Share this page
taka tsantsan ta yadda zai kasa ganeta koma me dinsa ce a tausashe sannan a mutunce cikin yaren turanci , irin kwararan nan da sai da ta dage ta saurara da kyau kafin ta gane me take fadi ta ce" ki taso mu tafi cen school din" Sai da ta kikifta ido kafin ta karra gyara zamanta tana kallonta ta ki yi mata magana sannan ta ki tashi Karasa shigowa ta yi ta zauna kusa da ita ta karra tausasa kalamanta sosai ta ce" ki yi hakuri zai dawo da wuri, sun tafi saudiya ne da mahaifinsa da mamansa, ya ce mu kula da ke sosai a makarantar ta yadda zaki goge ki iya komai na aikin hostess kin fahimta?" A hankali ta gyada kanta duda bata san wa ake baa hakurin a kansa ba, abinda dai ta sani shine kawai zata bi su, ta je ta koyan, tana kwarewa a maida ita kasar iyayenta dan ba zata zauna a garin nan ba , ta ina zata iya rayuwa da arnawa Da dan sosinta take biye da ita da sauri dan gaba dayanta a tsorace take balema da ta fito waje ta ga garin ya ganta Wata galeliyar mota ce wani soja ya bude suka shiga kafin a ja su a yi gana da su A yanzun kam makarantar da aka zo da ita sai ya zamana tsoron fitar da kafarta waje ya kamata dan tana tsoron ta taka ta saka masu dati Wasu mata ne a tsaye su uku kowace cikin shigar dogon wando da riga da dogon takalmin hils sunna jiran fitowarsu Da mamaki suke kallon Muneerath tun daga sama har kasa kafin su ringa kallon junnansu Babarsu ce da kusan idannuwanta kadai ke nuni da ta dauki shekaru sosai sai ko wuyanta da ya dan nuna shima da turancinta ta ce" ina yarinyar ne?" Wace ta kawota ne ta nuna mata Muneerath dake tsaye ta hade hannayenta a jikinta tana ta waige waige cike da tarin kauyanci da tsoro kafin ta maido dubanta kansu taga suma dukansu ita suke kallo sai du ta tsargu ta tsinci kanta da hade kafafuwanta waje daya kamar mai jin fitsari Kai babar ta dan juyar kafin ta nuna da hannayenta ta ce" Me da me yake bukata gyara a tare da ita?" Wata kyakyawar budurwa ce da cikinta tamkar zai hade da bayanta itama da kula ta ce" da farko dai fatarta, tana da kalar fata mai kyau sai dai hankalin fatar ba a kwonce ba, ba santsi ba alamun laushi, sai fuskarta tana bukatar gyaran da zai cire mata wannan fari farin abin na hancinta da wajen idannuwanta, tana da lebe masu kyau sai dai basu da laushi, gashin dake kwonce a kusan kunnayenta sun nunna yana da kyau gyara ne yake so, tana dauke da manyan bombom dan suke da bukatar kara rike kansu, sai matsalar tumbinta da dole a yi aiki kansa, sai mu dawo kan gwuiwar hannayenta da tafin hannayenta da faratunnanta sai wajen farin idannuwanta da yake da duhun haske yana da bukatar ya samu gyara, ni dai iya abinda na gani kennan" Dubanta ta maida kan dayar itama ta matso sosai kusa da Muneerath da ta saki baki da hanci tana kallonsu da mamakin wai du ita ce ake zancenta ko wa? Ai kam zata masu barin mahaukaciya a wajen nan idan suka nuna ita din kazama ce, yo kaf gidansuma waye yake wanka biyu in ba ita ba? Dayar ta ce" tana da matsalar tafia da dogon takalmi idan kun kula kafafuwanta sunna da matsala" Daga su har Muneerath din sai suka kai dubansu kan kafafuwan nata, da sauri ta dago gannin matar ta amshi waya tana maganar ttana son gannin docter kafin ta kale su ta ce" Gimbiya Aleesa ce ta ce ta zama perfect......dan haka zata zama perfect " Tana gama fada ta yi gab Daga wannan lokacin Muneerath ta shigo sabuwar rayuwa, Watau tana gannin rayuwa mai sunna rayuwa Airfa kala daban daban ta yau da kulun , ga wankan da ake darza mata ita kanta ta san da ace faa na kodewa dan wanka da tata ta gama kodewa , Hakowaranta kansu sai da aka sake koya mata yadda zata wanke su Abinda ya fi bata takaici irin yadda ake koya mata magana, yo in ba iskanci ba yaya ake so ta zama ne wai? Duwawunta kuwa haka za鈥檃 daura masu wani abu kamar igiya a tsayar da ita a kunna ya ringa rawa a jikinta Baban bakin cikinta cin abinta lokaci gare shi, kuma zaba mata ake, sanan bashi da yawa, tana gama ci ake bata wani hadin su lemun tsami ta sha ba dan dadi ba sai dan wahala Cikin nan nata da take alfahari da shi ne yake lumkewa yana shigewa sanann ana shafa mata abun nankarwa dan kar aje mai fitar da nankarwa ce fatarta ta fitar ta lalata mata fata duda bakin fatarta ba mai gagawar nuna nankarwa bane Yan guli guli din mamanta ne ta ga sunna dan girma duda ba cencen ba aman ta kula kumbura suke ga rigunnan mama kala daban daban a laye da pant dinsu wai du nata ne Abinda ta kasa ganewa shine a haka har yanzun bata dawo yadda babar take so ba dan da sasafe auke fita gudu tare tana karra koya mata karuwancin da ta rasa na uban menene wai du a aikin ne ko meye? A ranar da ta shiga ruwa da su kuwa su kansu sun sarawa iya ruwanta kuma sun shaida koda bata iya komai ba ta iya ruwa Sannu a hankali ta fara shiga kicin Yannayinta ya fara dauka, fatarta ta dauki gyara ta dawo wata irin bakar fata mai masifar kyau din man da maza ke hari, cikinta ya lafe sosai sai duwawunta suka kara budewa suka baje sosai abinsu gwannin kyau da su idan ta tsaya a tsaye daga sama kirarta kamar ta rihana zuwa duwawunta kuwa ta kusan kamo niki minaj sai dai basu yi girman na niki minaj din ba, kalar fatar tata kuwa kamar ta rihana din dan kuwa ta amshi guara ta kuma saje da sanyi ta yi minas da ita Tashin hankalinta bai wuce ko girkin nasarun ta kasa iyawa ba Yi ake a nutse, a rrubuce ake bata, a bayane ake bayana mata aman cikin ikon Allah ko wainar kwai da ta gwada soyawa ita kadai sai da ta kone kurmus tana shawarar ta soyu bata soyu ba! A haka take tare da mutanen nan da suke darajata ko dan wanda ya bada ita, sai kuma uwa uba su din sunna daraja kowa din ne Kusan watanta daya kennan tare da su bata ga kowa nata da ya kawota wajen ba, a yanzu ta fara damuwa da son gannin Sir dan ta tabata shi din zai kaita inda ya daukota ................................................ Gaskiya ne, masu abu da abinsu, A wannan kwanaki HANJA da iyayensa sunn zaga kasashe masu yawan gaske, sun yiwa saudiya shiga biyu kafin su fara shirye shiryen dawowa kasarsu A yau bayan ya dawo daga masalaci ya zame a falon da iyayensa ke zaune ya nemi waje ya zauna cike da gajiya yana kallon mahaifinsa da ya ga ya kura masa ido yana kallonsa Abansa ya yi takwaf takwaf da fuskarsa a sanyaye ya ce" 11/14/21, 12:47 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 2锔忊儯4锔忊儯 Ba edditing fa Sosai yakara kausasa fuskarsa kafin ya ce" ba zata zo inda kuke ba, ba wata bakuwar fuskar da zan kawo gidan nan kun ji na fada maku gaba dayanku" Tsuru ta masa da ido tana kallonsa har ya gama saukowa daga saman bed din fuskarsa a hade din nan ya nufi bayi ita kuma ta raka shi da kallo kafin ta cire dubanta ta mike ta nufi wajen suturarsa tana dan cije lebenta na kasa a ranta tana fadin 'ba dai naci kake so na maka ba? Zan maka shi har sai ka ji kamar zaka saka kuka domin yarinyar nan ni shaida ce bata da kowa a nan, sannan irin damuwar da na gani karara a kwonce a fuskarta sai na maye mata da farin ciki a kansa' Kaya ta ciro masa bakaken swttt da abubuwan hadinsa harta da agogo sai da ta ciro ta ajiye kafin ta tafi falonsa ta zauna ta gyara zamanta sosai tana jiransa da karamar waya a hannunta ta kirayi yarinyarta da take wajenta ta shaida mata abubuwan da take so sannan ta dora zaman Ta dauki a kadan awa guda har bayan kanta ya fara sara mata kamar yadda ya saba yi mata sukan nan tana zamanta sai ya soketa ta dafe kadan ta lumshe idannuwanta tana tofa adu'a ya fito daga dakinsa A hankali ya karasa ya duka gabanta yana kallon fuskarta kafin ya saka hannunsa ya shafa gefen fuskar tata a hankali ya ce" Me yake damun Mah? " Mah ta sauke ajiyar zuciya ta cire hannunta tana kallonsa ta dan girgiza kanta a sanyaye ta ce" ka dauko min ita, ina so ta zo kusa da ni please" Kansa ya kawar ya kama hannayenta ya juyo yana facing dinta a hankali kamar baya son magana ya ce" Duniya ta rikice, mugayen mutane sun cikata da muguntarsu a cikin zukatansu, ku....kune duniyata, kune farin cikina, sai yaushe zaku gane cewa bana tunanin idan har zan iya aikatuwa idan bakwa gefena? U see da hannuna zan shaketa sai ta daina motsi koda musu ta yi da ke bale ta ilata min ke, Mah koda tokarta ce sai na kona na kuma konawa na kuma konawa, na shiketa na busarta na kuma jiketa na zuba a kwata!, Ba zan iya kwatanta maki tsorona da dukan halitar da zata rabeki bayana da abuina, kin ga ko wannan da kike riko mai kallon tsiyar nan ba wani yarda na yi da ita ba!" Murmushi ta yi cike da kaunarsa a kasan zuciyarta inda fuskarta ta bayanar da shaukin kauna irin na uwa tana tuna yarintarsa da irin yadda ko bata da lafia yake adu'ar Allah ya sauke mata ya dora masa,watau wata irin shakuwa ce ta ban mamaki a tare da su, ko mamansa da tana raye da iyakar shakuwar nan kennan A hankali ta shafa itama wajen sajensa a sanyaye ta ce" Burina ka zama mai tausayi, ka zama mai taimaki, ban ki ba duniya yanzun ta zama abin tsoro sosai, aman kuma a cikinta akoy na kirki cike fall, hakama akoy innocent cike da ita, Son akoy marayun da suke da iyaye, akoy bayin Allahn da suke manyan mutane ne a boye abinda ya hanna su bayana just dan taimako ne na manyan da suke sama da su, Son ka faranta min dan Allah" Idannuwansa ya lumshe yana kallonta a hankali ya kawo hannayenta wajen bakinsa ya lumshe idannuwansa ya manna mata kiss a bayan hannayenta sannan ya dago da dan tsugunnin da ya yi a gabanta ya mana mata wani kis din a saman goshinta a hankali ya ce" I love u " A bayane ita kuwa ta dafe saman gashin kansa ta shiga kwararo masa adu'o'in tsari kafin ta karashe da furta masa kalmar Allah ya yi masa albarka sannan ta mike ya riko hannunta sunna tafe a hankali har suka fito waje kafin ya yi gaba tana daga masa hannu ya je wajen motar da aka bude masa ya shiga sauranma du auka shishige da gudu suka tada suka kama hanyar tafe tafen da zai yi ciki harda zuwa ya ga Zakanyarsa. Da dan sauri ta koma bangaren mijinta, tana zuwa ta zauna kusa da shi tana murmushi ta ce" Idan ya zo da ita Khalb sai ka soya min kwon nan yau" Murmushi ya yi mata yana daga kafadarsa yana yatsine baki na maganin da ta matsa masa ya sha wanda a saudiya aka yi ta saukar alkur'ani aka hada da wasu ganyayaki nasu wai ya ringa sha in sha Allah sai dai idan ciwonsa ba na warkewa bane, idan dai na warkewa ne zai warke ne cikin sauki a lokacin da shi kansa bai tsamata ba, watau sun nuna masa cewar ayar Allah ita ce magani, babuaganin da ya kaita karfi hakan ya sa yake sha aman ba wai dan ya saka a ransa wai zai warke ba, wani warkewa kuma? Ai warkewa mai gaba daya na tunkaro shi a kowani second wanda ya tabata yana yinta an kare, haka kulun ta dafa masa su percil, su sasake sasakenta ita dai mijinta kar ya barta, sai da ya yatsina fuskarsa kafin ya ce" Wanene zai daukota? Kin manta irin tsanarsa da mutun bako? Bama zai daukota ba" Kanta ta dora a gefen kafadarsa jikinta a sanyaye ta ce" ni kuwa da sai na masa kuka, kuma na je na daukota da kaina" Murmushi ya kuma yi yana girgiza kansa a hankali ya ce" Noor, ba zaki zubar da kwalarki na ko na wasa ne idan dai ina raye " Shiru ta masa dan bata so a yi nisa da maganar idan yana rayen nan domin ba abinda ya gagareshi yanzun ya zurmiyar da ita a kogin tunanin rayuwa babu shi .................................................. Idan aka ce nutsuwa, ana nufin nutsuwa,barci ne take na nutsuwa, cikin nutsuwa, bayan tarin gajiyar da ta kwasa na yau Tabas kasashen waje sun yi nisa irin nisan nan da hankali ba zai dauka ba sai idan ido ne ya gani Na sha gani a cikin familly Kardashian da cikin emission kala daban daban na irin yadda mutun ke sawaya lokaci daya watau a cikin sati daya idan aka fara bashi kulawar idan ka ganshi zai zama bako a wajenka har sai ka kuma tambayar kanka da kokowa da tunaninka kafin ka tirsasawa zuciyarka yarda cewa shine ba Girman jikinka na iya ragewa ya koma sakwaikwai , tumbi na iya shafewa ya komai luwaiwai ba tare da ya bar tarin fata ba ko nankarwa irin na mai jiki idan ya rame ba domin akoy mayuka da kuma sport din da zai ja maka fatarka sosai ta janyu ta yi kyau sosai Shi ba shirurgi ba, ba kuma tsafi ba, reality ne wanda sai ka bi tashohinsu zaka ringa gani ko idan ka je inda suke zaka karda du girman jikinka yana iya raguwa ya daidaita ya yi kyau, haka kuma du tumbinka yana iya shafewa ya dauki kala, komai girman duwawunka idan baka so akoy irin aport din da zaka yi su ragu da irin kalar cimar da za'a doraka a kai ......watau zaka cenza iya cenzawa sai dai halayenka su shaida ko wanene kai domin hausawa na cewa idan ka rabu da mutun tambaya idan ya yi arziki aman halaya na nan........... Shi ne ya faru da rayuwar MUNEERATH a tsayin sati uku, wanda ta amshi wani irin kulawa tun daga yannayin jikinta da sam ta ki a rage mata duwawunta ta nuna a kan me a barta da halitar da Allah ya mata, sai dai tumbin nan nata gaba dayansa ya lafe ya shafe ya tafi duniyar da takan kamuwa da mamaki ta ringa shafarsa tana juyawa dan son gannin ina ya je ya lafe, domin ko ta ci baya nuna kansa ya rigaya ya amshi gyara mai yiwuwa shi da ya tasa sai ko yaro ya shiga, Fatar jikinta kuwa ta hadiyi na hadiya ta shafa na shafawa, bakin nan nata ya zama baki na mararin farar fata ko wacece, bakin nan ya zama baki mai birge kowa, fatarta ta yi wani irin laushi na mamaki domin tun AC na sakata mura har ya yi hakuri ya ba kansa lafia ya zubawa sarautar Allah ido dan kuwa duda kasancewar garin garine mai sanyi shi yasa ba ko'ina suke da AC ba yawancin guraren sunna dauke ne d chauffage, aman haka Take kwonciyarta a cikin sanyin nan ko ta yi kai kawonta a cikinsa ba tare da tana makuarkyatar sanyi ba, har wani sa'in takan tambayi kanta to yaya aka yi take jin tsoron sanyi a da a yanzu kuma bata tsoro? Gashin kanta ya gama bayanar da bakinsa da tsayinsa da laushinsa, ita kanta a yanzun takan saki murmushi tana hangota a Niger idan aka mayar da ita gata ga Oga ga mamansu ga yan gidansu uwa uba idan ta zagaya ta tabata a yanzu dogari sai ya yi kuka kafin ta yarda da maganarsu ita da shi! (Ciwo na dogari yana nan dan har yau har gobe tana kan bakanta) Ga sir a gefe guda ya zamto mata aboki, aminin shawara a ganninta, inda shi kuwa ya zuba mata ido yana son a hankali ya cire mata maganar wani wai dogari , domin ya kwatanta mata cewar wannan mafarki ne, inda ta shaida masa ko kasancewarta A wanann waje a matsayin hostess mafarkinta ne ya tabata, ta tabata wata rana zata ganta gata ga dogari a matsayin mata da miji..............watau dai su din zasu taka matsayi na yan uwan sarki, wanna. Daraja tana so ta zamo gaske dan ta san sarki ko dansa sun fi karfin yar oga..........sunna zantawa da shi ne ta yanar gizo gizo domin har yanzu yana nan a hannun HANJA bai sake shi ba A zabure ta farka daga barcin da take a lokacin da karaurawar da ake tashinta a barci ta dauki kuka kirrrrrrrrr A firgice cike da mamaki ta kai dubanta kan agogon dakin dan gannin hala har lokacin tafia gudun yama ne ya yi bata tashi na bayan ta kasance mai tashi a kan lokaci? Maganar dake shiga kunnenta ya sakata yin kasakai tana sauraro kafin ta sauko lalausan kafafuwanta ta zura cikin takalmin dake kusa da bed dinta ta saka hannunta tana kunce hular kanta sannan ta cire dan Siririn ribom dinta ta yamutsa gashin kanta a sanyaye ta ce" Prince kuma sir? Kin fa ganni fa cikin lokacin barcina ne fa ko so kike muna girki ina barci kuma ki ce laifina ne?" Murmushi ta yi daga zaunen da take tana kallon yadfa take turo baki ta ce" Yan mata, ki rufa mana asiri ki tashi ki je ki kimtsa kamki cikin minti goma ki fito domin nan d aminti talatin zai karaso, ki kula idan har wani abu ya kauce ni da kaina yana iya korata a nan, ko so kike a kore ni?" Kanta ta dago ta kai wajen camerar ta dan tsura ido kafin ta mike ta ja tawul ta nufi bayin Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta bi bayanta da kallo ta dan dafe gaban goshinta ta kali ta kusa da ita da ta ce" Banan tashin hankalina irin abinda zai faru a kan maganar girkinta da kuma kiyawa da ta yi a taba mata hips dinta, ki duba ki ga a da bai fito sosai ba domin a da tana da tumbi, a yanzu kuwa da tumbin ya shafe kina gannin yadda gaba daya ya gama bayana, bombom dinta ba zai boyu ba koda wandon jine ta saka , ina tsoron sanadiyar wadinnan matsalolin biyu yau ya wanke mu tas" Mai bima babar tasu ce ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Madame, me yasa wai kika ki taba mata duwawun nan nata kika biye mata aka bar mata su a haka bayan ga yadda suke da girma da fadi?" Dan murmushi ta yi ta ce" nan fa burinku ku samu duwawu koda rabin rabin nata ne, duda na san ba maganar ra'ayi bane aman wannan wajen fa waje ne da kowa da yadda yake son gannin nasa sai idan bai samu ba" Dan murmushi ta yi ta ce" ita bama wannan ne damuwarta ba, baki ga abinda ta ce ba, cewa ta yi kar izgilin ya yi yawa a bara mata halitarta haka ita kamta sun dameta aman bata so a rage su dan kamar za'a yi izgili da yawa wai" Mikewa madame jocyline din ta yi tana harhada takardu da sauri sauri ta ce" Wani lokacin haka musulmai suke, idan zasu yi abu sai ki ji sunna cewa kar su sabawa Allahn su, ban san me hakan yake nufi ba, aman ita da ta hanna a taba mata bayanta ya hauta sosai, wannan bayan nata du nimiji mai lafia zai motsa idan ya kalla , dan dai shi sir din ne ya zama ba wannan ne a gabansa ba, ni dai fatana kar a kore ni yau, mu tafi maza maza mu gama shirya dakin tuhumar, ban san me ta aikata da za'a tuhumeta ba" 11/14/21, 12:48 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 *DUTSE* 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍 RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10* 馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔 https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 2锔忊儯5锔忊儯 A gagauce ta gama shiryawa, ba kwaliya a fuskarta ko dis domin ba kwali aka koya mata sakawa ba , haka kuma lebunan nata bata shafa masu jan baki ko man lebe ba, abinda ta yi shine saka pant da doguwar riga har kasa wace ta dame mata kirjinta da ya dan yi tudu abinsa itama ta yi mama irin na mata Rigar kalar orang ce, aman mai duhu bata da kwaliyar komai a jikinta sannan ta auduga ce watau coton hakan ya sa ta lafe mata a jikinta ta bi jikinta har kusan duwawunta kafin ta dan saki kadan ta yi cen kasa Takalmi ta ciro baki sidik kafa ciki sannan ba mai tsini bane mai dan tudu ne dai kasansa na kwalba Sai turare da ta wanke jikinta da shi a nutse ta juya ta ajiye laptoo dinta da ta daidaita ta dauki hoto da shi ta ajiye ta juya bayan ta dora bakin dan kwali siriri a kanta hankali kwonce ta nufi wajen da aka ce mata ta je Kicibis suka yi da daya daga cikin masu basu horo ta damko hannunta bayan ta wara ido gannin riga da ta saka tamkar an zana abinda ba'a so ya fito din ya fito radau da shi gaba dayanta bombe ce yarinyar ko mace tana birgewa bale maza aman sun tabata yau sir sai ya ci ubansu baki dayansu Ita kanta madame ido ta zarro, da sauri ta kalli wajen da camera ke hasko motocinsa sunna shigowa , bata san lokacin da ta dora hannu daya saman kanta ba ta ce" Yanzu du a cikin kayanki kika rasa wanda zaki sa sai wannan rigar dake maki kyau?" Rigar ta bi da kallo ta kalli madame din , gani ta yi kaf a kayan wannan itace ta fi sutura kuma suke nuna a kan me ta saka ta? Ita ba zata saka wadinnan dingilalun sket din ba ta fito ko kuma ta saka wandunnan nan nasu matsatsu sun matse mata cinya idan ta wuce mazan cen sunna rakata da kalo haka kawai ba, ita da a niger ne wannan rigarma ba zata saka ba dan ta san sai an ci uwata da ihu rigar fa tsaga gareta fa har kusa da cinya fa! Kai ita ba yar duniya bace walahi Dan bakinta kawai ta turo tana kifta ido tana kallonta ta ki yin magana aman a kasan zuciyarta fadi take koma uban waye princ din nan ya yi ya gama ta koma ta maida barcinta Hannunta madame ta kama da sauri ta yi cikin dakin da ita Dakin ta bi da kallo, yana fitar da sansanyan kamshin da bata taba jin irinsa a duniyarta ba Table ne madaidaici a ajiye a tsakiyan kujeru biyu lafiyayu da su, sai katon madubi da kuma wani abu dake fitar da amon murya waje sai kuma camera har hudu kusurwa kusurwa da wasu abubuwan da bata san ko na meye ba ita dai, sai mutumen nata watau sanyi karara da dakin yake yi Wajen da zata zauna ta nuna mata ta tsaya a gabanta ta ce" Muneerah, ki saurara da

Chapter 13 of 42