Share this page
masa ba A hankali ta ce" To kuma mah dan Allah kema ki gane mana, cen da cen fa" Mah ta dafe kuncinta a hankali ta ce" Muneerath wani mugun abin take yi ne iman din? Ki fada min kin ji yarinyata?" Hanja ya kalli yadda mah jikinta ya yi sanyi ya kuma maida dubansa kan Muneerath kafin ya girgiza kai ya mike ya juya rai bace ya sauka daga wajen cin abincin ya koma falo ua dauki wayarsa ya shiga kiran wanda zai kawo masa zakayarsa wace yau ya farka da wuri dan a kawota ya sakata a dakinta kafin suke hakura ya koma gidansa da abinsa A hankali ya dago dubansa daga inda yake zaune jin ana bubuga table din sannan maganarta na tashi sama sama ya sauke dubansa a kanta Gabansa ne ya yanke ya fadi daidai lokacin da ya ga Iman na tsaye tana ta rantse rantsen bata yi komai ba, a daidai lokacin ne Muneerath ta cire hular kanta ta ajiye a zafafe ta ce" Bara ki ga abinda take yi din an gaya maki tsoronaki nake da ba zan fadi ba ko kuma an saurayi muka hada da zan maki shari? Kin ga fa...." Lokaci daya ta shiga bankarewa gaba dayanta tana dan juya jikinta kafin ta daga hannunta ta cusa cikin gashin kanta baki mai kyan gaske ta lumshe idannuwanta ta turo kirjinta , lokaci daya ta bude ta daidaita tsayuwarta tana haki ta ce" kai Mah wani abin ba zan iya nunawa ba dan gaskiya ni ba yar iska bace, wai wani na yi haka ta dora saman dp a turawa dogari, tsakani da Allah soyaya ko iskanci?" Mah ta rafka tagumi a hankali ta ce" Iman?" Iman ta sada kanta hankalinta tashe ta fara magana da kuka kuka ta ce" Mah, ni fa ba haka nake yi da maza ba dan in taimaketa ne na ga ko sannin zamanta bai yi wanda take so din" Munnerath ta girgixa kanta ta ce" kuma a haka ne zai so nin? Baki san mu a garinmu sarkin garinmu na kirki bane? Su fa sarakan garinmu basa son yan mata yan iska, haka kawai in ya ganni ba sutura ai sarki ba zai sakama aurenmu albarka ba ko?" Iman zata bata amsa Mah a sanyaye ta dago hannayenta ta ce" ku taho, ku zo gareni ku zo kun ji?" Kallon junna suka yi Iman da Muneerath , Muneerath ta sakar mata harara da dara daran idannuwanta ta dan kebe bakinta irin ta murguda mata shi din nan , iman kuwa ta lumshe idannuwanta hawaye suka zubo mata a hankali ta sauke dubanta a bayan Hanja da ya gama kallonsu ya mike wannan karron ba a zafafe ba ya juya jikinsa a wani irin mace ya juya tamkar wanda bashi da laka ya fice a falon gaba daya A hankali take saukowa da hannayensu a cikin nata har sai da suka gama saukowa suka karasa kusa da kujerun Maimakun ta hau kan kujerun da su sai suka zame saman kafet ta tankwashe kafafuwanta ta saka su gaba su biyun Iman , yar budurwa kyakyawa mai shekara ashirin da bakwai, mai karamin jiki irin nasu mai ilimin boko da na islama, mai dama da yawa a gabanta Sai Muneerath kyakyawar yarinya karama yar africa, mai ilimin boko daidai gwargwado da na islamiya, yarinya mai tatare da abubuwan mamaki, wace du wanda ya karewa rayuwarta kallo zai yi imanin rayuwarta na tafe ne bisa tsarin ubangiji, tana matakin da take a yau ne dan Allah ya tsaya mata A sanyaye ta ce" Kun kuwa san Mecece mace?,iman da Muneerath ku bani amsa idan an ce ku fadi wacece mace wacece ita?" Kallon junna suka yi, Iman ta sada kanta a hankali ta ce" Mace na nufin halitar da Allah ya halita mafi daraja a cikin halitunsa na dan adam aman macenta " Mah ta tsura mata ido kafin ta kalli Muneerath ta ce" Muneerath ?" Muneerath ta sauke ajiyar zuciya , cen kasan zuciyarta sai tana gannin wani bambarakwai, yanzun a cema mah ga laifin da iman ta yi maimakun ta kama yi mata ihu ta zazageta ta mata rantsuwar idan ta dauko mata magana cen ita ta sani ta karata da abinta sai ta wani zaunar da su kamar wa'inda suka yi abin kirki tana masu tambaya a hankali? Ita rayuwar mutanen nan har yanxu mamaki take bata, rayuwar wancen rusheshen ce kawai take dan shige da ta yan jagaliya irin ta gidansu sak, dan ta kula shi daga an taba shi so yake ya warci mutun ya buga, ita kuwa Allah ta tuba me zai sa ta zauna wannan mai hannayen murda murda ya cin mata? Haka kawai ya karyata ya barta da dingishi? A hankali ta ce" To mah mace ana nufin uwa ko? Mu a cen in aka cema wada ba'ai mata aure ba mace sai a ce yaro wawa ne, a nan dai ke kadai ce mace mu nan du yan mata sunnanmu, ko me yasa suke cewa haka?" Mah ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi a hankali ta ce" Mace, Mace itace uwar al'uma....., Kun ga mace ita ke daukan ciki, ta raine shi a cikinta, cikin ikon Allah ta haife shi, bayan ta haihu ta shayar, ta bada tarbiya.....wannan itace mace, Daughter Mace ya dace ta kasance mai nutsuwa, mai sanyi, mai mutunci, mace ya dace ta kasance mai kare suturarta................idan aka samu uwa marar tarbiya yaya kuke gannin yayanta zasu kasance ?" Bata tsaya sun bata amsa ba ta kara riko hannayensa da suka kasance fari tas da kuma baki mai haske tana kallonsu ta ce" ina jin farin ciki idan na ga mace ta kama mutuncin kanta, idan kuma na ga akasin hakan hankalina na tashi sosai, du sai wasu tunani su shigo cikin kwakwaluwana, shin kun san kuwa Mace na iya cenza akalar mugun nufin namiji ya dawo kyakyawa kamar yadda idan da kyakyawan nufi ya nufota tana iya ja ya lalata mata rayuwa?, Mace na iya hadasa haka idan ta kasance mai watsa kanta, kece kika nuna masa ke da kanki baki sandarajar kanki ba dan Allah ta yaya zai san naki?" Wata ajiyar zuciyar ta sauke ta dauko wayarta ta ajiye a tsakaninsu a hankali ta ce" Wannan abar, wannan abar lalacin dake tare da ita ya fi rinjayar dan adam fiye da alkhairinta........., Ta dalilinta dubu sun lalace, ta dalilinta dubu sun afka muguwar rayuwa a likacin da basu ankara ba, itace ke shagaltar da musulmi wa zuba sallah a kan lokaci, ita ke shagaltar da mace a cikin gidan mijinta wa aikata aikace aikacen da zata samu lada, wannan da kuke ganni har hanna yaro zuwa aiken iyayensa take, a haka take jan yan matanmu suke daukan hoto su ba karuwai ba, su ba kilatatu ba su watsa ta yanar gizon da basu san ina da ina zai zaga ba, wa da wa zai gani? Idan a tunaninsu sun goge da suka goge din ina ya je ya zubu? Ya salam wasun sai a lokacin da za'a tara masu kasa komai zai fito........Iman, Muneerath shin me ya dace mace ta yi? Muneerath ta saka hannayenta ta dafe kuncinta a sanyaye ta ce" Wollah mah ko? Watarana sai na ji ko karatun bokon nan kamar iskanci ne fa?" Mah ta kaleta tana kara karantarta Muneerath ta ce" to Mah du abinda nasarun nan suka kawo kana shagalta kake dawowa dan iska" Iman rai bace ta ce" 馃檮馃檮馃檮馃檮 Ba dai ni ba kau? Ni kuka hanama nvl馃槶馃檮馃檮馃檮馃檮馃檮 11/14/21, 12:51 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 3锔忊儯8锔忊儯 Iman rai bace ta ce" Sai ki ringa cewa dan iska dan iska, yanzun da kika fadi haka a gaban prnc me kike so ya dauke ni? Da kike cewa yar iska ce ni da wa na yi iskanci?" Muneerath ta tsareta da ido kafin ta tabe baki kasa kasa ta ce" Ai shi dan iska ba boyuwa yake ba, kuma ni ina ruwana dan yayanki ya sani ai gwarama ya sannin ko zai iya maii fada in kina jin tsoronsa malama ki daina min fada wollah kin ga dai ba tsoronki nake ji ba" Iman dake share kwallah tana hararanta ta ce" Ni din tsoronkin nake ne? Duba ki ga fa fada ne kike tankwalar Yaya Hanja fa, salon ya hada mu daga ni har ke?" Muneerath ta zaro ido tana dafe habarta ta ce" Kuma ya mana me yo?" Mah ta saki murmushi tana kallonsu idan wannan ta dauki magana ta ajiye wannan ta dauka, gaba daya wani irin nishadi y'ayan ke sakata, sai take gannin y'ayan da bata samu bane a gabanta suke rigima irin ta yaya da kanwa, duda na Iman na mata nuni da wani lamari irin na kishi, na Munnerath kuwa tsabagen yarinta da magana kai tsayenta ke birgeta Gannin sai yi suke a sanyayenta ta ce" Ku saurara " Kallonta suka tsaya yi su dukansu Mah ta ce" Dan Allah ku kasance masu rufe suturarku , ina rokarku kan ku kasance masu anfanuwa da abin anfanar dake tare da waya, kar ku yarda dan ya zama sabo ga yan mata da mata da samarin da wasu manyan mazajen da basu san me suke ciki ba suka mayar da waya filin baja kilinsu kuma kuce haka zakuna yi da taku rayuwar....idan zaka yi abu ka fara tuna ubangijinka, ka tuna mutuncinka, ka tuna na ahalinka, ka tunana y'ayan da zaka samu idan Allah ya hukunta maka haka" Cikin lumana, a sanyayenta ba tare da hargagi ko iface iface ba, cikin ilimi da tarin nutsuwa ta yi ta yiwa yaren nasiha daga karshema sai suka haye sama suka tare a bangarenta suka shige kicin din falonta suka shiga yin cake wanda Muneerath ta bada hankalinta cike da farin ciki tana kallon yadda Mah ta gama kwabawa ta zuba a abubuwan gashi masu kala daban daban, duka tana kallo aka saka a cikin abin gashi aka daidaita lokacin gasuwarsa sannan suka dawo wajen hada cream na shafawa a sama wato d茅coration Wani ikon Allah, yau ta fara gannin yadda aka yi haddin cake , yau abin ya shiga cikin kwakwaluwarta ya zauna mata wanda take tunnanin idan tace zata gwada tabas zata iya yi domin idan ana koya mata girki sam ganewama nema bata yi bale har ta rike wani abin, aman a wannan itace harda su tambayar kowani kalar cake haka ake daidaita masa lokacin gashinsa? , Hakama a lokacin da za'a yi crm din sosai ta samu kanta da bada hankalinta da rike abin a ranta sosai, nan Mah ta zuwa clr yelow mai haske ba carrr ba ta yi decoration ma mai heart din ta dora wlcm Pah Sosai suka cika dare da yan matan, bini bini Muneerath na hankalce da irin yadda Mah ke zuwa ta yi kiran Pah ta dawo, hakama da akai kiran sallah ki second daya bata kara ba ta kora su yin alwallah suka saka rufafen sutura suka gabatar da sallarsu cikin nutsuwa Sai da dare kowace ta nufi dakinta Muneerath na kwonciya bayan ta yi wanka ta saka yar rigar barcinta ta kwonta ta zubawa clng ido A hankali ta lumshe idannuwanta a bayane ta ce" Shin haka dama wasu gidajen suke? Dama akoy iyayen dake daukan y'ayan wasu tamkar nasu? Dama akoy iyayen dake yiwa y'ayansu nasiha?, Dama akoy gidan da ake wuni a kwana ba'a dankara ashar mai zafi ba?, dama akoy iyayen da zasu ji y'arsu na kokarin son kauce hanya su zaunar da ita a dabara su mata nasiha?, A gidansu da aka ce tana fita yawon iskanci ne Mamanta mahaifiya cewa ta yi Muneerath matsalarki ce, in dan maza ne kuma wasu ba'a haife su bama, sai sun cinyeki ya babunki su yarda banza! Mahaifinta kuwa cewa ya yi: lale yar oga yanzun kema iskancin zaki fara ko meye? To dahuwar mutun mai kosai............!, A hankali ta juya tana lumshe idannuwanta tana tunano magangannun mah Inda take masu nuni da idan sun kare mutuncin kansu sun rufawa har ita marikiyarsu asiri ne, sun cireta a kunya A hankali ta dora hannunsa saman yar fulawar da Mah ta ajiye mata mai kanshi tana shafawa tana lumshe ido dan barci ke fuzgarta ta kuma duba tsarin rayuwa irin tasu......................... Ba zasu taba daina bata mamaki ba Dan murmushi ta yi a saman lebenta kasa kasa ta furta" Inama ku farga ku gane mecece duniyar? Inama ku jawo mu a yanzun da lokaci bai kure maku ba? Inama ranar da zan dawo gare ku na tarda kabarin kun neme ni har kun yi kuka? Dama ina dawowa na tarda a gidanmu an fara bambance yaya da kani? " Kanta ta dan girgiza tana ta hangi badakala irin ta gidansu Ba ruwan kowa da kowa Ba abinda ya dami wani dan wani na cikin hali na mugun yannayi Ba ruwan kani da jin kunyar yayansa ko kuyaye wulakanta yayansa Sai a dambatu uwa ta shigarwa yayanta fada a daki dan mijinta dan abokiyar zamanta dan son kai irin nata koda kuwa yaron nata ne baida gaskiya Cike da tunani irin haka ta samu barci mai nauyi ya yi gaba da ita aman wayarta ta ma'aikata a kune kuma da sabis koda kuwa kira zai iya shigo mata a kowani lokaci dan a shaida mata idan tana da tafia Ragaitacen barci ta yi a washe gari, ba ita ta fito daga bed dinta ba sai da Mah ta yi shiga ta hudu tana dubata domin ko kari ta ki ta fito ta yi tana sheka barcinta a nutse Gaban mirror take tana dan masaging din wuyanta da take ji ya rike mata kadan A hankali ta dauki abin jan baki ta dan gogama lebenta mai ruwan ja Kurawa fuskar nata ido ta yi yadda takr sheki, a hankali ta shafa gefen fuskar nata tana bin jar rigar dake jikinta da kallo, rigar sakakiya ce sosai kuma doguwa ce har kasa Jan bakin da ta saka ta sa hannunta tana gogewa , sai dai ba mai fita kwata kwara bane domin ya bara mata sawunsa kadan ana ganni Turaren ruwan dake ajiye ta dauko a hankaki tana dan fesawa a wuyanta da jikinta Lumshe ido ta yi dan turaran wani irin sanyin kamshi ne da shi , kafin ta bude idannuwanta tana kara kallon yadda idannuwanta suka karra kyau masha Allah Cikinta da ta tabata yinwa ta gama cinsa ta shafa a hankaki ta mika hannu ta dauki mayafin rigar fari ta yafa a saman kanta kafin ta juya a nutse ta saka silifas irin tada biredin nan mai ruwan ja ta saka ta bude dakin a hankali ta rufe tana tafe tana dan danna wayarta tana kuma kallon gabanta Accenceur din ta dana ya bude ta shiga a hankali tana kara lumshe idannuwanta kafin ta dana kiran sir da ta tarar ya yi mata kusan kira shida Bayan ya daga a hankali tana tafe sunna magana Sir ya ce" Muneerath yar gata, plz ina son gannin ki yaya za'a yi?" Muneerath ta yi murmushi ta ce" In ba sir ba yau kwana uku kadai fa da muka rabu, wai ko dai an koreni a aikin ne na ga ba'a kirayeni ba har yanzu" Daria ta bashi dan haka ya dara yana gyara zamansa a gaban ruwan da ya gama iyo ya ce" Muneerath, kin fi karfin a kore ki a duniyar jirgi" Muneerath ta yi murmushi itama a hankali ta ce" To ka zo mana" Ido ya dan zarro yana gyara zamansa a sanyaye ya ce" Ni banma kai cen ba, na gankima ko ta vidio call be ya wadatar, an fada maki shigowa gidan na yiwa kowa sauki ne kamar naki?" A hankali ta fito ta nufo falon a sanyayenta ta ce" A shigowa nan ne da wahala? Gidan da ko dogarai masu tsaron kofa babu sai wasu dirka dirkan mutane rike da wukar wasa?" Yar daria ya yi a hankali ya ce" Plz, ki barni na ganki ta vidio call, nine fa freind dinki?" Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta dago dubanta ta sauke a kan Babar kujerar da ta kyautata zaton akoy mutun a zaune kuma ga dukan alamu ita ya kure da duba domin a jikinta take jin idannuwansa, Ido cikin ido suka kalli junna na kamar second goma kafin ya cire dubansa daga kanta yana kara hade fuskarsa tamkar zai kurma ihu dan bacin rai A hankali ta hadiyi yawu kafin ta murguna bakinta itama ta cire dubanta hankali kwonce ta nufi ratsawa dan zuwa saman table ta ci abinci a sanyayenta ta ce" freind, ka bani number oga mana dan Allah, da shi nake kwana nake tashi, a kasan zuciyata yake" A hankali ta dora kafarta daya ta fara hawa, Hanja ya dago dubansa daga cirewar da ya yi ya sauke a saman kanta cike da wani mamakin waya take a gabansa bata ajiye ba, bata gaishe shi ba, idonsa idonta sun kalli junna ba bata ganshi ba Idannuwanta ne suka sauka a kan Tgr dake kwonce a saman matatakalar tana kada wutsiyarta kanta a kwonce ta dan turo kafafuwanta gaba kadan irin dai yannayin da take kasancewa a ciki yawancin lokuta da dama idan tana zaune a kusa da uban gidanta, watau ta fi sakewa ta ringa kai kawo tana kada bindi tana kwonciya tana tashi tana juyi abinta hankali kwonce Wayar dake hannunta ta saki lokaci daya cikinta da ba komai ya juya a bayane ta furta" Muhamadu rasululahi salalahu alaihi wa salam, innalilahi wa ina ilaihi raj'une wayo na mutu na lalace" Daidai lokacin kuma tgr ta kula da mutun ce a gabanta Irin mikewar da ta saba ta yi hakan ya kara fitar da dukan girmanta da takamarta lokaci daya ta girgiza ta girgije ta juyo da nufin nufo Muneerath dan ta sinsinata ta ga ko ta santa ne ? Idan bata santa ba kuma ta dan tsakura a jikin nan nata Wani ihu Muneerath ta saka ta yi fatali da dan kwalin, da takalman a guje ta juyo wajen da Hanja ta harde kafafuwansa yana kallonsu ita da Tgr yana jira har sai tgr ta dan zagayata kamar sau uku kafin ya dakatar da tgr din domin idan ta gane bata sanka ba far maka take, a gidan ta san kamshin Mah, na Pah, na iman, na dukan wani da ya dace ta sani, sosai ya so ya ga yaya zasu wanye, sai dai bai yi aune ba, bai taba kawowa ransa ba, bai taba hasaso zata iya daga kafarta daga gaban tgr din ba, baima shirya tarbota haka a kwana kusa a jikinsa ba, sai jinta kuka ganninta ya yi ta yi wata uwar sufa ta dane jikinsa tana kwala ihu idannuwanta sun firfito gaba dayan Muneerath dare dare a saman cinyarsa zuwa yanzun ba salati da salalamin take yi ba ihu ne take yi bilhaki ta rike wuyansa da dukan karfinta ta ce" Zaki ne, zaki ne, ka ganshi kuwa zaki ne.................." Da wani uban karfi ta kara shigewa jikinsa gaba daya jikinta na wani irin uban bari tamkar zata side a lokacin da ta waiga ta ga Tgr din a jikinta domin tana kasowa da gudun biyota ta yi da wani irin gudu, sannan da ta ga ta dare uabn gidanta gaba daya yannayin masifa ne ya taso mata ta harzuko da niyar dafkarta ta saka shi yin abinda bai shirya ba domin hannunsa ya saka da sauri ya yi mata nunin da yake mata idan yana son hannata aikata wani aikin da baya so hakan ya sa ta ja birki kafin a hankali ta karaso ta shiga sinsinar Muneerath tana shafa kanta a jikin cinyarta da ta bayana dan dirka kokowar da take tana ihun za'a kasheta Wannan juyowar da Muneerath ta yi ta ga ga kan zakanyar nan ga cinyarta ya sakata nutsa kanta a kirjinsa kafin ta sauke wani dogon numfashin da daga shi ya ji dif gaba daya jikinta ya saki A hankali ya dago hannunsa da ya masa wani irin mugun nauyi ya nufo shi kusan gashin kanta da ya bazu a jikinsa , lokaci daya kuma jikinsa ya dauki bari hakan ya sa zabure ya...... 11/14/21, 12:51 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 3锔忊儯9锔忊儯 Ba san da wani baki zan gode maku ba馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀, ban cika azarbabin magana ko kurantawa ba, aman wollah idan ina tare da ku ko parrot zai ganni nan ya barni nan Allah ya saka maku da alkhairi baki dayanku, Kunna da yaea sosai walahi Kuma alkhairi ne ya hada mu Gaisuwa zuwa a gare ku yan uwa al'umar gidan DUTSE, tabas kuna saka ni nishadi duda kasancewata karama a cikin marubuta mai tatata sai kunna sakani jina wata gingirmemiya, ba zan ce komai ba sai fatan alkhairi Allahu ya datar da mu baki daya Hakkun *DUTSE AJIYAR ALLAH NE, DUTSE YA GAGARI GARA馃槍..............DUTSE YAKE SHI HANJA* Lokaci daya kuma jikinsa ya dauki bari , ya zabura da ita a jikinsa ya mike tsaye da ita din a jikinsa kafin ya juyo wajen kujerar gaba daya hannayensa na masa raea ya shinfideta saman kujerar A hankaki ya idasa mike tsayinsa tsaye zurbat kafin ya shiga bin hannayensa da suka tada gashin hannu da kallo watau tsigar jikinsa da ta mike gaba daya lokaci daya kuma ya kara sauke dubansa a kanta wace take kwonce rigar nan ta yi sama sosai wajen cinyoyinta a fili haka kuma wajen kafada guda ya yi kasa sosai hakan ya ba dan saman kumburaren mamanta ya dan bayana kadan Gashin kanta da ya yi lumbuk ya kuma tsura mata ido yana kallo da gashin girarta har zuwa wajen kanta A hankali ya waiga ya kuma waigowa gannin ba kowaa falon ashe sai shi kadai, gaba daya tunda ya fitar da tgr Mah ta gudu, dama iman idan yana zaune ba wajen take zuwa ba hakama masu aiki kowane yana wajensa a labe ba wanda ke dan kai kawo koda dan su yi kakabe kakabe ne Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yake dan baya baya Tgr kuwa na kusa da Muneerath din tana kara sinsinarta Wajen wayar tafi da gidanka ya je yana dan murza gaban goshinsa ya daga a hankali ya dora number bangaren Mah Dagawa ta yi tana salama aman kuma ya kasa buda bakinsa ya bata amsa hakan ya sa take ta hello? Hello? Aman shiru ba amsa ba alamun za'a amsa Ajiyar zuciyar da yake saukewa idannuwansa rintse yana son yin magana ya kasa ne ya saka Mah jin gabanta ya fadi A tsorace ta kalli wayar , abu daya ya fara diro mata a rai shine bashi da lafia, gashi kuma zaune kusa da zakin nan .....gabanta ne ya kara tsinkewa ya fadi da gudu gudu sauri sauri ta warci wayarta ta yi kiran dakin s茅curit茅 dinsu tana fadin" Maza maza a leko wajen da prnc yake me yake yi?" Domin gaba daya wani banzan tunani ne ya darsun mata kar a je tgr din ta haukace ta cinye mata d'a Da wani gudu ta idasa shiga cikin accenseur din ta dana ta lumshe idannuwanta tana ta adu'a a kasan zuciyarta jikinta kuwa na bari Daidai ta bude ta sako kanta cike da tsoron halin da zata tarda yaron nata, kwata kwata ta kawar da tsoron tgr din zata shigo wajen ne ko wace wace ta dano kai da dan sauri tana karasawa falon Shi ta fara ganni a zaune dangalgal saman cafet din falon, kafarsa daya a mike dayar a tankwashe, tgr a jikinsa ya rungumeta yana shafa gashinta yana kuma kallon Mah da ta taho Ja Mah ta yi ta tsaya tana kallonsa,a sanyaye ta ce" Khalb, me yake faruwa

Chapter 22 of 42