Share this page
da suka dauko a wannan garin har ya kai ya yi fada da ita? Aman a kan me ya ara mata wayarsa? Ya salam, ya salam................................ Muneerath kuwa kai ta kada abinta itama ta nufi kicin domin so take ta je a mata wainar kai yauma ta gwada soyawa da kanta ko za'a dace Mah a hankali ta idasa shiga da salama a bakinta Wajen da yake zaune ya rike kansa da hannunsa ta nufa watau saman wani kujera kamar na lybi din nan masu laushin gaske Zama ta yi ta tsura mada ido a sanyaye ta kuma furta" Asalamu alaika " A Hankali ya dago jajayen idannuwansa a saman lebensa ya furta" Amen wa alaiki sakam " Mah ta mika hannunta wajen dafe kumatunsa da ya yi muryarta a nutse ta ce" Me yake damunka? Me ya hadasa maka tagumi? " Hanja ya cire dubansa a kanta na dan lokaci kafin ya juyo a sanyaye ya ce" Mah, me yasa ina kiran waya bakya dagawa hakama Pah ?" Ajiyar zuciya ta sauke tana dan hade fuskarta ta ce" Dan na fara jin haushin amsa maganarka komai kankantarta " Ido ya tsura mata a kasan zuciyarsa kuwa mamakinta ke son kashe shi, lale ya yarda cewa Mah haihuwarsa ne kawai bata yi ba aman irin yadda take karantar dukan motsinsa sai abin ya ringa bashi mamaki.....wani lamarin sai uwa A hankali ya sauko ya dora kansa saman cinyarta muryarsa a sanyaye ya ce" Inafa neman auren, ko dazun sai da na so kallon wata a Hawai....to kawai sai na ga tana ta kalona ......sai na ji haushin hakan wai me yasa da sun ganni suke fara son nuna min sunna so na? Waye ni? Me na fi wani? Ni ina so na ga wace ban dameta ba, ina so na ga wace zata wahalar da ni ba kawai dan kina mai zaman jira ba daga kin ganni ki nunan so, Mah sam ban yarda cewa ni din take so ba sai na ga akoy dai abinda take so...... Dan Allah kar ki yi fushi da ni, rabona da mace tun da zamu yi tafiar nan sai yau" A hankali Mah ke shafa gashin kansa tana jin yadda yake sauke ajiyar zuciya wai shi a nan magana ce ya yi mai tsayi A sanyayenta ta ce" Anya kuwa za'a samu? Wace zaka nuna mata so ta nuna maka aa? Wacece zata ga yarona a tsaye a gabanta komai kyanta ta girgiza maka kai ? Anya son kana so ka yi auren nan kuwa ? " Hannunsa ya dago ya dora saman nata da take sosa masa ya dan dago ya kali fuskarta kafin ya maida kan nasa a hankali ya ce" Ni na san akoyta Mah, akoy wace ba kuduni, kyauna, ko mulkina ke gabanta ba,,ni na san akoy tawa a kilace a wani wajen duda zuciyata na cike da zulumin wacece ita?, Abinda na sani koma wacece ita din ba zata amsani a zuwan farko ba, ba kuma zan sha wahala dan tankwasata ba fa.......no ina dai so ra nunan ban mata ba ni kuwa zan saka a dauko min ita na aureta" Mah ta yi murmushi dan walahi irin yadda ya yi maganar sai ya bata daria domin ya wani takwakwabe fuska dan kawai ya sa ta manta fushin da take masa A hankali ta shafa gefen fuskarsa ta ce" wace uwa ce zata so yin fushi da yaronta?, Wace uwa ce zata kulaci yaronta? Idan ha uwa takai ga yin haka tana cike da tsoro ne, shin yaushe zaka daina? Bana so ka dauka cewar ai kai naka zunubin karami ne, a zunubi babu karami bale idan mutun na yinsa kai tsaye, kai musulmi ne, zina ta haramta a gareka Khalb" Hannun nata ya rike a hankali ya lumshe idannuwansa ya ce" Mah?, Zan daina ina ji a jikina zan daina" Mah ta ce" ka ce min ka daina, ka yi min alkawarin ka daina" Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce" Zan je nemo maki sarakuwar ki, zan kawo maki ita ki rungumeta......zan aurota ......zan samo wace zata zauna da ni, zafa iya rayuwa da ni....Mah bani da ra'ayin mace sama da daya shi yasa wani sa'in sai na shiga tunanin ko sakawa nake a kawo min yan barikin na zaba?, Ni kam a halin tunani nake" Kanta ta girgiza a hankali ta ce" Idanma yar barikin ka aura da niyar cetota daga aikata aikin nan....ceto ne, aman ka sani zan fi farin cikin ka samawa y'ayanka uwa ta gari" Murmushi ya yi a hankali ya kara dora kansa saman cinyar Mah din a kasan zuciyarsa kuwa yana aiyana' tarbiyar uwa a yanzu ta fi ta ringa nunawa yaro soyaya, ba ruwanta da inda zai shiga su waye abokanansa , idan kana son gane ita ta haifa a taba shi yanzu zata fito a shiga dibar albarka da ita, Mah a tunaninki akoy iyaye irinki kuwa ?, ni ko na yi aure zan ringa zuba mata ne tana haifowa ina tarbiyantar da kayana ko na kawo maki da an haifa ki bashi tarbiya dan ni ba zan ba mace ta lalata min yaro ba!' A batane kuwa sai ya ce" i miss u" Mah ta yi murmushi a hankali ta ce" Gashi yake fitowa a kansa, gashin kuma mai duhu......kuma, kuma...." Sai wata irin kunya ta hanata karasawa , saima ta rasa ta yaya zata fada masa kuma din Idannuwansa ya rintse yana jin yadda bugun zuciyarta ke cenzawa irin abin na taba mata zuciya a hankali ya ce" Kina so ya warke ko?" Mah ta gyada kai da sauri tana kallonsa Murmushi ya yi mata ya tashi ya zauna a kusa da ita yana rike da hannunta a hankali ya ce" Yanzun zamu je mu kaishi wajen likita, kuma sai ya je" Yar daria ta yi tana kallon yadda yake harhade girar gishinsa irin zasu raba hali kennan Mikewa ya yi yana fadin" mu tafi" Ai kam Mah mikewa ta yi ita dinma cike da farin ciki domin dama ta fi son su je din dan a cen akoy kayan aiki komai da komai idan kuwa zuwa ne zai yi daga shi sai yan kayan aune aunensa Da sauri ta nufi wajen nikaf dinta ta dauko ta cire mayafin dake kanta ta daura sanann ta kara yafa mayafin sosai a jikinta Shigar nata ya kurawa ido, kulun Mah cikin shigar abaya take koda kalar ba baka bace aman abaya ce kuma kowace kala zata saka da nikaf dinta, Haka kawai a ransa yake jin sha'awar irin shigar nan nata, ji yake idan aka ce yau zata fita ba shigar nan ba zai yarda ba, yana wani irin jin shigar a ransa Murmushi ya mata ya juya ya nufi waje Ita kuwa ta bi ta dayar hanyar dan fitar da Pah cikin dabara Tunda ya nufo falon yake jin dariyarta Haka kawai ya samu kafafuwansa da rage saurin da yake dan gannin ita kuwa mahaukaciyar yar nan da wa take daria? .....ntd Hanja din da ba abinda ya shafe shi da abinda wani yake yi? Yan mata biyu ne suma a tsaitsaye da plat plat a hannayensu masu aikin gidan ne sunna sanye da dogayen sket da rigar kicin kawunnansu da hulunna itin na chef, itama ta daura hular ta chef a kanta ta cire dan kwalin hakan ya sa gashin kanta bayana har gadon bayanta sannan ta daura abin daurawar nan da ake daurawa idan za'a yi girki Muneerath ta ce" ku tsaya ku tsaya ku tsaya na irga uku sai a taba a tare, kun ga du wace ta ce wainar kwon nan bata yi ba dadi na san dan kawai mu yi fada ne, kun ga dan ta yi duhu ai ba matsala bane magi ne ya isheta sosai" Wata dariar ta kusanta ta saka ta ce" Madame, wannan kwon konewa ne fa ya yi" Muneerath ta ce" lalala, tabas baki san shi kwai sai an masa haka vitamine dinsa ke fitowa ba?, Ai idan dai kwai ne ya soyu da kyau shine darajarsa yanzun dai ku tsaya wollah ku ce ya yi dadi dan in fadawa Mah ta yi murna kun ji?" Dayar zata yi magana idannuwanta suka sauka a kan Hanja, da sauri ta ajiye plat din dake hannunta jikinta ya dauki rawa , likaci daya ta tabo yar uwarta itama ta ajiye din suka duka kasa kawunnansu a kasa dan sam basu san cewa yana gidan ba da basuma shigo a warhaka din nan falon kasan ba, ba wai dan basa shiga ba domin su suke jera abincin sai dai daga wanann basa rabarbajewa har haka, yanzu haka sai da suka kiya ta tirsasa su kan a nan zasu taba konaniyar wainar kwonta Da mamaki take kallonsu jin gaisuwar da suke fada ta juya da sauri dan gannin ko waye Ido hudu suka yi da shi ya ja ya tsata yanzunma rigar dai ce singileti fara a jikinsa bai dora Wata ba ya rufe hannayen nan nasa, a kasan zuciyarta ta shiga fadin' Kai ban taba gannin sarkacecen kato marar kunyar nuna suturarsa irin kyankyasar injin nan, yana yawo tsirara salon a yi daria ya shake mutun kai dai ka shiga uku ba komai a ranka alamu sai iskanci ni kam ai na fada ba ni ba kai mafadacin banza mafadacin wofi, sarautar takuma da ba rawani ake maka ba fuska a bude kowani banza yana kalkonka in zaka fita....' daidai accenseur din yabude su Mah suka fito Mah na fadin cewa a rufe hanyar kasa zasu fita da PAH Idannuwansune suka sauka a kan Hanja da ya zubawa Muneerath ido yana jira itama ta kwashi rawar jikin ta sada kanta kamar yadda Iman ke yi, sauran ke yi, ga kuma Muneerath vry cute.....so muah yarinyar ta keru rigar kuma ta karbeta, da sauri Mah ta riko hannun mijinta da ido ta nuna masa sannan ta masa alamun ya yi shiru bata kula da su ba ita domin ya kare su da wannan kirjin nasa ya wani tsaya yana hararar mata kawaye, idan takamarsa gidansu ne ai mamansa ta kawota bale ya koreta kau? Dama irin wadinnan sai girman ba wayau Dan bakinta ta murguda ta juyo da dan fada fada ta ce" Kai dillah ku tashi mu yi wasanmu ku kuma" Wayo yaya zan yi da muni ni kwate馃槶馃槶馃槶馃槶馃槶馃槺馃槺馃槺馃槺馃槺馃ぃ馃ぃ馃ぃ馃ぃ馃ぃ馃ぃ馃ぃ馃ぃ 11/14/21, 12:51 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 3锔忊儯5锔忊儯 Wani irin luuuuuuuu ya yi da idannuwansa a tsayen da yake da sauri ya kara dora dubansa a kanta Kan iyayensa ya juyo da fuskarsa domin zuwa lokacin ya kula da sun sauko Irin yadda fuskarsa ta fara zama ja ransa ya nuna bacin rai karara kafin ya juya da waji irin sauri ya fice a falon ya saka mahaifinsa kallon Mah Murmushi ta sakar masa a sanyaye ta ce" Mu je mu dawo" Sai a sannan Muneerath ta ankara da su Ajiye nata plat din ta yi itama ta nufo su tana dan murmushi a nutse ta ce" Pah barka da warhaka, Mah kun sauko ne?" Mah dake kallonta tana sauraron Pah na amsa mata lokaci daya wani tunani ya ringa darsun mata a zuciyarta Murmushi ta yi a hankali ta shafi gefen fuskar Muneerath ta ce" Muna dawowa ku shiga kicin ku yi girki " Tana gama fada ta bi bayan Pah da yayi gaba tuni Tafia ce suka yi tamkar kurame, tafia ce ta sirri domin mota hudu kawai ta masu rakiya sai tasu ta tsakiya ta biyar Gari bai san da fitowarsu ba,hanyar kasa aka tsare su kadai suka bi har suka sada kansu da makeken asibitin inda likitan ya tarbe su ya gama aune aunensa Kwarai shima ya yi mamakin fitowar gashin, ya saka shi a injin yin scan ya gama daukan komai zai samu manyan likitoci a yau su duba result din a tare dan gannin me ya faru me yake shirin faruwa da shi Ya tabatar masu cewa bai taba gannin cas din da aka kai wannan matakin gashi ya fito ba,sannan bai taba gannin wanda ya kai wannan matsayin ya samu lafia ba, dan haka yana tsaka tsaki amsar da zai basu ma kan takardun dake hannunsa zai dawo da kansa da dare A haka suka fito a cikinsu Mah ce kawai bata wani karaya ba da maganar bayahuden, abinda ta sakama ranta harma take kara rikewa da karfinta shine Allah ya yi magana, sai da ya saukar da maganin cuta ko wata iri ce, ta tabata idan zai tashi zai tashi, kuma wannan alamu da suka gani ta tabata ba na banza bane dan haka baa cinkushe zuciyarta ba Mahaifin Hanja kuwa tarin tausayinta,da na yaronsa, da na al'umar kasarsa ke cinkushe a kasan zuciyarsa A lokacin da suka fito da ido yake bin du wa'inda aka tsare yana kallo , yakan nema masu sauki har kasan zuciyarsa kafin su shige su kamo hanya Hanja kam kansa a jikin madubi ya lumshe rinanun idannuwansa Gaba daya wani lokacin sai ya ji zuciyarsa banda kunna babu abinda take yi Kamar irin wannan lokacin na yanzu, ya rasa a wani mataki zai ajiye halin da yake ciki da tunaninsa da zuciyarsa baki daya, hakan sai ya hadasa masa tashin hankali mai tsananin gaske Idan ya kalli mahaifinsa sai ya ji dama yana iya gannin ciwon nan?, Idan ya kalli fuskar mamansa sai ya ji shi din ba kowa bane ba kuma komai bane tunda har gashi a tsaye a gabansu sunna cikin hali na rashinu walwalar zuciya aman ya kasa kawo masu mafita sai dai ya kale su Abinda ya fi sakawa a ransa shine zai ci gaba da kamanta faranta masu har karshen numfashin shi yana mai musu addu ar dawwama cikin farin ciki tare da kwanciyar hankali mai daurewa har suka iso gida hanja bai sani ba tsabar ya tafi duniyar tunani sai jiyayi mah na taba shi firgigit ya dago tare da fita a cikin motar ya shiga bin bayan su mah da tuni sun isa cikin kayataccen parlon su ciki ya shiga kamar marar laka a jikinsa ya samu daya daga cikin kujerun dake zagaye da parlon zaunawa yayi batare da ya ce musu komai ba Mah ce ta taso daga inda take ta iso gareshi da sauri ta zauna kusa dashi Dafa kafadun shi tayi cike da damauwar yannayinsa tace" son lafia kake kuwa gaba daya yau bana ganin ka daidai daga zuwan mu hospital har zuwa dawowar mu , shin mai yake faruwa dakai ne son pls tell me " ta karashe tana shafa gefen wuyansa Daidai lokacin aka gama gabatar masu da drinks dan su sha dan huce kishirwar hanya zabura yayi kamar wanda aka tsikara ya mike tsaye magana yake cikin fada yana cewa " Mah ba zai yuwu ba wllh, wannan yarinyar terrorist ce ni nasan kashemin ku take son yi !" Da sauri ya dora hannunsa a gefen kirjin shi da ya mishi mugun nauyi yace" Washhhhhhhhhhhhhhhhh" dadai lokacin da ya hada ido da muneerath suna karasuwa ita da iman dan yiwa su mah barka da dawowa basu lura da yanayin da hanja ke ciki ba sannu da dawowa sukawa su mah suka shige abinsu karasawa yayi gaban pah ya hade hannayen shi duka biyu yana rokon pah akan su masa rai su ni san tata da shi wllh shi bai taba ganin fitsararriyar dake kallon sa ido cikin ido tai masa fitsara irin yarinyar nan ba, Muryarsa a raunane ya ci gaba da fadin" pah baku ba har dani yarinyar nan take son halakawa sabida jiki na yana bani a duk lokacin da muka hada ido da ita inba terrorist bace ba zan ringa jiin hakan ba pah tabbasa akwai wata kulleliya da take shiryawa akanmu dan ra tsaka ta kona mu!" Ya kuma kallon Mah da ta tsare shi da ido tana karantasa cike da mamakin yannayinsa a hankali ya ce" Pah idan ka hada ido da ita baka ji gabanka ya fadi?" A sanyaye pah ya girgiza kansa shima cike da mamaki n wai me yarinyar ta tsare masa har haka? Hanja da ba abinda ya dame shi da lamarin wani shine du ya fitini kansa a kan yarinyar da bata tsare shi da komai ba? Idonsa cikin idon Pah ya ce" Ko daya baka jin haushinta a ranka?" Pah ya rike hannunsa yana kallonsa ya ce" Son me yake damunka ne? Me ta yi maka ne? Idan wani abin ne yake faruwa ka gabatar min da shi sai na nisantata da kai da mu baki daya, aman idan baka da huja ka barmu mu idasa ladanmu mana" Kalon mahaifinnasa yake a kasan zuciyarsa yana tunanin wace huja suke so da ta fi wada yake fada madu a yanzu? Wace suke so ne? tashi yayi cikin fushi ya bar parlon tamkar zai tashi sama inda Mah ta raka shi da kallo tana murmushi tana girgiza kai a hankali, Pah kuwa ya raka shi da kallon tashin hankalin yannayinsa mah ce ta karaso kusa da pah hannun shi ta kama ta zauna a kusa da shi sosai a hankali tana shafa gefen fuskarsa tace " mai ka fahimta gami da son ?" tagumi pah ya rafka yace" nikam da za abarni sai ince na fahimci wani abu" da sauri tace "kamar me?" Pah ya dan watsa hannayensa ya ce" Ba zan ce ga takamaimai ba, ban san me ta tsare masa ba, ba itace mutun ta farko da muka dauka ba, ba itace kalar bak'ar fata ta farko da muka dauka a cikin duniya ba, sai dai ita kadai ce ta africa, sannan kwarai haka ne ita kadai ce mai kallonsa cikin ido harma ta juya kai tsaye ta ci gaba da magana bayan yana wajen a tsaye tamkar kowani mutun ba abinda ya dameta, tabas itace ta farkon da na ga ta aikata haka ya yi diri diri ya wuce bai dora hukunci a kanta kai tsaye ba, na yi mamakin da yake nan shawarar barinta zai yi ko korata zai yi.....hakan sai ya sakani tunanin a cikin rudani yake cikin biyu watau barinta ko koratan, kin ga ya dora mata sunna wai terorist......ko wa ta tada a gabansa?, Kin ga Prince yana fada akan mace? Sai na ji ina son zama na ringa kallonsu, sai na ji ina so mu yi cij abinci a tatare da su a table daya a lokaci daya ina kallon su, sai na ji haka kawai ina son na zauna a daidai lokacin da zasu yi fada.....haka kawai nake jin koma meye na yarinyar nan alkhairi ce ga rayuwar son, tabbas na gano tanada matukar tasiri a cikin rayuwar sa ta halin fada ko jituwa......" murmushi mah tayi tace" isha Allahu lokaci zai nuna mana Allah yasa hasashen dana ke ya tabbata akan son da muneerath" fuskanta ya shafa ya kashe mata ido daya ya ce" ameen ya Allah kalb" Sunkuyar da kanta tayi tanajin kunyar pah saboda abubuwan yanzu da yake mata na soyayya tunda shekaran jiya zuwa yau kuma ba wasa yanzu ita har mamaki take yadda jarumtar shi ta dawo kamar ba shi ba, ba zara taba manta yau din nan ba, bata tunanin zata kuma samun ranar sai gashi ta sameta ido bude, ita kam me zata ce da wanda ya haliceta bayan ta kara ninka ibadunta? .....a kasan zuciyarta ta furta'Alhamdulilah' kama hannun shi tayi tace" muje kayi wanka ka huta lokacin shan maganin ka ma yayi" a tare suka mike pah yana dan bata rai sabida takura shi da take na shan maganin nan .............................. ....... Su muneerath kuwa suna komawa daki ita da iman wace ta biyota dakinta , haka kawai tunanin yadda aka yi ya bata wayarsa take hakan ya sa ta mugun sake da ita dan so take ta fada mata wai ta yaya hakan ta faru? toilet ta fada dan yin wanka saboda wainar kwan nan da ta soya wai ita a ganninta tayi wani babban aiki ne Iman ko guri ta samu a bakin gado ta zauna tunani ta fara na yadda zata bulluwa muneerath tabbas jikin ta zata shiga sabida a dan zamansu ta gane muneerath din ba wani wayo ne da ita ba sabida haka ta samu makamar da zata na cusa mata kiyayyar ko wane irin namiji kawai ta tsaya ga dogarin ta ya fi mata domin itafa ta hasasu kamar ta fara samun matsayi a gurin hanja so ya kamata tayi wani abu akai duda bata tunanin wai Hanja zai iya kula wannan yarinyar,aman fadan sun nan ya tsaye mata a rai Muneerath ce ta fito daga wanka daure da towel a kugunta gaban madubi taje dan daukar mataji ta taje kanta da ta wanke tare da abun busar da kai dagowa iman tayi dan jin mutsin muneerath din ta zubawa faffada kugunta ido ko keftawa batayi cewa take chab din gaskiya dole ma inyi wani abu akan yarinyar nan tun bata tafi da abinda na dade ina muradi a rayuwata ba oh ji yarinyar karama da kira kamar ita tayi kanta cab da sake wllh tasowa tayi ta matso kusa da muneerath din da take ta kokarin shafawa kanta data gama busarwa mai Da nata salon son kusanta kanta da Muneerath din ta ce" dan kawo na taya ki mana?" Muneerath ta dan kaleta a ranta tana ayana 'su yan gidan nan mamaki suke bani, sai su ringa shiga harkar mutun da sanyin rai bayan mu a namu gidan eh yane ne, kana kallon wanima zai dura maka ashar ya ce kallon fa? Ni du sai na ga wani salon munafirci ne sun kama yaro sun dura masa vitamine ya zama gabjeje yana yawo da yar riga a cikin mutane yana langwui......' dan murmushi ta yi tana girgiza kanta tuno tambayar da ta yiwa sir cewar wai dan Allah shi zai tuka mu? Sir ya mutu da mamakin jin dalilin tambayar nata dan cewa ta yi ita walahi du kallon wani dan baba da rai take masa, a anguwarsu kuwa idan aka matsawa mutun da sunnan dan baba da rai irin yayan nan ne da ake sangartawa basu iya komai ba sai sangarta da fada da shirme, Kumewa kawai ya yi a ransa yana ayana lalle duniya mai ba dan adam dama, lamarin rayuwar Munnerath na saka shi kallon duniya a yar mitsitsiya mai cike da abin al'ajab ......watau mai dauke da al'uma masu abin mamaki, A hankali Ta ringa taimaka mata tana dan janta da hira haka kadan kadan tana nuna mata yadda zata yi kwalliya da sauransu dake iman din yar gaye ce kwararriya ce kuma wajen iya kwalliya tuni muneerath taji dadin yadda iman din ta koya mata simple mak up wanda ya yu mata kyau ko ya zauna das a kyayyawar fuskarta Komawa bakin gado sukayi iman ta dago kanta ta kalli muneerath tace" niko in tambaye ki man ?" Muneerath ta dubeta tace "inajinki" iman tace" daman gami da dogarinki ne ni ban taba jinki kuna waya dashi ba ko irin ya kawo miki visit dinnan a bazatan nan duba da irin yadda na sha ji kina maganar dogari" Muneerath ta dago ta kalli iman irin a rikice dinnan ta turo dan bakinta tace" to ai ni dogarin ma bamu taba haduwa dashi ba sau daya ne ma wataran nazo wucewa ta kofar fadar garinmu na hange giftawar shi sa ilin da zai shige cikin fada, sai kuma a hanya idan zai wuce , sai kuma ranar da zaku sato ni, sai na nan na wasan karam da kuke cewa dogari, yo Allahna tuba dogari fa dan uwan sarki ne, shima fa rawani yake sakawa, kafar sarki kafarsa, Mamanmu ta ce idan na samu dogari na caba, jira dai nake na koma gida idan ba dogari bana tunanin zan iya aure ni kam" Da mamakin hirarta iman ke kallonta, abin mamaki, idan ta kula yainyar nan batama fara soyaya dogarin nan ba?, Da sauri ta mike ta

Chapter 20 of 42