Share this page
ne?" Idannuwansa da sukai masa mugun ja ya rintse a hankali kafin ya bude ya juyar da dubansa ya dora kan Muneerath dake kwonce Itama duban nata ta kai wajen, lokaci daya kuma ta zabura tana salalami ta karasa da mugun sauri tana kokarin dago Muneerath tana fadin" Me ya sameta? Meye meye haka? Bata motsi fa innalilahi wa ina ilaihi raj'une, son kama min" A hankali ya girgiza kansa daidai mutanen cen sunna neman izinin shigowa Da gudu gudu suka shigo sun kai soja goma aman da shiga ta suit a jikinsa kowane kuma da dan abin kunne a sakale a kunnensa haka kuma da bindigoginsu , kosasu ne, masu tsafta ne, dakarun Hanja kennan Du tsayawa suka yi daga nesa sunna masu tambayar halin da ake ciki me yake faruwa Mah da sauri ta dago ta ce" Ku kira min likita bata da lafia ne " Da sauri babansu ya basu umarnin du su fice kafin ya yi gagawar tabo lititan gidan Kafin kace meye wannan har sun karasa shigowa Sunna idasa shigowa su dukansu fara ja suka yi suka tsaya domin da Hanja suka fara yin tozali kafin ifannuwansu ya sauka a kan Tgr dinsu Gaisuwa suke kai masa a ladafce domin kuea kaf dinsu basu da karfin kokowa da yannayinsa sai dai su ja su dan tsaya A hankali ya sauke dubansa a saman kansu kafin ya dauke kansa daga kansu ya kuma maidawa wajen Mah dinsa A kasan zuciyarsa ya rasa tunanin meyake yi?? Meye ya tsayar da maganarsa me ya hanna harshensa sarafuwa ne? Me ya hanna masa kalaman da zai fada ne? Ta yaya zai iya buda bakinsa ya nunawa Mah irin bacin ran da yake ciki, ta yaya zai fada mata yarinyar nan a dumbin tarin raahin kunyarta itace yau harda hawan masa jiki dan kawai Tgr ta nufota? Ba zai dauki komai ba, bama zai gane komai ba, Rai bace ya cire dubansa a karro na ba adadi yana kara rike Tgr dake jikinsa tana hawansa sai dai bata nufi kowa ba dan tunda ya mata hannin nan ta hannun kennan fa Likitan ne.......... 11/14/21, 12:51 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 4锔忊儯0锔忊儯 Likita ne namiji docter ne da yake ja gaban likitocin palace din, Da sauri mutun uku ke biye da shi dadauke da yan abubuwan kawo agaji na kusa kusa Sai da chef din s茅curit茅 din nan ya caje su kafin su karasa wajen da Mah ke zaune rungume da Muneerath hankalinta tashe tana dan share hawaye gefe da gefen idannuwanta Dayar ce ra kama Mah dan ta taimaka mata ta dan matsa su duba Muneerath din Kwontar da ita suka yi saman kujerar suka aaunata Da sauri ya bukaci da a kawo masa oxyg猫ne domin ifan mutun ya suma wannan shine dama mafi sauki da ake yiwa mutun dan ya dawo da hankalinsa idan bai samu numfashi bane ake zuwa ga allurar karin ruwa wace ke dawo da mutun ana kiran da abubuwan nan R茅animation, idan ya ja dama ne ake kara daukaka bincike dan gannin abinda ya hannaka dawowa a hayacinka Wannan karonma basu dauki lokaci sosai ba sai gasu nan tafe da dukan abubuwan da ya bukata Mah na zaune gefen HANJA ko nace dan face da shi tana kallonsa Gaba daya a zaunen nan da yake zakin nan a jikinsa yake , kansa a saman kirjinsa, shi kuwa yana shafa bayansa ne aman kuma tsuru idannuwansa a wajen inda likitocin nan suke tsaye cikin nutsuwa sunna aikinsu, a hankali ta maida dubanta wajen likitocin ta ga irin yadda dukansu babu mai kwakwaran motsi sai da dalili du kuwa dan yana wajen ne kafin ta kara maido dubanta kansa a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana kara kureshi da duba dan burinta so take ta karanci abinda ya samu yarinyar nan dan ta kula dikim din ya tashi Irin yadda mutun ke farkawa a tsorace yawancin lokutan summa hakan ne ta faru da Muneerath wace dama a tsoracen ta summa sai kawai ta dawo a firgice bayan ta kwala ihu ta nemi rarumar wanda a tunaninta har yanzun a jikinsa take hakan ya sa da sauti likitan nan ya kama damatsunnan hannayenta cikin yaren turanci da rarashi ana taimaka masa dan kar ta cire abin numfashin da aka saka mata ya kara kusanta jikinsa da nata sosai a cikin aikinsa ba da wani abin ba yana kara dan matsar da ita kan kujerar yana fadin" Shuiiiiiiiiit, is ok, ya isa haka ba wani abin da zai kama ki, ki nutsu kar ki cire abin hancinki" A hankali ya bi hannayen likitan da cinyoyinsa dake kusa gak da gak da nata, Idannuwansa ya yi gagawar rintsewa jin irin dukan da zuciyarsa ta masa da bai san ko na wani daukar maganar bane Cire dubansa ya yi daga bangarensu ya juyo kann Mah dinsa Idannuwanssa ya lumshe a lokacin da suka yi ido hudu da Mah wace ta wara nata duban tana kallon yadda idannuwansa ke nuni da ransa a matukar bace yake A hankali ya mike tsaye daga zaunen da yake hakan ya sa Tgr ta ringa zagayarsa tana kada bindinta hankalinta kwonce domin ita kam nata bukatar a cike yake tunda gata ga uban gidanta Wajen agogo ya kai dubansa kafin ya juyo yana kallon Mah a hankali kuma ya juya ya nufi bangarensa inda Tgr ke biye da shi yana tafe a hankali kamar yadda jiya ya fita a hankali jikinsa tamkar ba lakkah ko daya Da ido ta idasa raka shi kafin ta sauke ajiyar zuciya ta koma kusa da Muneerath sosai tana kallonta ta rike hannunta tana shafa gashin kanta a hankali ta ce" Ki yi hakuri yar albarkana, ki daina zaburar nan" Muneerath ta lumshe idannuwanta tana kallon Mah kasa kasa muryarta ta ce" Mah?, Zaki ne ya biyo ni" Mah ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Ba fa zai cije ki ba, kin ga ai Hanja na nan ba zai bari ya cije ki ba" Sai a lokacin nan hoton wanda ta rukunkume ya shigo idannuwanta, cike da takaicin kanta ta jimke hannun Mah ta rintse idannuwanta da karfi hankalinta tashe tana jin haushin kanta Zuwa lokacin ne wayarta ta dauki tsuwa, Mah ce ta mike ta dauko mata ita cen yashe domin likitocin sun tafi, tana jujuya wayar tana kallon yadda ta ratatake da kyar ta iya daga mata ta saka mata ita a handsfr ta miko mata kafin ta kuma zama a hankali ta dagota tana mata apkin sannu ita kuma sai kara langwabewa take tamkar zata fasa kuka bayan ba abinda take ji a yanzun, da gaske ne a dan rikice take ta ji tsoro dazun sosai aman yanzu da ta ga Mah a kusa da ita sai take jinta cikin nutsuwa dan haka kawai take ji babu abinda zai kuma tabata a gaban Mah ciki harda danta, langwabewar nan kuwa da take gani ta yi kamar da wasa dan bata da lafia ne ake tatarotan nan to ai kuwa Mah ta shiga uku domin ita dai zata yi ta kwonci ne tana zuba iya shege, aman gabanan kafarta kafar Mah dan ta kula dan Nan na Mah bashi da lafia, sam ita ko wa zai ce mata yana da lafia ba zata yarda ba, yaya mutun mai hankali zai yarda ya ringa wasa da ransa? Haba dai walahi ita dai da ranta da hankalinta ba zata yi kawance da zaki ba! A hankali ta amsa muryarta a sanyaye Daga dayan bangaren aka shaida mata cewar tana da tashi karfe biyu na dare Da sauri Mah ta amshi wayar ta datse tana fadin" Ba zaki tafi ba yau kam, ke da baki da lafia?" Wani irin mikewa Muneerath ta yi tana kallon Mah ta dan girgiza kanta a hankali ta ce" Haba mahna, wollah nu kalau nake kin ga? Kalau nake Mah, zan iya barama na je na dan rintsa kadan kafin karfe goma dan Allah mahna ki tasheni wollah dan suma ne mu a garinmu da za'a maka dukan mutuwa kuma a sakaka aiki ka yin kuwa bale suma a kwonce cikin nutsuwa ? Wama ya san ko Niger zamu sauka na ga Oga? Mah plz ga wayata dan rike min bari na je na huta" Da gudu ta yi wajen accenceur, Mah ta rakata da kallo baki bude Dan murmushi ta samu kanta da saki tana girgiza kai da mamakin kokarin Muneerath din, sai ta ajiye haka a matsayin yarinta ne , dan yarinya ce ya sa da ace wata baba ce ta suma yanzu ai ba inda zata iya zuwa, kai bama zata iya aikata komai ba sai dai a ringa mata sannu Mikewa ta yi a hankali ta kurawa hanyar da zai sadata da bangaren yaronta So take ta san me ya faru? Yaya aka yi Muneerath ta suma a kan kujerar da yake zaune? Me ya kawota inda yake zaune? Ba dan komai take son sani ba sai dan tabatar da tsaro a tsakanin yan matan nata da yaron nata, sam bata zarginsa da komai suma haka, aman zata kasance mai taka tsantsan a tsakaninsu dan gudun tasiri irin na shedan ya yi karfi a tsakaninsu Komawa ta yi wajen accenceur da yar karamar wayarta da kuma ta Muneerath a dayan hannunta ta dana ta yi kiran matar dake kula da Camerar gidan Cikin nutsuwa ta shaida mata tana son vidion da ya wakana nan da awa biyu, sannan ta nemi da a kawo sabon phone ....... ........wannan kennan........... Ruwa ke zuba a jikinsa, idannuwansa a bude suke ruwan na ratsa masa idannuwan aman baya rintsewa kuma baya kiftawa har sai ya dauki dan lokaci kafin ya kifta din A hankali ya karadaga hannunsa dan so yake kwata kwata ya daina yi masa dan barin da yake masa Gannin ya daina kwata kwata ya jimke hannun nasa ya sada kansa yana hararan jikinsa cike da jin haushin wannan rashin kunyar, mema aka yi da har zai nuna kansa? Gannin zai bata lokaci sosai gashi zasu yi tafiar kwana biyu cif ya saka shi daura alwallah ya fice a bayin Sallah ya fara gabatarwa ta la'asar a dakinsa domin lokaci ya shige bai yi ba kafin yake karasawa wajen kayansa da yar wayarsa a hannunsa ya rubuta message ya tura a VIP na matan da yake dauka ya tura Tsai ya yi da ifannuwansa yana tuna magangannunta A hankali ya lumshe idannuwansa yana jin kansa ya fara daukan zafi........"BAKA JIN KUNYAR MAHALINCINKA? KA YI AURE, KA YI AURE" maganar da mah taje yawaita fada masa "IDA AKA CE DA KAI MEYE HUJARKA ME ZAKA GABATAR? RASHIN MUHALIN AJIYEWA NE, RASHIN KUDIN SADAKI NE? KO RASHIN LOKACIN BATA NE? KA JI TSORON ALLAH KA YI AURE"............ Idonsa rintse ya daki madubin jikin wrdrb din da karfin da ya saka madubin zubowa gaba dayansa kasa Bai kula da hannunsa ba ya dauki wayar a takaice ya rubuta sako kamar haka "A BARI!" Ya tura kafin ya juya a hankali ya nufi wajen bed dinsa Kwata kwatama sai ya fasa tafiar ya nemi wajen kwonciya inda tgr ta haye saman itama tana gyarawa ta kwonta kusa da kafafuwansa ya yi adu'a ya fara neman barci karfi da yaji cike dajin haushin abinda shi kansa bai san dalili ba..........ya fi ajiye hakan a gurbin rainin da wannan yar african ta masa, ta rasa wajen hawa sai jikinsa ? Ta rasa wa zara ringa cirewa kai sai shi? Lalema! Dukan abinda ya dace a yi an yi sun kama hanya tafia ta cikin dare ce wace bata da nisa sosai domin duka duka awa hudu ce ta sauke su a kasar da zasu je Wannan karronma dakunnansu suka shige suke hutar da gajiyarsu , sun samu isashen barci domin a garin ne zasu yi kwana har biyu kafin su juya dan akiy jirgin da zai duba wanda ya kakare a cikin garin ya ki tashi yana kampanin gyaransa , kasancewar jirgi ne da kampaninsu ya kera sai aka nemi da ya zo ya ga meye matsalar idan ba sai an kai jirgin Ingila ba sai kawai a fadi matsalar a kawo kayan gyaransa, idan kuwa sai an kai shi dole a ga ta wace hanya ya dace a kai shin Shi dinma wani barcin ya nema dan zuciyarsa a cinkushe take duda ya samu sun yi hira da Mah ta masu rakiya da wannan bakar har a茅roport dan ta ga yaya jikin yarinyar yake wai ita bata yarda ta yi tafia bata da lafia ba kamar wata yar goye har sai da ta ga tana tsalanta ta bi yan matan da zasu je tare hankali kwonce kafin tabara masa amanarta ta koma gida, aman haka kawai ransa ke bace har yanzu Ya sha barcinsa sosai, ko da ya farkama sai ya zame dakin motsa jiki dan kuwa sanyin safia ne Sai da ya gama motsa jikinsa kafin ya dawo dakinsa Zuwa wannan lokacin mararsa ta masa wani irin nauyi sosai, hakama jikinsa du a mace yake, babar bukatarsa ya sauke jarabar dake tare da shi Wani wankan ya sake sai ya dauki tufafinsa ya saka, watau jalabiya fara kal sannan ya dauki hirami ya dora a kansa domin kasa ce ta larabawa duda ba kowa ke irin shigar hakan ba, aman du wani musulmi shigarsa kennan, shi kuwa dama yana son shigar nan ba wai baya sonta ba Caf茅t茅ria ya nufa da kansa dan so yake ya je ya hada hadin lemun tsami ya sha ko zai dan samu rlif, idan kuwa ba hali to ya sada kansa da asibiti ya amshi na hadiya dan kuea ya rantse bafa zai yi ba wannan karron , to yama ce wa ya motsa shi? Aikin banza aikin wofi kawai! A lokacin da ya tura gilas din wajrn ya sanyo kansa, kamshi ne irin na kalolin abinci duda ba a nan bude ake dafawa ba aman kasancewar waje ne mai daukan jama'a koda yaushe, wasun har an kawo masu nasu abincin shi yasa dakin cin abincin baya rabo da dan kanshin abinci duda ana yawan kula da hakan Sai sanyin Ac karara da ya dake shi, sai ko idannuwansa da suka sauka a kan mutanen dake ciji yawanci table mai dauke da mutun biyu ne, sai mai dauke da mutun daya, sai daidaiku masu dauke da mutane kamar uku, ko hudu haka irin dai abokai sun zo, ko familly haka Komai na wajen kalar fari kal ne, da idonka zaka ha tsafta ke jan ragamar wahen hakan ya sa bai juya ba ya dan fara tafia a hankali har ya karasa wajen zaman mutun daya ya tsaya yana kallon kujerar kafin ya ja a hankali yana mai yin bisimillah ya zauna saman kujerar A hankali idannuwansa suka dago dan son gannin wa'inda ke gabansann nann da yake jin sunna ta kyakyata daria sunna hira kamar su kadai ne a wajen,gashi kuma muryar mata biyu ne da namiji guda Gabansa ne ya kwonci kwonci ya fadi a lokacin da ya yi arba da Muneerath d take facing dinsa, sanye da bak'ar Abaya ta yane kanta da bakin dan kwali, ta saka dan kwalinta sai ko dan lip a bakinta tana kallon namijin da bai san ko waye ba sai bayansa ne kawai ya gani yana maganar da ta saka wace ke kusa da namijin bushewa da daria ita kuma tana sanye da wando da riga wace sam bai gane cewar a cikin Hostess din take ba Lokaci daya ya ringa jin tamkar mai ciwon huka wani abu na masa yawo a gaban kirjinsa, idannuwansa na yin wani farfarfar kamar sunna son kaishi duniyar summa Ransa ne ya ji yana tafasa a lokacin da ya tuna cewar Mah fa amanar yarinyar nan ta bashi shine dan ta raina mutane daga saukarta a garin da ba nata ba ta dage take irin wannan abin da kartin maza? Ina wannan ba irin rikon Mah dinsa bace, ta kuwa san wacece Mah? Yarinyar nan ta san wani irin tarbiya Mah ke badawa? Dama shi ya san yarinyar nan munafurcin dake tare da ita ya fi zama saliharta yawa, gatanan dai gaban kato tana ta sakin murmushi to me take nufi ne? Me take nufi ne? Sunnan gidansu zata bata bayan da sunnaN Pah a saman takardarta ta aiki hakan ya sa aka sakata a dukan tafiar da shi zai yi? Kansa ya cire daga kansu a hankali yana sauraron ma'aikaciyar wajen tana tambayar command dinsa Wani balarabe da yake ta kallonsa dan yana son gabe wai shine ko ba shi bane ya taso ya karaso a nutse ya yi masa salama tare da miko masa hannu a bayane ya ce" Prince tun dazu nake son gane wai prince HANJA ne a wajen nan ko ba kai bane, ashe kai din ne?" Da sauri Hanja ke dan masa alamu na kar ya tona shi dan gudun masu son daukarsa hoto da masu son yi masa magana yana yi yana kara girgiza kansa dan ya gane , sai dai ya makaro, domin mutanen da yake kallo da mamakin su waye tare da ita sune suka fara juyowa cikinsu na juyawa a hautsine balema Sir da bai ga shigowarsa ba ya shagala da kallon halitar da yake bege ba dare ba rana yana shan dariyar hirarsu shima yana basu daria ya ji cewar uban gidansa ne a wajen Sai ko Muneerath dake zaunenta aman itama dubanta ya kai inda yake zaune Kafin kace menene wannan kamar yadda a kasasen waje kasasen turawa da larabawa ake yiwa manyan cele da kuma manyan masu kudi, balema masu mulki ko sarakai taruwa a kai idan aka gansy a wajen public ba dan a masu maula ba sai kawai dan a samu saka hannunsu ko a samu hoto da su, idanma aka yi rashin sa'a da yan jarida a kusa yanzun zasu yayameka kuma sai yadda Allah ya yi da kai ne idannuwanta suke kallon abin mamaki gannin nan da nan ana ta son a samu yi masa magana aman Sir da mutumen nan sun hakikance sunna tarewa tare da kakarewa dan shi dai ba yawo yake da gardawansa ba tsere masuma yake dan baya son takurar nan, ya yi fitowar nan ne dan ya samu ya huta shi kadai da ransa Kai Hanja ya girgiza yana sauke ajiyar zuciya a hankali ya mike yana dan tafia ta inda suke ta kokarin gannin sun kare shi A hankali take kallon yadda yake matsowa inda take zaunenta ita daya abinta bata tashi ba, haka kawai ta ji gaba daya yana neman cika mata ido dubansa na neman gagararta domin idannuwanta ne ta ji sun fara rawa rawa take jin kamar ya fi karfin kallonta kai tsaye A hankali ta cire dubanta a kansa, sai dai bata sada kan ba sai ta mayar da duban nata gefe A yan sekwani ta ji lalausan hannu fari kal mai dauke da birda birdan jijiyar da bata san haka hannun yake ko yanzu ne suka tashi ba sannan wanda ya fi girman nata nesa ba kusa ba ta ji ya kama tsintsiyar hannunta ya....... 11/14/21, 12:51 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 4锔忊儯1锔忊儯 Hannun nata ya warta a lokacin da ta afka a duniyar tunani ba tare da ta ankara ba ya damka ya kuma mikar da ita Ido ta kwalalo domin da dayan hannunsa ya saka a wajen kugunta ya karra mikar da ita sosai ya matso da ita dan daf da shi kafin kansa a gefe ya shiga tafia da ita da dan hanzarin da ya saka ta saka katabus sai tafiar da yake yi kawai da ita har ya fice a cafetariar baki daya kafin ya bude motar da ya zo da ita ya turata ya zagaya da dan sauri ya bude ya shiga ya tayar ya harba kan titi Idannuwanta a waje suke, gana daya numfashinta sama yake yana kasa da wani irin sauri tana wuki wuki sannan ta kasa zama waje daya sai ta yi kamar zata kama ta bude sai kuma ta ji hannayen nata sun kwashi wani irin bari tamkar ba zasu iya dannawa su bude mata ba Haka tana ji tana ganni ana watsa masu hotunna Sir na tsate yana binta da kallo hakama Kawarta Hanja ya ja motar nan ya yi gaba fa ita Wani masaukin ya nufa da ita, wanda yana tsayawa ya bude motar stil bai tsaya ya yi jiran ta fito ba ya kuma damko hannunta ya nufi ciki da ita Wajen dauke yake da dan fili daya kwal zagaye da gilas da alamu shine zagayen gidan wanda baya hanna a ga mutun dan yana ciki haka kuma wajen kamar shi kadai ne kwalin kwal a ajiye Ciki ya nufa da ita ya saka hannunsa ya danna cod din wajen kafin ta tura ya bude ya shige da dan sauri da hannunta wanda take ji zuwa yanzu tana ga ta karye nema Da dan karfi ya hankadota da hannun nata da ya riko, hakan ya da ta yi gaba tagal tagal ta je ta kifu a kan kujerar dake falon kafin ta dago a firgice tana kallon irin hararan da yake binta da shi Makwar ta hadiye yawun wahala tana jin kamar zata hira ta gudu dan tsoro ne fal a kasan zuciyarta na yannayin wannan mutun Kai kawo Hanja yake da wayar a hannunsa android yana ta tunanin yadda zai yi da ita A hargitse ya juyo kanta a lokacin ne kuma kira da message kala daban daban ke shigoea wayarsa Kiran ya fara dagawa domin na lauyan gidansu ne Shiru kawai ya yi yana sauraron abinda lauyan ke fadi cewar ya ga hotonsa yanzu yanzu an dora da wata wai matarsa ko budurwarsa duniya na son karin bayani, shi da baya yarda a dora hotonsa irin haka da mata menene kuma ya hada shi da aikata hakakodai budurwar tasa ce da gaske? Hannunsa ya daga ya kai wajen goshinsa ya dafe cike da takaici ya ce" AA " Lauyan nasa ya ce" Ok ina zuwa bara na dakilar da yade yaden sannan na ba yan jarida amsa, domin sunna ta tambaya ne dama kana fita waje ne ka yi yawo da mace a sake baka yi a kasarka? " Kit Hanja ya fara kashewa da sauri ya shiga yanar gizo dan tabatarwa kansa Hotunna kaloli ne aka yayada a wannan dan mintunnan har ya zaga ya kai wajen manyansa A hotunnan wa'inda suka fi bashi haushi sai wa'inda aka nuno karara ya riko kugunta da kuma dayan hannunta kam sannan ya janyota jikinsa sosai kafin ya fara tafia da ita Tabas du wanda bai san ba wani abu tsakaninsa da wannan yarinyar ba dile zai ce wata dinsa ce Da takaici ya ajiye hoton a gabanta ya zauna ya rafka tagumi yana kallon yadda take binsa da kallo a zaune dangalgal kafafuwanta a hade waje daya gaba daya jikinta na bari bari tana kallonsa a mugun tsorace, gashin kanta a fili dan dan kwalin ya zame, zufa ta jika gaban goshinta hakan ya sa gashin nata ya liliku a gaban ganta , sai idannuwanta dake yawo a fuskarsa da dakin , wannan kwayar idon ta kara girma tana ta yawo a jikinsa Hannayensa biyu ya rafka tagumin da su a lokacin da shi kansa bai san tagumin ya yi ba yana binta da kallon haushi da tunanin yaya zai yi da ita Ransa bace, sai dai muryarsa da sanyi ya ce"me ya kawo ki rayuwata? Wani ya aiko ki ne ki hada min ciwon kai?" Muneerath ta yi gagawar girgiza kanta tana kallonsa ta hade hannayenta ta ce" Walahi ka ji na rantse maka ni ba wanda ya turo ni, ka manta kaine

Chapter 23 of 42