kadan kadan, bana fada, bana sata ko daya walahi"
Stilll dai kallonta yake yadda take kai kawo da doguwar rigarta tun ta ranar ita ce bata cenza ba ta juyo ta yi takwaf takwaf da fuskarta ta ce" Matsalar daya ce ban iya girki ba, na yi na yi na kasa iyawa, ko tea ban iya hadawa ba, dan annabi kar ku koreni dan wannan"
Idannuwansa ya lumshe haka kawai yarinyar ke kashe shi, motsinta komanta ke haukata shi, a hankali ya dan karra bubuga byronsa yana son aro nutsuwa dan bai dace ya jima a haka da ita ba aman kwata kwata baya son motsawa ko nan da nan ya ce"
A sha 8knd lafia na people馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ
11/14/21, 12:45 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
1锔忊儯5锔忊儯
*GODIYA TA TABATA GA ALLAH SUBAHANAHU WATA'ALA, DUBUN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI YA TABATA A GAREKU MUTANEN KWARAI DA ALLAH YA HADA MU DA SU BAMU SAN JUNNA BA AMAN MUKE KAMANTA KYAUTATAWA JUNNA TA HANYAR ALKHAIRAI DA DAMA, JINJINA A GARE KU MUTANEN GIDAN DUTSE ........A DUNIYA DU WANDA YA TASHI YA YABA MAKA DA ADU'A MASOYINKA NE, KU HARDA KOKARI TA HANYAR MOTSA ACCT DINKU KUKAI MANA KYAUTA KUKA CE A SAKA KATI A YI DATA, TO BARA KU JI MAMAN JARIRI TA CE KAZI ZAMU CI ALKUR'AN馃槄......, KUN GANE, MUN GODE, BAMU DA BAKIN GODIYA SAI ADU'A A GARE KU, ALLAH YA KARRA MAKU BUDI YA KARRA RUFA ASIRI DUNIYA DA KIYAMA DA WA'INDA SUKA SAMU DAMAR SAKAWA DA WA'INDA SUKE DA NIYAR SAKAWAR ALLAHNE BAI YI BA, DA WA'INDA SUKA LULUBE MU DA ADU'O'I NA FATAN ALKHAIRI BAMU DA BAKIN GODIYA SAI DAI MU CE DA KU ALLAH YA KARRA RUFA MAKU ASIRI DUNIYA DA KIYAMA AMEN.....MR SPECIALLY AMINENENMU, DA ALEESA DA SUKA JAGORANCI WANNAN CONTRIBUTIONS, DA SISINA MAH SISI, HAJIATA, SISINA SIS BILKISU KANAR DA TA CE SAI AN AMSA AKA KUMA AMSAR DAN TA ISA, SAI MARUBUTAN DA SUKA NUNA FARIN CIKINSU HAR SUMA SUKA ZUBA DAN KARRIN KWARIN GWUIWA DA TAYA MU MURNA, DA MAS7 HALIN DATAKON BAYIN ALLAH DA SUKA ZUBA SUKA CE A BOYE.....ALLAHU YA BARMU TARE, YA SA SOYAYAR DA MEKE YIWA JUNNA DOMIN ALLAH CE WACE ZAMU SAMU KYAKYAWAN SAKAMAKON A RANAR KIYAMA AMEN....... DAGA BAKIN MAMAN JARIRINA WARAI SAMIRA HARUN...DA NI SAJIDA KULEY DAN BUZUWA MUNNA MASU YI MAKU FATAN ALKHAIRI DA ADU'A TA DARAJA DA FATAN GAMAWA DA DUNIYA LAFIA AMEN*
Sosai ya ari jarumta dan ya iya tsare dukkan yannayin da zai nuna mata da al'amarinta na neman saka shi a hali na tunani ya ce" Zamu koya maki a nan"
Ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ta karra rage muryarta sosai ta ce" Ka ga ita wannan din me yasa ta cika fada? Ni kuma tunda na ganta da sket a tsage uwa karuwa na ji bana sonta"
Dan gimshewa ya yi ya yi gyaran murya ya karra hade fuskarsa sosai ya ce" Yanzun na gama ce maki dole ki darajata, kina so mu fitar da ke a nan ne? "
A hankali take girgiza kanta ta matsa ta yi tsaye tana kallonsa
Mikewa ya yi yana sauke ajiyar zuciya a boye kafin ya juya ya bude ya mata umarnin ta shigo
Tunda ta shigo take son gannin wani abin da zata ce Muneerath ta mata aman bata ga komai ba, hasalima tunda ta yi tsaye a gabanta da yaren freinch tana yi tana jefo turanci a ciki tana mata bayanan dukan abinda ya zama wajibi ta kiyaya kanta a sade tana gyada mata kai cike da ladabi har sai da ta gama sannan ta bata minti talatin dan ta je ta kimtsa jikinta ta dawo
Kayan ta dauka cike da ladabi ta tambayi inda zata je din?
Shi dai yana jingine da garun yana kallonta, nan ta yi gaba ta ce ta biyota
Sai da ta dan dago ta saci kallonsa kafin ta bi bayanta jikinta a mace aman a kasan zuciyarta cike take da yannayi biyu masu karfin gaske
Farin ciki da murnar sabon al'amarin da ya sameta sai kuma yannayi na rashin jin dadi na irin yadda iyayenta suka banzatar da ita, aman kuma idan ta tuna ta fara taka matakin samun dogari sai kawai ta kawar da kai ga dukan damuwarta ta fawalawa Allah komai
A haka ta sadata da dakin da zai kasance nata har barinta a gidan baki daya
Dakin dauke yake da bed daya madaidaici, sai wrdrb da wani irin sif dauke da kayan kwaliya bitjik, sai madubi tafkeken gaske wanda zaka iya kallon kanka a ciki
Dubanta ta maida wajen bayin a hankali ta karasa ta shige da adu'ar shiga bayi a bakinta
Tsayawa ta yi tana kallon yadda bayin ya hade, ba wani mai girman a zo a gani bane aman irin tsarin da aka bashi ya isa ya birgeta duba da nasu bayin na gidansu yadda yake
A bayin kama daga abin wanke masai, da su Hypo da clean, da tsintsiyar wanke bayi, da soson wanka da broch da maclean , da sabulun wanka da na wanke gashi, da abin wanke kafa da abin aske gashi, da su abin jona turaran ruwa da na wuta kusa da soket dinsu
Komai a kilace yake harta da tawul kwaya biyu a ninke suke
A hankali ta idasa shiga tana karra bin ko'ina da kallo kafin ta gyara tsayuwarta ta kai dubanta wajen kayan wanke bayin, ba wani dati gareshi ba, aman haka ta maida hankali da gagawa ta shiga wankinsa, tana yi ta jona abin turaran ruwan sannan ta ci gaba da aikinta
Sai da ta gama tas sannan ta dauko tawul din masu dan girma ne dan zasu iya kawo mata cinyarta idan daurin kirji zata yi da su
Su dinma wanke su ta yi tas da hannunta bata saka su a washing machine ba ta shanya su a igiyar da ta gani duda ta cika da tunanin ta yaya zasu bushe a haka duba da nauyinsu da kuma yannayin wajen a dan matse ba iska bale rana
Daidai da pant dinta sai da ta wanke shi da rigar da ta cire tas sannan ta zuba ruwa masu zafi a bokicin ta dauki soson wanka sabo ta saka shi a ciki, harta da brush din wankin bakinta da macaji sai da ta dafa su da ruwan zafi kafin a gagauce ta yi wanka ta wanke bakinta sosai kamar wace zata dawo fara haka ya dirji fatar jikinta sannan ta ringa sanda dan fitowa domin ta wanke komai nata ta shanya bata sanye da komai a jikinta
A hankali ta bude ta leko kanta gashin kanta na digar ruwa ta duduba sosai, gannin hajiar dinkim ta yi waje ya sakata fitowa da sauri tana adu'ar fitowa a bayi a zuciyarta ta nufi kayanta
A gagauce ta saka suturar da aka bata cike da mamakin yadda ta rike mata jikinta taf bale wandon shi ya fi kamata du irin fadinsa ya rike mata kugu taf aman kuma na kaushu ne domin jayuwa yake sosai sai dai wata irin kunya ta sakata ja ta tsaya tana karra bin jikin nata da kallo tamkar zata fashe da kuka a bayane ta ce" Anya kuwa zan iya da matsalar fitar da tsiraici? Dama zasu amince min su bani wa'inda suka fi wannan girma da sun taimakeni"
Gashin kanta ta kama ko bushewa bai gama yi ba ta hade shi sosai ta dunkule shi cikin ribom ta masa dauri kamar na huhun goro sannan ta dauki dan kwalinta ta yi jeka ka dawo da shi ta daure kan nata taf kafin ta ringa sauke ajiyar zuciya tana kallon madubi sai kuma da sauri ta kalli agogo
Idannuwanta ta zarro dan ta karra mintunna har ashirin da bakwai a kan wanda aka bata..................................................
11/14/21, 12:46 PM - Allah Akbar: 鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
*DUTSE*
鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍鉀帮笍
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
馃挮鉁 *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽 *[ T.M.N.A]* 鈽 馃摉馃枈锔
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
1锔忊儯6锔忊儯
Da sauri ta saka slifas dinta ta yi waje , da sauri sauri take tafia tana dube dube, sai dai bata ga kowa ba sannan bata jin maganar kowa
Turus ta yi gannin wani gabjejen soja a gabanta , cikin daure fuska ya ce da ita ta biyo bayansa
Sai da ta yi dan jim kafin ta bi bayan nasa cikin sanda dan tana tafe ne tana tunanin idan fa ya juyo ya jibga mata dukan mutuwa? To ita bata ga alamun daria ko fara'a a tare da shi ba ko dai wani ya zage shi?
Sai da suka yi tafia mai nisa kafin su bayana a wajen da take hangen alamun ruwan sweeming pool
Sai a lokacin ta fara jiyo magana kasa kasa ba sama sama ba, sannan ta fara hango ikon Allahn
Gaba dayanta ta idasa bayana a wajen a lokacin da suke tsaitsaye
Zuwanta ya zamanto suma sun juyi sunna kallonta cike da mamakin wacece wannan kuma?
Gaba daya ta sare, gaba daya ta ringa jin wani abu makamancin sagewar gwuiwa da tsoro kasancewarta a gaban yan matan nan, yan matan tamkar wa'inda ke rayuwa a kasar kankara, mulmulmul fatocinsu suke kuma ba bak'ar fata a cikinsu dan ko mai duhunsu banasaria ce a kusa da tata fatar, irin shekin kuma da suke zai nuna maka koda a nan din ana basu gyara cen dama y'ayan hutu ne
A hankali ta kai hannayenta wajen kirjinta ta rungume tana kifta ido tana kallonsu
Atu ce ta yatsina fuska kasa kasa ta ce" Wannan fa mai sanye da irin kayanmu? "
Kafada Humaira ta guada itama ta kuma juyowa tana karra kallon Muneerah
Muneerath kuma kallon suturun jikinsu take, su dukansu sun saka kayan shiga ruwa ne irin yadda ake gwadowa a tv bakaken fatar ko nasaru na sanye da su, watau dai pant da bra, kowace tamkar cikinta zai hade da bayanta , kowace gashin kanta a fili da mai gashin da mai kurkur din kan ya sha gyara sai kyali yake yana karrawa
Kasancewar basu sanma da ita a gidan ba, dan ko ranar da ta diro an mayar da su dakunnansu ne an rurufe su an basu damar yin kalo ko au shiga internet su yi dube dubensu ba'a fada masu dalili ba, su dai an gwada masu cod Red an zanna masu kurtun ba zasu fito ba, hakan ya sa a yanzun da suka ganta sai suka ga kamar daga sama dai? A sanninsu an rufe dauka ai
Matsowa ta yi ko a yanzun dai sket din ne tsagage in ji Muneerath ta tsaya tana fuskantarta ta ce" Ki gabatar da kanki! "
Muneerah ta hadiyi wani yawu mai nauyi a makogwaronta a sanyaye ta ce" ASALAMU ALAIKUM "
su dukansu , baki daya taronsu ta kasa samun wace zata amsata, saima kallon kallo da suka shiga yi sannan su sauke dubayansu a kan AMEERAH wace take uwar gidansu
Gabanta ne ke faduwa da tsoron yannayinsu dan bata saba mu'amala da abokai ko yan makaranta da irin shiga haka ba, sannan ta gama yanke humuncin ba musulmai bane baki dayansu duba da salama ta masu ba wace ta iya amsata saima wani kallo da ta kasa gane na mamakin gannin bak'ar fata ne suke ko na kaskanci?
Murmushi Ameerah ke yi a kasan zuciyarta tana ayanna 'zaki fita ne da kafafunki, dan ko su basu ga irin fatarsu ba, in ba wulakanci irin na PPM (Shugaban kare yancin mutane) ba meye na wani dorawa da dafawa sir a dauke ki rana tsaka ko iliminki bamu tantance ba sai wani tuwon takashi dake rinjayarki ta yaya zaki iya kula da manyan mutane na jirgi? Wani kampani nema yana kallon yan matan nan namu sala sala zai dauke ki? Tun daga yanzu zan shaka maki azaba ta hanyar saka ki a cikin ruwan nan ke kadai!'
"Amen wa alaiki salam" wata siriryar murya ta amsata tana tahowa daga gefe , ita dinma sanye take da pant din da bras din sai dai ita ta saka wani dan kwali ta daura a kugunta ba daga ita sai pant din bane, duda wajen daga su sai su aman ita din tana daure da shi ne
Haka kawai Muneerath ta ji sanyi harda sauke yar ajiyar zuciya tana kallonta, ita dinma ita take kallo kafin itama ta kai dubanta wajen Ameerah su dukansu sunna jiran karrin bayani
Ameerah ta gyara tsayuwarta ta gabatar masu da ita a matsayin daya wace zata kasance a cikinsu ta amshi horo tare da su, sannan sunnanta Muneerah ta yi rashin lafia ne ya sa bata zo a kan lokaci ba
Da tsaftatacen faransanci ta masu bayanin , ba turanci ko daya a ciki hakan ya sa kowace ta gane bayaninta, da yawansu nan suka juya suka shiga harkarsu, su dai basu mata oyoyo ba, kuma basu nuna alamun ta gaje masu waje ba dan kuwa suma zuwa suka yi kuma ko dari aka karro basu da yancin hannawa
Wasun kuwa kawai kallonta suke yannayinta bai masu kama da yar gayu ba, kwata kwata irin shirin nata bai dauke su ba duda suturar dai iri daya ce aman sakatama iyawa ne, ga kuma dauri da ta daure ta matse kai
Hannun da yar budurwar nan ta miko mata tana murmushi ta ce" I'm Saudat Muhammad frm Arlit , nc to meet u Muneerath "
Muneerath ta lumshe idannuwanta kafin ta saki sansanyan murmushi a hankali ta bata hannun itama muryarta cen ciki ta budi baki zata yi magana Ameerah ta ce" Gaishe gaishen ya isa hakanan, oya ki zo ki shiga na ga yadda kika iya ruwa kafin mu je bangaren girki "
Sai da gabanta ya yanke ya fadi da ta ji maganar girki, aman kuma sai bata nuna komai ba, jikinta a mace ta kalli irin shigarsu cike da tunanin wai a haka zata shigan ne itama ko yaya?
Bata dai tambaya ba sai ji da ta yi kafafuwanta na neman makata da kasa domin gaba dayansu dakatawa suka yi da abinda suke yi sunna kallonta, ciki kuwa harda wa'inda suke kai kawo da wani zungureren takalma a kafafuwansu sunna wani irin laudi sannan su dauki tafiyar gagawa duka da takalmin da ta yi imanin idan ta cira kafarta a samansa sai ta karya kugu kafin cinya a gangaro gwabri da tafin kafa, kai harta da wanda ke cikin ruwan sai ta kama karfe kawai ta hau hawa har na uku ta fito sosai itama tana kallonta
Yawu ta hadiya, rana jin kamar ta je ta kama hannayenta ta ce da ita'ki rufan asiri mana na shiga daga ni sai ke?' Sai dai ta kula wannan mata ba mai rufa mata asiri bace
Kasa kasa saudat ta ce" ko baki iya ruwa ba?"
Juyowa Muneerath ta yi da sauri tana kallonta ta kasa magana
A hankali Saudat ta ce" Kar ki ji tsoron kowa a nan, yadda kika zo haka kowace ta zo, idan kina baya baya ko kina boye iyawarki rainaki zasu yi, idan kuwa HOTTESTE suka ga damarki kin bani, dan zaki zamo tamkar yarinhar aikinsu, ki daga kafarki ki shiga ruwan nan idan har kin iya iyo, duda basa daukan wanda bashi da takardar shedar ya yi cour na natation ba, aman duda haka ki nuna masu in ba haka ba harta a wajen Ameerah zaki sha wahala"
Shin ta yaya zata iya sakin jikinta da su, gaba daya jinta take bare a cikinsu tamkar ba halitu irinta ba haka take ganninsu, sun cika mata ido sannan du jinsu take tamkar ba yarenta ba
A hankali ta nufi ruwan da kayan dake jikinta, wanda hakan ya kuma saka Ameerah sakin murmushi a boye dan ta tabata in dai ta iya ruwa ba zata shige shi a haka ba domin babu picsine din da aka basu damar koya ruwa da sutura haka a jikin mutun
Sai da ta lumshe ido ta yi adu'a a kasan zuciyarta kafin ta cire slifas dinta tana kallon ruwan yadda yake kyali harma ana iya hango kasansa dan duka duka 3 mtr ne tsayinsa bayan ita ta koyi ruwa ne a wajen da bawa ba zai fadi zurfin ruwan ba sai wanda ya tara shi a wajen watau Allah
Kai ita gaba dayama sai take tsoron kar a je idan ta shiga ta ji ta buga kai da kasan nan dan kuwa a kusa kusa yake gashi irin shigar da suka koya mata ba ta a taka matatakalar a shiga cikin nutsuwa bane, na a shiga da karfi ne ta yadda za'a dira harta da ruwan sai ya yi karra ba wai kai ba
Kuma kallonsu ta yi ta ga kowace na kallonta da yannayi na son gannin me zata yi, a hankali ta juya wajen AMEERAH da ta tsareta da ido itama tana kallonta bata ce da ita komai ba
Tana kallon Ameerar, ya kasance ruwan na bayanta, ta dago hannunta na hagu a hankali ta kai wajen hancinta a bayane cen kasan makoshinta ta furta" Tawakaltu AllaLah.... "
Basu kawo haka a rayukansu ba, du jira suke ta dawo da sauri ta ce ba zata iya ba tsoro take ya mata zurfi , du jira suke ta fashe da kuka ta ce a taimaka mata kamar yadda da yawa suka yi sai a hankali suka iya shiga ruwan nan dan ya masu zurfi su ba da irinsa suka koyi ruwa ba a 2 mtr ko a 1,5 suka koya sai gashi a lokacin da su duka suke mata kallon bagidajiyar nan a ina zata ga ruwan da zata iya shiga har ta koya , ai iya ruwa a abin wasa bane ta fada cikin makeken ruwan nan ta baya baya bayan ta dan cira kafafunta ta tafi gaba dayanta wanda hakan da ta yi ruwa ya bada wani sauti Bacal.......mai karfin sauraro kafin wajen ya yi shiru domin a lokacin da ta fada ta nutse kasansa dan gannin yaya zurfinsa yake me da me ya dauka a kasansa, shin kamar ruwan tekun da suke shiga ne da kawayenta , shin akoy kifaye da halitu kala daban daban da cikin ruwa a nan ma? Shin ruwan na shiga ido ya hadasa kaikayin ido dan yar lakar dake kasansa idan suka tasheta?.....wannan nutsewa da ta yi dan son gannin ainahin tsayinsa shi ya kayarwa da kowa gaba, a zabure Ameerah ta matso kusa da ruwan lokaci daya tana kallo tana kuma bale botiran gaban rigarta sannan ta danna a bin dake cikin kunnenta da zai sadata da office din Shugaban makarantar a dan tsorace sa furuci rake shaida masa ai yarinyar nan ce ta fada ruwa da baya gashi kusan minti uku bata fito ba bata bayana ba su a hangenta da suke ta yannayin kalan suturar cikinta kamar wace ke kara shigewa kasa ne
Shi dinma a tsorace ya fice da gudu gudu da kuma equipe din dake ciro da mutun daga cikin ruwa suka nufo wajen, a lokacin yan matan du suka yi cirko cirko kowace a tsorace suka jira su ga ta ina za'a ciro da gawarta? Domin su dai a TV suke gannin mutun na iya daukan dan lokaci a kasan ruwa, kai yawancinsuma a cikin irin film din Sirene suke gannin hakan dan basu taba ganni ko ji a labari cewar mutun na iya rike numfashinsa a kasan ruwa ba, ta yaya? Ya rike numfashinsa kuma ya jima a ciki? Wannan sai SARAKAN RUWANMU NA GALGAJIYA..........sai ko wanda ya dauki lokaci mai tsayi yana faman koyon hakan
Sunna zuwa ya ringa jin hankalinsa na neman tashin da zai fara rufe kowa da fada a wajen, a hankali ya ringa rike kansa ta hanyar yin tambayoyi da hannayensa, gannin Ameerah na cire kayanta hakan na nufin tana gaf da fadawa ne
A kausashe ya ce" Kai tsaye kika sakata shiga ruwan bayan kin san baban burinta ta zamo Hottest ne ba zata yi maki gardama na shine kika sakata shiga ba tare da kin duba faiblesse dinta ba , ba tare da kin gaskata idan zata iya shigarsa ba , ba tare da kin kaita ta fara shiga wancen marar zurfin ba?"
Bakinta na rawa cike da tsoron kar dai ta kashe yar mutane ta janyowa kanta hawa media da balakin duniya baki daya da rasa aikinta da rasa komai nata ta budi baki zata yi magana a lokacin ne kuma du sun gama shiryawa dan bin bayanta sun saka abin numfashi a kasan ruwa dan a yanzu mintinta takwas har da yan sekwani a cikinsa sai dan buiiiiil dake dan fitowa jefi jefi a nesa da nesa da ba za'a taba kawowa cewar itace ke iyo da gudun nan ba , Ameerah ta budi bakinta dan ta kare kanta suka ji yan matan sun kwala ihun "Gata nan gata nan"
Da sauri Ameerah ta juyo , haka shima da sauri ya taka ya matsa yana kallon wajen da ta fito din, ta tafi cen fiye da rabin ruwan kuma bayanta suke gani gashin kanta ya warware ribom dinta da dan kwalinta sun zube a cikin ruwan gaba dayansu , bakin gashin kanta ya malalu a cikin ruwan , ruwan ya dago shi haka, kafin ta juyo a hankali tana karra kallon ruwan cike da shinfidadiyar fara'a ta jin dadin jinta kwalim a cikin ruwa, dan tana matukar jin dadin ta jita a cikin ruwa a rayuwarta
A hankali ta ringa binsu da kallo su dinma ita din suke bi da kallo, idan bata manta ba da zata shiga babu wadinnan tarin mutanen, hakan ya sa take kallonsu da mamaki sai kuma jin da take sunna cewa "Da ranta, abin mamaki, da ranta"
Idannuwanta ta kifta ta shafa kanta, sai kuma ta zarro idannuwan nata da dan daga murya ta shiga eaige waige tana karra tatara gashin kanta a bayane ta ce" dan kwalina, Ribom dina...." da yaren hausa kafin ta hango dan kwalin nata ya yi sama sosai kasancewar na raga ne , ribom din ne ya sha ruwa ya yi dan kasa kasa domin baya sama
Tsayin da dan kwalin yake akoy nisa kadan, kafin su ankara ta nufi wajen tana wana kafafuwanta da hannayenta ta kwaratiyar kwarewar iya ruwanta har ta idawa wajensa ta kamo shi ta rufa a saman kanta tana karra kallon mutanen da yar yatsarta ta nuno masu ta dan daga murya ta ce" Minti daya zan dauko ribom dina "
Bata tsaya ta ji amsa ba ta yi kasa abinta, a tare suka kalli junna da ameerah da Sir
Ameerah zata yi magana ya girgiza mata kai ya mata nuni da su je sannan ya salami wa'inda zasu bita cikin ruwan ya rage daga daliban sai ita suma sunna jira ta fito sun yi cirko cirko aman a yannayin fuskarsu yannayi ne na mamaki da sakin fuska
Bata jima irin na dazu ba ta samo abinta ta fito, tana fitowa ta nufo su ta kama katangar tana kallonsu
Wata mai sanye da wani tsohon kashi na punichment wato symbol wanda kana yin hausa za'a rataya maka shi du inda zaka shiga da shi zaka shiga gashi har wani dan wari wari yake na wuya du dan ka daina yin hausa ta duko tana dariya ta rataya mata da yaren freinch ta ce" Muna maki oyoyo a gidan HOTTEST"
Gaba daya suka saka ihun daria wanda sai da ta zabura sai kuma ta kura masu ido ta ga sunna ta daria, a hankali ta ji wani farin ciki da murmushi na wanzuwa yun daga cikin zuciyarta har saman fuskarta
Du zama suka yi a waje ruwan kowace na jefo mata tambayar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 42