Share this page
ba na zaune zai kama hararata, ki duba ki ga sau biyu ina suma a saboda shegen Zakinsa, Saudat ke fa shaida ce dan tsabagen tsana na ce Freind zai zo wajena ya ce ba zai zo ba dan yana gidansu ko?, Kuma sau uku yana zo min dan Mah ta ce idan ya kara ne zan samu ciki na ki ya karan fa, aman dan Allah me hakan yake nufi ke da kanki kin san koda Pah ya fadi haka ya fada ne dan ya kular da shi, baki ga haka yake tsokalarsa ya yi ta cika yana batsewa ba?" Dafe kai Saudat ta yi cike da tunanin ta inda zata fara kafin ta dago kanta ta ce" Da farko kar ki kuma budar bakinki a gaban kowa ki ce wai namiji ya zo maki, kin kuwa san menene ma'anar an zo maki?, Ciki baya samuwa sai idan mace da namiji sun kwonta sun yi hvng sex , idan na ce maki sex ina nufin sun samu moment a tsakaninsu da basu da shamakin komai babu wani hijabi da ya tarewa daya gannin tsiraicin daya, zasu raya sunna ce mai tsafta da tsayawa a rai, zasu zama abu daya ne , zai kasance sun samu nutsuwa da junnansu ne ta yadda a duniyarsu babu wani abu kuma da ya rage da zai zamo boyaye ko bako a garesu, na biyu ki fito min a mutun ki min maganar tsakaninki da SIR HANJA, na uku daga nan gidanku na nufa domin nawa iyayen sun yi tafia paris dan visite na rashin lafiyar mahaifina, kafin su dawo ba zan je gidanmu daga ni sai mai aiki ba , ba kuma zan kama h么tel ba" Muneerath ta dafe gaban goshinta itama cike da rikicin magangannun kawar tata, ita har ga Allah abin daria nema yake bata, kuma dukan abubuwan da ta zayana ta yi masu waje ne ta ajiye su a irin tsabagen kula irin ta Familly din Su Pah Gaba daya sai ta mata shiru ta tada motar, kai itafa abinda ya fi damunta shine tunanin yadda za'a yi Ta samu waje a gidan Oga ba tare da an kai ruwa rana ba Cike da shagalta da kallon garin haihuwarta, wajen da ya tara iyayenta kakaninta, danginta take tuki har ta dauko duguwar hanyar da zata sadata da kofar gidansu Abubuwan da suka cenza a garin basu da yawa sosai, sai gine gine da ta ringa ganni sai gyaran hanyar da aka yi wanda idan za'a hada da kasar da ta fito ne babu mahadi, sai dai abinda yake tsaye a kasan zuciyarta irin farin cikin dake daskare a zuciyarta ya wuce tunanin bawa A hankali ta yi kwana ta samu ta dakata dan nesa kadan da gidansu tana karra wara dubanta a kan wanda idannuwanta ke ganni A hankali kafafuwanta suka dan fara yi mata rawa rawa, zuciyarta ta shiga dokawa da dukan karfi, zufa da tsoron da Saudat bata taba ganni ba a tatare da Muneerath ya bayana a tare da ita Tabas da take ce mata idan tana so ta ga rauninta ta bari idan tana kusa da ahalinta A hankali ta ce" Muneerath ? " Muneerath ta juyo da sauri tana kallonta ta kasa amsata A hankali ta ce" Ina ne gidan? Kin ja kin tsaya jikinki na rawa kin kafe wancen mutumen da kallo?" Muneerath ta hadiyi yawu a hankali tana karra jimke hannunta dake saman cinyarta a sanyaye ta ce" Oga ne cem tsaye, wannan tsayuwar da Oga ya yi idan aka tabo shi ne, ni kuma bana so na fado daidai ran oga a bace, kin ga tsayuwar cen da ya yi ko dansa ya taba shi zai ga ikon Allah, ga kuma gidan namu a bude ham ban san me yake faruwa ba" Da mamaki da kuma tausayi ta karra kallon gidan da Muneerath ta fito, a kasan zuciyarta ta ayanna 'Lalle babu mai daukaka bawa sai Allah' Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" To ki tada motar mu karasa mana" Ido ta zarro ta ce" Wa ni?, Na je gaban oga da motar nan a haka mu yi kaka da shi?, Kin ga mu juya kawai mu koma karma idannuwansa su juwo kaina a haka idan ya bar kofar gidan sai mu dawo" " KUT Walahi baki isa ba!" Saudat ta ce , da sauri ta kama marfin mota ta bale ta fita kai tsaye ta durfafi wajen da Oga ke tsaye zuwa lokacin ya ga tsayuwar motar duda bai kure su da ido ba aman haka kawai ya ji zuciyarsa na yawan son ya kalli motar Da sauri Muneerath ta fito tama zarro ido ta ce" Kan balaki, Saudat ki fa bar balaki ya yi barci , karfa ki yi garaje fa" Wani marfin langa da aka jefo daga anyar kofar ya saka Saudat ja da mugun sauri tana kallon wajen da kuma hayaniyar dake fitowa sama sama Kafin ta idasa fahimtar komai wani uban dutse ya biyo baya ya sauka a kusa da kafarta harma ya shafi yar karamar yatsarta Da sauri Muneerath ta ja hannunta gefe ta nemi nausuwa cikin gidan ranta bace, sai dai kafin take idasa saka kafarta aka yi baya da ita Wani wawan mari dayar ta kifawa daya, da gudu suka karra kurmiyar junna sunna dukkan junna da kokowa Oga dake tsaye dadage yake dan gannin wai da gaske abinda idannuwansa ke gane masa ne? Gannin ta shige cikin al'umar gidansa ya saka shi nufar Saudat da ta yi mutuwar tsaye tana kallon ikon Allah Da sauri Saudat ta rufe fuskarta dan tsoro ne ya shigeta kar a je Oga ya wanka mata mari Oga ya kare mata kallo ya ce" Ke dillah bude idannuwanki ki fada min wannan yar wacece?, Kamar kamar y'ar oga sai dai abin mamakin kalar fatar wannan ba ta africa bace sam sam" A hankali ta bude idannuwanta tana kallonsa da tsoro, ta kuma hangi Muneerath ta hakikance a cikin yan uwanta ba mai ba yar uwarta hakuri domin a fadan harda kanwarta ana ta dakuwa A dan tsorace ta ce" Eh Muneerath ce" Sai da ya kwalalo ido kafin da sauri ya nufe su Da wani yannayi irin na yan daba ya ringa eartarsu da daidaya yana kifa masu mari yana maida su gefe da gefe kafin a haukace ya ce" Zaku nutsu ko sai na kira police ya kwashe min ku baki daya na huta da jaraba?!" Du wajen ne ya dauki shiru sunna kallonsa koea na huci tamkar kububuwa A dake ya ce" Yar oga? " Muneerath dake tsate rike da kanwarta gaba daya sun kara tara mata gajiya sai da gabanta ya fadi da sauri ta kale shi kafin a raunane ta amsa still tana kallonsa Du da mamaki suka juyo suma sunna kallon nata lokaci daya ana kare mata kallo tun daga kasa har sama Daya daga cikin matansa ne ta saki buda tana rike dan karamin hancinta ta ce" Lale bariki ta yi rana, wai dama wannan Muneerath ce? Tabdijan iskanci ga mai daure maka gindi a gidan Oga!" Muneerath ta budi bakinta zata yi magana idannuwanta suka sauka a kan fuskar mahaifiyarta Shigar maman nata ta so ta bada mata ko wacece, sai dai irin yannayin da ta tsareta da duba ya sakata karra kallonta da kyau Oga ya yi juyi ya kuma juyowa cike da mamaki ya ce" Wai yar oga da gaske dama a ingilar kike? Muhamadu rasululahi salalahu alaihi wa salam na shiga uku, wai yanzun ke din nan Hostess ce? Walahi ni du a tunanina kin hadu da wani dan iskan ya gama hore maki kunne irin na yar uwarki, Yar oga yanzun daga ina kike? Na shiga uku dama na san zuciyar nan taki tawa kika gado idan nace sai na yi sai fa na yi, gatanan Babarki da na ganta na nace sai ita na kuwa bi ta inda na bi itama ta haukace sai ni aka aura mata ni iyayenta suka yi fushin zuciya da ita suka salama min na rungumo abina gatanan wai yanzun ta saku ta daina sona aman saboda ke take zaune ta ga ta inda zaki dawo yau gaki Allah ya dawo min da ke shikenan sai ta daina fushin ta fuskanceni mu fuskanci junna" Da rashin fahimta take kallonsa tana son karrin bayani, sai dai bai bata wannan damar ba ya shiga kora yaren cikin gida Ruuuuuuuuuu da su da iyayensu suka aniya nufar cikin gidan Lokaci daya ya dakata ya tsare matan biyu da suka yi saura wa'inda ke dakuwa da junna ya ce" Kai,hala da nace na sake ku a tunaninki wasan yaa nake?, Ke delu dama saki daya ya rafe mana na cikashe maki shi, ke kuma sarai ai biyu na baki a jimulce dan haka ba sauran zama da ni da ku , ku kama gabanku jarabar ta isheni haka, inm lalatace ne ni da saka hannun matan nan, kun mayar da ni kamar dan dambe ni kunlum ina cakuwa da mutane ana abu kamar yam wiwi, ni ban ajiye ba ban ba wani ajiya ba, to ku sani na gaji iya gajiya, y'ayan oga kuma ku barmin su zan iya da fitinarsu, ke Bakuwa shigo mana na raka ki bangaren su Yar ogan" Da sauri Saudat ta daga kafa ta karasa ya ja hannunta ya turata ciki ya rufe kofar harda saka sakata kafin ya ja ashar da rantsuwar du shegen da ya bude shi da shi ne kafin ya tisa keyar Saudat da ta gama gane cewa lale Muneerath din yar ogan ce, sai kuma ogan ke iya mata A tsaitsaye suka same su a falon Mamansu Muneerath na tsaye tana kallon mahaifiyarta cike da mamakin yannayinta Oga ya yi dan gyaran murya yana dan wani abu kamar wanda yake tsoron shiga kai tsaye ya ce" To ki zauna mana wai tsayuwar ta mecece?" Muneerath ta juyo tana kallon Oga ta kuma kallon mamanta Mahaifiyarta ta dube shi a kausashe ta ce" Me kuma kake so Mutari?, Dan Allah ba sai ka shigo nan ba ka tafi kawai na ji da y'ata ta fada min a infa take! Ka koma ka barni da ita idan takamar y'ayanka ana masu taken sun gado rashin mutuncinka yau ta dake ni sai na san na hada jinni da shedan!" Da sauri Saudat ta juya zata fita a dakin Muneerath ta yi gagawar kamo hannunta ta janyota ciki A hankali Muneerath ta kalli Mamanta mahaifiya a gareta muryarta a sanyaye ta ce" Sai nake gannin kamar kin damu da son sannin daga inda nake, ko kuma kina son sani ne dan ki wulakantani?, Inace Sir ya shaida min an yi kira na nemi alfarmar a bani ke kin nuna ba sai kin amsa ba kawai na gaishe su?, Shin kin manta burina na son zama hostess da nake kwana da shi nake tashi wanda kika ce min ni mahaukaciya ce?, Ko kina son ce min a yanzu kin san darajata bayan na rayu da ke cikin rayuwa ta halin ko'in kula wace baki san darajar kowa ba sai oga?" Idannuwanta dake rintse tana sauraron datata mangangannun yarta ba taunawa ta bude rai bace ta dauke Muneerath da wani gigitacen marin da ya saka Oga yin tsuru tsuru har cikin zuciyarsa ya ji amsa kuwar marin kafin da sauri ya shigo gaba dayansa yana rike Muneerath din da ta buda idannuwanta da har suka fara yi mata ja tana kallon Maman nata Rai bace mahaifiyarta ta ce" Ki sada dubanki a cikin nawa kafin na saka yan yatsuna na kwakwale maki ido na zubar a wajen nan Muneerath !, Ki tausasa kalamanki a kaina tun kafin na koya maki yadda ake furuci wa mahaifiya!, A yau idanma karuwa ce ni, idan yar shaye shaye ce ni, idan mahaukaciya ce ni , nisawa na yi kika tsago jikina kika fito....kuma a haka da haukan nawa da iskancin nawa na shayar da ke na suturtar da ke!, Idanma kakan tsatson marar mutunci kika tsago kika fito ki kula ki tausasa muryarki a kaina in ba haka ba komai na iya faruwa ciki harda rasa harshenki domin ba zan maki baki ba ni, sai dai na ringa tsinguyar naman jikinki daya bayan daya har na karar maki da su!" Oga da idannuwansa ke rintse da bacin rai da abubuwan da matar tasa ke yi ya budi baki a sanyaye ya ce" Me zai hanna mu samu kebewa mu tatauna a nutse ta yadda kowa zai fahimci kowa ne?, Kina gani fa daga doguwar tafia take" Da dan daga murya, da bacin ran da take ciki ta juyo a hasale ta ce" Dillah ka rufe min baki azalumi, maci amana wanda ke raba y'aya da iyaye da kowa nasu dan cikar burinsa!" Wani marin ne ya sauka a jar fuskar mahaifiyar Muneerath wanda hakannua saka Saudat kaiwa kasa saman gwuiwowinta cike da tsoron al'amarin dake faruwa Shima yanzun cikin daga murya ya dubeta cikin ido ya ce" Ya isheki haka!, Na ce ya isheki haka kin ji? Na yi, na je na yin!, Me yasa a lokacin da na zo wajen ki da maganar soyaya dan kin ganni a kafa na yi aski irin na gayun zamanina kika tofa min yawu a fuska kika aibata ni kika nuna gidanku da irin motar da kike tukawa ta alfarma kika ce da ni aman mahaukaci ne ni kuma bani da magaya ko?, Kika aibata min iyaye kika aibata min dangi kika nunan ko akuyar gidanku ta fi karfin na yi zaman aure da ita bale ke yar gata mai gata gaba da baya?, A kan me da na zo baki yi min maganar kirki kika rabu da ni ta sigar da ta dace ba sai kika wulakantani mafi munin wulakanci harda watsa min ruwa dan na nemi soyayarki?, Ni bana tare da kuruciya ne ko bani da zuciya a cikin kirjina aka fada maki ?, Walahi walahi ban taba son mace kamar yadda na so ki ba, a kan dole dan na rayu da ke na kuma koya maki hankali na maki asirin da na raba ki da danginki da duniya baki daya ya kasance a duniya idan ba ni ba bakya gane yaren kowa, idan ba soyayata ba bakya fahimtar ta kowa, sai dai halayanki na yawo wajen biki wannan ba ni na dora maki ba, idan kika auna izina ce ta hau kanki Allah ya nuna maki shi ke shiryarwa, kin zageni da dan iska dan kawai na zo a shiri irin na yan gayun da basa jin magana, ke sai gashi da aurenki kike yafa dan gyale kina shagalinki duda na yarda cewa ba maza kike bi ba aman yawon ta zubar din da kike Allah ne ya nuna maki !, Ba zan iya ba, walahi ba zan lamuncewa kowa ya wulakanta yar oga ba, Halina kuma da kike zagi cewar mugun tsatso mugun hali na ji na dauka, ni dai bani da hali irin na izgili!, Idanma a yanzu kike son koyawa y'ata ladabi ki bita a sannu kar ki rikita min ita domin kaf cikin y'ayana zan iya rantse maki ita kadai nake iya shama kur'ani!" Yana gama fada ya juya har yana gannin duhu duhu a idannuwansa ya fito, nan fa ya ga y'ayan yan mata sun layu sunna saurare hakan ya saka shi tsayawa ya kare masu kallo gannin sun yi tsuru tsuru ya ce" Kowace ta fida mijin aure nan da sati biyu in ba haka ba in ban yi sadaka da ku ba ku ce min shege!" TABDIJANNNNNNNNNN 11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 5锔忊儯4锔忊儯 Marin da ya wankawa matar tasa tamkar wanda ya saka mata sakata a bakin nata ya gume mata Koda yake a kalamansa ta samu yaren shiru ta arawa kanta kafin da sauri ta juya ta nufo dakinta jikinta na bari ta rufo Zamewa ta yi nan kasa hannayenta na rawa baki daya ta kurawa waje daya ido Tabas an yi haka, a hankali ta shiga tunano ranakun da take shiryawa ta fita gari idan kucakin namijin da bai amsa sunnan namiji ba ya yi gigin tunkararta ya nuna mata so irin tizga ahin da take yi, ba zata manta ba har kara koyon karatun wulakanta namiji take yi Ba zata taba mantawa ba ranar da ya nuna yana sonta har ruwan bakinta ta furza masa domin a lokacin har kiransa ta yi da wani muninsa kamar gwogwon biri, ba zata manta tana masa diban albarka yana share zufa yana karra kallonta har ta dire aya ya ce da ita dan tana da kyau kuma tana yar mai kudi ne take masa irin wannan wulakancin ?, Shin shi ba dan adam bane ko ta ga alamun a halitarsa an rage shi da wani abu?, Dan ya zo ya nuna mata so sai ya kwashi kashi irin haka a hannunsa? Ba zata manta irin hucin da abokinsa ke yi ba yana fadin Oga ka barta a gidan nasu mu nuna mata muma irin namu ikon, aman sai ya ce da su wannan ta haramta wa irin haka a gare su, wannan din ajiyar oga ce, ta oga ce kuma sai ta haifawa Oga abin alfahari! Wani kukan ta kuma rushewa da shi na dana sannin mugun halaya irin na yan mata masu jiji da kai da neman fitina da tunanin su sun fi kowa Ashe ita ta janyowa kanta wannan rayuwa?, Gashi dai sanadiyar rashin lafiyar da ya yi ya karya abinda ya mata da kansa wanda yana da makarin tsayin shekarun nan wanda tamkar wace ta yi barci ta farka ta ganta da shekaru zagaye da ahalin gidan Oga masu wuyar fasara Hauka jajir ta zuba masa a sume ya kaita gidansu nan ta tarar da sai yayanta daya rak da iyalinsa mahaifinta ne dama ya rage mata shima ya rasu , bayan ta sanar masa komai ya karra yi mata nasiha ya lalabata kan a yanzu gidan mijinta shine kwonciyar hankalinta ta rungumi y'ayan da ta samu da shi ta yi kokarin basu tarbiyar da ita ta yi wasa da ita, koda kuwa Oga ya kasance mai baudaden hali da damansa a kan wani, tunda shi aurenta ya yi ya kilaceta , da wani ne a hakan zai aifata ya kuma murje ido ya mayar da ita dakin ziyararsa, duniya ta yi lalacewar da baka yiwa mutun komai bama yana son ya kasaraka bale ita din ta yi garaje da yawa, dan haka ta kula ta kiyaye ta yi hakuri Oga kansa tana iya mayar da shi yanda take so koda iya cikin gida zai dawo tausasashe wa su a waje kuwa a ogansa yake da kyau, dama shi rayuwarsa ta yan jagaliya ne shi ba barawo bane ba kuma mazinaci bane, da kyau a halayansa akoy na kirki tunda yana sallah ai a yi masa uzuri, shima kuruci ta saka shi aikatawa, duda hali na kuruci zafin sonki ya saka da ya maki hakan bai yarda makarin ba, a yanzu da lokacin ki dawo hayacinki ya yi kib ga ya karya gaki kuma da ranki da lafiyarki ,sai dai a karra yi masa adu'a Allah ya shirye shi, ya ahiryar masa da zuri'arsa Ta ringa rusa kuka a lokacin tana shaida masa batama san inda Muneerath ta shiga ba, ya ce Wai ta samu aikin Hostess aman bashi da tabas tunda bai je ya gani ba, wai a waya aka fada masa a waya, kuma yake zaune hankali kwonce y'a mace?, Ita kam ba zata iya zama da mutun irin Oga ba, zata koma aman da zarar yarta ta dawo zata kwaso y'ayanta ta dawo gidansu Shi dai rarashinta ya yi ta yi, a nan ya kwaso mara tsabar dukiyarta da aka raba gado ya jingine da takardun gidaje har kwaya biyar, da kudin dake banki milioyi na gadon da suka gada ita da shi a wajen mahaifinta, ya dora mata da fadin gadon Mahaifiyarsu bai taba zuwa inda suke ba, kasancewar kasa ce ta nasaru shi bama shi da ra'ayin bin kudin nan da dukiyar, wanda yake cikima sun ishe shi A hankali ta kara rike kanta dake sarra mata tana wani kukan na takaicin rayuwarta, tabas ta yiwa kanta ila, yanzun ta ina zata fara da tarbiyar y'ayanta?, Har yanzu ba wani jituwa suke da namijin ba, matan kuma su uku ne du a wani bambarakwai suke kallon cenjin da ya samu, aman ba komai kamar yadda datijuwar malamar islamiyar da take zuwa take fada mata cewar adu'a, da adu'a zata Wayi gari ta ga abinda yake impossible Allah ya mayar mata da shi possible, Oga kansa halita ne na Allah, akoy masu kashe kashe da suke dawowa su zamo tamkar basu taba yi ba, idan har ta jure kaima Allah kukanta kokowar da ya dace ta dankara a tunaninta tana barci Allah zai yi mata shi ta hanyar shiryar mata da zuri'arta baki daya Tuna wadinnan abubuwan ya sakata saurin mikewa ta shige bayin dakinta dan ta dauro alwallah ta hau salayarta har a yi kiran sallah Saudat dake tsaye a tsorace tana kallon Muneerath jira take ta fashe da kuka ta yadda otama zata samu ta fashe da shi na tsabagen tsagwaron tsoron dake cin zuciyarta na wannan hargitsi da aka yi A hankali ta dora hannunta dake rawa a hannun Muneerath a sanyaye ta ce" Munee kar ki yi kuka kin ji?, Dan Allah mu je idan ta huce sai mu dawo ki bata hakuri kin ga ba'a yima iyaye magana a haka, ki ga mu yan africa ne da mari iyayenmu ke nusar da mu ba da rarashi ba, mu je idan ta huce sai mi dawo ki yi hakuri" Da mamaki Muneerath ta juyo jin wai karta yi kuka tana kallon Saudat Me zata yi banda dariya, ai kam ta bushe da daria tana jan hannun Saudat da ta fara kokonton anya ba Allah ne ya hada ta da mahaukaciya kawance ba? Dakinta ta jata mai dauke da gadonta daya sai sif din kayanta Sunna shiga ta rufe ta saka hannunta ta kunce yalwatacen gashin kanta ta barbaza shi sosai ta zauna a kasa nan tana kara cusa hannunta cikin gashin kan nata kafin ta dago ta kuma yi yar dariya tana girgiza kanta tana kallon Saudat da ta kasa zama dan a tsorace take ta ce" Kin san me hakan yake nufi?, Kin san me wannan ranar take nufi a wajena?, Wannan ranar tana nufin babar ranar da ban taba riska ba mai dadi da farin ciki, wannan ranar itace ranar da nima zan fara tinkaho da kaina, kin kuwa gane me nake nufi?" A hankali saudat ta girgiza kai tana kallonta Muneerath ta nuna mata gefenta tana nufin ta zauna A hankali ta zauna a gefen na Munnerath din Muneerath ta kamo hannunta ta ce" Saudat, a da ba tafia ba idan namiji zan kawo a gaban Mamanmu walahil azim zata kare mana kallo ta cire kanta ne ba tare da ta fahimci jinsin namiji na kawo mata ko mace ba, ke bara na kare maki magana idan ana magana aka ce min yar iska sai ta daga kafada ta ce ita ina ruwanta in ina so na zama karuwama matsalata ce!, Saudat idan kin ga na yi doguwar magana da mahaifiyata to fa a kan kudi ne, shima kudin da take nema ido rufe dan kawai ta siyo maganin mata ko me? Ta kawo ta yi ta sha wanda ban san ko na menene ba, ita dai idan kin ga tana kwalkwaltu to fa dan ta gyarawa Oga ne, a kan Oga tana iya batawa da kowa, a kan Oga tana iya kisa, Saudat nakan yi kuka na tsayin wuni guda ina tambayar kaina me yasa ko irin na sauran yan uwana da zaki ga idan abu ne iyayensu sun shigar masu fada ne ko idan aka zagar masu y'aya iyayensu na tarewa ni tawa uwar sai dai ta taya mutanen a zage nin?, A lokacin da na kawo maganar ga wanda nake da

Chapter 31 of 42