ko shegen gyara ne d hutu? Aman tsufan bai gama nuna kansa sosai ba bale ga Muneerath da ba wani fahimta ne da ita ba, ita sam bata ga datijuwa a gabanta ba wollah, to ina wannan ina amsa kiran mama? Sam bata kawowa ranta ba shi yasa take kallon hannunta da kuma ita da bayanta dan so take ta hango wannan kumurcin da zakin da ya kawo dan ya kasheta
Cikinta ne ya fara kartawa alamun zai kuma juya mata hakan ya sa muryarta cen ciki ta ce" Ina zakin? "
Mah ta kaleta da kyau dan son fahimtar wani zaki take tambaya ? , Da sauri ta juya dan gannin Hanja ya bata karrin bayani, sai dai ba shi ba alamunsa da alamu ko ya shige ciki ko kuwa ga yi tafiyarsa abinsa hakan ya sa ta juyo ta dan watsa hannayenta ta ce" Wani zaki? "
Muneerath ta kikifta ido a sanyaye ta ce" Shi zakin da ya kawo ya cinye ni, sunna ina?"
Sai a lokacin Mah ta fara dago zancen, sai a yanzu ta karra lura da irin tsabar firgicin dake tare da Muneerath,
lebenta na kasa ta dan cije tana girgiza kanta a hankali ta karra mikaea muneerath hannunta ta ce" Babu zakin da zai cinye ki, kin baro zakin a cen gidansa, taho mu shiga ciki "
Muneerath ta ringa sauke ajiyar zuciya zuciyarta cike da mamakin irin ci gaban da duniya ta yi, dan har ga Allah a tunaninta wannan mota mai kama da dan daki bacewa ta yi ta bayana da ita a nan
A hankali ta dora hannunta cikin na Mah kafin ta zirro kafarta waje ta karasa fitowa gaba dayanta tana dan zarar ido
Da sauri ta rike hannun Mah tana karra bin irin tarin matan da suke tsaitsaye da kallo , muryarta cen kasa ta ce" Ina ne bayi? Ina son zagayawa"
Mah ta dubeta, kasamcewar mace ce kuma yarinyar da ta tabata ta haifi kamarta sai ta bi jikinta da kallo gannin rigarta fa a jike daga kasa
Cire dubanta ta yi ta jata suka shiga tankamemen falon da sanyinsa kadai ya saka Muneerath jin dan lisilama danma shi oga zawayi ba ruwansa da sanyi ko zafi , idan fa ya karta a kaishi a zubar ko ya fito da kansa dan kuwa shi bai san wata kalma ba wai hakuri ko kunya ba hakan ya sa ta ringa bin Mah da sauri sauri sosai har suka shiga accenceur ya yi sama da su suka kuma mika dan dogon coridor kafin su shiga wani dakin da bata iya gane komai ba zuwa lokacin dan ogan ya fara dan tsartuwa a guje ta nufi bayin da aka nuna mata kan shine wanda zata shiga ta aiwatar da uzurin da ya kamata a yanzu yanzu
Wollah, da ba dan ta jima a garin ba, ta kuma iya gane ramin masai a zamanta da su ba, da babu abinda zai sakata hawa wannan waje mai walwali ta zubar da dati
Kai jama'a, mutane duniya na inda take, yo wannan abin idan musulmi nada hankali an ce aljannah ta fi karfin tunanin bawa ai zai dage dukkan karfinsa ya ringa ibada dan ya ga wannan iko na Allah, haka kuma wanda ke cikin irin wannan idan ya yi wasa ko sallah ba zai yi ba, zai shagala da shagalalan wajen nan ne har sai ya ji guduma a saman kansa ya jishi a matsatsen rami kafin ya gane cewa da gaske fa mutuwa zai yi
Ido ta lumshe tana amayar da ogan mai kukan tsiya wanda yake tafe da damuwarta,
A hankali ta ringa jin sansanyar iska na kadata a lokacin da ta samu nutsuwa hakan ya sa ta ringa buda idannuwanta dan gannin ko a nanma akoy AC ne?
Ai kau akoy din sai dai ba a kunne ba, kawai nutsuwa ce irin ta idan ka gama zubar da wahalar nan hakan ya sakata sakin sansanyan murmushi tana yiwa Allah godiya da bata yi a jikinta ba
A hankali ta gama , nan fa tsaftar ta tashi domin bayan ta wanke da sabulu ta kara wankewa da ruwan dumi sai ta kasa mayar da komai nata daga pant din har rigar, gaba daya sai kyankyamin kayan ya sakata jin tamkar zata kelaya amai
Da sauri sauri ta tara ruwa ta shiga wanke su ba tare da ta tuna komai ba, har sai da ta masu ruwa hudu sannan ta matse su ta karasa ta cire tawul din da ta daura a kugunta ta wanke wajen tas sannan ta shige ciki ta tara ruwa masu dumi sosai ta zauna ta dauki sabulun nan ta shiga darzar fatarta da shi kadai mr spcly wajen da dan fitsarin nan ya bata mata na jikinta du ta wanke har sai da ta ji tana kanshi sanann zuciyarta ta aminta da tsaftar jikinta kafin ta fito tana mamakin kanta irin yadda ta yi wankan nan a wajen nan ba tare da ta wanke ba bayan du tsaftar waje sai ta tisa masa kafin take anfani da wajen
Kafadunta ta daga irin na oho din nan kafin ta dauki wani tawul din kuma ta ja ta tsaya cike da tunanin yaya zata yi ta fita
Mah dake zaune cikin zulumi take
Zulumin da take cikinsa na gannin kanta ba dan kwali da kuma fitsarin dake jikinta
Lale ta san na lalura ne, ba da gangan zata yi fitsari a jikinta ba, abinda ya fi damunta daya ne irin yadfa zata fito mata, shin da rigar zata fito a jikinta ko babu? Ita mah a duniyarta abu daya ke wahalar da ita shine tsafta, mace ce mai kuguwar tsafta, sannan mace ce mai riko da adinninta, du irin yadda dunia ta rikice ita ta ki ta dauki maganar cewa wai yanzun yan mata basa son saka dan kwali ba, sosai ta zauna cikin tunani bayan ta dauko mata wasu suturun da dan kwali tana jiran fitowarta,
Babar damuwarta shine bata san ta yadda zata zauna da kazamar yarinya ba
Na biyu kuma shine sam bata iya zama da mutumen da baya son rufe suturarsa ba, duda yaronta ba mazaunin gidan bane idan ya ga dama yake zuwa in ya ki kuma baya ko leko su sai dai ita ta je, aman sam bata so ta ga ana yawo ba dan kwali dan ko christocin gidan da yan dan kwalayensu a kawunnansu idan sun hau aiki, idan sunna so in sun tafi gidajenau su cire abinsu
Da sando ta fito da sauri ta ja shinfidar gadon ta aniya cikwuikuyewa a jikinta cike da jin kunyar matar nan wai dama tana nan? Allah sai yanzu ihun kukan abinda ta zubar a masai din cen ya ringa dawo mata hakan ya hadasa mata matsananciyar kunya har ya kasa dago kanta da kyar daga tsayen da ta cuimuimuye ta samu ta dan fitar da fuskarta ta kai dubanta kan Mah da fatan ta bar dakin
Ido hudu suka yi, hakan ya sa Muneerath rintse nata idannuwan a sanyaye da yaren turanci ta ce" Ki yi hakuri, ba da gangan ya kubce min ba, nama wanke kayan na matse su, kuma na yarda mayafina a cen makarantar da mijinki ya dauko ni, dan Allah ku yi hakuri idan wani laifin na maku"
Mah ta saki murmushi tana jin gamsuwa da nutsuwa da bayanan Muneerath kafin ta kuma yin murmushi ta mike ta nufota rike da kayan nan ta tsaya a gabanta kafin ta ajiye a saman bed din dan shinfidar ta zannin gado hudu ce na saman kadai ta yayuma
Dubanta ta yi ta kuma sakar mata murmushi ta ce" Ki cenza kayan ki, ki yi sallah, za'a kawo maki abinci ki ci, sai ki kwonta ki huta kin ji? "
Muneerath na kallonta da mamaki bata iya cewa komai ba
Har ta juya ta dawo ta kama hannunta ta cikin zanin gadon ta ce" Bama kisa, sannan d'ana ne ba mijina ba "
Tana gama fada ta sakar mata hannu ta juya ta tafi tana murmushi
Sakalau munnerath ta yi da bakicike da mamakin dake nemn kasheta kafin ta shiga tafa hannu a bayane ta ce" To ko dai da aka ce a inji ake kyankyashe su hakan ne? Ko kuma irin y'ayan nan ne na kwalba shi din shi yasa ya yi saurin girma?".......karshe dai a hakan ta ajiye ta gyada kanta kafin ta girgiza ta shiga saka suturar ta abaya fara ta kuma furta" Gaske yannayinsa sam ba na mutun bane, ashe shi din mutumen nasara ne gaske hannaye kamar an busa balan balan an saka masa ga karfi irin na aljannu.....Allah dai zai saka min yanzu haka na girme shi a haife ya shake ni munahiki kawai!"...............................................
________________________________
"Dama har haka suke da iko? Aman ko shi ya kawota a kasar nan na zata dan adam yana da yanci shakar da ya yiwa yarinyar nan ban zata idan na shiga zan ganta a tsaye ba, tunda suka tafi kuma na kasa zaune na kasa tsaye, shin idan fa ya kasheta?". Madame joyceline ta fada bayan ta gama sauraron bayanan jujun dake kare yancin yara da matasan kampanin nasu
Gaba daya ta kasa samun nutsuwa, ta sani sarai wannan abin da ta yi yana iya jaza mata baban balakin da ba zata iya kokowa da shi ba, aman ta jajirce ta dauki risk ba dan komai ba sai dan ta kuma san kasa suke ta yancin kai, yarinyar nan kuwa ko a musulmai ta shiga ranta sosai dan yarinya ce mai dadin zama, gudun nan da suke yi tare sosai ta ahiga ranta, a kasar nan kuwako uba ka kula yana takurawa dansa kana iya shunawa iko su kama shi ram a tuhume shi, idanma gaskiya ne kana iya yin kaso, ko tara mai yawa sanann a amshe rikon dan daga hannunka
Murmushi ya mata bayan ya dan shafa kansa ya ce" meye hujarki na ita din yar kasa ce? Sannan menene hujarki na ba ainda ta yi masa?"
Dan kikifta ido ta shiga kafin ta ce" ta nuna yannayi na innocent"
Kansa ya girgiza ya ajiye byronsa ya ce" Aman yaya aka yi aka baki mukamin nan? Har yanzu baki daina anfani da yannayin mutun ba ba tare da kin yi bincike ba?, Madame da gaske kike saboda yannayinta kika dauki wannan baban risk din MR HANJA ba aiki yake da iko ba shine iko, kina magana da a je a tuhumi sarkin garinki na nan da dan watani kan abinda baki da tabas dinsa? Kin san da dole za'a ambaci sunnanki a gabansa? Kin san da idan lalube kike ba gaskiya bane ni da kaina da kika saka kin saka ni a matsala? Kin fi kowa sannin Me Hanja baya daya daga cikin wa'inda muke neman laifinsa ido rufe domin shi din shi ya fitar da hukunce hukuncen bima mai haki hakinsa , shin zai yi gangancin takewa kuwa? Na san dan adam kowa nada abinda yake boyewa, aman idan har wannan da zamu yi ba shine abinda yake boyewar ba kin san da mu zamu zama boyayu domin lauyansa sai ya yi yadda ba za'a kuma tunawa da mun rayu a duniya ba domin ina mai tabatar maki lauyansa Mockar sai ya goge harta da labarinmu dake cikin yanar gizo dan wasa muka yi da ZAKI!?"
Ya karashe yana kallon yadda du ta rikice kafin ya ce" idan kuwa haka ne mun ciri tuta, zamu yi aunna sannan mu yi kudi, zamu samu mulki domin zamu kasance da masu mulkin, idan har kin yarda da maganarki ba damuwa sai mu fara shigar da kara da camerar abinda kuka dauka a lokacin "
Sai a lokacin wara zufa ta fara tsatsafo mata, a hankali ta zauna cike da tsoro tana tuna kashedin da ya masu na su guji fitar da maganar hannunsa ya taba mace dan gargadi domin yana jin kunyar a ji mace ce ya taba da hannunsa ba namiji ba,
Lokaci daya kuma ta tuna da baban sojan dake bashi kariya ya cire gaba daya vidion abinda camerar ta dauka
Wani yawu ta hadiye da ta tuna Muneerath ta sanar mata cewa tun daga kasarsu ya daukota, a hankali ta shiga girgiza kanta kafin ta mike da sauri ta bar office din cike da dana sannin zuwa da wannan maganar da fatan kar ta je ko kunnen karen gidansu ne!
______________________________
"She look so so so ya rab she look tn a prncss khalb" ta fada a sanyaye a lokacin da ta kai masa kofin maganinsa ta surba masa a bakin nasa
Murmushi sarki ya yi yana kallon HANJA da yake rike da kofi na kwalba wanda aka zuba wani dan tsurut din jus , hannunsa daya kuma rike da remot ya rage kukan TV din sosai ya maida kallonsa kan Mah ya ce" Yanzun y'ayanki mata biyu, to ita iyayenta suka baki ko cirowa kika yi?"
Murmushi ta yi ta bude rubutun da take shafa masa a kansa mai hade da su ruwan zamzam da su jibda ta diba kadan ta ahiga shafa masa ta ce" Allah ne ya bani,kuma ka ga ka tambaye shi hala shuna mata Zakin nan nasa ya yi?"
Yarinyar dake wajenta ce ta fito mai sunna Iman, sanye take da doguwar riga irin na dubai din nan, sai dai ba yane mayafin ta yi ba a kafadarta yake ta masa irin yadda indiyawa ke yiwa mayafi, ta tufke gashin kanta a bayanta ya mata lufluf abinka da jinnin larabawa
Yarinyar ruwan kyau tana da shi,
Tafe take a hankali gaba daya idannuwanta a kansa hakama tunaninta da hankalinta, ga hannunta dauke da butar shayi da ta dafo Percil din Sarki yana turiri
Sam bata san har ta iso kusan dan table din dake dauke da litatafai irin na adini a sama ba, sai da kafarta ta daki wajen ana dayanta ta tafi wajen da Hanja yake zaune ta.......
Comment dinku na kashe ni, ina ji da ku ainun
11/14/21, 12:48 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
2锔忊儯8锔忊儯
Gaba dayanta ta yi wajen da Hanja yake zaune domin nan table din ya wurgar da ita
Ido ta rintse tare da fasa ihu cike da tunanin ta kade har buzunta idan har ta idasa sauka a jikinsa, hakama shayin sai ta nemi azamar neman wurgar da shi gefe daya dan ba zata ao hasaso irin abinda zai iya samunta idan har ta dira kansa da wannan ruwan zafin ta tabata sai dai wata ba ita ba
Mahaifinsa ne ya fara mikewa yana furta" Subahannalah "
Mah da ta rintse ido gabanta na dak dak dak ta bude a hankali dan gannin mai afkuwa ta afku nan ta ga ikon Allah, HANJA ya tareta da abin dake hannunta na dan sekwani ita kuwa tar dubanta a kan fuskarsa tamkar kallon jaraba ta kasa cire duban nata a haka har ya cire butar a hankali kafin ya saketa daga kwonto masan da ta yi sakamakon shagalar da ta yi da kallon fuskarsa ta zube kasa gaba dayanta
Sai a lokacin ta ankare da irin kallon da take masa, lamari na zuciya mai saka bawa yin abu irin na rashin sannin ciwon kai ko mai kamun hauka sai ta kuma raka fafadan bayansa da kallo a lokacin da kama hannun Mahaifinsa ya mayar da shi zaune sannan ya dan rage tsayinsa ya mikawa mamansa butar shayin ya sakar masu murmushi ya juya ya fice a falon baki daya
Sai da ya bacewa ganninta kafin da sauri ta kai dubanta kan Mah da Pah
Bata san lokacin da ta mike da gudu gudu ta bar wajen ba cike da jin kunyar irin kallon nan, cen kasan zuciyarta kuwa cike da begen wannan bawan Allah, walahi har ajiyar zuciya kwace mata take idan har tana kallonsa, bata gajiya da kallonsa a kowani lokaci...................................................................
Barci Muneerath ta sha cike da nutsuwa, duda cenjin waje bata kasa rintsawa ba domin dama ba wai koshi ta yi da barcin nata ba dole aka tasheta
Kiran salar da ya sauka a dodon kunnenta ya sakata farkawa cike da matsanancin mamaki ta je wajen Windows tana lekawa sai dai bata ga inda masalacin yake ba hakan ya sa ta yi bayi da dan sauri da daura alwallah
Sai a lokacin ta ga an shanya kayanta a nan cikin bayin, ita dai ta dauro alwalarta ta fito da sauri ta dauki hijab din da ta yi sallar dazu ta gyara ta kabarta sallah
Tana gamawa ta ci gaba da zama tana adu'a idannuwanta lumshe hakan ya sa sam bata ji shigowa ba har sai da ta gama adu'o'inta ta shafa sannan ta buda idannuwanta dan cikinta fa kiran ciroma yake domin a dazun bata ci abinda aka kawo mata ba dan ita ba sanninsa ta yi ba tsakani da Allah, gashi yanzun bata da tumbi ba zata ringa fadawa komai ba ta yi tumbi haka kawai
Murmushin da Mah ke yi mata ya sakata dan yin sakalau a ranta ta ayana' ta ina ta shigo? Na shiga uku ita kuma wannan sai fara'a kamar wace bata da damuwa a dunia? Koda yake ina ita ina damuwa matar dake rayuwa a wannan gidan ai ko ita da ta shigo dazun ta sha barci sai da ta farka ne oga da mamansu da Dogari suka fado mata a rai'
A hankali ta ce" Ina yini "
Mah ta kuma sakar mata murmushi ta mike ta karaso inda Muneerath ke zaune sakalau da baki tana kallonta
Hannunta ta mika mata ta ce" Tashi mu tafi falo, ke kadai a daki ga abanku cen da kawarki a zaune "
Ido Munnerath ta kuma kiftawa a bayane ta ce" Wata sabuwa "
Mikewar dai ta yi dan bata iya saurin musu ba tana biye da ita tana shakar wani siritacen kamshi da take bazawa har suka ratsa wani corridor din kafin suka fito wata duniyar da ta saka Muneerath idasa sarewa rayuwa, kai jama'a ina ne nan? Wayo Allah ina ne nan? Sai ta ji gudun zuciyarta ya fara fin bugun normal, da sauri ta ringa saisaita numfashinta tana kale kale kafin ta sauke dubanta a kan datijon dake zaune d jalabiya fara tas shi din kansa fari kal da shi sannan fuskarsa dauke da yalwatacen murmushi da alkur'ani a hannunsa mai girma ya bude yana karantawa a bayane shigowarsu ya dasa aya ya bisu da murmushi kafin ya budi bakinsa a nutse ya ce" Marhababuki yar Mah "
Muneerath ja ta yi ta tsaya a hankali ta ce" Ina ne nan? Ku din su wanene ku? Dan Allah ki sanar min ko zan samu nutsuwa "
Iman dake kallonta cike da mamakin kokari irin na mamansu haka kawai daga gannin yarinya ta kwasota yanzun har falon Sarki yanzu ta mayar da ita kamar yar gida dan rashin tsoron mugwayen mutane, ita kawai haka take tunaninta yadda take haka kowama yake
Mah ta nuna mata wajen zama kusa da Iman dake zaune a saman lalausan kafet din kafin ta karasa kusa da mijinta ta zauna sosai ta ce" Wannan da kike ganni shine sarkin garin nan baki daya, ni kuma matarsa ce, wannan kuwa yar yar uwata ce, yaronmu kuwa shine wanda kika ce ya kawo ki watau HANJA"
Muneerath ta kwalalo ido tana kallonta kafin ta kuma bin su da kallo ta dire a kan Iman dake kallonta
Kaii ta gyada a bayane cike da mamaki ta ce" Sarki kuma? , Sarauniya ce ita? Aman sarki a gansa haka a dasha? Kai ko a garinmu sai a ce ana takama kamar wani sarkin ingila............"
Shiru ta yi ta kuma dubansu gaba dayansu kafin ta dafe gaban goshinta tana girgizawa wannan karron da yaren su watau turanci ta ce" Dama sarautar kasarku haka take? To ina ahalin gidan sarki? Ina su dogarai? Ina dawakai? "
Mah ta ce" Ahalin gidan nan sunna nan cike , basa zuwa nan ne dan basu da wannan damar, dawakai kuwa sunna bangarensu watau ranch, Dogari kuma ban san mene haka ba"
Sai a lokacin ta tuna dogari ta ce da hausa dan haka da sauri ta fada mata cewa masu gadin gidan sarki
Mah ta yi murmushi , sam bata ajiye haka a matsayin kauyanci ba domin idan ba zata manta ba a lokacin da suka je niger ta ga abubuwa da yawa da suka bata mamaki harma ta yi ta tambaye tambaye ana bata amsa a bayane, hakan ya sa ta ajiye Munnerath a matsayin wace ke tambaya dan ta karra sani, sannan ta ringa bata amsa a bayane ta yada zata fahimta, daga karshe dai ta mike da kanta ta kuma kashe Muneerath da wani mamakin a lokacin da ta umarce su kan su tafi kicin
Bata yi kasa da gwuiwa ba sai da ta samu kanta a wani dakin mai dauke da abubuwan aikin kicin wanda ake mata nufin cewa kicin ne duniya guda , sannan ta kuma zubawa wannan mata mai mukami da daraja a duniya baki daya tana kallo ta zagine tana yanka wata kalar albasa ba irin tamu ba domin wannan tasun wata jajawur ce da hannayen nan nata masu laushin na jariri bayan ta saka gan sannan wannan balarabiyar yar tata yar zumunta mai shegen kyau tana yanka mata tomatiri ita kuwa aka miko mata nata gan din da leda mai dauke da zabi fara kal ledar da kwano kan ta gyara sai ta ji wani takaici da zuciya irin ta mata sun motsa, haba ina ai nan da nan ta ji idanma aka bar mata zara iya dafe komai dan kuwa in dai wadinnan larabawan suka iya girki suka barta ta ji kunya ta dirko kasa ba nauyi ta ba batan africa kunya ( ehem )
Kamar da gaske ta zagine ta gyara zama a saman kujerar dake kusa da dogon table din ta saka wukar nan ta cira ledar
Zabuwar daya ta ciro tana binta da kallo, ita dai ba gashi a jikinta ko dis, sannan ba abin nan mai saka karnin miya a jiki, aman gaba daya sai ta mata girma fiye da tamu ta gida, ta zama kamar wata dan jariri ,
Kai ta dai samu ta karasata cikin kwanon ta kuma rike wukar ta zuba mata ido tana kallonta, walahi bata san ta inda zata fara sukar zabuwar nan ba, asalima bata san idan har ta yankata bata bata miyar ba......a hankali sai ta afka duniyar tunanin aminiyarta Amina, da kuma Kawarta saudat kafin murmushi ya bayana a kan lebenta tana ayana inama ace sunna tare, yau da an sha miya alkur'an
"Munnerath ?" Mah ta kuma fada tana kallonta
Firgigit ta yi ita dinma tana kallonta kafin ta mika mata wukar da kwanon da ledar domin hannu ta miko dan ta gama karantar bata iyan bane har yanzu,duda da wuya a koya mata dafa kaza aman ai mace iya girki ne kau? Ita kam zata yi iya kokarinta har Allah ya raba su dan gannin ta iya girki, hakan ya sa da zata juya ta koma gefe ta tsayar da ita ta shiga yanka zabuwar nan tana mata bayani cike da murmushi da fara'a har ta yanke su sannan ta hada su percil da su celerik da garlic aka zuba cikin wani inji inji ya zubo su a dake luf sannan aka cakuda da au mutarde da dan gishiri aka cakudewa zabin nan kafin suke zama su dukansu au dora yar hira, inda hirar gaba dayanta Mah ce ke janta su tsakaninki basu yi sabon da zasu yi hira ba sai dai su yi murmushi kawai
A kadan ta dauki kwana goma tare da wannan ahali bata leka ko nan da kofa ba tana gannin wata irin rayuwa ta mamaki
Soyaya bayananiya da ta badini ke wanzuwa a tsakanin ahalin nan , irin kulawar, irin yadda matar gidan ke tsaye kan kafafuwanta, da irin yadda wanda yake sarki ne ke tafiar da tasa mu'amalar da dukan wani wanda ya kwana ya tashi a cikin gidan bake wanda matarsa ta kira da yaronta shima
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 42