barta ne? A haka ta dawo ta ci gaba da rayuwa shiru shiru da ita Da yawan yan cikin gidansu kan yi daria su ce ta dogari yanzun aljannun shiru shiru ta dauko Yayan nan nata daya kwal shi ya san me take ciki, kuma abin na damunsa, ba dan komai ba sai dan ya san a kan sannin ciwon kanta take damuwa ba a banza ba Shawarar ta je zuwa University bya bata, ta tafi ta yi karatunta ya bata, a dole ta harhada ya nata ya nata ta fara tafia jami'a Abinka da abinda baka so, baka yi niyar yinsa ba gaba daya ba gane komai take yi ba, a UIT din idan ta je tana yin jeka ka dawo ne kawai, gashi wataran abinda zai maidota kadai tashin hankali ne dan har labe take dan kar a rage mata hanya, gashi babu yan anguwarsu a nan bake su ringa yin hanya daya Da yawan lokuta takan yi wani tunani , sai ta basar ta yi murmushi kawai idan ta tuna cewa ba lalene abinda bawa ke so ya zamo alkhairi a rayuwarsa ba, ba lale ne Allah ya bata burikanta duka biyu ba, ta tabata rashin wannan aiki na nufin zata samu Dogari ne Ta kasance mai fitowa da jakar makarantarta a baya, a cikin jakar nan tana dauke ne sa takardunta kaf na anfani harta da na Bac dinta dan bata barin takardunta na anfani dan gudun a shiga a cicira mata su Tafe take sanye sa doguwar riga irin yar kanti din nan, du yadda rigar ta kai da budewa daga kasa sai dai idan iska bata kado ba sai ta nuna abinda bata so a gani din Kanta sanye da farin dan kwali bata yane shi ba, sai farin silifas mai tudu Tafiarta take tana shawagi kamar wata tauraruwa duba da safia ce karfe takwas ne da kwata Bim bim bim................... motar dake biye da ita sai kara yi mata oder take aman sam ta ki ta tsaya ko ta kula shi Danewa ya yi da karfin da ya sakata juyiwa rai bace ta zo wajen motar Tana zuwa gannin ya tsaya sai da ta fara dukan tayar da kafarta kafin ta leka rai bace ta ce" Kai wai meye? " Jan buzun dake zaune ya tsume abinsa ya ga kalaci da safiar nan sai ya sakar mata murmushi da hausarsa irin ta bugaje ya ce" Sannu yan mata, yi hakuri yar budurwa shigo mana na kaiki inda zaki je" Kallonsa ta yi gannin bama wani baba bane sosai aman sai wani abu yake wai shi ya ga mace , da gatse ta samu kanta da fadin" Baka da isashen man da zai kaini har gidan Hottest " Gannin ba wani yannayi na yayan da zasu iya shiga wajen ta yi ba sai ya yi tunanin ko aiki take a cen na iirn wanke wanken bayinsu, ko kuwa gidansu a wajen yake, Cike da shakiyancin koma menene shi fa gidan hutu ya gani ya ce mata" Shigo mana ki gani idan ba zai kaimu ba" 馃檴馃馃槼 11/14/21, 12:44 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 1锔忊儯1锔忊儯 Ta

Chapter 6 of 42