Share this page
nan, aman yanzun nima zan faso zai ga rashin mutunci, Ke yar oga nawa ne kudin?" Ba Muneerath ba harta mahaifiyarta sai da ta zarro ido bale kishiyoyinta Da sauri ta sanar masa kudin na tsayin wata biyu har jikinta rawa yake lokaci daya mahaifiyarta ta ce" Aa oga gaskiya ba haka za'a yi ba, to ni nawa bukatar fa, na fada maka ina son kudi wayata ta fara samun matsala tun ranar nan ka ce na bari ranar aikina na faranta maka ka bani kuma yau ne ranar zaka wani bata kudi?" Da sauri kishiyarta ta cafa da fadin" Ke bama wannan ba, a kan me zai bata kudin koyon wani ruwa na kaniya? Ai muma nakuda muka yi muka haifa sai ka zana na kowa ka bada dan ba wanda ta fi a gidan nan Walahi ko a yi tashin hankali!" Murmushi ya yi ya mike ya soka wayarsa a aljihunsa ya kalli Muneerath ya ce" Sai ki san irin zaman da zaki yi da kowani shege a gidan nan, kina dai gani irin bakin cikin da suke maki, idan kika kware kika zama hamshakiya kika kula su inaga a nan zan tsine maki kowama ya huta!, bari in je in biya da kaina ki shirya gobe ki fara abinki yar oga!" Yana gama fada ya yi waje, nan da suka juyo gaba dayansu kanta, ba wanda baya fadin abinda ya zo masa bakinsa cike da bakin ciki da jin haushinta tamkar zasu cinyeta danya Ita kuwa gaba daya sai abin ya kara sace mata gwuiwa, mahaifinta ne wannan, ta zo masa da maganar da mai yiwuwa namiji ne zai koya matan, sannan ta yiwuwu su ki yarda da cewa zata yi da wando mai dan tsayi dan kare mutuncin kanta, aman bai wani dan tsaya dan binciken komai ba ya kada kai ya tafi, ga kuma mahaifiyarta na mata fada a kan dan me ta kawo bukatar kudi a lokacin da ita ta so kawo tata? To ta nemo mata cikon kudin wayarta ko ta ga iskanci .................idannuwanta ta lumshe a lokacin da ta rufe dakinta ta fada saman gadonta a sanyaye ta furta "YA ALLAH" 11/14/21, 12:43 PM - Allah Akbar: 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 6锔忊儯 Da kyar ta iya samun barcin da take son samu, da wuri wuri ta farka ta fada wanka , a gagauce ta gama shiryawa cikin shiga ta wani zumbulelen hijab mai ruwan madara ta dauki byro da convocation dinta na shiga aji da takardar shedar yar kasa ce ita da dan sauran cenjin da ya rage mata a jakarta ta makaranta Sauri take zubawa sosai domin a kafa take tafiar tana yi tana duba lokaci da kyar Allah ya taimaketa tana isowa ana ta kirate kirayen sunnate , harma an kirayi nata sunnan dan haka ta dakata a kofar ajin da zata gabatar da nata jarabawar sai da mai kiran ya gana kiran sunnan kowa sannan ya amshi convoction dinta ya duba sunnanta da number table dinta, gannin tana cikin wa'inda zasu shiga ya bata hanya ta shige Tunda ta shiga ta kurawa waje daya ido , gaba daya hankalinta take son kwontarwa a zaunen nan da take dan ta samu gabatar da jarabawarta cikin nutsuwa hakan ya sa ta shiga tunanin abinda zai sakata farin ciki, a sanyaye ta afka begen abin bege, cikin nutsuwa ta kama salati a kasan zuciyarta idannuwanta lumshe, a hankali take begen daha, dan aminatu sayadi, d'a ga abdulahi, sidi baban kasum, ya abul Ibrahim, shi dai Abul fatimatu zaharau, a hankali take dan motsa bakinta har wata dake bayanta ta dan tabota A hankali ta buda idannuwanta tana kallonta A sanyaye matar mai dauke da tsohon ciki sosai ta ce da ita" Kanwata lafia? " Kai ta gyada tana kallonta alamun eh lafia kalau Matar ta yi murmushi itama bata kuma ce mata komai ba Sunna haka aka fara shigowa sa takardun harabawar , Bayan malaman sun gama caje kowa da duba yannayin zama sun tabatar kowa na zaune a saman kujerarsa suka nuna masu camerar da aka saka dan su kula kowa ya yi aikinsa wannan rana bata kai ranar tsayuwa a gaban Allah ba aman itama kowa ya yi ta kansa ne, mulkin sabon shugaban kasarmu ya tsaya tsayin daka ya toshe dukan wata hanya ta sata a kasa komai kankantarta kuwa idan dubunka ta cika komai kusancinka da shi ba zai sasauta maka ba Takardun da aka raraba masu suka dukufa karantawa, sun fara ne da FRAN脟AIS dukan seri din da shi suka fara ba A ba D ba C domin shine yaren da kowa ke anfani da shi dan magana a makaranta watau school , shine yaren da nasariya ta kawo mana Tunda ta sada kanta kasa ta nutsu take rubutunta bata dago ba sai idan ta ji ta kage sosai take dan dagowa ta dan huta kadan sannan ta mayar da kan nata ta ci gaba da aikinta, lura da masu tsaron suka yi ita kanta bata damu da kallon wasu ba ya saka su yin cen ciki Cikin ikon Allah ba ita ta tashi daga zaunen da ta yi ba ko da ta kare ta ci gaba da biyawa sai bayan awa uku da mintunna kafin ta mike a hankali ta kai ta ajiye ta saka hannu a wajen saka hannu sannan ta fice a class din Tana fitowa ta nufi wajen masu siyar da abinci, dala arba'in ta bayar aka zuba mata dambu na dala talatin da biyar aka bata piyawata na biyar Cikin nutsuwa ta samu wajen zama ta kebe ta karya ta kora da ruwa, bata nemi komawa gida ba a nan ta zauna har ta shiga aji ta yi na yamma kafin ra kama hanyarta a kafarta ta koma gidansu .......................................... A ranakun nan da aka yi na jarabawa kwana biyar cif matar nan na hankalice da irin hankali da nutsuwar Muneerath, kasancewar ba wanda ya santa a ajin hakan ya sa lamarin dogari bai bayana ba har aka gama jarabawar lafia sannan suka je gida zaman jiran result A tsakanin ranar da jarabawar zata fito ta rasa gane kanta ita kanta, ta matsa da adu'a da tashin tsakiyar dare kamar yadda malaminsu ya basu adu'o'i tana fadawa Allah kan ya sa da rabonta a wannan jarabawa, kokari take, burinta ta wayi gari ta ga ta fado cikin masu sa'ar samun cin wannan jarabawa hakan ya sa take wuni da azumi sannan ta rike kafarta domin daga ita har kawar tata hankalinsu ba a waje daya yake a kwonce ba tunanin result ya saka su sun zama wasu shiru shiru da su sam basa iya anfanarwa kowa da komai bale kansu A yau kwana hudu kennan da gama exam dinsu kuma a yau suke tsaitsaye cirko cirko gaban manyan makarantar da suka zo daga wani garin dan gabatar da jarabawar sunna jiran jin sakamakonsu Idan ka dubi fuskar kowa a birkice take da tarin tsoro, ba mace ba namiji, ba mai kannanun shekarun ba datijo, sannan yawancinsu sun zo da masu rakiyarsu ne wasun iyayensu ne , wasun yayunsu ne, da wuya dai ka ga mutun shi daya kwal a irin wannan lokacin sai Muneerath kawai dake tsaye kafafuwanta na yi mata rawa A cikin zuciyarta maganar da ta rubuta ta shanye take maimaitawa kanta, kin ga Muneerath idan baki samu ba ba komai, haka Allah ya yi, kuma Dogari ba sai kina da BAC zai soki ba, kin ga muneerath ki kwontar da hankalinki burinki na son kasancewa HOTTEST ba dole a tashi daya zaki iya zama ba, idan kika jure a gabama sai ki ga an dace A hankali ta lumshe idannuwanta a lokacin da suka yi ido hudu da yayanta, tsayen yake shima kuma ya kurawa waje daya ido shima sakamakon yake jiran ji, 'Ko wa ya zo dubama?' Ta tambayi kanta a kasan zuciyarta sai kuma ta cire dubanta ta maida wajen masu fadin sakamakon a lokacin da suka fara bayanin sakamakon ta hanyar fadin adadin da suka fado Ecrit, da oral, da kuma adadin da basu samu ba A kashi dari 37% gaba daya suka samu , sauran nan sai dai su sake wata shekarar Nan fa ciki ya duri ruwa, iyayen yara da y'ayansu du suka shiga kama sunnan Allah, harta kiristocin sun rintse ido sunna tasu sallar "Wanda ya zo na farkon Centre, ya samu wannan kwali tare da mention TRES BIEN shine *ABDUL KARIM MUNEERATH*" Baban Jurry din ya fada wanda yake ba'adare ne, sai da ya fada ya dan saurari na kusa da shi da abinda yake fada masa kafin ya cenza maganar tasa cewa "TA MACE TA" (MACE CE DA YAREN ADARANCI), "TA Mace TA" A tsayen da take zata rantse da Allah a yau bata gane sunnanta ba, BAC jarabawa ce mai matukar wahala a kasar Niger, idan yaronka na yi kai hankalinka a tashe nasa a tashe, burinka ya samu jarabawar koda ita kadai dinta ne, ko a scnd grup ya fado akan yi maka barka bale idan ya fado a na farko, uwa uba ta zamana kaf school din ta dauke makin kowa, sai ita kanta ta kasa gaskatawa a lokacin da ake fada har ana maimaita sunnan a tsayen da take ta kasa wani motsin kirki bale ta iya gane da ita ake Da wani irin ihu ihu yayanta ya girgizata yana fadin" Ke muneerath kina ji kuwa? Kin samu fa" Idannuwanta da sukai mata nauyi ta lumshe da dukan karfinta ta bude a kansa, da kyar ta budi bakinta ta ce" Da gask........" Bata idasa fada ba ta tafi luuuuuuuuuuuuuu gaba dayanta zata jirkice kasa aka kakamata aka riketa cikin yan kamatan harda mai cikin nan kafin sojojin dake tsaye suka karaso suka amsheta suka nufi asibiti da ita da yayan nata domin sunna wajen ne dama dan hanna fada da dauke masu sume sume da matsar da masu ihun kuka Mai cikin nan ce ta mikawa yayan Muneerath wata yar farar takarda ta ce da shi" Dan Allah ka bata ta taboni idan ta ji sauki " Shi dai amsa ya yi ya soke a aljihunsa ya shige wuleliyar motarsu suka yi asibitin yana cike da jin dadin abinda ta samun, daga ball yake ya ce bara dai ya tsaya ya ga in da gaske karatun take, a rayuwarsa yana son karantun boko kamar me, shi yasa yake dan shiri da ita a gidansu, ba wani uwarsu daya ba uba ne kawai daya aman shi ba ruwansa ko wanda basu hada komai da shi ba idan ya ga mai ra'ayin karatu ne sukan dinke abinsu sunna shiri sosai Sunna isa aka amsheta bayan sun yi bayanin komai suka so ya bada number iyayensu, budar bakinsa sai ya nuna marainiya ce shi kadai ya rage mata, ba dan komai ba sai dan ya san idan ya bada din ba wanda zai zo ciki kuwa har mamanta domin shi kansa shaida ne ya sha jin sunna shewar wai ita ce ke yin bac ko wa zai bata? Dan haka sai ya ki badawa kawai ya zauna da ita aka shigar da ita wajen mararsa lafia dan a bata taimakon gagawa kasancewar asibitin gwamnati ce aka kawota ........................................ . Zaune suke su su uku, likitoci ne manya domin su dukansu doctarori ne, tataunawarsu ne suke cikin hira da raha kamar aminan junna , aiki suke sunna shiri tsakaninsu, kasancewar babu emergency ya sa suke zaunensu sunna hirarsu hankali kwonce Macen dake zaune itama doctern ce mai sunna Halima ta ce" To yanzu Moise kai ka yi hakurin ka aureta mana, kar ka ce dan ta kiya da farko yanzu ta dawo zaka kiya kaima" Moise din ya yi daria, da ganninsa Bashi da adinnin musulunci a tare da shi, bakinsa ya buda ya ce" Kya ji ki da wani lalatacen magana nan niya, ji ke an ce da ke ni din Doguwa ta min baki na da zan yarda mu koma da wancen makirar yarinya? Ni ai ba dan shagiya bana bale na yarda, ta je ta amri wanda taka so lumui nima na samo tawa lumui na amre abina mu yi zamanmu, ke ni nan da kika ganeni bana kara yarda da waral matata, zan samo bak'ata mu jesu zuwa mu yi amrenmu dan na gane wararen tunaninsu halitar na aljana aka zuba masu suke daga kawuna da su" Ba'adare kennan, cikin hausarsa ta adarawa ( *Ki ji wani banzan zance a nan wajen, an ce da ke Doguwa ta min baki ne da zan yarda mu koma soyaya da wancen makirar yarinyar? (DOGUWAR WATA ALJANARSU CE A CEN GARIN DOGON DUTSI), ni ai ba dan shegiya bane bale na yarda, ta je ta auri wanda take so lafia kalau, nima na samu tawa lafia kalau na aure abata mu yi zamanmu, ke ni nan da kika gan ni ba zan kuma yarda da farar mace ba, zan samo bak'ata mu je mu yi aurenmu dan na fahimvi fararan fatar nan tunaninsu halitar matan Aljanna aka zuba wajen hakitarsu shi yasa suke girman kai*) Dayan likitan namijin ne ya yi daria yana girgiza kai ya ce" Kai Moise to meye dan ta dawo? Kai ba musulunci bama ka zubar ka dauki Christanci ai bamu ce mun fasa zama da kai ba ko?" Zai bashi amsa nurse din dake gadi ta nemi izini ta shigo, cikin ladabi ta sanar masu an kawo wata da ta suma a wajen fadin sakamakon jarabawar da aka gama MOISE ne ya dubeta da kulawa kasancewar shine babansu ya ce" kya ji balaki bata samu ba ko?" Da ladabinta ta ce" Aa itacema premiere du centre, emotion din ne ya sumar da ita, a yanzu dai mun yi mata dukan abinda ya dace dan gannin ta farfado harma ta farfado din , kudin treatments ne muke son sannin a asusun gwamnati ko mu ba yayanta ordonance?" Kallon junna suka yi, haka kawai Moise ya ji yana son zuwa ya ga Premiere du centre din da ta sume dan tsabar jin dadi ko me? Yana son ya ga irin farin cikin da iyayenta suke yi a irin wannan lokacin, yana so ya ga irin nata farin cikin itama, dan haka ya mike yana gyara rigarsa ya ce da sauran yana zuwa sannan ya fito a office din suka raka shi da kallo Ajiyar zuciya Halimar ta sauke tana dan girgiza kanta Dayan abokin aikin nata ne ya dan rage muryarsa ya ce" Har yanzu sonsa kike ko?" Da sauri ta kale shi kafin ta dan girgiza kanta a sanyaye ta ce" Wani irin so kake so na yiwa mutumen da ya yi gagawar sakin adininsa dan kawai ya tsinci kansa a cikin hali na damuwa? Ka duba ka gani Musa daga fadawa halin kangin rayuwa mutanen nan suka ribance shi ya zama kirista shi kadai a familly dinsu, a da fa mahaifinsa baya amsa gaisuwarsa har ya dawo yake amsawa, shin baya tsoron mutuwa ta masa zuwan da bai shiryawa ba? Ko baya tunanin shiryuwa ? Ko har cen kasan zuciyar Musa ya gama zubar da adinin gaskiya adinin musulunci ya dauki na kafurci ne?" Shima ajiyar zuciyar ya sauke ya dauki byro ya shiga rubutu a baban kundunsu , tabas abin nan ya matukar girgiza su, basu taba tunanin wahala zata saka mutun ya bar adininsa ya fada wani ba a lokacin da yan wani adinin suka nuna masa idan ya shiga nasu adinin zai ji saukin wahalar dake damunsa, bale Musa nasu, Musan nan ba'adare ne gaba da baya, haifafen garin dogon dutsi ne, Musa akoy mutunci da faran faran shi yasa komawarsa dan yesu yake masu ciwo a zukatansu Tunda ya shigo ya ja ya tsaya yana kallonta A yanzu zumbulelen hijab din da ta zumbula baya jikinta yana ajiye saman gadon sai wata riga marar nauyi aman ba gajera ba a jikinta wace ta siyi abinta a gwonjo, rigar mai ruwan orange ce da dan baki baki kadan a jikinta, tana da kyau sosai rigar bata da dogon hannu gajeru ne aman kuma ba sirara ba A zaunen da take hawaye take wani na korar wani ta rike hannun dan uwanta gagam Cike da shashakar kukan ta ce" Ka gani kau? Inaga fa Aurena da Dogari zai tabata , ka ga na samu BAC yanzun sauran koyon girki, koyon ruwa, koyon allura da zama Hottest, daga nan Dogarina zai zo inda nake, ka ga ni ba mahaukaciya bace ko" Da mamaki yayan nata take kallonta kafin ya dan janye hannunsa ya ce" Ke tunda kin warware tashi mu je gida, ko in da hali ki ga likitan mahaukata kafin mu bar nan din, ke yanzu ina hadin samun Bac dinki da wani aljaninki wai shi dogari? Kai in ba dan ba da na ce Dogarin nan naki ya ci ......" Da sauri ta mike daga zaunen da take a saman gado ta kai hannunta ta rufe masa baki ranta ya soma baci , yannayi na tsiwar da ra watsar kwana da kwanaki ya dawo sabo fil a saman fuskarta ta ce" A sha weekend lafia 11/14/21, 12:43 PM - Allah Akbar: 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 7锔忊儯 Muryarta na fitar da amo marar dadi, sai dai ba zagi ba munanan kalamai, a yannayin maganarta zaka gane ciwon maganarsa take ji har kasan zuciyarta ta ce" Yanzu tsakani da Allah me na yi maka kuma? Du ka tsalake ka rasa wa zaka zaga sai mijin mutun? Ka ji tsoron Allah idan kana abubuwanka, shi dogarin me ya daka maka ne yo? Ka ga bana son tashin hankali a yau dan haka ka je kai da Allahnka ko ba dogari ba zaka zo neman Alfarmar a hadaka da sarki kiri kiri na kiya" Galala yake kallonta haka shima doctern, gaba daya rigar dake jikinta ya zubawa ido da wannan tsari na halitarta, dankari makari wannan kayan nasa ne, kuma zasu zama nasa, shi Moise ya wayi gari da wannan kaya? Ai wannan yarinya ko yar waye ko meye take takama da shi zai jure ko su waye samarinta zai kasa su ya riketa tasa shi kadai ya more iya morewarsa Murmushi ya yi a lokacin da ta juyo suka yi ido hudu bayan yayanta ya mata wani irin riko da yannayin fushi fushi ya ce" Ke, cika ni " Ido ta kikifta tana kallonsa Da hargagi ya ce" in baki cikani ba na wanka maki mari sai sun kara dana maki kirji zaki farka a wajen wannan! Yawu ta hadiye ta sake shi tana kallonsa cike da jin haushinsa, kai in ba dan tana tsoron ya nanata da kasa ba da ta tirje masa, da mace ce yar uwarta ta zagar mata dogari sai ta fyala mata mari ko wacece Wucewa ya yi fuuuu yana fadansa a bayane yana fadin" Na gama yarda baki da hankali, ba dogari ba dai jar rigama ta ci........." ya kuma auna ashar din abinsa A sanyaye ta dauki hijab dinta ta saka, Moise ya gyara tsayuwarsa yana gyara rigarsa ya dauki takardarta yana dubawa, cike da tausayi da son ya fara share fage ya kaleta ya ce" Aya Allah jikansu " Turus ta yi tana kallonsa kafin ta dan tsaya gannin docter din ne ta ce" Su wa fa? " Karra kallonta ya yi da kyau irin wushiryar bakinta ta matukar birge shi ya ce" Su iyayen namu " A yanzun kam ya kara dulmiyar da ita hakan ya sakata gyara tsayuwarta ta ce" Iyayen su? " Shima sai ya fara jin kamar kalaman bakinsa zasu kubce masa ta hanyar rasa me zai fada, da dan sauri ya ce" Ke ba marainiya bace?" Bakinta ta dan tabe kafin ta girgiza kanta a hankali ta ce" Basu mutu ba " Kwarai ya ji mamakin gannin an saka bayanin cewa marainiya ce, hakan ya sa ya kalli Nurse din da jiran karrin bayani Itama har tana inda inda ta ce" Yayanki ne ya ce shi yayanki ne iyayenku sun rasu" Muneerah ta girgiza kanta ta ce" To ni dai a fitowata daga gida da ransu ban sanba ko yanzun suka mutu, bara na je na gani" Kallon junna suka yi Moise da Nurse din suka kuma kaleta, ba komai ya basu mamaki sai irin maganar kamar ta daketa kamar bata daketa ba, domin da farko wani dan turus ta yi , sai dai amsar da ta bada kamar bata shaku da iyayen ba ko kamar idan sun mutun ba zata damu ba? Nurse din dai juyawa ta yi ta fita dan a yadda ta ga Moise na ta magana da sanyi da lalami ta tabata da abinda yake so, dan haka ta basu waje A sanyaye ya ce" Ki yi hakuri kin ji? Kamar ranki ya bace" Wannan karron ita din ce mamakin hakurin da ya bata ya kamata, wannan fa docter ne, a asibitin gwamnati ba na kudi ba, yake rarashin patient?, kowa ya san wasu likitocin yadda suke da gwagira da kwasar marar lafia bale a irin asibiti irin namu yaku bayi, lalamatan da yake ya sakata tsayawa da kyau tana fuskantarsa , a sanyayen itama ta ce" Ka yi hakuri dan Allah " Murmushi ya saki yana kallonta ya ce" Kina da kyau sosai Muneerath ko?, ina tayamu murnar samun Bac " Hannun da ya miko mata dan su gaisa irin yana tayara murnan nan ta bi da kallo aman ta kasa bashi hannun sai murmushi da ta masa da kuma nanata "MU" din da ya yi anfani da shi a karro na biyu kennan dan zai yi maganar da ta shafeta Da dan sauri ya ce" Sunna na Moise Ibrahim Mustapha, Docter ne ni ina aiki a nan da kuma manyan clinik din dake cikin gari, na jima ina aikin na samu abin hannuna daidai misali, bani da aure, kuma bani da budurwa bani da yaro ko yarinya bani da wace na ajiye a gida muke zaman Conquivinage (Zaman da christoci, ko mararsa adinin musulunci ke yi da budurwarsu kamar matarsu, ta masu girki su zo su ci su yi mu'amalar aure da ita harma su hayayafa, wasun sai sun tsufama suke yin auren wasun kuwa sai an hayayafan kuma a dawo a watse kowa ya kama gabansa dama ba aure aka daura ba) da ita ba" Kwarai ta yi kokari da bata ce da shi ba' Ni kuwa ina ruwana' , aman kuma irin kallon da take masa ba sai ta fadi cewar ina ruwan nata ba shi da kansa ya fahimci cewar abinda yake fada bai dameta ba dan haka ya gyara tsayuwarsa kamar a gaban sarakuwarsa yana jin nauyinta sosai ya ce" Ko zan iya samun number wayarki?" Wannan karron tsakaninta da Allah ta ce" Wani abin na yi ne? Idan kudin maganin ne dan Allah ka min alfarmar na je gida na samo na kawo maka, idan babanmu na nan zai bani na kawo maka ka ji? Yanzu so nake na je na ga aminiyara ta samu? Na tabata itama tana nemana ne" Dan matsowa ya yi kusa da ita sosai hakan ya sa ta dan matsa tana kallonsa da kuma kallon gadon wada ke kwoncen mace ce kuri kuwa su take kallo marar lafia ce Cike da kwarewa wajen sace zuciyar yan mata ya dadafe abinsa ya fitar da dukan iliminsa ta wannan fannin ya gyara tsayuwarsa da

Chapter 4 of 42