zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance
Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai馃馃徎鈥嶁檧锔廳uk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba
Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki
Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu
Sannan munada beauty kit馃duk me bukatan (flawless skin/perfect glow) toh yy kokari yamallaki set dinnan wn zncn baa mgn馃馃徎鈥嶁檧锔廲uz duk inda kayi se ankalleka馃榾
Buh gsky wnd besan yy haske karyayi using set din cuz gsky yn sa haske buh bn bleaching ne b zaidai murje fatane nd bring out that hidden beauty in you馃槏
Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself
100%tested nd trusted
Beauty kit:11k
Soap price:3k
Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free
Maiso kindly message 08062991549
Call 08064532391
Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai馃檹
Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta馃檹adade anayi sai gsky馃き馃
Mg's skincare
*Ba EDDITING*
Da wani irin wawan karfi ya rukunkumeta a jikinsa yana rintse idannuwansa
Hanneye biyu Oga ya dora a kai yana zuwa maimakun ya tsaya ya kula su sai ya zarce ya karasa kusa da baban dogarin nan ya ce" Salihu hala sarki ya daura masu auren ne ?"
Shashakai Salihun ya kale shi ya kasa magana ya sake maida kansa kasa dan sam bai san yarinyar yar gidab abokinsa oga bace, abokin shashancinsa kennan
Oga ya ce" Kai wai ba da kai nake ba? Muneerath ce fa yar gidan nana ka ga ya rungumeta a gaban al'uma Idan sarki ya daura ne wage muryar nan taka ka shela uban kowa ya sani ka fa san bana so a taba mutuncin yaringar nan haka kawai Allah ya saka min kaunarta a raina "
Salihu kasa kasa ya ce" Ka yiwa Allah Oga daina min magana baka ga wai umarnin sarki muke bi kawunnanmu a kasa ba, ka ja su ku shige ciki ta yaya sarki zai daurawa y'arka aure baka sani ba sai kace garin maguzawa, hala kwacen yar za'a maka?"
Oga ya ce" Na sani ne, ni kam dan Allah mu je gidan sarkin na fada masa idan da hali a daura auren nan, na rantse maka da Allah muna kwonce a wani irin gado mai laushin balaki yar oga ta saka aka daukomu a jirgi daga mu sai ranmu tana rusa kuka kamar an ce da ita Oga ya mutun nan aka kawo mu kasar nan aka zube kamar yan iska, ahine yanzu ya biyota dan bakin hali ta ki ta yafe masa ka ga ya rukunkumeta a jikinsa a gaban su Ladi? Kana hangen wata inuwar ciyayi ta jikin garun cen? Kan ladi mai kanwa ne fa komai a kunnayenta kuma a idannuwanta, kar ya cutar min y'a ya tafi ya barta na rasa mai aurenta ka ga Nana ta dawo hayacinta komai na iya faruwa, ni kuma idan Nana ta barni ai ra kare min Salihu"
Muryar Hanja da ya bude da karfintan nan kamar zai fasa wajen yana mai fadin Attahir ya matso da mota ta suma ne ya saka su kallonsa
Da turanci yake magana, a cikinsu babu wanda ya san takamaiman me ya fada sun dai ga kamar kuka yake rusawa ga shegiya yar Oga a kirjinsa luf har zuwa lokacin
Kai ya girgiza ya ce" Allah mai iko, da ace wata yar gagarumin malami ce ni nan zan ce asiri ne, ka ga y'arka ce kuma ake haukanta haka, kuka ne fa yake ko?"
Oga ya ce" Allah wadaran naka ya lalace Salihu da ka ga kukan da yar ogan ke yi itama sai ka yi mamaki, na zata yar nan ba zara yi hankali ba sai gashi ta yi shi tsaf abinta, ka ga mu je wajen sarkin in dai za'a barni na ganshi kawai walahi ni dai yau a yita ta kare gaskiya na gaji da iskancin yar oga da saurayinta"
Salihu dake kallon yadda ya talabeta ya shigar da ita motar sannan ya yiwa Saudat maganar da ta sakata juyawa da sauri ta nufi wajen mama dan ita har ga Allah bata san ina Oga ya nufa ba ya ce da Oga" ai ko ni nan kai tsaye yau na yi magana da sarki bale kai, kai fa inaga daga yau ka zama aminin sarki ni kuma amininka matsayi ya karru, kai idan kana so har ba sai an maka sarautar ba, Sarkin ingila ne fa, mu je kawai mu je na raka ka"
Ai kam ratsewa suka yi ta baya, suka fice a kafarsu dan kam Oga ya kai makura mafita yake so gaskiya
Saudat na zuwa bakinta na rawa ta fadawa mama abinda yake faruwa
Kafin mama ta yi magama kishiyarta ta dira ta ce" Suma? Suma ko munafurci, yanzu dama Muneerath aikin da take yi kennan?"
Mama ta rintse idannuwanta cike da tsoro, da firgicin lamarin ga kuma baki irin na yan uba ya fara shiga ciki
Saudat ta hade hannayenta a sanyaye ta ce" Mama, Muneerath na bukatarki, mama Muneerath innocent ce, bata san komai ba mama, dan Allah ki je wajen y'arki ki kula da ita sunna jira"
Mama ta sauke ajiyar zuciya muryarta a sanyaye ta ce" Saudatu ai ba motar tasu zan shiga ba ko?, Su yi gaba bara na dauko cenjina mu shiga sahu kin ga yayanku baya nan bale ya kaini a tawa motar"
Murmushi Saudat ta yi ta juya da sauri ta karaso daidai lokacin da Attahir ke kallonta ya ce da Hanja" Sir kar ka yi mata baki da bakin nan dan bata iska, ka yi hakuri mu a nan ba'a haka , ka bari ga Saudat din nan ta dawo mu karasa asibiti akoy a nan kusa in sha Allah"
Da mamaki ya dakata da niyar bata iska ta bakinta dan ya dawo da ita daga duniyar sumar da ta tafi yana kallonsa, mamaki yake na irin tsaurin al'adunsu, a halin na rashin lafiarma sunna da wani zabi da yannayin al'adunsu? Yana mamakin idan ana tunanin wai jikin Muneerath yake so, zai yi matukar mamakin idan aka yi tunanin jikinta yake so
Abinda Saudat ta fada ya saka shi rufe motar Attahir ya ja su suka nufi asibitin da ta fi kusa da gidan su Muneerath din, inda duka masu biye da su suka kuma kwasar ragamar taronsu suka bi bayansu
Yayar Muneerath ce ta fara kwala ihu tana zarro idannuwanta ta ce" Shiri ne ko? Wannan abin wasa ne ko? Wayo na shiga uku wacece ake so din? Da gasken dan sarkin ingilar ne? Yanzu du ya wuce mu ya sauka a kan Muneerath ? Walahi ba zai yiwu ba, ai in kyan ne mun fita, in kirar ne mun fita, shikenan sai oga ya sakata makaranta mu ya kyalemu yanzu kuma ace ta yi miji mai kudi jinnin sarauta? Bazai yiwu ba walahi!"
Nan fa wani tashin hankalin ya kaure, domin wa'inda suke adawa da abin sun kasa boye adawarsu, haka kuma wa'inda suke farin ciki da abin sun fitar da farin cikinsu karara sun nuna a gaban kowa
Mama kam ta buga, ta kuma buga wayar Oga tana ringin aman baya dagawa dan ta sanar masa cewa summa ne fa Muneerath ta yi kuma gasu zasu bisu asibiti, aman sam wayar oga na ringin ya ki ya daga, a kan dole ta fice da hijab dinta domin dama tunda ta dawo hayacinta suka dora yarjajeniyar in dai fita ta kama dole shi walahi ya yafe ta je kawai, shi har wata kunya yake ji idan tana tambayarsa wai zata fita, kai mace mai tarbiya duniya ce
______________________________________
Kawunnansu a kasa suke su dukansu biyun, tunda Oga ya yi magana ya kare Sarki ke kallonsa da mamaki da kuma al'ajabin abin
To wai ahi abinda yake tambayar kansa a ina suka hadu da junna yarinyar tasa da Sarkin Ingila? Lalle matar mutun du inda take sai Allah ya hada su ta hanyarsa mafi sauki a wajensa
To shi yanzun bai san ta inda zai fara ba gaskiya, daga zuwa ya nemi masalaha da yarinyar sai kuma ubanta ya fito da maganar nan?, Sai dai ya zama wajibi ya saurari korafin talakansa bale a gaskiya a wajenmu ba yi ake yi ba, ya ce a gabansa sau biyu ana rukunkume masa y'a, za'a bincika idan komai bai ahiga tsakaninsu ba a san yadda za'a yi gaskiya
Wayarsa ya bada umarnin a miko masa
Sai da ya fara duba kudin dake ciki domin kira Niger to Ingila ba abu ne na wasa ba koda hello ne kadai zaka ce bale doguwar hira ce gaskiya, kuma baya so su yita ta mesage ko ta whatsup
Gamsuwa ya yi da cajin kudin wayarsa kafin yake tura sako kamar haka" Asalamu alaikum, bukatar tataunawa da sarki a kan mahinmiyar maganar da ta shafi mai Girma Hs excelency HANJA"
Bayan ya gama ya ajiye wayar yana karra kallon yadda Oga ke kiririta da kafafuwansa yana dan kale kale, wai a haka an mugun yi masa gargadin ya nutsu fa idan ya samu kansa a gaban sarki, sai ya samu kansa da tunanin to yaya kuma tarbiyar yarinyar?
A nutse ya budi bakinsa , a gadarance da izar sarauta ya furta" Ko itace ta tafi aikin Hostess tare da Gimbiya KHADIJA?"
Ba wani irin a sada kan nan Oga ya saki murmushi yana kada kai ya ce" Ita da kanta, ai yarinyar tunda ta dauko kalar fatana na san ba karamar mutun bace"
Salihu ya yi saurin mintsininsa yana hararansa kasa kasa tare da tunanin Anya Oga ba zai saka su samu ladan bulala maimakun karin girma ba kuwa? Waye ya ce masa ana amsawa kai tsaye ba tare da an baka damar amsawar ba?
Kai sarki ya cire daga dubansa ya maida kan wayarsa da ta dauki ringin
Gannin kira ne daga masarautar ya saka shi yi masu alamun kan kowa ya yi shiru baya son hayaniya komai kankantarta
A nutse ya daga kiran ya gabatar da kansa sannan ya yi masu confirmen eh shine ya nemi da a hada shi da sarki kan maganar da ta shafi HANJA
Kamar da minti biyar wayar dakin Pah na ringin kafin ya daga a nutse ya yi salama yana rufe al'kur'anin da yake karantawa
Gaisawa suka yi sosai a mutunce kafin sarki ya ce" Dangane da ziyarar da Mai Girma Hanja ya kawo ne "
Sai kuma ya yi shiru yana tunanin me zai dora a kai
Pah a tausashe ya ce" Akoy wata damuwa ne ko yarinyar ta ki ta aminta da soyayarsa ne?"
Da mamaki Sarki ya ce" Dama ba soyayar suke yi ba?, Eh toh damuwar ba wata mai girma bace gaskiya sai dai ta fuskar da za'a fuskanceta ne, mahaifin yarinyar ne ya zo da maganar cewa yana bukatar a daura auren nan kawai ya juya da matarsa domin shi baya son ......baya son wasu dabi'u na rashin kunya a idannuwansa da suke nunawa su yaren a gabansa"
Da mamaki PAH ya ce" A daura aure kuma?, Wani irin aure ne haka kai tsaye ba shiri ba komai?, To ita yarinyar ta yarda tana sonsa ne zata iya rayuwa da shi ne? Dan a maganata da shi dai yana min korafin a kan me na hada tafiyar da mutanen da take so da kuma saurayinta, bayan na yi haka ne dan na kara isar masa da wani sakon cewa idan ya yi sake , saken zai gani, aman menene abin rashin kunyar da suka yin ne?"
Sai da Sarki ya dan yi gyaran murya kafin ya furta" Ya ce an rungumeta a cen cikin asibiti, sannan yanzun da kanta yarinyar ta fada kirjinsa ta rungume shi a gaban mutanen anguwa, ka san mu a nan bama haka Allah ya ja da kwana"
Murmushi ne ya subucewa Pah, ya ce" Dama sai da na fada masa naku al'adun sun bambanci namu, ya kiyaye, sai dai maganar ta fada jikinsa ta rungume shi shin da gaske ne?"
Sarki ya kallo wajen Oga ya ga shi kawai yake kallo yana murmushi da alama shima ya iya turancin ya ce" Eh haka kam ya fada, kuma haka abokinsa ya fada, yama ce tunda ta zo bata sha ko ruwa ba tana kukan ko yana kula wasu matan? Inaga soyaya suke yi ko nace ta yarda da soyayar tasa ne"
Wani murmushin Pah ya yi sannan ya dan yi shiru yana ta analysng din situation din
A nutse ya ce" Auren my PRINCE na so ace kaf kasashen duniya babu wanda bai halarta ba, na so a daura auren my hero a kasar saudiya, na so ace aurensa yana gefena mun saka fararan jalabiya mun dora hirami mu yo sujadah ana daurawa na bashi kujerarsa na sauka na rungume yar matata mu ci gaba da istgfari da neman gamawa da duniya lafia, Allah ya kara maka lafia Na so ace NANA KHADIJA na gefena ranar daurin auren yaronta dan na ga irin murmushin da zata yi idan ta ji yaronta ya zama mijin wata, watau shima mai gidan wata, zai bata farin cikinta da take ta mararin budar ido ta gani shine jika daga tsatson yaronta....." Shiru ya yi yana lumshe idannuwansa yana adiye damuwarsa hakan ya sa Sarki muryarsa a sanyaye ya ce" Allah ya karawa Gimbiya lafia, ya sa zakar jiki ne"
Pah kasa kasa ya amsa adu'ar kafin ya ja numfashi ya ce" kana gannin idan aka daura auren nan haka kai tsaye ba tare da an mata gayar da ta dace da komai ba an yiwa yarinyar adalci kuwa? Ka san fa mata yadda suke shirya aurensu da komai da komai"
Sarki cike da yarda da maganar da zai fada , dan shima fa gaskiya yana so a yi auren nan, taf a kasarsa Hanja ya fitar da mace? Ai abin murna ne dan haka ya ce" Ka san mu a nan iyaye na iya yankewa y'ayansu hukunci kai tsaye kuma su yi biyaya (uhum anya kuwa sarki ya san su waye Ogas familly?), Idan ya yanke aka yi ba zata taba tada kai ta nuna dan mi ba, gashi ya ce baya so a yi a kofar gidansa dan kar yan anguwa su ringa zaginta cewa yawon banza ta je abokin yin ya biyota ya aureta, ya fi so ya koma masu da maganar ai mijinta ta runguma , ka san lamarin wajen namu kennan, sannan a ganina kaima a yanzun ba zaka so a yi wani hayaniyar da duniya zata dauka duba da mamansa a asibiti, bama zaka samu nutsuwar yin hakan ba, shi din kansa ba zai samu ba"
Pah ya gyada kansa yana fahimtar maganar sarki domin shi yana cakuduwa da sarakan kasashe daban daban yana fahimta cewar kowace kasa da irin nasu al'adun, hakan ya sa sam bai ji wani abu dangane da lamarin da Oga ya gabatar ba, sannan adini bai hanna ba bale ace adini ya hanna a daura aure dan ba'a shirya bidi'a ba, dan haka ya ce" a fara shirin dukan abinda ya dace, a yi jiran saukar jirgin karfe biyar in sha Allah, za'a daura"
Daga haka suka yi salama Pah ya yi shiru ya shiga tunanin wa ya dace ya tura wakiltar daurin auren gudan jinninsa? Waye ya dace ya tura? Kanninsa kuma dan uwansa daya ya rage masa shi kuma ya bayana kansa a matsayin wanda yake adawa da au baki daya saboda kujerar sarautar, idan har ya tura shi lalle ya tura Hanja a bakin kura da kansa kennan?
Mikewa ya yi gannin lokaci na dan tafia dan ya lalubo ya ga wa ya dace ya tura kiran asibiti ya same shi da gagawa
馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ
11/14/21, 12:54 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
6锔忊儯6锔忊儯
Ba EDDITING
Da gagawa ya fito ya shiga mota aka kai shi
A lokacin da ya shiga docter ce ta tarbo shi tana farin ciki ta masa jagora ba tare da ta ce da shi komai ba
A lokacin da suka shiga suka tsaya a gaban gadon Mah tana kwonce ne, sai dai ba irin kwoncin da yake tardota kulun ba
A hankali ya ce" me yake saka ki farin ciki Docter?"
Likitar ta ce" Ta motsa kafarta da hannunta, ta buda idannuwanta harma mun cire mata abin bugun zuciyar "
Da wanin irin farin ciki ya karasa kusa da gadon a hankali ya duka ya dora hannunsa a saman nata ya jimke ba da karfi ba
Muryarsa a sanyaye yake fadin" Ki farka kin ji? Ki farka ki tarbi sarakuwarki da kanki, zan je a daura auren yaronki, ina so idan ya zo da matarsa rungume a jikinsa kema na rungume ki mu kwonta tare mu yi barci cikin nutsuwa, na so ma tura wani daurin aurensa, sai gashi Allah ya nuna min koda bana nan idan Allah ya yi zaki tashi zaki tashin ne, plz ki yi kokari kin ji? Ki kara kokari a kan wanda kike yi, ki tashi na fa hasken farin idannuwanki khalb"
Doctern waje ta fita cike da shaukinsu a zuciyarta, haka kuma zuciyarta cike da farin cikin kotsawar Mah
Pah bai kama hanya ba sai da ya tabatar tsaro ya wadaci wajen Mah haka kuma kula ta wadaceta, sannan ya umarta cewar bayan awa biyu da tafiyarsa a bada sanarwar za'a daura auren HANJA da matarsa Muneerath a africa kasar niger a yau, sannan a yada a social media
Tunda sakon Oga ya samu mama take zaune a tsakar gida bayan dawowarsu daga asibiti ta yi shiru tana kallon ikon Allah da kuma jiran gannin ikon Allah
Kasa kasa ya yi maganar cewa za'a daura auren Muneerath, bai bata damar fahimtarsa ba ya katse kiran, ga kuma Muneerath din da suka dawo daga asibiti da ita a falo a kwonce idannuwanta rufe ba irin yadda Saudat bata yi ba kan ta yi magana ta ki ta yi karshema sai ta shiga alamu na barci take yi bayan idannuwanta biyu,
Haka Hanja har cikin falon ya kaita a hannunsa a rungume ya shinfideta kafin yake tafia gida sarki bisa kira da ya samu wanda ya tafi da gagawa inda ahalin gidan da na anguwar suka samu damar sintiri sunna son gane me ake ciki ne wai?
Iyalan gidan kam sun yi fadan, sun yi masifar, sun yi yafe yaden maganar sun dawo yar zurru sunna kallon kallo kowa da abinda yake cikin cikinsa kuma yake son a bashi amsa aman maman Muneerath ta masu kunnen uwar shegu ta ba mahaukata ajiyarsu, hakama yayanta da ya zo gefe suka koma da mamanta ta masa bayanin abinda yake faruwa ya samu kansa da mata kallon anya kuwa tana da tabacin abinda take fada? Dan haka sai kawai ya garzaya ya nufi gidan sarkin duda ya san abu ne mai wahala a barshi ya shiga
Sai dai tun daga nesa ya ringa fara harda da maganar gannin irin taron al'umar da suka cike wajen , domin Sarki kamar jira yake ya yi gangami na mamaki, ya tara al'uma ta mamaki, ya cika wajen da abin mamaki inda aka baza tsaro aka shiga yanke yanke kamar cen dama an shiryawa wannan daurin aure, jama'a kuwa suka ce gasunnan ta ko'ina ba ji ba gani inda cen ciki kuma Sarki ya gama yiwa HANJA bayanin komai a nutse wanda abin ya nemi buga zuciyarsa dan a ba zata ya zo masa
Du irin kuncin da zuciyarsa ke ciki da ihun da Muneerath ta masa cewar zuwa ya yi ya kasheta? Zuwa ya yi ya yi wasa da zuciyarta? Me ta masa? Me ta tsare masa? Zuwa ya yi ya wulakantata dan ya ga ita ba kowa bace? Zuwa ya yi itama ya ga karshen tata rayuwar shine ya bilo mata da maganar soyaya? Ya daina taba ta, ya taimaketa ya daina kallonta, bata tunanin zata iya yarda cewar wai shi HANJA dan wane jikan wane zai diro kasarta da yake kyankyami, da ita kanta da yake yiwa kallon mahaukaciya ya ce wai yana sonta, du yan matan nan na kasarsu? Du yan matan nan na duniya? Babu inda zai saka kafa ya nemi mace a hanna masa , shine zai so har Oga?, Shin bai san Iman na sonsa bane? Dalilin son da fake masa ta tsaneta kamar ta kasheta har take fada mata yana taraya da wasu mata? Yanzu shi da baya jin tsoron Allah yake so su jona da ita ko me? Dan Allah ya rufa mata asiri ya barta ta iya da rayuwarta , kar ya hargitsa mata tunani, walahi ya fi karfinta..........
Sosai magangannunta suka rikita shi, har ya ji mamakin wai shi HANJA iman ke so? Lalle ya wulakanta kansa har ta kai yadda Iman ke tunanin ta kai macen da zai iya raba lokacinsa da ita? Lalle zina zubar da mutunci ce, yanzu yarinyar da yake yiwa kallon kanwa dan ta san ya kasance mai raba abin cikin wandonsa har ta kwadaitawa ranta? Shi ya tabata yarinyar nan karyata ne zai yi biyu ya zubawa tgr ta cinye kashin dake tare da fatarta sakamakon fadawa Muneerath sirinsa da ta yi kai tsaye
Ko daukotan nan da ya yi da farko wutsil wutsil ta fara kan ya sauke , da ya rungumeta kam a kunnenta ya rada mata cewa idan bata nutsu ba yana iya ladaftar da ita walahi
Shine fa ta yi luf a kirjinsa dan tana tsoron ya kuma furta mata kalmar so ya kara summar da ita, ita kam ta shiga uku ta lalace ta ga rayuwa gannin idannuwanta
Matsanancin farin ciki, da matsananciyar damuwa ne suka dirar masa harma ya kasa daukan tufafin da aka gabatar masa da rawani da sarkin sawanin da zai nada masa duda irin zumudin da yake kan ta ganshi da rawani yaya zasu kwashe? Tsoron rashin amsarta wa soyayarsa ya saka shi a gaba ainun harma ya fi damuwa da hakan fiye da komai
Shi dai ya san daurin auren nan daga Allah ne, damuwarsa yaya zai iya da rigimarta ne? Aman idan ya tuna ana daura aure ta zama tashi fa, shikenan bashi da wata damuwa ta kar a kwace masa ita, sai ya samu kwarin gwuiwa, a haka har Pah ya samu karasowa tare da dakarunsa shima inda duniya ta dauka ana ta neman hanyar da za'a yi magana da su abin ya gagara domin ba halin daga waya
Irin gaisuwar da suka saba suka yi da junna, a hankali Pah ya dan bubuga bayansa ya furta" Wani irin farin ciki kake ciki?"
Iskar bakinsa ya furzar ya furta" Da na fada mata ina sonta summa ta yi"..
Ido Pah ya zarro yana kallonsa , sai kuma ya yi dan murmushi a nutse ya ce" A haka za'a daura aurenka da shigar da ka zo da ita?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Baka fahimta bane? Inaga fa bata so na"
Pah ya yi dan murmushi ya ce" To sai ka koya mata sonka, ka san dai ba zan taso na baro matata kwonce na zo dan halartar wannan daurin auren ba kuma na koma ba'a daura ba dan kawai yarona ya kasa tankwasa zuciyar matarsa?, Fushi take da kai dan kana kula wasu matan , tuni a nan kana da maki mai girman gaske, kaine zaka tankwasata ta gane cewar sai da kai fa zata kai labari..........."
Kwarin gwuiwa ne ya same shi da nutsuwar zuciya, hakan ya sa ya sauke ajiyar zuciya ya bi bayan mahaifinsa yana karra wayar kansa da al'adun namu kasar, watau kasata mai albarka
Gari da yar ciki ce farare kal, basu sha wani muhun aiki ba so simple sai dai mai tsari
Bayan ya saka an gyara masa hannayen aka zo aka nada masa nadin Rawanin da aka bata lokaci ana yi har sai da ya gama gajiya da tsayar da kai waje daya inda Pah ke gefensa cike da kauna da shauki hakama mutanen da suke da damar hakan sunna gefensu, Attahir na daukan vidion dukan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 38 Chapter of 42