Share this page
maye Likitar ce ta gama daukan jinnin da yannayin bp dinta ta mikawa wace ke tafia dakin gwaje gwajen da shi sannan ta koma ta zauna ta shiga yi mata tambayoyin kamar haka Yaya sunnanki ke haifafiyar ina ce? Shekarunki nawa? Muneerath ta gyara zamanta a hankali ta ce" sunna na Muneerath M , ni haifafiyar kasar Nijer ce, shekaruna ashirin yanzun " Da mamaki ta kalli HANJA da yake kallon Muneerath dan shima maganar shekarunta yanzun ya ji, sai dai ba damar ta masa tambayar yaya aka yi ya ce yar mamansa ce da kuma karancin shekarunta, Sai kawai ta yi shiru ta ci gaba da tambayoyin kamar haka" Muneerath ke musulma ce ko christa?, Kina da aure ko baki da? " Muneerath ta bada amsar ita musulma ce, sannan bata da aure zuciyar fal tunanin ya aka yi sauran ba'a masu irin tambayar nan ba, bata san cewa dole bakuwa take sai an bi hawa hawa kafin a bata damar shiga Likitar ta ce" kin taba haihuwa ne ko kim taba samun ciki baki haife shi ba? Idan kin taba sau nawa? Da rai ko babu? " Da mamaki Muneerath ta waiga wajen Sir sai ta ga yana tsayen dai aman kasa yake kallo dan haka ta maido dubanta ta ce" Cewa fa na yi ban taba aure ba" HANJA dake dan kada kafarsa ya wurga mata wata irin harara dake nuni da ki bada amsar da aka tambaye ki a kai Sir ya matso da sauri domin dama yana wajen ne dan shine responsable din Hostesss ya kalli Muneerath ya ce" Amsa zaki bada daidai da tambayar da ta maki " Muneerath ta lumshe idannuwanta a hankali ta cike lalausan fizgegen pink lebenta da tsararun hakoranta na kasa sannan ta bude ta dora dubanta tar a kansu ta ce" Ban taba haihuwa ba, ban taba zubar da ciki ba, cikinma ban taba samu ba" Sukan amsoshinta tana rubutawa ne har ta gama ta dora da fadin" Saurayi nawa kika taba yi, da nawa kika kwonta ?" Tambayoyi ne da ake yiwa kowace bakuwar Hostess kafin ta fara aiki, tambayoyi ne da ba'a dauke au a bakin komai ba domin ana so aikin da za'a fara da kai a san waye kai a bayane a kuma gamsu da bayananka , sai dai gaba daya wadinnan tambayoyi suka zubawa Muneerath matsanciyar kunya da jin haushin masu yi mata itan , ita kuwa likitar tana cikin mamakin amsoshin Muneerath inda Hanja kwata kwata baya yarda da amsar shi bai wani yarda ba yan matan nan na yanzu ai sai su Muneerath a sanyaye ta ce" Bani da saurayi " A kufule HANJA ya daka tsawar da ta saka Muneerath rintse idannuwanta ya ce" Amsar tambayar da aka maki ake so ki bada ba raina mana hankali ba , a nan babu wanda ya damu da ke bale ki yi kokarin birge shi!" A rikice ta dago ta zubawa fuskarsa ido kafin ta bude bakinta lebenta na rawa ta ce" Na ce bani da shi, ban taba yi ba ban sanshi na, ni ba yar iska bace ta yaya kuke so na ce maku ni yar iska ce, bai ce yana so na din ba tukunnan sai na koma ko!".....sai kawai ta fashe da kuka tun karfinta ta kifa kanta saman table din gaba daya jikinta na rawa dan ita bata ga a wani dalili za'a ringa mata wannan wulakancin ba, a karuwa suke daukanta hala ko me? Hanja , chok, Hanja bakon lamari, HANJA madaukakin rainin hankalin yarinyar ya saka shi ruko ido da sauri ya kai hannunsa wajen bakinsa da mamakin da ya saka shi bude baki na irin ihun da ta yi a lokacin da shi Prince HANJA kuma shugabanta a wajen aikinta ya yi magana ta masa ihu da magangannun da ihunta suka dauka da kuma kukan da ta fashe da shi ta kifa kanta a yau ranarta ta farko a wannan waje ya saka shi jin wata juwa na son kwada shi da kasa.....ya Rab MAH da wa kika hada ni kuma? Likitar da ta ruruko ido itama ta mike tsaye tana kallon ikon Allah da sabon al'amarin yarinyar da kukan duka ta gama sakawa ranta shikenan yarinyar nan zata ja a koreta ko aikin bata fara bane ta kalli Hanja dan so take ta dan bashi hakuri kar ya yi gagawar furta kora a bakinsa dan ba zai dawo baya ba ta ji muryarsa a dan sanyaye na irin takaici ya kume kan nan ya ce" . . . ................ Alhmd 11/14/21, 12:49 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 3锔忊儯1锔忊儯 Ya ce" ta tashi ta tafi" Da sauri likitar ta ce" ur excellency ka yi hakuri kar k koreta da alama bata san kan aikin bane gata bakuwa sannan ba haifafiyar nan ba" HANJA da kukan ke neman hadasa masa juwa ya ce" Cewa na yi zan koreta? Ta je ta hadu da sauran a shirya su mu tafi" Wannan karron ba likitar ba, Sir kansa a mamakance ya kallo shi sai dai irin yadda ya hade rai ya juya yana mai dafe gaban goshinsa ya saka cikin gagawa likitar ta mikar da ita tana kukanta tana bata hakuri suka yi gaba da Sir suka nufi wajen da sauran suke A nutse likitar ta tsaya kusa da shi kadan ta ce" Sir " Kansa dake sade ya dago ya juyo yana fuskantarta bai amsata ba Abin aune aunen ta nuna masa a ladabce ta ce" zuwanka ne " Hanja da kansa ya dau ciwo na ihun kukan ya cije hakoransa ya zagaya ya je saman doguwar kujerar ya zauna yana mai tube rigar jikinsa ya ajiye hannayensa ya lumshe idannuwansa ana sauraronta ta shiga auna shi cikin nutsuwa da kayan aikinta tana rubutawa ta dago tana kallon wajen fuskarsa ta ce" Lafiar jikinka ingantaciya ce, abinda na ga yana kokarin damunka biyu ne, kanka da ya dauki ciwo sai kuma yannayin bukatuwarka wanda su dukansu yanzun za'a magance su" Idannuwansa dai a lumshe suke har ta dawo da magani cikin kofi ta zauna saman kujerar ta bashi ya amsa ya sha ya kuma lumshe idannuwansa na kusan minti goma bata yi magana ba sai dai tana rike da tap a hannunta mai kirar aple tana jiran ya motsa A hankali ta ce" Sir ciwon kan ya sauka? " HANJA da ransa ke bace yana ta tunanin ta inda zai samu mafitar da zai yakice yarinyar nan daga cikin ahalinsa ya dan motsa mata kansa bai amsata ba Ajiyar zuciya ta sauke cike da tunanin to wai ko dai da gaske yar maman nasa ce? To a afrika ta samu cikinta ko menene? Ita ta kasa gane yaya aka yi haka, sai dai ta yarda koma me dinsa ce tana da kusanci da shi mai karfi wanda ya zarce na maganar soyaya, hakan ya sa bata yi gigin yi masa wata tambaya a kan Muneerath ba Screen din tap din ta juyo masa bayan ta tsaya, Hotunna ne na wasu tsala tsalan yan mata na grup VIP na kasar baki daya wanda kampaninsu ya samu shiga dan samawa zaratan mazan abin bukatarsu a ringa cirewa a cikinsalarry dinsu wanda a haka kampanin ke kara wawusarsu.....hakan kuma nrmal ne nema ne A hankali take dan matsar da hoton ta sako wani, daga ringeshen da yake yanna kallo tarrr a idannuwansa ana ta wuce su yan mata ne masu fata mai sheki da tsayayu mama da dan kugu sunna cikin shiga ta tairaici sun yi kwonci irin na yan duniya ko a tsaye an wani wara kafa, ko a zaune an saka pom a baki an datsa masa hakori.....yannayiyika dai na talar abin cikin pant har sai da ya gaji da bi da kallo kafin ya maida kansa ya lumshe idannuwansa A ladabcenta ta ce" yannayinka na nuni da nan da dan lokaci mararka zata kule, lokacin bai fi yan mintunna ba sir ka fini sannin yaya ciwon mararka yake gashi zaka yi tukin awa hudu, idan kuwa ka fi so na je da gagawa na kawo maka wace ta yi sai na je yanzu yanzu na kawo " A gaskiya shi da kansa ya san a bukacen yake, sai dai wani lamarin wannan bacin rai da aka hadasa masa na yanzu ya kular da shi sosai, walahi da ace wannan yarinyar bata da daurin gindin gidansu da sai ya wanka mata mari kafin ya koreta, wannan yarinyar nan da wata uku ta saka shi hawan jinni fiye da nrml bp dinsa shi ya sani, dan dai mai hakuri ne shi ya sa yake sauka da wuri, haka kawai katuwar YA ki saka mu a gaba ki rushe mana da kuka? A kanta aka fara tambayoyin nan ko a tunaninta ita ta daban ce da za'a tsara nata? Ko tunani take sai an bi ta nan za'a iya korarta?, Dan bakin raini ta furta masu bata taba yin saurayi ba dan kawai ta basu aikin bincike na banza da wofi! Kai ba za'a yi binciken a kan nata ba dan shi yana ji a jikinsa verry soon zai tatara ya nata ya nata ya kara mata gudu, ina dalili tun bai fara haihuwar ba wata gandareriyar bak'ar y'a zata zo ta dame shi! Mikewa ya yi zaune ya shiga maida kayansa bai bata amsa ba har sai da ya gama sannan ya ce" No barshi, bana cikin mood din hakan zan sha magani ai tafiar ta yau ce kadai in sha Allah " Yana maganar ne yana tafia ya fice a office din gaba daya Ajiyar zuciya ta sauke, bata dan me zai saka ya ce bashi da ra'ayin hakan ba bayan ga yadda jikinsa ya nuna, kai su fa basa son abinda zai taba shi dan shi din adali ne a gare su, mutun ne mai kyautata masu hakan ya sa suke maraba da dukan ranar da zai shigo wajen su, irin yadda ya tsaya tsayin daka kan ma'aikatansu kuwa ya sa suke aiki da kuzarinsu domin da ace Sir HANJA ya kasance mai yin yan mata a wajen aikin nan da sun shiga uku, sai Allah ya taimake su ba ruwansa da y'a a wajen aikinsa ko yar waye, ko wata irin halita gareta, kai ko a wajen sai dai ya sayi wace ta baza hakan ya sa a irin halayan mutan garin ake respcting dinsa sosai Sir ne ya fito yana tambayar idan result dinsu sun fito Nan ta mike suka tafi dakin amsar result din suka amso suka dawo suka zauna sunna wawarewa Likitar ce ta kale shi ta ce" Ita ba'ai mata na gwajin cikin ba kar kuma ya kama ni da laifin hakan" Murmushi ya yi ya ce" a barta haka, za'ai mata zuwa gaba idan ta gama fahimtar a kan aikin ne ake mata tambayoyin ba dan ta yi wani laifi ba ko dan ana zarginta ba, kin san bata taba fuskantar haka ba shi yada ta ji tsoro" Kai ta gyada ta harhada mada komai ya juya ya tafi dan ya kai a dora a kan takardar kowace ya amso baje dinsu kafin su fito daga wajen likitar Tunda ta shigo wajen ta daina kukan tun karfi aman kuma hawayenta na dan zuba haka kuma tana ta sauke ajiyar zuciya Yan matan dake dan kara shishiryawa ne suka nufota, dama tunda ta fashe da kuka suke jiran gannin shigowa zata yi ko ita takardunta sun samu cika Wace ta fi rama a cikinsu ce tana kallonta ta ce" Korarki ya yi? " Muneerath dake kallonsu daya bayan daya ta girgiza mata kai Da mamaki dayar ta ce" ko dai kallonsa kike ta yi har ya kama ki da hakan? " Itama da mamakin ta kuma girgiza masu kai Sai suka samu kansu da kallon junnansu kafin daya ta ce" to kukan me kike? " Muneerath ta ja hanci ta ce" Gani na yi ana ta min tambayoyi kamar wata karuwa, dan Allah ina gamina da haihuwa ko ciki a yanzun ni da ko rana ba'a saka min ba kai ko saurayin bani fa shi ba'ai min auren ba za'ana cewa wai wani na tara da namiji to na cewa namiji me ya ce min me? Dama sai da Mah ta ce akoy yan iska a wajen nan na bi a hankali" A gaskiya, kwata kwata basu gane wai tana kuka dan an tambayeta idan ta tara da namiji ne bayan bata da aure, kai su sai suke son gane kawai haihuwar ce bata so dan an hadata da haihuwa take kuka, hakan ya sa suka nemi kwatanta mata cewar ba wani abu bane wannan ai Wace du ta girme su ce ta ce" Mun zata korarki ya yi kike wannan kukan, ki tashi ki share hawayenki mu idada kimtsawa mu tafi, kin san sai mun yi binciken kayan mutane bayan sun zauna dan an fara shiga da miyagun kwayoyi malesia yanzun ana cikin yin taka tsantsan ne Ita dai nan ta ringa binsu har ya dawo ya masu ja gaba baki dayansu suka tafi dakin da zasu layu ya kuma masu wani gargadin Kamar yadda Sir ya saba haka ya fada masu dukan abubuwan da ya dace su kula, su kiyaye, su yi taka tsantsan a tafia da PRINCE idan har sunna son aikinsu Sai da ya rage yan mintunna kafin ya shigo, ya cenza kayan jikinsa yanzun suturarsu ce ra matuka jirgi a jikinsa HANJA yana da sirrin kyau da kyan kallo, sai dai idan ka yarda ka kure mada kallon kana iya janyowa kanka abinda ba shikenan ba, hakan ya sa sauran yan matan da suka kwana da sannin tafiar da waye suka dukar da dubansu , banda Muneerath dake kallonsa tana hankalce da takun tafiyarsa dan bata so kwata kwata ya nufo wajenta dan a shirye take ta dankara da gudu idan ya nufota wollah, a cen kasan zuciyarta kuwa tana tana mamakin wai yanzu ace wannan mai jiran gado ne ba rawani, hm wani abin sai sarakan ingila Kamar yadda ya saba haka ya tsaya a gabansu ya gindaya masu cewar Aiki suka zo yi su nutsu su yi aikinsu idan ya kama su da wani laifin ba zai iya kyale su ba, sannan ya fara yin gaba, sir ya bi bayansa sannan suma suka bi bayansu A yaune zata yi shiga ta biyu,a yau ne take cikin hankalinta hakan ya sa tunda suka tunkaro shi ta daga kanta tana kare masa kallo Girmansa, girman tayoyinsa, girman fukafukansa biyu, gaban goshinsa da ya yi tsini, tsakiyarsa da kuma bayansa, matatakalar dake bude da sojoji da ma'aikatan dake kusa da shi gaba daya sai ta samu kanta da jinta tamkar a wata duniya daban, Wata irin connexion take ji da zuciyarta da tafkeken jirgin A hankali wani irin shauki da soyayar Jirgin ke ratsa gaban jikinta Tana taka matatakala tana hawa ne zuciyarta na kwadaita mata son gannin yaya cikin yake har kasan zuciyarta A lokacin da ta tsinci kanta a ciki bayan sir ya rabawa kowa irin aikin da yake so ya gabatar ya nemi fa ta biyo shi ita da take bakuwa ya shiga cen ainahin wajen da pasinger zasu zauna sunna tafe yana mata bayanin komai har sai da suka raba tafiar suka isa tsakiya sosai sannan ya juyo yana fuskantarta Murmushi ya dakar mata mai daraja kafin ya ce" kin daina kukan?" Muneerath ta daka fuska ita a dole haushinsa take ji domin yana kallo aka ringa wala gigi da ita ana mata tambayoyin mararsa da'a bai tsawatar ba, bama wannan ba tunda ta sanar masa tana Palas rabonsu da su yi wani zance sai fai su gaisa sama sama ya shaida mata a Palas komai na fara bi ta wajen dakin computern da ake binciken mesg ko call din du wanda ke cikin gidan more spcialy na kusa da sarkin, hakan ya sa ya daina dogon surutu da ita dan kar magana ta kai kunnen Hanja ya ce meye tsakaninsa da dalibarsa? A sanyaye ya ce" Fushi kike da ni? " Muneerath ta kawar da kanta gefe bata bashi amsa ba hakan ya sa ya ce" Yanzu kin iya girki? " . Muneerath ta juyo da dan sauri tana murmushi kafin ta gyada kanta ta ce" Yanzun ni nake dafawa Mah shayinta ta sha ta more" Murmushi ya mata yana gannin bai taba gannin mutun mai chance irin nata ba, kwarai yarinyar da Allah dogara Allahn kuwa sai yake dafa mata a dukkan lamuranta A nutse ya ce" Mutun ne da ya dauki aikinsa da daraja, yana daya daga cikin wa'inda suka malaki jirgin kansu a kasar nan da basu fi su uku ba, yana da arziki mai yawa, ya fara tuka jirgin fa ya kera da hannunsa na wasa kamar da wasa, a harkar da ta shafi jirgi harta yadda za'a ba pasinger kulawa ya karanta, son abin yake a zuciyarsa ba wai haye ne ya yi dan ya yi arziki ba, aikin nan ba aikinsa bane ya saka kansa ne dan yana so, ina girmama mutumen nan domin idan kika ga ya yi fada da dalili , kar ki dauki tambayoyin cen da wata manufa dukkan bakuwa haka ake yi mata wannan din ba wani abu bane dan a san irin aikin da ya dace da mace ne, domin idan kina da yaro a san irin doguwar tafiyar da ta dace da ke, idan kina da aure haka, idan da saurayinki kike rayuwa haka, Muneerath daga bakin wannan lokacin kin zama karkashin kulawar kampanin nan, idan baki da lafia sune, idan wani abu kike so sune, cin ki, shan ki, suturunki, bukatunki, wajen kwonciyarki baki daya a wuyan kampanin nan ne, basu maki dan wata manufa ba......ana yin tambayiyin nan ne dan a tantance waye kai da irin aikin da ya dace da kai kin fahimta?" Sai a wannan lokacin Muneerath ta samu wani nutsuwa a zuciyarta, sai a yanzu ta ji hankalinta ya kwonta harma ta ji kunya na son lulube mata zuciyarta domin sai a yanzu ta ga rashin dacewar kukanta hakan ya sa ta rufe fuska tana murmushi ta ce" Tambayoyin ne sukai min kama da wada ake tuhuma da aikata hakan" Murmushi sir ya yi yana girgiza kansa ya ce" ba maganar tuhuma, bama wannan ba har yanzu dogarin ake jira?" Muneerath ta ji batu an tabo mata zushiya sai ta murmusa ta langwabar da kai ta ce" Uhum, ka ga dai sai tsofewa nake bai motsa ba, aman na san da na koma niger zai yi bayani ne na tabata sai ya rikice a yanzun dan na iya saka kwali..." Ta fada tana murmushin tuna aminiyarta amina dake fadan ko kwali bata iya sakawa ba wani namiji take so yace yana sonta wadinnan mazan na yanzu da kyalekyali ke wartarsu A kadan zuciyarsa yake ayana' inama za'a bani ke, da na dauke ki mun ringa yawon kasashe, ni kam bana sonki da kwalin a haka kin fi min kyau, aman na san zaki amsani idan na fada wata rana' Kawar da tunanin nan ya yi gannin lokaci ya yi yanzu an fara kiran mutane su shigo ya ringa nununa mata wajen da mutane ke iya boye miyagun kwayoyi suka zarce har bayi ya nuna mata da irin mu'amalar da ta dace tsakaninta da pasinger kafin su koma su yi jiran jirgi ya gama cika , aka bata abin aunawarta tana tsaye abinta zuciyarta fesss da farin cikin wannan rana ___________________&________________ Kafin ka yi tafia ne kake da ita, idan ka yita ita take da kai, a wannan tafiar tasu sun sauka lafia a kasar malesia inda suka yi hotel din dake jikin a茅roport din dan samun hutu na dan lokaci kafin su daga zuwa gida, sai dai basu kai ga hutawar ba aka shaida masu tafiarsu zata dauki hanyar HAWA脧 Sakalau ta yi tana kallon yadda suke murnar zasu sauka a Hawa茂, ita dai bata san ina ne haka ba, abinda ya fi birgeta shine rabata da kwonciyar nan da aka yi, domin ita fa bata gaji da aikin ba, abin kasheta yake gata itane take wannan aiki, kai yaya Oga zai ji idan ya ganta a haka? Mamansu fa da tace bata da hankali idan ta ga yau gata tana wannan aiki? A yanzunma shine ya tuka su, ba su su sauka a kasar ba sai da sanyin safia gashi su basu rintsa ba Hakan ya sa sunna sauka wajen kwonciya aka fara gabatar masu domin basa tare da yinwa Dakuna ne a laye, daga su har ogan nasu du aka umarci yan matan da su shiga su huta Da ido ta raka bayansa da kallo a lokacin da yake tsaye a kan dokin kofar dakinsa da waya a hannunsa dayan hannun nasa kuwa yana dafe da cikinsa wanda ita bata gane cewar mararsa yake rike da ita ba, ga kansa tamkar zai tsage biyu A hankaki ta fara nufar infa yake tsaye, so take ta ari wayarsa ta yi kiran Mah ta shaida mata ga inda suke domin ta fada mata da ta samu sarari ta ringa sanar mata inda suke domin ta bata katin numberta ta gida wace ake samunta direct A hankali ta tsaya dan nesa da shi kadan ta budi bakinta a sanyaye zuciyarta na dokawa da tsoron kar a je ya mata wani ihun ta ce 11/14/21, 12:50 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 3锔忊儯2锔忊儯 "Assalamu alaika " ta fada a sanyaye sannnan a irin ciki ciki dinnan Sai da ya yi tsam dan tabatar da a bayansa ne aka yi salamar kafin ya juyo a hankali yana mai cire hannunsa daga wajen da ya dora Watau saman mararsa Yana juyowar idannuwansa suka sauka a kan pankamemen kugunta, da sauri ya yi sama da dubansa ya kai saman fuskarta,, mamaki ne ya kama shi lokacin yaga itace tdaye firit a gabansa, a cikin zuciyar sa ya amsa sallamar tata kallonta yake yana jiran yaji dame kuma tazo shifa ya fara tunanin ko gamo yayi agarin kwashe kwashen shi na mata Bai dawo daga duniyar tunanin ba ya tsinkayi muryarta mai sanyi da dadin sauraro tana cewa" Dan waya nakeson ka aramin zan kira mah " Mamaki ne ya kara kashe shi wai shi take cewa ya bata wayan shi? ikon Allah, ikon Allah, shin wai ba ita ce ya damki wuyanta ba? Ba itace ta masa fitsari a mota ba? Ko ba ita bace yanzun ta gama sheka kuka? hannunshi ya kalla wanda wayar tasa ke ciki kafin ya kalle ta, kai shikam wllh badan m Mah ba da ya batar da yarinyar nan a garin kawai kowa ma ya huta Tsintar kansa ya yi da mika mata wayar batare da yace mata komai ba yana kallon ikon Allah, hakama Sir da ya taho da servic din da suke kawo pizza da samari uku a bayansa ririke da katan katan din pizzar ya samu kansa da rage saurin da yake ya zubawa bayanta ido da kuma tsayin HANJA da ya kereta yana jingine da jikin garu gashin kansa ya yo gaba ya kurawa Muneerath din ido hannunsa kuwa ya miko mata abinda shi dai bai san ko menene ba, haka kawai ya tsinci kansa da faduwar gaba har ya ji kamar ya kasa idasawa kofar dakunnan nasu Ita ko muneerath kanta tsaye ta karbi wayar ta juya cikin takunta mai birgewa wanda idan mutum bai santa ba zai yi tunanin cewar da gangan take karkada bombom dinta , ita kuwa baiwar Allah abin ne ya mata pantsam a bayanta kuma ba hadaden nan bane yana juyinsa ne da an bashi damar hakan watau

Chapter 17 of 42