take tare, yaushe ta dauki rdv din shigowa gidan nan? A wajen wa ta samu damar hakan?
Da mamaki Muneerath ta budi bakinta ta ce" Aman giya ka sha yauma kau? Yanzun dan zan shigo da kawata sai ta bi layi kamar wace ta zo maula ko wani abin?......"
Yana niyar mayar da kawar tata baya akai masa magana a blootoof din dake kunnensa hakan ya sa da sauri ya dakata kafin ya juya ya basu hanya inda Muneerath ta girgiza kai ta ja hannun Saudat da jikinta ke rawa na tsoron wannan drnnn din dake saman kansu sunna biye da su
MAH dake tsaye cike da mamakin yannayinsa ga irin tarbar da sukai masa sam bai basu damar gabatar masa da murnar taya shi cikar shekararsa ba ya shigo a wannan hargitsen falon gaba daya, tunda ya shigo kuma ya aniya surfa masifa yana nuna mata waje cewar bashi da damuwa aman kar ta kuma bashi amanar yarinya marar hankali du ta hada masa ciwon kai, ta yi meye, ta yi meye, itace harda shigewa cikin maraya hostesss tana tikar rawa bata gannin irin jikinta ta wani silale ta bi Attahir shine ya kawo su har gidan nan, toh lale zai kori Attahir din idan har shi aikinsa ya lalata y'ayan mutane ne ko kunya baya ji yace yana me da dalibarsa? Bayan ya san abinda ya fi tsana kennan shine yake masa a kampanin kasarsa? Tare da wata cen da ta raina mutane?......da karaji ya karashe wanda maimakun ya tayarwa da Pah Hankali sai kawai ya zauna saman kujera ya dora kafa daya kan daya yana kadawa yana ta sakin murmushi, inda Iman dake tsaye rike da wani Plate da Mah ta yi zanen Happy birthday da wani walkiyar abu da hotonsa a jikin plate din ta yi kasakai jikinta na rawa coke da tsoron fadan da yake yi
Mah a sanyaye ta ce" Son, menene ya daga maka hankali har haka.......son me yasa abin ke taba maka har kasan zuciyarka?"
HANJA da a tsayen nan yake ji kamar zai yi fifike da bacin rai ya shiga fadin" Me ya batan rai? Ni sa'anta ne da zata gudu ta barni a cen ta tafi bayan ke kila ce amana na kular maki da ita?, Salon wani abin ya tsoratata ta rukunkume Attahir ta suma? Haka fa take yo fa rukunkume mutumen dake kusa da ita take yi fa! MAH na gaji! Na gaji!"
Pah ya yi gagawar cije lebensa na kasa yana dan rauda kansa yana danne dariyar dake cinsa
Mah kam hankalinta ba a kwonce ba, tsakani da Allah baya fada haka, baya tada jijiyoyin wuya haka ya ringa bambami bale a irin wannan ranar da suke fita gaba dayansu su wuni sunna farin ciki tare? Hakan ya sa a hankali ta mika hannunta ta riko nasa ta ce" Idan mutun ya tsorata ai dole ya kama wanda ya fi kusa da shi kau? Laifi ne a cikin hakan?, Son ko rike ATTAHIR din ne damuwar?"
Rai bace zai yi wata maganar lift din da ya ajiye au suka fito Muneerath ta bude kofar falon tana kyakyata daria da hausa ta ce" Wai ni yar bakar gidan Oga? Allah zaki yi ki gama ni na san ba wani sona yake yi ba yanzun yace min wasa ne , tsakani da Allah ina ni ina kai kaina inda Allah bai kaini ba?????????"
Turus ta yi gannin mutumen na halin, ana ta wani riko masa hannu gabjeje da shi yana bautsewa ko wa kuma ya taba shi oho馃し鈥嶁檧锔 , , ta dan yatsina dubanta a lokacin da suka yi ido hudu ta ga kamar wanda ya harareta kamar mai jin haushinta, a kasan zuciyarta ta ayana' to shi dai idan ba kasheni ya yi ba , ba zai daina min hararen makiyiyarsa ba!'
ta kamo hannun saudat da ta tirje cike da jin tsoron gannin Sor HANJA na wajen ashe, da kuma matsanancin mamakin yau itane a tsaye a falon sarkin kasar nan da matarsa harma da baban dansu kwalin kwal jal , ta janyota da sauri suka nufo su ta budi baki kasa kasa ta ce"
11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
4锔忊儯5锔忊儯
Kasa kasa ta ce" Ke dillah ki saki jikinki kin wani kankame mu je mu runringume sun, wai a nan fa sai ka rungume mutun, aman walahi kar ki rungumi maza ni dai ba ruwana sai mu je dakina na fada maki abinda Mah ta ce da lamarin maza"
Ita dai Saudat, kiri kiri take kallon ikon Allah, a lokacin da tana tsate Muneerath ta idasa jikin Mah da farin ciki ta rungumeta a cikin jikinta ta bata peck tana mai farin ciki da fada mata ta yi kewarta kafin ta zana mata irin salar da aka yiwa HANJA a cen, ta karashe da fadin ita kam yanzun kuma bata san wa ya bata masa rai yake fada ba
Tana nan tsaye ta ga irin bahagumen rungumar da ta ba Iman ta rada mata cewar fatan dai yanzun an daina iskanci?
Sannan ta karasa ta duka har kasa ta gaishe da Pah wanda abin mamakin ya dafa kanta ya saka mata albarka yana ta sakin murmushin da ta rasa ko na meye kafin ta tashi tana kallon hannun Iman da ta yi kici kicin gaba daya yannayi na bacin rai da tashin hankali sun tataru sun nuna kansu a tare da ita ta tabe baki ta ce da Maj zasu ke da kawarta aminiyarta ce tun niger sai yau Allah ya sada su ta fito itama yanzun Hostess ce, inda Mah ta gyada mata kai domin gaba daya hankalinta a kan rigimamenta da ya zama kamar status kawai bin Muneerath din yake da kallo har abin na bata tausayi
Har sun fara tafia Muneerath ta daka birki ta dawo tana murmushi ta kalli wannan ta kalli wancen, a hankali ta kara kunnenta a kusa da Mah wadda ta yi tsai dan sauraronta , sai dai dama Muneerath ko rage murya ta yi ba wai iya rada ta yi ba domin bata iya yinta cen kasa ba ta ce" Mah wayo Allahna, Mah sir dinmu wannan freind din nawa da na fada maki shi kadai ne abokina namiji a duniya wai yace wai wai......."
Sai ta rufe fuska tana ta murmushi kafin ta juya da gudu ta ja hannun Saudat ta nufi lft da ita ta danna suka shige inda Mah ta saki dan murmushi bayan ta raka su Muneerath da kallo cike da sha'awar sakalcinta da yarintarta har suka gushewa ganninta kafin a hankali ta maido dubanta kan HANJA
Sai da gabanta ya fadi,
Gaba daya fuskarsa ta gama hadewa tsaf haka kuma fuskar ta yi wani irin ja
Huci yake fitarwa wanda yake nuni har gaban kirjinsa
A hankali ta kara mika hannunta ta matso shi sosai ta roke hannunsa da hannunta guda kafin ta kai dayan hannun nata wajen kirjinsa cike da tausayawa ta ce" Son, kalle ni, plz ka kalle ni, dan Allah ka sasautawa kanka fushin nan, Son so kake a maidata ne? Idan har a kasan zuciyarka so kake ta fita daga nan zan yi hakuri son, zan yi, dama bana so ace bata rigaya ta idasa cika burinta na son zama Hostess mun barota a cen an koreta ne, domin D'a na kowa ne, aman idan har yanzun so kake ta tafi shikenan ka shirya mata tafiyar sai na yi mata rakiya in sha Allah, dan Allah ka bari haka ka ji? Yau fa birthday dinka ne, ranar da take baba a wajenka da mu baki daya, ka ga kuwa cake dinka? Na maka girki da kaina...... plz ka dube ni Son?". .......ta katashe tana kara sado dubansa kanta domin idannuwan nasa a kan hanyar da suka shige
A hankali ya lumshe idannuwansa , hannunta dake cikin nasa ya kawo wajen kirjin nasa a hankali ya danna kafin ya rintse idannuwansa
Muryarsa wannan karron ba da babatun ihun da ya shigo da farko ba, ba da fadan da ya shigo ba, a hankali sannan a sanyaye lafuzan wani na korar wani a hankali ya ce" Mah i'm seek "
Gabanta ne ya fadi da yannayinsa, da kuma furucinsa,
Haka ya fada a jiyama a cikin waya kuma daga baya ya ce wai ya warke
Aman a yanzun itama irin bugun zuciyarsa da irin yadda idannuwansa suka rikide sai ta tsorata, dan haka da sauri ta umarci Iman kan ta kira mata docter kafin su yi ciki tana rike da hannunsa gaba daya hankalinta ba a kwonce ba ta tsaya kisa da Pah tana gannin yadda hankalinsa kwonce shi ko a ka bai wani nuna damuwa da yannayin Hanja dinba sai ta ji haushin hakan ta idasa jan hannun yaronta da nufin kaishi bangarensa sai kuma suka dawo domin tunawar da ta yi akoy tgr ta taimaka masa ya kwonta saman kujera ta shiga cire masa takalmansa da safa da komai kafin ta zauna tana rike da hannunsa tana cika tana batsewa da yannayin Pah, kuma har kasan zuciyarta a yanzun kam ta hakura da rike Muneerath din tunda dai haka zaman Muneerath din ke rikita shi, ta hakura, Allah yana ganni dama yarinyar ce ta shiga zuciyarta , irin hakurin yarinyar da courage dinta kuma ya sakata sakawa ranta abubuwa da yawa
Jinninsa aka diba, bayan aune aune likitan ya tafi da sauri da kayan dan dubawa
A hankali ta talabe shi da dan jus din da ta zuba a dan kofi ta kafa masa a bakinsa ya dan surba ta maida kan nasa tana shafawa ta kalli Pah dake dadana Computer yannayin fuskarta na nuni da fushi take ta ce" Aman me yasa zaka yi zamanka kana kallon halin da son yake ciki ko magana ba zaka matso ka masa na ji dadi ba?"
Pah ya dakata ya dago ya zubawa HANJA ido, irin kwoncin da ya yi fuskar nan tasa a hade tamkar wanda aka watsawa kashi, ya yi wani irin kwonci gaba daya ya yi ja hakan na nuni da abinda ke damunsa na nukurkusarsa daga cen kasan zuciyarsa ne
Abin tausayin shine shi kansa bai gama gane me yake ciki ba, ko kuma baban girman kan dake damunsa ya hanna masa ganewar
Ya kasa gane cewar yana cikin bacin ran tunanin ta yi magana da waninsa ne? Ya kasa gane cewar dariyar da take saka shi bai shirya ba a cikin tsarin abinda ya rike masa wuya ne
Uwa uba ya kasa gane cewar babu halitar da aka halita ba kishi a jinsin dan adam ko wani iri ne sai dai idan bai hadu da ainahin abinda zai yiwa kishin ba.....ko kuma ya gane baya so a gane ya afka dan gudun kar a masa dariar shi mai fadin bai san KISHI ba?
Ko kuma yaron nasa na cikin duhu ne? Idan kuwa yanna cikin duhu har haka lalle yana tsoron yaron nasa ya fada a mugun halin da ba zai iya ciro shi ba
A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Hurul ayn, yaya kike so na masa ne? Ni da na yi nawa wa ya kama min?"
Tsatsareshi ta yi da ido kamar zata dauke shi da su , a hankali ta cire dubanta tana ta kokarin fasara maganarsa, rashin lafiar da yake ciki ko me yake nufi?
Mikewa ta je yi dan ta karasa kusa da shi ta samu gamsashiyar amsar da take son sani ta ji an rike mata hannu
A hankali ta juyo tana kallon HANJA kafin ta duka kadan tana kallonsa a hankali ta ce" Son, yanzu za'a kawo maka magani ka ji? Ko na kira wajen aikinku ne na sanar masu?"
Idannuwansa ya rintse da abinfa yake kasan ransa wanda ya ki gushewa, a rarabe ya iya budar bakinsa ya ce" Me ya ce mata?"
Ita har ga Allah ta manta cewar Muneerath ta mata maganar cewa Sir ya ce mata wani abin aman bata idasa fada masu ba, hakan ya sa ta rasa me aka cema wa?
Da sauri ta kara kai hannunta tana taba jikinsa hankalinta tashe ta ce" Khalb, dan Allah ka duba bashi da lafia fa?"
Pah ya dafe gaban goshinsa yana kallonta kamar wata yar baby du ta rikice ta kasa gane cutar dan nata ba wani abu bane sai na kokowar watsar da abinda ke damunsa da yake yi tun karfinsa ya girgiza kai ya rufe computer ya mike ya karaso inda suke
A hankali ya kai hannunsa jikin Hanja ya taba kafin ya kaleta
Dan murmushi ya sakar mata a hankali ya kalli Hanja da ya lumshe idannuwansa tamkar mai yin barci bayan idannuwansa biyu kawai abu ne ke nukurkusarsa ya ce" Cewa ya yi yana sonta "
Hanja da idannuwansa ke rintse bai san lokacin da ya bude su a kan Pah ba
Dama tunda ya zo ya fara fada ya kula Pah sai wani murmushi yake yana kada kai, bai san yaushe Pah ya fara fifita yarinyar nan akansa ba, gashi dai yanzu kuma yana fadin haka?
A hankali ya nemi tashi zaune hakan ya sa Mah da sauri ta so taimaka masa sai dai Pah ya rikota a jikinsa yana tatare mata goshinsa da yannayin kamar zai yi fada sai kuma ya kane mata ido daya yana mata murmushin da ya kara dulmiyar da ita a duhu
Hanja ya idasa zama da kyau a hankali ya ce" So kuma? "
Pah ya gyada kai da sauri yana dan daga kafadunsa kafin ya saki murmushi ya ce" Kuma da alama itama tana sin nasa dan ka ga kunya ta ji ta fada, ashe dai ka kusa zama yayan ango ka daura mata aure abinta"
HANJA har wani duhu duhu yake ganni na bacin rai, abu ne da bai saba ba, abu ne da bai taba tsintar kansa a ciki ba, ransa bace ya ce" A kan me zan daura mata aure ni kuma? Bama za'a yi mata ba walahi ba wanda za'a aurama ita!"
Pah ya ce" a kan wani dalili fa?"
Hanja ya kalli Mah dake kallonsa ya kuma kalli Pah, sasautowa ya yi daga saman kujerar ya hade hannayensa ya furzo da wata iska daga bakinsa ya ce" Aman ai amanarta muka dauko ko?"
Da wani irin mamakin jin a yau ya ce da shi a dauko amanar Muneerath Mah ta kara tsatsareshi da ido
A hankali ta samu kanta da fadin" Son, kishi nake gani a tatare da kai?, Son kishin Muneerath ne nake gani? Son ka fada soyaya? "
Lalala kamar wanda yake jira hakan ya fito daga bakinsu, nan fa hali ya motsa kamar ba shine yanzun take kamawa tana kwontarwa tana lalasa kamar wani dan goye yanzun ya firfito ido cike da mamakin furucinta a birkice ya ce" Mah so? Soyayar yau na fara? Wani irin kishi? Ni? Kishi? Ni ban san kishi ba! Ke fa kike cewa yar amana ce kuma ta kiyaye du wani hulfa da wani, kuma ni fada ne nake mata in na ga na hanna ta tana yi, barama na tarda ita sai ta fada min abinda wannan sakaran ya fada mata kuma shi sai na kai shi conseil kafin na kore shi dan na kula yana cikin masu lalata mana ma'aikatanmu!""""""""""""
Fuuuuuuuuu ya mike kamar ba shi aka gama rikewa bashi da lafia ba ya nufi lft
Da sauri Mah ta mike tana kiran sunnansa
Pah ya tiko hannunta yana daria a bayane yana girgiza kansa ya dawo da ita saman kujera sunna facing din junna
Irin yadda hankalinta yake tashe ya saka shi kara yin dariar da ta jima bata gani ba
Har dafe kansa yake a hankali ya ce" Alhamdulilah"
Mah a sanyaye ta ce" Du sai na ga kamar ba kai na, du sai na ga kamar baka damu da damuwarmu ba, duba fa ka ga halin da yake ciki, kuma duba ka ga ya bi bayanta kar ya daketa"
Pah dake daria a hankali ya ce" Ba zai iya dukanta ba"
Mah da bata gamsu da maganarsa ba ta ce" Ka fa san zafin ran son idan ransa ya baci, abu kalilan yake zartarwar da hukunci mai tsanani, bana so ya taba lafiyar yar mutane kafin na maida ita wa ahalinta"
Pah ya karra yin daria domin shi rabonsa da gannin nishadi irin wannan har ya manta, wai shine yau da idannuwansa da ransa da lafiyarsa ya gama gannin sc猫ne din kishin yaronsa? Ya ce" Ya yiwa wa duka? Ni sai kawai na ga idan abu ya shafi yaronki ne sai ki rikice ki kasa gannin komai, ai Muneerath ta fi karfin dukansa sai dai ta dake shi! Kuma idan kika yi gigin mayar da ita wa iyayenta a yanzun a awani kusa zaki zama wada zai yiwa kallon mai son raba shi da numfashinsa.......yaronki ya yi wasa ya zurma da yawa, ya yi sake ya zurma a duniyar da bata damu da shi ba, ina mai taya ku da adu'ar kar ku yi wani wasan da zaku haukace ku rikice ku rasa gane yarenku!, Kin ga barni na gama bincikena a kan lamarin Muneerath"
Jikin Mah a mace, cike da rashin karfin jiki ta dora kanta a gefen kafadar Pah a sanyaye ta ce" Ya Allah ka kama masa, yarona karami ne, bai iya kokowa a kan abu ba, Allah ka bashi , ka sasauta masa ya rab, ka sa wannan rigimar ta zama mai sauki a tare da shi, ka sa yarinyar nan yi masa kallo irin wanda yake mata...."
Murmushi kawai Pah yake ya kurawa hanyar da ya bi yana jiran gannin saukowarsa a haukace馃槀
Hauka suke zubawa tuburan
Gaba daya Saudat ta kasa yarda cewar wai da gaske dakin nan na Munnerath ne
Ihu suke na arziki sunna bude bude da ciro dogayen rigunna
Kida na wakar hausa suka saka sunna casu abinsu tare da kyakyata dariar shirmensu
Saudat ta ce" Muneerath, girman ubangiji ya fi gaban tunanin bawa, wai da gaske baki da shamaki a palace din nan? Muneerath kina kallo Sir HANJA gamu ga shi a gidansu yana kallonmu? Munnee wai kuma baya maku fada a nan?"
Muneerath ta zauna saman gadon da yar rigar dake jikinta sai dogon wando ta talabe habarta ta ce" ke sangarta ce fa irin ta yan baci, wollah a nanma bini bini yana fada, bini bini mamansa na rarashi har mamaki nake, yo da gidanmu ne oga da matansa ba sai dai su idasa haukata zuciyarka ba dan ka kasance mai fushi wollah matsalarka!, Aman a nan kin ga idan ya shigo an kama kamo shi, ana wani shafar kansa, ana wani zabura ana kawo masa abin tabawa, kai kudi jaraba ne, kamar wani sarki saima kinnga yadda wannan yar uwar tasa take masa haukan so? Sonsa take kamar ta mutu"
Saudat ta zarro ido ta ce" Tap, aman ta dauko ruwan dafa kanta, baki ga wata rantsatsiyar budurwa da ta shigo da bakar riga a jikinta ba? Wannan budurwar ni nan ni nake kallonta ina karawa baki ga kyau ba, luwai luwai da ita, yar wannan mahaukacin mai kudin ce kuma ita kadai ya malaka a duniya, ke itace fa budurwarsa ita ta bada makudan kudade wa kampanin aka shiga shirya masa karya karyar nan, daga baya da kampani ya nuna na zai amshi kudinta ba ta nuna wannan kadan ne ta shirya masa wata salar ta birthday dinsa a wani wajen wannan tana so ne ta ga yaya zai dauki lamarin, ke kin ga abin wai? To Allah sai ta yankata a kan Hanja, kuma da kike cewa kamar sarki an fada maki ba sarki bane? Shi fa zai gaji abansa"
Muneerath ta yatsina baki tana girgiza kai ta ce" lale, to ita tsakani da Allah kashe kashen kudin na menene? Ni mamaki suke bani da suke nunawa kato so, yo Allah na tuba ka ja zarenkama yaya ka kare da namiji bale ka nuna zakewa? Da hakuri ta yi har ya nuna yana sonta sai ta yarda, kuma ni du in kika ce sarki daria kike bani kali fa kin taba gannin sarkin garinmu fuskarsa a bude? Ji fa shi wannan fuskar tasa kulun a bude take gashi dan kyakyawa da shi sai fada kulun kulun"
Saudat ta yi daria tana bude computern Muneerath ta zauna gefen bed din ta ce" Ba zaki gane ba, bara na shigar maki tarihin masarautar kasar nan sai kin haukace
Tankwashe kafafuwansu suka yi inda Saudat ta shiga duniyar yanar gizo dan ta nunawa Muneerath me ake kira da sarauta , ta kuma ganar da ita cewa Allah ne ya tsaya mata ba kowa ba da har ta samu arzikin nan, ta ganar da ita cewa Hanja sarki ne mai mulkar saraki, ta kuma ganar da ita cewa ba wai rawanin bane shedar sarautar domin da rawanin ne da kowama ya naa ya kirayi kansa da sarki
Sunna shirin fara afkawa duniyar saraki aka shiga dukan kofar tamkar za'a karyata, karan da take ke iya nuna maka cewar ba mai karamin karfi ke dukanta ba
A tare suka zabura sunna kallon kofar
Saudat ta ce" Mun shiga uku waye?"
Muneerath ta diro da sauri ta je ta dan buda ya kofar da kake lekawa dan gannin mai bugawa dannita kanta tunda ta zo gidan nan ba'a taba buga mata kofa a haka ba, hakan ya sa ta tsorata da jin dukan kofar na yanxu
Da sauri ta dora hannunta saman kanta ta kallo saudat ta budi baki ta ce" Ubanmu zai ci walahi zaki ne da shi min shiga uku"
Saudat ta fita kidimewa domin ita cen dama tsoronsa take din, duda baa gane waye din ba kalmar ubansu za'a ci ya sakaa rikicewa ta duka tana kokarin fashewa da kuka , sai dai bata yi ba gannin Muneerath ta nufi kofar kuma da nufin budewa a haukace ta ce"
11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
4锔忊儯6锔忊儯
A rikice saudat ta ce" Kar ki bude dan Allah kar ki bude kin ce zaki kuma zaki bude?"
Munnerath ta ce" Idan ban bude bane zamu kara laifi, to wai mema na masa daga dawowata? Kin ga walahi idan ban bude ba ya fara ihu a wajen nan abin hauhawa zai yi sai gyaran Allah, na tabata Mah na kusa dan bata bari ya dakeni, kakarinta shaka ce da ya shakeni kuma kafin Mah ta iso wataranan sai na gala masa cizo a hannu wollah"
Tana fada tana murda ky din ne ta bude dakin gaba daya
Irin dukan kofar da yake, irin yadda yake jijiga kofar kai kace daga an bude zai dauke wanda ya bude din da mahaukacin marin da sai ta ga walkiya, Saudat kanta da ta duke ta rufe ido cike da tsoro da gannin gangancin Muneerath a kan wai tunanin da wanda zai amsheta ta bude kofar nan j'ai n shirun ya yi yawa a hankali ta shiga bude idannuwanta dan gannin ko ha ya shaketan ne ya yi waje da ita
Ido ta kura masu kamar yadda ta ga ikon Allah Muneerath ta bude kofar aman kuma ta ja baya kadan ta tsaya da shigarta tana kallonsa
Tun daga kafarta ya dauko kallonta har ya dire saman fuskarta da ta yi wuki wuki tana kallonsa ta kwashashabe fuskar tamkar zata fashe da kuka
A hankali ya mika hannunsa ya damko nata hakan ya sa Muneerath fadin" Innalilahi kuma taba min hannun zaka yi? Dan Allah ka daina min haka ni walahi irin abin nan naka mamaki yake bani bayan mamanka ce da kanta ta hanna kuma kake yi!"
Hanja ya lumshe idannuwansa a lokacin da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 42