ana anfani harda bak'ar fatar da kuma yannayin tsarin halitar mutun da irin yaren da ya iya da iliminsa , sai dai halitar MUNEERATH halita ce da bawa ba zai fahinta ba sai a nan gaba, da ace ita din ta san me Allah ya tara mata a wajen duwawunta da ta ja wa'inda ke yawo da zariyar wando a hannu a kasa ba da komai ba sai da kada luntsuma luntsuman duwawunta da gaya, sai dai rashin sannin ya saka take rayuwarta a yadda ta zo mata
Kansa ya kada ya barta a nan tsaye ba tare da ya bata amsar burinta ba, haka kuma bai karfafa mata gwuiwa ba, sai kishiyar mahaifiyarta da ta gyada kai ta shige dakinta take sanarwa da d'anta cewa lale a yau ta kara yarda cewa MUNEERATH bata da hankali, domin kuwa a yanzu bayan mafarkin dogarin da take ta dawo burinta na kasancewa Hottest, in ba jaraba irin na yarinyar nan ba ina ta ga yannayi na Hottest? "
A haka ta ci gaba da tafiar da tata kalar rayuwar, karatu take ba ji ba gani, abin birgewar sai ka ji tana karatun alkur'ani, tamkar ba yar cikin wannan gida mai wuyar rayuwa ba
Da farko MUNEERATH bata kula samari, bata kula da ko dan gidan waye, daidaikun samarin da a yanzu suka ja suka tsaya suka rike nasu ra'ayin na ba zasu taba kula matan zamani da koda da farinmu muke kara bealiting ba bale bakak'en da muke zama farare dare daya dan lalacewar abokanan rayuwar da suka nuna su sai hasken gida, sai alkyabar mata ba, suka jajirce suka nuna mata kauna, da wa'inda suka gane wannan yarinya mota ce da za'a jima ana tukawa nan gaba, irin manyan motocin zamani masu tafe da bed, watau hutu ce, dunia ce guda suka lalabo dan gwada tasu sa'ar ko za'a dace sai dai ina haka ta ringa tizgawa duda rashin kwaliyarta, haka ta ringa nuna cewar lalala bata yi komai kyankya da kudinka! , sai da ta zauna ta yiwa kanta karatun ta nutsu a kan halayar mahaifiyarta da ta kula cewar eh lale uwarta ce ita ta kawota dunia, aman idan so take mu'amalarsu ta dore ya kasance tana da saurayi mai dan yi mata ihsani , hakan zai saka itama ta samu yanci da soyayar uwa irin na kowa, ba wai dan mamansu bata samu bane, aa, tana samu na mamaki a wajen abansu da yayansu, aman cewa take yaro tun yana yaro ya san ciwonta ya yi mata idan ta mutu ba shikenan ba? Ta more tun harshenta na gane dandanon magi da siga, a haka ta dage, ta mike tsaye, take kula samari daidaiku daga nesa kafin Dogari yake kawo kansa inda take, dan kuwa a soyayarta da dogari Allah kadai take fadawa , ba zata taba iya tarbar namiji ta ce da shi tana sonsa ba, ba wai dan ta san irin ilar da hakan zai iya haifar mata ba, aa, sai dan kawai ita bata ga anfanin aikata hakan ba!
A yanzu shekarun MUNEERATH goma sha takwas ta kawo matakin zana jarabawar dake iya bata damar ahiga University a maysayinta na wace ta bada hankalinta kai da fata take karatunta ya kasance a jarabawar uku sa ake yo har zuwa yanzu bata fadi a ko daya ba, haka kuma a ci gaba daga karamin aji zuwa na gaba da shi ba'a taba mayar da ita baya ba
BAC shine jarabawar da ta damka, wace ta zama mai wuyar samu, a yanzu da shugaban kasarmu ya tsaya tsayin daka ya rufe ido kan irin yadda wasu malaman makarantar da iyayen da son y'ayansu suka rufe masu ido suke mika dan abin ihsani ana tsalakar da y'ayansi, da samarin dake yiwa yan matansu, da mazan dake tsalake matayensu, da dangi, da sannin sanni du ya ture ya ja ya tsaya a kan kafafuwansa ya kafa matalan tsaro ta yadda iliminki zai kwato maka, sai ta kara daura damarar karatu ba dare ba rana, idan suka je aji suka dauko karatun da malamai ke masu duda yawanci a irin shekarun nata yan mata kai na hayaki, ido na tsaitsaye, abinda suka fi hangowa shine show......a je makarantar a ki yin karatun a hade da yan mata a restaurant a ci abinci a bige da selfi, a saka kida a sha casu, a ringa kule kulen samari ana abubuwa sai an zo shiga a haukace ana kame kame.....sam sam Muneerath bata kasance a cikin irin yan matan nan ba, wannan abin ya saka take da masu son kulata sosai, ko dan mutun ya karu da baiwar ilimin da Allah ya yi mata, ita din ba za'a kireta da mafadaciya ba domin bata fadan da ba dalili, idan ka ga fadanta tabata an tabata ne, wannan kuma takan ce a gaskiya ba zata iya kawar da kai a mayar da ita sakarai ba
..................back
Yinwar da take ji tun ta rana da ta riko daga makaranta ita ta ci gaba da rikewa har dare ya yi kafin ta cenza tufafin jikinta ta shanya wa'inda ta cire din bayan ta wanke su a bayin tsakiyar gidan ta zo ta dauki litafinta ta zauna ta dukufa ta shiga karatu tana jin juwa na son kadata a zaunen da take
Yayanta ne daya daga cikin yayunta mudaseer ya shigo har dakinta
Ido hudu suka yi kafin ya zauna saman yar kujerar dakin nata yana bin dakin da kallo ya ce"
*Sajida ce*
11/14/21, 12:43 PM - Allah Akbar: 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
*膼 挪 泞 搂 茝*
3锔忊儯
Ido hud'u suka yi kafin ya samu waje ya zauna saman kujerar d'akin nata yana bin d'akin da kallo kafin ya sauke idonsa a saman kanta ya ce "Kin tabata cewar ba shashancin mafarka mafarkan dogarin bane kila yi ya saka ki zama hottest? Kin kuwa san menene hatsarin aikin hottest? Kin yarda zaki iya d'aukan risk d'in kasaccewa Hottest?"
Littafin dake hannunta ta ajiye da sauri tana kallonsa a sanyaye ta buda bakinta mai dauke da fararan hakora tas tas da yar siririyar wushiryarta tana kallonsa ta ce" Aa, walahi ba dogari ya sakani ba, hasalima bana tunanin idan har dogari zai hanna ni wannan aiki domin aikin da nake mafarki ne, shi kuwa ai masoyina ne kau?"
Dan k'aramin tsaki ya ja yana karkacewa ya zaro wata takarda a aljihun wandonsa ya ajiye mata a nan kusan litafinta ya mike ya kama hanyar fita yana fadin" Ni na koma makarantata wannan jaraba ta Dogari Allah dai ya sa ba mahaukaciya bace ke ake zaune da ke kalau ana tunanin mai hankali ce!"
Yana fad'a har ya fice, ita dai da sauri ta saka hannunta ta d'auki takardun ta bude ta maida hankalinta ta zuba idannuwanta tana karantawa cikin nutsuwa, suna d'asawa da wannan yayan nata sama sama ba dan komai ba sai dan irin yadda take kaunar karatu, shi din kuwa a rayuwarsa mutun ne mai shegen son karatu hakan ya sa yake dan sauraronta shima ba wai cen cen din nan ba aa, yakan tsayawa ya ce anya ba ta yi gamo ba kuwa? Wani sa'in maganama yake daina yi mata kwata kwata aman da zarar ta kawo sakamakon makaranta sai su shirya, har taimaka mata yake da litatafai da sauransu, ko yanzun ta jima ta yi masa tambayar ta yaya zata iya samun damar kasancewa Hottest? Shine yau ya kawo mata information din da ta ji kamar gaba daya dukan mafarkanta ne zasu tsaya a iya wajen nan.
Na farko dai idan kana son kasancewa Hottest ba kai tsaye bane zaka zo da dukkan yannayin jikinka ka ce ka zo neman aikin.
Ya zama wajibi jikinka kar ya zama katon jiki kar kuma ya zama busashen jikin da ba za'a anfani komai da shi ba, kai dai kar ka wuce kl sittin da biyar haka kuma kar ka yi kasa da arba'in da biyar.
Na biyu kalar fatarka, basa daukan fatar da bata zamo daya baki dayanta ba, ina nufin idan baki ne kai ya kasamce bak'in nan naka mai kyau ne ta yadda baki daya jikinka bak'in ne kar ya zamo wani wajen fari wani wajen bak'i hakama idan fara ce ya zamo duka fari ne babu digo digon baki ko ja, ko ylw d'in fata.
Baban tashin hankalin shine bayan mutun ya yi Bachelor's degree ya samu, ya zama wajibi ya je ya yi shekara biyu na wani karatun domin ana son mai Bachelor's degree +2
Dole mutun sai ya iya yaren inglish ba lale a rubutu ba aman ya iya a harshensa idan da hali da wani yaren ko wasu yarukan.
Ya zama dole mutun ya iya Ruwa watau ace ya iya iyo.
Ya zama wajibi ka samu CCA watau CABINE CREW ATTESTATION.
Idan da san samu ne ka samu experience a harkar kasuwanci, watau kana iya karantar harkar Marketing 馃し馃徎鈥嶁檧锔
A hankali ta ajiye takardun tana jin wani salamamen ciwon kai na son salamo mata a irin wannan lokacin
Wacece ita? Waye babanta? Ko tace shin babanta ya san da zamanta? Mahaifiyarta kanta daria take yiwa furucinta, shin ko dai zata kare a mahaukaciyar ne? Ina zata shiga da baban burin nan dake cikin zuciyarta?
...........................
Talatainin dare ne , a irin wannan lokacin da yawancin bayi ke baci wasun sunna bauta wa ubangijinsu, da yawan passinger dake cikin ROYAL AIR Plane na baban birnin LONDRE barci suke, kadan daga cikinsu ne suke farke suma sun kasance wa'inda basa iya barci idan sun tsinci kansu a cikin jirgi komai tsayin tafia.
Ya d'auko su daga DUBAI international airport, daga baban birnin Dubai tun karfe Shida na yama sun dauki tsayin awa takwas da minti hamsin da hudu kennan yana tuki ba tare da sun tsaya a wani garin ba cikin amincin Allah ya ringa rage gudu a lokacin da service na duban yannayin garin da zai iya sauka suka bashi tabacin yana iya sauka lafia domin babu gagarumin hadarin dake iya hadasa muguwar iskar dake iya kayar da jirgi ta hanyar hanna masa ganninsa ne ya samu ya yi ta zagaye a tsakanin Airport din Londres Heathrow har sai da ya samu confirmation din yana iya dira kafin ya koma daidai hanyar da zai dira saman doguwar kwaltar shafafiya mai haske wace ta dauki hasken wutacen dake zagaye
A hankali tayoyin jirgin suka fito daga maboyarsu suka yi wata dira jib mai nauyi kafin su falfala da gudun da tamkar ba zasu taba tsayawa ba.
Ba kowa a hanyar, ba wani a tsakar hanyar tun yana gudu sosai har ya dawo ya rage sosai kafin yake kara ragewa cikin nutsuwa ya idasa baban wajen da ya dace ya parker.
Zuwa yanzu motoci ne biyu a gaban jirgin dake nishi da masu jansu a ciki sunna sanye da cask a kunnayensu.
Cike da kulawa wanda ke tafia a hankali a tsakanin motocin cikin yaren turanci ya kuma maimaita tambaya ga matukin jirgin, sai dai still bai samu amsa ba hakan ya saka shi cike da yar damuwar jin shirunsa ya tabo cen manyan dake gaban computer sunna biye da dukan motsin jirgin ya sanar da su cewar matukin jirgin har yanzu bai basu amsa ba.
Amsar da aka bashi da sunnan wanda ke jan jirgin ya saka shi gyada kansa a hankali ya ci gaba da yi masa nuni yana ta jest da hannayensa da kafafuwansa da gudu gudunsa su kuwa masu tuka moyar suka zagaya gefe da gefe aman nesa da jirgin sosai sunna ta biye da dukan takunsa har suka karaso wajen da zai tsaya kafin ya samu ya tsaya a wajen tsayuwarsa.
Ya dauki yan mintuna kafin kofarsa ta bude, kamar da minti biyar mutane suka fara fitowa HOTTEST na tsaye a bakin hanya sunna masu barka da sauka da fatan hutar da gajiya lafia ta yaren Inglish sunna kara nunawa mutun hanya sannan wasunsu na kara duba wajen ajiyar kaya na cikin jirgi da waje zama idan wani bai manta wani abin nasa ba.
Sai bayan kowa ya gama fita sannan wasu yan sharsharun mata biyu suka sauko cikin shiga mai kyau duda ba shiga ce irin ta y'ayan musulmai ba aman dogayem wandunansu da rigunnansu basu dame su ta yadda zasu hanna su tafia ko su hanna su walawa ba.
Wani irin tukuki ne ya taso mata mai nauyi ya dane gaban kirjinta, a hankali ta lumshe idannuwanta cike da takaicin halayan *PRINCE*.
A hankali ta jingina da jikin doguwar farar motar dake nishi a parker, da sauri wasu tsala tsalan yan mata maratsa kiba masu shiga iri daya sket marar tsayi sosai da kuma fararan rigunna suka shiga bata kulawa ta musaman ta tambayarta ko zata koma ciki ne ta huta idan ta gaji da tsayuwar?
Kai kawai ta iya dan girgiza masu kafin ta ci gaba da hangen hanyar da yake iya fitowa.
A kala sun dauki minti arba'in a wajen nan tun sunna saka ran fitowarsa har aka bude mata ta koma ciki ta zauna tana sauke ajiyar zuciya tamkar wace ta yi tsere.
A nutse yake dano kansa kafin ya shiga hada tafiarsa sannan ya idasa bayana.
Ya rab, Barakhallah masha Allah, Lalle halita mai kyau akoyta a dunia, kuma du yadda marubuci ya kai da zuzuta kyau ba wai kowane ne ya zarce misali ba, waima da zaka karyata kyau din kai iya ina yawonka ya tsaya?, akoy halitu a duniya akoy kyawawa a duniya kuma ba lallene ka ce ka gama ganninka ba.
*HANJA ABEDEEN* PRINCE din babar kasar Ingla, wanda yake na farko a cikin su ashirin da hudu daga matan har mazan.
HANJA dogo ne ba irin tsayin da ya wuce musali ba, HANJA a fatar jikinsa idan akoy baki to yana wani wajen boye wajen da idannuwana ba zasu hango min ba, domin ko gashin kansa ba baki sidik bane no maroon yannayi yannayin pink haka.
Hanja nada kakarfan jikin da ba zaku fahimci inda na dosa ba sai mun kai ainahin wajen da ya samo yannayinsa, Sanye yake da sutura irin ta Pilots, Pilots dinma masu manyan matsayi, domin yana sanye fararan kayansu ne masu dauke da galoli a kasa da galalin an makala farin azurfar na karfe dake nuni da bayan matsayinsa na GENERAL yana daya daga cikin masu d'aukan ma'aikata a abinda ya shafi jirgin watau cikin jirgin ba wajensa ba.
A nutse yake tafia sai dai yannayin fuskarsa zai bak'a tsoron tunkararsa
Tunda ya fito ya sauko d'in suke gaishe shi, bai kula kowa ba sai da ya karasa kusan farar motar nan ya bud'e bayan ya saka k'afarsa ta dama ya zauna da kyau yana kwonce abin dake hannunsa a d'aure wanda ke nuni da yannayin bugun zuciyarsa da kuma zafin jikinsa ya ajiye sannan ya saka hannunsa na dama a hankali yana barbaza gashin kansa kafin ya dan saci kallonta sai kuma cen k'asan mak'oshi cikin yaren turanci ya ce" Ina take (Where is she)?"
Ajiyar zuciya ta sauke cike da tashin hankalin irin yadda ko a kwalar rigarsa kafin ta bud'i bakinta kamar wace zata balbaleshi da fad'a sai dai abin mamakin ta sanyayar da muryarta sosai ta k'ara tausasa kalamanta ta shiga fad'in "...
*Masha'Allah*
11/14/21, 12:43 PM - Allah Akbar: 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
4锔忊儯
"Barka da sauka Londre"
Bai amsa gaisuwarta ba sai fitar da dayar kafar tasa ya yi ya fice a motar gaba dayansa
Da sauri ta raka shi da kallo tana kallonsa ta ga an bude wata bak'ar mota kirin da ita kirar kampannin Bintley Limozine
Bai kuma kallon kowa ba aka ja su a cikin motar tare da yan matan nan biyu da suka fito daga cikin jirgin
Wannan karron kasa rike abinda ke zuciyarta ta yi a hankali ta hade kanta da jikin kujerar bayan sun taso ita daya kwal a bayan sai masu tsaronta a gaba wasu a wasu motocin da gayar da suka zo dan tarbarsa sula juya palas ta hade kanta ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya tana girgiza kanta, sam bata san me ya dauki kansa ba aman ba komai zata je ga Sarki ta sanar masa komai shi ya isa da shi ai
Wani irin falelen plt
Wajen ba a wani zagaye yake ba sai shukoki da suka zagaye shi
Wani bangare guda daya ne tal mai dauke gls wajen kamar an yi shi a tsakiyar filin ne wanda yake da kofar shiga daya tal
Fitowa ya yi ko matan bai yiwa magana ba bale wanda ya tuko shi ya yi ciki cikin nutsuwa
Yar yatsarsa ya dora a kofar shigar wajen wani farin madubin da na yi tunanin na kallon kai ne, sai dai yana dorawa wajen ya bude bayan ya gama scanning ya gane mai wajen ne ya bashi damar shiga
Da sauri masu biye da shi din du suka shige sai iya masu escorted dinsan ne suka ja suka tsaitsaya sunna kara expect din place din
Dan ja ya yi ya tsaya a lokacin da ya ga yan matan nan biye suke da shi
A nutse ya juyo yana kallonsu sai da ya bale babar rigar dake saman jikinsa yana kallonsu da yar yatsarsa ya masu nuni mai hade da tambayar da suka gane ba tare da ya yi masu magana ba
Kallon kallo suka shiga yiwa junna su biyun, du da irin tarin jin haushin junna da suke ji aman basa taba bari su nuna a gabansa
A hankali dayar cikin sanyi ta dan daga kafarta da nufin karasawa inda yake tsaye muryarta na dan rawa ta ce" My Prince, ka gama da ni ne?"
Dayar kuwa bata matsa din ba aman kuma ta tsura masa ido tana karantarsa, domin ita din ta kasance baba yar manya kuma mai tarin ilimi, tana tare da shi ne dan nata manufar ba dan wani abin daban ba
A hankali ya motsa labansa cen kasa ya ce" Ku tafi ba zan yi fly ba "
Kallon junna suka kuma yi a lokacin da ya juya ya nufi babar kofar da zai fita gaba dayansa a falon nan
Murmushi ta yi ta juya ta nufi waje dayarma ta bita dan sun gama sannin tunda ya ce su tafi hakan na nufin ya gama morar ganga zai yarda kwalonta ne
Da dan sauri sauri ya karasa wakeken kejin, hankalinsa a tashe ya karasa wajen da take kwonce
Cike da tausayawa y kai gwuiwarsa kasa ya dora hannunsa a hankali yana shafata yana karawa kafin a sanyaye da yaren turanci ya ce" i'm sorry, yaya jikin ki?"
Da kyau na kara wara idannuwana cike da tsoro da kuma mamaki kafin na fala a guje gefe na labe sosai ina hangen ikon Allah
Wani dankareren kosashen ZAKI ne mai tarin gashi da yannayi na karfi mai dogayen hakora ya je ya rungumunma a irin wannan lokaci da ba dan haram bane mutun ya ci naman mutun ba da wasu sun yanka junnansu sun cinye dan halin rayuwa bale shi da ya zame masa wajibi kuma aikinsa kisa da cinyewa ya bi ya farauta ya dane ya cinye tas bale har an kawo masa a gida? Aman maimakun ya dane ya saka kan wannan bawan Allan da na kasa tantance balarabe ne ko jar fata ne ya masa danysa daya tak ya raba kashin wuyansa da dogon wuyansa da gangar jikinsa ya masa tauna daya ta yada kwala kwalan idannuwansa zasu bultso ya taune su tas ya hadiye kafin ya farwa sauran jikin ya dandantsa cikin nutsuwa ya yi karin safe da shi ya kora da ruwan dake ajiye, sai na ga ya dan jijiga daga inda yake ya mike tsaye kan kafafuwansa kafin ya shiga wani irin jijiga yana cira daga inda yake yana dora jibga jibgan hannayensa masu dauke da tarin gashi a wajen kafadun *HANJA* sannan yana kawo bakinsa dake bude yana shafa masa uban gashin dake wuyansa yana ta karra goga masa
Sai a wannan lokacin na ga yana ta sakin murmushi kamar ya samu dan uwansa ya bashi kyakyawab runguma yana karra shafa shi a sanyaye ya ce" Nima na yi farin cikin ganninki, na damu da rashin lafiarki sosai, ina fatan yanzun da sauki my royal freind?"
Kamar wace take jin yarensa haka ta sake shi ta yi baya baya tana tafia cike da kasaita da karfi da jin kai da wata irin isa wace daga inda nake a labe nake jin takun a cikin kirjina haka kuma zuciata ke yin dak dak dak domin wannan zaki ko nace zakayar ba karama bace , tabas da ake cewa yannayin girman kashinsu da zakin kiwo na gidan zoo da na jeji sakaku ba daya bane sai yau na yarda, tsarin kwalin dake cikin idannuwansu kadai abin shagala da kallo ne, sai da ta yi nesa nesa kadan da shi kafin ta wani irin girgiza sannan ta durfafoshi a gujen da ya saka na nemi sakin mutumen daga tsaye, aradu ban taba yarda cewar akoy masu wasa da rayukansu ba sai yau, tsaye yake a gabanta jama'ar rasululahi (S.A.W), ba tsoro, ba firgici, ba alamun zai juya ya fita a guje, baya tsoron kar a je koda mugun sabo ne suka yi da junna a yanzu kwakwaluwarta ta juye tana isowa inda yake ta cire masa kai? Bama wannan ba shin jama'a dama Zaki abin sabo ne? Kai jama'a
Haka ta iso inda yake ta kuma neman dare shi, tagal tagal suka yi da sauri ya iya rike kansa da karfi yana murmushi ya kai hannunsa har kusa da bakinta hakan ya saka na kwalalo idannuwana ina kuma kallonsa kafin ya karra shafa gashinta sosai sannan ya saketa ya shiga tafia hankali kwomce tana gefensa itama tana tafiarta cike da kasaita har suka fito daga wajen da yake rufeta idan zai yi tafia
Wani wajen suka je ya tsaya ya kurawa wani tableau ido, ita kuwa ta shiga dan zagaye shi cike da kasaitarta
Habarsa ya dan dafe ya juyo inda take zagayen nata ya dan dafe kugunsa yana kallonta a hankalin nan dai kamar wanda yake yin rada dan baya so wani ya ji shi ya ce" Kin kyauta kennan? Kin rage cin abinci sosai dan baki da lafia ko? Idan nine kin iya zuwa kina son tayar da ni na ci ko? Zan rama ne"
Ajiyar zuciya ya dan sauke dan hutawa da doguwar maganar da ya yi kafin su ci gaba da tafia, da hannunsa ya ci gaba da nunawa ya ce" I'm tired, u see ko cofee ban sha ba tafia ta tsayin awa takwas dan ina tunaninki "
Ita dai Allah bai bata damar magana ba, aman wani ikon Allah idan ya fara magana har kamar mai dago kai ta kale shi kafin ta ci gaba da tafiarta
A haka suka karasa kusa da bayinsa, abin mamaki a lokacin da ya saka kafarsa ciki sai na ga ta shiga kai kawo a kofar maimakun ta bi shi
Wanka ya yi mai daukan lokaci kamar rana ce bayan yanzun lokacin sallar asuba ne ya gabato, hasken fitilun garin da gidan kansa sai ya saka bawa a cikin tunanin ko dai safia ta waye
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 42