kyau, mutumen da zai shigo yanzun ban san takamaiman me kika masa ba, domin idan lafia ne ganninsa na iya zamewa har ki koma ga mahalicinki baki samu gannin nasa ba in dai ba a jaridu ba ko a tv ba, abinda nake so da ke ki tsaya a nan ki hade hannayenki waje guda ki yi jira, kar ki saki ki zauna ko ki shiga wani abin daban , idan ya shigo kafin ya shigo sai an shigo am bincika dakin da ke kanki, kar ki yiwa masu bincikarki gardama dan abu kalilan na iya sakawa su sumar da ke a wajen nan, ki kula ki saurara da kyau ladabinki shi zai fitar da mu duda ban san tsakaninki da shi ba domin shi ya sa aka kawo ki nan, aman abinda na sani shine halayansa da kuma irin yadda yake da karfi da mulkim da zai zartar maki da hukinci a nan kuma kin kade har buzunki, ki sani kar ki sake ki zauna sai ya zauna bara na fita ki tsuaa a tsayen nan fa"
Tana gama fada ta fice ta bar Muneerath tsaye baki da hanci da ido a bude ta bita da kallo, wanda ya kawota? Wai tsaya hala sir abokinta? Kai aman kuwa dama shine zai zo bai fada mata ba ko menene? Kuma wai shine ake tsoro haka? Aman kuwa yau zasu sha mamaki idan ya zo yana wangale mata baki tana cin magani dan ba zata sakar masa fuska ba sakamakon zai zo bai fada mata ba walahi!
Tsayawar ta yi tana hamma tana tarewa da hannunta tana dan kale kale a kadan ta dauki minti goma sha biyar ba shi ba alamunsa hakan ya sa ta tabe bakinta ta nufi kujerar da ba ita aka nuna mata zata zauna ba watau kujerar da shine zai zauna a sama ta hau ta zauna tana lumshe idannuwanta sakamakon barcin dake cike a cikinsu ta dora hannayenta saman table din ta dora kanta a sama ta kwontar tana limahe idannuwanta wani dadadan barci ya zo ba sanya ya sureta irin mai tafe da dadadan mafarkin nan nasa ta lula duniyar gidansu bayan ta gama tsakin wai wani tsaya sai ya zauna ta zauna kamar shine OGA!
Wanda ke zaune a gaban computern ne ya gama kallon ikon Allah gannin ta zauna saman kujerar da Sir ne zai zauna a sama uwa uba ya ga ta kwonta abinta ta yi barci ya mike da niyarr zuwa kusa da abin maganar da zai yi dan ya tasheta ya tuna mata abinda Madame ta fada domin sun fita tarbo shi ne gaba dayansu, kawai sai gani ya yi an bude wajen, sojoji suka fara shigowa dafka dafka da su fuskar nan a hade sunna rike da bindigoginsu lokaci daya suka shiga bincikar wajen baki dayansa kafin oga kwata kwatan ya shigo shima cikin takunsa na kosashen ingarman namiji inda dukan manya manyan wajen ke tafe a bayansa sun yi shiru ba mai kwakwaran motsi
Kai tsaye shine ya fara zuwa kofar da aka saka Muneerath, sannan ya gama fadawa sojojin cewa yarinyar bincikensa ce ya dauki abin nan da ake karawa jikin mutun dan a ji idan da wani mugun abin a jikinsa abun ke yin kara ya shaida hakan ya rike a hannunsa na dama ya nufi kofar da aka bude masa inda wanda aka bari gaban computer ya ji wasu hawaye masu dumi na son zubo masa sakamakon tunanin yau sun cira bata nuna ba du sai sun fadawa yan garinsun da ya yi , sannan ya kalli madame da ido yake nuna mata cewar ba kanta fa idan har ya shiga a yanzu aman sam bata gane ba har sai da ya sa kai sanann aka basu damar su tsaya a gaban alon da zai nuna masu abinda yake faruwa a cikin ne
Cikinta ne ta ji ya mata wani irin kuka a lokacin da ta ga HANJA tsaye da mamaki yana kallon Muneerath kwonce tana sheka barci a saman kujerarsa kafin ta ji kafafuwanta sun gaza daukanta ta yi kasa tana zarar ido jiki a mace
Da mamaki yake kallonta na tsayin minti biyu ya gama yarda cewa da gaske barci ne take yi a saman kujerarsa, ta zauna kafin ya zauna harma ta yi barci, nan da nan zuciyarsa ta fara tafasar bacin rai ya gama yanke nata hukuncin shine zai saka jirgin da zai tafi africa ya dauketa a yau ya watsar da ita a duk inda ya ga dama idan ya so a cen ta nemi danginta bayan ya gama kurce baki daya al'umar kasar da ya daukota a kan list din wa' inda zasu ringa horar da Hostess dan ya kula basu san meye ma'anar hakan ba!
Rai bace ya juya zai bar office din , lokaci daya kuma ya ja ya tsaya sakamakon lalausar fuskar mamansa da ta bayana a cikin kirjinsa da kalamanta da tunanin irin nacin da ta nuna a kan yarinyar
Juyowa ya kuma yi ya kara ja ya tsaya ya kuma zuba mata ido, Bukekiyar banza bukekiyar wofi! Ya saba idan ya zo ma'aikata yan aikin wajen suka yi laifi ya hukunta uban gidansu, aman a yau yana tunanin ya zama wajibi hukuncin nan ya hau kan yarinyar nan kafin ya hade baki dayansu sauran daya bayan daya , kai ya zama wajibi ne yau yarinyar nan ta san menene iko! Ya zama dole ya bata tarbiya ya nusar da tsagerancinta domin ba zai manta irin yadda ta zo masa kai tsaye gabansa tana masa irge da wasu yatsunta ba tana fama da wani shegen tumbin tsiya wai ita Hostess ! Kai dolema ya kara hukunta wa'inda suka dauketa suka sakota a duniyar JIRGI!
A DAKE YA RINGA DAGA KAFARSA YANA KARRA TAKU KUSA DA TABLE DIN, WANDA DU TAKUNSA SAI GABAN MUTANEN DAKE GABAN ALON SUNNA KALLONSU YA RUGUZA YA DUGURGUZA YA FADI.....INDA DA YAWANSU SUN GAMA SAREWA CEWAR TASU TA KARE A YAU A GIDAN NAN, DADIN ABIN DAYA IDAN YA KOROKAN KO YA MAYAR DA KAI MAKARANTA KO YA BAKA WANI AIKIN BA ZAKA DAI YI ZAMAN BANZA BA
Lokaci daya ya ajiye hannayensa da abin cajetan a saman table din kafin ya dago hannunsa na dama ya daki table din da dan karfin da ya saka ta a firgice tana jan tsaki ta dago kanta a hankali ta saka idannuwanta masu dauke da launin abin barci a cikin nasa masu dauke da kakausan kallo da yannayin fushi a cikinsu
A tsorace ta zabura ta mike tsaye hakan ya sa yan dugwui dugwui din mamanta motsawa dan ba bra ta saka masu ba sanann dan kwalin da ta daurawa kanta ya kunce ya fadi saman dayan hannunsa dake saman table din kafin ta fito da sauri ta zagaye shi ta koma gefen kujerarta da aka ce tata ce ta zauna a rikice ta kuma mikewa tuna maganar Madame ta tsaya ta sada kanta hannayen nata a hade inda shi kuwa mai zai yi banda tsura mata ido mamakinta na neman halaka shi kafin ya mike tsayinsa gaba daya yana kara kare mata kallo dan idasa fitar da dukan abinda ya dace a hukuntata a kansa kafin ya kai hannunsa ya ciro yar Silent bindigar dake jikinsa ya direta a saman table din yana mai binta da idannuwan nan nasa tamkar zasu dauki mutun da kallo a dake ya ce"
More cmmnt......more pags馃ぃ馃ぃ馃ぃ馃ぃ馃ぃ
11/14/21, 12:48 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
2锔忊儯6锔忊儯
A mugun dake ya ce" Yaya sunnan ki? "
Muneerath ta dago innocent face dinta a sanyaye ta ce" Muneerath "
Bakin nata ya kala kafin ya yatsina fuskarsa ya gyada kansa da yan yatsunsa ya nuna mata wajen zama yana jira ya ga ikon Allah shin zaman zata yi ko meye?
Ai kam Muneerath, ta gyara tsayuwarta ta zauna abinta tana kara sada kanta, sai dai bata idasa zaman ba ta ji wata irin razananiya firgitaciyar tsawar da ta tabata har na wajen nan idan dai sunna ji Sun firgita da wannan tsawar,
Bata idasa mikewa a kan kafafuwanta ba ta ji an jijigota daga zaunen da take an yi baya baya da ita an hadeta da jikin garu kafin cikin yaren turancin da da kyar take ganewa ya shiga fadin" wacece ke? Me kike takama da shi? A duniyar mararsa kunya wani mataki kika taka? A duniyar yan ta'ada wacece ke? Ko a duniyar yan bariki awa nawa kike iyawa da namiji mai sunnan namiji?"
Da dan ihu ya karashe maganar hakan ya saka Muneerath rintse idannuwanta zuciyarta na dokawa tamkar zata faso daga kirjinta ta fito, gashi dai hannu ne mai laushi ya taba fatarta, ya makureta, sai dai abin takaicin hannun garjejen katon da ba muharaminta bane,
uwa uba zafin da take ji a makurar nan tamkar za'a kasheta
A gigice ta buda tsumamun idannuwanta da suka tsumu da ruwan hawaye ta sauke a cikin nasa wanda yake binta da wani irin kakausan kallo wanda ya taru da tsagwaron tsana ,
Numfashinsa na dukan nata sakamakon irin matse mata wajen da ya yi , gaba daya numfashinta neman gagararta yake a irin wannan lokacin , jinta ya fara yi mata nisa kafin ta tsinkayo wannan murya tasa mai dauke da amo irin na zaki ya ce" Babu macen da zata shigo ni da raini dan ta birgeni da kowace irin halita take takama da ita domin a mace ba kalar da ban gani ba , ban ganta ba, ba'a haliceta ba, bale a filin aikina dukan mata maza suke a gabana!
Tsagera kuwa ni babansa ne!, Dan ta'ada ni ubansa ne domin bana daukan kalmar ta'adanci, bama sasancin da dan ta'ada, kuma babu maganar sulhu ko yafiya tsakanina da dan ta'ada! Kin fahimta?" Ya idasa da wata tsawar da ta saka Muneerath kuma rintse idannuwanta kafin ta bude da karfi tana kallonsa
Zuru zuru take yi da idannuwanta kafin ya cikata ta samu didigenta a kasa ta karasa kasa ta zube gaba dayanta yadda ka san an jijiga bera an sake shi sai zarar ido take kamar ta zagi babar sarki , jikinta kuwa yadda ka san an jonna mata soket rawa yake gab gab gab kamar zazabin bana idan ya maka mugun kamu
Kamar ba shi ba ya gama hayaniyar ya juya ya koma saman kujera ya zauna a saman wace ta tashin yana gyara hannayyen rigarsa dan sun dan ja baya zuciyarsa cike da takaicin wannan rana da shi hanja ya kai hannunsa jikin mace ba dan ya yi having sex da ita ba sai dan yamata kashedi, ashe shima zai iya aikata wannan shirmen? Ashe shima aikata wannan shirmen na iya hayo masa kai tsaye? Tabas wanan yarinyar ko yau ya maida ita kasarsu sai ya rubuta ya ajiye cewar ya kai hannunsa wuyan mace ba namijiba da nufi shaka irin na kashedi
Da sauri madame ta shigo ita kanta jikinta na bari, sai da ta ja kanta a sade ta bashi hakuri kafin ta yi wajen Muneerath ta kamata ta mikar da ita a sannu ta nufo wajen kujerar da ita
Da sauri Muneerath ta ja ta tsaya jikinta na bari ta kalli Madame tana girgiza mata kai ta ce" Me na masa? Kar ki kaini wajen cen kasheni zai yi kin ga bindiga ce ya ciro"
Ita dinma jikin nata na rawar ta ce" No baya kisa ba zai kasheki ba, aman rashin zuwan naki zai hadasa mana matsala baki dayanmu,baku yi maganar ba ai"
Muneerath wannan karron sai ta gama yarda cewa garin jarabarta ta kawo kanta wajen da zata rasa rayuwarta, ya salam wani irin basu yi maganar ba? A wannan maganar ai ya yi ya gama fadin komai kuma ta yarda ta dauka ina ita ina kokowa ko fada ko dayan abin da ya fada wa wannan mai karfin yan film din indian?
Sai dai tana ji tana gani madame ta karasa da ita auka tsaya bata zaunar da ita ba sunna jira ya basu damar zama
Kansa ya dago tun daga kan gashin kanta ya bita da kallo har kafarta kafin ya sake kallonta daga kanta ya dire a wajen tumbin da ya gani wancen karron ya ga yanzun babu shi ko kadan
Kansa ya cire a kanta ya karra hade fuskarsa sosai yana kallon yadda jocyline ke karra hade hannayenta tana karra bashi hakuri kafin da yar yatsarsa ya nuna tana iya zama
Da sauri Jocyline ta zaunar da ita kafin ta juya ta fita tana share kwallah ta tausayin kanta da kanta
Sai da ya gama shan iskarsa kafin ya bude litafin tambayoyin da aka tanadar dan a yiwa wanda ake tuhuma
A nutse ya bi rubutun da kallo kafin ya tabe bakinsa ya rufe ya hade hannensa cikin junna yana kallon yadda idannuwanta ke yin marmarmar ya ce" Ba a maki lesson na 茅ducation ba?"
Muneerath ta ringa hanna kanta sob dagowa ta kale shi, aman cikin ikon Allah sai da ta ji gaba dayanta ta dago da dubanta ta kuma masa duba a karro na uku ido cikin ido
Nasa idannuwan ya cire a cikin nata, ba dan komai ba sai mamakin kwayar idannuwanta da kuma yadda suke da kyan kallo, du irin yadda take cikin tashin hankali basu nuna ba saima wani walwalwal da suke
A takaice ya ce" kin san wanene ni? "
Muneerath ta kuma bin gashin kansa da kallo a sanyaye ta ce" Kaine ka kawo ni daga garin mu, tare da matarka"
Da sauri ya kale ta jin ta ce da matarsa, matarsa kuma? Sai ya kuma cire duban nasa ya girgiza kansa yana ayana ya sani dama bata san waye shi ba, da ta sani du tsaurin idannuwanta ba zata iya fuskantarsa da yannayi na rashin kunya ba
Sai kawai ya ga ashe bata lokacinsa ne ya yi na yin hargagi a gabanta , yanzun tsakani da Allah idan na wajen nan suka fita suka yada yanda ya yi da yarinyar nan me za'a kale shi ? A ce masa me du ya tsalake manyan mutane ya zo kan sa'ar kanwar bayansa ya yi hayaniya?
Dan shafa gaban goshinsa ya yi ya mike tsaye ya dauki bindigarsa ya mayar jikinsa a dake ya ce" Mu je "
Da sauri ta mike tana kallon bayansa ta ga yadda nan da nan ya kai kofa a dan kankannin taku ta waiga ta kuma waigowa ta ga ba kowa bale ta arce ta labe a bayansa, ta ga ba dakin buya bale ta shige ta labe sai kawai ta bi bayansa jiki a mace tamkar kwai ya fashe mata a cikin cikinta
Daga nesa take kallon yadda gaba daya manyan wajen suka nutsu sunna gyada kai sakamakon maganar da ta kula yana yi da yannayi na bacin rai yana nunawa da hannunsa kafin ta ga ya dago dan yatsansa na kusan babar ya kada ya kuma kadawa ya yi wata maganar da bata fi biyar ba kafin ya ga du sun gyada kawunnansu a tare sunna amsawa sannan ta ga ya juya ya yi hanyar dogon coridon da zai fitar da shi waje
A hankali ta sauke ajiyar zuciyata bishi da kallon uma ta gaida asha, sannan a bayane cen kasa kasa ta ce" Who are u?"
" Muneerath tunanin me kike, wuce mu je na raka ki wajen motar, mu kam abin ya zo mana da sauki my munnee sai wata haduwar"
A dan firgice ta kaleta kafin ta ce" Mu je ina?"
Joyceline ta kaleta da mamaki ta ce" tare zaku tafi fa, ya ce kin gama formation din "
Muneerath ta girgiza kai ta ce" kai ina, na je ina? Haba kamar mahaukaciya na bi wannan mutumen mu je ina? Nononono ba inda zan je babu inda zani koda da bindiga a kaina, baki ga matse min wuyan da ya yi ba? Hala so kuke ya kasheni? Me na maku? Ku mayar da ni niger na fasa aikin na fasa walahi"
Wani katon soja ne ya zo fari ya tsaya ran nan a hade ya ce" Sir zai shiga mota fa mu je "
Da ido Muneerath ke girgizawa alamun ba zata je ba, sai dai daga ita har Joyceline din sai suka samu kansu da nufar motar da aka nuna mata zungwui zungwui tamkar zata fashe da kuka har suka karasa aka bude mata ta shiga motar da bata taba tunanin akoy irinta a duniya ba tana ta kyafta ido tamkar zata balo ta bala a guje dan firgici da tashin hankali
Ita kadai ce a bayan a zaune a wawakeken wajen, sai direba da soja daya a gaba hakan ya sa ta yi zama irin na zulumi, ta kurawa waje daya ido tana kalo a lokacin da motocin ke sharara wani matsiyacin gudu har suka karasa ainahin gidansa
Da ido ta bi shi har ya fice ya shige wannan waje na gilas watau falonsa kafin ta kuma duban sojojin da suka hadu suka baje ta ko'ina a wajen kowane ka kalla ba zaka so kuma kallonsa ba domin fuskokinsu sanye da mask, hannayensu da gam, kafafuwansu da manyan takalma hannayensu rike da manyan bindigun da ta tabata da alburusai na balaki a cikinsu
Ajiyar zuciya ta kuma saukewa wasu zafafan hawaye suka zubo mata a hankali ta dora hannunta ta talabe habarta da kumatunta kafin a bayane ta fashe da kuka irin mai karan nan ta ahiga rusa shi tana fadin" Wayo oga, wayo mamanmu, wayo yan uwana ku zo ku dauke ni daga wannan gidan kar su kashe ni, wayo Allahna na shiga ukunna ni ba yar daba ba, ni ba barauniya ba, ni ba karuwa ba, ni ba kisa na yi ba aman an tiso ni da bindiga an tare min hanya bayan an gama cin kaniyata, wayo na shiga ukunna garin nacin son zama Hostess zan zama gawa a garin arnawan da basa sallah bale au salaceni au kilaceni irin na musulmai, wayo ni wayo Allahna ni ta dogari yau kuma a nan na tsinci kaina? "
Hannayenta ta dora saman kanta sosai ta langwabar da kan ta dora da fadin" du wannan wulakancin kaine sanadi, dogari da ka nuna kana ra'ayina da na wuce wulakancin kowani namiji, aman sai ka tashi ka saka kafa ka haure ni ka kasa tunkaro ni ka kasa nuna min so, haka nake hakuri ina kallonka dan ba zan yi irin na yayata ba na nunawa namiji so ya dawo yana wulakanta ni ba, aman ba komai na tabata adu'a nake watarana zaka dube ni, idan kuma ka dube ni wannan garjejen sai ya yi dana sannin sanina, dan daraja ce da ni, ni ba kanwar lasa bace!"
Daga inda yake zaune gaban computer dukan bayananta yana ta saurare ne ba tare da yana gane yarenta ba, daga kasa kuwa dankareriya zakanyarsa ce ke kai kawo tana kada bindinta irin yau a farin ciki take ga wanda ya ajiyeta ya dawo daga yawace yawacensa
Da sauri ya shiga dadana computern nasa yana ta aikin neman yarikan kasar Niger
Nana da nan aka gabatar masa da yarika na kasar niger kwaya takwas daidai
HAUSA
ZABARMANCI
FILATANCI
BUZANCI
TUBANCI
BARBARCI
GURMANCI
Larabci
A nutse ya ci gaba da aikinsa ya nemi translate app na yare kala daban daban
Kasancewar duniya ta ci gaba, abubuwan ci gaba na duniya sun rigaya sun cika duniya, ya sa a zaune da yake a saukake ya samu mai amon murya cikin kwarewa da iya aiki da computer da bincike bincike ya saka wannan yare nata a layin translate na yarukan nan banda larabci domin ya tabata ba shine take yi ba kafin ya mike ya nufi ciki dan ya samu ya yi wanka ya dan taba wani abin
Hankali kwonce ya yi dukan abinda ya saba ga zakin nan du inda ya bi yana biye da shi haka kuma yana mata hira yana dan murmushi itama takan dira ta ringa markayarsa tamkar ta samu jikin dan uwanta zaki, shi'q hankali kwonce ba da tsoro ba yake biye mata har ya cenza kayan nan zuwa sweet maau ruwan Ash ya daure da nekti mai ruwan blue da baki baki ya saka bakar safa da bakin takalmi ya caje gashin kansa ya saka bindigarsa yana aikin mika ta ainahin abinda yake missing wanda rabonsa da mace a kadan ya dauki wata biyu sakamakon irin tafiar da suke yi shi da iyayensa inda mamansa ke mugun saka masa ido da nasihohi kala daban daban
Tsayawa ya yi yana daura agogo ya saki murmushi gannin zakanyarsa ta nufi wajen kofar fita tana kai kawo kafin ya girgiza kansa a ransa yana ayana 'wai dabama ta san ra'ayin kanta'
Tsayawa ya yi facing din tankamemen madubin falonsa haka kawai ya zo wucewa ta wajen
A hankali ya dan gyara gashin kan nasa kafin ya lumshe idannuwansa ya saki dan murmushi a fili ya furta" Aure zan je nema"
Sai kuma ya dan daga kafada ya nufi wajen computern dan ya tabata zuwa yanzun dukan bayanan da ya dace ace ta yi ta kwatanta zai saurara ya ji yanda ya kamaya yi da ita, ya gama mata shirinta ne idan har dan ta cuci mamansa ne ta biyo su a yau a nan zai harbeta kowama ya huta, idan ya so ya turawa kasarta labarin ta mace, in kuwa bai ga haka ba dole zai kaiwa Mah ita a yau, daga baya ya ci gaba da bin dukan motsinta dan shi sam baya da saurin yarda da kowa a duniya!
Kasakai ya yi da baki yana sauraron shirmen da computer ke fadi a lokacin da ya dana ta karanta masa abinda ake fada, sai dai bata fasara sunnan dogari ba, hakan ya sa ya dafe goshinsa cike da jin haushin bata lokacinsa ya nufi waje da zakanyarsa yana furta "Yanzu haka bata da hankali ganewa ne ba'a yi ba"
Ido ta kwalalo gaba daya a lokacin da taga yadda zakanyar nan ke ta makalkalarsa tana juyi a jikinsa
Idasa sauka ta yi kasa tana rike fitsarin daya gama fara fitowa a mararta tana zarar ido ta ce" shikenan zaki ne ajalina............
馃槍馃槍馃槍馃槍馃槍馃槍
11/14/21, 12:48 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
2锔忊儯7锔忊儯
Tsabar firgicewar da ta yi, da kuma lafiyayiyar hanya irin ta kasar ingila, da babar mota watau mota mai sunnan mota ba moto ba ya saka sam bata san cewa sun motsa daga inda suke ba, sannan bata san cewa sun dauki lokaci sunna tafia ba, sai jin budewar motar da ta yi lokaci daya cikinta ya juya wani lafiyayen gudawa ya faa hada kansa wanda ta gama tabatawa cewar yana kusa , idan aka yi wasa a nan take zai bale mata ta kai dubanta a kan fuskar Mah da fuskarta ta kasa boye farin cikin da take ciki sai washe fararan hakoranta take kafin ta karaso wajen da direba ya budewa Muneerath motar kan ta fito ta miko mata hannunta tana murmushi ta ce" Marhababuki daughter"
Ido Muneerath ta zuba mata cike da mamakin ina ne nan kuma yaya aka yi suka zo nan da kuma matar nan ,
Sai kuma ta karra ido jin tana ce mata daughter, nan take ta shiga tunanin to ko da yarensu wani abun yake nufi ne? Ita fa sam bata gannin tsufan matar walahi hasalima matar ba wani jiki ne da ita ba sannan koda yaushe cikin shiga ta kamala take wace ko dis din gashinta ba'a gani bale a ga wani yannayi na tsufan, fuskarta kuwa bata kai wajen fara yaba ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 42