Share this page
hau suka karasa gaban amsa kuwar da aka tanadar da wani farin teburi dan dogo da tissu a ajiye da dan abin goge hannun nan A gefensa ya yi mata waje, a nan ta sauke dubanta a kan mutanen dake gabansu wa'inda suke tsaitsaye kowa cikin kyakyawar shiga irin tasu, watau mazan da suit, matayen kuwa daga mai dan bingilin sket, sai mai dan wando da riga dai da sauransu , haka kuma du sun saka huluna yawanci da dan flower a jiki mai kyau ba kalar na zuwa sutura ba Namijin dake tsaye da takardar da akai masa rubutu ne ya mike ya gabatar da barka da zuwa wa sarki da kuma sarauniyar kasarsu, tare da nuna tarin Flowers din barka da zuwa da aka ajiye masu da kara yi masa barka na daurin aurensa, da sheda masa cewar sun tanadar masa biki na musaman idan ya huta tare da iyalinsa Sannan ya bada damar a haudo surprise dinsu Ai kam wannan surprisd din da aka tanadar masu baki daya ba komai bane sai Mah da PAH ke turata a saman kujerar tura mararsa lafia, domin ba wai garas ne ta mike kai tsaye ba, sai dai tafoar ce bata iya yi da kanta sai a hankali Farin ciki, murna duka sun bayana a saman fuskokinsu, a hankali ya duka a gabam kujerar ya kama hannayenta a sanyaye ya ce" Mamanah" Mah ta hade daria da kuka tana shafa gefen fuskarsa sanann ta riko hannun Muneerath ta hade da nasa ta ce" Jarumina, albarkana " Su dukansu murmushi suka yi suka rungumeta, itama tana dan taping din bayansu sannan ya furta" Kin ga ya tirsasani ko?" Pah ya yi yar dariya yana karra kallon mutanen dake gefe da gefe Mah ta ce" Ya min adalci , ya cikan burina " Sai da suka gama farin cikinsu sanann ya samu kansa da maida kansa da kansa ya fuskanci al'umar dake sauraron bayanansa Dan murmushi ya yi ya karra duban wajen su Muneerath ya kafeta da ido kafin ya dan girgiza kansa a sanyaye ya ce" Tabas na ji tsoro mai karfin gaske a yan kwanakin nan da suka wuce da barazanar rasa mata biyu da suka fi soyuwa a zuciyata da duniyata ta tunkaro ni, sai dai gashi yau sunna gabana tare da ni sunna kuma saurarata, Ban san ko na cencenci zama sarkin kasata ba?, Domin ba dan ka zama prince ne zai zamana dole kai ya dace ka mulki kasarka, sai dai abinda ma koya a yan kwanakin nan sune sannin darajar lokaci, anfani da shi, mutunta dan adam, kare hakinsa, yabawa kokarinsa, talafa masa a dukan yinkurinsa, dan Adam yana da daraja ko wanene.......da wannan nake da burin Allaah ya dafa mani mu kasance a sauratar mulkin HANJA" Tafi aka kwasa hakan ya saka Muneerath kara wangale baki da mamakin shikenan hala?, To kuma shikenan su sun gamsu?, Murmushi ta yi itama ta tafa dan kuwa ta gama yarda jan mutun na yarda da kalaman baki ba tare da an gita masa rantsuwa ba, ba kuma sai an nuna masa alkur'ani ba, haka kawai sai mutun ya ce da kai ya rantse da kan babansa ka yarda Sosai ya ringa gaisawa da manyan kasar sunna masa barka, sai dai sam bai basu damar su kai kansu wajen matarsa ba, domin a yanzu baya jin in har zai iya hakura yana kallo wani ya rungumar masa hannun mata ko ya nemi hade kirjinsa da nata, sai a yanzu yake gannin lalle Pah yanaa gaskiya, a da sai ya ringa gannin kamar PAH din na wani irin abinda bai dace ba, aman a yanzu sai ya samu kansa dumu dumu da gudun hakan wa iyalinsa Sun dauki dan lokaci kafin su nufi gida a mota daya gaba dayansu, inda HANJA ke rike da hannun Muneerath yana dan shafawa a hankali haka kuma gefensa na hagu Mah zaune cikin kyakyawar shigarta ta abaya baka sidik mai kyan gaske marar kyalkyali A hankali Mah ta ce" Son, sai nake gannin kamar kana abu irin na mai kishi bayan kai ka ce ka waye baka san kishi ba" Da farko yi ya yi kamar bai jita ba, sai kuma ya yi dan murmushi kasa kasa ya ce" A da ban san menene so din ba, haka kuma ban san darajarsa ba, a yanzu kuma bana jin zan iya kawar da ido a kan matata Mah, ina sontaa kuma ina kisshinta sosai" Ko da suka isa gidan wata tarbar suka samu Sai dai a yanzu kiri kiri Muneerath ta kalli HANJA a lokacin da ta kula da irin kallon da Iman ke masa ta ji wani irin abu na mata yawo a kai kamar zata hau bori da kakausar murya kasa kasa ta ce" Walahi ba gaisuwar larabawa ba, ko ta su waye kar ka yi da mataan dake wajen nan, ka ga karma ka rike hannayensu HANJA, idan kuwa ka yi in ban je na gaishe da wancen bodyguard din naka ta hanyar rungumeshi ba ni ba yar oga bace, ai gaisuwa ce ka yi na yi kawai" Dan bakin nata da take maganar tana murmushi chau chau da shi ya kurawa ido kafin ya dago ya kafe sauran matayen dake masa oyoyo sunna jiran lamari na runguma ga kuma abinda mai shi din ta fada Sai kawai ya hade hannayensa da nata ya yi mata murmushi ya ce" Na zabi kowa kar ya yi, dan bana son farkon fara aikina na ba Tgr naman mutun ta ci, wannan ba adalci bane" Sai da gabanta ya fadi ta kale shi a zabure ta ce" Tgr, tana ina? Hala da kai take barci? Ni walahi ba zan iya kwonci da ita ba, idan kuma mukaa raba daki ai abin wancen fa da muke yi fa?" Daria ta kubuce masa har ya so ya kasa hanna kansa kokarin rukunkumeta , sai dai gannin da gaske yake ta tsere gefen Mah ta kama kujerar Mah tana dan turata sukai ciki ta barshi da bakinsa _______________________________________ Sarauta yake yi da nasa salon da tsare tsarensa cikin aminci da kwonciyar hankali inda mahaifinsa ke gefensa yana taimaka masa da dukan abubuwan bukata, Mah dinsa na gefe tana karra talafa masa da shawarwari da adu'a, sannan matarsa na gabansa tana bashi dukan kulawar da ta dace Karra kame kansa da yi , ya daina harkar biye biyen mata sai ya karra wanzar da lamari na shayi, da tsoron haye masa, harma da yawa kan masa ikirari da sunna *DUTSE AJIYAR ALLAH, KA FI KARFIN GARA* Iman ta kama kanta, ta kwatanta har ciwo ta yi sai dai fahimtar da ta yi ba yarenta yake ganewa ba, matarsa kuwa ta mayar da ita taamkar mahaukaciya domin har tsokanarta take tana kuma bata tsoron cewa zafa ta fada masa ita ta fada mata maganar mata, sai kwata kwata ta nemi danganaa ta yafawa kanta harma ta fara ba samari damar zuwa wajenta dan ta fitar da gwaninta tunda zamtowa sarauniyar ingila ya gagareta kiri da muzu Tashin hankali aka sha na rigimar aikinta Sosai ta tayarwa da kowa hankali har sai da aka sadata da Oga da Mamanta inda Oga ya ja doguwar rantsuwa ya dire kan cewa idan ta tagawa sarki hankali a kan rabe raben kayan abinci a cikin jirgi in ba sai ya biya jirgi da aljihunsa ba ya zo ya ci yan garin babarta ba Allah ya sa kar ya ci zaben zama mai anguwar anguwarsa da yake nema, idan kuma wasa take gannin yake ga babarta ta fada mata Ai kam mamantamaa maimakun ta saurareta sai ta rufe ido ta dora daga inda ya tsaya ta ce bataa cikin wannan shirme, Gannin dai zasu karra rikita masa abarsa bayan rarashinta yake, lalabat yake kamar kwai,, domin tunda Mah ta kwatanta masa ba ita daya bace haka kuma kar a yi ta sani dana kar ta hanna kanta sukuni duba da haki zanen rai sai ya mayar da ita abu mai darajar daa ya fi tatalawa fiye da komai a duniyarsa,, baya wasa da laamarin yar Oga, baya wasa da soyayar yar oga , itace ta farko kuma yana fatan ta birne shi Dan haka ya riko abinsa ya rungume a jikinsa sosai a sanyaye ya ce" Kin ga aiki ne da ni a nan, idan na ce zan bari na bijirewa Pah na koma tukin jirgi yaya kike so na gama da duniya ne? Ko har yanzu bakya sona bakya so na gama da duniya lafia ne?" Da sauri ta girgiza kanta tana karraa cusa kanta a wajen wuyansa a sanyaye ta ce" Hanja ina sonka fa " Idannuwansa ya lumshe dan jin dadin kalamanta, ta sha fada masa aman idan yana aikata mata aiki mai lada, a haka garas sai dai idan kubce mata maganar ta yi, A hankali ya ce" Muneerath ina son ki sosai" Dan murmushi ta yi a hankali ta ce" Shikenan ba zan kuma aikina ba?" Yana shafa mararta yana karasawa kusa da gadonsu ya dan haya sama da hannunsa wajen abinda yake son cinma ya dan shiga lailaya a hankali ya ce" Zaki yi, idan kina tafia da mijinki sai ki bani ruwa na sha, ki bani abinci na ci, sannan ki dafan bujenki........" Da sauri ta rufe masa baki tana jansa saman gadon suka fada da karfi sannan ta ja masu labulen jikin bed dinsu gannin ina tata son lekawa Daga wannan na kawo karshen labarina mai sunna DUTSE a page 70馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ Alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah *YAH ALLAH KA YAFE MIN KURA KUREN DAKE CIKINSA, KA BANI LADAN DAKE CIKINSA ALLAHNA* DUKAN MAI SON CI GABA DA KARANTA LABARAINA YA GARZAYO YA BIYA KUDIN NASA WATAU *WATA KOKOWAR* A NAIRA DARI BIYU KACAL TA HANYAR YIN TRENSFER KO TURO KATIN MTN IN SHA ALLAH GA NUMBER NAWA 93811618 SAJIDA 馃グ馃グ馃グ馃グ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 42 of 42