Share this page
kallonsa, ta riga ta gama tsara cewar tana zuwa gida zata fadawa Mah abubuwan da suka faru a nan, idan ya so sai a san abin yi domin bata so ko daya a ga laifinta, sannan a gaskiya tana komawa zata nemi da a maida ita gida wajen nata iyayen ya isa hakanan yawon taburadar! A hankaki ta mike ta karasa kusa da kwalin Sai da ta kuma satar kallonsa kafin kasa kasa ta ce" Kai yinwa nake ji, shi kuma sai waya yake kamar tsohuwar karuwa yana lumshe ido, gaskiya ci zan yi ina dalili mun fito dan mu yi ciye ciyenmu ka kawoni nan kuma ka manta cewar mutun ce ni" Kwali daya ta dauka tana ta adu'ar Allah ya sa ta kaza ce, ba ta alade ba! Ai kam sai da ta idasa dubawa ta gane ta kaza ce sannan tana fara dandanawa ta ji dandanon kaza sai ta saki murmushi ta dauko ta zauna ta shiga ci tana tunanin ta wannan kampanin ba dai dadi ba Da idannuwansa yake binta da kallo, baya jin abinda take fadi idan ta yi hausarta a nan, a gida ne du ya saka abinda zai kai masa sakon kalamanta ya fasarce masa a lokacin da yake mata kallon terrorist, wanda ya yi niyar sunna komawa zai cicire dan a yanzun ya gane cewar ba terrorist bace, haka kuma ba ta makale masu bane dan ta ci dukiya ko wani abin ba, ya gane cewa hukunci ne na ubangiji kasancewarta tare da su a irin wannan lokaci, sai dai kuma dayan abin yana da tantama a kan kwakwaluwarta Irin yadda take kara gyara zamanta tana daukowa tana ci ya sak shi shagala da kallonta, kafin a hankali ya ce" I'm seek Mah " Mah dake ta jero tambayoyi kan ina yarinyar mutane, me ya sameta, menene wannan hotunnan da yanzu Iman ta kawo mata tana kuka? Me ya kai hannunsa nan dinta a waje public ? Me ya sameta? Tana ina? Ta ji amsarsa cewar bashi da lafia sai ta samu kanta da sasauta muryarta a hankali ta ce" Kana clinik ne? Me yake damunka son?" HANJA ya sauke ajiyar zuciya a hankaki ya ce" ina gidana, kuma gatanan" Mah ta kai zaune saman kujera a sanyayenta ta ce" Kana nufin kana tare da Muneerath ? Dan bani ita mana dan Allah?" Idannuwansa ya kuma saukewa a kan Muneerath , a hankali ya nuno mata wayar kafin idannuwansa cikin nata ya yi gyaran murya a lokacin da ta dago dubanta tana kallonsa a saman lebunnansa ya ce" Mah " Muneerath ta taso da sauri tana kallon bakin nasa a ranta tana ayanna 'To ko dai wani ya dakar masa leben ne?' Amsa kiran ta yi da sauri a tsaye a kansa kafin kuma lokaci daya ta shiga kai kawo , sai kuma ta ja ta tsaya tanarike da kugu da hannunta daya idan Mah na magana daga Mah ta yi shiru sai ta ciro hannun nata ta shiga bata amsa tana kai kawo tana nunawa da hannunta yadda ka san tana gabatar da wani shiri hankalinta kwonce tana kara nunuwana da hannayanta shi kuma yana biye da ita da ido yana hasko dukan abinda take fadi da irin yadda ya faru da irin nunin da take kamar Mah din na kusa da ita kafin ta kare maganarta da fadin". A gaskiya ni dai ban san ko me yake damunsa ba, idannuwansa dai kamar ya sha kuka , aman kuma bakinsa kamar yana masa ciwo dan dazun dai yana dan magana yanzu kuma ta dauke dif, sai kuma kamar ransa a bace yake, to dai abin nasa ni dai Allah ya sa kar ya motsa ina kusa, a yanzun dai da dama fushin ne ke dan nuna kansa aman Mah abinda na fada maki kaf iya gaskiyar kennan na jiyan nan kadai na san na tsero wajensa kuma ashema ba samansa na fada ba dan na farka na ganni saman kujera, na yau din nan ne kawai na kula cewar kamar bayan ya taban gefen kafada sai ni kuma na rike shi dan ya ceceni daga zakin ashema zakin na wasa ne?" Mah ta ringa sauke ajiyar zuciya tana ta adu'a a kasan zuciyarta kafin ta ce" Yarinyata kina ji?, Ki kula kin ji ko? Ki karra rike mutuncin kanki, idan ya kara tabaki ne abin zai iya tabatuwa kin ji ko? Dan Allah ki kiyaye sallah a kan lokaci, sannandaga an yi ki fada masa ya yin shima kin ji? Kuma yanzu ki sa ya nemi likita dan bashi da lafia kin ji?" Muneerath ta amsata kafin ta maida masa wayarsa ta kuma tsaya tana jira ya kare Sai da Mah ta idasa maganarta yana sauraronta a hankali ya amsa mata kafin ya kashe kiran ya daga dubansa a kan Mubeerath da ta ce" Yauwa Mah ta ce ka ga likita baka da kafia, kuma dai ka tashi ka yi sallah nima bara na gama cin nawa abincin sai ka nunan bayi " Zuwa yanzu lamarinta ya daina bashi mamaki, sai dai dam baya tunanin zai daina binta da kallo dan ya gane ita din wace irin halita ce? Yana nan zaune ta gama, ta miko masa jus din ta ja ta tsaya ya bude ya mika mata yana kallonta ta koma gefe ta saka bakin dan kwalinta wai kar ta hada baki ta sha iya shanta domin bashi da gaz haka kuma bashi da karfi sai ta ji dadinsa a bakinta sannan ta ajiye masa a kusa da shi tana fadin" ga naka " Shi da da ido ya kuma rakata har ta nufi bayi sannan ya mike yana tafe a hankali ya nufi wajen da wrdrb dinsa yake ya buda yana bin kayan da kallo dan ya dan jima rabonsa da garin Sai da ya yi adu'a sannan ya dauko wasu tufafin ya ja ya tsaya har sai da ta gama ta fito Bai kulata ba , aman kuma ya ajiye mata abin sallah ya nufi bayin Da ido ta bishi kafin ta gyara ta tada sallarta Tana saman salaya kanta sade ta gama sallar aman kuma tana ta istigfari ya fito ya fita a falon daa sauri ta bishi da kallo ta waiwaiga cikin dakin kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba da adu'arta A fitar Hanja wajen motarsa ya nufa ya ciro salaya Sai da ya gabatar da sallarsa cikin nutsuwa kafin ya ninke salayar ya shige motar ya nufi kampanin da jirgin nan yake A lokacin da ya karasa aiki ya hau tukuru sannan a tsanake , hakan ya sakashi cire du wani tunanin dake damunsa, ba shi ya gama ba sai cen kusan jarfe biyun dare Daga nanma hotel din nan ya wuce ya je ya dauko abubuwansa da basu da yawa sannan ya bude nata dakin Bin dakin yake da kallo a nan dai ya dan bata lokaci domin sai da ya shiga bayi ya ga kayanta na uniform da ta wanke ta shanya a bayin, ya hado brush dinta da soson wankanta kafin ya fito ya dauki jakarta ta baya ya shiga ninke kayan yana sakawa a cikin jakar har ya zo kan pant dinta Da sauri ya dan zarro ido sai kuma ya girgiza kansa yana yatsine fuska tamkar ya ga abin kyankyami ya cusa mata shi a jakar ya zuge zif din sannan ya cire wayarta da cazarta ya nufi kofa yana dadana wayarsa ya tura kira a lokacin da ya zauna cikin motarsa A kausashe ya furta kalmomi kamar haka" tashin safe zamu yi" Daga haka ya kashe wayarsa baima gama jin ok sir din Sir baya tada motar ya nufi gidan a ransa yana fadin'Na san yanzun ta yi summa goma, yarinyar sam ba hankali a tare da ita' A lokacin da ya karaso har karfe uku ta gota A hankaki ya idasa shiga falon da yake ciki daya ne kwal sai bayi sai wajen tufafi, akoy gado aman idan ba sani ka yi ba ba zata taba sannin akoyshi ba domin a cikin bangon yake A hankaki yake takawa ba tare da ya cire takalminsa ba har ya idasa kusa da cafet din dake ahinfide fari kal Ido ya tsura mata, irin kwonciyar da ta yi da dan nadewar da ta yi A yanzu dan kwalin baya jikinta haka kuma gashin kanta ta cire ribom din jiki, a kusa da ita kuma dayar pizzar ce ta bude ta ci iya cinta ta bar sauran a nan, sai jus din da ta kara ta ajiye sauran A hankali ya duka kusa da ita ya kai hannunsa gefen wuyanta ya taba Hannun nasa ya dago yana mai karra binta da kallo, abu daya ke masa yawo a ransa.....shin bata da lafia ne? Me yasa du sanyin garuruwan nan ita kulun jikinta da dumi? Bata da lafia ne? Aman idan bata da lafia hakan na nufin tun ba yau ba fa? An samu circonstanc da yawa da hannunsa ya kai kan nata ko wani waje na jikinta ya ji dumi a jikin nata Jakarta ya ajiye mata ya karasa ya dana wajen bed dinsa Bed din ya fito mai dauke da yan gida gida a jikinsa Budewa ya yi ya ciciro zanin gado ya nufi wajen Muneerath dake kwonce A hankaki ya samu kansa da warware guda ya rufa mata shi kafin yake kara zubawa fuskarta ido sai kuma ya mike a dan zabure ya yi wajen bed din Bai cire kayansa ba ya haye saman gadon yana shafa mararsa tare da dan rintse idannuwansa ya juya bayansa ya shiga adu'ar baci kafin ya ringa bitar karatu a kasan ransa ko zai samu barcin ya dauke shi Shi ya kwonta ba da wuri ba, kuma shi ya rigayeta tashi domin motsinsa ya farkar da ita A hankali take kara wara dubanta a kansa yana zaune yana opprat din laptop a saman kujerar da bata san a ina ya daukota ba Kayan dake jikinsa a yau farare ne kar kar masu shegen kyau irin na Pilot Sun karra haska fatarsa sun masa wani irin kyan da ya birgeta har ta samu kanta da sakin murmushi tana kallonsa tare da dafe kuncinta a bayane ta ce" Kai kamar mutanen da ake nunowa a TV wollah, kai kam ka ringa shan maganin baki kar a cinyeka" Sai kuma ta kai dubanta da sauri wajen kofar da sauri ta zabura ta mike tsaye tare da nufar bayi da dan gudu gudu ta shige ta rufe bayin Hakan ya saka shi bin bayanta da kallo kafin ya dan girgiza kai Yana ta aikin nan ta fito ta dauki kayanta dake cikin jakarta dan tana farkawa ta fara gannin jakar ta kuma komawa da wayarta tana karanta cewar nan da minti talatin zasu tashi ta kuma duba lokaci ta ga har tara ta wuce da sauri sauri ta saka suturarta sannan ta ciro hijab dinta na sallah ta tayar da sallar bayan ta gama gungunnin yana kallonta ana kiran sallah bai tasheta ba Sai da ta gama sallar sannan ta kuma daukan wayarta, nan ta ringa gannin message din Mah tana ta afkin tambayoyin nata kafin ta fada mata yau Birthday dinsa ne sun shirya masa dan karya karya surprise kar ta sanar masa Dan bakinta ta tabe a kasan zuciyarta tana ayana'Ku yi shagalinku kudi ke maku kaikayi' Tana nan zaune ya mike yana rufe Laptop din ya dauke shi a hannunsa dama ba jona shi ya yi ba ya dan kaleta ya sakar mata harara gannin kale kalenta take hankali kwonce ko yar gaisuwar nan bata yi masa ba ya cira kansa ya shiga tafia Da sauri ta mike gannin a shirye yake, sannan ta ga an saka lokacin tafiyarsu tana biye da shi tana hararar keyarsa idan ta daga kanta a ranta tana ayana' Bakin hali ba zaka min magana ba bayan ba gaba ba muke, sai me karma ka min wollah nima ai ba yi makan zan ba malan mu dai je garin namu a maida ni kasata ya isa hakanan a zamana da kai ba abinda baka nuna min ba, bindiga ce, shaka ce, hankada ce, ka kunto min zaki, ka ajiye min zaki duka kaf dan ka halakani Allah ne ya tsaya min kuma na san zai kare ni' Sun yi tafia cikin nutsuwa da kwonciyar hankali kamar yadda suka zo Pilot din su biyu ne , dayanma fararan kaya ne jikinsa , kuma bakin fata ne mai fara'a, yana tafe ne da nufin ya karra gogewa a harkar tafia, sai kawayenta da Sir wanda tuna suka dawo ido kawai yake binta da shi, yana jiran su kadaice ya isar mata da sakon zuciyarsa, shi kam wannan lamari na bashi tsoro da ba dan ya ga abinda aka rubuta a shafin masarautar cewa ba matarsa bace ba budurwarsa bace bama kawarsa bace yarinya ce da mamansa ta dauko Hostess ce bayan wannan ba komai a tsakaninsu ya dan samu nutsuwa ba da shima gaba daya hankakinsa ya tashi da lamarin A baban dakin da suke haduwa ya yi maganarsa ta karshe kan kowa ya rike wayarsa a hannunsa suka shiga gaba dayansu inda Muneerath ta kebe baki ta dan karkace gannin da duhu a dakin duda basu saba gannin haka ba ta hade fuska tana rike da hannun Saudat ta ce" Bara ki ga yadda zai yi daga ya shigo" Ta dan yi gaba ta dawo ta ce" fuska kamar kunnun safe zai kalle mu ya ce" Kun dawo daga aiki,aiki kuka rafi yi, kun yi kun sauka hakan baya nufin ba zaku samu kira a kowani lokaci ba, idan kira ya same ku ku amsa ko ku samu takardar kora". Ta karashe tana kebe bakinta ta ce" kamar wani aikin shiga aljannah" Saudat dake daria kasa kasa zata yi magana tare da mamakin duhun wajen ta yi gagawar ja ta tsaya gannin gaba daya wajen ya dauki wani irin haske da walwali yana walwalwalwalwal Da sauri suka karta wara dubansu sunna kallon lokacin da HANJA ya shigo tare da wasu ma'aikatan gidan lokaci daya dakin ya dauki dan sanyayan kida irin nasu na taken sarakan garinsu mai hade da wakar Happy birthday, sai kuma yan matan da suka shiga rawa su shida rawar iri daya ne da alamu cholegrafi suka shirya suka hardace abinsu Yan matan masu kyan gaske farare kal kal kal sunna takunsu cikin tsari sunna juyi hakan ya sa sauran suka kama tafi duka ana dan taya rawar ana taya wakar ta hapoy birthday din w HANJA wanda ya ja ya tsaya tunda ya shigo yana kalonsu baki daya fuskarsa bata bayana me yake ji game da da abinda ake yi ba, aman ga dukan alamu ya ji dadin hakan domin da bai birge shi ba da ya yi tafiyarsa A hankaki Muneerath ta fara gyada kai, dan lokaci daya ta ringa jin wakar na shigarta sai kuma ta ga rawar da suke sam ba haka ya dace su yita ba, rawar da ya dace su kada su juya su rakarkashe su kai dan idi idi su kara a gaban makadi sai wani jimke hannu suke maimakun su bada kala su saki jiki su tafki rawa ba A hankali ta janye hannunta daga cikin na saudat dake murmushi Ita kanta bata san abin ya debeta har ya karasa da ita tsaka tsakan rawar ba sai da ta yi kamar juyi hudu ta kula da ana tafa mata kamar yadda du wace ta yi abin bajinta ake tafa mata ana shan dariya da morewa ba sai da idannuwanta suka sauka a kan fuskarsa ne gabanta ya fadi lokaci daya kuma ta nemi tsayar da kanta rawar ta kasa a lokacin ne aka shiga turo katon cake din da aka yi masa mai yannayi da jirgi masu rawar na tikar rawarsu masu tafa gannin cake din na tafawa har aka kusan turowa gabansa inda yake tsaye kikam tamkar idan ya budi baki aman wuta zai yi na bacin rai da kuma jin haushin shirmen yarinyar nan da ya gama yiwa jawabin ta kama mutuncin Mah dinsa itace ta cire da rawa a cikin mutanen nan A hankali ya daga kafarsa zai karasa inda take, daidai wani lalausan hannu ya shiga cikin nasa , hannun mai dauke da sanyi da kuma laushi sai kamshin turaran da ya dakeshi hakan ya saka ya juyo da dan sauri dan gannin ko waye lokaci daya idannuwansa suka sauka a kanta, A hankali ya lumshe idannuwansa ya kuma budewa ya kai dubansa kan hannun kafin ya dagoda wani yannayin na ya shaka ya budi bakinsa ya ce" 11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 4锔忊儯4锔忊儯 Ba edditing.................. Kasa kasa ya furta" Sake min hannu " Hannun nasu itama budurwar ta bi da kallo kafin ta saki a hankali ta sanyayar da muryarta sosai ta ce" Me ya hadasa maka bacin rai a rana irin ta yau? Ranar birthday dinka my prnc?" A hankali yake binsu da kallo sunna yin duku duku suka fice ita da saudat Kafin ya kuma bin Sir da kallo wanda shima ya silibe ya fice da dan sauri ya yi gagawar maido dubansa jin PDG na yi masa happy birthday tare da gayatarsa ya karasa ya yanka cake din da ma'aikatar ta yi masa dan su yi surprsd dinsa abinda da yadda nasara ya ba cikon shekara mahinmanci , irin yadda du wani baba a wannan kampani harma da wahen kampanin suka gayato ya kuma amsa gayyar, irin yadda suka kayata wajen ya kayatu yake walwali A hankali ya daga kafarsa ya nufi wajen cake din bayan ya yi iya yinsa ya tataro du wata jarumta ya yabawa fuskarsa tare da sakin lalaisan murmushin da bakinsa lebensa a likacin da baban sojan dake kula da lafiyarsa da kuma yannayinsa yake dan fada masa cewar ya saki fuskarsa dan hotunnan mdia ya dan lumshe idannuwansa zuciyarsa cike da jin haushin lamari irin wannan da yawancin abu za'a saka ka yi ba dan radin kanka ba sai dan kawai ka birge wani , kuma ya zame maka wajibi ka yi duba da irin yadda mahaifinsa ya kawo sunnansa ya dora kan wanda zai gaji kasarsa A hankaki ya taka ya tsaya gaban cake din, masu dauka na dauka, manya manyan ma'aikatan suka saka shi a tsakiya a hankaki ya dora yar siririyar wukar da aka bashi ya dago dubansa ya kai wajen da take dirka rawa kafin a hankali ya kai hanyar da suka bi wace bai san waje zata fitar da su ko sunna ciki ne tare da wannan katon da kuma kawar nan tata da aka fito yau ta fara aiki tare da su A hankali ya maida kan cake din ya dan saki wani murmushin kafin ya yanka cake din inda aka shiga tafawa "Freind, " ta fada muryarta a sanyaye a lokacin da suka durfafo palace din aman suka ja suka tsayar da motar ya juyo da dubansa muryarsa a sanyaye ya ce " Muneerath, plz..........saudat ki saka baki ban san me yasa take damuna da maganar Dogari ba" Muneerath ta kuma kallonsa ta juya ta kalli Saudat wace ta sada kanta tana dan murmushi, dama ta san a rina, walahi ta gane son Muneerath yake ba yau ba, aman ta yi mamakin da bai fadi ba sai yanzun A hankali Muneerath ta ce" Dogari, Freind me yasa kake so na bar maganar dogari a rayuwata ?, Ka kuwa san tun ina yar karamata nake dakon wannan buri?" Da dan sauri ya ce" Buri ne ba bukatar zuciyarki ba My Muneerath, shin zama zaki yi ta yi kina jiran kila wa kala? Ko kina tunanin kina iya ba wani dake sonki damar ku yi soyaya?" Muneerath ta kuma satar kallon Saudat, haka kawai take jin bata son maganar ta yi nisa sosai , aman ya ta iya su da suka kasance a mota daya a nan bata tunanin zata waske A hankali ta ce" Buri na ne" Sir ya kara kureta da ido kafin ya ce" Ni kuma kece burinahhhhhhhhhhhh my Munee" Sai da gabanta ya fadi, da sauri ta kura masa ido da wani irin duba tana jin zuciyarta na bugawa a hankali a hankali kafin ta cire dubanta tana kallon waje Ta kasa gane a wani hali take, Ta kasa gaskata kunnayenta Ta kasa gane a yanzu a wani yannayi zata ajiye wannan rana Wai ita? Ita Muneerath yar kuryar dakin kauyen anguwarsu, itace ta hadu da daukakar ubangiji a yau har ta samu furucin so daga bakin mutun mai daraja irin sir? Sir ATTAHIR musulmi ne, mutun ne mai tausayi da taimako, mutun ne mai girmama mutane mai girmama talaka, ya kasance mai bata talafi a kowani yannayi take ciki "Dan Allah, bana so ki bani amsa haka kai tsaye, bana so ki so ni dan wani dalili daban, ni ina son ki, kuma ni gani a gabanki bana so ki daidaita ni da mafarkinki, Muneerath ni realty ne, Muneerath ina son ki........idan dai ba wani ya rigaya ya fito wanda ya fi karfina ba.......bana tunanin zan iya barinki a kan tsumayi da kike, My munee idanma so kike na je na saka rigar dogari zan saka na rike sanda irin na dogari dan na amsa sunnan miji a gareki" ya karashe yana kara sanyayar da muryarsa yana kallonta Wani irin yuyu take ji a kunnenta,wani irin lamari mai wuya fasara ya kara ziyartarta Meye aibun SIR? Meye zai saka ta kasa aminta da shi ? Ahi din baban mutun dinta ne Shi din mai tausayi ne A hankali ta ja hancinta dan ji take kamar iskar ta mata kadan A sanyaye ta ce" Haba sir" Sir ya karra tsatsareta da duba kafin ya kuma cire idamnuwansa a kanta yana kallon Saudat ya ce" Ko dai ta kamu da sin wanina ne?" Saudat da ta ji wani shaukinsu na dibanta ta ringa murmushi a hankali ta ce" Ka bamu lokaci da kawara na san zamu bada amsa mai kyau, ka karasa da mu gidan sai mu nemo amsa kwana kusa" Ajiyar zuciya ya sauke ya kuma kura mata ido ya ga sai dantse hakorinta take, a hankali ya tada wuleliyar motarsa ya fara tafia motocin Hanja suka wuce da wani irin gudu gaba dayansu suka nufi eriyar palace din A lokacin da suka karaso sai da ta fito ta nuna cd dinta kafin ake basu shiga damar shiga daga ita sai saudat bayan Bodyguard dinta sun karaso da sauri sunna fadin a cen suke basu ganta ba suka biyo tawagar Sir tuna ya ce su dawo tare Ita dai bata da karfi, a hankali ta juya ta bi motar Sor da kallo kafin ta saki dan murmushi sunna shiga ta saka ihu harda dira ta riko hannun Saudat ta ce" Wayo na shiga uku, Saudat Freind fa? Freind ya ce yana sona?" Saudat dake murmushi tana ta bin tsarin Palas din da kallo cike da kauyanci duba da yaune rana ta farko da ta sako kafarta albarkacin albarkaci duda irin yadda kafafuwanta suka taka kasashe daban daban ta kuma kai ziyara da mahifinta da yake baban mai kudi a wazaje daban daban sai nan din ya zame mata abin kallo harma ta kasa boye kauyencinta take ta juyi tamkar zata kifa Muneerath ta tabata tana girgizata ta ce" Kina tare da ni kuwa? " A dan firgice ta rike hannun Muneerath ta ce" Munnee mu gudu, kalli yadda sojawa suke baje a gidan nan, kina gannin da makamansu da wadinnan kannanun jiragen droon din dake yaeo san kanmu sunna iya rufemu da harbi fa a kowani lokaci aka bukaci da su yi hakan" Muneerath da bata san asalin aikin dronn ba , ita dai a tunaninta du isa ce ta mai kudi ya saka suka zuba kannanun jirage sunna masu yawo a cikin gifa ta ce" Ke wadinnan sojojin bafa bindiga bace a hannayensu yar wukar roba ce, kuma wadinnan jiragen na wasa ne ai" Ido saudat ta zarro zata yi mata magana ta yi gagawar hadiyewa sakamakon sojan da ya nufo su furkarsa hade ya ja ya tsaya a gabansu fuskarsa hade ya shiga tambayar da wa

Chapter 25 of 42