Share this page
zai kire shi ne da yaronta, a lokacin ta ringa tunanin wai dama haka sarakan suke ko menene? A lokacin ta ringa tambayar kanta shin sunna da wani boyayan hali ne da suke boyewa a gabanta ko menene domin wannan zaman lafia da kwonciyar hankali na bata mamaki fiye da tunanin mai karatu, shin su basu da damuwa ne? Menene sirrin haduwar kan ahalinsu? , Komai na ba Muneerath mamaki a wannan gida domin a nasu ba haka ta saba ganni ba, a anguwarsu kuwa yayan gidansu idan suka fita har daga kai da tinkaho suke ana kada masu taken yayan mai kudi dan kawai Oga ya kekyara gini ya zuba su ba tarbiya!, Tabas idan ta ga Mah na girkin abinda su yan matan zasu ci takan ji wani iri domin ba abinda suke ci Sarki ke ci ba, shi nasa girkin tana girka shi ne da sinadarai na magungunnansa sai an zo ci a yi ta daru ya ce sai dai ya ci nasu mai dandanon kayan dadi ita kuwa tamkar jaririn goye ta ringa lalaba shi kan ba zai ci nasun ba a saman makeken table din cin abincin gidan A kwana goman nan kadai da ta yi da su ita da kanta ta dafa shayi wai ita Muneerath ya kuwa yi mata mahaukacin dadi a bakinta duda Mah ta ce kayan hadin sun yi yawa, watau kayan dafa shayin sun yi yawa ita dai dandano ta ji ram A kwanakin bata hadu da kyama, ko hantara ba, bata hadu da lukucin dansu ba, aljana ce ta duniya ta samu wace bata hannata tuna gidansu a dukan motsinta ba, wannan yannayi na rayuwar nan ya bata sha'awar da idan ta tuna nata iyayen sai ta labe ta fashe da kuka, akan tambayi kanta anya a yanzu Mah zata iya wuni bata ganta ba bata nemeta ba? Aman gashi wa'inda suka fi kowa sannin ciwonta suka kawota duniya sun manta da labarinta, tana da buri a rayuwarta bayan na dogari da zama hostess wanda suka haifar mata, shine ta ganta a gaban Oga da Mamansu, tana so ta masu tambayoyin da take da bukatar amsoshi, gaba daya ta kasa ajiye tunaninta waje daya, shin matan oga da aure da aure su?, Shin da gaske su suke haifo y'ayan su?, Shin da gaske musulman suke har yanzu ?, A in malsarar take a zamantakewar ne ko a tubalin zamantakewar ne? Watau ginnin auren.................. Da yaya oga yake neman aure?, Shin ya yi koyi ne da fadar ma'aiki kafin ya sama masu iyaye ko ya gani ya kyasa yake yi? Da wannan zulumin ta kwonta da kuma zumudin wai gobe zata fara aiki Hakan ya sa tun karfe biyar ta farka a barci ta yi wankanta na mamaki ta kuma gabatar da salarta sannan ta dauki man da take 11/14/21, 12:49 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 2锔忊儯9锔忊儯 Shafawa ta shafa cikin nutsuwa ta warware gashin kanta a hankali ta shiga binsa da kumb tana caje shi Sai da ta gama caje shi ta dauki ribom zata saka Mah ta shigo hakan ya sa ta gaisheta bayan ta rage tsayinta sosai Wannan gaisuwa a kulun itama mah din sai ta birgeta, ta kula irin nasu ladabin ba'a gaishe da baba a tsaye kikam, hakan sai ya birgeta sosai ita kuwa sai ta matso ta yi mata irin nasu na larabawa watau ta rungumeta Ribom din ta amsa ta nuna mata wajen zama, hakan ya saka Muneerath zuwa ta zauna ta dan hade jikinta tana jiran gannin abinda zai faru Ai kam Mah ta hade gashinta ta kame mata shi a tsakiya sannan ta tufke mata shi simple ba da wata kwaliya ba ta nade mata shi a kanta Kwali ta ciro sabo ta fitar da shi tana kallonta ta ciro tsinken ta kamata ta zira mata shi Ai kam ido ya kama ruwa ya ki ya bude sai rawa yake da kyar ta daina murzarsa Mah na mata daria har ta daina jin mugun zafin sannan ta saka tissu du ta goge mata bakin kwalin kafin ta umarceta kan ta saka suturar ta ma'aikatarta Sai da kwallah ta zubo mata a lokacin da ta saka wando kalar fari da dan sket a samansa ta saka rigar ta saka safa ta saka takalmin kafa ciki mai dan karamin tsini sannan ta kalli madubi Mah ta juyo tana murmushi ta dauki dan abin na wuya ta zagaya ta daura mata shi sannan ta dauki dan karamin fari kal din dan kwalin ta nade mata gashin kanta da shi Murmushi ta yi mata a hankali ta ce" Masha Allah " Muneerath ta kalli Mah sai kawai ta fashe da kuka ta dora kanta a saman kirjinta tana yi , ita kuwa Mah na dan tapping din bayanta sai da ta yi ta more sannan ta dago da dubanta tana kallon Mah Mah ta ce" Ki ce Alhamdulilah" Munnerath ta gyada kai a hankali ta ce" Alhamdulilh " Mah ta ja hannunta kusa da bed ta zaunar da ita, itama ta zauna kafin ta ce" Muneerath, a kowace ma'aikata akoy bata gari, akoy na kirki, a cikin manyanku akoy wa'inda sunna nan ne dan su lalata rayuwar yayan mutane ba tare da jin komai ba, basu da haram fa, Muneerath basu da haram domin sunna iya nuna maki soyaya ce suke maki sunna sonki ne zaku yi soyaya ne dan su samu ku yi kyakyawan karshe irin na aure , aman kuma abin takaici karya suke,karya suke yi maki Muneerath ba abinda suke so sai su cinma abinda ke boye a cikin pant dinki, baban burinsu su mayar da ke karamar karuwarsu wace idan sun zo office gaki a kusa sunna iya zubar maki da datin su, Muneerath baban abin takaicin ba dagake zasu tsaya ba domin ba a kanki suka fara ba, kema zaki zamo ne hanyar da zasu hau su bi cikin garaje da iko ba tare da sun biya ko sisin dalarsu ba..............." Ta kamo hannayenta ta rike ta ce" Hakan na saka mu iyaye a cikin zulumi da tashin hankali, da ace zamu iya hanna aikin da mun hanna harta mazan fita nema........., Sai dai hakan ba zai yiwu ba dan kuwa a yau ilimi anfani ne da shi koda na iya zama da mutane ne," Habarta ta kama ta dan dago da dubanta ta ce" Muneerath, zaki hadu da mutane kala daban daban a aikin ki, zaki hadu da na kirki da na banza, aikin ki na iya sakawa ki kwana a wata kasar, wani sa'in kina iya yin kwana biyar ko sama da haka, kin ga idan ke din mai sake ce komai zai iya faruwa da ke................" Hannayen nata ta kuma jimkewa sosai tana kallonta ta ce" sai dai ina so ki kasance wace ta san ciwon kanta first, ki ringa tunanin cewa idan har kika yarda aka lalata maki rayuwa da farkon fari kanki kika yiwa, Muneerath kanki kika fara wulakantawa, rayuwarki kika tozarta , Muneerath zai bi har yayanki, zai bi gaba daya ahalinki har jikokin jikokinki domin daraja na shafar iyali,.......... sannan idan namijin nan ne kika biya ya rude ki ki sani alherin dake tare dake yake yiwa zai gama da shi ya kuma damki na wata kina ji kina gani namijin da ya gama sukuwa a kanki yana murmushi gaisuwar kirki zata gagare ku domin zai dawo kyamatarki ke ya ga damar ya zageki da ke din mazinaciya ce yar iska ce bayan shi ne ya iskantar da ke, harma zaki kula da kunya yake a ga yana maki magana.......wannan shine shari irin na mugun aikin nan, ya fi bibiyar rayuwar ya mace Muneerath, sannan sai ki tuna wanda ya halice ki, shin a rayuwar da ya baki, da lafia, da hankali, da wadata ya cencenci ki saka masa ta haka? Shin idan kina da bukatar namiji ba aure ya fi cencenta ki yi ba?, Idan kuwa wani abin duniyar ne akoy wanda ya isa ya baki ba tare da gori ba bayan shi? Kin roke shi bai baki bane? Ko bakya iya rokarsa ne?......idan kika mutu me zaki ce da shi? Idan bakya jin kunyar kowa ki ji tasa!, Sai kuma iyayenki, Muneerath sunna da haki a kanki, shin kina so ki yi abinda Allah zai kama su da shi sannan duniya ta yi ala wadai da su?, Daga su a gangaro kan wa'inda suka amshi amanar horar da ke aikin nan....har zuwa kaina da na amshe ki kike hannuna, Mubeerath muma muna rokon ki da ki rufawa kanki asiri ki kame mutuncin kanki na y'a mace ki yi aikin ki domin Allah domin aiki kika je yi a duniyar jirgi ba yawon ta zubar ba, Muneerath aiki kika tafi yi ba wulakanta kai na, Muneerath burinki muka baki damar cikawa ba banzatar da kai ba, domin ke din mutun ce mai daraja, mace kike uwar al'umah, wace muke so muke fatan gannin mun wanketa cikin salama mun mikata da dumbin daraja Muneerath ki ji tausayin ahalinki, ki tausayawa marikanki ki taya mijin da zai aure ki kishin kanki, ki kare mutuncin y'ayanki kin ji?" Hawaye ne masu dumin gaske masu tafe da dumbin kauna da bege da madaukakin gannin girma da darajar Mah suka gama wanke fuskarta, bakinta ya mata nauyi ta kasa furta komai, bata taba jinta a matsayin mutun cikakiya ba irin na yau, yau gata itama mutun ce ana mata nasiha irin wannan mai daraja da girma? Ashe dama haka mu'amala take tsakanin datijan kwarai da yara? Ashe ana yiwa mutun fadan ya gyara kayansa? Ta kasa cire dubanta a kan Mah a lokacin da suka fito kusa da Katon Falon Pah bayan sun masa salama ya gama tsokanarta sannan ya dora mata da tasa nasihar suka rakota harda iman kusa da wuleliyar limozine din dake dauke da direba da soja daya za'a kaita wajen aikinta ita MUNEERATH YAR OGA sai kawai ta samu kanta ta sumbatar bayan hannun Mah kafin a sanyaye ta ce" NA GODE" Wannan kalma ita kadai ce ta fara fito mata daga bakinta domin ita ce ta fi cencenta da ta furta a wannan lokacin, ta tabata sai ta zauna zata iya gane a wani hali take ciki hakan ya sa ta shige bayan motar da aka bude mata ta zauna ta limshe idannuwanta suka harba hanya zasu sadata da baban a茅roport din da OGA HANJA ke janye da ragamomi masi yawa a ciki harda tukin da zai yi na yau dan zuwa kasar malesia 馃槖馃槖馃槖馃槖 Malamai to wai ba'a hutu hala馃槖馃槖馃槖馃槖馃槖 11/14/21, 12:49 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 3锔忊儯0锔忊儯 Maganin warin hamata a saukake shine lemun tsami, ka yanka shi gida biyu ka gurza a hamatarka kafin ka shiga wanka, kana shiga ka wanke kamar yadda ka sana wanka shine maganin warin hamata da dukan wani lungu idan kana so, sannan bashi da wani aibu, kuma ba dole kulun sai ka yi ba yana iya yi maka kwana hudu bai dawo maka da bugawar hamata ba domin wani sa'in da turaran da komai aman idan aka sha rana akan hadu da bugawar hamata har kai da kanka ka ringa jin sai a hankali jikin naka, to ba wuni a rana ba ko a ina ka wuni idan ka yi haka ba zaka yi warin hamata ba komai zufar da zaka yi Bale mu mata, mu sani turarukan nan na hamata akoy masu mugun karfin da suke balo ciwon nono boyaye, na gani da idona matar da daga fesa turaran fesawa na hamata hamatar ta dan kaikaita mata sai zuwa nono daga nan kafin dare nono ya sundume nata ashe tana da kansar nono bata bayana ba, wannan turaran ya bayanar da ita da karfin gaske, danma hannu da shuni aka fita da wuri karshe dai sai cire shi aka yi .....wannan ciwo ne kuma haka Allah ya kadaro mata ....aman akoy musababi, turare a hamata bashi da kyau bale irin na kantin nan na fesawa...........mu bincika dan tabarwa.....na gode馃槍馃槍馃槍馃槍馃槉馃槉馃槉 Sun dauki lokaci a hanya kafin suke karasawa wajen aikin Kasancewar waje ne da hanyar ma'aikatan wajen daban da ta passinger sai bata gane ta kofar da suka shiga ba, abinda dai a yau ta samu kanta da yi shine admirern abinda idannuwanta ke ganni domin a yau tar take gannin wannan duniya tasu da idon basira, a yau da hankalinta yake jikinta ya kasance wannan doguwar tafia da suka yi sam bata kula ba dan idannuwanta na nuna mata duba irin na mamaki Yan karafunnan dake bakin hanya idan suka karaso sai direban ya rage gudun motarsa sosai sai karfen ya yi kasa kafin su bi su wuce, haka idan suka tunkaro wajen duwatsu masu tsini summa sai su kauce kafin su wuce kafin su fara isowa wajen camerar da du idan sun tsaya sai ya zuge gilas din gefen da take camerar ta dauketa da kyau kafin ta nuna wata blue din wuta sannan suke sammun shigewa idan ta nuna ja kuwa baka isa ka taka gaba ko kace zaka yi baya ba domin idan bayan ka ce zaka yi da gudu wadinnan abubuwan da ka wuce ba zasu kau a hanyarka ba dan daga cen za'a hanna hakan kafin sojoji su tarboka da bindigunsu .....wannan abubuwan na cikin tsare tsaren bada kariya wa ma'aikatan wannan ma'aikata wanda ba wai dan kawai muneerath na sanye da suturar Hostess dinsu bane ya saka suka samu shigewa ba, no dan akoy hotonta da computer ke ajiye da shi sannan sunna da sannin cewa yau zata fara aikinta A haka har suka karasa wawakekiyar rumfar ajiye motocin da ta ga motoci sun fi a kirga a kimtse wula wula da su hakan ya sakata karra yin sharan da baki tana kallo har sai da ta ji an bude mata bangaren fitowarta kafin ta daga kai ta kalli sojan da ya bude mata yana jira ta fito daga motar Irin shigarsa take karewa kallo tun daga irin hular dake kansa da kuma farar wukar dake hannunsa wace ta tabata ita ce makamin dake tare da shi kadai , shigar kakin jikin sojojin oalas din ba iri daya bane da na sojan cikin gari, hakama hulunnansu ba iri daya bane sannan su ba kowane ne ke rike da bindiga ba, wa'inda ke rike da bindigogi iya wa'inda ke yawa da Hanja da ko da Sarki ne, suma gugunsu da yawansu bamgarensu daban , salarrynsu daban domin ko formation din da ake basu ba iri daya bane da wadinnan Dan murmushi ta yi a lokacin da ta ga wani dan hancinsa zuwait da shi a bayane ta ce" Allah daya gari bamban, su kiwa ga irin nasu dogarin " Shi dai a yadda ya kame mata bai ajiye ba sai da ta fito kafin ya rufe ya kuma shiga bin bayanta tamkar jela fuskar nan tasa a hade kirin da ita Da mamaki ta ja tana kallonsa kafin ta ce" Kaini zaka yi wajen? Ka ga kuwa ban san inda zan bi ba" Da yannayinsa na bata girma ya ce" eh aikina shine na nuna maki hanya sannan na baki kariya a du inda zaki je " Ido ta ruko tana kallonsa a zuciyarta tana maimaita kalmar kariya? Gannin ya nufi wata kofa ya dana wasu butom kofar ta bude ya saka ta biyo bayansa ta shiga kafin shima ya shigo da sauri ta dora hannunta ta rike dan karfen ailbar dake jiki dan ra kula irin na Palas ne mai yin sama ko kasa da bawa ya tsilira shi a yan sekwani, kai ita dai tana gannin garajen dan adam yanzun idan ya makale da kai kuma yaya zaka yi? Shikenan ka mace ko akoy yadda ake yi? Sanyin kamshi da ya buso ta da haske ne ya sakata tsayar da tunaninta a lokacin da suka bayana a cen sama wajen baban filin taron ma'aikatan A hankali ta sako kafarta waje tana kiftawa tana kallon yadda mutane ke kai kawo, gaba daya wajen sai ya so sakata juyawar kai domin waje ne mai girman gaske ga kuma mutane maza da mata sanye da suturu yawancinsu sanye ne da irin suturar dake jikinta ko kuwa dan bingilalen sket ko dogon wando irin dai kayan sweet na maza aman kowace ka kala kayanta kamar sabo dal domin ba alamu na yamutsa ko na dati a jiki bata dai san kuma bangaren wari ba, sai dayan abin takaicin ita dai bata ga daya mai kai a rufe ba, gaba dayansu kawunnansu a bude suke haka kuma irin yadda suturun suka matse su kamar da sun yi wani wawan motsi zai yage Mazan kuwa sanye suke da nasu kalas costume din watau swt baki dayansu ba mai jalabiya ko mai riga da wando na dinkin yadi ko shada, bambancin suturarsu daga color ne sai ko tsada aman baki dayansu sun sha karanpasan swtt dinsu gasu farare har idannuwanta sunna neman mata ciwo kafin take hango yan tsirakun kalarta a cikinsu, haka kuma yannayin mazan su sai ya fara sakata a tunanin to ko dai baki daya mazan su kyankyasar inji ne? Dirka dirka da su malan sai dai a yannayin baban jikin akoy mai kyau akoy kuma wanda zaka ga kawai ya yi wani sandandam, wani kuwa da katon tumbi irin an ci an tada kai a kasar nasaruma馃槍 Sai da ta gama kauyancinta ta kula ba wanda ya damu da ita kafin ta juyo ta kale shi yana tsaye ita dai yake jira ya ce" An ce na kai ki asibitinsu sai an gama maki binciken lafiyarki sannan ku tashi kunna da tafia nan da awa uku da minti goma sha bakwai" Ajiyar zuciya ta sauke ta bi bayansa suka nufi cen ciki Sun dan yi tafia kafin su karaso wajen, daga sama an rubuta sunnan dake nuni da wajen likitoci ne da inglish , nan ya ja ya tsaya ya yi mata nuni da tana iya shiga Sai da ra waiga kafin ta yi adu'a ta saka kanta Dan ja ta yi ta tsaya tana karanta waje waje dake rubuce har ta kawo kan wajen dake bayanin nan ake gannin hostess hakan ya sa ta yi murmushi ta karasa ta dan kwankwasa ta tsaya har aka bata damar shiga bayan an dauki lokaci sannan ta dafa abin ta bude ta shiga a hankali Sama sama muryarsa ce ke bada dadadan amo cikin yannayi na yana yin fada fada , bayansa ne ya ba kofar hakan ya saka ya miko hannunsa ba tare da ya juyo ba ya ce" John bani " Tsuru ta yiwa hannun nasa da kuma idannuwan da suka sauka a saman kanta na tsararun yan matan dake laye au biyar , sai uwa uba SIR da ta gani yana tsaye cen gefe shima cikin yannayin nan nasa da yakan yi masu a Nijer idan yana cikin aiki Zuciyarta ne ke dukan tara tara , tarin tsoro ya darsun mata a kasan zuciyarta na abinda ka je ya zo duda ba fuskarsa ta gani ba aman ba zata manta yannayin gashin kansa da irin tsarin kirarsa ba A hankali ta lumshe idannuwanta nan da nan ta kamo abinda ta tabata ba dai mutun ba sai dai idan Allahn ne ya kadaro mata samun matsala da wani a nan ta shiga yi shine adu'ar neman tsari ga dukan abinda zai iya cuta mata Da karfi ya juyo dan jin shiru bayan ya mikowa John hannu kan ya bashi takardar da ya saka shi daukowa dan yana so ne a masa bincike na kirki a kan su domin tafiar da aka yo da jirgin ghana an tafi da biyu a yannayi na maye, hakan ya sa ransa baci yau tunda ya shigo yake balbale au da masifa wadincen din ya kore su ya saka kuma an kaisu centre dan a yi traitment dinsu, hakan ya sa ya shigo yau komai a gabansa za'a yi bayan wannan aiki da ake masu mai yawa ne ga takale takale sai a hankali dai A kan fuskarta da ta bayanar da yannayi na tsoro ya sauke fuskarsa Da sauri ya cire da dubansa sakamakon bugawar da tasa zuciyar ta yi , sai dai cirewar ko second biyu bai bari ya yi ba ya maida saman kan fuskarta Maganar da yake yi ne take kai kawo a makogwaronsa , lokaci daya ya ji hankalinsa na neman tashi dan ba komai ya saka a ransa ya buga masa da zuciya dan ya kalli fuskar wannan rusheshiyar ba sai dan tana muguwa lale lale tana tare da wata mugunta ne, hakan ya sa ya maido dubansa cikin nata tar kafin ya ya iya jimke hannunsa da yake wuwurgawa yana fadan ya lumshe idannuwansa ya bude ya sauke a kan John da ya shigo dalilin gannin kofar bata rufe da kyau ba Hannunsa ya mike ta gefenta, sai dai ya yi daf da ita sosai ya amshi takardar ya juya da yannayin takun nan nasa ya kai saman teburin likitar sannan ya hau kan kujerar dake kusa da ta likitar ya zauna Da sauri ta lumshe nata idannuwan itama tana jin bugun zuciyarta na ta tsananta har sai da Sir ya karaso kusa da ita muryarsa kasa kasa ya ce" Ki je ki tsaya kusa da su har a zo kanki, dukan tambayar da aka maki ki yi kokarin bada amsa a kan tsari idan har kina so a yi tafiar nan da ke yau" Sai a lokacin ta sauke ajiyar zuciya ta gyada kanta kafin ta karasa kusa da yan matan ta tsaya, Sir ya bita da kallo cike da mamakin yadda ta sauya sosai kamar ba ita ba, fatar jikinta, wannan kiba tata da tumbinta du babu, sai abin kwalin da ya nuna masa harta da idannuwanta aun kara fari masha Allah, bama a maganar abubuwan da suka fi saka shi shagala da tunaninta wanda yake gannin ai normal ne idan dai namiji na iya zayane abinda yake so da mace dan ya yi tunanin nan ba matsala bane tunda dai ba tabawa ya yi ba A nutse take bin dukkan yannayin tambayoyin da ake masu da irin amsar da suke badawa cikin ladabi da kallo harta da comportement dinsu Yawu ta hadiye a lokacin da ta kusanta ta je ta zauna itama bayan an bata damar hakan tana kallo aka tsikara mata allura itama aka dauki jikkinta , aka kuma auna idannuwanta da hawan jinni akai mata tambayoyin nan kafin a umarceta kam ta je ta yi fitsari ta bada dan a tantance mahaifarta idan bata dauke da ciki Ba yadda zata yi ta iya hanna kanta barin jiki Ba yadda zata yi ta iya hanna kanta jin tsoro Babu yadda zata yi ta iya hanna kanta kallonsa domin shine dodonta, shine abinda yake bata tsoro, shine wanda ta ganni yana wasa da zakanya hankali kwonce, shin idan aka ce ya yi wasa da mutun fa yaya zai gabatar da wasan? Zai cire kan bawan Allah daga gangar jikinsa ne ya wurgar, zai kama ya raba mutun biyu ba tare da ya saka wuka ba, hakan ya sa du takunta ke saka jinninta hawa wanda ta tabata ana aunawa za'a ce ta koma gida ba zata iya tafiar nan ba Zama ta yi ta sauke dubanta a kan farar takardar dake ajiye dan idan ta dago idannuwanta a cikin nasa take saukewa wa'inda suke mata kama da zaki, domin ja ne da su sosai kamar ya sha abin

Chapter 16 of 42